Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part A.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da Shadila ta tambayi kanta a cikin zuciyarta cewar ‘Anya kuwa Hailur yana raye a duniya amma bai nemeta ba? Kuma ta kasa baiwa kanta amsa sai idanunta suka kekashe ga barin barci ta kasa koda risinawa a wannan dare haka dai taci gaba da mutsu mutsu akan gadonta taci gaba da tunanin jarumi hailur.
.
A wannan rana dai shadila kwata kwata bata rintsa ba har sai da alfijir ya keto a sannan ne barcin ya saceta ba tare da ta sani ba.
.
Al’amarin su yarima hulkas kuwa lokacin da gari ya waye ya farka yaga mahaifiyarsa na ta barci bata ma da niyyar farkawa sai ya ki tashinta cikin doki da zumudi hulkas yaje yayi wanka ya kimtsa gama hakan ke da wuya sai ga yarima e ka ya shigo cikin dakin shima ya caba ado fuskarsa cike da annuri ko da yaga hulkas ma ya gama shiri tsaf sai yayi murmushi yace hakika naga alamar cewa ka fini dokin son zuwa kallon wannan gasar jarumtakar da za ayi Yau.
.
Hulkas ya maida masa da martanin murmushin yace Ai ji nake ina ma kamar na tafiyar da rayuwar da tsuntsu na ganni a can ba don komai ba sai don ma kawai na sake ganin kyakkyawar fuskar nan ta jaruma siyama kuma naga yadda zata fafata yaki da manyan mazaje barmas ya kyalkyale da dariya yace Ai dama nasan cewa tatsuniyar Gizo Bata wuce ta Koki, to ai saikayi sauri kazo muje muyi buda baki a can turakar mahaifiyata amma me ya faru naga har yanzu mahaifiyarka tana yin barci bata farka ba?
.
Koda jin wannan tambaya sai yarima Hulkas yayi ajiyar zuciya yace ina kyautata zaton cewa jiya da daddare ba tayi barci da wuri ba shi yasa yanzu take ramuwarsa cikin alamun damuwa yarima barmas yace aukuwa NA kwanaki t ke Kai by tt tttt I will t a few minutes ago rr I t I r a little more time I t a little more time t r I will have a talk a rt I t tr I have a meeting at a t a t tr a r f I r tr I will forward it t a little more time I will be rr I will be in touch soon to be in the office tomorrow and tr to get the kids to the park and ride from my account ff for Friday rr for TR he is a good guy and I think the office and I can get tytt ummina ma ba zatayi buda baki ba sai tare da mahaifiyarka don cewa tayi nazo na tafi da ku muje muyi buda bakin gaba daya kuma tare zamu tafi can filin yin yoga gasa har da sarki da kansa kana ganin cewa ba zaka tasheta daga barcin ba?
.
Hulkas yace A’a bai kamata na tasheta ba tunda akwai bashin barci a tare da ita muje a yiwa mahaifiyar taka bayani koda jin haka sai yarima barmas ya juya ya fice dagacikin dakin shi kuma yarima hulkas ya bishi da sauri suka durfafi turakar Luzuraina.
.
Turakace babba wadda aka cikata da kayan kawa irin na sarakai. A gefe daya an ajiye wani dogon teburin cin abinci mai
dauke da kujeru goma sha biyu, A kan wannan teburi an shirya abincin kalaci iri iri har kala goma sha daya bisa farantai luzuraina ce kadai zaune akan wannan babban tebur tana jiran isowar sushadila.
.
kwatsam ! Sai ta hango yarima hulkas tare da danta barmas su biyu kacal sun shigo cikin falon. Al amarin da yai matukar bata mamaki kenan domin su uku ya kamata ta gani tun kafin su karaso gareta luzuraina ta dubi yarima hulkas cikin alamun damuwa tace ina mahaifiyarka?
.
Me yasa bata biyoku ba kun taho tare, yarima hulkas ya risina cikin biyayya ya gaida luzuraina yace ina zaton cewa ummina batayi barci ba jiya da wuri sakamakon labarin dana bata akan inda muka je jiya nida barmas.
.
Koda jin wannan batu sai luzuraina tayi shiru tana tunani na tsawon yan dakiku sannan ta mike tsaye ta dubi yarima barmas tace ku zauna kuyi kalaci kai da abokinka ni ba zan yi ba har sai shadila ta tashi da kanta idan kun gama cin abincin kuje ku jira sarki a falonsa domin yana fitowa sai ku tafi filin gasa tare idan ya tambayeni ku gaya masa cewa zamu riskeku a can nida kawata shadila koda gama fadin hakan sai luzuraina ta mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta tafi can cikin turakarta ta barci, barmas da hulkas kuwa sai suka zauna suka yi buda bakinsu cikin sauri, suna kammalawa sai suka tafi zuwa can falon sarki hulbasu ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai ga sarki hulbasu ya fito a cikin gagarumar shiga ta alfarma da kasaita fuskarsa cike da annuri kallo daya mutum zaiyi masa ya gane cewa yana cikin walwala da murnar zuwan wannan rana ta gasar jarumtaka wacce ake yi a birninsa a karshen kowacce shekara, koda sarki hulbasu yaga yarima hulkas da yarima barmas su biyu kadai a zaune babu iyayansu sai annurin fuskarsa ya dauke ya dubi barmas cikin alamun damuwa yace ina iyayan naku mata?
Me yasa basu zo nan ba tare daku?
Nan take barmas ya yiwa sarki hulbasu bayani kamar yadda luzuraina tayi masa. Koda jin haka sai sarki hulbasu ya dubesu yace shi ke nan ku tashi mu tafi filin gasar nan domin na san cewa tuni an gama hallara ni kadai ake jira a fara wannan gasa
nan take su hulkas suka mike tsaye suka bi sarki a baya suna isowa babbar haraba ta bangaren turakar sarki hulbasu sukayi kicibis da dakaru a tsai tsai cikin shigar yaki bisa dawakai wadanda za su yiwa sarki rakiya izuwa filin gasar a gefe daya kuma ga dokin sarki tare wadansu dawakan guda hudu
.
Ba tare da bata wani lokaci ba aka kawo wa sarki dokinsa ba tare da bata
.
Wani lokaci ba aka kawowa sarki dokinsa ya hau barmas da hulkas ma sai aka kawo musu biyu daga cikin wadannan dawakai guda hudu suka hau aka dunguma gaba daya aka nufi filin gasar.kuma hardani kaina AlQuyraemey Ina binsu a baya
sai dai wannan filin anyi shine a tsakiyar gari kusa da babbar kasuwa ta garin wacce take gagarumin ci a duk ranar da za ayi wannan gasa.
.
Filin ya kasance katon gaske kuma an kewayeshi da katanga doguwar gaske daga cikinsa an kewayeshi da kujeru sama da guda miliyan biyu amma duk ranar da za ayi wannan gasa sai mutane sun rasa wajan zama saboda cikowa sai dai ka rinka ganin jama a akan katanga, kai wasu ma basa samun damar shigowa cikin filin gasar sai dai su hau saman benayen gidaje da bishiyoyi suna hango abinda ke faruwa a cikin filin.
.
A gefe daya ne na filin aka gina inda sarki da mukarrabansa ke zama don kallon wannan gasa duk wanda bai kasance jinin sarauta ba to bai isa yaje ya zauna ba a wannan wuri ba face ya
kasance babban attajiri ko mashahurin boka ko kuma makusancin sarki kamarni Al Quyraemey ke tare da ku.
.
Al’ amarin siyama kuwa da iyayanta lokacin da gari ya waye suka gama shirin tafiya filin gasa si mahaifinta ya rufe fuskarsa da rawani ya zamana cewa idanunsa kadai ake gani sannan suka hawo dawakai guda uku suka durfafi filin gasar jarumtakar. Lokacin da suka iso bakin kofar filin gasar sai suka
iske gurin ya cika makil da mutane babu masaka tsinke ganin hakan ne yasa hankalinsu ya dugunzuma ba don komai ba sai don sun san cewa siyama ce kadai za a bari ta shiga cikin filin gasar tunda tana da shaida ta jaruman takara su kuwa sai dai su hau kan bishiya ko wani gidan mai bene.
.
Koda siyama ta lura da irin damuwar da iyayanta ke ciki sai ta nunawa masu gadin filin shaidarta ta jarumar gasa kuma ta gaya musu cewa ga iyayanta a tsaye tana son ta shiga tare dasu ciki koda jin haka sai shugaban masu gadin wani narkeken katon badakare ya dubi siyama sama da kasa cikin raini ya bushe da dariya yace yanzu ke wane ganganci ne ya sa kika shiga wannan gasa kina matsayin mace, kuma yarinya karama haka ? Shin iyayan naki sun gaji da ke ne shiyasa suke so su ga irin kisan gillar da za ayi miki? Toki sani cewa indai fili ya cika babu mai sake shiga ciki face sarki da mukarrabansa, ko ki shiga ke kadai ko kuma ki fasa yin gasar gaba daya, a wannan lokaci su kansu tsirarun ‘yan kallon dake tsaye a kofar filin wasan kallon siyama suke yi kawai wasu suna mamaki wasu suna ta sheka mata dariya suna yi mata kallon mahaukaciya wacce ta gaji da zaman duniya, wasu ma sai suka kama tsegumi suna cewa bata da iyaye, baiwa ce kawai iyayan gijinta suka gaji da ita.
.
Lokacin da jaruma siyama ta ji cewar ba za a bar iyayanta su shiga filin gasar ba sai ranta ya baci ta yunkura zata bude kofar da karfin tsiya su kunna kai ciki kawai sai mahaifinta ya dubeta yayi mata inkiyar kada ta aikata hakan ta hakura, cikin sanyin jiki ta juyo ta fuskanceshi tace yakai abbana yanzu mene ne abinyi?
Zamu koma gida ne ko kuwa zamu hau sama ne muyi kallo abul siyama ya gyada kai yace mu dakata har sarki ya iso na tabbatar muku da cewa zamu shiga wannan fili na gasa yayin da sarki yazo nan, koda jin wannan batu sai mamaki ya kama siyama domin bata ga dalilin da zai sa a barsu su shiga cikin filin wannan gasa ba idan sarki yazo tunda dai su basu kasance masu sarauta ba ko wani matsayi haka dai siyama tare da mahaifanta suka koma gefe daya suka tsaya suka zuba idanu kawai.
.
A wannan lokaci tsirarun attajirai da masu fada aji ne kadai ke wucewa cikin filin gasar kuma suna shiga sai a janyo kofa a sake rufewa kawai jim kadan kuwa sai ga sarki Hulbasu tare da
yarima basmar da yarima Hulkas sun nufo kofar filin gasar bisa dawakai dakaru na take musu baya ana busa Algaita gami da buga tambura nan da nan jama a suka dare aka basu hanya jama ar gari kuwa suka kama yiwa sarki Hulbasu kirari gami da jinjina sabo da nuna soyayyarsu a gareshi.
.
Koda ganin wannan al amari sai yarima hukas ya tuno da rayuwarsa ta can birninsa yadda jama ar gari ke sonsa da nuna masa soyayya sannan kuma ya tuno da yadda talakawa ke tsananin tsoron sarki Shardas saboda rashin imaninsa da cin zalinsa nan take hulkas ya tambayi kansa a cikin ransa yace wai shin menene dalilin da yasa mahaifina ya kasance azzalumi ? Kuma sabo da me halayansa suka banbanta da nasa alhalin ance barewa bata gudu danta yayi rarrafe amsar da yarima hulkas ya kasa baiwa kansa kenan yana cikin wannan haline sarki hulbasu da tawagarsa suka sake kusanto wajen tun daga nesa dasu yarima barmas suka hango jaruma siyama tsaye a wajan tare da iyayanta sai suka cika da mamaki
sabo da kamata yayi ace ta dade da shiga ciki tun daga nesa da sarki hulbasu ya hango mahaifin siyama tare da matarsa a tsaye da kuma ‘yarsu siyama sai ya kura musu idanu kawai har
suka iso bakin kofar shiga filin gasar da isowarsu sai mahaifin siyama ya risina ya gaida sarki ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Saboda tsananin mamaki da kuma ganin wannan mahaifina siyama a wajan nan, amma kafin nan zanso ku biyoni a labari na gaba domin jin yadda za a kaya a tsakanin su shin meye dalilin da yasa shi tsayawa yana kallonsa hm Nima ban sani ba.
Sai Kuma Allah ya kaimu Gobe kenan ku huta lafiya…….
Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part B.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja lin zamin dokinsa ya tsaya cak, take kowa dake bayansa ma ya tsaya sarki ya sauko daga kan dokinsa fuskarsa cike da annuri ya durfafi mahaifin siyama, yana riskarsa sai ya rungumeshi sannan ya janye jikinsa daga cikin nasa ya dubeshi cikin mamaki yace yakai babban masoyi menene dalilin da yasa baka amsa kirana ba bayan mun rabu a daji a wannan rana.
.
Koda jin wannan tambaya sai mahaifin siyama yayi murmushi
yace ya shugabana kayi hakuri mu sami lokaci saimu tattauna yanzu kamata yayi mu shiga cikin filin gasa domin zuwanka kadai ake jira.
.
Koda jin haka sai sarki yayi murmushi ya kama hannunsa yaja shi izuwa cikin filin gasar shima sai ya ruko matarsa yarima barmas da yarima hulkas kuwa sai suka jera tare da jaruma siyama suka shiga cikin filin gasar, yayin da shima.
.
Koda su sarki Hulbasu suka shiga cikin filin gasar sai kowa ya mike tsaye don nuna girmamawa a gareshi filin ya cika da shewa aka ci gaba da yiwa sarki jinjina da gaisuwa ehm har sai da sarki da mukarrabansa suka je suka zauna a inda aka tanadar musu sannan filin yayi tsir aka yi shiru kamar mutuwa ta gifta a dai dai wannan lokaci ne mai gabatar da taro ya tashi yayi jawabi kamar yadda aka saba sannan yaci gaba da fadin sunayan jaruman da za su yi gasar a yau da gobe har tsawon kwanaki bakwai, a wannan lokaci jaruma siyama na zaune a tsakiyarsu yarima hulkas da yarima barmas amma sai ta lura da cewar yarima hulkas yana ta satar kallonta kuma yana son yayi mata magana, haka ma yarima barmas koda ganin haka sai ta murtuke fuska taki yiwa dayansu magana kuma taki basu damar yi mata magana ta hanyar kin sakar musu fuska, ba tare da bata wani lokaci ba aka buga gangar fara gasa aka kirawo sunan wadansu jarumai guda biyu suka shigo cikin filin kowannansu na rike da takobi da garkuwa daya dogo ne kuma kakkaura mai kwarjini da kirar sadaukai ana kiransa da suna MULAGUS, dayan kuwa gajere ne amma shima yana da kirar sadaukantaka ana kiransa da suna KUMAR, A cikin dokar wannan gasa an yarda a soki mutum ko a sareshi da a ko ina koda kuwa hakan zai iya zama sanadin ajalinsa amma ka idar nasarar gasar shine kawai akai mutum kasa ya kasa mikewa tsaye kafin a kirga bakwai, Malagus da kumar suka gyara tsayuwarsu suka fara kallon kallo kowannansu yana nazarin abokin gwaminsa, a dai dai wannan lokaci ne Hulkas ya dubi yarima barmas yace yakai abokina a ganinka wane ne zai lashe
wannan gasa tsakanin Mulagus da Kumar?
.
Koda jin wannan tambaya sai Barmas ya tuntsure da dariya sannan yace haba ai da ganin kura an san taci mutum Ga abu nan a zahiri kowa yana gani ai ko a ba a gwada ba linzami yafi
karfin bakin kaza….
.
Kafin Hulkas ya budi baki ya sake cewa wani abu sai jaruma siyama ta tari numfashinsa tace ai sai an gwada akan san na kwarai tunda komai zai iya faruwa a ko yaushe. Koda hulkas da barmas sukaji siyama ta tsomo baki a cikin zancensu sai farin ciki ya lullubesu hulkas ya dubeta ya ce ashe dama mahaifinki
da sarki sun san junansu amma baki gaya mana ba
.
Sa adda siyama taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace ni kaina nayi mamaki ban san cewa sun san junansu ba sai yanzu, amma dai abin da na ke zargi shine a daji suka hadu a wajan farauta sabo da duk su biyun babu abin da suke so a rayuwarsu sama da farauta, zan tambayi abbana dai naji daga gareshi, gama fadin hakan keda wuya sai sukaga mulagus da kumar sun ruga izuwa kan juna sun kacame da azababben yaki suna masu kaiwa juna SARA DA SUKA cikin zafin nama juriya da bajinta, ana fara gumurzun ne filin yayi tsir ba a jin sautin komai face karar takubbansu ihunsu da karajinsu da takun sawayan kafafunsu, nan take kowa ya gane cewa Mulagus yafi karfin damtse to amma kuma shi Kumar yana da tsananin naci juriya da kwarewar iya yaki da farko duk sa adda mulagus ya kawowa kumar sara idan kuma ya kare da takobinsa sai kaga har darkushewa kasa yakeyi saboda karfin saran da nauyinsa, wani lokacin kuma sai kaga mulagus ya gabzawa kumar naushi ko bugu da hannu ko da kafa har kumar na durkushewa kasa amma kafin mulagus ya kaiwa kumar sara ko suka sa adda yake durkushen tuni kumar ya mike tsaye zumbur ya ci gaba da kare kansa kuma yana maida martani.
.
Abin ka da wanda yafi ka karfi cikin kankanin lokaci mulagus ya hadawa kumar jini da majina kuma ya sami nasarar yankarsa da takobinsa har sau uku ya zamana cewa jini na zuba a jikin kumar kuma jiri na dibarsa amma saboda masifaffen naci da azababbiyar juriya yaki yarda ya fadi a wannan lokaci gaba daya jama ar dake wajan sun saddakar da cewar mulagus ya gama samun lagon kumar don haka a ko yaushe zai iya bazar
da shi kasa a haka dai suka ci gaba da gumurzu har tsawon rabin sa a mulagus bai sake samun wata nasara ba akan kumar abin ka da jiki da jini sai shima mulagus ya fara gajiya haki ya yawaita gareshi da yawan numfashi shi kuwa kumar sai ya samu karfi a wannan lokaci tamkar ma a sannan ne ya fara gumurzu sai gashi nasa karfin Saran da sukan yafi na mulagus nauyi da karfi hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo ! kuma ance a dade ana yi sai gaskiya domin dadewar da jaruman biyu sukayi suna fafata wannan masifaffen fada yasa aka gane jimrau a tsakaninsu kuma aka fahimci wanene mayakin kwarai
cikin kankanin lokaci kumar ya kuntata mulagus ya hanashi sakat ya zamana cewa kwata kwata mulagus baya iya maida martani sai kokarin kare kai, koda kumar yaga ya sami wannan nasara sai ya shammaci mulagus ya daka tsalle sama ya doki fuskarsa da kafa, saboda kargin dukan sai da mulagus ya juya sau biyu a tsaye, kafin kumar ya duro kasa tuni ya sa takobinsa ya sarewa mulagus hannunsa na dama mai rike da takobi, take hannun ya fice fit jini ya kama feshi da tsiri daga cikin dungulmin a lokacin da mulagus ya kwarara uban ihu wanda ya firgita komai da kowa dake wajan har dama halittun dake cikin gari da kewaye take mulagus ya kife kasa sumamme, ai kuwa sai filin gasar ya rude da shewa gami da jinjina a lokacin ne shima kumar ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa sakamakon gani da yake dishi-dishi da idanunsa da kuma jinin dake zuba a jikinsa nan take likitoci suka rugo cikin filin gasar da dakaru aka dauke jaruman biyu aka shige dasu izuwa cikin wani babban daki dake gefe daya a cikin filin gasar wanda aka tanadeshi a matsayin asibitin da za a rinka duba jaruman gasa, ganin yadda aka zubar da jini ne a filin wannan gasa yasa hankalin yarima hulkas ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take ya aiyana a ransa yace in da zan zamo wani babban sarki a wannan nahiya tamu da sai na hana gabatar da irin wadannan wasanni wadanda ake zubar da jini domin ban ga amfanin ace zubar da jini shine Jarumtaka ba.
.
Bayan an gama dauke jaruman gasar biyu daga cikin filin gasar sai mai gabatar wa ya kirawo sunan jarumi na gaba wanda yayi
wasa waishi DURKUS, koda yan kallo sukaji sunan wannan jarumi sai filin ya cika da shewa tamkar dodon kunne zai dode, shidai wannan jarumin Dukrkus din a gaba daya nahiyar babu wani jarumi da ya kaishi girma, da iya yaki tare da kuma daukaka kuma duk shekara shine yake lashe wannan gasa ta jarumtaka dukkanin jaruman da suke zuwa wannan gasa daga
sauran kasashe na duniya komai girmansa da iya yakinsu suna tsoron durkus babu wanda yake son a hadashi dashi, ba don komai ba sai don sadauki Durkus ya kasance gabjejen kato mai kirar mutanan Farko sannan kuma yana da tsananin karfi na Allah ya isa gashi da tsawon tsiya kamar ba mutum ba kuma kakkaura ne sosai a takaice dai kirarsa ta samudawa ce baya ga wannan rashin imanin Darkus yayi yawa domin duk jarumin da ya hadu dashi sai ya mutu sadauki Darkus bai taba yin wasa ya bar abokin gwaminsa da raiba don tsantsar zaluncinsa, kuma kafin ma ya kashe abokin gasar tasa sai ya sassare masa gabban jiki yai gungudwa gungudwa da sassan jikinsa sannan ya kashe shi kisan wulakanci bisa wannan daliline yasa duk sa adda zaiyi yaki a filin gasa masu raunin zuciya basa iya
kallon wasansa, domin duk sai dai kaga suna ta kumallo a filin gasar suna koke koke yayinda yake aiwatar da zaluncinsa ga abokin gasarsa.
.
Koda aka kirawo sunan wannan Jarumi wato Darkus ya shigo tsakiyar filin gasar sai aka kama yi masa jinjina da kirari sai shima ya kwarara uban ihu mai karfi da firgitawa ya fara dukan
kirjinsa da tafkeken hannunsa ya shiga rerowa kansa kirari yana mai cewa,,,
Ina bakon lahira to ya fito ya tareni, Nine bakin takobi mai raba kowa da masoyi, nine dajin mutuwa kowa ya shige ba rai zai fita ba a raye ba. Kuma nine ISKAR ANNOBA kowa ya shakeni sai ya kwana kiyama. Guguwar kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya sawun giwa nake wanda na take na dukkan dabbobi Ina mai jida jarumta da juriya da naci to ya fito ga dillalin mutuwa hm Ni AlQuyraemey sai naji kamar na fita haka dai Darkus yaci gaba da yiwa kansa kirari har ya gama ya tsaya cak a waje daya yana huci da muzurai tamkar wani bakin kumurci kai yaran dake cikin wannan filin gasa boye fuskarsu
suka kama yi domin da zarar sun hada idanu da darkus sai suga kamar dodo ne tsaye a gabansu wanda zai suresu da hannu daya ya jefa baki ya lankwame…
Nima dai bari na dakata a nan wajan saboda tsaro Amma
kafinan Nidinne dai mai deɓe maku kewa.
Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Uku Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part C.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
A dai dai wannan lokaci ne filin gasar yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kawai sai mai gabatarwa ya kira sunan jarumin da zai kara da darkus ba wani bane jarumin face jaruma SIYAMA.
.
Koda jama a sukaji an ambaci sunan ya mace sai kowa ya gwale idanunsa domin yaga ko wacce jaruma ce haka mai tsautsayi wadda ta gaji da zaman duniya. Domin manyan mazaje ma da suka kasance sadaukai kuma wadanda suka sha gwagwarmaya iri iri a filin daga suna tsoron a hadasu gumurzu da darkus don su san cewa ajalinsu ne ya zo.
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga wata yar matashiyar budurwar yarinya ta taso daga wajan da su sarki ke zaune tana sanye da kayan yaki ta shigo cikin tsakiyar filin gasar ko garkuwa babu a hannunta kuma takobinta ma na cikin kube sakale a kuibin cinyarta ta hagum nan fa mamaki ya turnuke jama a wasu suka kamu da tsananin tausayin siyama har suna zubar da hawaye saboda suna ganin cewa mugun kisan gilla darkus zaiyi mata.
.
Wasu mutanan kuwa sai suka kama tsinewa
mutanan da suka yi sanadiyyar shigar wannan kyakkyawar yarinya cikin wannan gaasa yarima hulkas da barmas kuwa hankalinsu ne yayi matukar dugunzuma ainun har jikinsu ya kama tsuma bisa ganin cewa Siyama zatayi Yakine da DARKUS hm Nimafa nayi mamaki kamar na tsaya da typing amma muje kawai.
.
Duk da cewa sun ga irin jarumtakarta sai da zuciyoyinsu suka karaya yarima barmas bai san sa adda ya taso daga inda yake zaune ba
yaje inda sarki da mahaifin siyama ke zaune ya dubi mahaifin siyaman a dimauce yace haba ya abul siyama yanzu kana gani za a kashe yarka amma kayi shiru hm AlQuyraemey nake tabbas wannan hadi da akayi babu adalci acikinsa kawai so ake a kashe yarka koda jin wannan batu sai mahaifin siyama yayi murmushi ya dubi yarima barmas cikin girmamawa yace kwantar da hankalinka yakai yarima babu abinda zai sami yata, ka koma wajanka ka zauna ka morewa idanunka da kallon abin mamaki cikin alamun tsananin damuwa yarima barmas ya juya ya nufi can wajen zamansa yana waigen mahaifin siyama amma duk sa adda ya waigo din sai yaga shima ya kurawa hulkas idanu yana yi masa wani irin kallo mai dauke da ayar tambaya.
.
A wannan lokaci ne sarki Hulbasu ya dubi mahaifin siyama cikin alamun mamaki yake yakai abokina wai shin mene ne dalilin da yasa ko yaushe kake rufe fuskarka ne da mayafi, ni kaina ban taba ganin irin kamanninka ba kuma ko yaushe a haka kake koda kuwa a cikin daji kake shin ina dalilin yin hakan?
.
Sa adda mahaifin siyama yaji wannan tambaya sai yayi murmushi ya ce ya shugabana kayi hakuri ba zan iya baka amsar wannan tambaya ba a yanzu saboda wani muhimmin dalili da ya shafi rayuwata amma nayi maka alkawarin idan lokacin da ya kamata ka sani yayi zaka sani, ina boye wannan sirri ne sabo da samar da tsaro ga rayuwata data iyalina ya shugabana idan ba zaka damu ba nima ina da wata tambaya guda daya a gareka wai shin wane ne wancan yaro wanda ke tare da danka yarima barmas daga ina ya fito kuma mene ne dangantakarsu da sarauta?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarki hulbasu ya kyalkyale da dariya sannan yace akan wanne dalili zan baka amsar wannan tambaya da kayi mini alhalin nima ina da nawa tambayoyin kwatankwacin irinsu a kanka kuma kaki ka bani amsa tun daga ranar da na fara ganinka ?
.
Nima ba zan iya baka amsar wadannan tambayoyi na ka ba saboda tabbatar da tsaro a kan wannan yaro domin kuwa idan wani abu ya sami lafiyar wannan yaro bama niba gaba daya jama ar dake cikin wannan nahiya tamu sai sun shiga uku, sa adda mahaifin siyama yaji wannan batu daga bakin sarki sai kansa ya daure ya cika da mamaki fiye da ko yaushe har ya budi baki da nufin ya sake yiwa sarki wata tambaya sai kawai yaga dakus ya ruga da gudu izuwa kan siyama yana mai daga takobinsa sama kuma yana mai kwarara uban ihu mai tsananin firgitawa irin wanda ka iya tarwatsa dubunnan dakaru a filin daga kuma ya furta tane a cikin mugun nufi na gamawa da ita farat daya ita kuwa siyama sai ta tsaya cak a inda take to gezau batayi ba kuma ko kifta idanunta ba tayi ba koda dakus ya iso daf da ita sai ya kawo mata wani irin wawan sara a wuya da nufin ya cisge mata kai cikin bakin zafin nama jaruma siyama ta tale kafafunta tayi kasa, takobin darkus din ta bysari iska ya sake kai mata wani mugun sara a fusace siyama tana durkushe a kasa tayi wata irin alkafira cikin gwaninta ta kaucewa harin nasa, koda takobin darkus tasari kasa sai ta nutse izuwa cikin karkashin kasar gaba dayanta saboda tsananin karfin saran nasa da nauyinsa kafin darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki kasa da tafin hannunta na hagu tayi sama sai
kawai ta doki gadon bayansa da kafafunta biyu darkus yaji kamar wani dankareren kato ne yayi masa dundu a gadon baya kuma duk da tsananin girmansa da nauyinsa sai da ya tafi taga taga da gaba kamar zai kife kasa, da kyar ya iya cijewa ya tsaya kyam a tsaye.
.
Al amarin da yai matukar razanashi da bashi haushi kenan, domin wannan ne karo na farko da aka taba samun jarumin da ya sami nasarar
.
Dukan jikinsa har ma ya kusan kaishi kasa, koda yan kallo sukaga wannan gagarumar jarumtaka da siyama tayi sai suka cika da tsananin mamaki filin ya kaure da ihu gami da shewa aka shiga yiwa siyama kirari gami da jinjina, yarima hulkas kuwa saboda murna ma bai san sa adda ya daka tsalle ba daga kan kujerar da yake zaune yana shewa shewar tasa ce tasa har siyama ta juyo ta dubeshi kawai sai tayi masa murmushi, take hulkas yaji wani irin farin ciki mara misaltuwa da dadi ya lullubeshi saboda wannan murmushi da tayi masa shi kuwa sadauki Darkus fusata yayi ainun ya juyo da sauri ya sake rugowa izuwa kan siyama aikuwa itama sai tayi wuf ta zare takobinta ta tareshi suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da razanarwa, gaba daya jama ar dake filin wannan gasar sai da hankalinsu ya
dugunzuma gaba daya saboda tun da aka fara wannan gasa ta jarumtaka tsawon shekaru ba a taba ganin gumurzu ba irin wannan mai tsananin hadari wow.
.
A can gidan sarauta kuwa gimbiya shadila bata farka ba daga barci har sai bayan lokaci mai dan tsawo koda ta bude idanunta taga ashe ma tuni gari ya dade da wayewa har rana ta kwalle kuma taga babu jarumi hulkas kwance a kusa da ita akan gadon da take kwance sai ta mike zaune zumbur a lokacin da zuciyarta ta buga da karfin gaske, kawai sai ta sauko daga kan gadon da sauri ta leka bandaki don tunanin ko hulkas na ciki yana wanka amma sai ta iske bandakin wayam babu kowa a cikinsa a gigice shadila ta gaggauta tayi wankanta sannan ta kimtsa gama shirinta keda wuya sai taji an kwankwasa mata kofa saiga wata kuyanga ta shigo, kuyangar ta zube kasa bisa guiwoyinta ta ce ya shugabata sarauniya ta turoni nayi miki jagora zuwa can turakarta domin tana jiranki kuyi kalaci, cikin mamaki shadila ta dubi yadda rana ta kwalle ta cikin tagar dakin nata sannan ta dubi kuyangar tace yanzu kina nufin kice har yanzu sarauniya bata yi kalaci ba, kuyangar ta sake risina tace ai saboda kina barcine shi yasa taki tayi kalacin da kanta, amma tafi sa a biyu da gama kimtsawa har ma sarki dasu yarima sun dade da tafiya kallon GASAR JARUMTAKA.
.
Koda jin wannan batu sai shardila taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta ji babu abinda take so sama da ta ganta a filin wannan gasa, don haka cikin sauri tace da kuyangar yi maza ki kaini wajan sarauniya ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai kuyangar ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin shardila na biye da ita, luzaira na zaune akan teburan cin abincin dake falonta ita kadai tana jiran sai ga kuyanga tare da shardila sun shigo, cikin murna luzaira ta mike tsaye da sauri ta taryo shardila ta kamo hannunta ta kawota izuwa kan kujera suka zauna tare, ba tare da bata wani lokaci ba suka kama cin abincin har suka kusan gama cin abincin dayansu baice kala ba a sannan ne shardila tayi gyarar murya ta dago kai ta dubi luzaira tace yake kawata ki gafarceni na bata miki lokaci da kika kawo har yanzu baki yi kalaci ba domin barcina ne yayi nauyi, kafin shardila ta gama wannan magana sai luzuraina ta tari numfashinta tana mai kallonta cikin murmushi tace haba yake kawata kada ki sawa kanki damuwa akan hakan domin danki ya gaya mini cewar yana
zaton jiya bakiyi barci da wuri ba shin kina da wata lalura ne ta rashin lafiya ko kuwa akwai wata matsala dake damunki.
.
Koda jin wannan tambaya sai shardila ta yi murmushi tace kawata babu abinda yake damuna kuma bani da wata matsala haka kawai dai naji idanuna sun bushe jiya da daddare wata kila bakunta ce ta janyo hakan
koda jin haka sai luzuraina ta kyalkyale da dariya ta yiwa shardila wani irin kallo na rashin yarda domin ba ta yarda da abinda ta fada ba sai dai ta dubeta tace ko dai kewar sarki shardas ce ta hanaki barci kinga tashi mu hanzarta mu tafi filin gasar nan domin na san cewa yanzu tuni an dade da fara wasa babu mamaki ma an shiga kewaye na uku. .
.
Kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni shardila ta wanke hannayanta ta mike tsaye saboda dokin zuwa wannan filin gasa, nan dai suka gama kimtsawa suka nufi wani babban fili inda aka tanadar musu keken dokin da zasu hau tare da dakarun da zasuyi musu rakiya tun daga nesa shardila ta hango dakarun sai tayi sauri ta rufe fuskarta da wani
bakin kyalle ya zamana cewa idanunta kadai ake gani ba komaine yasa shardila ta rufe fuskarta ba face a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da mutane suyi ta kallonta, abinda bata sani ba shine tsananin kyawun fuskarta da kyan surar jikinta ne ya janyo mata kallon da ake yi mata nan dai su luzuraina suka shiga cikin keken dokin aka ja
aka fice daga cikin gidan sarautar aka durfafi filin GASAR JARUMTAKA.
.
NIMA KUMA sai na dakata anan na nufi Filin daga Wato neman na Abinci Kuma sai Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba
Nidinne dai
TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part D.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
A can filin gasat kuwa lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama sai da suka shafe rabin sa a cif suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba
.
Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan da yawa daga cikin yan kallo dai sun firgice ne da al amarin siyama kai harni AlQuyraemey da nake wannan typing din na rikice da lamarinta, Kai wasu ma sai suka rinka cewa siyama ba mutum bace Aljana ce don babu yadda za ayi ace tana ya mace yar shekara tara kacal a duniya ta sami irin wannan gagarumin karfin damtse da iya yaki haka, lallai akwai aikin sihiri acikin lamarin.
.
Abinda basu sani ba shine siyama tasha Sadaukantaka ne a nono kuma tun tana da shekaru hudu kacal a duniya mahaifinta ya far bata horon yaki. Ana cikin wannan haline aka jiyo sautin tashin tambura da bushin Algaita alamar cewar ga sarauniya Luzuraina nan ta iso, take farinciki ya kama sarki hulbasu ya dubi mahaifin jaruma siyama yace
abokina ga matata nan ta iso tare da kawarta babbar bakuwarmu
.
Koda jin haka sai abul siyama ya budi baki da nufin ya tambayeshi ko wacece bakuwar, amma sai ya kasa sakamakon ganin wani irin mugun naushi da darkus ya yiwa siyama a fuska cikin tsananin shammace, saboda karfin naushin sai da jini yai tsartuwa daga cikin hancinta kuma ya yi feshi daga cikin bakinta ta tafi luuu ! Kamar zata kife kasa da baya amma sabo da tsananin juriya sai ta mike tsaye kyam ta doki kasa da kafarta guda tayi sama cikin shammace itama ta doki fuskar darkus da tafin kafarta ta dama tana mai jera masa duka uku a saman, sannan ta duro kasa ai kuwa sai gashi shima hancinsa da bakinsa na yoyon jini har shima yaji wani jiri ya kwashe shi ya tafi luuu ! Zai kife da rub da ciki amma sai yai sauri ya tokare jikinsa da hannu guda ya taso sama kamar sifirin suka ci gaba da sabon masifaffen yaki kamar ma lokacinne suka fara yakin, A dai dai wannan lokaci ne gimbiya luzuraina da shardila suka shigo cikin filin gasar suka durfafo inda su sarki ke zaune dakaru na take musu baya, tun daga nesa Abul siyama ya hango shardila sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi irin bugawar da bai tabaji ba a rayuwarsa
.
Koda ya sake yin arba da dakarun dake yi mata rakiya wato su sadauki Murzanu sai jikinsa ya kama tsuma nan da nan gumi ya fara karyo masa domin a sannan ne ya tabbatar da abin da yake zargi duk da cewar kuwa shardila ta rufe fuskarta da bakin kyalle.
.
Al amarin shardila kuwa tunda ta shigo filin sai ta kama raba idanunta a cikin yan kallo ba don komai ba sai domin taga Abul Husna wanda danta yarima Hulkas ya bata labari domin ta gusar da wasu wasin dake cikin zuciyarta bisa wannan daliline ta yi ta ware idanuwa ko zata ga mutum mai hannu daya da nakasashshiyar kafa kuma ta rinka kallon fuskokin mutane don ta tabbatar da cewa tana yin arba da fuskar tsohon mijinta take zata shaidashi, amma har suka iso inda su sarki hulbasu ke zaune amma bata ganshi ba, abin da ya sa ko kadan hankalinta bai kawo kan Abul Siyama ba shine ta san cewa babu mai ikon zuwa kusa da sarki Hulbasu ya zauna face ya kasance jinin sarauta ko kuma wani mai fada aji a birnin, bugu da kari kuma fuskar Abul siyama a rufe take cikin rawani kuma ya lullube gaba dayan jikinsa da wanibabban mayafi na alfarma, luzuraina da shardila suka zo suka zauna kusa da sarki hulbasu daga hagunsa shi kuwa abul siyama yana zaune a damansa tun da suka zauna abul siyama bai yarda ya kalli inda suke ba shi kuwa hulbasu da yake gaba daya hankalinsa ma yana kan gumurzun da ake yi a tsakiyar filin gasar tsakanin jaruma siyama da sadauki durkus ko tunanin gabatar da Abul siyama bai yi ba awajan su Luzuraina yayin da shardila ta kyalla ido ta hango siyama a tsakiyar filin gasa wacce ke ta faman gumurzun yaki tayi arba da fuskarta sai taji zuciyarta ta buga da karfi ba komai ne ya haddasa hakan ba face jaruma siyama tana matukar kama da mahaifinta, nan take shardila ta gane cewa lallai jaruma siyama yar tsohon mijinta ce wanda take tunanin cewa ya mutu fiye da shekaru bakwai baya lallai hakan ya tabbatar mata da cewar kenan Hailur na nan a raye kuma a cikin wannan gari.
.
Koda gama aiyana hakan sai shardila taci gaba da kalle kallen ko ina a cikin filin gasar ko zataga Hailur shi kuwa Hailur da ya lura da ita da kuma halin da take ciki sai ya noke yana mai sunkuyar da kansa kasa yaki yarda su hada idanu, saboda ya tabbatar da cewa suna hada idanu zata shaidashi duk kuwa da cewa ya rufe fuskarsa da rawani idan kuwa ta shaidashi a gaban kowa zata fashe da kuka ta rungumeshi, tana yin hakan kuwa asirinsa zai tonu su sadauki Murzanu su shaidashi idan kuwa suka shaidashi komai ya tabarbare ke nan domin sai labari ya riski sarki shardas cewa har yanzu yana nan a raye, da zarar hakan ta faru kuwa hatta sarki hulbasu ya shiga cikin tashin hankali kenan da masifa don sarki shardas Cewa zaiyi ya boye babban makiyinsa a birninsa don haka sai ya yakeshi ya kau dashi kuma ya mallake kasar ma gaba daya, nan take idanun Hailur suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye domin shi a zatonsa ma tuni shardila ta dade da mutuwa, amma yanzu da ya ganta a cikin shiga ta alfarma irin ta sarakai, kuma yaga su sadauki Murzanu na take mata baya sai ya kamu da tsananin bakinciki mara misaltuwa domin ya gane cewa lallai a yanzu ta zama matar sarki shardas, aikuwa bayan su shardila sun zauna sai hailur yaga yarima
hulkas ya mike zumbur ya tafi izuwa wajan shardila ya rungumeta nan take zuciyar hailur ta sake bugawa da karfin gaske a karo na biyu ya tambayi kansa acikin zuciyarsa yace ‘ shin wannan yaro dana ne ko kuwa dan sarki shardas ne tabbas wannan yaro da uwarsa yake kama don haka bani da tabbacin cewa dana ne, tabbas shardila na dauke da cikin dana, wai shin kana zaton cewa sarki shardas zai amince ne shardila ta haife danka a cikin gidan sarautarsa, kai hailur ! Idan ma mafarki kake yi toka farka ”
.
Wannan shine gargadin da zuciyar hailur takeyi masa nan fa yaji cewar babu abinda yake bukata sama da ya sami damar tattaunawa da shardila domin ta bashi amsar wadannan tambayoyi dake yi masa yawo a cikin zuciya lokacin da shadila tayi arba da jaruma siyama taga fuskarta a zahiri sai hankalinta ya dugunzuma ainun kuma taji zuciyarta taci gaba da dukan uku uku ba komaine ya janyo hakan ba face ganin cewa tabbas siyama tana tsananin kama da tsohon mijinta hailur babban abin ma da ya kara dugunzuma hankalinta shine ganin irin yanayin yadda take yin yakinta iri daya ne sak dana tsohon mijinta Hailur.
.
Kafin shardila ta ankara tuni ta fara kuka tana mai zubar da hawaye gami da ci gaba da kalle kalle da waige waige a cikin filin gasar ko zata hango masoyinta hailur amma shiru kamar maye yaci shirwa ashe duk wannan hali da ta shiga Hailur ya lura da ita duk da cewar fuskarsa a rufe take cikin rawani kuma yana zaune a daman sarki ita kuma tana tare da luzuraina abarin hagun sarkin.
.
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
sukaci gaba da fafata kazamin yaki a karo na biyu sai ya zamana cewa karfi yazo daya an rasa wanda zai iya cutar da wani a cikinsu, duk da tsananin karfin damtse irin na darkus sai gashi naci da juriyar siyama da tsabar horon yaki da ta samu a wajen mahaifinta yasa ta iya kwatar kanta awajensa tun suna kaiwa junansu sara da suka da takubban hannayansu har sai da suka gaji ainun makaman nasu suka subuce daga hannayansu suka ci gaba da gabzar juna da hannu, Duk irin naushin da darkus yayiwa siyama sai aga ta rama wato dai itama tayi masa irinsa. Kai ! Tun suna tsaye akan duga dugansu tsabar masifar yaki sai da takai ga sun durkushe kasa a tare kuma a lokaci guda suka ci gaba da gabzar junansu a hakan kowannansu ya kama layi kamar wanda ya sha giya suka bugu har izuwa lokaci mai tsawo suna cikin wannan hali daga can kuma sai duk su biyun suka bingire da baya luuu ! Suka baje a kasa tare suna numfarfashi kamar ransu zai fita………..
.
A nan ne Littafin Tsatsuba Na Hudu Yazo Karshe Marubucin Littafin yace….
.
YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZATA KASANCE TSAKANIN SADAUKI DARKUS DA JARUMA SIYAMA ???
.
WAYE ZAI SAMU NASARAR ZAMA ZAKARAN GASAR JARUMTAKA A TSAKANINSU ?
.
MAI ZAI FARU IDAN GIMBIYA SHARDILA TA GANE MASOYINTA KUMA TSOHON MIJINTA HAILUR DA SUKA RABU TSAWON LOKACI ?
.
SHIN ASIRIN ABUL SIYAMA YANA TONUWA HAR LABARI YA KAI KUNNEN BABBAN MAKIYINSA SARKI SHARDAS WANDA ABUL SIYAMA KE ZARGIN YA AURI MASOYIYARSA KUMA MATARSA?
.
MAI ZAI FARU IDAN YA SAMU LABARI ?
.
Don jin Cigaban wannan labari na Tsatsuba Littafi na 5 sai ku danna bulun rubutun nan