Hausa novels

Fentin Zina Page 12 Hausa Novel

**A lokacin tana ss3 ta hadu da wani saurayi da ake kira Ahmad yazo gurin abokin shi staff ne a makarantar tasu.Tunda ya kyallara ido ya ganta ya kasa natsuwa yaji gaba daya komai nashi ya tsaya, ya parka motar shi a inda ake ajiye motoci ya zarce office din staff din, examinan sune, bayan sun gaisa yace dashi, baba naga wata cika fah ina ahigowa gate din ku kuma gaskiya na tsunduma ciki.Ajiye pen din examina yayi yana duban shi yace amma kasan dokar makarantar mu ta hana malami neman dalibar sa balle kuma kai da kake abokina gaskiya da kamar wuya hakan bazan iya taimakonka ba saidai akwai shawara.Gyara zama Ahmad yayi yace ina jinka.Yawwa zan bincika koda zan samu address dinta sai mubi ta wannan hanyar muje gidan nasu amma ina dai fatan bawai kamar sauran ‘yan mata ba?.Me kake nufi?.Ina nufin ba da wata manufa zaka je mata kamar yadda ka saba da sauran ‘yan mata ba.Girgiza kai Ahmad yayi yace zanso hakan.Well yayi.Ka bincika yanzu please.Taya zan bincika bayan bansan wa kake nema ba.Dafe goshi yayi yace oh God na tabbata idan na kwatanta maka ita zaka ganeta domin banga kamarta a duk fadin makarantar ba ko dana duba.Ok ci gaba.Fara ce tana da dan manyan idanu tsaka tsaki ce a yanayin tsayi sannan tana da dan kauri kadan daidai wanda ake so ehem kuma sanda tayi magana wa wanda suke tare naga wushirya da kuma tayi murmushi tana da dimple masu kyau i hope zaka gane ta.Kada yatsa yayi sannan yace correct na fahimta domin ita kadaice keda duk wadannan abubuwan dana lissafa.Natsuwa Ahmad ya karayi yana saurare.Examiner ya cigaba da cewa Ameena Ibraheem kenan tana a ss3B class ne ART kenan da sauran courses din yanzu zansa a kira mun ita sai ta bamu adress dinta.Ya fada yana mikewa ya fita ba’a jima ba ya dawo Ameena na biye dashi a baya cikin sanyi.Zama yayi a kujerar shi ya nuna mata kujerar kusa da Ahmad yace ki zauna ki saki jikin ki.Ta zauna tare da kara gaishe shi ta gaida bakon shi.Duk suka amsa.Examiner ya dubi Ahmad yace is she the lady?Ahmad ya gyada kai yana kallon Ameena.Examiner ya kalle ta yace na kiraki ne domin wannan, ya nuna Ahmad aboki nane shigowar shi kenan yaci karo dake a school premises yamun bayanin cewar yana sonki amma kinsan yadda dokar makaranta take shiyasa don kada a samu matsala nace barin kiraki ki fada mai adress dinki in yaso sai yaje gida kuyi magana domin na sanshi farin sani da nacin tsiya idan baki fada mai ba bazai bar zuwa makarantar nan ba karshe ya saka mu a matsala daga ni har ke abunda bazan so ba.Ta gyada kai ba don ta so ba ta fada mai adress din ta kara da cewa mahaifina bai yadda da a tara mishi samari a kofar gida da sunan hira ba zaifi kyau ka fara neman shi idan ya baka izinin magana dani Alhamdulillah idan kuma yaki sai ince kayi hakuri kawai, tana maganar ne idanunta a kasa.Kada ki damu indai nine insha Allah kamar yadda kika bukata zan fara zuwa gurin baban naki zaki iya tafiya.Ta mike sum-sum ta wuce, Ahmad ya maido hankalin shi ga examiner bayan ya raka Ameena da ido yace, ya ka ganta itace irin zabin da na dade ina fatan zamu gashi yau nayi ram da ita gaskiya ina da sa’a.Na sani, amma dai fatana ace kyakkyawar alaka ce zata ginu a tsakanin ku ba mummuna ba kuma bana fatan ka yaudari yarinyar nan domin tana da hankali da natsuwa ga ilimi da tarbiyya,.Haba mana ya kake mun haka ne kai kullum bazaka yabe ni ba sai fadin aibu a kaina?. Ahmad ya fada yana daure fuska.Ahmad kenan na sanka fiyeda yadda ko mahaifiyarka bazata fada mun halinka ba kada ka manta tare muka taso kiriniya tare muka yishi komi tare and na sanka babu mace duk kamun kanta da natsuwarta da baza ka sanyata a tarkon kaba sai dai kariyar ubangiji zai fidda ita.Hmm Ahmad ya fada yana mikewa tsaye nikam na tafi sai munyi waya.Examiner din ya mike Yana cewa saboda na fada maka gaskiya ba? Kai kullum baza’a yi fada da kai ba sai akan fadin gaskiya? Ya kamata kawa kanka fada tun kamin dare ya maka.Naji mr man, Ahmad yace yayinda suke fita daga office din, examiner na tsaye har ya shiga motar shi ya tafi kamin shima ya koma ciki.Kamar yadda Ahmad ya fada yaje ya samu mahaifin Ameena bayan dumbin tambayoyin daya sha karshe dai ya samu baba malam ya bashi izinin neman yardan ta idan ta amince sannan ya jaddada mai baya bukatar soyayya mai tsayi yafi so da zarar ta kammala ssce dinta ayi aurenta, babu wata wata ya amince da bukatar baba malam din suka rabu cikin mutunta juna da girmamawa.Sannu a hankali soyayya mai karfi da shakuwa suka shiga tsakanin Ahmad da Ameena har takai kowa dake cikin ‘yan uwa da abokan arziki da duk ma wanda yake tare da ita yasan da zaman Ahmad.Kamar Koda yaushe suna hira adan karamin zauren gidan su da yamma cikin raha da nishadi cikin son nuna soyayyarsa gareta yace Ameena ina son tambayar ki wani abu amma ina fatan duk amsar da zata fito daga bakin ki ta zama tsagwaron gaskiya.Murmushi tayi tace ina jinka insha Allah duk tambayar da zaka mun baza kaji sabanin gaskiya ba.Ba wani abu bane kawai so nake insan irin soyayyar da kike mun yaya girmanta yake? Shin zaki iya komai akai na, idan nace komai ina nufin komai? Ya fada yana tsare ta da ido da salon daya san yana kashe ‘yan mata dashi.Ka daina bata bakinka wajen tambayata irin haka, indai a wannan rayuwar ce da wannan duniyar dunbin kaunar da nike maka baza’a hada ta da komai ba, ni kaina bansan iya adadin son da nike maka ba.Baki amsa tambayata ba sahibata, kai tsaye kice dani eh ko a’a.Zan iya amma matukar bai sabawa addini na ba.Ok fine naji dadi, yanzu ki shiga gida ni zan wuce akwai inda zana je kuma ga lokacin sallah ya gabato kada mutane suzo wucewa suyi ta kalle mun ke.KU GAFARCENI DAN ALLAH BAN SAMU LOKACIN TYPING BA SAI YANZU, KUYI HAKURI DA WANNAN.INA KAUNARKU MASOYA NA.EESHERT ADAMU.MATAR MAJEEDADI✍️.

Back to top button