Hausa novels

Fentin Zina Page 11 Hausa Novel

*****Buga kofar yakeyi yayinda zuciyar shi ke dada zuwa wuya.Still tana kwance a inda take har sai da taji ya furta kalmar da tayi matukar gigita tunaninta don bata dauka tsaurin idonsa har ya kai ya furta mata haka ba.Cikin buga kofar yace wallahi Ameena idan na kirga biyar bakizo kin bude kofar nan ba a bakin auren ki, daya, biyu.Share hawayenta tayi data ji ya kai uku a kirgen nashi tazo ta bude kofar kafin tayi wani yunkuri ya sauke mata maruka guda biyu masu kyau yana nunata da yatsa cikin kumfar baki yace saboda kin raina ni ban isa in fada miki magana kiji ba ban isa ni da gidana ince ga abunda nike so ayi ba toh wallahi da sakel bazan yadda da wannan tijarar ba kuma yanzu ba sai anjima ba ki shiga ki daura mana abunda zamuci nida maryam na baki mintuna goma kacal ki kammala idan ba haka ba wallahi zaki kwana a gidan ku kinji na fada miki, shashasha kawai don kinga ina raga miki ina daga miki kafa toh an daina tausayin naki daga yau ya fita ya barta tana gunjin kuka tare da nadamar wannan auren.Fita tayi zuwa kitchen ta dau indomy guda biyu ta dafa musu mai kwai iya zallar shi takai kan dining ta ajiye bazata wahal da kanta ba suyi manage da iya indomy din kawai tunda hakan ya zaba.Bata kwankwasa musu ba ta zarce zuwa dakinta ta hau gado ta kwanta tana mai jin zuciyarta kamar ta fashe don bakin ciki tama rasa wani irin tunani ya kamata tayi akan wannan abun kawai sai tahau istigifari da salati sannan ta dan samu sassauci domin ragewa kanta kewa yasa ta kunna datar ta ta haw WhatsApp taci karo da fateema kamar kullum don ita da wuya baka sameta a online ba.Daga ta bangaren fateema tana ganin notification cewar Addan ta tana online taje kan number dinta ta danna kiran video call.Ameena tana ganin shigowar kiran tayi murmushi ta danna received da yake dakin akwai haske sosai kamar rana hakan yaba fateema damar fahimtar wani abu na damun addan ta daga yanayin fuskarta da kuma idanunta da sukayi jajur, ina yini adda.Lafiya fateema yaya kuke ya gidan ya su inna da baba malam.Lafiya kalau dukkansu meke damunki adda kinga idanunki kuwa?.Murmushi Ameena tayi tace me sukayi? Babu abunda ke damuna.A’a dai adda kowa zai ganki a wannan yanayin yasan baki jin dadi ko wani abu na damun ki dan Allah ki fada mun menene?.Fateema sarkin naci ciwon kai nakeyi fa kawai.Allah ya sawwaka ta fada ba don ta yarda ba.Ina shureim?Yayi bacci tun dazun, ta fada tana haska mata shureim din.Murmushi tayi tana jin kewar danta a tare da ita tana jin gurbin shi saidai babu yadda zatayi ne kawai.Adda kina Lafiya kuwa?. Fateema ta tambaya.Me kika gani?Naga kina tunani ne dan Allah ki fada mun meke damunki kada kisa na shiga damuwa.Kada ki damu kinji kanwata babu wani abu da akwai ai zan fada miki saboda bani da wacce ta kaiki balle ta fiki.Shikenan Allah ya mana magani.Ameen ya Allah.*****Abdul ganin lokacin daya dibar mata ya cika harya gota babu ita babu labarin ta yasa ya tashi da kwarin gwiwar zuwa ya mata fada ya fita sai dai yayi turus sakamakon ganin abincin a dining, kwafa yaja ya koma ya kirawo maryam suka fito tare suka zauna ya zuba musu indomy din, maryam ta karya wuya tace masoyi banga juice anan ba kuma kasan bakina babu dadi shine zai taimaka mun abincin ya samu ya wuce.Wani iri kike so in dauko miki akwaisu a fridge.A’a ba shi nake so ba hadin gida za’a mun na lemu zan danji dadin bakina.Kema dai akwai rigima baby bakiga lokaci yaja bane kuma ni ban iya hadawa ba Ameena ce ta iya kuma nasan yanzu kila ma tayi bacci.Yauwa masoyi please kasa ta hadamun in ba haka ba bazan ci abincin ba, ta fada tana tura baki gaba.Ya mike yana fadin baza’ayi haka ba barin same ta.Murgudawa bayan shi baki tayi tana dariya kasa-kasa.*****Tana kwance tana video call da fateema yayi knocking ta bude murya tace waye…Daga inda yake tsaye a bakin kofar yace waye kika san zai buga miki kofa da wannan daren ko kinyi appointment da wani zai zo ne?.Fateema ta cikin wayar ta zaro idanu waje tace what? Me nake ji yana fada? Mutumin nan fa ya fara wuce gona da iri.Babu ruwanki fateema tunda ba kece yawa ba ki kyale shi.Haba Adda ai tunda ya miki kamar ni ya mawa.Kinga ina zuwa kada ki katse kiran don ina jin dadin hirar yana debe mun kewa, daga haka ta isa bakin kofar ta bude bai shigo ba kawai yace maryam ce bata da appetite ki hado mata orange juice ki kawo mata muna dining kuma kada ki bata lokaci don naga yanzu kin koyo mugun hali.Gyada kai kawai tayi ya juya ita kuma ta rufe kofar da makulli ta juyo tana cewa yanzu kuma baka isa ba wallahi.Daukar wayarta tayi fateema tace Adda menene yake faruwa a tsakaninku ne na fuskanci akwai matsala dan Allah ki fada mun.Kada ki damu fateema zan fada miki amma sai kinzo don bana so inna taji.Shikenan gobe idan Allah ya kaimu zaki ganni.Toh nagode ki gaida inna da shureim.Zasuji sai da safe.Allah ya tashe mu lafiya.Ta ajiye wayar a gefenta tana sauke numfashi.*****Shiru shiru har yanzu Ameena bata kawo orange juice din ba maryam kuma na jira bata fara cin abincin ba ta kasa hakuri tace masoyi kaga fa bata kawo ba har yanzu.Kwafa yaja yama rasa me ma zaice mata bayan haushin Ameena daya cika ranshi yana ganin tama raina shi da zata dinga tsallake umurnin shi lallai ya kamata ya koya mata darasi.Masoyi inafa magana kayi shiru kasa ta kawo mun.Baice komai ba kuma baida niyyar tashi sannan ya tamke fuskar shi babu alamar yasan meye murmushi.Ganin haka ta mike da nufin tafiya dakinta yayi saurin riko hannunta yana cewa ina kuma zaki je baki ci abincin ba?.Masoyi daki mana zanje ai na fada maka bazan iya cin shi gaya ba dole sai na hada da lemu idan ina so ya shiga tunda bazan samu ba gara kawai inje in kwanta tunda naga kamar tsoronta kake ji.Kinga kiyi hakuri ki zauna barin kawo miki.Zama tayi shi kuma ya mike ya nufi kofar dakin Ameena ya tura yaji a rufe take ya hau bugawa yana kiran sunanta.Tana jinshi ta mai banza don ta gaji da rainin wayon sa itama zata gwada masa akwai zuciya a kirjinta bazata sake daukar raini ba.Haka ya gaji da bugawa ya gama fade faden shi ya koma ya shiga baiwa maryam hakuri akan taci indomy din ta hada da ko cock ne ko fanta, ba don taso ba ta hakura taci haka nan sai dai cikin ranta kudururruka ne fal ta yadda zata kuntatawa Ameena cikin sauki.Bayan ta gama cin bata damu data tattare gurin ba anan suka bar kulan da plate din suka shigewar su daki.Daga wannan ranar Ameena ta kuduri aniyyar zata fito tayi ayyukanta ta ajiye musu abinci a dining ta komawarta dakinta ta kwanta tana latsa wayarta, domin a wannan ranar ce ta fahimci batada abun da zai sanyata farin ciki sama da wayarta a cikin wannan gida nasu, a yanzu wayarta itace zata zama abokiyar ta itace zata zama mai debe mata kewa, ta kashe wayarta ta rufe idanunta tare da tunanin rayuwarta ta baya.*****WACECE AMINA?Ameena Ibraheem cikakken sunanta, mahaifiyarta Ruqayya suna ce mata inna su uku mahaifansu suka haifa yayanta Abubakar sai ita sai fateema itace autar su.Sun taso a gidane wanda yake cike da tarbiyya da sanin addini domin mahaifinta babban malami ne a garin nasu hakan yasa duk cikinsu babu wanda baiyi sauka ba kuma ya haddace Qur’ani tun suna kananan yara ‘yan shekaru sha hudu.Ameena da fateema tazarar shekaru biyu ne a tsakaninsu hakan yasa suka taso tamkar kawaye yayinda yayansu Abubakar an haife shi da shekaru goma sha daya har sun fidda tsammanin samun wata haihuwar sai Allah ya basu Ameena bayan shekara biyu ta kara haihuwar fateema daganan bata sake haihuwa ba.Ameena da fateema suna kama sosai har wasu suna kiransu da tagwaye domin idan kaga fateema zaka dauka Ameenace ba kowane ke iya bambance tsakaninsu ba sai in suna tare, don fateema tafi Ameena fadin fuska kadan da manyan idanu.ASSALAMU ALAIKUM, JAMA’A INA ROKON ALFARMAR DUK WANDA YACI KARO DA WANNAN LIGTTAFIN YAYI KOKARIN BIYAN KUDINSA DOMIN MALLAKINA NE KUMA HAKKINA,EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI✍️

Back to top button