Mijin Marigayiya Page 10 Hausa Novel
Ta gyara zama tace ‘Me kake cewa?’’Baki bawa yara abinci ba kin zo kin kama bacci.’Tana jijjiga kai tace ‘Kowa fa na bashi abinci baka gani bane?’’Habib da Nasreen nake magana fa.’’Oh, ba sun ce cornflakes zasu sha ba, ai akwai a kitchen din.’ ta fada tana kokarin kwanciya.’To ai sai ki zo ki hada musu ko?’Ta gyara kwanciyarta a cewa ‘Wallahi babe na gaji, idan ban yi baccin nan ba ko abincin dare ba lallai na iya dafawa ba. Suje su hada cornflakes din mana ko su ci tuwon da kowa ya ci.’’Ya ina miki magana kina kwanciya Khadeeja, haka zaki bar min yara da yunwa.’ ya fada a fusace.Ta gyara kwanciyarta tayi banza da shi. ‘Ina miki magana kina ji na fa Khadeeja bana son wulakanci.’Ta tashi zaune, lokacin ya riga ya mike tsaye. Ta gyara zama tace ‘To me zan ce maka?’’Ba zaki zo ki hada musu cornflakes din ba kenan?’’Hada cornflakes din ba wani aiki bane shi yasa nace su hada kawai, wallahi kaina ciwo yake.’ Ta ture abinda ta rufa da shi ta sauko daga kan gadon ta wuce bandaki saboda yanda bakinta ya cika da yawu, ta mako kofar bandakin ta tsaya a gaban sink; wallahi babu wani abinci da zata hada sai dai yayi duk abinda zai yi.Tana ji Nasreen ta leko tace ‘Abba yunwa nake ji.’Ya ja tsaki ya kama hannun Nasreen suka fice daga dakin bayan ya maka mata kofar a fusace.Haka ya je ya hadawa yaran cornflakes din suka zauna suka ci.………..Tun da ya hada musu cornflakes din nan kuma sai ya shiga share Khadeeja, gaba daya ya ki kulata ko zama inda take. Ta kula da hakan don haka ita ma sai ta ja jikinta, domin bata cikin yanayin ma da zata iya saurarensa.Ko da dare yayi ma har ta kwanta a dakinta sai kuma taga rashin dacewar hakan, tunda dai bai koreta ba kuma ita ba fushi takeyi da shi ba shi kadai yake fushinsa. Don haka bayan ta kwantar da yara sai ta shirya ta wuce dakinsa ta kwanta.Can wajen sha biyun dare motsin shigowarsa ya tasheta, yana tsaye a gaban wardrobe yana saka kayan bacci. Ta sauko daga kan gadon ta wuce bandaki don tayi fitsari ta kuskure baki. Tana fitowa ta wuce ta kwanta, ta kalleshi yana zaune a gefen gadon yana dannan waya; so take ta ce masa “good night Babe” kamar yanda ta saba amma bakinta ya ki furtawa saboda yanda take cike da haushinsa. Don haka sai kawai ta juya masa baya ta kwanta.Kamar wanda yake jira ta kwanta sai ya gyara zama a kan gadon yace ‘Tashi muyi magana Khadeeja.’Ta juyo ta kalleshi sannan ta tashi zaune ta jingine da jikin gadon; tana bakin cikin yanda yake kiranta Khadeeja gatsal sai kace shi ya yanka mata ragon suna.Bayan ta zauna ya kara tsuke fuska sannan yace ‘Bana son yanda kike yi min taurin kai da neman kawo min raini a gaban yara, idan ma wani abu ne a ranki gara ki fito ki gaya min.’Tayi murmushin yake tace ‘To, sai dai ban san lokacin da nayi maka taurin kan ba.’’Dazu nace ki hadawa Habib da Nasreen cornflakes kin ki, nan kika shige bandaki kika barni a tsaye ina miki magana.’Ta kalleshi suka hada ido ta kura masa ido har sai da shi ya kawar da kansa, ta bude bakinta wanda ya fara tara yawu tace ‘To in sha Allah zan kiyaye, amma nima don Allah ka dinga saukaka min rayuwa a gidan nan. Idan baka yi min saboda kauna ba to kayi min saboda yanayin da nake ciki tunda nima ba lafiya ce ta isheni ba duk abinda ka ga ina yi daurewa nake yi.’Ya dan fara saukowa yace ‘Duk don na nema miki saukin ne ai nace a kawo mai aiki, kuma da ta dawo zata cigaba da tayaki. Itama mahaifiyarsu haka take kula da su ko da kuwa tana da ciki don wannan ba wani abu bane a wajen macen da ta san me take yi. Bana son ki dinga yi musu abubuwan da zasu ji maraicin uwarsu, ki rike su kamar ke kika haifesu. Shine abinda zai samar da zaman lafiya tsakanin mu.’Ta gyada kai tana kallonsa cike da tsananin mamaki tace ‘To.’Ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki ta tofar da yawun bakinta ta daurayo bakinta ta fito ta kwanta bayan ta kashe fitila.Tana kwanciya hawaye ya fara bin idonta; wannan wace irin rayuwa ce? Wai dama haka ake aure ko kuwa itace bata dace ba? Shikenan shi da ‘yayansa ne kawai mutane? Kiri-kiri sai a kirkiri laifi a dora mata kuma a saka ta bada hakuri. Da ya barta da yaran tabbas tayi niyyar ta rikesu kamar ita ta haifesu, domin har addu’a takeyi kada Allah ya bata ikon cutar dasu. Sai dai zuwa yanzu gaba daya sun fice daga ranta, duk wata kauna da ta tanada don ta nuna musu bata jin zata iya tunda ga dukkan alamu ma ba zai barta ba. Shi ba so yake ta nuna musu kauna ba so yake kawai ta bauta musu, bata jin zata iya hakan kuwa.………A cikin wannan yanayin Khadeeja ta cigaba da lallabawa tana iya kokarinta wajen kulawa da yaran da gidan gaba daya.Kwana biyar aka yi da lockdown aka bada wuni daya mutane su fita su dan yi sayayya, don haka a wannan ranar Khadija take sa ran dawowar Habi mai aikinsu tunda Mustapha yayi wa Yaya Jidda magana.Tun safe take kiran Habi amma har azahar ba a daukan wayar sai bayan azahar sannan Habin ta dauka. Nan ta sanar da ita cewa mahaifiyarta ce bata da lafiya don haka wanen mai magani suka je, sai dai ko zuwa lokacin da za a sake bude gari shine zata samu ta taho idan mahaifiyar tata ta sami lafiya.Kamar tayi kuka haka ta ji domin tana ganin kamar dawowar Baba Habi zai rage mata wata wahalar; gashi azumi saura abinda bai fi kwana goma ba.A take dabara ta fado mata, ta dauki wayarta wadda ta juye; har ta nemo lambar Mommy zata kirawo sai kuma ta fasa ta kirawo lambar Baffa. Bayan sun gaisa ta sanar dashi tana so Nabila ta zo ta tayata zama zuwa lokacin da za a sake Bude gari in ya so sai ta tafi. Sai da ya Dan yi jim sannan yace ‘Kiyi hakuri Khadeeja,ba zata zo ba, haka aure yake. Kanwarki balagaggiya ba muharramar mijinki bace gashi gidanku ba wani Kato ba, ba zai yi ma’ana ba ana wannan zaman na wuni a gida na turo miki ita. Amma dai zuwa lokacin da za a sake Bude gari zan sa Mommy ta duba Miki dattijuwa wadda zata zo idan Kuma Mai aikin naki ta dawo ma shikenan. Kin gane ko?’’Na gane Baffa.’Sukayi sallama ta ajiye waya.Wani malolo ne ya taho ya tokare mata makogoro saboda takaici; yanzu Baffa ba zai bata Nabila ba kenan yana wani zance? Take hawaye ya wanke mata fuska, ta dauki wayarta ta shige daki saboda kada yara su sameta tana kuka.Tana ji tana gani aka sake mayar da garin aka kulle babu Baba Habi babu Nabila, haka ta cigaba da bautawa Mukhtar da ‘yayansa babu abinda ya sauya.……….Saura kwana biyu azumi aka sake bude garin na wuni daya saboda a dan yi sayayyar azumi. Tun da safe Mustapha ya sa ta shirya yaran ya kwashesu sai gidan Hajiya. Basu dade da fita ba aka buga mata kofa, kamar ba zata Bude ba da oda tana tunanin ko almajiri ne. Amma sai ta daure ta fito don ta bude da aka cigaba da bugawa.Tana budewa ta ci karo da Mommy tare da Nabila, Ahmad ne ya ajiyesu ya juya sai da yamma zai dawo ya daukesu. Tun a bakin gate ta rungumo Mommy suka shigo gidan tare tana ta murna.A nan parlor suka baje, ta sa Nabila ta dauko musu ruwa da lemon suna Sha suna hira.Daga baya Nabila ta tashi ta fara gyara mata gidan; ta barsu a zaune ita da Mommy suna hira.Mommy tace ‘Baffa dai yace kada a bar Miki Nabila, Mai aiki Kuma Ina ta cigitawa. Kin san yanzu duk tsoro ake ji saboda wannan lockdown din.’’Watakila ma yau Baba Habin zata dawo, zai iya yiwuwa ma tana can gidan Yayarsa tasa sai ya taho da ita idan zasu dawo.’…
