Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 35 By Ayshercool

Ba ta ƙara kula shi ba wunin ranar, dama kuma ficewa yayi ya bar gidan, ta rasa sai zuwa yaushe Al’amin zai yadda ya karɓeta su yi rayuwa, kullum ba shi da magana, sai maganar da zata tayar mata da hankali na zai rabu da ita, gaba Al’amin yayi hannun riga da duk wani nau’i na  tausayi.Abun da zuciyarsa ta raya masa kawai yake yi, ko ya yi maka daɗi, ko akasin haka ba damuwarsa bane ba.’yan yaran da suka din ga shigo mata yawon salla, su ne suka din ga ɗebe mata kewa da rage mata damuwa.Sai bayan sallar magariba sannan ta sake ganinsa, tun da ta yi masa sannu da zuwa, ta ajiye masa abinci, ta koma gefe ta na danna wayarta.Sai da ya ci ya ƙoshi, ya samu wuri a kusa da ita ya zauna, ya ce “Abun wasan, ya dai?”Ta ɗaga kai ta kalleshi ta sunkuyar, ta hau wasa da yastun ƙafarta.Hannunsa ya saka shi ma a yatsun ƙafarta yana tayata wasan da take yi da su.”Master””Mmm””Meyasa ka ke son lallai sai ka sake ni ne? Saboda ka ga bani da makoma ko? Ban taɓa burgeka, duk ƙoƙarin da nake yi, ba ka appreciating kullum cikin tsorata ni ka ke, kana gaya mini abun da zai ɗaga mini hankali, me nayi maka ne?””Baki dace da ni ba, da salihin mutum nagari ki ka dace. Da zan iya samun mutum mai amana da zai riƙe ki, zan iya rabuwa da ke ya aura, you  have an innocent soul, that doesn’t deserve someone like me, shiyasa nake yawan gaya miki haka. Ko jiya a fusace nake, na yi miki tsawa sai da ki ka yi kuka, ina ɗaukar hakkinki””To ni na ce maka bana son zama da kai ne? Ina yi maka addu’a, wataran zaka daina ai ko?” Tayi maganar tana kallonsa.Yayi shiru bai yi magana ba, “Dan Allah ka yi magana, zamu iya rayuwa tare, irin damuwar mu ɗaya, matsalar iyalan da muka tashi a tsakanin su, ba sai mu zama familyn junanmu ba, mu rayu cikin aminci da walwala. Amma master meyasa ka ke shaye-shaye bayan ka san yana da illa ga lafiyarka? Yana saka aikata abubuwan da bai kamata ba, kayi faɗa da mutane a zubar maka da jini, ko ka zubarwa wani, har kisan kai fa yake saka”.”Wa na kashe?”Ta ce “Ranar da na fara ganinka, a unguwarmu, gawar wani na ganka da ita ka soka masa wuƙa”Yayi murmushi, ya haɗiyi wani abu mai ɗacin gaske.”Ban taɓa kisan kai ba, ranar ce haɗuwarmu ta farko ko? Ban kashe kowa ba”Cikin damuwa ta ce “Amma wuƙa fa na gani a gefen cikinsa, kuma meyasa ka ke shaye-shaye?””Bana son silly question, rabu da ni” ta gyaɗa kai kawai ta ƙyale shi.Ranar hawan salla kuwa,  Jauhar ba ta san me ake yi ba, Al’amin ya haɗa yaransa, da miyagun makamai, da sunan tsaro kar wasu daga wani wurin su zo su fake da kallon hawan salla, su kawo musu farmaki su cutar da wani.Sai dai sun yi ba ta kashi da wasu marasa jin sosai da sosai, ciki kuwa har da yaran madaki.Sai da ‘yan sanda suka yi kame sosai da sosai, daga wurin hawan Al’amin bai koma gida ba, ya wuce cikin gari, saboda kar jauhar ta ganshi da makami, da jini.A cikin garin ma, sai da suka yi wata fitinar, aka yi sare-sare da faɗace-faɗace.Sai bayan kwana biyu, jauhar take jin labarin abun da ya faru a wurin hawa, ganin Al’amin lafiya ƙalau ya sanya ta kwantar da hankalinta, tare da bawa kanta yaƙinin cewar babu shi a rigimar.Kwana na huɗu, tana kitchen tana girki, tana shirin kaɗa miyar cin tuwo, maman halimatu ta shigo gidan a gigice.Jauhar ta ce “Maman halimatu lafiya kuwa?””Ke kina nan baki san abun da yake faruwa ba?”Cikin rashin fahimta ta ce “A ina?””Wani ɗan daba ne wai madaki, daga can unguwar ku ya zo unguwar nan wai neman mijinki, wai ya illata masa yara, sai tarwatsa mutane suke yi, suna sara kan mai uwa da wabi a guje na ƙaraso”Cikin tashin hankali ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un” take kanta ya sara, jikinta ya hau rawa, ta ɗauki wayarta ta kira lambar sa, sai dai tayi ta ringing baya ɗagawa.Hijjabinta ta ɗauka, maman halimatu ta ce “Ina zaki? Saran mutane fa suke yi, duk wanda suka samu duka ko sara”.Ai ba ta ko tsaya bata amsa ba, ta fita cikin matsanancin sauri da tashin hankali.Ba ta san in da za ta nufa ba, addu’a kawai take yi da roƙon Allah, Allah ya tsare mata mijinta.Mutane na guje-guje ita kuwa kutsawa take tana duba ina zata ganshi tana kuka.A wani layi ta hango shi, ya riƙe wani matashi, idon Al’amin kawai ta kalla ta san a buge yake, babu alamar mutunci a idonsa, idanun sun yi jawur sai gumi yake yi, yanayin sa ya tabattar mata da ya tafka ɓarna, kafin ta ƙarasa, ya fito da harshen sa waje, kamar yadda yake yi, idan ya ƙudirci aniyar yin wani abu, ya ɗaga sweazland ɗin sa, babu tsammani ya ganta a gabansa, ta riƙe rigarsa tana girgiza masa kai cikin tsananin tashin hankali.”Idan ka kashe shi, rufe mini kai za ayi, ba lallai na sake ganinka, ka yi haƙuri kar ka yi kisan kai dan Allah”Jikinsa tsuma kawai yake yi, ya aiwatar da abun da zuciyar sa take raya masa, saboda yadda haɗin da yayi amfani da shi, yake fizgar kansa yake jin sa tamkar jinjirin doki, zuciyarsa kuma kamar an kunna wuta.Ta rirriƙe hannun da ya riƙe wuƙar da shi, da hannu ɗaya ya yi jifa da matashin gefe, shi kuma ya saki wuƙar, sai tangaɗi yake yi, ya kasa tsayuwa, sai gumi da yake tsatsafo masa ya furta “Madaki” kawai ya yanke jiki ya faɗi, sai a lokacin ta ga uban saran da yake gadon bayansa, ashe duk abun nan an sare shi a baya, rigarsa ta rine da jini ta baya.Wani irin gigitaccen kuka ta saki, ta ce “Na shiga uku, dan Allah ku taimaka mini a kai shi asibiti” tayi maganar tana girgiza shi. Ya kalleta da idanunsa, suka yi jawur, jikinsa ya fara rawa ga gumi ya jiƙa masa fuska.Ragowar mutanen da suke wurin, suka dare suka bar ta da shi, a wurin.”Master dan Allah kar ka rufe idonka, yanzu zamu tafi asibiti, Allah ka kawo mini ɗauki, Allah ka duba lamarin nan”.Guduma ne ya shigo cikin layin da gudu, ya jefar da makamin hannunsa ya ƙaraso, wata irin ajiyar zuciya ta saki, yana zuwa ya jijjiga Al’amin ya ce “Master” sai dai idanunsa sun lumshe, saboda jinin da ya zubar.Yayi ƙoƙarin ɗaga Al’amin, ya saɓa shi a kafaɗarsa, amma abu ya gagara, ba ƙiba ce da shi ba, sai dai akwai nauyi.Ya kalli Jauhar da ta rikice, take ta kuka ya ce “Anty ki kwantar da hankalinki, in sha Allah yanzu zamu kai shi asibiti”.Ya din ga wani irin fito, kan ka ce kwabo, wasu matasa suka din ga ɓullowa da ɗaya ɗaya, su ma suna fiton wasu suna fitowa.Suna zuwa suka yi tara-tara suka sunkuci Al’amin, guduma ya saɓa shi da ƙyar, suka nufi titi. Da ƙarfin tsiya suka ƙwaci ‘yar ƙurƙura a titi, suka ce mai ita ya bi su Asibiti ya karɓa.Sai dai da suka je, ma’aikatan lafiya, suka ce ba za su karɓe shi su duba shi ba, sai da jami’an tsaro.Cikin kuka ta ce “Dan girman Allah kar ku yi mini haka, ku ceto ransa kar ya rasa ransa, dan Allah ku fara duba shi, kan a kawo ‘yan sandan” ma’aikatan suka ƙeƙashe ƙasa suka ce, sai fa jami’an tsaro sun zo”.Ta din ga rusa kuka a cikin emergency, guduma sai bata haƙuri yake yi.Ta kasa jurewa, ta tashi ta bi wani likita, ta riƙe rigarsa tana kuka ya ce “Dan girman Allah ka ceto rayuwar mijina, kar a rasa ransa dan Allah”Ya ce “Ba laifina bane ba, dole mu san meyafaru kafin mu taɓa shi”.Kan kace kwabo, sashen emergency ya cika da ‘yan daba, saboda an kawo al’amin.Babu tsammani ta ga shigowar liti tare da Walid, da wasu tawagar marasa jin suna take musu baya.Suka ƙaraso, in da jauhar ke zaune, da Al’amin a gabanta.Walid ya ce “Madam, ya aka yi haka ta same shi?”Ta girgiza kai ta ce “Ban sani ba, kawai ce mini aka yi ana faɗa, na je na tarar da shi, da zai cakawa wani wuƙa amma ya fasa, kawai dai ya ce madaki ya faɗi ashe an sare shi, kuma sun ƙi duba shi wai sai ƴan sanda sun zo, dan Allah ka saka baki yaya Walid.Ya kalli liti ya ce “Zan ɓallo ruwa, a toshe magudanan daga waje” liti ya jinjina kai, ya ja guduma suka fita.Wasu daga cikin matasan suka shigo, suka koro wasu daga cikin majinyata waje, suka ritsa likitoci da makamai, sai sun duba Al’amin.Aka ce su kai shi kan gado, Walid ne ya ɗauke shi, suka kai shi kan gado, saran da aka yi masa ba ƙarami bane, yayi zurfi, hakan ya ƙara razana Jauhar.Liti ya ce “Wannan yankan madaki ne yayi masa shi, wannan shegiyar wuƙar da aka ce ta tsafi ce, da ita yayi masa saran”.Jauhar ta ce “Na shiga uku, ba zai tashi ba kenan?”Walid ya ce “Zai tashi ki kwantar da hankalinki”Aka yi wa Al’amin ɗinki, kamar ƙwarya aka ɗinke bayansa, sai dai walid ba su bari an yi a gaban jauhar ba, aka ɗibi jininsa, dan dubawa idan sai an ƙara masa jini, sai dai baya buƙatar ƙarin jini, sai dai an saka masa ruwa saboda jirin da yake yi ya hana shi tashi.Ana tsaka da duba shin, jami’an tsaro suka iso, Walid ya ce kar matasan nan su bar su su shigo, sai an gama yi masa komai.Aka din ga artabu da ‘yan sanda da dandazon, yaran da suka yi wa harbar emergency ƙawanya, da kyar ‘yan sandan suka shiga.Da ƙyar aka tarwtsa tarin matasan nan, tana zaune ta ƙurawa fuskarsa ido, ƴan sanda suka ɗauki statement ɗin abun da ya faru.Jauhar sai addu’a take yi, tana fatan Allah ya sa ya farfaɗo.Ta riƙe hannunsa, tana shafawa a hankali ta ce “Allah ya shirya mini kai, ya baka lafiya master, inuwarka ce kawai nake tsaye a ciki nake saka ran samun farin ciki, dan Allah ka daina zuwa ana cutar mini da kai”Idonsa a rufe, ya ɗaga hannunsa a hankali, ya shafi fuskarta sannan ya buɗe idon a hankali ya kalleta sai dai bai yi magana ba.”Sannu master, an yi maka ɗinki a bayanka, akwai abun da yake yi maka ciwo ne?” Ya girgiza kai almar a’a.Ta shafi sumar kansa ta ce “Allah ya baka lafiya”Juyi yayi a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, muryarsa ƙasa-ƙasa ya ce “Idan kina kuka ciwon ƙara zafi yake yi” ta goge hawayenta ta ce “To na daina, amma idan aka ji maka ciwo, zuciyata ce take kuka ba na so master” tayi maganar hawaye na kwarara daga idanunta.A hankali yake matsa hannunta, yana jin wata nutsuwa ta mussaman, da sassaucin zafin da zuciyar sa take yi masa.Zuwa magariba, ya miƙe ya ce sai sun tafi gida, Jami’an tsaro suka ce za su tafi da shi, sakamakon tayar da tarzoma a unguwa.Walid ya ce “Saboda hauka ake yi, master ku ware gida, ni ku tafi da ni mu muka je muka tayar da tarzomar”Ana fito da Al’amin, guduma ma ya taso, da sauri, Al’amin daga shi sai dogon wando, suka tari napep suka tafi gida.A wurin maman halimatu jauhar ta karɓi mukulli, ta buɗe musu gidan suka shiga.Ta saka yayi wanka, yayi alwala ya rama sallolin da ake bin sa, ta kawo masa abinci ya ci.”Master” ya kalleta “Dan Allah ka fita daga shirgin madakin nan, ba shi da imani, kar ya hallaka ka dan Allah”Ya girgiza kai ya ce “Sai dai ɗaya yayi ajalin ɗaya ko ni ko shi, shari’ata da shi, Allah ne kawai zai rabata”Cikin rauni ta ce “Ina haɗaka da girman zatin Allah””Shhhh, ki daina haɗa ni da Allah, kin san nauyin abun da aya aikata mini?””Ban sani ba, amma ina da yaƙinin koma me zaka yi masa, ba zaka huce ba, ka yi haƙuri ka bar wa Allah mana, idan wani abun ya same ka ya zan yi ne? Yanzu kalli halin da ka sakamu a ciki, na san yanzu haka a cikin pain ka ke, ciwon a jikinka yake, amma a zuciyata nake jin raɗaɗin, haba master, haba dan Allah” tayi maganar wasu zafafan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta.Ya miƙa hannunsa ɗaya da ba a side ɗin ciwon yake ba, ya janyota jikinsa, ba ta musa ba ko yi masa gardama, ta kwanta sosai ta cigaba da kukan, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa sosai, kasancewar babu riga a jikin sa.”Ba zan ɓoye miki ba, ban taɓa tunanin zan yi wata alaƙa da wata ‘ya mace ba, saboda ina yi musu kallon azzalumai, ke ki ka fara canza tunanina”.Al’amin Ibrahim shi ne cikakken sunan Al’amin, mahaifinsa haifaffen garin kano ne, gidansu gidan yawa ne, baban Al’amin shikaɗai ne a wurin mahafiyarsa da ta daɗe da rasuwa, sai tarin ‘yan uba da galibinsu mata ne.Yayi karatu daga primary zuwa sakandare har yayi diploma, sai dai aikin yi ya gagara samuwa, akwai abokinsa sammani da suka yi karatu tare, tare suke yawon neman aiki, ya ja shi garin su tofa, aka samo musu gona, suka fara noma.A can ya haɗu da Zahra’u, ya ce yayi mata, da fari tsokanarta yake yi, saboda kwalliyar da take yi ta ‘yan ƙauye ce take bashi dariya, daga baya soyayya ta ƙullu a tsakaninsu.Abu kamar wasa, har ta kai ga aure, duk da bashi da wata ƙwaƙƙwarar sana’a, sai kame-kame.Sun sha gwagwarmayar rayuwa tare, sun yi faɗi tashi, sun yi fama da yanayin rayuwa, kafin Allah ya buɗa masa ya fara samu.Lokacin da suke cikin wahala babu mai taimakonsa, daga shi sai ita suke wahalar su, ta samu ciki a lokacin ta haifi ɗan ta na fari, aka saka masa Abubakar Assidiƙ, sai lokacin da Allah ya fara buɗa masa, ‘yan uwansa suka saka musu ido, da surutun yana zaƙewa da yawa a kanta.Komai ya samu ita, ya tashi daga tsakiyar cikin garin kano, ya koma gwauron dutse yayi mata gida mai kyau.’yan uwansa suka fara tsangwamar ta, da cewa ta shanye musu ɗan uwa, Ibrahim ya mayar da ita makaranta ya samo mata admission a FCE, ta ke karantar English islamic. Kasancewar ta mace mai kyauta, da fara’a da sakin fuska ga mutane, ya sanya take da masoya sosai. Sai dai duk da kyautarta, da son mutane dangin mijinta ba sa ƙaunarta.A can gwauron dutsen, ta haɗu da wata mata rahila, maƙwabciyarta ce, tana yawan zuwa ta kawo mata complain a kan mijinta ba ya kula da ita da yaranta, hakan ya sanya tausayin rahila ɗarsuwa a zuciyar Zahra’au, kusan kullum cikin yi wa rahila aike take, na abun da zata kula da yaranta, kuɗi, sutura, abinci kayan masarufi, saboda Ibrahim yana sakar mata sosai baya yi mata iyaka da komai.Tana NCE 2, Sadik ya shekara biyar, ta samu ciki, tayi ta fama ga laulayi ga karatu, rahila take barwa Abubakar ta tafi makaranta, ƙarshen wata, take biyanta da kuɗi mai kauri saboda ita ma ta samu.Ta haifi ɗanta na biyu, aka saka masa Muhammad Al’amin, saboda haihuwar maza da take yi, dangin miji, suka ƙara yi mata caaa wai tana ta haifar maza, dan ta kwashe komai na gado idan ya mutu. Tana iya ƙoƙarin ta wurin saka Ibrahim ya yi kyautata musu su ma, amma ba sa gani sam.An yi shagalin suna sosai da aka haifi Al’amin, saboda yana tashen kuɗi a lokacin.Tana kyautatawa ‘yan uwanta na ƙauye ma, ciki har da sauran danginta da ‘yan uwanta.Rahila ta shiga ta fita, ta zama ƙawar Zahra sosai da sosai, Ibrahim ba ya ɓoye son da yake yi wa zahra, dan ko a gaban waye ko sun yi faɗa ba ya canza mata suna daga baby Zahra, ciki har da gaban ‘yan uwansa.Makaranta mai tsada sosai ya saka Abubakar, tun Al’amin bai cika shekaru uku ba, shi ma aka saka shi, saboda kukan da yake yi idan Sadik ya tafi makaranta.Akwai soyayya mai ƙarfin gaske da shaƙuwa, a tsakanin Abubakar da Al’amin, cikin soyayya da kulawa suke rayuwarsu a tskanin Abbu da ummin su.Ibrahim ya biya wa kansa umara, ya je da shi da Sadik, shekara ta zagayo, ya biya wa Zahra da Al’amin suka tafi, hakan ya ƙara hiafar da cecekuce a tsakanin dangin Ibrahim, wai saboda tsabar mugunta, ya biyawa yaran da zuwansu umara makaruhi ne, alhalin su ga su.Sai dai a lokacin da suke maganganun, a lokacin yake ƙara nuna wa duniya irin son da yake yi wa Zahra da yaransa, a cewarsa ita ta juri tsantsar talaucinsa, yanzu kuwa dole ta huta fiye da kowa. Ta kammala karatun ta, ya ce sai ta juya degree, ta ce ta gaji, hutawa za ta yi, ya ce bai yadda ba.A lokacin ba ta da wata aminiya da ta wuce rahila, rahila ta yi ta cewa kashe aurenta za ta yi, saboda ta gaji da zama da mijinta baban su Abba, Zahra tayi ta rarrashinta da nuna mata illar hakan, ta ƙara ƙaimi wurin taimakawa rahila, dan kuɗin makarantar su ma, ita take biya, tana bawa Rahila haƙuri a kan ta zauna ta kula da yaranta.Dangin Ibrahim tsanar da suke yi wa zahra’u, suka haɗa har ‘ya’yanta, suka din ga cewa asiri ta yi masa ta mallake shi.Duk ƙoƙarin da Zahra ke yi a kan rahila, sai da ta kashe auren nan, ta ce ba zata iya ba ta gaji da rayuwar matsi, zahra ta sha bata labarin wahalar da suka sha, kan Ibrahim yayi arziki sun sha kwana fiye da uku, ba su ɗora tukunya ba, amma ta ƙi fahimta.Ibrahim yana ta fafutukar, ta tafi bautar ƙasa, ta hau laulayin wani cikin, dan ma Allah ya taimake ta, ba ta ɗaukar ciki a kai a kai, dan lokacin, Al’amin ma ya kusa shiga Jss1 Abubakar yana da shekaru goma sha biyar.Ta haɗu da ciki mai laulayi sosai da sosai, hajiya mamanta ta ce, ta koma gida ko wata ɗaya tayi, a kula da ita, Ibrahim ya ce tayi haƙuri, a bar masa matarsa yana kula da ita.Rahila tayi ta zuwa tana yi mata aikace-aikace, da kula mata da su Abubakar.Sadik da Al’amin su na da banbancin halaye, Sadik yana da haƙuri, da fara’a kamar ummin su, Al’amin kuwa sa ne, ba ka dariya sai hamma. Ba ya fara’a ko wasa a cikin yara baya yi. Idan kuwa yayi wasa cikin yara to tabbas sai wani yayi kuka, domin kuwa wasansa na kasada ne, kwaikwayon tsalle-tslle, da wrestling shi kawai yake yi.Idan ka ga yana wasa wasu lokutan, ko yana dariya, tare da Abbu ne, ko Abubakar, Ummin ma faɗa suke yi, saboda tana yi masa faɗa a kan, rashin jin da yake yi na kasada.Tun da suka ga Ummi da ciki suke murna, Abbu ya ce musu, baby girl za a haifar musu, Al’amin ya din ga murna, shi ma za ayi masa ƙanwa, yana son ya ga yana da ƙanwa mace, ya din ga hasaso irin kulawa da gatan da zai yi mata.Yana jss1 sport master ɗin su, ɗan karate ne, Al’amin ya takurawa Abbu yayi masa register a makarantar karate, Ummi ta ce ba ta so, ya daina biye wa Al’amin, amma ya ce mata ba a dankwafe yaro.Ta sha wahalar cikin nan sosai, da ya isa haihuwa, sai tiyata aka yi mata, aka ciro baby girl mai kama da ita, tun a asibiti ya ce sunan zahra zai saka mata. Nan ma ‘yan uwansa suka hau surutun, bai saka sunan uwarsa da ta mutu ba, sai na mace, macen ma ‘yar ƙauye.Al’amin ya ƙallafa ransa a kan jaririyar nan, ko Sadik da yake yayansa, sai ya yi da gaske yake bari ya ɗauketa, ‘yan barka ma rashin mutunci yake yi musu, ya ɗauketa ya ƙanƙame ya haɗa rai yana muzurai, ba za a ɗauketa ba.Ana ta shirin suna, jikinta yaƙi daɗi daga ita har jaririyar, jaririyarma jaundice ya kamata, sai da aka sakata a kwalba, kwananta biyu ‘yar ta koma ga Allah.Al’amin ya shiga tashin hankali, ko abinci ya ƙi ci, saboda yadda Allah ya saka masa son yarinyar.Zahra ta din ga wani irin zazzaɓi, haɗe da jijjiga, sai da aka kaita ɗakin duhu, an kaita da daddare da asuba ita ma ta koma ga mahaliccinta.Tamkar ƙaramin yaro, haka Ibrahim ya din ga kuka, ya fita hayyacinsa, duk da ƙanƙantar shekarun Al’amin, ya san mutuwa, ya san idan aka yi ta ba a dawowa.Sai dai ya kasa kuka, baya magana, baya cin abinci, saɓanin sadik da ya din ga kuka, da yawa sun ɗauka tsabar taurin rai ne, na Al’amin ya sanya ya ƙi yin kuka, sai dai a kwana na uku da rasuwar zahra’u, aka wayi gari aka tarar ya sassanƙare, jikinsa babu numfashi. Shima aka kwashe shi zuwa asibiti.Ibrahim da sadik, suka ƙara shiga matsanancin tashin hankali da kiɗima, sai Alhaji sammani da dangin zahara’u da rahila, su ke ta damuwa.Sai da Al’amin yayi sati biyu a asibiti, ƙarƙashin kulawa ta musamman, bai taɓa zaton haka yake ƙaunar ummi ba, haka yake sonta ba sai bayan ta mutu.Aka watse daga zaman makoki, Hajiya ta ce “A bata su Sadik ta tafi da su, kan ya samu yayi wani auren”. Nan ma ya ce shi dai tayi haƙuri ta bar masa yaransa. Ta ji haushin hakan, saboda a ganinta ita ma ‘yarta ta rasa, yakamata ko yaya a ɗan bata yaran za ta ji daɗi.Ya zamana daga shi sai su a gidan, wtaran haka yake saka su a gaba, yayi ta kuka, Sadik yana taya shi, Al’amin kuwa sai dai ya kom gefe yayi shiru idanunsa sun yi jawur, yayi ta ciwon kai.Ibrahim ayi musu wanka, ya kai su makaranta, lokacin tashi, ya baro kasuwa ya zo ya kai su restaurant su ci abinci, su shirya zuwa islamiyya.Sanin halin ‘yan uwnasa ya sanya ya fito da duk wani abu, da abu da ya san mallakawa zahara’u, ya ce a raba wa su Al’amin, shi ya yafe gadon.Nan ma ya sha caccaka da baƙaƙen maganganu, gaba ɗaya walwalar gidan ya zamana babu, rahila ta tsiri sintiri, da zuwa ganin su Sadik, ta yi musu hidima, Ibrahim ya nuna mata ba ya so, ita kuma ta ce saboda Allah take yi, da zumuncin da yake tsakanin su da Zahara.Sai dai a gefe, ta fara shiga malamai, dan ya auret, ta bi ta wurin sammani abokinsa, a kan ya lallaɓa shi ya aureta, ta kula da yaran Zahra’u, ita dai tana ƙaunar su fisabilillahi.Sammani kuwa ya wuce mata gaba, duk da Abbu ya nuna ba ya so, shi hana cikin alhinin rashin matarsa, amma tasirin sihiri, da yadda sammani ya din ga lallaɓa shi, da nuna masa saboda yaran zai yi auren, ya haƙura ya auri Rahila, ta tare da nata yaran har su uku.Hajiya ta ji haushin hakan, ta san alaƙar rahila da Zahra’u, amma ta so ko yaro ɗaya ya bata, saboda Zahra ce kawai ta rage mata, sai da ta binne ‘ya’ya bakwai, ita ma da ta tsaya, ta koma ga Allah sai ƙanwarta guda ɗaya da suke uba ɗaya, baban su ya rasu babarta ma da ta kasance abokiyar zamanta ta mutu ta bari, ta riƙeta kamar ‘ya.Da fari kamar gaske, Rahila take kula da su, dan sadik ya fara sakewa da ita, tun da dama sun santa, ban da Al’amin da mutuwar umminnsu ya ƙara masa miskilanci.Aka shafe shekaru uku, ko ɓatan wata ba ta yi ba, duk da tana kamantawa, amma ba ta iya ɓoye banbancin su da ‘ya’yan da ta haifa. Ibrahim ya riƙe mata nata yaran, ganin nasan ma suna samun kulawa daga gare taSannu a hankali, ƙawaye da dangin Ibrahim, suka nusar da ita, duk wannan wahalar da take yi, a banza, tun da ba ta haihu da shi ba, kuma yaransa maza ne, dan haka ta nema wa kanta mafita.Nan ta ƙara riƙe wa bin bokaye wuta, ta fara ƙoƙarin cire wa Ibrahim son yaransa, saboda yadda yake tsara irin rayuwar da yake son ɗora su a kai, duk da yana kamanta yi mata kara a kan ‘ya’yanta kamar nasa, amma yana nuna wa su Al’amin so, mussaman Al’amin da yake ƙarami, kusan kullum yana tare da shi, wataran ya ƙi cin abinci, sai ya zaunar da shi ya bashi, ko ya kwana da shi wuri ɗaya, saboda ya ɗebe masa kewa.Wannan soyayar ba ƙaramin ƙular da rahila take yi ba, dan haka ta zage, da shiga da fita, a hankali soyyayar da yake yi musu, ta fara ja baya, ta fara wulaƙanta su, tana hantarar su, ba ta tsaya a nan ba, ta haɗa da hana su abinci.Sadik take iya sarrafawa, yadda take so, ban da Al’amin, da kome za ta yi masa ba zai yi abun da take so ba.Ibrahim ya zo ba ya iya cewa komai, azaba iri-iri, duk wani laifi da Al’amin zai yi, Sadik zai karɓi hukuncin, ba ya ƙaunar ya ga an taɓa masa Al’amin.A haka ta samu ciki, tana murna tana fatan ta haifi namiji, ta haifo ‘ya mace,  wato shahida.Ba haka ta so ba, amma ko ba komai dai hankalinta ya kwanta ta haihu da shi.Ta frara yi wa su Al’amin horon yunwa, tunanin Sadik, yaya zai samo abun da zai bawa Al’amin, ƙiri-ƙiri da gatansu, amma Sadik har jari bola yake yi, saboda ƙaninsa, ya san Al’amin ba ya ga maciji da yunwa ko kaɗan.Mutanen unguwa suka fara surutu, amma tayi burus da su, a lokacin ne suka sake komawa cikin gari ɗan agundi, saboda matsalar da Abbu ya samu a kasuwa, na damfara da aka yi masa amma gida suka koma mai kyau shi ma.Ta saka Abbu ya ɗaukar mata yaranta, Abba da Nazir yake tafiya da su kasuwa, amma ta hana ya din ga tafiya da su Sadik, lokacin Sadik yana da shekaru ashirin, Al’amin kuma sha biyar.Ta saka ya cire su daga makarantar kuɗi zuwa ta gwamnati, ta nu na wa ‘yan uwansa ta fi su iya barikanci, ɗan tallafi duk da yake ba su ta hana gaba ɗaya.Hajiya sai dai ta zo ganin su Sadik, ba za a taɓa barin su, su je in da take ba, wani zuwa da tayi ta shiga tashin hankali, ganin Al’amin na yawo ko takalmin sawa babu. Ta ce “Rahila ki ji tsoron Allah, zumunci bai ce haka ba, wane irin riƙo ki ke yi wa yaran nan haka?”Ta kada baki ta ce “Irin riƙon da ya dace da su mana, idan bai yi miki ba ki kwashi tsiyarki ku koma ƙauye”Ibrahim ya dawo, ta kitsa masa ƙarya da gaskiya, ya ce wa Hajiya kar ta sake zuwa, idan yakamata ya sako su a gaba ya kawo mata su ta gansu.Tana kuka Sadik na kuka, ta koma, ta ce da yardar Allah, ba zata sake taka gidan ba, da sunan zuwa ganin su Al’amin.Al’amin duk ranar da yake jin yunwa, sai ya kwanta ya ce ba shi da lafiya, ba za shi makaranta ba, aikin ƙarfi babu wanda Sadik baya yi, saboda kar Al’amin ya zauna da yunwa saboda ya san baya jureta ko kaɗan.Ta kai ta kawo, Rahila har sakawa take Abbu ya kama Sadik ya zane shi, dama Al’amin ba ya taɓuwa, tun ranar da ta saka aka dake shi, Abbu na fita, ya kama Nazir a waje, yayi masa dukan kawo wuƙa, duk wani skills da yake samu, a wurin karate ya sauke su a kan Nazir da ya ma ɗan girme shi.Amira kuwa bala’in tsoronsa take ji, tun da ya taɓa ball da ita, ta targaɗe hannu.Rayuwa ta cigaba a haka, har Al’amin ya yi candy, Sadik ya tsaya tsayin daka, ya shiga polytechnic.Abbu ya bar su babu sana’a, ba abun yi, ya cire hannunsa daga kan karatunsu, amma ya ɗauki agololi ya kai kasuwa.Ana haka ‘yan daba ƙanana masu tasowa suka addabawa unguwar , su yi sare-sare, ko su je su tsokano ‘yan wata unguwar. Ga Al’amin da yawon tsiya, idan yayi dare sai Sadik ya fita nemansa, idan ya gano shi da ƙyar suka dawo gida, sai su tarar Abbu ya rufe gida, wai sun tafi yawo, su koma in da suka tafi su kwana.Rayuwa ta yi wa su Al’amin tsanani, ga rashin uwa, ga ƙiyayyar uba, da makircin matar uba, ga ƙiyayyar dangin mahaifi, dangin uwa kuma sun watsar da su.Aka zaɓi Al’amin a cikin matasan da zasu je youth game, su wakilci Nigeria, Rahila ta ziga Abbu ya ce ba za shi ba.Aikuwa ya zuciya, ya bar gidan, ya ce barin garin zai yi, Sadik ya dawo yana nemansa, Amira ta gaya masa abun da ya faru, ya bazama neman Al’amin, da ƙyar ya gano shi, ya lallaɓo shi suka dawo gida, Amma suka tarar Abbu ya rufe gida, ya ce shi ma Sadik ɗin ya bi Al’amin su bar duniyar ma gaba ɗaya ba garin ba, ba ɗan iska bane shi, da za su din ga dawo masa gida bayan goma na dare.Sadik ya din ga rarrashin Al’amin, da ya riga ya zuciya, ya samo musu aron tabarma, suka shimfiɗa suka kwanta a waje, Cikin dare aka tashi faɗan daba, suna cikin bacci Al’amin ya ji an buga masa abu a ka, ya tashi a gigice, bai gama wartsakewa ba, aka danƙo shi, za’a soka masa almakashi, Sadik ya tashi a rikice, ya riƙe almakashin ya ce “Bawan Allah me muka yi muku? Mu ba ‘yan daba bane””Amma ai ‘yan unguwar nan ne ko? Fansa muka shigo ɗauka, dan haka duk kan wanda azal ta faɗa shikenan” ya fizge Almakashin ya soka wa Sadik a cikin sa! Maimakon Al’amin.

Ayshercool 08081012143

Back to top button