Hausa novels

Fentin Zina Page 3 Hausa Novel

Ka taimakeni kace? Ka rufa mun asiri? Na rokeka ne? Ko na tsugunna a kasa na rokeka ka aureni? A gidanmu a wahale ka ganni? Kona munafurce ka ban fada maka gaskiya game dani ba iyye?Ta durkushe a gurin tana fasa kuka mai karfin gaske yayinda ko ina a jikinta ya kama bari.Abdul kam rasa ma me zaiyi yayi domin nadama ce ta shige shi lokaci daya, mema yasa ya bude baki daya sani shiru yayi, magana zarar bunu idan ta fita bata dawowa, ya rasa inda zaisa kansa sai ya tsugunna ya kai hannu zai tallabeta.Da wani irin power ta mike tsaye kada ka tabani, nii…Ta nuna kanta da yatsa har yanzu bata bar kuka ba, bana bukatar taimakon ka! Bana bukatar ka rufa mun asiri Allah! Tayi pointing saman silling Allah shine gatana shi zai rufa mun asiri amma ba kai ba, don haka yanzu ba sai gobe ba gidanmu zan tafi inyaso ka biyo ni da takardar sakina.Ta fice fuuu kamar zata tashi sama ta shiga dakinta tana kuka sosai abubuwan da suka faru a shekarun baya suna dawo mata cikin kwakwalwar ta kamar yanzu ne abun ke faruwa.A kidime ya biyo bayanta ko kafin ya iso harta banko kofarta, dafe goshi yayi kana ya isa ga ainahin kofar falon ya rufe da makulli ya zare makullin ya koma kan kujera yayi tagumi cike da tarin nadamar abunda ya aikata bai taba jin ya tsani saurin fushin shi ba da rashin iya sarrafa kai sai yau.Bai jima da zama kan kujerar ba ta fito jaye da trolley dinta sanye da hijab daya kusan kai mata kasa don rabin hijabanta haka suke.Ko kallon inda yake zaune bata yi ba ta nufi kofa ta murda da nufin budewa saidai me? Taji ta a rufe jingina tayi jikin kofar idanunta a rufe ta gangara ta zauna a kasa sam bata jin kuzari a jikinta kona sisin kwabo.Saukar numfashinsa taji a saman fuskarta wanda ya tilasta mata bude ido ta saukesu a tashi fuskar.Hankalin shine ya tashi sakamakon ganin idanunta yadda sukayi jajur tamkar gauta.Kama hannunta yayi ta fisge, ya kara kamawa ta kuma fisgewa karshe jawota yayi ya rungumeta sai kuwa ta fashe da kuka sosai take yin kukan.Bubbuga bayanta yakeyi domin yasan bayada wata kalma data rage da zaiyi amfani da ita wurin rarrashinta daya wuce wannan hanyar daya ke bi yanzu.Sai da yaji ta lafa da kukan sannan dakyar ya harhado kan kalmomin da suka danyi saura a kwakwalwar sa ya ja iska cikin bakinsa ya huro waje cikin kwantar da murya yana ci gaba da buga bayanta cikin wani irin salo yace.Nayi kuskure! Ni mai laifine a gareki amma ina neman sassauci daga dukkannin hukunci da zaki yi akaina, kiyi mun ko wani irin hukunci zan dauka amma dan Allah na rokeki ki agajeni ki sassauta mun kada kice zaki rabu dani, rayuwata zata zam tamkar tokar da iska ke kwasa yayinda babu ke a cikinta, nayi nadamar abunda na aikata tun ba’aje ko ina ba kiyi hakuri bazan sake ba na rokeki.Da wani irin karfi wanda bata ma san tana dashi ba ta leave jikinta daga nashi ta mike tsaye tana kada kai.Bazan iya yadda da maganarka ba a halin yanzu bansan ko nan gaba ba Amma ka riga da ka rusa duk wata martaba da kimar da take tsakanin mu, kullum magana daya kake fada mun cewar bazaka sake ba sai yaushe zaka daina tozartani kana cin mutumcina akan abunda ya wuce? Meyasa mutane bama yiwa juna uzuri ne? Ni dai nayi Imani da Allah duk tarin laifukan dana aikata a baya na nemi yafiyar ubangijina nayi tuba tuba ta taubatan nasuha ba tuba irin ta muzuru ba, ina da yakinin ubangijina ya yafe mun domon shidin gafuru raheem ne amma kai, ta nuna shi da yatsa tana girgiza kai.Koda naso in manta da abubuwan da suka shude sai Kayi kokarin dawo mun dasu cikin rayuwata ta hanyar tozarci da bakaken kalamanka yaya akeso inyi ne?Ta kara fashewa da kuka tana kaiwa kasa.Ya rarrafo kusa da ita yana fadin, dan Allah ki gafarceni ba abunda kike tunani bane wallahi ba haka nake nufi ba.Murmushi tayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo, na fahimceka don haka na riga na yanke hukuncin da zai kawo karshen takaddamar nan da sabanin fahimtar da muke ciki saboda haka ka bude mun kofa in wuce.Kiyi hakuri dan Allah nasan na aikata babban kuskure kada ki barni, shima zuciyar shi a karye take domin yana sonta sannan yasan idan ya rasa ta rayuwarsa ta samu babban gibi kenan.Tsawar data buga mishi ta dawo dashi hayyacin shi.Ka bude mun kofa in wuce nace maka!Baice komaiba ya tashi ya wuce dakin shi ya turo kofar ya rufe ta ciki don kadama ta bishi can.Ganin haka yasa ta kwanta a gurin tana cigaba da rera kukanta har bacci ya sureta bata sani ba.Da asuba yana fitowa ya hangota kwance kasan tiles kusada kofar tana bacci a takure saboda sanyin gurin, komawa yayi dakinshi ya hado kan abunda yake bukata na tafiyarshi office don daga ya fita bazai sake dawowa ba sai dare akwai inda zaije da sassafen nan, ya fito ya ajiye mata farar takarda a kusa da ita ya fita.Ba’a jimaba sosai da fitar sa ta farka tana mai jin wani iri a jikinta kamar zazzabi ke son kamata, tashi tayi zaune nan tayi arba da takardar daya ajiye mata, bata bude takardar ba yadda take a ninkenta haka ta bude zip din bayan jakarta ta saka a ciki ta shiga dakinta tayi sallah ta watsa ruwa ta sauya wasu kayan lokacin gari ya soma haske ta fito don bata sauya kudurinta na tafiya gida ba.Mai adaidaita ta tara drop ta dauke shi ya sauketa kofar gidan su ta shiga jaye da trolleynta lokacin inna ta fito tana kokarin hura wuta fateema kuma tana wanke-wanke.Kallonta inna takeyi kirjinta na bugu da yadda taga fuskar Ameena tasan babu Lafiya gata da akwati.Cikin hanzari taja hannun Ameena tayi daki da ita ba tare da taba fateema damar yin magana ba dukda ta lura tana ta yiwa Ameena murmushi.Zaunar da ita tayi saman gado kana ta dubeta cikin natsuwa bayan itama ta zauna tace.Me kuma ya faru?Nan Ameena ta kwashe komai ta fada mata bata rage ko abu daya ba daga abunda ya faru din, bayan ta gama ne inna ta dauke ajiyar zuciya tana dubanta.Amma kin bani mamaki aminatu.Cikin tsoro ta kalli mahaifiyarta amma batayi magana ba.Inna ta cigaba, banyi tsammanin har wannan kankanin abun zaisa kiyi tunanin baro gidanki kizo nan da sunan yaji ba..Toh inna ya zanyi? Na gaji da cin mutumcin da yake mun yana tozar tani akan abunda bai kai ya kawo ba.Keda kika sanshi abu mafi muhimmanci shine ki koyi zama dashi, na fahimci yana matukar sonki tunda har zai dage da baki hakuri akan laifin daya aikata miki, zuciyace dai da kuma yanke hukunci a yayin da yake cikin fushi shine kawai matsalar shi idan na fahimta.Ta gyada kai.Toh kina ji, cikin sauki zaki magance wannan sabanin dake shiga tsakaninku, ya zama dole ki kara hakuri domin ba ko wani namiji ne zaki aura a irin wannan yanayin ace ya iya kame bakin shi daga kin gorantawa a gareki kan abunda kika aikata ba wanda ke kanki kinsan da hakan don haka inaso kiyi hakuri ki kara akan wanda nasan ki dashi sannan ki gujewa duk wani abu Koda da kwayar zarra ne da kika San zai iya daga kishin shi akan ki wadannan abubuwan zasu taimaka sosai a zamantakewar ki insha Allah.Shikenan inna zanyi yadda kika ce.Allah ya muku albarka, yanzu ki tashi ki koma gidanki kafin mahaifinki yaji labarin zuwan naki Allah ya rufa asiri ya kuma kauda SHAIDAN a tsakaninku.Ba musu ta tashi dauki jakarta tayi waje ta juyo taceda fateema.Sai munyi waya.Toh Adda Allah ya kaiki Lafiya.Ameen tace ta fita a gidan tayi sa’a napep ya sauke passenger yana kokarin juyawa ta tare shi ta shiga ta fada mai inda zai kaita.Saida ta mayar da jakar ciki ta gyara ko ina duk da a gyare yake amma tadan kalmasa ta dawo falo ta zauna ta auna maganganun inna a kanta tare da hasasowa kanta dacewar abunda zatayi, a zahiri tana qaunar mijinta saidai wasu daga cikin halayensa sun soma gundurarta ta kuma rasa yadda Zata yi domin iya saninta bazata iya kaucewa munanan kalaman shi ba domin bazata iya goge tabon da yake kallonta dashi ba Koda a lokacin mu’amalarsu ta aure wani lokacin yakan ji ya tsani ya shigeta saboda ainahin radadi da daci yake ji a kasar zuciyar shi saidai soyayyarta dake rinjayarsa, itama da kanta kusan kullum cikin tsarguwa take jinta a game da hakan.Ajiyan zuciya mai dan sauti ta sauke kana a hankali ta furta, na jawa kaina FENTIN ZIN🅰️ bazai taba wankuwa daga jikina ba Allah na tuba ka yafe mun nan ta cigaba da zama har dai bacci yasoma fisgarta ta tashi firgigit.

Back to top button