Karfe A Wuta Chapter 63 By Ayshercool
Ta share hawayenta, ta ɗaga kanta ta ga ita yake kallo ta ce “Ka ce mini ka yi wa Indabo aike, me ka aika masa?””Hotona ne””Hotonka kuma?””Eh, hotona ne da ni da wani yaronsa da yake zaton ya saka an kashe masa shi”Ta zaro ido ta ce “Wai shi mutane nawa ya kashe kenan a rayuwarsa?”Ya rausayar da kai ya ce “Mutane sun ɗauki duniya fiye da yadda ki ke tunani. A baya bayan matsalar da nake fuskanta a gidanmu, fatan da nake yi kullum, Allah ya bani abun yi, ko iya abinci in din ga samu ina ci, sai da na haɗu da uban gidana dodo, ya haska mini duniya da in da mutane suka saka gaba. Da na so na yi kuɗi da yanzu ni hamshaƙin attajiri ne.A lokacin da jauhar take ciyar da ni, da fari babu abun da yayi mini zafi, gani nake kawai auren dole aka yi mini, sam ba ta gabana, sai dai abun mamakina da ita, duk abun da zan yi mata bata jin haushi, naga yadda take sana’a tuƙuru iya yin ta, dan kar mu zauna da yunwa, daga baya nayi noticing idan abinci ba zai isa ba, sai ta bani ita tayi kame-kame ba ta ci ba, a lokacin ba wai dan tana so na bane take yi mini haka, ta rungumi ƙaddara ne, kuma tana tausayina.Daga baya sai na fara jin kunyarta, lokacin da ta roƙi na sayo mata omo, naga responsibility ɗina, amma na zuba mata ido take yi, kuma bata taɓa nuna mini ta gaji ba. Sai dai a lokacin ba ni da wata sana’a sai sayar da wiwi da ƙwayoyi, yadda take yi mini addu’a Allah ya wadata ni da halal, ya nesanta ni da haram, ya sanya na ji ba zan iya ciyar da ita da kuɗin wiwi ba.Sai a lokacin naga ashe, bayan mutuwar Sadik kukan daɗi nayi, da na ce na rasa sana’a, dan a lokacin na din ga faɗi tashi, saboda kar na ciyar da ita da kuɗin ƙwaya.Da in ciyar da ita da wannan kuɗin, gara na dawo na maze na ce bani da kuɗi, na san ba ɗaga mini hankali za ta yi ba.Gashi lokacin tana ta ƙoƙarin rabani da hulɗa da Indabo, wataran idan na ga wahalar tayi mata yawa, haka nan nake zuwa na tsitsiye Indabo ya bani kuɗi.Zuciyata ta sha raya mini, na faɗa mummunar hanya, na samu kuɗi saboda jauhar ta huta, bana nuna mata hakan a zahiri, amma zuciyata kullum a takure babu daɗi. Duk da tsamin alaƙar da ke tsakanina da mahaifina, sai da na din ga jin tamkar na je na ce ya bani aron kuɗi nayi jari, amma na kasa, mussman tuna halin matarsa.A lokacin da tausayinta ya fara zama tsananin so a cikin raina, da tana uzzura mini ko yi mini tashin hankali, da babu abun da zai hanani kauce hanya, dan yahoo zan fara, kuma kuɗi zan samu sosai da sosai, haka nan na san in da zan yi dillancin miyagun ƙwayoyi a tsakanin manyan mutane, har da ƙasashen ƙetare na samu kuɗi, amma ban taɓa burin tara kuɗi da mummunar hanya ba.Ina ga lokacin da tayi ɓari ne, bani da wasu kuɗi sai na wiwi, shi ne aka yi mata magani da su, amma banda haka, ban taɓa ciyar da ita da kuɗin ƙwaya ba”.”Viper, labarinku abun tausayi, kuma gwanin daɗi, Allah ya bani ikon zama kamar jauhar, ina sonta sosai””Sai dai ki kamanta, ba zaki iya ba, ke mafaɗaciya ce, matata kuwa kan tayi faɗa sau ɗaya ana daɗewa, shiyasa nake kiyaye abun da zai ɓata mata rai ya sa tayi fushi, har ta yi faɗa. Na gode sosai da saka ni kuka da ki ka yi””Saka ka kuka kuma?””Eh, tun da na rasa jauhar, ban zubar da hawaye ba””Ai kai jarumi ne, bari na tashi na tafi gida, ka yi mini addu’a, gobe in Allah ya kaimu zamu zauna a kotu”Ya jinjina kai ya ce “Allah ya bada sa’a, bani maganina””Dan Allah ka daina shan magungunan nan, lafiyarka fa”Ya ce “Duba na na menene?”Ta ciro maganin ta duba, cikin magungunan sa ne na Asibiti, ta ajiye masa ta ce “Allah ya baka lafiya mai amfani, ya bamu nasara a kotu, in sha Allah case ɗin ka ne next, ka yi mana addu’a” ya jinjina mata kai.Ta tashi ta ɗauki jakarta tana ɗaga masa hannu.***Daren yau Nabila tayi ta addu’a, suka yi waya da Barrister Habib, ya ce su haɗu a kotu.Ya ƙara mata ƙarfin gwiwa, kafin shiga shari’a, suna tsaye a harabar kotu, tana dudduba abun da zata tsaya a gaban shari’a da shi.Nabila ta tsaya a gaban kotu, ta ce my lord, kamar yadda na gabatar da hujjojina a wancan zaman da aka yi, akwai voice na muryar mahaifiyar ramma tana kokawa akan a nema mata hakkin ‘yar ta.Haryanzu ina da ja, a kan zargin da ake yi wa wanda nake karewa, a hirar da aka yi da mahaifiyar ramma, a gidan rediyo, wanda suka yi iƙirarin ya yi wa ramma fyaɗe, ya sha banban da wanda aka gabatarwa kotu.Haka zalika, voice message ɗin da yake yawo, na mahaifiyar ramma, ta koka a kan wanda ya yi wa ƴar ta fyaɗe, ya dawo ya ɗauketa ta ƙarfin tsiya daga gabanta.Lauyan gwamanti yayi suka, ya nemi da a gabatar da mahaifiyar ramma, ba wai kame-kame da abun da babu wanda ya san tushen sa ba.Nabila nan take ita ma ta buƙaci, a gabatar da ramma, tayi mata tambayoyi.Lawyan gwamnati ya ce Ramma na ƙarƙashin kulawar, likitoci haryanzu, dan haka ba za a gabatar da ita a gaban kotu ba.Nabila ta sake cewa Wane irin illa aka yi mata, da har zuwa wannan lokacin za ace ba ta warke ba, a shekarun baya shekara sha uku sha huɗu ake yi wa mata aure, ba a samun matsala, suna zaune lafiya, a report ɗin da aka bayar na case ɗin ramma, abun bai zama complicated da za ace tsawon wannan lokaci tana Asibiti ba.Lauyan gwamanti ya soki maganar Nabila, tare da neman a bashi dama ya gabatar da shaidunsa na gaba.Wata mata ce ta fito, aka tambayi baba mai gadi, ko ya santa? Ya ce Eh, ita ma mai aiki ce a gidan.Aka tambayi me ta sani, a game da abun da ake tuhumar mai gadi da shi, babu kunya babu tsoron Allah, ta bayar da shaidar zir, tare da tabattar da mai gadi ne yayi laifin, sai bayan da yayi aika-aikar, ta dawo daga sayen kayan miya, ta tarar da ramma, kuma daga shi sai ramma ta bari a gidan.Baba mai gadi ya sunkuyar da kai cikin matsanancin ɓacin rai da mamaki.Nabila ta ce ya za ayi ace gida kamar wannan babu cctv camera, akwai buƙatar idan da cctv camera a duba abun da ya faru.Daga nan Nabila ta nemi a bata damar ta gabatar da nata shaidar ma, aka bata dama, ta buƙaci wata mata ta fito.Nabila ta buƙaci matar ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a matsayin maƙwabciyar su ramma a can garinsu.”Me ki ka sani game da abun da ya faru da ramma?””Eh to, bayan an dawo da ramma gida, ta cigaba da jinya, dan sallamo su aka yi daga Asibitin birni, saboda rashin isashshen kuɗi. Babar ramma ta gaya mini wata mata ta zo ta ce zata taimaka musu, amma sai sun yarda sun janye shari’ar.Da suka ƙi, ta ce zasu gani, bayan wasu ‘yan kwanaki, wani mutum ya zo da shi da wasu, ya gaya mata shi ne ya yi wa ramma fyaɗe, kuma ta ƙarfin tsiya, ya kama hannunta ya tafi da ita”Nabila ta ce “Ko ta gaya miki sunan wanda ya keta wa yar ta haddi?””A’a, ba su san sunansa ba, ramma ba ta daɗe da fara aiki a gidan ba, amma ta tabbatar da ƙanin matar gidan ne. Bayan ya sace mata ‘ya, ta je birni gidajen radiyo ba a saurareta ba, haka zalika wurin jami’an tsaro, kawai lokaci ɗaya muka nemeta muka rasa”.”My lord, shaida ta tabbatar da cewa wanda ya yi wa ramma fyaɗe, ya dawo ya saceta, wanda nake karewa da ake zargi yake tsare, tayaya zai je ya sace yarinyar. Kuma har zuwa wannan lokacin, ba mu ga ramma a zaman kotu ba, shin ina ramma take?”Lauyan gwamanti ya ce bai kamata a karɓi shaidar maƙwabciyar su ramma ba, tun da ba a kanta abun ya faru ba, dan haka ayi fatali da shaidarta.Duk yadda Nabila ta so bayyanar da nagartar hujjojinta, amma kotu ta din ga soke su.Nabila tana ji tana gani, aka yankewa dattijon shekara goma sha huɗu a gidan yari, wata irin bahaguwar shari’a, mara fasali balle ɗigon adalci, yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da kammala tabattar da ingancin shaidun kowane ɓangare ba, sai dai an basu damar ɗaukaka ƙara.Yanayin yadda ta fito a gigice kawai zai tabattar wa da mutum ba a hayyacinta take ba, sumayya da suka zo ɗaukan report ce ta nufeta da sauri, watsi ta yi da file ɗin hannunta, ta faɗa jikin sumayya tana kuka.Barrister Habib ya ƙaraso, ya ce “Haba Nabila, wannan ai sai ki saka ayi mana dariya, akwai appeal a gaba, dan Allah ki nutsu.Cikin kuka ta ce “Sumayya mu tafi gida, ba zan iya sake haɗa ido da mutumin nan ba, i try my best, ai kun ga yanayin shari’ar da aka yi, dama haka aka koyar da mu, an bi Principles na law a wannan shari’ar?”Sumayya ta din ga rarrashinta, suka sakata a mota, barrister Habib ya ce “Bari mu kaita gida, Bashir kai ka tafi da motata”Suna tafe a mota tana cigaba da kuka, Barrister Kabir ya kira Habib, ya ce “Ya ake ciki ne?””Gamu zamu tafi, ba ta yi wining ba, sai kuka take yi”Kabir ya ce “Ai dama na gaya mata, waye ya gaya mata jayayya da mutanen nan abu ne mai sauƙi?””Dan Allah kar ka saka ta sare gaba ɗaya, za mu yi appeal, kuma saboda ita nima zan yi abun nan kyauta fisabilillahi i really appreciate what she did” ya ajiye wayar yana cigaba da yi wa Nabila nasiha.Bunkure ta ƙyaƙyace bayan kammala wayar da ta yi, ta kalli badi’a.Badi’a ta ce “An kammala komai kenan?””Eh, an ƙarƙare shari’ar a yau, uba ya yi abun da ya dace, wallahi da bai yi wani yinƙuri ba, sakar musu zan yi su ƙarata daga shi har ɗan nasa, su ta shafa, amma a wannan karon dole na ɗauki mataki a kan yarinyar nan, da gaske so take yi sai ta tona mini asiri, dole zan tattauna da indabo, ya ɗauki mataki a kan ta””Amma kina ganin hakan zai yiwu, tun da abu ya shiga social media, kuma ta fara samun masu mara mata baya?””Iyayen gidanta ma, ba su kai ko ina ba, amma an ce mini an hangeta da barrister Habib, kuma ina kyautata zaton da saka hannunsa a wani abun da take yi, amma duk na san matakin da zan ɗauka akan dukkansu” ta ƙarasa maganar tana haɗiye ƙwayoyin da suke hannun ta, ta bi su da ruwa.Nabila bayan sun kaita gida kuwa, ba ƙaramin kuka tayi ba, gaba ɗaya sai ta ji ta karaya, komai ya fita daga kanta.A ɗakin Nasir, ya sameta bayan ya dawo daga aiki, ko da ya tarar da Nabila ta sha uban kuka, tuntsirwa yayi da dariya, ya ce “Haba barrister, ina ƙwarin gwiwar ta ki? Har kin karaya haka?. Abun da na yi ta nuna miki kenan, nake gargaɗinki a kan ki fita daga sabgar nan, ba ke kaɗaice mai gaskiya a ƙasar nan ba, amma tun da ki ka ga kowa ya ja baki yayi shiru, to abun ya gagari kundila, amma ki ka ƙi ganewa ki ka cigaba da dagewa, ki gode Allah da ba su yi wani abu da za su taɓa lafiyarki ba ma” ya gama surutansa ya fita, ba ta ko kalleshi ba.Yana fita ta mayar da ƙofa ta rufe, tana ƙoƙarin kiran Viper, wayar Alhaji wada ta shigo. Ajiye wayar tayi, ta ɗauki ƙaramar ta ta, ta kira Viper.Bugu ɗaya ya ɗaga, kawai ta saka masa kuka.”Meye ne?””Kana kallon wulaƙancin da aka yi mini a shari’ar nan, kaga wata irin shari’a da aka yi mai cike da wulaƙanci da zalunci, wallahi gaba ɗaya na karaya, na gaji da aikin nan, ina ji ina gani, mutumin da bai ji ba bai gani ba, zai tafi prison, zuciyata kamar ta fashe na gaji”.”To ni kuma wa zai tsaya wa tawa shari’ar?”Nabila ta ce “I give up, na karaya” tayi maganar tana kuka.”Ke kin isa? Ai tun da muka fara, sai mun kai ƙarshe, tied your belt against next trial”.”Ni ba zan iya ba, ina ga ma ciwon zuciya ya kama ni, duk na tsani komai, haka zamu cigaba da tafiya, mai kuɗi ne kawai ɗan gata? Ƙiri-ƙiri fa aka murɗe komai”.”Sai ki gyara, kar ki gaji, sai kin gama da ni tukuna, anyway an hukunta wanda ya aikata laifin, saura kuma ki matsa ki gano in da ramma take da mahaifiyarta””Wai kai wane irin mutum ne? Na gaya maka dattijon nan ba shi yayi laifin nan ba, kuma ni ina zan ganta?”Ko a jikinsa ya ce “Wannan matsalar ki ce ai, ki ƙarasa wannan ki zo ki yi nawa”Katse wayar ta yi, ta ajiye ta cigaba da kuka.*****”Lakwari, ka je ka samu P.A ɗin Indabo, ka gaya masa ni na aikoka, ya uzzura mini da kiran waya, a kan lallai sai na je, wai mai zamani ya yi masa aike, dan haka dolena na nemo masa shi, haryanzu ban sanar masa da halin da nake ciki ba, amma ka je, idan ka je wurin P.A ɗin, ka kira ni zam yi masa bayani”.”Shikenan, amma kana ganin ba za a samu matsala ba?””Ba za a samu ba, daga nan ma sai ka samo mana kuɗin zuwa asibitin nan, dan na tattara kuɗin hannuna gaba ɗaya na aika a kawo mana ganye, shi ma kuma na ji shiru, idan ka dawo daga wurinsa ka biya ka duba mana”.”Shikenan an gama”***Nabila kuwa ba a iya Nasir ba, hatta yan gidan suka sakata a gaba da tsokana, suna yi mata dariya, bisa yadda ta shiga matsananciyar damuwar rashin nasarar da ta yi, a kotu. Ba ta taɓa yin shari’ar da ta shiga ranta ba kamar wannan, gashi dai kyauta take shari’ar babu ko sisi, amma duk ta bi ta damu, hatta hawa social media ya gagareta, saboda yadda ake yi mata dariya, ƴan koren Bunkure ke cigaba da nuna cewar Nabila hassada take yi wa bunkure, kuma kwangila ta karɓo a hannun wasu.Sosai ta fusata, ta hau social media tayi posting, ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin faɗa ne. Kuma ko bayan shekara dubu, sunan gaskiya baya taɓa canzawa, a saurari fitowa ta gaba.Ɓangaren Nasir ma, yana fuskantar matsin lamba sosai daga wurin Indabo, da kuma manyansa a wurin aiki, a kan kama Viper.Gefe guda ga fargabar abin da Nabila za ta janyo musu, tun da ita ba ta so a zauna lafiya, yana matuƙar fargabar Indabo ya yi mata wani abun.Gaba ɗaya ta daina walwala, ko fitowa ta daina yi, sai idan fita zata yi, sai dai a kai mata abinci ɗaki a ajiye.Ganin ta takura kanta da yawa, Nasir ya sameta yana rarrashinta, da bata baki a kan ta jure ta karɓi ƙaddara.”Ba wata ƙaddara da zan karɓa” tayi maganar tana hura hanci.”Ke saɓo zaki yi kenan?”Nabila ta ce “DSP, abun da Allah ya hukunta shi ne ƙaddara, ba abun da mutum ya ga dama yayi da son rai ko son zuciya ba, ko da me matar nan take yawo, sai na tona mata asiri wallahi, gara ma ka ƙyale ni da wannan nasihar””Na ƙyale ki, amma idan kin ƙi ji, ai ba kya ƙi gani ba, tun gashi yanzu kin fara ganin ma, amma ba wannan ba, wai haryanzu babu wani news da ki ka samo a kan Viper ne? Na ga duk kin yi sanyi, kin daina taimaka mini”Ta kalleshi ta ce “Ba dole na yi sanyi ba, ai dama ka ce na daina saka kaina a abun da babu ruwana, dan haka wannan ma babu ruwana da shi”Yayi murmushi ya ce “Haryanzu a fusace ki ke arfa, to ba ni ne dai Naja’atu Bunkure nan ba, amma yakamata idan da wani hints a taimaka mini”Ta kalleshi ta ce “Babu wani hints, ban san komai ba””To shikenan, idan kin huce sai mu cigaba da maganar” ta harare bayansa har ya fice.Kasa samun nutsuwa ta yi, ta sake ɗaukar wayarta ta yi posting, “Idan har mahaifiyar ramma ba ɓata tayi ba, kuma da gaske Bunkure foundation na kula da ramma ne, to tana ina, al’umma yakamata su samu update a kan halin da take ciki, kuma shin suna da masaniya a kan ɓatan mahaifiyarta? Idan eh to ina tafi? Tana tare da ‘yarta ne ko kuwa?” Tayi posting ta nemi wuri ta zauna, lissafi da tunani daban-daban suka din ga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar Nabila.***”Indabo, yakamata fa ka sake matsa Abdul, ya gaya maka in da yarinyar nan take, hankali ya fara dawowa kanmu, yarinyar nan fa ta matsa, kuma ban ga alamar, zaka ɗauki wani muhimmin mataki a kan ta ba””Ya ce mini ya kasheta”Bunkure ta ce “Ya kashe ta ta yaya? A binciken da na yi, an tabattar mini uwar yarinyar ba ta garin nan, tafiya ta yi babu shiri, kuma Abdul ya je gidan fiye da sau ɗaya, bayan ya ɗauke yarinyar, me ya je yi, ni fa ba na son a din ga gaba ana baya, kar asirinmu ya tonu fa”Indabo ya numfasa ya ce “Abubuwa sun fara caza mini kai Naja, ga takarar Abdul da nake ta fafutuka, ga auren nan da ake shirin yi na shi. Ga ɓangaren ki taki matsalar, duk is a minus case, bababr damuwata yanzu Viper, aiken da ya yi mini ya tayar mini da hankali, idan ba a kama shi an kashe ba, hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ga ƴan adawa sun sako mu a gaba, ga tunanin jafar da yake tsare na rasa wane tunanin ma yakamata na yi””Ai wanda ya fi muhimmanci shi zaka yi, wallahi idan aka cigaba da ƙyale yarinyar nan, muna raina abun da take yi zata bamu mamaki fa”Ya jinjina kai ya ce “Na ga alama, kuma ba zan taɓa bari hakan ta faru ba”.P.A ne ya kaste su, ta hanyar yin sallama, suka amsa duk suka ɗago suna kallonsa.Ya kalli indabo ya ce “Akwai matsala fa””Again?””Ƙwarai kuwa, madaki ne ya yi aike, wai ya samu rauni a ƙafarsa, yanzu haka ko iya tafiya ba ya yi, ɗazu ya turo yaronsa har ya buƙaci a bashi kuɗi ya je asibiti, amma wai duk wani abu da yakamata, yana da yaran da za su iya yi maka”Indabo ya buga tsaki ya ce “Maganar banza kenan, zuwa yaushe zan cigaba da rarraba sirrina, wannan yayi mini aiki wancan yayi mini, kalli yadda haryanzu jarabar ɗan tahaliki ɗaya take ta ɗawainiya da rayuwata. Na gaji ya je Allah ya kyauta, na nemi wata mafutar””Amma kana ganin watsi da shi, ba zai zame mana wata ɓarakar ba ko barazanar ba?””Babu abun da zai zame mana sai wahala, tun da ba shi da wani amfani yanzu, Viper da na bari ya ci karensa babu babbaka, saboda yaron dodo ne, ina matuƙar jin tsoron abun da ya sani a kaina, kuma kamar yadda na yi tsammani, ya san abubuwan da idan yayi magana kashinmu ya bushe, dole fa a nemo Viper akwai matsala wallahi” yayi maganar yana zazzaro ido cikin tashin hankali.Sai da aka kusa sati da yanke hukunci, sannan Nabila ta tafi wurin iyalan dattijon nan, tare da sake rarrashin su, a kan su yi haƙuri su ƙara mata lokaci, zata ƙara shiryawa sosai a appeal ɗin da za su yi, tana saka ran za su yi nasara in sha Allah.Suka yi ta yi mata godiya, sai da zata tafi, ƙaninsa ya keɓe da ita, ya ƙara yi mata godiya, sannan ya ce “Dan Allah ki ƙara bincikar ɗan uwana, kamar fa ya san wanda ya yi laifin, barazana aka yi masa Shiyasa ya kasa gaya miki komai””Barazana kuma, wace irin barazana?”Ya ce “Eh, akwai ziyara da na kai masa, ya gaya mini amma ya nemi kar na gaya wa kowa, ya san sunan wanda yayi laifin, da alaƙarsa da matar gidan, amma bai san ɗan waye ba”Ta ce “Ya salam, to amma meyasa ni bai gaya mini ba, babu yadda ban yi da shi ba a kan idan ya san wani abu, ya sanar mini, amma ya ce mini babu abun da ya sani, sunansa ma bai sani ba, kawai dai ya san ɗan yayan matar gidan ne”.Ta ce “Subhanallah, shikenan zan san abun yi, a cigaba da yi mana addu’a”Ya ce “In sha Allah, kullum cikin yi muku ake, Allah ya jiƙan magabata mun gode sosai da sosai”.Tana kan hanya saƙon Viper ya shiga wayarta, a kan yana son su haɗu.Ji tayi kamar ta maze taƙi zuwa, amma ina, ba ta ji alamar zuciyarta zata bari ta aikata hakan ba.Garden ɗin da suke haɗuwa, a can ta same shi, ta tsaya tana kallonsa ya rage sumar kansa, yayi kyau sosai.Wata tab ta gani a hannunsa, cikin basarwa ta ce “Ina wuni?””Wayarki zaki bani”Ta kalleshi ta ce “Wai baka san meya same ni bane? Baka jajanta mini rashin nasara da nayi ba, abu duk ya dame ni””Yanzu ki ka fara, idan har rashin nasara ba zai saka ki ƙara jajircewa ba, sai dai ki yi kuka”Nabila ta ce “To idan ban yi kuka ba ya zan yi?”Ya kalleta ya ce “Babu””Waye ya sai maka waya?” Yayi mata shiru.Ta sake cewa “Haryanzu fa ina da tarin tambayoyin da baka amsa mini ba””Wanne daga ciki?””Meyasa Indabo ya ce zai yi maka tarko da ni ya kama ka? Ni meye haɗina da kai?”Ba tare da ya kalleta ba ya ce “Wataƙila ya san kina zuwa wurina””To amma ya aka yi haryanzu bai kama ka ɗin ba? Kuma ni haryanzu kana ɓoye mini wasu abubuwa”Ya saka ƙaramar wayarsa a kunnensa, ya ce “Ɗan mama ya ake ciki?””Oga Viper, mun ƙwamuso Lakwari fa, yanzu duk in da madaki yake, dole ya bayyana, tun da babu mai taimaka masa ko ya kula da shi”Viper ya ce “Good job, zan gaya muku what next”Cikin zaro ido Nabila ta ce “Viper kidnapping?””Eh ina son na sauƙaƙa miki aiki ne, shaidu na fara tattara miki, kafin a fara shari’ata, Madaki yayi jigatar da ba zai iya musa laifin da ya aikata ba””Amma ka gaya mini me ka ke yi da wayoyi? Ka daina yi mini ɓoye-ɓoye. Sai kin zo kan shari’ata zaki ji koma me ki ke buƙatar ji”Kamar shashasha haka take kallonsa, gaba ɗaya ta ma rasa me za ta ce masa.Ya miƙa mata wayarta ya ce “Angry bird””Am confused””Sorry” Kamar ta sake fashewa da kuka ta ce “Zuciyata kamar a kurku, haka nake jin ta, mai laifi daban yana can yana rayuwarsa, mai karɓar hukunci daban, wane irin abu ne wannan?”Viper ya gyaɗa kai ya ce “Kamar dai ni a kwanakin baya, idan aka kama mai laifi, sai ayi musanye a saki wancan saboda ɗan gata ne, ni kuma a tsare ni a matsayin mai laifin”Ta ce “Kuma dai? Wani yayi laifi kai kuma a tsareka?” “Mmm, a saka matata tayi ta yawo tana wahala ba, wata Shari’a sai a lahira, duk rintsi kar ki yadda ayi amfani da ke ki ci amana, ba kowa ne yake da zuciyar yafiya ba”Jiki a sanyaye ta jinjina kai, ya ce “You can leave”.Kusan a tsukin lokacin, Nabila ta zama topic of discussion a social media, sai dai ba ta karaya ba, wurin cigaba da posting a kan bunkure foundation.***”Abdul tun muna shaida juna, ka gaya mini ina yarinyar nan take? Ka kashetan ko kuwa? Sannan uban me ya sake mayar da kai gidansu, bayan ka je ka ɗauki yarinyar, kuma saboda hauka maimakon ka saka ayi? Kawai sai ka wanke ƙafa ka tafi da kanka ka je ka ɗauki yarinyar, kamar baka san matsayinka ba? Idan ka san uwar yarinyar nan ma, tana tare da kai, ka gaya mini, na san matakin da zan ɗauka a kai”Ya girgiza kai ya ce “Ni ban ɗauki uwar yarinyar ba, ban san in da take ba””Da ka kashe yarinyar yaya ka yi da gawarta?”Abdul ya ɗan yi jimm sannan ya ce “Ruwa na jefa ta”Indabo ya ja guntun tsaki ya tashi, maganganun da bokansa ya gaya masa ne suke ta yi masa kai komo a zuciyarsa, wai dutsen da ya gaya masa zai ci karo da shi, lokaci yayi da shi bai san ya za ayi ba, dole ayi ɗayan biyu, ko dutsen yayi nasara a kansa, ko kuma su yi mutuwar kasko, amma babu yadda za ayi, ya iya maganin dutsen nan da kansa.Nabila fa ta sake jajircewa, da cigaba da ƙoƙarin gano bakin zaren matsalolin da take tunkara.Bayan shari’ar ramma, akwai shari’oi da dama a gabanta, amma wannan c ta fi ci mata tuwo a ƙwarya, sai kuma ta Viper da zata fuskanta.Kasancewar da sassafe ta je wurin aikin, duk babu mutane, ta shiga office ɗin ta, ta ajiye jakarta, ta yi addu’a ta zauna, ta buɗe computer ta fara aiki.Ƙaurin wayar wutar lantarki ta fara ji, ta ɗaga kanta, ba ta ga komai ba, ta sunkuyar ta cigaba da aikinta.Wata irin ƙara wearing ɗin office ɗin ta yayi, ya fara ci da wuta, a razane ta tashi cikin tashin hankali, ta nufi ƙofa zata buɗe, ta ji an kulleta ta waje, ta jijjiga iya ƙarfin ta, amma a ƙofar a kulle gam, ga wuyar wuta sai cigaba da ƙara take yi wuta na kamawa tana tarwatsi.Da ƙyar ta iya ɗaukko jakarta, ta ciro wayarta, tuni ta fara gani dishi-dishi, saboda hayaƙi, tari ya turnuƙeta.Hannunta na rawa, lambar Viper kawai ta iya gani, ta danna.Ya ɗaga wayar sautin tarinta ya fara ji, tana ta yi haɗe da haki, da ƙyar ya iya fahimtar ta ce “Wuta” daga nan ya ji ɗif
Ayshercool 08081012143



