Hausa novels

Ruwan Zuma Page 21 Hausa Novel

(21) “An d’aga aurena za’a had’a tare da naki.�? Fad’in Mas’ud bayan ya dawo daga aiki ranar da dare. “To ai hakan yafi akan ayi aure cikin gaggawa babu shiri.�? Laila ta amsa masa. “Kalti ina son muyi magana akan aurenki. Ina so ki nitsu kiyi tunani kar kiyi abunda zai dameki daga baya saboda zaman aure da wanda bakya so ba mafita bace.�? Shiru tayi tana tunani har na kusan minti d’aya sannan tace, “Alhaji Abdul shi zai zama tamkar uba a gurin Abul, saboda naga yana da ikon mishi magana kuma ya nitsar dashi. Mu bar maganan nan don Allah domin baza a koma baya ba.�? “To yaya zaki yi da Haydar?�? Laila ta mishi kallon rashin fahimta tace, “Ban gane yaya zan yi da Haydar ba! Soyayya nake yi dashi da har in yaji zan yi aure zai ce na yaudareshi? Of all people Mas’ud kai kake kawo mini wannan maganan a wannan lokacin?�? Tana fad’in hakan ta tashi ta shige d’akinta. Tana rufewa ta jinginu da k’ofar tana ajiyar zuciya. Runtse idanunta tayi na wasu sakanni kana ta bud’e ta isa bakin gadonta ta kwanta tare da kashe wutan d’akin gabad’aya. Shirin biki ake yi ba kama hannun yaro, domin Alhaji Abdul so yake yi ya nunawa duniya cewa ya samu burin zuciyarsa. Ta gefen Laila kuma ba yabo ba fallasa, domin ta k’i yin wani gyaran jiki da irin sinadaran nan na gyara aure. “Wallahi baki isa kije haka sam6al babu gyara ba, shekara ashirin kina zaune sannan kice bakya buk’atar gyara?�? Fad’in Hajiya Maryam bayan ta kawowa Laila wasu tsumi, had’in gari da kuma gumban mata. “Na fad’a miki ni ba wannan bane a gabana. Idan baya sona a haka sai ya dawo dani inda nafi wayo.�? “Ai baki isa ba, yanda na cire kud’i na saya dole kuwa kema kiyi amfani dasu. Ji mini mata fa, tsofai-tsofai dake zaki shiga d’akin miji amma kice baza kiyi gyara ba? Alhaji Abdul wasu irin mata ne bai gani ba amma ya nace sai ke? Don haka kema sai ki gyara masa kanki ya gane cewa bai yi jiran banza ba.�? Dafe kai Laila tayi tana sadda kanta k’asa. To ita ta yaya ma zata fara kwanciyar aure da wani d’a namiji ba Aliyu ba? “Bana buk’atar gyara saboda babu abunda zai shiga tsakaninmu.�? Ta fad’i hakan kanta a k’asa bata d’ago ba. Wata irin shewa Hajiya Maryam ta saka tana dariya tace, “Kune ma jaruman Hausa novels, dama yawanci haka mak’aryatan marubutan suke rubutawa mutane.�? Ta bud’e goran tsumi ta mik’awa Laila. “Ki shanye wannan a take a lokaci d’aya.�? “Hajiya Maryam baza ki tursasani yin abunda ban yi niyya ba.�? K’arshe sai da Laila ta k’ar6i tsumin tasha tana yamutsa fuska don d’and’anonsa bai mata dad’i ba. “Zan sha sauran a hankali.�? Ta fad’i hakan tana kar6an sauran ta ajiye a gefenta. “Kar ki mini asaran kud’i, don Allah kiyi amfani dasu.�? Laila a kad’a kai amma nan amai take ji. Tashi tayi tacewa Hajiya Maryam tana zuwa, direct band’akinta ta shige ta kwaza aman duk abunda tasha a toilet. Kuskure bakinta tayi kana ta wanke fuskarta ta fito ta samu Hajiya Maryam na sallah a d’akin Sabrin na daa. Har Hajiya Maryam ta tafi bata gane abunda ya faru da Laila ba, ita kuma Laila sauran maganin da aka bata da wurgasu can cikin wardrobe d’inta inda tasan babu wanda zai gani, akan idan an gama biki kowa ya watse zata kyautar ga masu so. Ranar talata da rana Laila na zaune a falo tana waya da Alhaji Abdul taji ana bugun k’ofar falonta. “A shigo.�? Ta fad’i hakan da d’an k’arfi. “Wallahi inaga Abul ne ya dawo daga rabon Iv….�? Bata kai ga k’arisa maganan ba ta ga Haydar tsaye a kanta yana sauk’e numfashi kamar wanda yayi gudu hannushi rik’e da IV irin wanda Alhaji Abdul ya aiko mata ta raba. “Kika ce bakya son kowanne event? Ko d’aya Gimbiyata?�? Kawar da kanta tayi daga kallon Haydar tace, “We already talk about this Alhaji Abdul, girma ya zo sai a barwa yara suyi.�? “Ko walima baza kiyi ba?�? Ya k’ara tambayarta domin shi yaso suyi dinner ne yanda za’a yita labarinshi a duk fad’in Kano. “Alhaji Abdul kenan. Sau nawa zamu yi wannan maganan ne?�? Ta fad’i hakan tana murmusawa cikin k’arfin hali. “Shikenan, ai duk yanda kika ce haka za’a yi Amaryata. Ko kaina kika ce in cire zan cire babu 6ata lokaci.�? Wannan magana ya bawa Laila dariya. Dariya tayi mai sauti kana tace, “Baka rabo da abun dariya. Nayi bak’i zamu k’arisa maganan anjima.�? “Gashi ni kuma ban gaji da jin muryarki ba, ji nake yi kamar jumma’a tayi nisa a d’aura auren yau.�? Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tace, “Hmm, sai anjima.�? Bayan ta kashe wayar ne ta d’ago kai ta kalli Haydar wanda fuskarsa tafi ta daa had’ewa, wannan karon tamkar zai yi kuka haka Laila take gani. “Haydar lafiya kazo ka tsaya a bakin k’ofa? Ka shigo mana.�? Ta fad’i hakan tamkar bata lura da halin da yake ciki ba. “Da… da gaske aure zaki yi?�? Ya tambayeta yana mai takowa cikin falon yanayinshi abun tausayi. “Ehh, kamar katin na gani a hannunka. Baka karanta bane?�? Itama ta tambayeshi fuskarta a yamutse domin lokaci yayi dashi da ita zasu daina wannan wasan, aure zata yi, kuma ubangidansa zata aura. “Meyasa?�? Shine tambayar da ya k’ara mata yana zama a kan kujera mai fuskantarta. “Ban gane wannan wani irin tambaya bane Haydar. Idan baka da abun fad’i ni ina da abun yi a gabana da yawa.�? Ta fad’i hakan ranta a 6ace. “Meyasa kika kasa za6ina a matsayin mijin aurenki? Ko baki yarda da irin son da nake miki bane? Ko don ni talaka ne bani da komai?�? “Saboda kai yaro ne Haydar, lokaci yayi da zaka daina yaudaran kanka cewa ni Laila zan iya aurenka. Na biye maka munyi wannan wasan a daa, amma a yanzu ba zai yiwu ba. Zan baka shawara kar kayi sanadiyyar aikinka akan wani maganan shirme.�? “Soyayyar da nake mini ba shirme bace Laila. Idan hujjarki cewa ni yaro ne ki tuna cewa Annabi Muhammad SAW wacce ta girmeshi ya fara aure kuma a bazawara ya ganta ya aureta. Ba a kanmu aka fara ba, haka kuma ba’a kanmu za’a daina ba. Don Allah kar ki mini haka, wallahi kece mace ta farko dana fara so bayan mahaifiyata.�? Ya fad’i hakan hawaye na taruwa a idanunsa. Zuba mishi ido Laila tayi tana jin tausayinshi a ranta, amma tasan idan ta nuna mishi a fuska bazai tafi ba. K’ara had’e fuskarta tayi tace, “Haydar abun naka yana son ya wuce gona da iri, bansan ko sake maka fuska da nayi yasa ka rainani haka ba, da har zanyi aure zaka zo kana fad’a mini maganar banza ba. Ka tashi ka tafi, bana son k’ara jin wata magana daga gareka.�? Ta fad’i haka a numfashi d’aya. “Don Allah…�? Ya fara magana ta katseshi ta hanyar d’aga masa hannu tace, “Kar ka 6ata mini rai please. Ka tafi.�? Mik’ewa yayi tsaye amma bai tafi ba, illa kallonta da yake yi tamkar mai mata kallon k’arshe. “Kin za6i Alhaji Abdul ne ba don kina sonshi ba sai don ya fini a shekaru wanda ke a gurinki hakan na d’aya daga cikin qualities na aure. Idan har soyayya ce ta gaskiya batun yawan shekaru ba zai samu damar datseta ba. Yanzu na yarda cewa ni kad’ai nake haukan sonki ke bakya sona duk tsawon wannan lokacin da nake tunanin kina sona, ashe ni nake yaudaran kaina da nake tunanin kema kina jina a zuciyarki kamar yanda ni nake jinki a tawa zuciyar. Nagode da lokacinki da kuma taimakonki a gareni tun daga farkon had’uwarmu har rana mai kamar ta yau, amma zan dawo miki da d’aya ba don na raina ba sai don hakan na nufin nisanta kaina daga kallonki bayan kinyi aure. Na ajiye aikina a Lu’a Ventures.�? Yana fad’in hakan ya fice daga falon yana goge idanunsa. Laila bata kirashi ba, illa juyar da kanta da tayi gefe tana jin zafi a zuciyarta. Har ga Allah tana son Haydar, tana son barkwancinsa, tana son hankalinsa, tana son iliminsa sannan shi karan kansa abun a gani a so ne. Amma ina zata iya auren da mutanen duniya zasu hanata jindad’insa? Ina zata iya auren da za’a dinga zund’enta ana yamad’id’i da ita? Ko waye ya ganta tare da Haydar cewa za’a yi ta cuceshi taci zamaninta kuma tazo tana cin nasa. Za’a yi mata kallon mace mai son duniya da bin yara k’anana. Halin data rayu a ciki ma ya isheta, bata buk’atar wani drama a rayuwarta. (Duk wannan abunda ta lissafa akan gudun bakin mutane ne! Shin d’an adam yasan cewa harshensa na iya yanka takobi? Maganar mutane na iya lalata rayuwar wani ko kuma ya ingantashi. Harshe na gyara, yana 6ata abu, sannan zai iya kai mutum wuta ko aljanna.�? Ranar alhamis da yamma gidan Laila ya cika da jama’a ko’ina ka duba jama’a ne a zaune an zo tayata farincikin wannan rana da ita kanta bata d’aukeshi a abun farinciki ba. Duk da cewa bata gayyaci wasu wanda suka zo ba, bai hanasu amsa gayyatar Ummii ba wacce itama take nata bikin a gidan Madu. Shi kuwa Madu yaji labarin auren Laila a bazata domin bai tsammaci zata bada kai cikin sauk’i haka ba. Wannan farinciki da yake ciki yasa shima ya kasa zama yayi kati da kanshi ya rabawa abokansa amma banda wanda suka ta6a neman soyayyar Laila, wanda shi a ganinshi idan ya aika musu katin aurenta kamar mari ne a fuska. Da dare Abul yana kwance a d’akinsa duk abun duniya yabi ya dameshi akan wannan aure da mamanshi zata yi. Shi da kanshi ya raba mata IV ba don ranshi ya so hakan ba. Ko da ya nuna mata baya son zuwa rabawan cewa tayi, “Wa kake so ya kai? Sannan in ban manta ba kai ka damu inyi aure kuma ka za6a mini wanda zan aura Abul. Idan hakan da nayi duk akan farincikinka bai maka ba ka ajiye mini katin ni in fita in raba.�? “Ki bani zan je.�? Kuma yaje ya raba ya dawo jiki a sanyaye. Computer ya d’auka fara danne kamar mahaukaci lokaci-lokaci yana kiran wasu abokansa suna tura mishi link yana dubawa. Har k’arfe hud’u na dare ya kai kafin ya samu abunda yake so kana ya tashi ya nufi d’akin mamansa. Yana bud’e k’ofar ya ganta kwance a kan gado ga wasu mata sun yi shimfid’i a k’asa ta yanda bazai iya tsallakasu ya wuce gurinta ba. Komawa yayi d’akinsa da niyyar jiranta ta tashi zuwa k’arfe biyar tunda yasan bata bari sallan asuba ya wuceta. Sai dai yana kwanciya idanunsa ya rufe ruff ya fara nannauyan bacci ba tare da ya saka alarm ba. Washe gari tun asuba ‘yan uwa suka farka aka fara d’aura tukwanen breakfast a backyard tare da taimakon wasu masu girki da Laila ta kira. Karfe goma da rabi na safe Abul ya farka daga nannauyan baccin da d’aukesa ya duba yaga haske a kansa. A firgice ya mik’e tsaye da yaji hayaniyar mutane a cikin gidan, ba dai har an d’aura auren ba? A take ya d’auki wayarsa ya duba lokaci sannan hankalinsa ya kwanta kad’an domin yana da sauran lokaci wato minti talatin, tunda k’arfe sha d’aya za’a d’aura auran. D’aukan Laptop d’insa yayi zai fita waje ya tuno cewa bai yi sallan asuba ba, k’arshe sai da yayi sallah sannan ya fita yana neman mamanshi Sabrin ta fad’a masa tana gidan Ummii. Kid’imewa yayi ya fito harabar gidan yana duba agogon hannunsa, mutane na kiransa d’an amarya amma ko kulasu bai yi ba. “Abul ya naga baka shirya ba gashi saura minti sha biyar a d’aura auren?�? Fad’in wata mata ‘yaruwarsu. “Zan shirya.�? Kawai ya fad’a ya fice a gidan da gudu yana ciro wayarsa a aljihu ya danna kiran kawunsa. Ina zai fara zuwa? Wa zai nunawa abunda ya binciko ya hana wannan auren? Za’a d’aura auren ne duka a babban masallacin jumm’an dake kusa da gidansu Naana matar Mas’ud, saboda hakan ya zama sauk’i ga mutane masu son zuwa d’aurin auren Mas’ud da kuma na Laila. “Uncle Mas’ud kar a d’aura auren Mama.�? Ya fad’i hakan yana tare d’an acha6a saboda shi zai fi yin gudu. Mas’ud dake cikin taron abokansa ya matsa gefe yana rage sautin muryarsa yace, “Abul yau ma wiwin ka sha? Ina kake?�? “Gani nan zuwa amma karku d’aura auren sai nazo don Allah.�? Mas’ud kashe wayarsa yayi cikin takaici domin halin Abul ya fara isarsa, yana son fad’awa Laila inda ta gaza amma baya son abunda zai sa ta kalleshi a matsayin wanda baya son ‘yayanta. Saka wayar yayi a silent ya jefa a aljihunsa kana ya koma gurin abokansa aka cigaba da jiran lokaci a d’aura aure. Auren Mas’ud da Nana aka fara d’aurawa a bisa sadaki dubu sittin. Madu waliyyin Amarya Laila ya matso tare da waliyyin Ango Abdul (wani k’anin babansa) shima ya matso suka fara magana. “Wai a dakata da d’aurin auren nan domin Ango bai iso ba, an je d’aukoshi a airport ya dawo daga Abuja.�? Wani abokin Alhaji Abdul ya fad’i hakan aka sanarwa masu bada aure da k’ar6a. “Ba dole sai an jirashi yazo kafin a d’aura ba, ya za’ayi mutum yayi lattin zuwa d’aurin aurensa? A ina aka ta6a yin hakan?�? Wannan fad’in Baffan Alhaji Abdul kenan cikin 6acin rai, domin tun ba yau ba ya tsani halayensa. Madu ya d’ago kai yace, “Tunda yace a jirashi sai a jirashi Alhaji, nasan nan da minti goma zai iso.�? Wannan magana yasa aka dakata da d’aurin auren Mas’ud kuma da abokansa suka fara hotuna a wajen masallacin. Minti biyu da haka Abul ya iso a jikkace kamar wanda yayi gudu ya dinga kutsawa cikin mutane yana tambayar ina kawunshi Mas’ud. Ko da yayi arba dashi tsayawa yayi cakk idanunshi na tara kwalla yace, “An d’aura?�? “An d’aura.�? Mas’ud ya bashi amsa yana lura yanda mutane suka tsaya cirko cirko suna kallonsu. “Kace mishi an d’aura aurenka amma banda na mamanshi. Kai yaro baka rasa auren ba, ana jiran Alhaji Abdul ne saboda bai samu isowa ba.�? Fad’in wani abokin Mas’ud yana dafa kafad’ar Abul. Wata wawuyar ajiyar zuciya Abul ya sauk’e kana ya dubi Mas’ud wanda yake jiran yayi abun rashin hankali ya sakashi a mota a mayar dashi gida. “Uncle Mas’ud kazo kaga wani abu kafin a d’aura auren don Allah.�? Mas’ud na jin haka ya ja hannunsa suka koma gefe ya fara masa fad’a sosai tamkar zai mareshi. “Ka tsaya ka kalli abunda zan nuna maka kafin ka mini fad’a. Don Allah ka saurareni kafin a d’aura auren in cuceta.�? Wannan kalma ta ‘cuta�? tasa Mas’ud ya dakata daga fad’an da yake yi masa yace, “Menene yake faruwa Abul? Me zai cuci Kalti?�? A take Abul ya bud’e masa laptop d’in dake hannusa ya kunna masa video mai d’aukan 20 seconds yana cewa, “Jiya a Abuja yayi Bachelor Party. Mas’ud na gama gani ya lalumi wayarsa ya kira Laila gumi na taruwa a goshinsa tamkar wanda ake watsawa ruwa. “Kalti ki kira Madu kice a dakata da d’aurin auren yanzu zan turo miki wani video ki gani.�? “Wani irin magana ne haka Mas’ud? Me yake faruwa?�? Laila dake d’akin Ummii ta fad’i hakan tana fita waje gurin da babu mutane. “Ki duba Telegram dinki yanzu yanzu Abul zai turo miki sak’o.�? Yana fad’in hakan Abul yayi danne-danne na sakanni biyar yace, “Na tura.�? Laila dake tsaye a bayan d’akin Ummii ta bud’e sak’on tana kallo, sai dai bata san lokacin da tayi zaman ‘yan bori a k’asan gurin ba tana jin hawaye na cikowa a idanunta, lokaci d’aya kuma suka fara silalowa kan k’uncinta. Share hawayen tayi cikin sauri kana ta tashi tsaye ta kira numbern Yayanta Madu. “A fasa d’aurin auren, ina son ganin Alhaji Abdul kafin nan.�? “Baki da hankali ne? Wani irin shashanci ne haka? Mun tara mutane sai kuma kice a dakata saboda me kenan? Babu dakatawan da za’a yi, Alhaji Abdul yana isowa za’a d’aura auren.�? Ya fad’i hakan cikin 6acin rai tamkar zai doketa ta waya. “Kar ka manta da bazawara kake magana wacce in babu yawun bakinta baza a d’aura mata aure ba, sannan ka sani har yanzu ban kar6i sadakin kowa ba.�? Tana gama fad’in hakan ta kashe wayar ta kira Mas’ud. “A dakata da d’aurin auren, na fasa.�? Tace dashi bayan ya d’auka. “Da waye za’a d’aura yanzu?�? “Babu kowa, na fasa yin auren har abada zan zauna a haka babu miji.�? Abul dake gefe yaji wani sanyi a ranshi har yana murmushi mai bayyana hakwara. “Bani guri.�? Mas’ud yace dashi Abul yayi saurin barin gurin yana had’iye dariyarsa. “Idan baki d’aura aure a yau ba wallahi tallahi zan sake matata muci gaba da zama haka ni da ke. So ki za6i duk wanda yayi miki cikin masu son aurenki ni zan bada aurenki tunda na zama cikekken mutum.�? “Mas’ud karka fara wannan maganar banza. Hankalinka d’aya kuwa ko kaima ka fara shaye-shaye ne?�? “Na miki rantsuwa da Allah Kalti, kuma ke kanki kinsan bana rantsuwa a kan abunda ba zan aikata ba. Ki za6a ko kuma in aika mata da text d’in saki yanzu nan.�? “Mas’ud kar ka mini haka, kar ka 6ata auren da ko awa d’aya bai yi ba.�? “Ki za6a kafin na k’irga uku. One….two….three.�? “Shikenan, na za6i a d’aura auren da Haydar.�? Wani murmushi Mas’ud yayi mai bayyana hakwara yace, “Shi kike so Kalti kuma kin sameshi Insha Allah.�? Yana fad’in hakan ya kashe kiran ya kira Haydar. “Kana ina?�? Tambayar daya masa kenan babu wata sallama ko gaisuwa. “Ina wajen d’aurin auren naku.�? Haydar ya bashi amsa kamar wanda bashi da lafiya. “Ka mini kwatancen inda kake.�? Madu yana gama magana da Laila ya mik’e tsaye a fusace yana cewa, “Yarinyar nan bata da hankali, mu zata mayar k’ananan yara? Zan je gida yanzu inji dalilin da yasa tace a dakata da d’aurin auren nan.�? Ya fita daga masallacin mutane suka bishi da ido suna mamakin me yake faruwa da Amarya da Ango duk suka kira suna cewa a dakata kar a d’aura aure? Alhaji Abdul yana hanyar zuwa masallaci Laila ta kirashi tace, “Abdul ina nemanka cikin gaggawa, kazo gidan Ya Madu yanzu.�? Alhaji Abdul da yake bayan motarsa ya tashi daga kishingid’ar da yayi cikin sauri. “Lafiya Laila?�? Ya fad’i hakan yana cire bak’in gilashin da yake idonsa. “Ka zo zaka ga dalili.�? “Driver juya ka kaimu gidan Yayan Laila.�? Ya fad’a yana mai mayar da gilashinsa domin bazai so kowa yaga idonsa a halin da yake ciki ba. Mas’ud yana had’uwa da Haydar ya ganshi a birkice kamar wanda ya kwana bai yi bacci ba, “Lafiyanka kuwa?�? Ya tambayeshi yana mai janshi gefe. Murmushin k’arfin hali yayi kana ya dubi Mas’ud yace, “Babu komai. Na tayaka murna Allah ya baku zaman lafiya.�? “Ameen. Kaima anjima za’a maka wannan addu’an, ka shirya auren Yayata?�? Haydar ya gyara tsayuwarshi cikin rashin fahimta yace, “Ban gane ba.�? “Ta fasa auren ubangidanka, tace a d’aura da kai.�? “No, no wasa kake yi. Kar ka mini haka domin baka san wani hali nake ciki ba yanzu. Kar ka d’auki alhakina saboda kana son rama abunda na muku.�? Ya juya zai tafi Mas’ud ya jawoshi ya tsayar dashi guri d’aya. “Kai ka saurareni, Laila ta fasa auren Abdul tace kai zata aura. Idan baka sonta yanzu In d’aura aurenta da wani don ba wai ta rasa masoya bane ta za6eka.�? “What the fuck, me yake faruwa ne?�? Ya k’ara tambaya domin shi har lokacin bai yarda da zancen Mas’ud ba. “Language young man. Kana so ko baka so?�? “Ina so mana.�? Yayi saurin amsawa. “Nawa ne a jikinka?�? Mas’ud ya tambayeshi yana lalumar aljihunshi. Haydar shima ya lalumi aljihunsa ya fitar da dari hud’u da naira ashirin yace, “Canjina na komawa gida kenan.�? Mas’ud ya k’ar6e d’ari hud’un ya had’a da kud’in hannunshi suka cika dubu hamsin yace, “Na cika maka dubu arba’in da tara da dari shida. Muje a d’aura muku aure.�? “Don Allah mafarki nake yi ko wasa kake mini.�?“Babu ko d’aya.�? Mas’ud ya dubeshi yaga yayi wani iri dashi kamar ba ango ba ya cire garensa da hulansa ya saka mishi yana cewa, “Zaka dawo mini da kayana idan aka d’aura aure aka gama hotuna.�? Da haka ya jashi suka kutsa cikin mutane har gurin waliyyin Alhaji Abdul yayi k’asa da muryarsa yace, “Yalla6ai kuyi hak’uri an fasa d’aura auren Laila da Abdul, kuma ta yarje mini in d’aura mata aure da wannan sunanshi Aliyu Haydar.�? “Me yake faruwa ne? Naga yayanka ya fita a fusace har yanzu bai dawo ba. Shima Abdul da ake tsamamnin isowarshi bai iso ba.�? A gurguje Mas’ud ya bashi labarin halin da ake ciki kana ya k’are da cewa, “Duk auren da za’a d’aurashi a kan zargi ba zai yi tasiri ba.�? “Kira mini ita inji ta bakinka ba don na k’aryataka ba.�? Fad’in Alhaji Shettima (waliyyin Alhaji Abdul). “Ni na amince a d’aura mini aure da Haydar kuma na yarjewa Mas’ud ya zama waliyyina.�? Laila ta bada amsa bayan Mas’ud ya tambayeta. Wani irin ihu aka yi a gefenta Mas’ud yayi saurin kashe wayar yana cewa, “Ina ga Madu da Abdul sun isa gida.�? Murmushi Alhaji Shettima yayi kamar mai farin ciki da hakan yace, “Ni zan k’ar6awa Aliyu Haydar auren Laila Kashim a gurinka, yaro ina sadakinka?�? Minti uku da haka aka d’aura auren Aliyu Haydar da Laila Kashim a bisa sadaki dubu hamsin ciff. Mutanen da suke waje suka cika da mamaki jin sunan Ango ya canja ya koma wani daban. Mas’ud ya fito da Haydar wajen masallacin yana nuna Haydar yana cewa, “Ga Angon.�? Daga nan danginsu da jama’ar Laila suka fara gaisawa dashi suna mishi fatan alkhairi. Shi kuma murmushi kawai yake yi amma zuciyarsa babu nitsuwa sam saboda har lokacin bai yarda da abunda yake faruwa ba. Dama Ammi ce ta matsa mishi yazo auren bayan nasiha mai had’e da fad’a data mishi. “Idan Laila matarka ce babu wanda ya isa ya hanaka aurenta Haydar, hakan zai sa ka gane cewa tun farko Allah bai yi kai zaka aureta ba. Kaje d’aurin aurenta ka tayata murna ka kuma yi mata fatan alkhairi domin ta soka da zuciya d’aya. Ka tayata farinciki idan har ka cika masoyinta na gaskiya.�? Gashi da yaji maganan mahaifiyarsa sai hakan ya zame masa alkhairi ya zama mijin Laila a lokacin da yake tunanin ta ku6uce masa har abada. Ana d’aukan hoto aka ga Haydar ya matsa gefe yayi sujjadar godiya. Mas’ud ya d’agoshi yana cewa zai 6ata mishi garensa da k’asa. Wasu abun ya basu dariya wasu kuma tun a gurin suka fara sukan auren suna cewa ta auri yaro k’asa da shekarunta. “Laila me yasa kika kirani nan alhali mun tara mutane a can masallaci babu wani gamsheshshen bayani.�? Wannan fad’in Alhaji Abdul kenan bayan ya iso gidan ya samu Laila a falon Madu. Bata ce komai ba ta bud’e wayarta ta nuna mishi videon ta bata son k’ara kallo a rayuwarta. Yana fara kallo ya cire gilashin idonshi wanda suka yi jaa kana ya dafe kanshi ya zauna akan kujera yana cewa, “Wallahi zan kashe duk wanda yayi mini wannan video koma waye shi.�? Ba komai bane a cikin video sai Alhaji Abdul tare da wasu abokansa biyar a wani Hotel a Abuja suna zaune a kan kujera ‘yan mata goma suna rawa a gabansu tsirara, Alhaji Abdul da yake rik’e da wata kwalbar giya sai ta6a sassan jikin biyu daga cikin matan yake yi yana jawosu jikinsa. “Ashe jiya k’arya ka mini cewa zaka je Abuja wani meeting d’in gaggawa? Ashe tsiyar da zaka je aikatawa kenan kuma a hakan ka aureni ba tare da na sani ba? Wallahi tun da na rabu da mijina har yau ban ta6a rik’e hannun wani d’a namiji wanda ba muharramina ba. Ina kiyaye dokokin Allah ban ta6a zina ko sha’awarta ba. Tunda har na iya kare kaina daga gareta bazan kuma auri wani mai yinta ba. Na fasa aurenka a karo na biyu Abdul domin tun farko bana jin sonka a zuciyata.�? “Karya kike yi munafukar mata, ke wani irin yawon bariki ne baki yi ba? A tunaninki bamu san kina neman yaron nan da fasik’anci bane?�? Furucin Madu kenan a yayinda yake shigowa cikin falon yayi kan Laila zai kwad’a mata mari Alhaji Abdul ya shiga tsakaninsu ya hanashi yana cewa, “Karka ta6ata Alhaji, Laila ta wuce duka, lalla6ata za’a yi.�? “Ka barni inyi k’asa-k’asa da ita ta gane cewa mu ba k’ananan yara bane.�? “Laifi na mata, kuma she have the right to be angry.�? “Idan laifi ka mata bata isa ta yanke hukuncin rashin aurenka ba. Ai komai namiji yayi ado ne, kuma idan kayi aure zaka daina duk abunda kake yi.�? Laila ta dubi yayanta Madu cikin mamaki ta takaici tace, “Kenan kasan halayensa kuma a hakan zaka bari in auri mutum irinsa? Wani irin tsana kake gwada mini Ya Madu? Wai me na maka ne ka tsaneni da har zaka iya jefa rayuwata cikin masifa ba tare da ka damu ba?�? Ta k’arisa maganan hawaye na tsiyaya a idanunta cikin bakin ciki. Bata zina, bata ta6a yi ba amma ya mata k’azafin cewa tana yi, sannan gashi wanda yake yin zinan a gaban idonshi ya rufa masa asiri har yana cewa wai zai daina idan yayi aure!! Me suke nufi da ita ne kuma me suka d’auketa? “Saboda kina da taurin kai da nuna isa. Ka bata sadakinta mu koma masallaci a d’aura auren nan.�? Madu ya fad’a yana mik’awa Alhaji Abdul hannunsa. “Ba zan auresa ba, kuma baka isa ka tursasani in auri wanda banyi niyya ba.�? Ta fad’a tana mai kafewa guri d’aya cikin dakewa. Wayarta ce ta fara ruri tayi saurin d’auka tace, “Mas’ud?�? “Ki fad’i shawarar da kika yanke saboda Alhaji Shettima na son ji daga bakinki.�? Ta san waye Alhaji Shettima, kuma ta san dole su nemi k’arin bayani akan canjawar al’amura cikin sauri haka, don haka ta bud’i baki tace, “Ni na amince a d’aura mini aure da Haydar kuma na yarjewa Mas’ud ya zama waliyyina.�? “K’arya kike yi Laila.�? Madu yayi maganan cikin d’aga murya yana nunata da yatsa. Wani irin zabura Alhaji Abdul yayi zai fita daga falon Madu ya rik’oshi. “Ina zaka je? Ai kafin ka isa an d’aura auren, ga wacce zaka matsawa ta kirasu tace ta fasa auren. Laila ki kira Mas’ud yanzu kice kin fasa auren.�? Tana jin hakan tayi cikin gida cikin sauri Madu da Alhaji Abdul suka rufa mata baya suna kiran sunanta. A can gurin d’aurin aure kuwa mutane sun fara watsewa zuwa inda za’ayi reception. Haydar ya yiwa Mas’ud magana murya k’asa-k’asa yace, “Ni fa hankalina bai kwanta ba, ina son zuwa wajen Laila kace yayanku da Alhaji Abdul suna tare da ita.�? Sai a lokacin shima Mas’ud hankalinshi ya tashi ya jashi suka isa gurin motarsa abokansa na kiransa yace, “Don Allah Jamil ku isa gurin reception muna zuwa.�? Yana fad’in hakan ya shige mota Haydar ma ya shiga suka wuce gidan Madu. A can kuma tashin hankali ake yi tsakanin Laila da maza biyu; Madu mai neman tursasa mata auren Alhaji Abdul har yana kai mata hannu zai daketa dashi kanshi Angon dole wanda yake rok’anta yana kuma hana Madu kai mata hannu. Mutane kuwa sunyi cirko-cirko suna kallon wannan abu cikin mamaki kamar a film din Hausa. Madu fad’a yake yi ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, Laila kuma ta kasa yin gaba ta kasa yin baya, domin bata son shiga d’akin Ummii su bita su tayar mata da hankali har hawan jininta ya tashi. Kiran wayar Alhaji Abdul da ake yi ba k’akk’auwa yasa ya d’auka a fusace yace, “Menene kuke da damuna?�? Abokinsa da ya kirashi yace, “Wani irin abu ne zaka kiramu d’aurin aurenka sai kuma muji an d’aura auren da wani…..�? Bai kai ga k’arasa maganan ba Alhaji Abdul ya jefar da wayar yana cewa, “Har an d’aura auren Madu, Shikenan ta faru ta k’are.�? “Bata k’are ba, domin a yanzu zata kira yaron ya saketa ka aureta.�? “Yaya Madu kana da hankali kuwa? Kasan me kake fad’a?�? Ta fad’i hakan tana ja da baya zata gudu d’akin Ummii domin yanda taga Madu ya canja kala kamar ba mutum ba yasa ta sha jinin jikinta domin bata tsammanin yana cikin hankalinshi. Hannunsa ya kai da niyyar kwad’a mata mari yaji an rik’e hannunsa ta baya wanda yasan ba k’aramin mutum ne ya mishi wannan rik’on ba. Juyawan da zai yi yaga Haydar, wato wannan yaron da ya wargaza musu shiri shi da Alhaji Abdul. Da ka ganshi a lokacin zaka gane cewa Ango ne, yana sanye da hula da gare fara wacce sai walkiya take yi tana d’aukar idanu a cikin rana. “Kar ka manta ita matar aure ce a yanzu, kuma ni mijinta bazan lamunci hakan ba.�? Yana fad’in hakan ya sake masa hannu kana ya koma gefe Laila ya sanya hannunsa a k’ugunta ya jawota kusa dashi har tana d’aura hannayenta saman k’irjinshi, domin bata tsammaci rikon ba. Kallonshi tayi tana ganin yanda ya had’e fuska tamkar bai ta6a dariya ba. “Haydar.�? Ta kira sunanshi a hankali. Ya sauk’ar da idanunsa kanta lokaci d’aya fuskarsa ta cika da annuri yace, “Na’am Matar Haydar. Ban fad’a miki cewa idan kika auri wani bani ba ba soyayyar gaskiya nake miki ba? Love conquers all and I’m here to protect you Mrs Aliyu Haydar.

Mum Fateey 👌

Back to top button