Karfe A Wuta Chapter 27 By Ayshercool
Biyo bayansu tayi, tana wani irin kuka mai ban tausayi, tana yi musu magiyar su sake shi, ba shi da laifi, amma babu wanda ya saurareta a cikinsu.Maƙwabta na jiyo kukanta, amma babu wanda ya iya ko leƙowa ya ga abun da yake faruwa.Shi kuwa Al’amin ko a jikinsa, kukan da take yi ne kawai ba ya so.Suka saka shi a mota, ta ce “To Yallaɓai ina za ku kai shi dan Allah””NDLEA, daga nan zamu miƙawa ‘yan sanda shi, su kai shi gaban kotu”.”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, yanzu dai sai kun kai shi NDLEA ɗin kenan? Wancan karon baku kai shi ba sai yanzu, dan Allah ku duba lamarin nan”Suka saka Al’amin a mota, suka tafi da shi, a falonta ta zauna, ta fashe da kuka, ta daɗe a wurin tana kuka, ganin hakan ba mafita bane, ya sanya ta tashi ta ɗauro alwala ta koma ɗakinta, tayi ta sallar da ba ta da tabbacin tana karanta ayoyin daidai saboda tashin hankali, ta ɗaga hannu tayi addu’a, amma ta kasa kawai ta mayar da kanta sujuda ta fashe da kuka.Har asuba ta yi idonta biyu, ta yi sallar asuba ta idar, ta zauna tana karanta duk abun da ya zo bakinta, wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirji, ta ji tamkar numfashinta zai ɗauke gaba ɗaya.Bayan sallar asuba magidantan layin suka tsaya suna salallamin, jiya da daddare ma’aikatan sun shigo layin, amma babu wanda ya fito.Malam lawan ya ce “Har kwa tambayi lafiya? Ai tun da ɗan daba ya tare muku a unguwa, sai abun da Allah ya yi, wurinsa suka zo, wataƙila ma wata ta’asar ya je ya tafka, suka zo suka yi masa ɗaukar amarya tsakar dare”.Suka yi ta salallami da fatan Allah ya kyauta.Har rana ta yi haske, jauhar tana zaune a wuri ɗaya, idanun ta sun yi ja, duk sun kumbura fuskarta tayi ja ta kumbura saboda kuka.Maman halimatu da wata mata mai kallon gidan na jauhar suka shigo, sai da suka yi ta sallama, da ƙyar ta iya amsawa sam ba ta ji sallamar ta su ba ma, ta fito falo ta ce su shigo.Maman halimatu ta ce “Jauhar, lafiya kuwa? Wai meyafaru ne jiya mun ji hayaniya, babu damar mu fito.Take wasu hawayen suka ziraro mata ta goge su ta ce “Jami’an tsaro ne suka zo suka tafi da shi””Subhanallah, laifin me yayi?”Ta girgiza kai ta ce “Ban sani ba””To ki yi haƙuri, ki samu ki ci abinci, sai ki nutsu a san abun yi, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba”Ta amsa musu da to ta gode.Kai ka ce takaba take yi, duk ta fita hayyacinta, ba ta san wurin wa za ta nufa da maganar nan ba, kuma ba ta san ina hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin take ba ma, balle ta je, ba kuma ta san ta tambaya a gano wani abun, gashi ko gidan su Al’amin ɗin ma ba ta sani ba, balle ta je ta gaya musu, ko da wani abu da za ayi a kai.Ta dudduba ta tattara ɗan kuɗin da take da shi, ta fita, ta samu mai napep ta tambaye shi idan ya san ina ne hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.Ya ce mata ya sani, ya ɗauke ta ya tafi da ita.Ta din ga yawo a cikin hukumar, aka ce mata ba ya wurin, ba a kai shi ba, sai da ƙyar aka ce mata yana nan, amma ba zata ganshi ba, babu irin magiyar da ba ta yi ba, amma suka hanata ganinsa, ƙarshe sai gida ta koma a matuƙar galabaice.Ta rama salollin da suke kanta, ta din ga addu’a da fatan Ubangiji Allah ya fitar da shi lafiya, da ta san abun da zai faru kenan, da ba ta karɓi abun da ba ta san ko menene ba ta ajiye masa.Ɗaya maƙwabciyar ta ta wasila, wadda mijinta ya taɓa raka su wurin mai chemist ta shigo gidan.Ta ce “Jauhar yaya ake ciki, kin same shi kuwa, kin je wurin ‘yan sandan?”Ta ce “Eh na je, ba su bari na ganshi ba””Kuma ba su gaya miki abun da yayi suka kama shi ba?” Ta jinjina mata kai alamar eh, wasu hawaye masu ciwo suna zubo mata.”Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki jauhar, in sha Allah komai zai wuce kamar ba ayi ba, kuma in sha Allah zai fito”Ta ce “To Allah ya sa”.Yau ma haka ta kwana salloli, da kai wa Allah kukanta, da fatan Allah ya saka mijinta yana lafiya ya kuɓutar da shi.Da safe ta sai ƙosai da buredi, ta dafa tea, ta kuma wanke ƙafa ta koma wurin nan, amma suka sake ce mata ba za ta ganshi ba, tayi magiyar har ta gaji, ta basu abincin ta ce su bashi.Ta koma harabar wurin, ta nemi wuri ta zauna, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, rabonta da abinci tun a jiya, gaba ɗaya tunanin halin da Al’amin yake ciki, da wanda zai shiga a nan gaba ya dame ta, ta gaji da zama ta tashi ta nufi gida.Ɗakinsa da suka shiga duk suka watsar da kaya ta shiga, dan damuwa ba ta bari ta shiga ta gyara ba.Duk sun watsar da komai na ɗakin, ta tattare masa kayan, tana cikin gyarawa ta gano wayarsa, ta ɗauka tana duddubawa sai ta ga tarin kiran walid da liti, cikin hanzari ta kira lambar walid.”Ya ne maza? Tun shekaranjiya ban sake jin ɗuriyarka ba, na zo gidanka ba kowa ka kuma ƙi ɗaga waya”.”Assalamu alaikum” tayi masa sallama.Ya ce “Ahh madam ke ce ashe? Ya ake ciki yana ina?”Muryarta na rawa ta ce “Shekaranjiya da daddare jami’an tsaro sun zo sun tafi da shi””Kamar yaya? Me yayi?”.”Abu aka kawo aka ce na ajiye masa, su kuma suka zo da daddare suka ga kayan a leda, suka tafi da shi na je sun hanani ganinsa” tayi maganar cikin kuka.Walid ya ce “Ya isa haka yi shiru, bari na zo gidan gani nan”Sai ta ɗan ji sanyi a ranta, tamkar yana zuwa zai fito mata da Al’amin ɗin.Kusan awa ɗaya da rabi, ta ji ana knocking gate.Da sauri ta tashi ta je ta buɗe, liti ta gani da Walid, har ƙasa ta durƙusa ta gaishe su.Walid ya amsa ya ce “Ya aka yi, meyafaru?””Yadda dai na gaya maka, wani ne ya kawo wata leda ya ce a ajiye masa, na manta ban nuna masa ba, kawai suka zo cikin dare suka tafi da shi, naje na je hukumar sun hana ni ganinsa”Liti ya ce “Ki yi haƙuri, ki daina kukan haka, kuma kin tabattar bai yi wani laifin ba?””Ni dai a iya sanina bana tunanin yayi wani abun, duk da ba tare muke yawo da shi ba, amma dai sun ce a kan kayan da suka gani a gidan nan ne”Walid ya ce “Ki kwantar da hankalinki, in dai Viper ne, mutum ne mai sa’a koma menene zai fito, amma ki kwantar da hankalinki, yanzu idan muka je babu lallai su sauraremu, amma in sha Allah gobe in Allah ya kaimu da wuri zamu je mu ga yadda za ayi”.Ta ce “To shikenan na gode sosai, bari na kawo muku ruwa””Kar ki damu a ƙoshe muke, ki kwantar da hankalinki idan da wani abu ki kira lambata”Ta ce “To na gode”Ta rufe ƙofa suka tafi, liti ya ce “Ikon Allah””Menene?””Kawai rayuwar Mai zamani nake kalla, yadda yake gararambarsa da kamar babu mai so, idan muka faɗa cakwakiyarmu, iya mu muke warware kayarmu, babu wanda ya damu da mu, shi kalli Allah ya kawo masa mai kula da shi”.”Haka ne, amma tausayi ta bani wallahi, yarinya ce sosai. Yana ta buyagi da rashin mutunci an yi masa aure, amma sai da ya mari madaki saboda ya tankata”.Liti ya kwashe da dariya ya ce “Kai mace fa aka ce maka, na raba ka”Walid ya kwashe da dariya ya ce “A ƙi faɗinsa, da madaki ya ce ya kashe ta, mazewa yayi ba zai motsa ba, wai ba shi ya aiketa ba, amma ka ga wasu jijiyoyi da suka tashi a goshinsa, ga wani gumi da yake a iya karan hancinsa, bai san yana wasu abubuwan ba” suka sake kwashewa da dariya.Liti ya saka su guduma ɗan gidan mai unguwa, su din ga kaiwa sun komowa, suna ɗan zagaywa a layin gidan viper, idan suka ga wani abu da ba su yadda da shi ba, su sanar masa.Suka cigaba da kaiwa suna komowa a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma su ma ba su samu ganin Viper ba, suka ce sai dai idan sun kai shi wurin jami’an tsaro su je can su ganshi.Hankalin Jauhar ya ƙara mummunan tashi, ta rasa in da za ta saka ranta ta ji daɗi.Ta sake amfani da wayarta, ta kira walid a waya, da yake sun ce kar ta sake zuwa hukumar, ta bari za su din ga zuwa su.Ta duba wayar kaf, babu sunan wani mutumin kirki a ciki, balle tayi tunanin akwai lambar wani ɗan gidansu, ta kira duk sai sunayen su Liti da ire-iren su.Sai kuma ta fara tunanin ko ba shi da kowa ne? Amma da ba shi da kowa ai ba zata ga kakarsa ba, kuma an nuna mata Rahila ranar da aka yi bikinsu Anty Zakiyya ta ce mata wai babarsa ce, amma tana tantama tun da aka yi auren, bai taɓa kai ta gidansu ba, kuma babu wani wanda ya zo daga gidan.Walid suka Kuma dawowa suna rarrashin ta, a kan suna ta ƙoƙarin ganin ya fito, ta gaza haƙuri ta ce “Dan Allah to ina ne gidansu, yakamata ace sun sani”Walid ya ce “Taɓ ke ‘yan gidan na su da suna ta tashi, da baki gansu ba, ki manta da maganar su kawai ki cigaba da addu’a”.Ta ce “Amma kamar yakamata a gaya musu halin da yake ciki, ko ba za su yi komai a kai ba”.Walid zai yi magana, liti ya ce “Bari na kwatanta miki gidan na su” yayi mata kwatance sannan suka yi mata sallama suka tafi.Liti ya ce “A irin wannan yanayin da take ciki, idan ba ka kwatanta ba sai ta tsaneka ai, idan ta je ta ganewa idonta shikenan””Haka ne, amma ka san wannan matsiyaciyar matar gidan na su ba mutunci gareta ba, kar ta ƙara mata zafi”. Suka cigaba da tattaunawa.Kusan kwanaki bakwai da kama Al’amin, idan ka ga jauhar sai ka ce tayi jinyar shekaru, duk ta ƙare ta fita hayyacinta.’yan sana’oin ma ba ta iyawa, saboda tunani da damuwa.Liti ya zo da safe, tana falo tana karatun Alkur’ani, ta ga kiran waya a wayar Viper, ta tashi ta fita ya ce “Sako hijjabinki mu je, sun bawa ‘yan sanda shi, idan Allah ya taimake mu, wataƙila mu ganshi” cikin tsananin zumuɗi, ta yafo mayafinta, ta rufe gidan suka tafi.Sai dai da suka je ɗin ma, tsugono ba ta ƙare ba, dan sun fi ƙarfin awa biyu, walid da liti suna safa da marwa, da faɗi tashin su ga Al’amin, Jauhar addu’a kawai take yi, tun da ta ga haka ta san lamarin ba ƙarami ba ne.Da ƙyar aka ce za su ganshi, aka tafi da wasu wani wuri, suka jira a reception ɗin sashen.Babu tsammani ta ɗaga kai ta ga yana tahowa, yana ɗingisa ƙafa, cikin hanzari ta miƙe tsaye ta zuba masa ido, kansa a ƙasa jami’an tsaro sun taso shi a gaba, su liti ma miƙewa suka yi tsaye, da ya kusantota sai ta ga jikinsa duk alamar duka, gefen fuskarsa a kumbure, haka wuyansa, shirt ɗin jikinsa tayi datti, duk busasshshen jini, take jikinta ya hau tsuma cikin tashin hankali.Ya zo ya nemi wuri ya zauna kamar basarake, gabansa ta ƙarasa cikin tashin hankali muryarta na rawa ta ce “Master, dukanka suke yi haka?””Maza wai meyafaru ne? Me ka yi haka aka kawo ka nan?” Walid ya tambaye shi cikin damuwa.Jauhar ta ce ‘Yallaɓai, dan Allah ku sake shi, dan Allah ku yi haƙuri ba zai ƙara ba, wallahi kayan da ku ka gani a gidan lafina ne, bai san da su ba, dan Allah ku yi haƙuri ku sake shi”Ɗaya daga cikin ‘yan sandan ya kalleta ya ce “Yarinya yayanki ba ya ji, ba zamu sake shi ba, wanda aka kama da cocaine ki ke cewa a saki ba shi da laifi? For more than 7days ya amsa laifinsa yaƙi, ga kaya an kama shi da shi, yayi magana yaƙi kamar dutse”Gaba ɗaya sak suka yi suna kallon ɗan sandan.”Wace irin cocaine kuma? Ka ga malam ba ma son rainin wayo, haba kai tare fa muke sabgar nan da shi, a gidan uwar wa zamu ga cocaine ɗin?” Walid ya yi maganar a matuƙar fusace.Cikin tsawa wani ya ce “Kai ka san a ina ka ke?””Na sani mana, ai ba lahira ba ce, balle ace mutum ta sa ta ƙare, ƙarshen abun dai ku kashe mutum, kai da muna harka da cocaine zaku ganmu a haka ne?”Jauhar ta yadda sai hali ya zo ɗaya ake abota, daga Al’amin har abokansa ba su da tsoro.Fashewa ta yi da kuka ta ce “Wallahi Yallaɓai zan iya rantsewa ba ya ta’amalli da cocaine, bai san ma in da zai same ta ba”.”Yayi bayani da bakinsa mana”Cikin hanzari ta koma wurinsa, ta ce “Dan Allah Master ka yi musu magana ko zasu ƙyale ka mu tafi, ka gaya musu ba taka ba ce ba, laifina ne”Yadda ginin wurin ba ya motsi, balle yayi magana haka Al’amin yayi kirim a wurin.”Dalla malam ka yi musu bayani, ka gaya musu ba ka ta’amalli da ita kar su yi ta tila maka na jaki a banza su nakasa ka” Walid yayi maganar cikin ƙunar rai, dan ya san ƙage kawai aka yi wa Al’amin.Liti ya ce “Kai ma ka san ba zai yi ba, wasu lokutan zuciya in dai irin ta shi ce ba ta yi ba”Jauhar ta riƙe hannunsa za ta yi magana, sai dai jikinsa kamar wuta Saboda zafi, sai yanzu ta tuna bai gama warkewa ba aka kama shi, durƙushewa tayi a gabansa ta cigaba da kuka.”Lokacinku yayi, zaku iya tafiya”Liti ya ce “Ko ba ku ce ba zamu tafi, kowa yayi na gari dai kansa ya yi wa”Al’amin ya miƙe tsaye, ya saka hannu ɗaya ya ɗagata daga durƙushen da take, ya juya zai koma, ta saka ƙarfinta ta rirriƙe shi tana kuka.”Ke wai meye haka, da ki ka samu aka bari ki ka ganshi” ɗan sandan ya daka mata tsawa.”Wallahi sai dai ku rufe mu tare, ni ba zan tafi ba, wai ya ake so na yi ne? Ya zan yi ko ina babu daɗi, ni komai nawa ba sa’a. Na gaya muku ba shi da laifi, amma dukansa ku ke yi, tayaya hankalina zai kwanta idan na tafi? Ba laifinsa ba ne wallahi, laifina ne na karɓi abu daga hannun wanda ban sani ba dan Allah ku ƙyale shi”Matsanancin tausayin da jauhar ta bawa liti, ya sanya ya fice ya bar wurin, kuka take iya ƙarfinta, Al’amin har mamaki yake yi, tsakaninsa da ita ba wata shaƙuwa ko kulawa ta musamman amma idan abu ya same shi, gaba ɗaya sai ta rikice.Walid tsayawa yayi ya ga viper zai rarrasheta ko kuma ƙasaitar zai tsaya ya cigaba, da kuwa ko ‘yan sandan za su rufe shi, sai ya zage shi.Ɗaya daga jami’an tsaron yayo kan jauhar, da nufin ya ɓanɓareta ta ƙarfin tsiya, su mayar da Viper, cikin hanzari ya ja baya da ita a jikinsa, ya ɗaga masa hannu yana ƙara tsuke fuska.Ya saka hannu, ya ɓanɓareta daga jikinsa, ya riƙe hannayenta, gaba ɗaya kammnin fuskarta sun canza saboda idanunta sun kumbura sosai ta koma pink saboda kuka.Ya sunkuyo dai-dai fuskarta ya ce “Kin kusa fara exam, ki yi karatu sosai, kar ki zauna zaman shiriritar nan, ki yi ƙoƙari ki yi karatu ki zama lawyer ko likita, ko dan saboda fitinannen mijinki, ki gaida mini da kwaɗinki da ƙadangaru idan kin koma gida” tana jin yadda jikinsa yake fitar da hucin zafi da warin datti, kwana bakwan nan babu alamar wanka ko wadataccen abinci a tare da shi.Ya kama kafaɗarta, ya saita ta hanyar fita ya ce “Kar ki sake zuwa wurin nan saboda ni” ya kalli walid ya nuna masa Jauhar, ya yi masa wata inkiya, ya juya suka mayar da shi.Suka fito tana kuka, liti ya girgiza kai ya ce “Wallahi Mutanen nan ‘yan wuta ne”Walid ya ce “Kai wannan hurumin Ubangiji ne, amma ko dan hakkin yarinyar nan Allah sai ya kama su, a gidan uwasu zai ga cocaine ɗin, wallahi ƙila su suka zo da abar su suka saka masa””Zasu aikata ai ba tsoron Allah suke yi ba” sun yi gaba suna ta surutu suna zage-zage da tsine-tsine.Suka nemi jauhar suka rasa, suka waiwaya, tana bakin ƙofar in da suka baro, ta zauna dirshan tana matsar hawaye.Liti ya ce “Taɓ lallai sabga da mata sai haƙuri, wannan ko mutuwa yayi abun da za ta yi kenan”Walid ya ce “Sai an yi mata uzuri, ba ta saba ganin wannan tashin hankalin ba, ina zuwa”.Ya koma da baya wurinta, ya zauna ya din ga rarrashinta, tare da ba ta tabbacin Aminu zai fita.Cikin kuka ta ce “Ba ma fa shi da lafiya, zazzaɓi ne a jikinsa””Ki yi haƙuri, Allah zai bashi lafiya”Ta sake cewa “To yanzu daga nan me za su yi masa?””Wallahi ba mu sani ba, amma zamu cigaba da bibiya in sha Allah, sai mun ga abun da ya ture wa buzu naɗi” da ƙyar ta taso, suka kaita har gida, Walid ya ba ta kuɗi, ta ce ba zata karɓa ba, sai da ya ce mata Al’amin ne ya ce ya bata sannan ta karɓa.Har ta shiga falo, aka buga mata ƙofa, ta dawo ta buɗe, ta ga Malam lawan baban su halimatu a tsaye.Ta durƙusa ta gaishe shi, ya ce “Wato duk na san ke da mijinki, kuna jin haushina, amma ni duk in da gaskiya take sai na faɗa. Ke yanzu ki ji da halin da mijinki yake ciki, amma kin zo kina tara mana maza a layi, kusan kullum sai sun zo, shi fa aure abu ne mai daraja da muhimmanci”.Jiki a sanyaye ta ce “Tara maza kuma?””Eh mana, wannan da ku ke fita tare da su ku dawo, muharraminki ne?”Kalmar ta yi mata nauyi sosai, amma ta dake ta ce “Aboknsa ne, su ne suke taimaka mini a kan case ɗin sa””To ke me yayi miko zafi? Ki koma gidanku mana, idan ya fito kya dawo, ko ma ki haƙura da auren, da kyanki da ƙuruciyarki nan da nan wani zai aureki, shi kuma ya cigaba da shashancinsa”.Ta ce “To na gode sosai””Ai gara dai ki san abun yi, ni Allah ya sa ma ba iyayenki ki ka bujirewa a kansa ba, Allah yake jarabatarki ba” gaba ɗaya sai ta ji kimarsa ta zube a idonta.Jauhar ta kama Alƙur’ani da da carbi, tayi ta Addu’a tana gaya wa Allah.Aka sake shafe kwana biyar, su liti suna yi mata yawo da hankali, suka kuma hanata komawa wurinsa, sai su ce mata sun je yana lafiya yana gaisheta.Haka kurum ta ji a ranta ƙarya suke yi mata, ba tare da sun sani ba, ta sake ɗaukar ƙafa ta tafi wurin ‘yan sanda, har da abincinta ta tafi da shi, sai dai suka tabbatar mata sun kai shi kotu, har alƙali ya aike da shi gidan gyaran hali, zuwa lokacin da za a cigaba da shari’a.Cikin tashin hankali ta tambaye su, zuwa yaushe zai fito.Suka ce mata ta tafi kotun ta tambaya, suka din ga yi mata wasa da hankali, har da wanda suka biyota da maganar lalata.A ƙofar gida, ta tarar da su walid, sai jan ƙafa take da ƙyar, ta ƙarasa.Walid ya ce “Madam ina ki ka tafi ne, mun zo ba kya nan?”Ta kalleshi cike da karaya ta ce “Dama an kai shi prison ba ku gaya mini ba?”Liti ya ce “Komawa ki ka yi kenan, ke ana ta ɓoye miki, dan kar ki tayar da hankalinki, shi muka zo gaya miki, sai da muka tsara yadda zamu gaya miki, yadda ba zaki damu ba, amma kin tashi kin tafi kin jiyo wa kanki damuwa”Ta ce “To ya zan yi, na kasa jurewa”.Walid ya ce “Yanzu dai tun da kin riga kin je kin ji da kanki, shikenan amma ki yi haƙuri zamu nemo wata hanyar mijinki zai fito in sha Allah”Jinjina musu kai kawai tayi, ta shiga gida. tuna da liti yayi mata kwatancen gidan su Al’amin, kamar korarriya, ta sake ɗaukar hanya, ta tafi unguwar su Al’amin tare da fatan Allah ya sa idan ta je gidan su Allah ya sa a dace a samu hanyar fitar da shi.Sai da ta haɗa da tambaya, sai dai gidan na su ba ɓoyayye bane ba, mussaman ma sunansa da ya riga ya shahara sosai.Sau biyu tana sallama aka amsa, mata wata matashiyar budurwa, da zata girme mata ta leƙo ta amsa.Ta ce “Ya aka yi?”Jauhar ta yi murmushi ta ce “Baƙuwa ce”Amira ta ce “Baƙuwa daga ina?”Rahila ta ce “Amira ki bari ta shigo mana”Ta bawa jauhar hanya, ta ƙarasa ta shiga falon da sallama.Rahila na ganinta ta washe baki, cike da duniyanci ta ce “Amrya ba kya laifi, ko kin kashe ɗan masu gida” jauhar ta zube har ƙasa ta gaisheta.”Lafiya ƙalau, zauna a kan kujera mana jauhar” ta sunkuyar da kai tare da girgizawa ta ce “Nan ma ya isa””Amira matar Aminu ce fa, kawo mata ruwa dan Allah” kallon banza ta yi wa jauhar, ta gyara zamanta ta cigaba da danna waya.Rahila ta ce “Ke fa ‘yar wulaƙanci ce amira”.Jauhar ta ce “Ai a ƙoshe ma nake””Allah sarki, ya mijin naki, tun da aka yi auren ba ki zo mana ba” tayi shiru tare da sunkuyar da kai tana murmushi.”Bari yanzu babansu zai shigo, sai ku gaisa”.Amira ta saci kallon jauhar, kyakywar bafulatanar yarinya, daga muryarta kawai zaka san ba ta da hayaniya, ita aka aurawa Al’amin.Abbu ne yayi sallama suka amsa masa gaba ɗaya, ko da ya shigo sau ɗaya jauhar ta kalle shi ta mayar da kanta ƙasa, babu in da Al’amin ya bar kamanin mahaifinsa.”Abbu ga ‘yar ka fa, sirikarka matar Aminu”Ya ce “Subhanallah” ya zauna yana faɗin “Yarinyar kirki, tuba nake yi yakamata ace na zo gidan naku, tafiya ta kama ni ne, ina ga yau kwanana huɗu da dawowa, kuma ina maganarku sosai wallahi, dan Allah ki yi haƙuri””A’a babu komai, ai mu ne masu laifi, tuntuni yakamata ace mun zo, ban san gidan nan ba ne shiyasa shi kuma bai kawo ni ba”Rahila ta ce “Hmm, dama ya za ayi ya kawo ki, ai ko za a shekara sai idan rashin mutuncin sa ne ya kawo shi” yanayin maganganun da rahila tayi, ya tabattar mata da ba ita ce mahaifiyar Al’amin ba.Abbu ya ce “Ina fatan dai ba wata matsala, ba yayi miki wani abu na rashin kyautatawa?”Tayi ajiyar zuciya ta ce “Ba ya yi mini sai dai..” sai kuma ta yi shiru.Rahila ta yi farat ta ce “Sai dai me, ki faɗa ba wani abu, ai mu duk iyayenku ne”.”Ƴan sanda ne suka zo mana cikin dare, suka kama shi suka tafi da shi, naje na kuma zuwa anƙi sakinsa, wai suna zarginsa da ta’amalli da hodar iblis”.Rahila ta ce “Taɓ! Ki ce shi likkafa ce ta cigaba a harkar shaye-shayen har ya kai wannan matakin?”Jauhar ta ce “A’a ba ya amfani da ita, wani ne ya kawo ya ce a ajiye masa, ban san kowaye ba, su kuma suka zo amma wallahi ba shi da laifi, shi ne na ce bari na zo, dan Allah baba ko da hanyar da za a bi a sako shi, ba ma shi da lafiya wallahi, da na je dukansa suke yi, jikinsa duk shaidar duka” ta ƙarasa maganar tana kuka, duk yadda ta so riƙe hawayen amma abu ya gagara.Rahila ta ce “Au dama shi ne dalilin zuwan naki? Sai da matsala ta afku ki ka nemi gidan ubansa, in dai wannan ne ya saba, kina zaune ‘yan iskan da suke bashi goyon bayan yin rashin mutunci za su saka a sake shi”.Abbu ya ce “Ya isa haka rahila” ya kalli Jauhar ya ce “Ki daina kuka yarinyar kirki, case da ya haɗa da irin wannan case ne babba ba ƙarami ba, Al’amin ba ya jin magana ko kaɗan”.”Wallahi baba ba shi ya kawo su ba, ban taɓa ganinsa da ita ba”.”Idan ma yana ta’amalli da ita, ba gaya miki zai yi ba ai”Abbu ya ce “Ki kwantar da hankalinki, idan da wata matsala ki koma gidanku, zuwa lokacin da komai zai daidaita, zan je na ga abun yi””Abbu ka san cocaine kuwa? Wallahi ka je suka fuskanci belinsa ka ke son yi, za su iya haɗawa da kai, ka dai koma gefe ka taya su da addu’a, duk masifar da ya janyo ta ƙare masa a kansa idan yana da rabo ya fito, idan babu ya ƙarata a can”.Kalaman rahila suka yi wa jauhar zafi da nauyi, ba shiri ta tashi ta ce “To bari na tafi sai anjima”.Rahila ta ce “Ki je gida ki yi ta addu’a, idan babu dama ki koma gida, amma shigar mahaifinsa wannan case ɗin ba mafita bane ba, kina zaune za a sako shi”.Abbu ya ce “Ki yi haƙuri kin ji, zai fito in sha Allah, zan san abun yi””Ka daina saka mata rai da zaka yi wani abu fa, haka kurum wani abu ya sameka gani ga ‘ya’ya ka barmu”Bayan tafiyar jauhar, Abbu ya ce “Rahila, anya ban yi wauta ba da na biye miki aka aura wa yarinyar mutane Al’amin ba, kalli yadda take cikin tashin hankali da damuwa fa”.”Wannan yarinyar fa da ka ke gani, ba a bar tausayi ba ce ba, ko ka manta kangarewa iyayenta ta yi suka nemi maraba da ita?””Duk da haka rahila, ni fa tantama nake yi a kan maganar nan, gaskiya ina ga zan jagoranci raba auren nan, Al’amin ba zai yi hankali ba””Abbu ina ruwanka, dan Allah ka bar maganar yaran nan”Jauhar kuwa bayan ta fita, ba tare da tunanin komai ba, ta nufi unguwar su, ta je ta samu baba, ko da wani abu da zai iya taimaka mata, ba tare da tuna haɗarin da hakan ka iya haifarwa ba, kodayeke wanda yake cikin ruwa ko takobi ka miƙa masa kamawa zai yi.
Ayshercool 08081012143
