Mijin Marigayiya Page 50 Hausa Novel
Ranar laraba aka kirawo su Mustapha, jirginsu zai tashi karfe biyar na yamma don haka aka basu shawara su kasance a cikin airport din tun kafin azahar. Sun gama hada kayansu shi da Najan kuma ya riga ya sanar da Khadeeja, ya danka mata duk wani abu da take bukata don kula da gidan.Wajen karfe sha daya yana zaune a parlor dinsa shi da yara Khadeeja ta fito daga dakinta ta shige kitcen don dora abincin rana. Ya tsallake yaran ya bi bayanta ya tsaya daga kofar kitchen din ya rungume hannuwansa a kirji sannan yace ‘Kada fa ki dafa abincin da ni yanzu zamu wuce airport, ki dafa ke da yara kawai.’‘To.’ Ta amsa murya kasa-kasa.Ya kula tunda sukayi maganar zubewar cikinta take son tada masa fitna shi kuma ba zai saurareta ba, fata yake kawai Naja ta gama hada kayanta su fice su bar mata gidan kafin ta takalo rigima. Don haka ya juya ya koma cikin yara ya zauna.Har ta dauko tukunya zata dora shinkafa sai kuma ta fasa, ta ajiye tukunyar ta fito daga kitchen din ta koma dakinta. Tana shiga ta wuce gaban mudubi ta ja kujerar ta zauna; bata san me ya sa ta fasa dora girkin ta zo ta zauna ba. Kamar dai tana bukara wani wanda zasu yi magana ne amma ta rasa wanda zata gayawa damuwarta ya fahimceta. Ta daga fuskarta ta kalli kanta a cikin mudubin, at yiwa kanta murmushi sannan ta sake sunkuyar da idanuwanta. Yanzu haka zata cigaba da rayuwa a gidan nan a matsayin ‘yar aiki? Tunda matsayinta bai wuce hakan ba, duk wasu alamu sun nuna. Mustapha ya tabbatar mata ba zai taba iya yi mata adalci ba tun ma tana ita kadai matarsa balle yanzu da ya hadata da wadda yake kauna. Ta sake daga ido ta kalli kanta a mudubin; to wai zaman me take a gidan Mustapha ne? Shi dai ya gama nuna mata ba zai taba canzawa ba; duk wani abu da yake yi mata a halin yanzu zata iya yiwa kanta. Bukatar aure ce kawai wadda dama sai ya gama dama yake zuwa wajenta tunda ta daina binshi dakinsa. Ta yanke kauna daga samun adalci a wajen Mustapha komai yawan kaunar da zata nuna masa da kulawarta ga ‘yayansa. Ta tabbatar shi ba zai iya nuna mata kauna da kulawa ba; watakila sai dai idan ana kwatan soyayya ta kwata ta karfin tsiya daga wajen Mustapha; to idan sai an kwata kuma ya koma ba so ba. Ta ja gwauron numfashi, ta zuba fuskarta a tafukan hannayenta, dumin hawayenta ne ya sa ta daga fuskar tata ta kalli hawayen da ya diga a hannuwanta. Ta jijjiga kai tana murmushi a lokacin da hawaye yake gangarewa a kumatunta; ta gaji, ba zata iya ba, ta gaji da wannan kokawar, ta gaji da kokawar kwatowa kanta mutunci da so a wajen Mustapha, ta gaji ba zata iya cigaba ba.Ta mike kamar wadda aka tsikara ta nufi gaban wardrobe, ta sauke akwati ta fara zuba kayanta. Ba zata iya cigaba da wannan rayuwar ba, gara kawai ayi ta ta kare.A hankali ya turo kofar dakin ya shigo da sallama, fuskarta fayau kamar ma farinciki take. Ta dubeshi ta amsa sallamarsa ta cigaba da jera kayanta a cikin akwatin. Ya dubeta da mamaki yace ‘Ya naga kina hada kaya, ko wardrobe din kike gyarawa?’Ta dan tsaya da zuba kayan ta kalleshi tace ‘No ba gyarawa zan yi ba, gidan mu zan tafi.’Mamakinsa ya karu, ya karsa matsawa kusa da ita ‘Ban gane gidanku zaki tafi ba bayan yanzu zamu tafi, shigowa ma nayi na gaya miki ki fito kuyi sallam da Naja zamu wuce.’Ta rufe akwatin ta zuge sannan ta juya cikin wardrobe din ta dauko jakarta ta sake ajiyewa a kan gadon. Ta kalleshi tace ‘Ka bani minti biyar na karasa hada kayana na fita sai ka rufe gidan gaba daya don nima gidanmu zan tafi.’Ya dan fara fusata ya matsa ya sha gabanta yana cewa ‘Bana son wulakanci Khadeeja, wai ke me yasa ne duk lokacin da mutum yake cikin uzuri yake so kiyi masa wani abu sai kin yi fitna ne? an gama magana dake amma yanzu saboda kina so ki sa muyi missing flight zaki fara maganar zaki tafi gida.’Tayi murmushi ta daga kai ta kalleshi tana cewa ‘In sha Allahu wannan itace fitna ta karshe da zan yi maka Mustapha, daga ita ba zan sake ba. Gidanmu zan tafi Mustapha saboda na gaji da aurenka, kuma na gama aurenka daga yau. Zaka iya sakina yanzu ko kuma duk lokacin da ka sami natsuwa ka rubuta min takardar sakin ka aiko gida; amma ba zan sake zama a matsayin matarka ba.’Gaba daya yawun bakinsa kafewa yayi saboda bai taba zaton Khadeeja zata iya fada masa haka ba, ya saketa! Kuma a wannan lokacin; ya kalleta ya sunkuyar da kai, jimawa kadan ya sake kallonta sannan yace ‘Saboda kujerar Makka kike so ki kashe aurenki Khadeeja? Kujerar da na gaya miki next year dake za a tafi. Tukunna ma kin san hukuncin matar da ta nemi saki a wajen maigidanta ba tare da wani dalili ba?’Ta jijjiga kai tana murmushi a daidai lokacin da kwalla ta fado daga idonta, ta share kwallar sannan tace ‘Ko daya, kujerarka ba ta kai ta daga min hankali ba tunda dai kasar Makka ta Alla ce ba taka ba. Alhamdulillahi ma kace wadda ta nemi saki ba tare da dalili ba; don ni ina da dalili kuma Allan da ya halicceni ya fi ni sanin dalilin. Amma tabbas yau zan bar gidanka da aurenka Mustapha.’Ya ja baya ya sake kare mata kallo, yace ‘Kin san me kike fada kuwa Khadeeja? Please idan wasa kike ki bari kada ki saka muyi missing flight.’Tayi yar dariya yayinda ta ware hijabinta ta saka tana cewa ‘Ba wasa nake ba, amma dai kana da zabi. Ka sakeni yanzu ko kuma ka tafi idan ka dawo ka rubuta min takardar ka aiko min gida.’Ta kwayeshi ta bude dauko jakarta daga kan gadon ta nufi gaban mudubi.Yana tsaye mamaki ya hanashi magana. Yana daga kai idonsa ya sauka a kan agogon bangon yake kafe a saman dakin; 12:52pm agogon ya nuna; shi da aka cewa su zama suna cikin airport kafin azahar.‘Mteww!’ ya ja dan gajeran tsaki sannan ya fesar da iska daga bakinsa. ‘Khadeeja yanzu ya kike so nayi da yaran bayan mun gama magana dake? Kuma me nayi miki da har zaki rike a matsayin hujjar da ta saka zaki ce na sake ki?’‘Yara kam ai yanzu ba matsalata bane, duk yanda kayi da su daidai ne. Ni dai zan tafi, yanzu in sah Allah.’Ta sauke akwatinta ta fara ja tana nufin koafr dakin.Ya bi bayanta da kallo; to me yayi mata da har zata ce ya saketa a wannan lokacin? Anya kuwa ta san menene zawarci? Kawai saboda bakin cikin ba da ita zai fara tafiya aikin Hajji ba? Ko ma me take nufi ya kamata ya cika mata burinta, watakila kafin ya dawo ta dawo hayyacinta kuma ta gane mahimmancin aure a rayuwarta. In ya so idan ya dawo da ita sai ta hakura ta zauna tunda dai shi bai ga wani abu da yayi mata ba.Tana daf da karasawa bakin kofar yace ‘Khadeeja.’Ta juyo ta dan tsaya ‘Ki je na sakeki saki daya.’Ta yi sauri ta juya fuskarta saboda kaucewa hada ido da shi; duk da ita nema kuma da yakinin zai aikata haka amma sai da fitar kalmar tayi mata ciwo. Ta sake juyowa cikin murya kasa-kasa tace ‘Nagode.’‘Zaki yi nadamar rabuwa da ni Khadeeja.’ Ya fada a gajarce.Ta kalleshi tayi murmushi sannan ta kawar da kanta ta faki idonsa ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta.Bugun kofa ne ya klatsesu da Shukra tana cewa ‘Abba Anti tace zaku makara fa.’‘Um, gani nan zuwa.’ Ya amsa daga cikin dakin.Ya wuce Khadeejan ya bude kofar ya fice. Ta bi bayansa janye da akwatinta. Shukra ta tsaya a gefenta tace ‘Anti kema harda ke za a tafi?’Ta kama hannunta tace ‘A’a ni gidanmu zan tafi ba da ni za a tafi ba.’‘Gidan Mommy? To damu zaki tafi?’ ta tambaya da mamaki.‘Eh, gidan Mommy zan tafi amma ba daku zan tafi ba. Abbanku zai gaya muku wadda zata zauna da ku.’Gaba daya yaran suka zuba mata ido suna kokarin gani me take fada. Ta kwalawa Hafsa kira ta bata umarni ta hada kayanta su tafi gida. Ba tare da bata lokaci ba ta juya.Ta dubi Naja wadda take zaune tana binsu da kallon mamaki tace ‘Maman Rukayya sai kun dawo, Alah ya amsa ibada Alah ya maimaita mana.’‘Amin.’ Ta amsa a gajarce sannan ta dubi Mustapha tace ‘Ban fa gane ba, me yake faruwa ne?’
