Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 11 Complete Hausa Novel

Ƙarar famfo da ta ji yana zuba ya farkar da ita

Shiru tayi tana tuna a inda take, 

Zumbur ta miƙe zaune tana kallon jikin ta

Ita dai ta san bata hau gado ba, amma ya akai ta ganta akan gado? 

Bata samo amsar tambayar ta ba, Abdul ya buɗe ƙofar toilet ya fito fuskar shi duk ruwa alamar ya ɗauro alwala ne

Kallon ta yayi yaga tai saurin janyo hijabin ta da ke a gefe ta saka

Murmushi yayi ya ɗaga mata gira ɗaya, murya ƙasa-ƙasa yace

“Daga baya kenan yarinya”

Murguɗa baki tayi ta sakko daga kan gadon, gab da zata shige toilet itama tace

“Thank God ba itace ta mayar dani kan gadon ba”

Tai shigewar ta ciki da sauri.

Murmushi kawai Abdul yayi, amma can ƙasan ranshi damuwa ce danƙare a ciki

Kabbara sallah yayi, sosai yake ma Allah godiya da abubuwan da suka same shi, ya jima a sujjadar shi ta ƙarshe kafin ya ɗago

A gefen shi zainab data fito itama ta kabbara tata a cikin nutsuwa 

Ɗan matsawa kaɗan Abdul yayi ya ƙure ta da kallo, yana tuna yarda taita ture shi a cikin bacci

Murmushi yayi yana miƙewa daga wajen ya koma kan kujerar dake gefen gado ya zauna

Wayar shi ya ɗauka yana duba saƙonni da kuma calls ɗin da yayi missing

Kaf ya gama scrolling, amma be ga saƙo ko kiran muslim ba

Ƙwarai da gaske abun da ya faru a jiya ya tsaya mishi a rai, ƙoƙari kawai yake ya danne tunda har Allah ya mallaka mishi warda yake ji a ranshi zata zame mishi mar’atussaliha

Sosai Abdul ya yi zurfi a tunanin shi, 

Tunda zainab ta idar ta waigo da niyar tai mishi magana taga ya afka can duniyar tunani

Yarda ya ƙura ma waje ɗaya ido haka itama ta kafe shi da nata idanun tana nazartar shi.

idon shi ta ga ya kaɗa yayi ja, gashi ya ɗan fara tara ƙwalla

A hankali ta matso kusa da ƙafar shi tasa yatsun ta biyu ta mintsile shi

Da sauri ya kalle ta yana janye ƙafar shi, 

Itama kallon shi take, seda ta ɗaga mishi girar ta biyu tukun fuska a ɗaure tace

“Tunanin ta kake yi halan?”

Zuciyar shi ɗaya ya ɗaga mata kai alamar eh

Da sauri zainab ta gyara zaman ta ido waje tace

“Wai da gaske kake? kace dama kana son ta ake son a raba ku?”

Da mamaki Abdul ya kalli zainab dake ta mishi muzurai da idanu, dan shi sam be ma gane me take nufi ba.

Gyara zaman shi yayi, ya maida hankalin shi kacokam kanta, yace

“Banfa gane me kike nufi ba”

“amma ka amsa min da eh? kawai waskewa zakayi dan kaga na gano ka, anjima nan zan kira Abie in gaya mishi su sani sun shiga tsakanin laila da majnoon”

Sosai yarda take magana ya bashi dariya, 

seda ya gama dariyar shi tsaf tukun ya dungure mata kai yace

“Mahaifiya ta nake tunani ZAINAB”

Yarda Abdul ya ambaci sunan ta ba ƙaramin dakar mata zuciya yayi ba, 

First time kenan da ta ji sunan ta a bakin shi

A ranta tace “inama ze sake maimaita sunan ni jikar IYA”

Jin ya ce mahaifiyar shi yake tunani abun ya bata mamaki, dan bata manta ba jiya Amal take cewa da wuri zasu tafi kar ummie ta nemesu ta rasa.

Can dai tace “Hummm, ashe maza ma na kewar iyayen su in sunyi aure?”

Murmushi Abdul ya sake yi a karo da dama, yace

“I wish auren ne kawai yasa nake kewar ta,” ya ƙarashe maganar raunin shi na bayyana ƙararar

Be jira ta sake cewa komi ba yace

“nasan Ammah zata so ta ganki zainab, ta rungune ki a jikin ta sannan tace miki ki kular mata da Abdul ɗin ta”

Gaba ɗaya Zainab ta kasa gane me yake nufi

Itama jikin ta a ɗan sanyaye tace

“Anjima base ka kaini muga juna ba?”

Murmushi yayi wanda ya sakko da ruwan hawayen da yake ta ƙoƙarin ganin basu fito ba, yace

“Tun ina shekara goma Ammah ta tafi ta barni, kuma a lokacin da nafi buƙatar ta a rayuwa ta Zainab!”

Dum,dum,dumm, haka  gaban zainab ya bada sound, 

Magana take son yi amma ta kasa, se mui-mui da baki da take.

Da ƙyar ta daure tace

“Kana nufin ta rasu wai?”

Gyaɗa mata kai kawai ya iyayi, dan in ya bata amsa da baki ze iya rushewa da kuka

Wani tausayin shi ne yazo ya lulluɓe ta, tanajin ƙaunar warda ya kira da sunan Ammah yana shigar ta.

A hankali ta tashi daga inda take ta koma kusa da shi

Hannun shi ta kamo ta saka a nashi ta fara shafa bayan a hankali,  kwantar mishi da hankali take son yi amma sam ta kasa buɗe baki tai magana, banda haɗiyar yawu ba abinda take.

Kallon ta Abdul yayi yaga yarda itama idanun ta suka kawo ƙwalla 

A nutse ya saƙalo hannun shi ya ɗora a kafaɗar ta, ta ɗan kwanto jikin shi, still kuma tana shafa bayan hannun shi

Cike da tausayin shi zainab tace

“Allah ya gafarta mata, Allah ya sake sada ku a aljannar firdausi, 

Addu’a zamu ci gaba da yi mata, shine kaɗai soyayyar data fi buƙata a nuna mata”

Sake matsota yayi sosai a jikin shi, yana jin wani sonta na daɗa shiga ranshi, bama musamman yanzu data nuna damuwar ta ƙiri-ƙiri akan damuwar shi.

Sun ɗau tsawon lokaci suna zaune a hakan ba wanda ya sake cewa komi suna sauraran bugun zuciyoyin su

Murya a hankali Abdul yace

“Ina kume me baki haƙuri da kika faɗo cikin rayuwata me cike da ƙalubale kala-kala Zainab, ana kawo ki kuka fara da ganin tashin hankali, sam ba hakan naso ba, amma ba yarda na iya tunda taƙi jin haƙuri balle lallashi”

A hankali zainab ta zare jikin ta daga jikin shi, ido cikin ido ta kalle shi tace

“Ina son sanin  waye kai, ya kayi rayuwar ka, ataƙaice dai ina son in san waye mijina”?

Gyara zama Abdul yayi, seda yayi mata murmushi tukun yace

“Anya wannan kunnuwan naki sun shirya jin waye mijin ki kuwa, na san ki sarai fa, abun kuka da wanda ba na kuka ba, ke kuka kike mishi”

Hararn shi tai, sannan tace

“Baka dai sanni ba kam, ni jaruma ce fa”

Tai maganar tana daria,

Lakuce mata hanci yayi yace

“Rannan fa madara kawai kika zubar, ki ka ɓare baki kina kuka”

Dariya zainab tayi, tana kallon shi, tace

“Baka san da yarda akai na samu kuɗin nan ba ne, kuma ka zubar, Allah dai ya temake ni ka biya”

Dariya sukai gaba ɗayan su, sannan Abdul yace

“Me zakiyi da madara a lokacin, ko ƙwaɗayi kawai yasa kika siyo?”

Nan da nan zainab ta koma kalar tausayi, ta bashi labarin magunan ta da Baba Ibrahim ya aza wa makamakan mazaunan shi suka mutu, se ƴar baƙa kawai da tai saura a cikin su.

“eyyah, Allah sarki, gaskiya nima naji miki mutuwar su, yanzu ina ƴar baƙar take?”

Taɓe baki Zainab tayi tace

“Mama tace zata haɗo da ita a kawo min in su Iya zasu dawo yau”

Ambaton Iya da zainab tayi seda yasa ka Abdul murmushi, tambayar ta yayi yace

“Ya kike da Iya ne?”

Dariya zainab tayi, tace

“Iya masoyiyata ce, iya kakata ce, iya ɗaliba ta ce, iya ƙawata ce,”

“wow, duka ita kaɗai?

“Anjima kaɗan zaku saba da ita, tana da saurin sabo”

“Allah ya kaimu kawai Abdul yace, amma can ƙasan ranshi yasan da wahala Iya ta dawo gidan nan, tsoron da ya gani a idon tsohuwar nan ba ɗan kaɗan bane”.

Har Abdul ya buɗe baki ze sake sako mata wata tambayar, ta saka hannu ta rufe mishi baki, tace

“Ni na fara tambayar ka fa, yanzu dai bani labarin rayuwar ka inji”

Gyara zama Abdul yayi ya janyo ta jikin shi, yace

“Kwanta da kyau yarda labarin zefi shigar ki matar Abdul”

Rufe fuska zainab tayi jin me Abdul yace, tana dariya ƙasa-ƙasa

Cikekken sunana shine Abdul’aziz…

Kafun ya ƙarasa faɗin sunan shi suka jiyo ana bubbuga ƙofar gate ɗin su da ɗan ƙarfi.

Tashi sukai dukan su, Zainab hada ɗan ɓata ranta, ta baje tana son jin labari.

****Tunda garin Allah ya waye Iya ta kasa samun nutsuwar zuci, da ƙyar ta yunƙura ta fito daga ɗaki ta nufi can in tafi jiyo hayaniyar sauran ƴan bikin

Tunda ta fito take amsa gaisuwa, har ta dangane da palon Abie

Waje ta samu ta zauna, bayan ta amsa gaisuwar su yaya muhammad da suma basu jima da zuwa gidan ba

Ba ta sake cewa uffan ba, se tagumi data rafka tana kallon yarda mama da yaran ta ke haɗa abubuwan da za’a kai ma zainab

A hankali take fakaitar idanun su ta share ƙwallar idon ta

Abie na hankalce da ita,

Kasa haƙuri yayi yace

“Lafiya dai ko Iya?”

Jira dama take a tambaye tace

“Yanzu fisabilillahi maza zaku haɗa da kayan nan?, 

a nawa shawarar me ze hana ai ma shi mijin zainab ɗin waya ya ɗakko ta su fito hanya se a haɗu da su a ƙarasa can gidan sirikan nata, muyi komi yarda aka saba yi, kar aja ma zainabu na gori a nan gaba”

Abie yace “Iya da dai an barshi kawai yaran nan su kai”

“A’a wallahi, na zan so ayi mata gori ba, al’adace akeyi tun zamanin iyaye da kakanni, kawai dai yanzu kayi yarda nace ɗin”.

Ba yarda Abie ya iya da ita, 

Yaya Abubakar yasa ya kira mishi Abdul ɗin

Bugu biyu Abdul ya ɗaga kiran, bayan sun gaisa yake sanar mishi da saƙon Abie

Anan gidan Abie ɗib kuma, mama bata sa da Iya ba, ƴan’uwan ta tai ma bayanin ba gidan zainab ɗin zasu je ba, 

Can gidan sirikan ta za’a

Da ƙyar dai aka samu mutum biyu suka yarda zasu je, suma dan ba su ga abinda ya faru jiya bane.

Tas aka haɗa komi a motar yaya Abubakar, se ɗayar motar kuma ƙannen mama suka shiga, har sun shiga Iya ta fito ɗauke da ƴar baƙa a hannun ta tace

“Nayi alƙawari, bana son Allah ya kamani da saɓa alƙawari, gashi ku kai ma zainabu na, kuce mata nace ayi ta haƙuri da zamantakewa, Allah ya sake haɗa fuskokin mu a aljannah”

Ƙin shiga motar ƴar baƙa tai, da ƙarfi da yaji Iya ta saka ta a motar.

Seda suka tafi tukun ta juya ta koma ciki, kafin ta kai ga shigewa sukai kiciɓus da Abie

Kallon ta Abie yayi yace

“fita kika yi ne Iya?

“Eh, na basu alƙawarin zainab ne su kai mata”

Be sake cewa komi ba, ta shige shima ya wuce.

Seda Abdul ya takura mishi da kira da naci tukun muslim yazo ya ɗauke su,

Ƙiri da muzu yaƙi ƙarasowa gate ɗin gidan Abdul, sedai suka taka suka same shi a farkon layi tukun ya ɗauke su suka tafi

Tunda suka shiga motar, Abdul be tanka ma muslim ba, Zainab ce ma da ta shugo tace mishi “ina kwana”

Sun ɗanyi nisa kaɗan muslim ya waigo ya kalli Abdul da ya rufe idon shi, kanshi na jingine da kujerar motar, 

Murya ƙasa-ƙasa yace

“I’m sorry guru, na kasa controling tsoro na sam, amma kayi min uziri pls”

Be buɗe idon shi ba yace

“Ba komai guy, na saba da hakan”

Harga Allah muslim beji daɗi ba, amma ba yarda ya ‘iya da al’amarin 

Zainab na zaune tana jin su, haka kurin taji ranta na ɓaci, a ranta take ta mitar

 “ai ba shi ya ɗora ma kan shi abin da suke gudun shi a kai ba, da sannu komi ze wuce da izinin ubangiji”

Ƙwata kawai tayi taci gaba da kallon titi, amma fuskar nan tata a tamke ba wani alamar murmushi.

Koda motar su yaya Abubakar ta isa gidan Abbah, basu shiga ba, ba kuma su fito daga motar ba

Suna nan a zaune har motar muslim ta yi parcking a gefen su kaɗan

Abdul ya fara fitowa ya ƙarasa saitin ƙofar yaya Abubakar da shima ke ƙoƙarin fitowa

Hannu ya miƙa mishi suka gaisa, tukun yace

“ku ƙarasa shiga ciki mana”

“Ai ni ba se na shiga ba, kayan cikin motata naku ne, can gidan ku zan sauke su,

yaya muhammad ne ya ɗakko wanda zasu shiga da zainab nan gidan”

Tare da Abdul ɗin suka ƙarasa ɗayar motar, 

A ladabce Abdul ya gaishe da su, sannan ya miƙa wa yaya muhammad hannu suka gaisa.

A nutse Abdul yace

“Ku ƙarasa shiga ciki”

Da “to” ya Muhammad ya amsa, sannan Abdul ya juya zuwa motar muslim

Zainab na kame a gefe tana ta baza idanu taga ta ina Iya zata ɓullo, Abdul ya ƙwanƙwasa mata glass, 

Seda ta ɗaga kanta ta ganshi tukun ta sauke glass ɗin

 sunkuyowa saitin fuskar ta yayi tukun yace

“Zaku shiga ciki, ni da Abubakar zamu koma can mu aje kaya”

Da “to” ta amsa, sannan tace “kayi addu’a in zaka shiga da fitowa gidan pls”

Murmushi yayi yace “inshaAllah”

Zagaya wa ta saitin muslim yayi, 

“guy, ku shiga ka aje ta, zamu je can gida na”

Kallon shi muslim yayi, kafin yace wani abu, Abdul yace

“Nasan ko nace kazo muje ba zuwa zaka yi ba guy”

Tsaki muslim yayi ya yi wa motar key, sannan yace

“Bari na aje ta inzo muje mana, Allah dai ya tsare mu da tsarewar sa”

Sosai dariya ke cin zainab, 

Yarda muslim yayi magana kokai ze baka dariya,

Ƙiri-ƙiri zaka ga tsoro a fuskar shi, amma a maganar shi ya dake shi ga namijin nan.

A tsaƙiya ƙannen mama suka saka Zainab,

Muslim yayi musu jagora har cikin palon ummie, 

Da Amal ya fara cin karo ya ce ta ƙarasa da su wajen su ummien, shi kuma ya juya ya fita

Ba wasu mutane a gidan, kamar ba jiya gidan yake a damƙam ba

Ƴan tsirarun mutane na da basu wuce a ƙirga ba

Har palon Abbah, Amal ta kaisu sannan tace “ku zauna, bari na kira ummien”

Juyawa ta yi tana satar kallon Zainab da fuskar ta ke rufe a hijabin ta

Ummie na can tana fama da fauza akan taci abinci, Amal ta shiga ɗakin da sallama

“Ummie ki zo kin yi baƙi”

Kallon ta ummie tayi tace “su waye?”

“Amaryar yaya Abdul ce da wasu suka zo”

shiru Ummie tayi, can tace “kice ina zuwa yanzu”

Juyawa Amal tayi ta fita, 

Seda ummie ta ga fauza ta saka wani abu a cikin ta tukun ta tashi ta fito itama

Bata yarda ta wuce palon Abbah kai tsaye ba, seda ta kira yayar ta da wata sistern Abbahn ta gaya musu zuwan su zainab ɗin

Sistern Abbah tace “Mu je, daman ai ana yin ƙore a al’adance, kuma ana damƙa amana ga iyayen miji”

Ba yabo ba fallasa ummie tace, “hakane, bari in ɗakko mayafi na a ɗaki”

Bayan gaishe-gaishe da akai, duk wani abu da ake na al’ada suka gabatar da shi, haɗe da damƙa amanar zainab ɗin

Sosai akai ma juna tarbar mutunci da dattako

Basu wani ɗauki lokaci ba suka ce zasu koma, 

Dukan su suka tashi suka fito harda zainab dake lulluɓe taƙi yarda aga fuskar ta

Har mota su ummie suka rako su,

Ganin zainab na ƙoƙarin shiga motar ne yaya muhammad yace

“Ke anan zaki zauna, mijin ki ze dawo ku wuce tare”

Shiru zainab tayi bata ce komi ba, sema ja da baya da tayi tana ɓata rai

Kallon ta ummie tayi, sannan ta ƙwala wa Amal kira,

Da sauri Amal tazo, ummie tace

“Kuje da zainab can ɗakin ku, akawo mata breakfast”

Da “to” Amal ta amsa, sannan ta kama hannun zainab ɗin

Har ta juya zata tafi ta dawo ta wajen saitin yaya muhammad, murya ƙasa ƙasa tace

“Yaya muhammad, IYA fa?”

Haka kawai yace “Bata samu zuwa ba, tace a gaishe ki”

“kuma bata baka saƙo ka kawo min ba?”

“eh ta bayar, Abubakar ya wuce da ita can gidan ki”

Bata sake cewa komi ba, tabi bayan Amal suka shiga ciki.

Se yamma lis tukum Abdul ya dawo gidan, Zainab nata kwasar bacci a ɗakin su Amal ya shigo

Yana shigowa, Fauza ta sakko ta bar ɗakin bayan ta gaishe shi

Saitin fuskar ta ya tsaya,

Daga ganin bacci da take kasan a takure take yin shi

A hankali ya ɗan taɓa fuskar ta yana mata tafiyar tsusa a kuma tu

Cikin bacci take jin waiwayi a fuskar ta, caraf ta riƙe hannnun shi gam a cikin nata taƙi saki, seda ta manna mishi mintsili tukun ta sake shi tana miƙewa zaune.

Sosa wajen yake yana kallon ta, murmushi yayi yace

“yarinya na kusa fara ramawa”

Miƙewa tsaye tayi tana gyara hijabin ta, ɗan taɓe baki tayi tace

“shine kaje kayi zaman ka ko?”

Kwaikwayon muryar ta yayi yace

“Naje nayi siyayyar abubuwa ne madam”

“Naji to, mu tafi gaskiya, na ƙosa naji labari na wallahi, tun ɗazu nake ta mita a cikin raina” ta ƙarashe maganar tana kallon shi.

Murmushi ya sake yi mata, idon shi a kanta, kai tsaye yace

“InshaAllah komin dare zaki san waye mijin ki,

Yanzu muje ki ma ummie sallama se mu wuce”

Har ƙasa Zainab ta tsugunna tai ma ummie sallama, 

Waigawa inda Abdul ke tsaye ummie tayi, tace

“Ba zaku jira Abbah ya dawo bane?”

“munyi magana da shi, zan kawo ta wani lokacin, yanzu ana ta zuwa ba’a samun ta”

“to shikenan, Allah yayi albarka, ya kaɗe fitina, ga abinci can nasa Amal ta kai muku mota”

Godiya sukai mata, sannan suka fito

Amal na tsaye jikin motar shi ɗauke da basket ɗin abinci a hannun ta

Kafin ya ƙaraso ya buɗe mata motar ta saka kwandon

Kusa da Amal zainab ta tsaya, 

“Se yaushe zaku zo Amal?”

Dariya Amal tayi tace “Aunty zee se munyo babban shiri tukun, wannan gidan na ku so yake yafi ƙarfin mu”

Murmushi kawai zainab tayi, itama ta tambaya ne kawai, amma ta san da kamar wiya, wai gurguwa da auren nesa.

Har seda Amal taga fitar su tukun ta koma cikin gidan, ranta fal tausayin yayan nata.

Suna tafe tsit, kowa da abinda yake saƙawa a ranshi, shi yana tunanin ta inda ze fara bata labarin shi

Ita kuma tana tunanin yarda kowa baya son zuwa gidan ta, bama kamar rashin zuwan IYA duk yafi damun ta

A yarda tasan anayi, washe gari in an kai amarya dangi na dawowa ayi ma amarya gyare-gyare amma ita kam wayam bata ga ƙafar kowa ba.

Ɗan waigowa yayi ya kalle ta,yace “tunanin me kike yi?”

“Bakomai” kawai tace taci gaba da kallon hanya har suka ƙaraso gidan

Da kanshi ya fita ya tura gate, sannan ya dawo ya shiga da motar

Kafin ya gama daidaita tsayuwar motar zainab ta zuruf ta fito

Gate ɗin ta tura da bisimillah, sannan ta sakaya shi.

Tana shiga gidan da ƴar baƙa ta fara cin karo, aikuwa da gudu  ta maƙalƙale zainab, tana kuka tana kaɗa bindin ta

Murnar da Abdul ya gani a fuskar zainab ba ƴar kaɗan bace, 

Amma hankalin shi sam be kwanta ba da ganin wannan baƙar magen, dan sarai ya sheda ta.

Basarwa yayi ya ce “Duk murnar ganin ta ne haka?”

Marairaice fuska zainab tayi, tace “dole inyi murna mana, tunda ita kaɗaice me sona yanzu”

Shiru Abdul yayi yana ci gaba da kallon ta, gaba ɗaya tausayin ta yake ji wallahi.

Seda suka ci abinci sukai sallah tukun suka dawo palo suka zauna

Suna a zaune Abdul ya haɗa TV ya kunna,

Zainab kam na can gaban bunner tana banka maganin da Abie ya bata 

Sanda zata shigo taga wata mujiya nata shawagi a waje, tasan sarai Abdul be lura da ita ba, kuma ita sam bata yarda da mujiyar ba.

Bayan ya kunna Tv ya dawo ya zauna akan kujera me cin mutum uku, 

Cikin kulawa Abdul yace

“Hayaƙin nan baze dame mu ba kuwa?”

Tasowa daga wajen tayi, sannan tace “beyi yawa ba ai”

Be sake cewa komi ba, se miƙa mata hannu da yayi

Ba musu ta miƙa mashi nata, 

Anan kusa da shi ya zaunar da ita, idon shi a kanta yace “kin shirya?”

Da saurinta ta ɗaga mishi kai.

***LABARIN BAYA***

Asalin suna na Abdul’aziz Usmanz, an haife ni a nan garin a anguwar babban layi,

Mahaifi na haifaffen nan garin ne, mahaifiyata kuma ba ƴar nan bace, a can garin su, Abbah na yaje ya auro ta.

A yarda Ammah take bani labari kafin a haife ni, tace min sun yi soyayya sosai da Abbah na kafin Allah yasa daga baya su mallaki juna, ya ɗakko ta daga garin su ya kawo ta nan cikin ƴanuwan shi da iyayen shi.

Abbahn su uku kacal baban su ya haifa, shine na farko se ƙannen shi mata guda biyu, suma suna aure a nesa.

Abbah be jima da auren Ammah ba, ciwon ajali ya kama mahaifiyar shi, ta rasu, ba wani tazara a tsakani shima mahaifin shi ya bita.

A wannan lokacin zumunci se yayi wahala, shi yana a nan garin, su kuma suna a wani garin daban, se lokaci zuwa lokaci suke ɗan haɗuwa.

A lokacin suna da shekara biyu da aure Ammah ta samu cikin ta na fari, 

Be yi wani ƙwari ba ya ɓare.

Sun ɗan shiga ruɗani, daga baya kuma suka haƙura suka fauwala ma Allah komi.

Bata wani sake jimawa ba Allah ya sake azurta su da ciki na

Sanda Abbah ya san da cikin sunyi murna sosai sunji daɗi, a lokacin ba wani wadata ce ke akwai ba, kawai dai ana gungurawa ne a haka

A haka yau da daɗi gobe akasin hakan, sukai ta rainon cikin har Allah yasa na fito duniya a ranar wata laraba da daddare.

Abbah na yayi murna da samun ɗa daga wajen abar son shi, kuma ta haifa mishi ɗa me kama da shi sak, har seda ya rinƙa tsokanar ta da “shi ɗin ba na wasa bane”

  A ranar Abbah na ya mallaka wa Ammah wannan gidan da muke a cikin sa, yayi mata kyautar shi duk da shima bashi da wani bayan wancan gidan da muke ciki a da

Ammah tayi murna ƙwarai, haka ma ƴan’uwan ta

A haka na taso cikin so da kulawar iyayena.

A lokacin da na fara wayo na gane mene fari da baƙi, rayuwar iyayena ke burge ni, dik da ina ƙarami a lokacin, amma tabbas ban taɓa ganin wata ruyuwar ma’aurata da suke so da ƙaunar junan su ba kamar Abbah da Ammah, ban taɓa jin daidai da rana ɗaya suna sa’in sa ba, 

Komi Abbah yace, to tabbas daidai ne a wajen Ammah, indai be saɓa ma Allah ba.

A ɗan tsukun nan ne, Abbah ya samu aiki a lagos, inda yake tafiya duk sati biyu yake zuwa gida

A lokacin ne na lura da Ammah kan dafe cikin ta lokaci zuwa lokaci, in na tambaye ta ammah mene, se tace min “bakomai, kawai cikin ta ne ke ɗan murɗawa”

Lokaci kaɗan kuma se ya sake ta yaci gaba da harkan ta.

Ammah macece me sanyin hali, kykkyawa fara tas da ita,

ba ruwan ta da abunda be shafe ta ba, sannan kuma bata taɓa tsallake umarnin Abbah, 

So take mishi na haƙiƙa.

Tun ina yaro Ammah ta kan kalle ni tace “yarona sena tantance matar ka da kaina, dan wannan kamar da kake da usman ɗina (Abbah) Ba ko wace mace ya kamata ta samu ba

Nidai nakan yi murmushi tun a lokacin dan ban fiya dariya sosai ba.

Wata rana da daddare ina kwance a cikin bacci naji kukan Ammah sama-sama, Abbah na ta faɗa kamar ze ari baki

Lamo nayi, saboda wannan abun sabo ne a wajena, ban taɓa ji ba

Can naji Abbah yan cewa “baki kyauta min ba murjanatu, kawai dan karki ɗaga min hankali shine zaki zauna a cikin ciwo ba zaki sanar min ba, ai ko bana nan zanje kije asibiti a duba ki”

Ita dai bata ce komi ba se kuka da take yi ƙasa-ƙasa

Asubar fari Abbah ya tasa ta muka tafi asibiti, 

Nidai ban san me likita yace ba, Ammah ɓacin ran da na gani a fuskar Abbah ya rikiɗe ya zama farin ciki.

A haka har Abbah ya koma lagos

Bayan tafiyar shi ne, Ammah ke ce min ta kusa ta yi min ƙanwa warda zamu rinƙa shawara tare, a lokacin ba wani gane magana nake a lanƙwashe ba

Ammah naji daɗi da tace zata min ƙanwa

Tunda Ammah ta samu cikin nan yake bata wahala, wani lokacin haka zata tasa ni a gaba taita kuka, in na tambaye ta menene? se tace min “itama bata sani ba”

Haka nima zan ta kuka, har se na ga ta dena

Haka kurin ko ina bacci se inji  Ammah ta rungume ni a jikin ta gam, wani lokacin har se na ɗanyi ƙara, seta ɗan sassauta riƙon da tai min,

Wani lokacin kuma se taita shafa kaina, tana cewa “Allah yayi maka albadka Abdul, Allah ya shiga lamuran ka”

A wani dawowa da Abbah yayi, aka sakani a makaranta, dama ina zuwa islamiyar Abie dake nan bayan layin mu.

Jin ya ambaci sunan Abie, zainab ta ɗaga kai ta kalle shi, 

Ɗaga mata gira ɗaya yayi yace “lokacin ba’asan za’a haifi wata ba”

Murmushi sukai a tare, sannan yaci gaba.

kullum da safe zanje boko, da yamma inje islamiya, a haka har cikin Ammah ya kai wata shida amma duk da hakan batai lafia ba

Ganin wahalar da take sha sosai yasa Abbah ya ɗauki hutu a wajen aikin shi ya dawo zama tare da Ammah.

Wata rana, an tashi a makaranta banga su Ammah sunzo tafiya dani ba

Dama indai Abbah na gari, zaka ga sunzo ɗauka na su biyu, 

Haka naita jira amma shiru ba alamar su, da yake makarantar ba nisa da gidan mu, haka na tawo ina bin gefen hanya har na ƙaraso gida

Tunda na tura ƙofar gidan na fara cin karo da jini, haka nai ta bin jinin nan, har ya dangane dani ɗakin kwanan su Ammah, tun da ni a lokacin sun dena kwana dani a ɗaki ɗaya

Ina shiga nayi mummunan gani Ammah ce kwance a cikin jini tana ta nishi sama sama

Da gudu na ƙarasa kanta, ina taɓa ta, kuka nake sosai ina tambayar me ya same ta

Kafin ta bani amsa Abbah ya shigo a guje yana faɗin “ga mota nan na samo murjanatu, yanzu zan kaiki asibiti”

Da ƙyar Abbah ya saka Ammah a mota, gaba yace in shiga, shi kuma yana baya tare da ita.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

AYI MIN AFUWA NA JINA SHIRU JIYA, JIKI DA JINI.

Kafin mu kai ga ƙarasawa asibitin Ammah ta jigata sosai, 

Muna shiga akai ciki da ita da gaggawa

Bayan wasu awanni Drn ya fito daga ɗakin da aka shiga da Ammah,

Be wani ɓata ɓana lokaci ba yace ma Abbah “sedai haƙuri ta rasa cikin”

Abbah sam ba ta kan cikin yake ba, tambaya yake “ya ita jikin ta yake”

Da sauƙi yace, 

Muna nan a tsaye aka fito da Ammah daga ɗakin aka canza mata wani

Sannan babyn  da ta haifa warda ba’a gama mata sauran halitta ba aka bamu a kwali

Rasa ya zeyi Abbah yayi, haka ya roƙi wata nurse ta ɗan zauna da Ammah ze je ya dawo

Kama hannu na Abbah yayi mu ka tafi, gidan inna gaje wata ƴar’uwar shi yaje ya sanar mata abinda ke faruwa,

Aikuwa ba ɓata lokaci ta shirya, muka dawo asibitin tare, seda ya nuna mata ɗakin tukun ya sake fita

Gida ya nufa ya ɗakko wa Ammah da ni  kaya, sannan ya dafo ruwan zafi tukun ya dawo.

Kwanan Ammah biyar a asibiti aka sallame ta, duk da dai ba wani ƙwari taji ba

seda aka fara sauke baba gaje a gida sannan muma muka wuce gida

A lokacin ni da Abbahna muke komi da komi na gidan har Allah ya ba Ammah lafia taji sauƙi

Bayan kwana biyu, da kanta taita ma Abbah magiya ya koma bakin aikin shi tunda ta warke

Da ƙyarnta shawo kanshi ya yarda, shima da sharaɗin cewa in har taji ciwo ko yaya ne ta garzaya asibiti,

(a lokacin wayar hannu bata shigo ba)

Hakanan Abbah ya shirya a washegari ya koma wajen aiki cike da kewar mu

Tunda Ammah tai wanna ɓarin ta dena walwala, kamar da, bata cika yin wani aiki ba, kusan koda yaushe tana a zaune

Haka zamu zauna, taita koya min abubuwan da ta san zasu amfane ni, 

irin su saka kaya, yin wanka, zata zauna ta wanke min bayana, se tace in ƙarasa tana kallo na, 

Ni kuma naita jin daɗi, an fara bari na yin wanka

Innaga shurun Ammah yayi yawa se in dame ta da surutu, har se ta biye min muyi ta yi 

Allah yayi min surutu ada, 

Na sha kama Ammah na kuka cikin dare ita kaɗai, amma in na dame ta da tambaya se tace min wai kewar mu ta fara

Sam ba san me take nufi da zancen ta ba

In taga nayi shiru ina so in fasa kalmomin ta, se ta kawar da hankali na ta hanyar yi min cakulkuli ko dai wani wasan.

A haka har Abbah ya sake zuwa yayi kwanakin da zeyi ya koma

Wata ranar alhamis da yamma bayan na taso makaranta, Ammah ta shirya ni tace unguwa zamu je

ni kuma Ina ta murna zamu je unguwa

Da muka fito daga gida, bamu tsaya ko ina ba se a wannan gidan da muke ciki

Lokacin gida ne irin na da, bama bene bane, ɗakuna ne kawai se babban palo, se kuma ƙatuwar tsakar gida

Ammah da kanta ta saka key ta buɗe gidan muka shiga, muka zagaya ko’ina

Ina ta mata surutun gidan yayi min kyau, mu dawo nan

Dariya ammah tayi ta kalle ni, sannan tace ” da gaske gidan ya burge Abdul ɗina?”

Gyaɗa kai naayi ina tsalle, sannan nace “Ammah na mu dawo nan gidan da zama”

Dariya tayi, sannan tace” Zamu dawo wata rana”

Oho, nikam wasa na kawai nake, dan ban ma gane can me take nufi ba

Seda ta gama zagaya ko’ina tukun tace “mutafi”

Kusan kullum se nayi maganar mu dawo nan da zama, 

Rannan da na ishe ta da maganar gidan, se tace “in ka girma kayi aure se ka saka matar a gidan”

Haka naita jin daɗi, tun daga lokacin na dena cewa mu koma can, sedai ince in nayi aure can zan zauna.

Ammah itace komi na a wannan lokacin,

Innace komi ina nufin komi

Munyi shaƙuwar da baki kaɗai baze iya fasalta yanayin shi ba

Wata rana Ammah taje ta ɗakko ni daga makaranta nake nuna mata abokina guda ɗaya da nayi, shine muslim, wanda ya ɗakko mu  ɗazu.

Ammah ta ganshi taga yarda nake ɗoki da murnar nayi aboki, shafa kan shi tayi tace “Allah ya ɗorar da abotar ku da alkairi”

Kullum zance wa Ammah ni da muslim munyi kaza da kaza, wanda ya dace ta hana se ta hana, wanda taga ba wani problem bane se ta tayani da jin labari

A haka har shaƙuwa ta shiga tsakani na da muslim, mu ka saba sosai, islamiyar mu ɗaya gidan su kuma ba wani nisa can sosai da gidan mu

Ni ban taɓa zuwa gidan su ba, amma shi duk ranar da ba makaranta yakan zo gidan mu muyi wasa, muci abinci a tare, sannan in Ammah taga yamma ta kusa, zata ce yaje gida kar a neme shi.

Wata rana mun samu hutu a makaranta, muka shirya nida Ammah muka kaiwa Abbah ziyara a lagos, 

Tun a hanya Ammah ke murƙususu ciwon cikin da yaƙi barin ta tun lokacin datayi ɓarin nan

Na shiga damuwa sosai, dan har kuka na fara, 

Seda cikin ya lafa mata tukun ta kalle ni, ta dungure min kai tace

“Kai fa namiji ne, ka dena saurin kuka a abu kaɗan mana,”

Ɓata fuska nayi, nace “Ammah bana son ki mutu ai”

Da mamaki Ammah ta kalle ni, ta buɗe manyan idanun ta tace “Abdul ɗina ya san mutuwa ashe?”

Nima ɓata rai nayi, nace “eh mana, malamin mu yace in an mutu baza’a sake ganin wanda ya mutun ba, ni kuma bana son in dena ganin ki”

Shiru Ammah tayi a lokacin, shafa kaina take, amma da na lura da kyau idanun ta sun cika da ƙwalla sosai.

Hannu na ɗaya na saka na matsa idon ta ɗaya, sega ƙwallar ta zubo

Da sauri ta saka hannun ta tashare tana kallo na da murmushi a fuskar ta, tace

“Ina nan inshaAllah, se na ga matar Abdul ɗina, na goya ƴaƴan Abdul ɗina a baya na”

Daɗi ne ya kamani, a lokacin ina ƙaunar inji Ammah tace zan yi aure,

Kuma ba dan komi ba se dan tace sena girma nayi aure tukun zan zauna a gidan nan, ba wai dan nasan mene auren ba.

nai ta surutun ni mata fara zan aura, me dariya irin na Ammah na, sannan me irin wannan abun

Hannun shi ya saka a goshin Zainab ya taɓo tabon sallar ta

Ammah na tana da shi, shiyasa nake son shi, gashi Allah ya bani, 

sedai ban sani ba ko ƙwaƙwido ce ke. ya yi  maganar yana ƙoƙarin janye ɗankwalin kan zainab

Da sauri ta dafe hannun shi ta galla mishi harara, tace

“Ni ba ƙwaƙwido bace”

Murmushi yayi, sannan yaci gaba.

Tun lokacin nan Ammah ke tsokana ta da mijin ƴar fara.

Bamu wuce sati biyu ba a garin lagos muka dawo harda Abbah

Haka rayuwa taita tafiya, har na shiga aji biyu a primary lokacin ina da shekara tara da wani abu.

Nai ta murna ina ƙara jin na fara girman da gaske.

BAƘAR RANA

Da daddare ina kwance bayan na gama homework ɗina, naji kakarin Ammah, dama ta kai sati biyu da ciwon ya dawo

Da sauri na tashi na shiga ɗakin, na iske Abbah zaune a gefen ta, hannun ta riƙe a cikin nashi

Sanda na shiga magana take mishi, amma tana gani na tayi shiru

A hankali na ƙarasa kusa da ita na riƙe ɗayan hannun ta, nace

“Ammah na menene?”

Shafa kaina tayi tace “bakomai Abdul ɗina”

Sosai ciwon ya sake murɗa mata, nan tai ta fama kafin daga bisani ya lafa

Hannu na dana Abbah ta kama ta haɗe waje ɗaya, idon ta akan Abbah tace

“Ga amanar yaro na nan na bar maka, ka kular min da shi dan Allah, kar ka bari yayi maraici na Hamza”

Sosai kukan da Abbah ke riƙewa ya sake shi, mirya na rawa yace “ki dena wannan maganar murjanatu, inshaAllah tare zamu ci gaba da kula da Abdul”

Murmushi kawai tayi itama tana share ƙwallar ta, nikam dama a lokacin saurin kuka ke gare ni, tuni na jima ina yin nawa

Sosai jikin Ammah ya lafa, har na fara bacci akan cikin ta

Cikin bacci sama-sama naji tace ma Abbah da ya barni taga naji daɗin kwanciya

Ina jin hakan na ƙara lafewa a jikin ta, saboda akwai wani abu da nake ji a lokacin kuma bansan mene ne ba

A nan gefen mu Abbah ya kwanta, kafin wani lokaci bacci ya ɗauke mu duka.

Huci me zafi Abdul ya fesar, idon shi sun kaɗa sun yi jaa

Kallon shi zainab tayi tace “in kawo maka ruwa ne?”

“a’a” yace, sannan yaci  gaba.

Gab da asuba na farka, kai na yana akan ƙirjin Ammah dake kwance, 

Sunan ta na kira nace “Ammah zanyi fitsari”

Ammah na bata da nauyin bacci sam, ko motsi ka cika yi zaka ji tace “ya akayi”

Shiru bata amsa min ba,

Da sauri Abbah ya farka yace min “kar ka tashe ta, zo muje in kai ka”

Abbah ya kaini nayi fitsari muka dawo, a hankali na koma in da na tashi na kwanta, se na ga hannun Ammah ya lanƙwashe, na ja zan gyara mata se na kasa

juyawa nayi nace “Abbah hannun Ammah ya lanƙwashe, kar yayi mata ciwo”

Tasowa Abbah yayi da niyar gyarata, yana janye hannun ta kamar dama jira take ta kifo gaba ɗayan ta

Da sauri Abbah ya taro ta yana kiran sunan ta

Ni dai ina gefe ina kallo

Can naga Abbah ya juyar da ita, kuma nan da nan naga jikin shi ya fara rawa yana kiran sunan Ammah a hankali yana tattaɓa ta

Da sauri naga Abbah ya kara kunnen shi akan ƙrjin ta

Daga ƙarshe kawai naga Abbah ya durƙushe a wajen ya fashe da kuka yana mai-maita kalmar “innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”!.

A hankali nace “Abbah me ya sami Ammah na?”

Be cemin komai ba, se kuka da yake ta dirza, can ya ɗago kan shi yace “sakko daga nan”

Ba musu na sakko, tashi yayi ya kama min hannu muka fita daga ɗakin,

Ɗayan ɗakin ya kaini yace “kwanta a nan kai baccin ka, Ammah bata son hayaniya yanzu”

Ba musu na kwanta, shi kuma ya fita a ɗakin

Har bacci ya fara ɗauka na naji sautin kukan Abbah ya daɗa yawa

A hankali na sakko daga kan gado na fito, a lokacin naji fitar Abbah waje, ni kuma se na shiga ɗakin da Ammah na take

Ina shiga na iske Ammah a rufe da zani, kuma tana nan a yarda na barta

Ban yi tunanin komi ba naje na cire zanin daga fuskar ta nace

“Ammah ba kince ba kyau mutum ya rinƙa rufe fuskar shi ba in yana bacci?”

Shiru Ammah bata ce komi ba, 

Ban damu ba saboda na san bata da lafia, ƙila bata son yin magana ne, da kaina na gyara mata rufar na bar idon ta a buɗe, sannan nima na shiga cikin zanin na rungume ta nai pilo da ƙirjin ta

Ina a hakan bacci ya ɗauke ni me cike da mafarkai kala-kala wanda bazan iya tuna su ba a yanzu.

A cikin bacci nake jiyo hayaniuar mutane, a hankali na buɗe ido na nagannin a ɗayan ɗakin ba’a kusa da Ammah na ba,

Mutane na gani sosai a zazzaune a ɗakin, wasu na kuka wasu sun yi jugum

Ƙannen Ammah na gani da kuma mahaifiyar ta, se wasu maƙotan mu da ake gaisawar mutunci

A hankali na sakko ina kallon kowa da kowa, mahaifiyar Ammah ce ta kamani ta rungume ni tana kuka take cewa

“Allah sarki Murjanatu, Allah ya raya maki Abdul, ke kuma Allah ya jiƙan ki”

Kallon ta nayi nace “Me ya samu Ammah na wai”

Shiru tayi tana ci gaba da kuka, 

Zare jiki na nayi na fita a ɗakin, ɗayan ɗakin na shiga, na iske Abbah tsugunne gaban gawar Ammah, shima yana ta ɓarzan kuka

Dafa shi nayi nace “Abbah ina Ammah na wai?”

Rungume ni yayi yana kuka yake ce min “ga Ammah nan kwance a gaba na, ta tafi ta barmu Abdul”

Bansan me nake ji ba a wannan lokacin, Ammah tashin hankali na shige shi bare in natuna da malamin mu yace “duk wanda ya mutu baza’a sake ganin shi ba”

Nayi kuka, nayi kiran sunan Ammah, amma ina taƙi amsawa

Inaji ina gani a ka fito da ita, mutane da yawa suka sallace ta

Bazan manta ba, Baba jazuli ne ya ɗauke ni ya maida ni gida, wai kar a barni na fito.

Da ƙyar na ƙwace na fito da gudu, lokacin har sunyi nisa

A baya, a baya na rinƙa binsu har maƙabar ta, ba wanda ya lura dani

akan ido na aka saka amma a makwancin ta, aka rufeta, haka akai ta watsewa, Abbah da yaƙi tashi a gaban ƙabarin wasu mutum biyu da ban san su ba suka zo suka kama shi suka tafi

Ni kuma ina nan laɓe a bayan wata bishiya ina ta kuka, kukan abubuwa da daman gaake kuwa.

Seda ƙafar kowa ya ɗauke a wajen sannan na fito daga maɓuya ta na ƙarasa gaban ƙabarin Ammah na.

Kasa ƙarasawa Abdul yayi, 

Ya fashe da kukan da yake ta dannewa, Zainab dake jikin shi ma ta jima da fara nata kukan.

Cikin dakiya Abdul ke share mata hawaye sannan yace

“Tsugunnawa nayi, ina kallon tulin ƙasar dake wajen, ina tuna duk wani rayuwar da mukai da Ammah, amma wai tana a cikin wajen nan

Kuka nake sosai a wajen, ba kowa ba kuma kajin motsin komi se kukan tsuntsaye

Ina zaune a wajen wata dabara ta faɗo min a rai, 

Tun da na shiga makaranta nake tara biro a aljihuna, wani lokacin harda red pen ma

Ina laluba aljihu na naji biro a ciki, ina fito da shi naga red pen ne

Tashi nayi daga wajen naje na samu dutsina guda uku ƴan madaidaita na ɗakko

Buɗe biron nayi ta ƙasan shi na cire hancin na janyo hanjin biron 

Ɗaya bagan ɗaya na rinƙa ɗaukan dutsinan ina zuba musu ink(ruwan biron) a jiki, seda na ƙarar da shi tas akan duwatsun, tukun na jera su akan ƙabarin Ammah.

Haka naita kallon wajen, in haddace wajen, 

Wajen kallon da nake ne naga wata bishiya a ta ɗan gefen ƙabarin Ammah, kamar an jani wajen naje, ina zuwa na kama gefen rigar shaddar jikin na saka haƙori na yaga da ƙyar, 

Na iya hawa bishiya, caraf na kama na hau, sannan na samu reshe ɗaya na ɗaura wannan shaddar tawa da na yaga a jiki, sannan na sakko na koma jikin ƙabarin Ammah nayi zamana har bacci ya ɗauke ni.

Su kuma a can gida ana ta nema na, ban san wanda ya bada shawarar a zo maƙabar tan a duba mi ba

Sedai na ga Abbah da kuma wani abokin shi sun ɗageni sama, ina ta kuka Abbah ma nata kuka mu koma gida.

Ko da muka je  gidan ban sani ba, dan tun a hanya naci gaba da yin bacci na me haɗe da ajiyar zuciya

Haka mutane sukai ta sintirin zuwa gaisuwa.

Lokacin da aka share zaman bakwai, mahaifiyar Ammah tace zata tafi dani tunda dai Abbah ba zama yake ba kuma bashi da wanda ze bari ya kula dani.

Abbah ya rufe ido yace be san da zancen tafiya ba, 

Baze taɓa iya rabuwa da ni ba

Mutane da dama sun saka baki akan ya bari a tafi dani, amma Abbah yace sam be yarda ba, shi ze zauna ya kula da amanar murjanatu da kan shi

Abun yaso ya kawo saɓani a tsakani, kuma cikin su kowa nada hujjar sa na kafewa akan riƙon nawa.

Aminin Abbah na yaja Abbah gefe yace

 “Usman sun fika gaskiya fa, ba yarda za’ai ace kana zuwa aiki sannan kuma ka haɗa da kula da yaro, abun zeyi maka yawa, amma shawara ɗaya zan baka, in har kana so ka rufe bakin su har su barmaka Abdul to tabbas lokaci yayi da zaka amsa tayin da Asiya ta jima tana  maka”

Shiru Abbah yayi yana tuna wacece ma Asiya, 

Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke, sannan yace

“mu bar wannan maganar mu samo wata mafitar dai, amma gaskiya bana son Abdul yayi nesa dani sam”

Ina daga gefe zaune shiru, na ɗaga kaina nace

“nima Abbah bana son na tafi na bar Ammah na da kai”

Wannan maganar da nayi itace ta warware duk wani shiri na Abbah na, tsananin tausayi na ya sa ya amince da auren ummie da kwata-kwata bata a gaban shi.

Auren Ummie shi ya kawo sanadiyar da mahaifiyar Ammah ta haƙura da tafiya da ni

Kwanan Ammah goma sha huɗu da rasuwa aka ɗaura auren Abbah da ummie.

A kuma ranar ne ƴan’uwan Ammah na suka shirya komawa garin su, an sha kuka sosai a ranar, kuma sun roƙi Abbah na da ya rinƙa kaini in har mun samu hutun makaran ta.

Tunda ga nan na fara gane lallai nayi rashi, in Abbah na a gida to ummie zata jani a jiki sosai, in kuma Abbah baya nan, to ba ruwan ta dani.

Kullum kafin Abbah ya fita ze min wanka ya shirya ni sannan ya fice.

Ganin bata a gaban Abbah yasa ta tsiro da karɓan ragamar komi nawa ya dawo hannun ta

Shi kuma ganin yarda take kula dani yasa ya fara sakin jiki da ita, har sukan zauna suyi fira

Dani tayi ammafani har ta samu matsuguni a wajen Abbah na, alhalin bayan idon shi ba haka bane.

A gefe kuma, kullum in har da kaina zan tafi makaranta bawai kaini za’ayi ba, se naje ƙabarin Ammah na, na maita ban ruwa sannan na zauna naita mata labari,

 wani lokacin in ta kuka, wani lokacin inyi bacci, shiyasa ba ko yaushe nake zuwa makaran ta ba.

Ana a hakan, Abbah ya shirya ze koma lagos wajen aiki, 

Amana ta kacokam ya ɗauka ya ba wa ummie.

Da ka kalli fuskar ta zaka san ba hakan taso ba, amma haka nan ta karɓa tai mishi fatan dawowa lafia.

Daga nan ne na fara shiga gararin rayuwa🥺

Kwata-kwata,  an dena tashi na sallar asuba, sedai da safe nake yi, 

Kuma bazata taɓa kwaɓa min aduk wani abu da zanyi ba, wala me kyau ko akasin hakan

Wanka dama Ammah ta fara koya min duk da ba wani iyawa nayi sosai ba,

Haka nan Ummie ta barni nake facaccala shi na watsa, in nagama ko mai bana shafawa

Da sauri da sauri in saka uniform ɗina da se ayi sati bata wanke min ba, in tafi makaranta ko wajen Ammah

A da ina ɗaya daga cikin yara mafi tsafta a ajin mu, 

Seda na koma nine mafi ƙazan ta, ba aski ba wanki ba kuma guga, 

uniform ɗina har wani tattara suke saboda rashin kula

Teachers su dake ni, akan rashin tsafta

 sannan babu wani wanda yake ƙawance da ni se muslim saboda bani da tsafta

Kullum a yunwace nake zuwa makaranta, shiyasa na dena gane komi da ake koya mana

 muslim ne ze zo da abinci sannan ya tsammini inci

Haka ko na koma gida ba lalle na samu wadatar abincin ba, zata bani ba wai bazata bani ba, amma baya isata

Sanda Ammah na da rai bana yawo daga islamiya se boko nake zuwa, se ko in da ita zamu fita

Amma rashin ta yasa na iya yawo kwararo kwararo, duk da bawai gidan kowa nake zuwa ba, se dai in ta zagaye na, in na gaji, ko kuma yunwa da ƙishirwa sun ishe ni se in koma gidan ko Allah ze sa in samu wani abun inci.

In nasamu inci, in ban samu ba haka zan kwana da yunwa ta kuma washe gari in ɗora daga inda na tsaya.

Tun da na gane kullum se an min dukan makara ko dukan rashin tsafta a makaranta, se na dena zuwa 

Kullum zan saka kayan makarantar, amma wajen Ammah nake tafiya

Haka nake zama a gaban ƙabarin ta nai ta kuka, ina gaya mata yunwa nake ji, haka nan zan ƙaraci surutu na har na gaji nai shiru

A lokacin ne na lura da wata farar mujiya da kullum in nazo wajen Ammah itama zata zo ta ɗan gefe ta tsaya,

Haka zatai ta kallo na, manyan idanun ta su cika da ƙwalla,

 tun ina jin tsoron ta har nazo na dena tunda bata taɓa yunƙurin cutar da ni ba

Wani lokacin ina nan a zaune zan fara jiyo hayaniyar mutane sun zo kawo mutum, haka nake tashi da gudu in ɗane kan wannan bishiyar da nayi ma sheda da kaya na, har su gama rufewa su tafi, sannan na sakko

Naje nayi kwanciya ta inda na saba kwanciya.

Se yamma liss nake tafiya gida shima ba dan na gaji da zama a inda nasan Ammah na tana wajen ba.

Kafin inje gida zan tabi ta gefen bola haka, in naga ɗan Abinda zan iya saka ma ciki na in tsaya in ɗauka inci, in ban samu ba haka nan zan haƙura na shiga gidan, kuma Ummie baza ta taɓa buɗe baki tace daga ina nake ba, ko kuma ga abinci naci.

Wani lokacin in na ɗaga ƙafa banje wajen Ammah ba, se in tafi gidan su muslim, bama kamar in inajin yunwa, zan daidaici lokacin da an gama musu abinci se inje

Muslim baya ƙyamata sam, duk da maman shi in ta ganni korata take, amma haka nan muslim ze saɗaɗo da abincin shi yazo muci tare

Da dai na gane maman sun da gaske bata son abokantakan mu da shi, se na dena zuwa,

Haka nan zan zauna nai ta kuka ni kaɗai, ga Abbah se yayi wata be zo ba a lokacin, ba kamar sanda Ammah na a raye ba.

Duk ranar da ummie ta san Abbah ze dawo, to ranar zata tasani a gaba tace inyi wanka, 

Haka zan ta cuɗa jiki na ina wankewa, har se taga na fita fes tukun take ƙyaleni, 

A ranar zata hana ni fita ko’ina, tai ta ja na a jiki har se na ɗan saki jiki na

Wani lokacin Abbah ze ta kallo na kamar me son gano wani abun, amma se ta janye hankalin shi

Yasha tambayana meke damuwana in mun keɓe, 

se ince mishi “ba komi”

Haka ze haƙura ya ƙyale ni.

Da ya koma bakin aiki se in koma ruwa.

Tun lokacin da na fara samun abinci a gefen ƙabarin Ammah na dena damuwa, 

Da naji yunwa komin dare zan tafi can, naci abinci na nayi tam sannan na dawo gidan

Ban taɓa tunanin ta yarda ake aje min abinci ba 

Wani lokacin in ina tafiya in har da duhu to za’a rinƙa haska min fitila har inje inda zani

Kuma zan rinƙa jin takun tafiya alamun ana raka ni

Tun ina jin tsoro har na dawo na dena

Sannan koda yaushe zan ga an wanke min kaya na an goge su tas, suyi ta zuba ƙamshi

In lokacin makaran ta yayi,haka kawai zanji ana sauya min kaya i zuwa uniform, kuma ta  kama hannu na ta  kaini har cikin ajin mu,

 sannan duk rashin

 gane karatuna saboda rashin zuwa makaranta, na dawo na fara ganewa

Haka nazo nafi kowa ƙoƙari a ajin mu, kafin teacher ya koya mana abu, ni na iya, teachers ɗin har mamakin sauyin da suka gani a tattare dani suke, anan na samu suna (guru)

To haka rayuwa taci gaba da tafiya, kuma rana bazata taɓa zuwa ta faɗi ba banje wajen Ammah na ba

A da a wajen nake samun abinci naci, yanzu kam har ɗakin da nake kwana ake ajiye min abinci na me rai da lafia, kuma in gama ci a ɗauke sannan a gyara min ko ina.

Wata rana na taɓa jin Ummie na fira da wata ƙawar ta akai na,  tace

“Ai tunda nayi banza da shi, gashi nan yayi ma kan shi da kan shi faɗa yana tsafta, 

Ai dama ni ba raino nazo ba, duk sun bi sun sangarta yaro be iya uban komi ba, in gaya miki da yaga ƙazan tar na gaf da kaishi lahira ai gashi nan ya koyi tsafta ta dole”

Nan sukai ta maganganun su, ina jin su.

*******

Wata rana ina gaban ƙabarin Ammah ina ta zuba mata ruwan da na ɗibo a rijiyar maƙabartan naji muryar Abbah a bayana

Da mamaki ya kalle ni yace

“Kana nan dama Abdul”

Shiru nayi ina aje bokitin hannu na, duk da na daɗe ban gan shi ba hakan besa nayi ɗokin ganin shi ba

Murya ciki-ciki nace “eh Abbah, ina nan”

Nan da nan naga idon Abbah ya kawo ƙwalla, rungume ni yayi yana shafa baya na

Be ce min komi ba, be kuma sake ni ba, mun jima a haka kafin daga baya ya juya wajen ƙabarin Ammah yayi mata addu’a sannan ya kama hannu na mu ka tafi.

A zaman da Abbah yayi a gida, anan ya gane sam bana zama a gidan, balle har inci abinci, da ya tambayi ba’asi a wajen ummie se tace ko ta aje bana ci kuma ko ta hana ni fita bana ji, itakuma bata so ta takura min shiyasa take ƙyale ni.

Layi-layi Abbah yabi yana nema na, ranshi ne kawai ya bashi yaje maƙabar ta ya gani

Gab da rana zata faɗi ya isko ni a wajen ina zaune gaban ƙabarin bayan na gama bashi ruwa na jingina da shi

A ranar seda Abbah ya zane ni, naita kuka kuma yaƙi lallashi na.

Da daddare ina kwance bayan na gama shan kuka na, naji kawai kamar ana jana 

Haka na tashi nayi ta bin wajen da naga ana jan nawa, har muka fice daga cikin gidan

Akwai duhu sosai Ammah ni ina ganin haske a gabana

Can bayan gidan mu aka zaunar dani, sannan aka buɗe min takarda shaƙare da nama me ƙuli.

A ranar na fara jin muryar ta, tace “Ci ka ƙoshi Aziz”

Naji tsoro sosai, jiki na babu inda baya rawa, amma se na fara jin sarewar da har a yanzu in na fara jin ta nakan mance komi da kowa a kunne na

A haka a haka har na dena jin tsoro, kuma na cika ciki na da naman nan na bar sauran a wajen.

Karkace wa nayi na kwanta, nan da nan bacci yayi awon gaba dani, se dai na ganni a ɗaki na da safe.

Kafin Abbah ya koma, kusan kullum se ya je ya tasoni daga maƙabar ta, abin ya dame shi sosai, har mamakin yarda nake gane ƙabarin yake, duba da yarda aka rufe mutane da dama a ƴan shekarun nan

A shekarar da na gama primary a shekarar ne na dena gane ƙabarin Ammah😭

Duk alamun da nayi an cire su, alamar da na saka a jikin bishiyar ma duk an sare su

Nayi kuka a lokacin kamar zan haɗiyi zuciya, 

Anan Abbah yazo ya same ni, ina kuka shima yana yi ya tasa ƙeya ta zuwa gida.

Wannan dalilin na tarewa ta a maƙabar ta yasa Abbah ya bar aiki a lagos ya dawo gida sannan ya nemi wani.

Wata rana, ummie na da tsohon ciki, lokacin in da shekara goma sha shida, ta aike ni na siyo mata kayan miya

A hanya ta tazuwa kuɗin suka zube, na koma gidan na sanar mata

Aikuwa nan ta haɗa ni da Abbah, tace haka nake, kullum in ta aike ni se na kashe kuɗin inzo ince sun faɗi

Abbah yaji haushin abun nan, yazo ya dena bani kuɗin kashewa na makaranta 

Sannan ya dena sakar min fuska,

To a wannan lokacin ne Aziza, ta sake bayyanar da kanta sosai gareni, inda tace duk wani abu da nake buƙata zata rinƙa bani,

Kuɗi kam se dai nayi kyauta da su, dan da na laluba aljihu na zanji kuɗi, kuma inje in siya duk wani abu da nake so.

Lokacin da Abbah ya farga da hakan, hankalin shi yayi bala’in tashi, dan yasha ya shigo ɗaki na ya iske muna fira da ita

Yayi ta mamakin yarda nake magana ni kaɗai

Daga ƙarshe da ya buncika ya gane nayi gamo ne, nan fa hankali ya sake tashi

To dama Abbah na zuwa wajen Abie time to time ɗaukan karatu,  a nan yake sheda mishi matsala ta na yarda bana son zama a cikin mutane, da kuma surutun da nake yawan yi ni kaɗai

Tun daga wannan lokacin Aziza ta dena bayyanar mun, sedai bata rabu dani ba

Dan har na fara karatun medicine ta temaka min ƙwarai da gaske, in ban gane abu ba zata buɗe min ido na tsaf na fahim ta, kuma a lokacin ne na lura da duk wata mace a faɗin duniyar nan kallon namiji nake mata ba mace ba, kuma duk warda tayi yunƙurin ta matsa min to tabbas se Aziza ta nakastata, da haka yawancin mata suka kiyaye ni.

Kuma gaba ɗaya ta dena min wanki da duk wani abu da take min, sedai gaba ɗaya na dawo bana son ƙazan ta ko kaɗan

Da ruwa da babu ruwa kullum se nayi wanka so uku, sannan bana fashin sharar ɗaki da dai wasu abubuwan.

Lokacin da Abbah ya gane irin riƙon da Ummie tai min, anyi babban tashin hankali, daga baya ta nuna mishi kuskuran ta, kuma kin san tsakanin mata da miji se Allah, ya zo ya gama fushin shi ya sauko.

Ido jajir Abdul ya kalli zainab da gaba ɗaya ta kasa dena kukan ta, yace

“Kaɗan ke nan daga cikin abinda na tsakuro miki a labari na,

In nace komi da komi zan faɗa miki ƙila se ruwan hawayen ki sun ƙare” ya ƙarashe maganar yana ƙirƙirar dariyar da ka gani kasan bata kai ciki ba.

Tashi zaune zainab tayi ta rungume shi ƴam-ƙam a jikin ta, tausayin shi da kuma ƙaunar shi na ratsa duk wata ƙofa dake jikin ta

Hannu biyu ya saka shime ya tallafe ta yana sakin ajiyar zuciya me sanyi.

A hankali zainab tace

“Lallai, a bola ko a maƙabar ta kayi gamo da Aziza, ta tausaya maka a lokacin da ba wanda ya sani

Yanzu ta gama nata, inshaAllah zan kula da kai fiye da yarda zan kula da kaina”

Kafin zainab ta sake cewa komi, suka ji muryar Aziza tace

“Duk da labarin nan da kika ji ba ze sa ki barmin Aziz ba?”

Tun maganar zainab na ƙarshe Abdul ya dena jin ta saboda bayyanar Aziza,

Da sauri zainab ta saki Abdul tana kallon hanyar kitchen da anan ne taji muryar ta

Da sauri ta miƙe tsaye tace

“Baiwar Allah ki fita ki barmu dan Allah, ban da son zuciya na jinsin ku, ina ku ina auren wanda ba jinsi ɗaya kuke ba?

In har temakon da kikai mishi saboda Allah ne, to ki jira ladan ki a wajen wanda kikayi domin shi mana, 

Haba dan Allah, ai se ki zoɓe ladar ki a wannan wahalar da shi da kuma mu da kike yi, to wallahi ki fita ido na kar kisa na taso ki a gaba!!!!”

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

ƳAN FACEBOOK INA MIƘO GAISUWA, SHARHIN KU DA KUMA ADDU’AR KU GARE NI, ALLAH YA BAR ƘAUNA❤️

TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!”

INA MATA ƳAN ƘWALISA?

A.A.G COMPLEX YA ZO MUKU DA NAGARTATTUN KAYA, WRAPPERS, LACES, SHADDA, SHOES, BAGS, KAYAN KITCHEN, ROBOBI PLASTIC AND MORE.

A FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA, MUNA MARABA DA KOWA DA KOWA

DOMIN ƘARIN BAYANI, ZAKU IYA TUNTUƁAR MU TA WANNAN NUMBER

07035046805.

Back to top button