Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 32 Hausa Novel

Idanun ya ɗan tsayar a kan Abeeha kan yayi baya da su kaman zai ɗauke sai ya sauƙe a kanta ya ɗan tsayar kan ya janye ya mayar kan abincin shi ya cigaba da ci in his majestic way.Wani irin bugawa zuciyarta ke yi fiye da misali, ko da wasa bata ji Mammi na maganar zuwanshi ba daga ita har Abeeha kasa gaba suka yi kuma sun kasa baya, ita dai Afeefah tsabar bugun zuciya har idanunta sun tara kwallah kiris take jira ta sako su, a tare suka juya za su bar wurin suka ji muryarshi ya ce “Ku zo nan!”Wani irin tsalle zuciyar dake bugawa yayi, ita dai bata san Meyasa bata iya controlling heartbreat ɗinta ba in dai akan magananshi ko kallonshi ne ta ajiye akan tsananin tsoron shi da take ji ne ya janyo hakan, Dukda bai taɓa dukan ta ba amma ya sha yi mata faɗa, faɗan ma babu kaman na ranar da ta fara ɗora idanunta a kanshi a rayuwarta.Kaman waenda kwai ya fashe musu suka dawo, Abeeha da ta san halinshi ba lallai ma ya kara magana ba ta ja kujera ta nunawa Afeefah kujeran da idanu, kaman ba zata zauna ba sai kuma ta zauna Abeehar ma ta ja wani ta zauna ta ɗauki plate a hankali ta yi serving ɗinsu Rice ɗin daban daban Allah ma ya sa shinkafar da tsokar nama suka yi da babu protein za su ci don shi zallar kifi da irish ɗin yake ci.Abeeha ta fara ci a hankali kan ta buɗe baki tace”Sannu da dawowa Yaya”Kai ya ɗan gyaɗa har lokacin bai ɗago ba, ita dai Afeefah ko spoon ɗin bata ɗauka ba gashi tana tsoron magana, kuma kar bata yi ba ya zama laifi da kyar ta ce a rarrabe “S..sannu da d..dawowa”Yadda tayi maganan ya sa ya ɗago slowly ya kalleta kan ya mayar da kanshi yana kai fork na karshe baki bayan ya haɗiye ya ɗauki ruwa daga fari kal ɗin glass cup dake gefenshi ya sha kan ya miƙe ya bar wurin, a tare suka sauke ajiyar zuciya Afeefah tace “Adda Abee Meyasa da ya dawo da mu kika sa muka zauna?”Tayi murmushi tana cin shinkafar tace “Har yanzu baki san Yaya Rayyan ba, ai ya tsani saboda shi ka ƙi yin abinda ke gaban ka yanzu da za mu tafi bayan ya kiramu ya kuma san me za mu yi anan muddin muka tafi haka zai titseyemu ya tsare gida ya ce sai mun faɗa mishi dodo ne shi da muke avoiding ɗinshi…””Shi dai komai kayi baka burgeshi?””Aikam bana tunanin akwai abinda yake burgeshi muddin ba abinda ya shafi Mammi bane”Ajiye hirar shi suka fi suka cigaba da cin abinci don hanyar lafiya a bita da shekara dazu sun tsira gaba basu san me zai faru ba.Bayan sun gama wurin Mammi suka yi suka samu ma tana waya ne da wata cousin ɗinta akan boxes da ake haɗa mata na auren, ita dai Afeefah a kunyace ta zauna don yanzu sai take jin kunyar Mammin na rufeta, bayan Mammin ta gama waya ta dube ta “Afeefah yaushe ne kuke gama exams ne? Bana so kina yawo cikin rana ana wannan gyaran jikin””Mammi wednesday za mu ƙare”Ta mayar mata da amsa.”Da sauƙi, saturday ne ɗaurin auren Abeeha ya zancen telan?”Sai da gaban Afeefah ya faɗi ita ta kasa sabo da zancen auren sam, ji take kaman ana daddaureta ne in aka yi maganar sai ta ga kaman ba gaske ba ita ce zata yi aure, auren ma Rayyan za ta aura? Ya subhallah wani chill take ji yana running over her spine.”Mammi kin san telan Jannah ne zan ƙirata na ji ko ya gama haɗawa ko ni sai in je in karɓo”Hira suka cigaba da yi akan bikin da za’a yi shi ne a yini guda, ɗaurin aure, yini, walima da miƙa amarya ɗaki in ji mutanen garinmu suka ce Jollof, ba ana yinshi bane saboda talauci ko wani abin, ana yin hakan ne saboda sauƙaka zirga-zirga expecially a irin situation na Mammi da bata bukatar stress ko kadan.Ranar Juma’a ana yi mata lalle sai ga su Fa’iza da fauziyya har da Ummusalma matar Sulaiman da ta sake da ita sossai a yanzu, ga Abeeha da Jannah sai suka zama kaman bridemaids suka cike ɗakin da hirarraki ana yi ana dariya, Mammi kuwa sai sawa take ana turo musu abubuwan taɓawa sossai hakan yayiwa Afeefah daaɗi sai take jin nishadi a ranta na taruwansu ko ba komai Allah ya haɗa ta da tarin mutanen kirki, wani irin kyau lallen nata yayi baƙi da ja ya karɓi hannu da kafafunta duk suma ‘yan matan sun yi. Mammi ma tayi ja a yatsun hannu.Sai dare suka tafi har Jannah akan sai gobe da sassafe za su dawo.Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, yau aka wayi garin Asabar kuma a yau ne ake shirin ƙulla wani babban al’amari mai tarin nauyi tsakanin Afeefah da Rayyan, da misalin karfe takwas ya shigo ɗakin Mammin don ta kalli kayan da ita ta bashi ya saka a ranar don rana ce ta musamman a gareta da ma shi baki ɗaya.Ɗan uban sun Men lace ne fari kal mai shegen tsada ƴar ciki da babban riga ya wani zauna mishi sak kaman don shi aka halicci yadin, hula da takalminshi bakake ne haka agogo tsadadde dake ɗaure tsintsiyar hannunshi zuwa azurfa mai baƙin dutse da ke ƴar yatsar shi, fasalta irin fita a angon da yayi ma ɓata lokaci ne sai kamshi kam kaman an yi barin turare, fuskar Mammi ya zubawa ido kawai don bai taɓa ganinta cikin nishadin da ya ganta a ranar ba sai ya ji wani abu mai sanyi na sauƙa cikin zuciyarshi, matsowa tayi ta kama hannunshi tana murmushi tace “Za ka tafi a saurayi ka dawo matsayin magidanci Saraki, ba zan ce komai ba illah Allah ubangiji ya tsare muku hanya daga zuwanku har dawowanku”Yayi murmushi ya juya zai fita tace”Saraki…!”Ya waigo ta ɗauko turarenta ta sake fesa mishi ya fita ranshi fess Dukda wani abu da yake ta ji na tsungulinshi akan auren.Ga dumbin mamakin shi yana fita ya tarar da motoci sun fi sha biyar dauke da tarin ma’aikatan asibiti da ma ‘yan uwanshi sojoji, a hankali ya juya ya kalli Sulaiman da ke mishi murmushi sai yaji wani abu na mishi yawo a jiki, bai taba zaton za’a mishi irin wannan karan ba duba da gaisuwa ce kawai ke hada shi da kowa, wani iri yake ji a sadda ya shiga gaban motan Sulaiman suka fara barin unguwar babu saleem, ya nemi saleem a waya har ya gaji baya samunshi ko da ya dawo gidan ya je mai gadi ya tambaya ya tabbatar mishi sun yi tafiya da madam, ya tambayi su mommy yace basa nan suma. Ko jiya sai da ya koma amma bai same shi ba akan basu dawo ba bai ji daaɗi ba sam da hakan ta kasance.Bai gama shan mamaki ba sai da ya kalli tarin dangin Mammi, iyalai da jikokin uncle ɗinta motoci kusan nawa har da abokanan arziki don a matsayin auren jikan Uncle ɗin za’a yi, kan su tafi Mammi ta roƙi uncle Musa akan duk runtsi a dawo da sadakin Afeefah wanda Saraki zai bayar in ya so ko wani abu ne a bashi daban amma sadaki na Afeefah ne.Mutanen Dutsen-wai suna zaune kawai suka fara ganin lafiyayyu kuma tsararrun motoci suna shigowa one after the other, babban masallacin garin da bashi da wani girma sai haraba suka yi wa tsinke tuni dama Uncle Mansur ya aiko da masu canopies an kafa dayawa a harabar don masallacin ba zai ɗauki mutanen ba, an shimfida carpets-carpets anan suka yi masauki, Kawu an nemo na ƙasan akwati don maƙon shi ma bai barshi yayi sabon ɗinki cikin dubu hamsin din chan ba bai tashi jin kunya ba sai da ya ga mutanen alfarmar da suka taru a wurin, kowa mamaki yake yara sai leke suke wasu matan ma na maƙale saman katangu ana kallon ikon Allah, kowa Allah Allah yake a ce wannan shine mijin Afeefah Annoba su kare mishi kallo…Fara haramar ɗaurin aure ake, a hankali Rayyan ya kalli Sulaiman “Nawa ake bayarwa?”Sulaiman ya ɗan juya hannu alamar mene kenan?”Sadakin?””Duk abinda kake dashi hawa hawa ne amma last da na duba a masallaci ƙarancin sadaki yana dubu ɗari da tamanin da uku ne”A lokacin aka fara ambatan sunayensu a hankali ya karkata ya zaro bandir ɗin dubu-dubu guda biyar ya miƙawa Uncle Sanusi aka miƙawa liman an ɗaura auren Afeefah Kamal da Rayyan Moh’d Khamis akan sadaki naira Dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba, wani irin yanayi ne yake ratsa shi da ya kasa fahimta, idanunshi da suka sauya ya runtse yana ji ana ta rabon goro da dabino da sweets. Sai hannu ake bashi ana mishi murna da kyar yake iya kawo murmushi fuskarshi don yanayin da yake ji baya misaltuwa mishi, kawu sai kallonshi yake baki galala yana ayyana lallai wannan zai iya zama maye tunda gashinan irin mazan da yake kallone idan yara suna kallon India, a fina-finan ma wannan ko ya aka yi kuɗinshi daban ne, limami ne yake rike da kuɗin sadakin kawu yaje ya fara kokarin karɓa sai uncle Musa yayi interrupting ɗinsu “Kun dai san sadaki hakkin mallakar matar ce ko?”Limamin ya gyaɗa kai “Toh zan tafi da wannan tunda ita yarinyar na gabana zan bata”Yana kai nan ya nuna Mansur shi kuwa ya karɓi kudin gabaɗaya wani irin kullutun bakin ciki ne ya tasowa kawun har wuya, uncle Musa ya murmusa ya fiddo dubu hamsin ya ba kawun Dukda haka bai huce ba sai kumburi yake, anan aka yi reception ‘yan kauyen sun ga abinci da kaji iya gani, yana ta mamakin ya aka yi Mammi ta shirya waennan abubuwan with her condition, duk kauyen babu gidan da ba’a ci shinkafa da kajin auren Afeefah ba don enough aka yi shi.Karfe goma sha ɗaya suka fara barin garin, kawu ya tafi zai shiga mota Uncle Musa ya janyo shi “Malam Labaran na ga kana kokarin shiga mota?””Eh wai dama in je ne in kalli inda ‘yar tawa za ta zauna””Ah ai ba’a yi haka ba, ba yanzu ba zaka bari sai ta kwana biyu da kaina zan zo in kai ka yanzu ka ga mutanen da ka tara dole ka tsaya ka ga sun tafi cikin salama”Yana maganan ne yana tuna zancen Mammi da tace duk rintsi kar su dawo da kowa, tana so ta dasa musu wani bakin ciki ne a rai gashi dai wacce suka kora sun haɗa ta da ƙaddarar ta rabonta shine ya kawo ta har cikin Kaduna, sannan gashi sun gani kuma sun shaida a yanzu ta shallake wa tunanin su kuma babu yadda za su yi babu abin da suka iya. Kwalelen biri da hantar kura.Shi dai bai gamsu ba amma haka uncle Mansur yayi ta mishi zaƙin baki har motocin suka watse illa Sulaiman da Rayyan wanda yake jingine jikin mota ya harde hannayenshi a kirji yana mamakin ikon Allah wai yau shi ne da aure. Ko sha’awar kallon kawun baya yi don ko da kawun ya zo yana washe mishi baki tattare girarshi yayi ya haɗe fuskarshi ta koma ainihin shi mai tarin kwarjini dole kawun ya kyale shi.Su ne karshen barin garin sai masu canopies, sai cece kuce ake to Annobar ya saki Afeefah ne ko an mata maganin mayun ne? Kap kauyen babu yarinyar da aka ɗaura mata aure kwatankwacin na Afeefah, sadakinta kaɗai yayi sadakin mata ashirin a kauyen kaf… Inna Larai na zaune da suntumemen kafa da kullum kara hauhawa yake tana jin komai tana hawayen bakin ciki, inna Asabe ma sai uhmm uhmm take tayi abin duniya ya taru ya masu yawa barin ma da aka aiko kulolin abinci wai na gidan kawun, ko da Afeefah ke mata abincin sayarwa wannan yayi jarinsu sau goma don daga ganin shinkafar ka san ba na yara bane ga kaji baja baja.Suna gani Afeefah ta haye? Garin yaya duk basu sani ba. Ni kam na ce Allah take dashi.Ko da suka iso Kaduna shi kadai ya nufi babban parlorn akwai mutane ciki sossai don yan uwa Mammi duk suna nan ga su Umma duk sun zo yara ana ta ciye ciye ana wasa, kai tsaye karamin parlorn Mammi ya leƙa sai ya ga wata cousin ɗinta tace mishi “Tana sashen ka Rayyan”Bai amsa ba don duk ana ta ango ango kanshi kasa da kyar yake dan murmusawa don kanshi sara mishi yake.A parlorn shi kuwa ya samu Mammin da wasu, tsayuwa yayi kawai yana kallonta ta ci wanka cikin leshi blue doguwar riga ta ɗora gyalen da ya shiga da leshin a kanta da aka yi wa dauri mai kyau, daga wuyanta kunnenta zuwa hannayenta da yan yatsunta gwalagwalai ne da suka kawata adonta ta mishi kyau ainun har bai san ya fadada murmushin shi ba ya shigo ciki. Ta tako a hankali ta kama hannunshi sai hawaye suka shiga zubo mata “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana, Allah na gode kwarai da ka ba ni lafiyar kasancewa da ɗana a rana mafi muhimmanci cikin rayuwarshi, Allah ka dube su ka basu zaman lafiya Allah ka sanya musu tausayi, jin kai, bege da kaunar junansu ka bashi ikon bata kariya da sauƙe duk wani hakki nashi na aure… Rayyan…”Sai ta kasa magana sai hawaye, kaman zai yi kukan shima yana jin adu’o’in nata har a cikin zuciyarshi ya sa hannu yana dauke mata hawaye, jan shi tayi suka zauna ta zaro wayanta ta kira Abeeha”Ku zo da ita”Daga haka ta kashe.A gefen Mammin ya zauna yana gyara mata gyalenta nan masu hoto suka shiga aikinsu, sossai suke yin kyau don shine yake ba ta kulawa bayan ya gama gyara mata gyalen ya sake share mata fuska kan ya kalleta yana murmushi duk ana ɗaukar su, suka kalli cameran suka murmusa a tare ba karamin kyau suka yi ba, zai yi magana suka yi sallama suka shigo ganin murmushin Mammi yayi yawa ya sa ya kai idanunshi inda take kallo.Afeefah ce ke tahowa a hankali kaman wacce ke tafiya a kan ƙaya, tayi masifar kyau cikin wani exlusive luxery lace da aka yi wa ɗinki na amare, ko ina na jikinta a rufe ne ruf banda hannu da fuskarta makeup da aka mata ya matuƙar amsarta ko don shine karo na farko a rayuwarta ne bata sani ba, amma kam tayi kyau Tabarakallah.Mammi ta miƙe ta tarbota “Masha Allah, Tabarakallah ɗiyata you made a beautiful bride”Shi kam kallon seconds biyu yayi mata ya janye idanun har suka zo suka zauna Mammi tana tsakiya Afeefah na gefenta na hagu yana zaune a gefenta na dama, idanunshi ya ɗan tsayar akan yatsun Afeefar da suka yi kyau ainun har yanzu mamaki yake, Mammi ce ta kama hannun shi ta kamo na Afeefah ta haɗe a tare suka ɗago sai zuruf idanunsu suka faɗa cikin na juna, idanunta da suka sake haske suka yi mai saboda kwallin da aka saka mata ya tsayar da kwayar nashi a kai, ba zata iya jurar kallon ba sai ta duƙar da kanta daidai Mammi ta ɗora nata hannun a kan nasu camera man yayi musu magana suka kalleshi aka shiga ɗaukar hotuna. Ko da za’a musu su biyu Mammi bata tafi ba don ta san in ta bar wurin shima sai ya bari, ta miƙe ta mishi umarnin komawa mazauninta ya koma ɗin amma har lokacin da space tsakanin shi da Afeefah mai hoton ya kalleta yace “Amarya ki ɗan matsa kadan sai ki sa kan ki akan kafadarshi”Irin bugawar da zuciyarta ke yi tunani take kila saura kiris ya fashe ta mutu, kamshinshi presence dinshi a kusa kusa da ita haka sai ya nemi ruda ta, yana so ya tashi don ya gaji hakan ya sa ya ɗan matsa kaɗan Jannah da duk tsoronta ta zo ta kama hannun su ta haɗe sai suka kalli juna don duk sadda jikinsu ya haɗu su suka san abinda suke ji, kallon ya ba da wani ma’ana na daban nan aka shiga daukar hotuna. Sossai yake a takure na tsaye aka ce shine last Mammi dai bata yi magana ba amma idanunta ne ya hana shi barin wurin wallahi.Bayanta ya koma, ya matso sossai har tana jin kirjinshi na taɓa bayan nata babu zato ta ji hannunayenshi duk biyu ya zagaye cikinta, a ɗan razane ta ɗora nata biyu a kan nashi “Kin natsu ko sai na karyaki biyu? Baki san mutum ya gaji bane??”Da ɗan faɗa yayi maganan a kausashe amma wanda suke tare za su dauka wani abin arzikin yake rada mata aka daddauka ya zame ya bar wurin su ma suka fice.An yi yini an ci an sha an yi hidima har la’asar kan aka sake wanka aka fito harabar gidan walima, amarya na sanye da wani tsadaddiyar Abaya da yanayinshi kaɗai ya bayyana tsadar shi canopies da kujeru aka shirya sossai aka yi walima aka ci aka sha kan mutane suka fara watsewa don bayan isha aunties ɗin su Jannah za su kaita part dinshi dake cikin gidan, Mammi bata mishi maganan wani gida ba saboda ta sani ne ba zai taɓa tafiya ya kyaleta a gidan ba, kuma parts dake gidan kenan don a tsare aka yi ginin Allah ma ya sa dakuna biyu ne a nashi part ɗin da kitchen da store sai parlor da dining section kaman flat ne mai zaman kanshi.Aiko kan bayan isha mutane kadan ne a gidan masu aiki sai aikin tattare gidan suke, Afeefah tayi sallah aka shirya ta again cikin atampha aka ɗora mata lafaya aka miƙa ta wurin Mammi, sossai ta yi mata nasiha tana hawaye itama kuka take don bata da bakin godiya ga Mammi, ta yi mata abubuwan da godiya sun yi kadan ta cika mata burinta na ganin ta auru, ta rungumeta ta zame mata uwa da uba ta bata duk wani gata da take tunanin ta rasa to da me zata saka mata in ba da zama lafiya da kuma zuciya ɗaya jal da ɗan ta mafi soyuwa a gareta ba? Sossai take kuka tana tuna mamanta da Aunty zee ina ma Aunty zee na nan ta ga wai Afeefah ce a ɗakin miji? A haka aka kaita ɗakinta da Adu’a a Bakinta.Mammi waya ta ɗaga ta kira shi, ba’a yi mintuna biyu ba ya shigo sanye da kananun kaya ash har da hoodie don zazzabi yake ji tsabar hayaniyar da yake ji ya mishi yawa ya saukar mishi da ciwon kai sossai.”RAYYAN….”

Back to top button