Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 21 Book 2 Complete Novel

 

A razane Ilham ta cewa Jalila

” Ubanwa ya gayamiki wani abu na zuba a ciki, ke bayan munafunci hada sharri a lamarin naki, ai na dade da gano sonshi kikeyi, kalleki a haka kaman ta Allah amma tsabar rashin tsoron Allah da idona na ganki kina rungume Jalal, se anyi magana kice aike basanshi kike ba, in ba sonshi kike ba uban me ya kaiki jikinsa, meye naki nasamun ido iyee, munafuka kawai” Jalila tai murmushi tace “inkika daga murya kanki zaki tonawa Asiri baniba, danni ba ruwana, sannan dan na rungume Jalal, damace nasamu kema kije ya rungumeki mana inkincika mace” Jalila takarasa maganar tana dariya, tacigaba da cewa 

“Ilham tsabar mugun abunkine yasa kullum idonki yake ganemiki abunda ze hanaki sukuni tsakanina da dan uwanki, amma ko makamancin so na wancan abun babu araina fatan kin gane, for now Jalal beci wannan tsafin ba sekije kiyi wani shirin kuma” tana gama fadin haka bata jira me Ilham zatace ba ta juya zata fita, Ilham tasa hannu ta janyota, ta waigo sukayi ido hudu, Ilham kaman ta fashe da kuka tace “wannan karon kinyi Nasara, amma ki saurari abunda ze biyo baya nan gaba” 

“Idan har Allah shine abun dogaron mutum to a koda yaushe nasara tasace, dan haka inaji ranki, sannan kisani bani kadai yakamata kigabaya ba, Hanna ma tana nan tana target akanki, sekin kara tunani kin rarraba hankalinki, dan hanna bazata barki ba,” Jalila ta fizge hannunta tai gaba abunta.  Ilham taji wasu hawaye na bacin rai suna bin idonta Allah yahadata da Jaraba, mezatayiwa Jalila ta huce ne? Gani take da za’abata wuka seta kasheta, ita hannah ba barazanace a gurinta ba Jalila tafi tsayamata a rai, da Jalal yaci abun nan da yanzu anmawo karshen komai, amma Jalila ta wargaza komai, ajiyar zuciya Ilham tayi “dole in sanar da umma abunda ke faruwa, na dauka zan iya shawo kan lamarin nan amma abun yafi karfina” 

Jalila kam takuma silalewa ta fice ba tareda kowa ya ganta ba ta tafi gida. Koda Jalila takoma gida, sabgoginta ta shigayi, amma takan tuna nasihar da Jalal yaimata dazu, babban abunda yabata mamaki yace jikinsa yana bashi ummi tana raye fatanta Allah yasa hakane ummi tana raye, har akayi sallar isha’i sannan Nana ta dawo gida, da fara’arta ta tafi gurin Jalila ta zauna, Jalila ta kalleta “se yanzu kika dawoko? Dan kinga Abba bayanan” “Aiko yana nan baze hananiba, Allah sarki Yaya Jalal se murna yake yaga yan uwansa” 

“Hmm Nana ai dan uwa dadi ne dashi, sedai abun tausayin naga yan uwannasa duk nutsatsu amma banda shi” 

“ya akayi kika gansu bayan kina gida?” “naje naga palourn a cike bazan iya wucewa ba dan haka na dawo” Nana ta dan girgigiza kai “bari kawai Jalila, Jalal abun tausayi ne, Allah ya kyauta kawai” daga nan Nana bata kuma cewa komai ba ta tashi, ta bar dakin

Jalila ta dauki wayarta ta hau internet, batun abunda yafaru da Alhaji Kabiru ya zaga duniya, hada masu kara abunda ba’ayiba, yan makarantarsu Jalila kuwa se murna suke da kama su Sameera da akayi suke, dama dayawa suna jin haushin su Saleema, sabida yadda suka gallabi makarantar, ga bata yaran mutane dasuke, se zancen ake tareda Allah wadaran da suu saleema ace ankamaka kaida mahifinka a gidan karuwai,

Jalila tace dole taje station din da aka kai su Alhaji Kabiru, kuma yanzu amfanin Yallabai Sulaiman yazo. Don kuwa setayi me yuwuwa ta tabattar da ta kawo karshen Jeje da Alhaji Kabiru, taji dadi da Allah yasa aka kama da jeje a wannan kamen, Dagashi har Alhaji Kabiru sesunyi danasanin shiga gonarta, Tagama abunda takeyi tana shirin kwanciya, sa’ada tace “ya haja? Ba dakin halima zakije ki kwana ba ai dakin zaki barmana malama, mu a ina zamu kwanta” shiru Jalila taimata tana kokarin jan bargo, Naja tasa hannu ta rike bargon “malama maganafa ake miki, ki tashi ki bamu guri kitafi dakin yan aiki ku kwana a can dan bazamu kwana dake a daki daya ba” mikewa Jalila tayi a zaune, ta kalli su Naja “da Abba yake gina gidan nan gudunmuwar nawa ubanku ya bayar” bude baki sa’ada tayi “ke karki sake ki zagarmana uba wallahi, dan kika zagi ubanmu semunyi kasa2 dake” 

Download>>> Babban Yaya Complete Document

“inna zage shi mekuka isa kuyi, aiba karya nayiba, in ya kawo gudunmuwa lokacin da ake gina gidan nan ku fadi nawane a biyaku, kudena min gori, inkuma bebada ko sisi ba, kar shashar data kara cewa inje in kwana a dakin me aiki, tunda ba da gudunmuwar tsoho a gina gidan alfarma akemuku, koni nawa iyayen ba mutane bane da kuke zaginsu ? Inkun ji haushi a daren nan kukoma gidan naku iyayen, kuma wallahi duk wadda takuma yimin maganar banza sena gayamata maganar dabazata iya bacci ba” ta juya ta kwanta akan pillow tana murmushi. Haka suka hakura suka tafi dakin Maama suka kwana a can, dan Jalila ba karamin taurin kai gareta ba. 

Hannah duk ta rame sabida dorawa kanta masifar son Jalal dakuma kishinsa, tayiwa kanta alkawarin muddin bata aureshiba sedai ayi biyu babu, dan in har tana raye bazata bari ya auri wata mace ya zauna da ita ba, kodai ya aureta cikin dadin rai, kokuma ya aureta kota tsiya, yanzu yazma dole ta hada kai da jeje, ta yaudareshi su hada kai taga bayan Ilham, Ita Jalila nata me saukine, Ilham ce tafi tsayamata a rai, ta dakko wayarta taita kiran lambar Jeje, amma taki shiga, tayi2 harta gaji ta hakura, da niyyar gobe taje ta sameshi, (bata san ankama shi ba) 

Da sassafe wayar Jalila tafara ringing, cikin magagin bacci ta kai hannu ta daga wayar, muryar Jawwad taji “Am sorry baby na tasheki ko?” ya fada a hankali 

“bakomai Yayana, fatan ka tashi lafiya” 

“Lafiya kalau, hope kinyi bacci me dadi?” 

“Alhamdilillah yayana” “yawwa baby wata alfarma nake nema a gurinki” 

“fadi kanka tsaye komenene indai zan iya dole ayi shi” 

“Yawwa baby, kinga a gidansu Jalal na kwana muna tareda su mahmud, gari ya waye babu alamar Mummy zata basu breakfast, na shiga cikin gidan yanzun naga ta kulle kitchen dinta, daddy kuma ya fita kiran gaggawa da akayi masa da asuba ya tafi Abuja, to banason Jalal yasani, dan Allah ki dafa abunda yasamu abawa bakin nan” mamakine ya cika Jalila to meyasa Mummy zatayi haka, meye ma’anar hakan datayi, ajiyar zuciya Jalila tayi 

“bakomai karka damu, zan hada abunda ya sawwaka inkawo” 

“Yawwa Baby, Allah yayi miki Albarka” 

“Ameen bloody” gajiyar jiya bata saki Jalila ba. ta tashi ta tafi kitchen ta dora girki, ba a dade ba Nana ta fito taji karar kwanuka a kitchen ta leka setaga Jalila nata fama a kitchen “Jalila kekam meyasa ba kyason hutawa rankine, da sassafen nan kowa na bacci kekina kokawa da kwanuka, gashi gajiyar jiyama bata sakeki ba” 

Jalila ta gayamata duk abunda yafaru, Jinjina kai Nana tayi tace “Tabdijan itakam har yanzu Mummy abu baya wucewa a gurinta, to Allah ya kyauta” 

Da mamaki Jalila tace “meye baya wucewa a gurinta? ” Nana tace

“manta kawai, bari inzo in tayaki, bekamata kiyi aikin keka dai ba” Nana ta tayata suka karasa aikin, duk yadda Jalila taso Nana tagayamata wani abu, amma Nana taki ta basar da zancen. Maama tafito kitchen zata dauki plate,  Jalila tace “Maama ina kwana” “lafiya” shine amsar data bawa Jalila, ta kallesu “wai wane irin girkine da har yanzu ba’a gama breakfast ba” 

Nana tace “Yaya Jawwad ne yasamu aiki, mummy tahana bakinsu Abincin safe” dan zare ido Maama tayi

“Are you serious, ita har yanzu bata dena wannan abunba? Itama dai Mummy by now yakamata ace komai ya wuce, kodan danta, amma Ai shikenan” 

Se Karfe tara na safe Suka gama aikin Abincin, suka dauka suka kai gidansu Jalal, a palour suka tarar da wata mata me fara’a, tana kama da daddyn Jalal sosai, zatayi shekara talatin da biyu,  Jalila bata santa ba amma dagani tasan yar uwar daddy ce, Nana ta santa, suka gaisheta, ta amsa musu cikin fara’a, suka tsaya suna hira da Nana,  Jalila bata da saurin sabo, gashi bakomai take ganewa a hausar matar ba, dan haka Jalila ta mike takoma gida ta dakko sauran kayan, tana dawowa tundaga harabar gidan tafara jiyo hargowar Jalal kaman a filin yaki, a ranta tace “jarababbe Allah yayi dare gari ya waye a gaban mutanen ma baze dena wannan jarabar ba” tana shiga palourn ta ganshi a tsaye a gaban Mummy idonsa jawur yana surfa masifa, wata mekama da wadda suka tarar a palour dazu tana rikeshi tana masa magana da yarensu, cikin fushi yake kallon Mummya yana cewa

Download>>> Yar Harka Complete Document

“Wace irin macece ke mara Adalci, ai Abincin banakibane ba dazaki hana ‘yan uwan babana ci, kodaga gidanku aka kawoshi, amma kinsan ki diba har kibawa wanda basu kamata ba, akanme dan uwansu ne yake nema yakawo zaki hanasu Abinci, ke wace irin mara adalcicene meyasa kika fiye sonkanki, su basuyi fushi dakeba seke zakiyi dasu, why? Mummy why? Wace irin zuciya ce dake haka”

Mummy tace “Jalal nikake ciwa mutunci agaban mutane, kake zagina a gaban mutanen daba kaunata suke ba, nikake gayawa wannan miyagun maganganun, uwarkace nifa nikake ciwa mutunci haka” takarasa maganar tana hawaye, jiyo hargowane yasa Ilham ta fito da sauri daga dakinta, don ganin meyake faruwa, ta tarar Jalal yanata baka’i

“Eh nayi din, dan sunfiye minke a matsayin uwata, haifata kawai kikayi amma sam bakisauke hakkinki na uwaba meyasa kikazamo uwa a gareni, a rayuwata sam banyi dacen uwaba, kowani da yana farinciki yana murna in aka ambaci uwassa amma bandani Jalal, baruwanki da ya rayuwata zata kkasance se cikar miyagun burikanki sukikasa a gaba, har yau kinkasa yin nadama akan rayuwar da nakeyi saboda rashin kulawa irin taki, dakuma laifukan dakika aikata a rayuwarki, wallahi mahaifina da danginsa sun fiyemin ke wallahi” cike da masifa da bacin rai Jalila tafara magana

“ABDUL JALAL Kaji kunya wallahi, agaban mutane kake gayawa mamanka wannan maganar, ba ladabi babu da’a ba komai, kome tayi maka tunda tariga takawoka duniya tagama yimaka komai, kalli ‘yan uwanka dasukazo kowa a nutse tunda ga fuskarsu shigarsu da kamalarsu amma banda kai, ta yaya kake tunanin zaka cigaba a rayuwa da wannan wulakancin da kakewa mahaifiyarka,kana tozartata kana nunawa duniya kai baka da tarbiyya, tirr da hali irin naka Jalal, Allah ya shiryeka inme shiryuwa ne, ba yadda za’ayi kaga haske ko cigaba a rayuwarka alhalin kana tozarta mahifiyarka, tir da halinka wallahi”

A mugun fusace ya juyo, ya kalleta ido cikin ido, kan Jalila yayo gadan2, itakuma taki motsawa balle ta gudu, kafin ya karaso gurinta, matar dazu dasuka tarar a palour tashiga tsakaninsa da Jalila, tana girgizamasa kai “Allah ya huci zuciyarka, kayi hakuri, ka kyaleta” 

Yare ya canza yana magana,ya cigaba da tunkaro su idonsa jawur cike da masifa, tareda kwalla, ya nuna Jalila yanawa matar magana da yarensu, a cikin maganar da Jalal yake taji ya ambaci sunanta, JALILA!!! 

Abunda tunda take bata tabajiba, sedai yace mata ke, koyace wannan yarinyar kokuma yacewa Jawwad kanwarka, 

Matar tacigaba da bashi hakuri da yarensu, ta kalli dayan tace “mahmud jashi kufita, kabashi hakuri” Mummy tuni tabar palourn yayinda Ilham agabanta akayi komai, Nana ma rasa bakin magana tayi, 

Matar nan taja hannun Jalila suka fita daga palourn, bayan gidan taja Jalila ta zaunar da ita akan wasu fararen kujeru, sannan itama ta zauna ta kalli Jalila tace 

“Dama kece Jalila?” Cike da mamaki Jalila ta kalleta “Eh nice, ya akayi kika sanni?” Ajiyar zuciya matar tayi tareda murmushi, “kece baki sammu ba, amma mu duk munsanki ai” 

“Amma naga bamu taba haduwa ba, ya akayi kuka sanni” 

“ba abun mamaki baneba Takwararmu, duk family dinmu munsanki, amma meyasa kikewa Jalal hakane?” da mamaki Jalila ta kalleta

“me nayi masa kuma?” 

“duk lokacin dakika bata masa rai seya gayamun, kina yawan sakashi fushi meyasa?” dan dauke kanta Jalila tayi tace

“Anty Jalal baya kyautawa abunda yakeyi, kullum yana jefa rayuwarsa a cikin hatsari, ace mutum yakai munzali kaman Jalal amma ace kullum cikin sa’insa yake da mahifiyarsa bekamata ace yana daga mata murya haka ba? Banda sauran abubuwa dayake dabasu dace ba, kema kinsani, amma meyasa bakwa zuwa inda yake maybe dakuna zuwa da ganinku zesa yarage wasu abubuwan da yakeyi, rayuwarsa ta gurbace dayawa, baya ganin girman kowa, shaye2 shine babban abokin rayuwar Jalal, be damu da ibada ba sam, ko abokan kirki bashida su sena banza, yayi shaye2 a club yayi a gida, kuma ko a gaban waye, baya ubangiji, da sauran abubuwa marasa dadi dayake aikatawa”

Ajiyar zuciya matar tayi

Download>>> Maraicin Nawaff Complete Document

“Jalila tabbas maganarki gaskiyane, Jalal baya kyautawa duk rayuwarsa ta gurbace, amma meyasa kika damu akansa haka?” Jalila tace

“nima bansaniba, kawai dai soyayyar da Jawwad yakemasa ne, dakuma kokarin dayake dan ganin Jalal ya shiryu yasa banajin dadin abunda Jakal yakeyi”? 

“kin taba tunanin meyasa babu soyayya da tausayi na da da uwa a tsakanin Jalal da mahifiyarsa?” 

“eh nayi wannan tunanin, amma nakasa samun amsa, nayi2 Jawwad yagaymin amma yaki” 

“meyasa baki tambayi Jalal dinba?” zare ido Jalila tayi “taya zan tambayeshi nida muke fada, ya shakeni a banza” murmushi tayi “baze shakeki ba Jalila” Jalila ta kalleta

“tab lallai wallahi ze iya shakeni, har dukana yakeyi” matar tayi murmushi “Jawwad yacika dan uwa nagari, daya boye sirrin Jalal, dukda a yau zamu bar kano, zamu koma garinmu, tunda matar gidan bata son zuwanmu, amma yanzu a takaice zan baki labarin waye Jalal, sannan ya ingaya miki ya akayi muka sanki, idan nabaki labarin sekiyi masa alkalanci” 

Khadija munir shine cikakken sunan mahaifiyar Jalal, malam munir shine mahaifinta suna zaune a unguwar dorayi dake cikin garin kano, malam munir malamin makarantar secondary ne, sannan yana yan sana’oinsa domin rufawa Iyalansa asiri, yanada mata uku, hauwa itace uwargida, se sadiya itace matarsa ta biyu, da zulaihat itace matarsa ta uku, yanada yara goma sha uku, khadija ‘yace ga sadiya matar malam munir ta biyu, khadija su ukune agurin mahaifiyarsu, itada yayyenta maza biyu, Abubakar da Aliyu, itace yarinya ta tara a gurin mahaifinsu, khadija tana da kyau daidai gwargwado, wanda har wasu suke cewa duk tafi yaran gidan kyau, dukda kasancewar ta ba fara tas ba amma tanada kyau, khadija yarinyace mara kunya, bata dagawa kowa kafa, duk wanda yayi mata duk yarintarsa duk tsufansa zeta cimasa zarafi babu ruwanta, tun yayyenta na kamata su daka intayi rashin kunya harsuka gaji suka kyaleta, saboda rashin mutuncin ta bata bar kowaba ciki harda matan babanta da yayyenta, mahaifiyarta ta sangarta ta kasancewarta ita kadaice yarinyarta mace, duk wanda ya daki khadija ranar se anyi tashin hankali da mahaifiyarta, har kirari takewa khadija cewa “ni ‘yata matar manyace, se wanda yaci yatada kai zan bawa, dan khadija na ba kalar talakawa bace” hakan yasa abun yafara tasiri a zuciyar khadija tun tana yarinya, takejin cewa kota isa aure seta samu me kudi zatayi aure idan kuwa bata samu me kudiba, gara ta tsunduma ita tanemi kudin dan bazata iya auren talaka ba, kuma batason rayuwar wahala. 

indai khadija nason abu, kaya kona uban waye koda kudi ko a bashi, mahaifiyar khadija zata siyamata su. 

Saudat kanwace ga khadija sakuwarta ce khadija tabata shekara daya da rabi, ita saudat ‘yace ga zulaihat amaryar malam munir, itace ta biyu a dakinsu, wani lokacin suna matukar shiri ita da khadija saboda halinsu yazo daya dukkaninsu tsagerune, Sedai Khadija tadama saudat ta shanye a tsageranci, dukda wannan shiri dasukeyi baya hana in tsiyar khadija ta motsa tayiwa babar saudat rashin mutunci a hadu aita masifa a gidan nan, makaranta da yan unguwa babu wanda besan halinta ba, karamin aikintane ta zagi malami agaban dalibai, in an koreta mamanta seta canza mata makaranta, dama islamiyya tuni ta dena zuwa, a cewarta tunda tasamu na salla shikenan, dan bazata jure wannan masu gemun kaman brush suna dukan kyakyawar fatarta da fatar bunsuru ba, abun dukan doki, malam munir yayi iyayinsa gurin ganin khadija ta nutsu amma abu yaki yuwuwa, 

Abinci se wanda taga dama zataci, sutura se wadda takeso zata saka, wani wanki da guga almajiri uwatta take biya yayiwa khadija, haka dai rayuwar khadija ta tashi a mugun sangarce, ga rashin tarbiyya. 

Tun tana jss2 tafara samari, inda a nan ne ta hadu da saurayinta Kabir, Kabir yana matukar sonta kaman yayi hauka, Kabir marayane, mahaifinsa ya rasu, dagashi se mamansa da kannensa mata biyu, shikadaine namiji gashi mahaifinsa bebarmusu wani abun kirkiba se gidan dasuke ciki, seyaje yayi aikin wahala yake samo abunda zasuci yake biyan kudin makarantarsu, tunda yafara soyayya da khadija abubuwa suka fara tabarbarewa saboda yawan bani2, yazamana da kyar yake iya morawa mahaifiyarsa da kannensa wani abu sedai yayiwa khadija haka yadinga dawainiya harta shiga sss, nan manyan mutane suka dinga fitowa suna sonta, duk cikin manemanta babu wanda yayi mata saboda ita burinta ta auri, namiji kyakyawan gaske sannan wanda ya tada kai da naira, sannan tanada burin tazaga duniya, tayi ilimi me zurfi a kasashen waje, yadda zata goga kafada da manyan mata a kasar Nigeria dama nahiyar Africa gaba daya, shiyasa duk wanda yazo indai yanada kudi zata wankeshi son ranta sannan ta sallemeshi, dan har yanzu bataga dai dai da itaba, malam munir yayi iya yinsa dayimata nasiha itada yar uwatta saudat amma abu ya gagara, ana cikin wannan haline Allah yayiwa malam munir rasuwa, mutane sunji mutuwarsa saboda mutumin kirki ne kwarai dagaske, bayan an gama makoki khadija tacigaba da tsiyarta daga inda ta tsaya, ganinda Kabir yayi masu kudi na neman aurenta yasa kara zage damtse, dayasamu kudi ko anmusu albashi dayake yasamu aiki a wani kamfani, seyaje ya kashewa khadija su, har rawar jiki yake wasu kudin sushigo yakuma kaimata, alhalin gidansu wataran se a kwana biyu ba a dora tukunya ba, se ayi term biyu ana korar kannensa saboda kudin PTA, amma baze iya basu ba sedai khadija.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Mahifiyar Kabir ta zubda hawaye ba’adadi amma bayadda ta iya da wannan hali na ko inkula da danta Kabir yake musu itada kannensa, sam takasa gane kansa. 

In khadija ta dau wanka ta taho seka dauka wata yar hamshakin Attajiri ce, saboda ‘yar kwalisa ce ga karya data dorawa kanta, khadija tayi candy amma taki cigaba da makaranta tace seta auri mekudi zataje abroad tacigaba da karatu, sabida abun kunyane a ce nan gaba intazama wata a Nigeria ace za’ ayi interview da ita tace a Nigeria tayi karatu. 

Yauma yammace taci uban ado tana taku kamar tana taka kwai, taji anamata horn da babur amma tayi banza taki matsawa, mutumin yadinga horn amma taki ko daga kai balle tabashi hanya ya wuce, parking yayi ya kalleta yace “baiwar Allah kokurma ce ne? Inata horn kibani hanya zan wuce amma kinyi banza” wani mugun kallo tayi masa, “idanni kurma ce kaikuma mara hankali ba” zaro ido mutumin yayi saboda yasan a haife ya haifi wannaan yarinyar

“nine mara hankalin yarinya?” 

“kwarai kaine mara hankali, ya za’ayi ina tafiya zaka isheni da horn da wannan rubabben gwangwanin naka, kana nema ka kashemin dodon kunnena, aida seka tsaya in wuce, kokuma ka canza hanya, tunda bakai ka gina hanyar ba ai” 

“Amma kina ganin ya dace ki kirani mara hankali da girmana da komai” 

Cikin tsiwa tace “to semenene? Ai abun rashin hankalin kayi” 

“shikenan in abunda kikayimin dai2 ne za’ayiwa mahaifinki kiji inda dadi” 

“to ya mutu wata uku dasuka wuce, inkuma kabarin za’abishi ayi masa se inji, aikin banza mutane suyita abu kaman wasu yan kwaya” 

Cikin rawar murya yace “nine kaman dan kwayan”? 

“kaimana da dawani nake, wayasanima ko ita kaje kasha, kake nema kayimin akuya nonsense” tayi gaba abunta, mutumin nan seda ya zubda hawaye, ya kunna babur dinsa yazo daidai saitin khadija ya tsaya ya kalleta yace “Insha Allah sekin haifi dan kwaya, sekuma ya miki abunda kikayimin” 

“kai kasani, koma kwayar zan haifa, shirmen banza kawai, adai dinga kula, da irin kwayar daza’asha in bahakaba a kare a gidan mahaukata” bataji mezece ba tayi tafiyarta. 

A fusace ta shiga gida tana ta mita, saudat na tsakar gida tana danna waya, ta dago ta kalli khadija tace “Ahh kaga manyan mata a gidan Kabir ya akayine, waya taboki kike mita?” 

A wulakance khadija ta kalli saudat, “waye kuma kabir, karki kara hadani da wannam matsiyacin, a tunaninki mace mai daraja kamarni zan iya auren wani Kabir, tausayinsa kawai nakeji wanke dan banza zangama, da zarar nasamu my dream hubby inyi dumping sha3 aside inyi aurena, idan na auri wannan fakirin ta ina burina ze cika” murmushi saudat tayi, “angaisheki matar manya, banga laifinkiba, nima ina bayanki wayakeso  talauci ai kudi kawai alaji, amma meya bata miki rai haka?” 

Nan khadija ta gayamata abunda yahadata da wannan mutumin, saudat tace “ke manta dashi, kinsan irin wannan mutanen, basa raina abun magana” 

“aikuwa yajawa kansa dan sedana masa rashin mutunci naji dadi a raina” sukayi shewa gaba daya, uwar gidan malam munir tana jinsu tace

“khadija baki kyauta ba abunda kikayi” 

Khadija ta murguda baki “ai dama banyi dan in kyauta ba, kinganni ba ruwana, da kusanci, ko girman mutum ana mun nake ramawa ehee” 

“to Allah ya shirya” 

“Ameen ya shirya abunda yafi hakama”. 

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, khadija tana gwara kan samari, yau ta wanke wannan gobe ta wanke wancan, ba wanda yake da ikon yin Magana, gefe dan wahalarta wato kabeer yanata faman wahalta mata, uwarsa da kannensa kuma ko oho. 

    Yau ake sa ran za’a kawo kudin auren kanwarsu khadija, wato surayya babbar yayarsu maryam tanatayiwa khadija da saudat fada akan su tsaida miji sudena wannan shiriritar, zumbura baki khadija tayi “waike Anty Maryam akanki muke zaune ne? Duk kinbi kin ishi mutane, itakanta surayya guda nawa take za’ayi mata aure, yarinya da kuruciyarta shekara iyanzu ta haihu, ga mijin shiba kudi ba, gaba wani ilimi me zurfi duk tabi ta tsofe da wuri” bude baki Anty Maryam tayi “lallai sannu khadija, surayya ce tayi yarinta da aure, kuma shi arziki na Allah ne ai, sannan ita ya mace darajarta shine dakin mijinta, ba gararamba a layi tana tara samari ba” 

“eh ansan arziki na Allah ne amma ba wanda yakeson talauci ai, tara samari yanzu muka fara semun wankesu munci rabonmu mayi auren” 

Saudat ta kwabe baki sannan tace “batta ai ita na fuskanci so take kowama yayi rayuwar wahala kaman yadda tayi, kuma babu wannan zancen” 

Anty Maryam dataga abun nasu dagaske suke tace “to Allah ya baku hakuri matan masu kudi” 

Khadija tace “Ameen Anty Maryam, Allah yabamu mutemakamuku tunda ku baku da rabo” suka kyalkyale da dariya itada saudat. Ana haka sega surayya ta shigo dakin goye da yarinyar Anty Maryam tace “Anty kinga  humaira tayi bacci a bayana gaskiya na iya raino” Anty Maryam tace “Aikuwa dai kin iya raino, badi iyanzu in Allah ya kaimu Insha Allah kinkusa haifar naki” rufe ido surayya tai tace “gaskiya inajin kunyarki Anty maryam amma dai Ameen” dan zaro ido khadija tayi “au kekinayin auren zaki zage kiyita barin yara sekace kazar hausa” 

Saudat da sauri tace “ganemin hanya dai” 

Surayya tace “to meye a ciki yaya khadija, yara rahama ne bakasan wanda zaka huta dashi ba” 

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

“Ai seki zage kibada himma, ga auren talaka ga haihuwa, nan da nan ki ragwabe akasa banbance tsakaninki da mamanki, kinga bari in tashi in je in abunda yake gabana wannan batamin rai zatayi” khadija ta fice daga dakin, Anty maryam ta girgigiza kai “Surayya kyale wadannan sunyi nisa basajin kira, se fatan Allah ya shirya”. Haka rayuwa tacigaba har akayi bikin surayya, yayinda su saudat duka dorawa ransu dogon buri musamman khadija, bata saurarawa duk wani saurayi da yashigo hannunta, duk tsiyarka duk arzikinka seta wankeka sannan ta sallemaka, amma duk da haka tana tare da Kabir, sha wuyanta kuma yana cigaba dayimata hidima iyakar yinshi, ya wofantar da mahaifiyarsa da kannensa. 

Kawayen saudat sun san khadija sosai, duk da kasancewarta me izza da jin kanta, ko kawayen kirki khadija bata da su se yaran manyan masu kudi, yaran masu kudin ma se yarinyar da akasan ubanta wanda ya tara dukiya sannan tayi kawance dake. 

Ranar wata laraba suna zaune, saudat tayi bakuwa, kai daganin yarinyar kasan kudi sun zauna, saboda ba tayi kalar wahala ba, motar da aka kawota ma a ciki ba karamar mota bace, kawar saudat din me suna Salma ABDUL JALAL Tajudden, kawar saudat ce sosai tasanta da dadewa dasuka hadu a gurin wani biki, khadija tanajin sunan salma a gurin Saudat, tana bata labarin kudin da familyn su salma ke dashi, bayan Salma sun gaisa da mutan gidan, taciro iv card a Jakarta ta bawa Saudat tace “ga iv din nan, saudat dan Allah kizo gurin bikina saura three weeks” saudat tace “Insha Allah zanzo, ashe abun yazo yama za’ayi kice bazanzo ba bayan nayi duk ankon bikinki” 

Salma tayi murmushi tace “Ainasan halinkine saudat, yanzu in bakiga dama ba sekice bazaki ba” 

“zanzo Insha Allah” 

“kinga bari inyi sauri, akwai guraren danake son zuwa, se anjima” har Salma ta mike zata tafi, khadija tace “Salma ni baza’a gayyaceni ba, anyway ina miki murna Allah yasanya Alkhairi” murmushi salma tayi “ni na isa, kema ga naki, ina gayyatarki yaya khadija” ta mikawa khadija iv, tasa hannu ta karba, bayan fitar Salma suka duba iv din nan, kwana bakwai cif za’ayi ana bikin nan, khadija tace “Saudat wai ita kam wannan wazata aura haka” 

“mhmm yaza’ayi insani khadija? Najidai ance dan uwanta ne, boyeshi take kaman ciwo batason aganshi, iya sanina da ita tana son gayen nan kaman ranta, ko sunansa bata fada, kinga jikin iv dinma sunan tane kawai, Allah ya kaimu bikin dai muje muga wazata aura haka” 

“Ainima dole inje bikin nan, dan naga alamar irin bikin da nake sone, dan haka dole a kece raini, muyi wanka kaman yaran senetes, inje inyi sababbin kamu” dariya sukayi gaba daya suka tafa. Kafin lokacin bikin Khadija tasa Kabir a gaba, seda yasamomata kudi kusan dubu arba’in ta sai less din dinner, ta dinga bin samarin ta, tana karbar kudi a gurinsu da haka seda ta sai komai sabo, tayi anko kafin lokacin bikin nan

  Ranar da’aka fara biki, khadija da saudat sun dau wanka, kaikace sune dangin amaryar, khadija takira wani saurayinta yazo ya daukesu a tsaleleliyar motarsa, ranar kamu da bridal shower, da mother’s evening duk ango bezoba, amma anci an sha, anyi barin kudade, kai dagani kasan wannan family sunci sun tada kai, naira ta koka a wannan bikin, gasu kyawawa kaman su sukayi kansu, daga mazansu har mata, gasu dayawansu ba farare baneba amma sunada matukar kyau, sunada dogayen hanci mazansu da matansu, wanda hakan ze tabattar maka family dayane, saboda suna kama da juna, khadija tayi samari a gurin bikin nan, saboda tayi kwalliya tayi kyau harta gaji, kaman uwa daya uba daya suke da amaryar, bangaren saudat ma hakane tasamu samari a gurin bikin. 

Ranar dinner hall ya cika taro yayi taro, manyan mutane maza da mata daga bangarorin Nigeria sun halarci bikin, Mc yabada announcement cewar ango da amarya zasu shigo, nan aka shiga yimusu kirari “Ango Alhaji Habib kamal tajudden, matashin Attajiri me ji da kansa, me gwalagwalai da zinare, Ango kayi dacen amarya hajiya salma ABDUL JALAL Tajudden, me kyautar zinare da dama hagu bata saniba, me ado da  sarkar zinare, abu naku maganin a kwabeku” haka aka cigaba da yimusu kirari tareda saka musu kida flower girls ne suka fara shigowa, se wasu kyawawan ‘yan mata sannan ango da amarya a tsakiya. 

Amarya da ango sun hadu, sunyi kyau harsun gaji, tunda khadija tayi tozali da angon nan tarasa nutsuwarta, ya hadu karshen haduwa bata taba zaton akwai kyakywa a maza irinsa ba, da farine toda tabbas zaka iya rantsewa kace bayajin hausa, wannan shine irin mijin datake tsarawa zuciyarta tana son aure, wanda bata taba zaton ganinsa a gaske ba, Habib ta maimaita sunansa a hankali kaman yadda taji Mc yafada dazu, gumi taji yana tsatstsafo mata a goshi. Shikam ango se fara’a yakeyi cameras kota ina se hotuna akeyimusu, Saudat ta janyo hanun khadija sukaje suka dinga hotuna da ango da amarya, bayan sun dawo gurin zamansu ne saudat tace “khadija kinga wannaan bawan Allah kaman shi yakera kansa, dan Allah ga kyau, wallahi yafita kyau sosai” da kyar khadija tace

“mhmm aikam dai yana da kyau” duk bata cikin hayyacinta, haka aka gama dinner din nan aka watse, a hanya khadija tacewa saudat “Sauda amma Salma ba hausawa baneba ko?” 

“eh to rabinsu hausa rabinsu kanuri, yan borno ne, kasuwanci yakawo wasunsu kano” 

Download>>> Babban Yaya Complete Document

“lallai kam, gasu da kyau gasu da kudi” haka suka cigaba da hira har sukaje gida,ranar khadija kwana tayi tana tunanin habib, tareda mafarkinsa. 

Suncigaba dazuwa gurin bikin nan har akayi akagama. yayinda kullum khadija insukaje suka dawo, soyyaya da tunanin habib ya cigaba da ninkuwa a zuciyarta. 

Ranar daza akai amarya, juyin duniya saudat tayiwa khadija akan suje kai amarya tace bazata ba, tun tana lallabata har itama ta hakura tace tafasa zuwa gurin kai amaryar, taje daga baya, in Salma ta tare. Ranar Khadija ta kwana da matsanancin kishin Salma, kasa bacci tayi daren ranar dan tayi mamaki yadda kaunar habib ta mamaye zuciyarta lokaci daya haka, haka ta kwana sake2 da tunani har gari ya waye. Koda gari ya wayema bata fito tsakar gida ba tana tana kan gado tana juyi Saudat ta shigo dakin tazauna gefen gadon ta kalli khadija tace “yar uwa tashi muyi wata magana kibani shawara dan Allah” khadija ta kalli saudat idonta duk yayi ja alamar rashin bacci, ta mike zaune ta dan yatsina fuska ta kalli saudat “fadi inajinki?” Saudat ta gyra zama tareda kallon khadija sannan tace “Khadija nifa tunda mukaje bikin salma, nayi ido hudu da mijinta naji wallahi inasonshi, shiyasa nazo kibani shawara yazanyi, Dan gaskiya bazan iya hakuri ba, bazan iya auren kowa ba seshi, dan Allah sister bani shawara ta ina yakamata in fara?” 

Gaban khadija ne yafadi, zuciyarta ta shiga bugawa da karfi, ga wani gumi dayake tsatstsafo mata a iya goshinta, taiwa Saudat wani irin kallo, sekuma tayi murmushi seda hakoranta suka fito, ta kalli saudat” Kin tabatta kinason Habib? ” da sauri Saudat tace” Wallahi khadija so bana wasa bama, wallahi ina sonshi, aurensa nakesonyi” khadija ta gyada kai takuma yin wani murmushi.

Ta dafa kafadar saudat “bakida damuwa zanyi meyuwuwa inga burinmu yacika, amma kisani dole abu daya yafaru, ko kiyi nasara, kokuma akasin haka” “hakane amma ni nafi sa ran nasara dan kome zefaru sedai yafaru”

“gara kidinga sawa ranki nasara da akasin haka, yanzu dai macigaba anjima, inada abunyi yanzu”

“to shikenan bari zan dan fita dama, sena dawo”

Saudat nafita khadija tabi bayan saudat dawani mugun kallo, sannan tayi kwafa “gaskiya Saudat bakida hankali, kekin isa inso abu kema kice kinaso, zakiga tsiya dake zanyi tarkon cikar burina, ita kanta Salma seta barmin Habib” ta sakeyin kwafa ta nemi guri ta kwanta. 

Sati daya da kai Salma gidan habib, Saudat ta shirya taje gidan Salma, ba karamin tsinkewa Saudat tayi ba da ganin aljannar duniyar dake gidan Salma, gidane na alfarma kaman ba a Nigeria ba, ga shi an kashe masa kudi da kayan alatu, haka Saudat ta sake taita kallo tana video gidan dan ta nunawa Khadija, bangaren kayan Abinci ba a magana, tasamu kyakyawar tarba daga salma, ta karramata da kayan Abinci sukayita hira Saudat tace “Salma kawo in turamiki hotunan da nadingayi miki lokacin biki” ba musu Salma tabawa Saudat wayarta, tana cikin yimata turi ta faki idonta ta dauki lambar Mijin Salma wato Habib, haka suka dinga hira se la’asar sannan saudat ta tafi, saudat taso taga habib amma bata ganshiba salma tagaya mata baya gari. 

Tunda saudat taje gida tana rawar jiki taje tasamu khadija tadinga nuna mata video gidan salma, gaba daya khadija ta rikice da ganin aljannar duniya, tabbas habib shine mijin daya dace da ita, 

Daga nan ta nuna mata ta samo lambar Habib “khadija ga lambarsa na samo ta ina yakamata in fara” 

Hanzarin me kike ne, ba tace miki baya gari ba, kibari se kaman  nan da sati daya mana maybe lokacin ya dawo”

“anya zan iya jira har sati kuwa, nifa banki ace ko a satin nan a daura aure ba dan ba karamim so nakeyiwa gayen ba, kokuma ince nakewa dukiyarsa ba” 

Khadija ta jinjina kai tace “to wai yazakiyi da kawarkine, in ta gane zaki aurar mata miji” tsaki saudat tayi “wayake tawani matarsa, ai ranar biyan bukata rai ba a bakin komai yakeba, indai buri zecika, to babu batun kunya da cin amana, inma ta gane ita tasani nidai fatana in ganni a cikin wannan daukar” “hmm Gaskiyar ki yar uwata, Allah ya ida nufi”

“Ameen khadija, ammafa in Salma tagane ba karamin hauka zatayu ba, dan tana masifar son gayen nan, gata da kishi kamar bala’i, amma tasamu dai dai da ita indai nice” murmushi khadija tayi

“gaskiya zata taro match kishi da hajiya Saudat” sukayi shewa gaba daya. 

Kwana biyu da zuwan saudat gidan Salma, khadija ta shirya tun safe ta fita ashe wayar saudat ta dauka tun dare ba wanda yasani, ta fita ta cire sim din saudat tasa a wayarta ta dauki lambar Habib, sannan ta kakkarya layikan saudat ta zuba a kwata, sannan ta jefar da wayar tai tafiyarta, bata koma gida ba se bayan magariba yaje ta tarar anata jimamin wai barawo yashigo gida jiya da daddare yasace wayar saudat, ta shiga sahu akaita jajantawa saudat, saudat tabiyo khadija dakinta kaman tai kuka tace “wallahi khadija ba batan wayatane yabani haushi ba, rasa lambar habib itace ta konamin rai” 

“don’t panic dear, karki damu, inkika canza waya seki kuma samo lambartasa, aibawani abu a ciki” 

“haba khadija kinsan da yadda nasamo lambar nan kuwa idan nakoma mezance mata inkuma karbar wayarta, kuma kwata2 yaushe naje gidanta dazan koma” ta karasa maganar kaman zatayi kuka

“haba saudat kefa kikace ranar biyan bukata raiba abakin komai yake ba, amma kibari kaman in akayi sati biyu sekikuma zuwa, kinga ba wanda ze zargin wani abu” 

Saudat ta kalleta “haba khadija har sati biyu, anya kuwa zan iya jurewa” 

“Saudat idan kikabari matarsa ta gane zaki aurar mata miji to tabbas bazata kyaleki ba, gara kibi komai a sannu in lokaci yayi taji” 

Saudat tayi nannauyar ajiyar zuciya tace “kuma kinyi gaskiya khadija, shiyasa nakeson shawarwarinki nagode sosai, bari anjima Mukhtar zezo se in sashi yakawomin wata wayar” 

“eh hakan ma yayi kyau” 

“hakane nagode bari inje inyi salla” tana fita khadija tai murmushin mugunta. 

Khadija tasa kabir yasiyo mata sabon waya, me madannai tayi saving lambar habib a ciki, kullum safiya da dare seta tura masa zazzafan text messages da addu’oi , hakama da daddare zata tura masa  bata taba kiransa a waya ba, shima kuma betaba biyowaba balle yaji waye. Amma habib yana mamaki wacece take turomasa wannan messages haka, shidai yasan ba Salma bace bata da wannan lambar, kuma tunda sukayi aure bata yimasa tex kamana yadda take masa kafin suyi aure, amma bari ya tambayeta ko itace take turo masa, salma na gaban mirror tana taje kai, habib yana kan gado a kwance ya kalleta yace

“my sweet lambobinki nawane?” kallonsa tayi “meya farune??”

‘No bakomai na tambayeki ne dai”

“fadamin gaskiya ko watace take kiranka ka zata nice” gabansa ne ya fadi ya kalleta, amma yakasa magana a hankali ta tako tazo ta zauna a kusa dashi tace

“yanaga ka tsorata, nafada dai2 kenan” 

“A’ a kam kinbani mamakine kawai, daga tambaya kin canzamin magana, kaman kina zargina” 

Tayi Ajiyar zuciya “Habib kada Allah ya nunamin ranar da wata mace zata dinga kiranka, amatsayin budurwarka, inaga a wannan ranar se zuciyata tayi bindinga, bazan iya jure ranar dazanyi sharing dinka da wata mace, inasonka habibi da’iman” seda cikin habib ya duri ruwa, amma ya dake yace

“I love you too hibbaty, karki damu zuciyata kekadai ce a ciki, zan rayu dake har zuwa karshen rayuwata” yai mata murmushi tareda yin kissing dinta a goshi, ta dora kanta akan kirjinsa tanata ajiyar zuciya, message ne yashigo wayarsa, yasa hannu ya dauka ya bude message ne na nuna tsantsar soyayya da kauna da khadija ke turomasa, sauri yayi yasa lambar a blacklist, ba tareda salma ta dago ba tace “habiby waye ya turomaka message?” 

“Alert ne, kayan dana siyar aka turomin kudin” har cikin ranta ta yadda da abunda yace. 

Haka khadija takuma canza layi tacigaba da turawa habib messages baji ba gani, abunne yafara damun habib kar by mistake Saudat tagani, gashi layinsa ne dayakeso wanda huldodunsa na kasuwanci duk akai suke da se ya cire layin ya yar, besan mezece ma Salma idan taga wannan messages dinba, dan Yasan halinta da mugun kishi, yanzu se cibi yazama kari, ba dan haka ranar ya yanke shawarar yakira yaji kowacece, da safe wajen karfe goma khadija tana kwance tanata tunanin habib tana kallon hotunansa, karamar wayarta datake kiran habib da itane tafara ringing, ga mamakinta taga Habib ne nannauyar ajiyar zuciya tayi tareda yin murmushi ta rungume wayar a kirjinta tanajin ringing din wayar harcikin zuciyarta, wayar tayita ringin harta katse bata daga ba taitajira koze kuma kiranta amma be kirata ba. Kusan kwana uku bekuma kiranta ba itamuma tacigaba da turamasa, rana ta ukun da daddare yakuma kiran wayar khadija seda ta kusa tsinkewa, sannan khadija ta tattara duk wata nutsuwarta ta daga wayar, tana dagawa kafin tayi magana a fusace yace “wai dan Allah wacece haka, kina nema ki hadani fada da matata meye hakane, karki kara turomin wannan rubbish din nagaya miki” maganganunsa sunyimata zafi, amma ta dake tace “ohhh masha Allah, zanyi bacci irin wanda bantabayiba yau habib, naji muryarka Ina sonka, kayi bacci me dadi kaman yanda zanyi cike da farinciki” tunda tafara magana gaba daya jikinsa ya mutu yakasa cewa komai, itama bata jira meze ce ba ta kashe wayarta, tace “Lallai Habib bakasan wacece khadija ba bazaka taba kufcemin ba tunda kayi gangancin kirana” khadija bata taba gajiyawa ba gurin yi masa aiken zafafan kalaman soyayya. 

Yau sati biyu cif tacika da zuwan saudat gidan Salma, tun karfe goma na safe ta shirya, tazo tayiwa khadija sallama cewar zataje gidan Salma, ita khadija ta manta ma cewar sunyi da khadija yau zata koma gidan Salma, khadija ta dake taimata fatan nasara, bayan ta fitane ta dinga mata dariya. Koda saudat taje gidan me gadi yasanar da ita cewa masu gidan basanan sun tafi Abuja karfe 2narana zasu bar Nigeria zasu wuce Dubai, Saudat jitayi kaman ta dora hannu akai tayi ihu, tacewa me gadin “dan Allah yayana kozaka temakamin da lambar me gidan?” zare ido yayi “lallai da alamu kina da tabin hankali yadda tsaro yayi karanci zakice abaki lambar megida, to ni kaina bani da lambarsa, seta PA dinsa, se in abun me mahimmanci ne sannan ya hadaki dashi kuyi magana, inkuma bame mahimmanci bane ba yakamaki yace bakida gaskiya, indai baya gari tokomenene hakura nake”dafe kai saudat tayi takuma cewa” dan Allah kabani lambar P. A dinnasa mana” “waike wace irin mayyace ne, bar kofar gidan nan ko inyi waya azo a tafi dake wallahi” “No yi hakuri zan tafi, insun dawo senazo” daga nan ta juya ta taho gida, tareda tsinewa barawon dayasaci wayarta albarka, tasamo lamba a bagas an sace wayara haka ta dawo gida jiki a sanyaye, kallo daya khadija tamata tagane babu alamun nasara, nan Saudat tabawa khadija labarin abunda yafaru taita rarrashinta tareda bata karfin gwiwa kaman gaske. Khadija takoma daki ta tsarawa Habib text 

“Hayateee ashe zakabar kasarnan ba labari, masoyi masoyine ai at least yakamata in sani ai, Allah yakaika lafiya, yatsaremin kai yakareka ya kare dukiyarka, Allah ya albarkaci neman ka, ya doraka akan makiyanka, dukda ni baka damu daniba amma ni kullum soyayyarka ninkuwa take a zuciyata, gangar jikina tana Nigeria, zaka tafi da rayuwata Dubai, kaine rayuwata habib ka kulamin da rayuwata, zanyi kewarka rayuwata, Ina sonka Hayateee” Habib yana harabar hotel din dasuka sauka yaji message din yashigo koba a gayamasa ba yasan na wannan mayyar ne, yana budewa yakaranta sakon yana kuma karantawa, to ya akayi tasan zebar kasar, kiranta yayi seda taja aji sannan ta dauka

“barka da wannan lokaci Rayuwata” 

“ke wai aina kika samu lambata kike takuramin haka, sannan wayagaya miki zan bar garine yau” 

“haba hayatee, kaifa rayuwata ne, yaya za’ayi inkasa sani, dukda nibani da mahimmanci a gurinka, kai kanada mahimmanci a gurina, Habib yakamata ka girmama kalmar so” tayi ajiyar zuciya, cikin kissa kaman zatayi kuka tacigaba da cewa “Habib bansan da wani kalman za gwada maka yadda nakeji a zuciyata ba” 

“kinga dakata, wai bakisan inada aure ba kwata 2 wata biyu kenan da yin aurena, yazaki dinga turomin messages na soyayya in matata tagani fa?” “shiyasa bana kiranka nakemaka message, kuma mata hudu Allah ya halatta maka, karkayi garkuwa da aurenka ka wulakanta bukatata” 

“Ke inkece a matsayin matata yazakiji idan akayi miki haka, inason matata kuma ni bazan kara aure ba mace daya Salmana ta isheni” 

“Habib da kaine a halin danakeciki nake maka abunda kakemin yazakaji, nafara sonka tun kafin infara ganinka” tayi ajiyar zuciya sannan tace, “shikenan Habib ka dawo lafiya Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwar aurenka, nikuma zan dawwama cikin bakinciki har karshen rayuwa ta, zancigaba da rayuwa da soyayyar ka” takarasa maganar tana hawaye “kakula da kanka rayuwata ina sonka rayuwata Habib, i will miss you, zanshiga yanayi mara dadi habibina” kafin yayi magana ta kashe wayarta, habib yacigaba da jujjuya kalaman yarinyar, dan tabe baki yayi yakoma masaukinsu. 

Seda habib ya shafe wata shida bezo Nigeria ba shida Salma, suna dubai yana business dinsa suna cin aamarcinsu, sam khadija bata samun habib a waya saboda bata da lambarsa ta Nigeria, ta turamasa message harta gaji, ta bibiyi har gidansa taje tabawa megadinsa makudan kudi da zimmar duk randa habib ya dawo zekirata a waya ya sanar da ita, sannan tace masa idan har Saudat takuma zuwa gidan ya hadata da ‘yan sanda, yace musu su tuhimeta, sannan ayi mata iyaka da zuwa gidan habib, ganin kudi yasashi amsawa yace yadda takeso haka za’ ayi. Wannan kudin databawa megadin gidan Habib Adashin da kabir yayi ne a gurin aiki yakawo mata fiye da rabin kudin yace ta sai kayan kwalliya, shine ta dauki kusan dubu tamanin tabawa megadi dan yayi mata aiki. 

tsawon watanni shidan nan haka tayisu kaman mara lafiya, zazzafar soyayya da takewa habib ta wuce misali, har rashin lafiya tayi, gaba daya yan gidansu sun kasa gane kanta, juyin duniya taki gayawa kowa abunda yake damunta, ta rame sosai. Haka bangaren Saudat tayi zarya gidan habib harta gaji, kamar yadda khadija tagayawa megadi haka ya hada Saudat da yansanda, yace musu be yadda da itaba da alama, irinsune wanda yanfashi ke hada kai dasu, haka yan sanda suka kama Saudat, ranar wuni tayi a cell, yayyensu maza sukace ba ruwansu bazasu belinta ba, dama bata da kunya gara a koyamata hankali. Maman Saudat ta dinga hadasu da Allah suje sufito da Saudat sukaki, sukace “aibasu suka aiketa yawon gidan masu kudiba” Khadija da kanta takira kabir a waya tace yazo yanata rakiya, tasa Kabir agaba sukaje police station sukayi belin Saudat, yadda khadija tasaki jiki da yansanda suka dinga hira hada exchange na number ba karamin batawa Kabir rai yayi ba, tunda suka fito yake mita “haba khadija kinsan bana sonki da irin wanan abun, danmene zaki saki jiki da wasu mazan a gabana hada basu lambar wayarki” 

“kai dakata malam, aurena kake dazaka dinga takuramin, inbahaka nayiba kana ganin zasu sakarmin kanwata ne? Nifa banason wanan shirmen naka wallahi, inka gama mitar ka iya tafiya” tai shigewarta gida tabarshi a nan a tsaye. Tunda suka koma gida Saudat tayi wanka takasa ko cin Abinci, khadija taje kusada ita ta zauna “Saudat wai meye na damun kanki, bagashi naje nafito dake ba?” 

“mtsee khadija ba wanan ya dameniba, ni yanzu tashin hankali na rasa habib, wallahi khadija inason habib, zanyi duk meyuwuwa nima inshiga wannan daular in dama, kome zafaru dani a gaba sedai ya faru amma sena auri habib” 

“Saudat kibi komai a sannu, karkiyi gaggawa, se komai yazo miki da sauki, inkikace zakiyi garaje to zaki lalata komai ne” 

“hakane amma ni yazanyi zuciyata kaman ta fashene khadija, ni kawai burina inganni a wannan daular” khadija aranta tace “yarinya man kaza, niba dukiyarsa kawai nakeso ba, har shi kanshi habib din nakeso, dan haka zan cigaba da wasa da hankalinki yarinya” ta riko hannun Saudat 

“yar uwa, duk macen dataga habib taga dukiyar daya tara dole tasoshi amma kibi komai a sannu, in baki iya takunki ba garin wannan rawar jikin naki wataran prison za’a kaiki, yanzu abunda ze faru kidanyi hakuri kibari su dawo kasar nan semuga ya zamuyi tunda ba abunda zamu iya a yanzu tunda baya kasa” 

“shiyasa nake sonki khadija, kin damu da damuwata, zan bari se ya dawo kasar nan” 

“idan ya dawo dinma karki sake kikuma zuwa layin gidansu, kibari zansa aje a dan dinga survey din anguwar tasu da anga ya dawo za’asanar damu, Nikaina zanyi alfahari inganki a cikin wannan daular, inkika samu aina samu” rungume khadija tayi da sauri “nagode sosai, inaji dake yar uwa” 

“zakigane baki da wayo, bazan taba bari kikuma rabar inda habib yakeba” 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Share please 

I want comments not stickers or just thanks 

Daga alkalamin Aysher cool.

Back to top button