Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 70 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔🥺

*Daga alƙalamin Hafsat Boss Bature✍️*

💋PRISONERS💋

Prisoners sun ga rayuwa, Sun ɗanɗani raɗaɗi mai ɗaci a cikin zukatan su, babu wanda ke a cikin hayyacin shi, bayin Allah sun ji jiki fiye da a misalta, sun ga tashin hankali tsirarar shi, Yinin ranar babu wanda Ya motsa tun bayan da aka kawar da gawawwakin su Majnoon, kamar matattu haka su ka koma, su batul da ke a cikin toilet kamar gumaka, sun ƙame babu mai magana, hawayen dake zuba akan fuskokinsu tuni sun jima da ƙamewa, sun bushe ƙamas a saman faces ɗinsu, kukun zuciya su ke yi wanda yafi ciwo, mutun huɗu da suka suma a cikin toilet ɗin daga ciki akwai parveen, hibba, Yasmin da Rubina, waɗanda suka rage basa motsi, batul da ta lagwa6a kanta jikin bango, eve ta ɗaura kanta saman Laps ɗin batul, Sarah dake kwance ƙasa, Hanna ta ɗaura kanta saman waist ɗin Sarah, kamar hotuna babu mai moving.

A cikin bedroom ɗin su, har ila yanzu su Angel basu motsa ba, tana anan inda ta suma saman gadon majnoon, yayin da su Deeja su ke a sume saman floor, Hatta Jamima da ta rage tana kuka tuni kanta ya fara sara mata da matsanancin ciwo, zazza6i ya yi mata mugun kamu, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, ga shi babu mai motsi a cikin su balle ta samu wanda zai jata a jikin shi ya rungumeta ya lallasheta gwanin ban tausayi.

A ƙarshe da ciwon yaci ƙarfin ta a saman bayan Angel ta kwantar da kanta tare da sanya hannayenta biyu ta ƙanƙameta, Allah ne ya sawwake mata ciwon nata ta hanyar bacci da ya ɗauke ta, mutuwar Majnoon da Unaiza sun ta6a zuciyata ni kaina da nake rubuta littafin, na zubar masu da hawaye tamkar rayuka ne masu numfashi, duk da ina ɗaukar labarin tamkar true life story ne saboda akwai waɗanda suke fuskantar irin wannan uƙubar, tabbas akwai su babu tantama, laifin me unaiza ta aikata data cancani wannan sakamakon daga mahaifinta? Laifin me majnoon ya akaita da ya cancanci irin wannan rayuwar, unaiza just 16 years mahaifinta ya wulaƙanta rayuwarta, ya barta acikin duhun jahilci, saboda mugunta da son zuciya na wasu mutanan masu hali irin na dabbobi, masu neman duniya ido arufe wai ace yau ɗanka na cikin ka zaka sadaukar don ka biya buƙatar kanka wadda a gidan duniya zaka bar koma me ka mallaka.

Ya hana ta mori duniya sannan lahirar ma ya hana ta nemeta, da ya ke Allah ba azzalumin bawan shi bane sai ya haɗa ta da Angel agidan kurkukun ƙaddara, Abunda yake baƙin cikin ta sani game da addinin Shi, Angel ta fahimtar da ita, finally Unaiza ta koma ga mahaliccin ta amatsayin musulma, ta tafi atsarkaken ta, tamkar a ranar aka haife ta, don haka unaiza ba ita bace abun tausayi, mugun ubanta shi ne zai ji tausayin kan shi, domin kuwa ire iren su tun a gidan duniya zasu fara gir6ar abun da su ka shuka, ya yi asarar rayuwar shi, saura ya jira haɗuwar shi da mahaliccin shi, Ya Allah duk masu Hali irin na Uban unaiza Jan wuya, ka hanasu jin daɗin rayuwarsu Allah ka toni asirinsu ka kawo mana ƙarshensu, saboda basu da amfani acikin rayuwar mu, Idan muka koma 6angaren majnoon, Yaron baisan komai ba, just 12 years ahaka aka sadaukar dashi! Shin su wanene iyayenshi? Dabbobine ko makafi ne ko kurame ne? yaron da bashi da ƙoshin lafiya, ga ta6in hankali ga ƙuruciya, a haka aka samu wani mara imanin mai zuciya irinta kafuran farko ya sadaukar dashi, Tsakanin iyayen shi ko danginshi, tabbas zasu ɗanɗani kuɗarsu, wannan alwashine alƙalamina ya ɗauka, kowa sai yaji a jikin shi! Ɗaya daga cikin su bazai sha ba! Muddin ina numfashi! In sha Allahu.

Kusan kwana uku da rasuwar Majnoon da Unaiza, Ko ruwa bai gifta maƙoshin su ba, waɗanda suka suma har yau basu farfaɗo ba, tamkar ba zasu rayu ba, Jamimah kaɗai ce ta ke rayuwa acikin ɗakin nasu, ta yi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, babu mai jinta balle a samu wanda zai lallashe ta, Yadda suka ga rana haka su ke ganin dare, yadda ake kawo masu abinci haka ake ɗaukar shi ba tare da sunci shi ba, Jamimah kaɗaice wani lokacin ta ke kwasar shi a kwando ta 6oye, ko ta yi niyar cin abincin bata jin daɗin shi, kayan marmari kaɗai take iya sha, sai ruwa, Haka zata dinga bin su tana ambaton sunayen su haɗi da yayyafa masu ruwa don su farfarɗo su dawo cikin hayyacin su amma babu mai motsi, hatta su batul ga dukkan alamu suman su ka yi su ma.

A cikon kwana na huɗu ne, Batul ta motsa, da matsanancin ciwon kai da zazza6i, idanuwanta biji biji take kallonsu kamar matattu, daƙyar ta iya buɗe baki ta soma ambaton sunayen su ɗaya bayan ɗaya.

“Sarah! Hibba! Hannah! Parveen! Pls ku tashi, ku tashi mu rungumi junan mu, bana so na ƙara rasa wani a cikin ku……….” numfashi taja tare da ɗaura hannunta saman sumar kan eve tana ɗan bubbuga shi”Eve ki tashi, wai ba ku ji ina kiran sunayen ku,” ta yi maganar a wahalce sautin ke fita, A hankali ta janye kan eve daga saman laps ɗinta ta kwantar da shi bisa floor, ta yunƙura ta matsa kusa dasu Parveen ta sanya hannu tana bubbuga jikinsu, Haka ta dinga binsu tana tatta6a su tare da ambaton sunayen su, Jin muryar Batul yasa Jamimah ɗago da kanta daga jikin Angel, don anan take wuni, rungume da ita, duk da bata motsi, jikinta na rawa ta sauko daga saman gadon da gudu ta nufi sashen toilet ɗin, tana shiga ta tura ƙopar makewayin da su ke a ciki ta shiga, a zuƙunne ta samu batul tana yin shessheƙar kuka, sanyi ne ya ratsa zuciyar Jamimah.

Ta ji daɗi sosai ganin sun fara farkawa, idanuwanta a cike tab da ƙwalla ta ambaci sunanta”Sister BATOOL” jin muryar Jamimah Yasa ta yi saurin juyar da kanta don ganin me magana, suna haɗa ido da Jamimah, a hanzarce ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi bakin ƙopar, ta zuƙunna tare da janyota a jikinta ta rungumeta sosai tana cigaba da matse ƙwallar dake acikin idanuwanta.

Cikin muryar kuka jamimah take faɗin”Sun tafin min da majnoon ɗina, bazan sake ganin shi ba, ko zai dawo ne? Ta yi tambayar tare da ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul, sam takasa amsa mata tambayarta, saboda bata fahimci me take nufi ba, tun da su basu san cewa hada Majnoon ya mutu ba, su na acikin toilet, ko lokacin da giant ya shigo ya ɗauki corpse ɗin Unaiza basu fargaba.

“Majnoon ɗina jikin shi duk jini, inata kuka ina kiran sunan shi, babu mai jina, pls sister batul ki faɗi min gaskiya, mai ya faru da majnoon ɗina zasu dawo min dashi, ko in fidda rai,” Tana magana hawaye na bin cheek ɗinta, fuskarta ta yi jawur da ita, har rama ta yi, tsananin tausayinta ne Ya kama batul, ta sanya tafin hannayenta biyu tana share mata mata su.

“Sister batul, baki bani amsa ba, yau 3 days kenan, Ni kaɗai nake motsi a cikin ɗakin mu….” bata ƙarasa maganar ba, ganin yadda batul ta zazzare idanuwanta tsananin mamaki ne akan fuskarta, jin abunda tace A ruɗe ta maimaita 3 days! Ras gabanta ya faɗi don bata fahimci cewa sun ɗauki tsawon kwana uku basa a cikin hayyacin su ba, sai da Jamimah ta furta mata.

“Ina ta kiran sunayen ku babu mai amsa min, gashi bani da lafiya zazza6i da ciwon kai, Har ruwa nake watsa maku a jikin ku don ku farka amma babu wanda ya motsa, itama Genie ɗita taƙi farkawa inata kiran sunanta…….”

Tun kan jamimah ta ƙarasa maganar batul ta zabura ta miƙe Jiki ba ƙwari ta soma ƙwala masu kira na fitar hayyaci, tamkar maƙoshin ta zai 6allo, babban abunda take ji ma tsoro kada ace zuciyoyin su ne suka buga, da sauri ta tsallake su ta nufi bucket ta ɗebo ruwa a fanfo, kusan rabi ta cika, daga inda ta ke a tsaye ta ɗaga bokitin ta daddage ta watsa masu Sarah saman jikin su, Cikin sa’a suka soma jan numfashi, da sauri ta juyar da bokitin saitin jikin su Parveen ta watsa masu ruwan a jikinsu, nan take suka soma Jan numfashi da ƙarfi, Ganin ruwan ya qare ne yasa ta sake ɗebo wani abakin fanfo, ta sungumi bokitin zuwa cikin room ɗin su, tana shiga tsakiyar ɗakin inda su Deeja su ke a kwance, ta ɗaga bokitin ta daddage ta watsa masu ruwan a jikinsu A figice Azeeza da Deeja su ka farka suna faman sauke ajiyar zuciya, ragowar ruwan daya rage a bokitin ta watsa ma Angel da ke kwance saman gadon Majnoon, koda ruwan ya sauka a jikinta, bata buɗe idanuwanta ba, sakamakon nauyin da su ka yi mata, sai dai ga dukkan alamu ta farfaɗo, duba da yadda take motsa la66anta kamar tana ambaton sunan Allah.

Sanyayyiyar Ajiyar zuciya batul ta sauke, a yayin da ta ke bin su da kallon, A galabaice su ka miƙe zaune saman floor suna ambaton ruwa zasu sha, maƙoshin su zafi, ƙishi su ke ji, ‘ ajiye bokitin hannunta ta yi a ƙasa da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta tana laluban robobin ruwan da Jamimah tace mata ta ajiye masu, kusan guda shida ne, ta rungumo huɗu A ƙirjinta, taje ta miƙa ma Deeja da azeeza yatsun hannayen su na kerma suka kar6a tare da cire murfin, Yanayin yadda su ke shan ruwan ne ya bata tausayi, Kamar ta fashe masu da ku ka.

Motsin da Angel za ta yi ke da wuya ta ƙundumo daga saman gadon ta faɗo saman floor, kanta ba ƙaramin buguwa yayi ba, Da sauri Batul ta nufe ta tare da zuƙunna agabanta, sai da ta fara A jiye bottle waters dake a hannunta a ƙasa kafin ta sanya hannayenta biyu wurin tallabo da kanta ta ɗaura shi saman laps ɗinta, muryarta a sanyaye ta soma yi mata magana.

“ƴar uwarta rabin raina, Pls ki tashi, nasan kina jina, ki yi haƙuri ki jure, komai ya wuce, bana son abunda ya faru ya yi silar tarwatsewar farin cikin mu” a hankali Angel ta buɗe idanuwanta waɗanda suka canza launi sun ƙanƙance, biji biji ta ke ganin fuskar batul.

Hannu batul ta miƙa ta ɗauko ɗaya daga cikin robobin ruwan da ta ajiye gefenta, bayan ta cire murfin, ta ɗago da kan Angel zuwa saman ƙirjinta,
“Nasan kina jin ƙishin ruwa, Ki buɗe baki kisha” ganin taƙi motsa lips ɗinta ne yasa ta cusa mata bakin robar abakinta, don dole tasha ruwan, sosai ta kur6e shi, kusan rabin robar ruwan ta shanye, yunƙurin amai ne yazo mata gaba ɗaya ta sheƙar da ruwan data sha saman jikin batul, a ruɗe batul ta ajiye robar ruwan da ke a hannunta, ta rungume Angel ajikinta, tamkar zata mayar da ita cikin cikinta, ita kanta ba lafiyar ce da ita ba, a haka ta dinga lallashinta, Azeeza da Deeja sun yi zugudum babu mai iya magana a cikin su, Bayin Allah sunyi fatan ace mafarkine abunda ya faru ba gaske ba, Sai da kash ƙaddara ta riga fata, idanuwansu akan gadon majnoon, jinin shi ne daskare akan zanin gadon, Allah sarki rayuwa kenan babu wanda yafi ƙarfin mutuwa, idan ajali yazo dole ka miƙa wuya.

“Deeja Yakamata Mu daina zubar da hawayen mu, mu lallashi ƴan uwan mu tunda mune masu juriya a cikin mu, idan har bamu fi ƙarfin zuciyoyin mu ba, zamu rasa ƙwarin gwiwar da mu ke dashi, dama su abunda su ke so kenan, saboda basu san ciwon kan mu ba, da biyu suka dawo mana da Ƴan uwan mu bayan sun san cewa mutuwa za su yi, meyasa basu ruƙe su a wurin su ba? Suna so ne kawai su kashe mu da ran mu shiyasa su ka dawo mana da su a wulaƙance don muga irin mutuwar da za su yi, Allah ya isa tsakanin mu da su!” daƙyar ta ƙarasa maganar cikin ƙunar rai.

Shigowa Cikin ɗakin su parveen su ka yi, Hannun su ɗaya dafe da goshin su, Tafiya su ke yi tamkar zasu kife ƙasa, saboda jirin da suke gani acikin idanuwansu, ga ciwon kai da yunwa da ke addabarsu, ga damuwar da ke ƙunshe cikin zuciyoyin su.

Gaba ɗayan su ne na cikin toilet ɗin suka fito a jere, a saman floor su ka zazzauna, Parveen na ƙoƙarin zama idanuwanta su ka hango mata gadon majnoon.

A gigice ta furta “Innalillahi….” ba tare da ta ƙarasa maganar ba, tsananin tsoro ne da firgice su ka bayyana a cikin akan fuskokin su, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, musamman parveen a ruɗe ta nufi gadon majnoon ganin daskararren jini asaman shimfiɗarsh, hannayenta biyu ta ɗaura saman bargon shi, yayin da zuciyarta ke tafarfasa.

Muryar Hannah na rawa ta furta”INA MAJNOON YA KE? JININ MENENE MU KE GANI A SAMAN SHIMFIƊAR SHI, DAN ALLAH KADA KU CE MANA YA MUTU SHI MA”!

Babu wanda ya iya buɗe baki ya basu amsa, hakan yasa su ka fahimci cewa Majnoon ya mutu babu shi, hawaye ne masu ɗumi su ka wanke fuskokinsu, A saman shimfiɗarshi Parveen ta kifa kanta da ke sara mata da ciwo, ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, bakomai take tunawa ba face Irin rayuwar da su ka yi dashi, ta yi matuƙar tsaya mata arai, ta yi danasanin duk wani bugu da ta yi mashi, tun ranar farko daya fara kasancewa a cikinsu, Ya 6arar masu da Cake, Tana matuƙar son yaron tsanar da ta yi mashi a lokacin saboda 6arnar da ya ke yi masu ce, ɗago da hannayenta tayi tare da ɗaga su sama tana kallon fingers ɗin ta da ke kerma, Hawaye jaga jaga akan fuskarta, sautin kukanta ya cika ɗakin nasu, Muryarta da wani irin sauti ta ke faɗin”YA ALLAH KA ƊAUKI RAINA IN HUTA! BAZAN IYA JURAR TASHIN HANKALIN NAN BA! Bana fatan na sake yin tozali da gawar wani a cikin ƴan uwana, So nake na mutu in huta, Narasa Majnoon abokin Faɗa na ga Unaiza ma ta tafi tabar mu da kewarta, wayyo Allah nah! ‘ sosai ta rushe masu da kuka, kamar mahaukaciya haka ta cusa hannayenta cikin sumar kanta, ta dinga hargitsa gashin cikin ƙunar rai, kafin ta mayar da kanta saman mattress ɗin Majnoon.

Duk suna jin sautin kukanta, Jikin su duk ya yi sanyi, mutuwar mutun biyun nan ta raunata zukatan su, ta sagar masu da gwiwarsu, komai ya fita aran su, babu mai sauran walwala acikinsu, ba don zuciyar Imani ba da tuni wasu daga cikin su sun zauce, musamman Azeeza ta shiga halin ha’ula’u, tsoro da firgici sun hana ta sak, har zufa ke tsastsafo Mata saman goshinta, tun da ta farfaɗo daga suma ta zauna ko motsi ta gaza yi sai dai tabi su da ido.

Miƙewa tsaye Sarah Ta yi jikinta kamar zai 6alle, saboda rashin kuzari, fuskarta a bushe muryarta asanyaye ta soma magana”Idan har mu ka cigaba da zama ba tare da mun ɗauki mataki ba, za’a cigaba da yi mana ɗauki ɗai ɗai ne ana kashe mana rayuwa, Yakamata musan abun yi, wlh na tsorota Na firgita da ganin irin mutuwar da Unaiza ta yi, Tare da ita fa aka kawo mu cikin ku, bazan ta6a manta farkon gani na da ita ba, ban ta6a tunanin cewa zan shaida mutuwar ta ba, na girgiza sosai, please na roƙe ku, idan zaku iya ku kashe ni zaifi min kwanciyar hankali akan aƙara zuwa a ɗauki wani acikin mu, saboda na fahimci cewa rayuwar mu bata da amfani awurin su, mutuwa ta zamar mana dole yanzu ma aka fara yinta, bansan wanene next zai mutu ba, bana so na gani shiyasa nake so in mutu…………….” daƙyar ta ƙarasa maganar, saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta, miƙewa tsaye Hannah ta yi, idanuwanta jawur dasu ta soma magana tana fuskantar sauran ƴan uwan nasu da ke a zazzaune ƙasa

“Meyasa har yau Allah bai dube mu ba? Mu ma fa bayinsa ne kamar kowa, Angel ke da kan ki kika faɗa mana cewa wanda ya halicce mu yana sane damu, but why mu ke fuskantar irin wannan tashin hankalin? bawani mai taimakon mu, sau nawa muna hana idon mu bacci don mu kai kukan mu agare shi, amma shiru…!

Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yai ba, jin maganganun da Hanna ke yi, duk da matsanancin halin da ta ke a ciki sai da ta girgiza, ganin sun soma ƙoƙarin kauce hanya, dama ba wadataccen ilmin addini gare su ba, ba lallai bane a yanzu da suka fara fuskantar tashin hankalin nan su iya jurewa ba, saboda suna da raunin imani da tawakkali, a haka ma sunyi ƙoƙari saboda basu ta6a ƙaryata maganar ba, sai dai awannan karan tana tsoron Su juye mata su canza ra’ayinsu.

Runtse idanuwanta ta yi sosai tare da cusa kanta a ƙirjin batul, ba ta yi tsammanin zata samu sauran hawaye a cikin idanuwanta ba, sai gasu sun soma tsastsafowa saman kuncin ta masu ɗumi.

zuciyar batul ba ƙaramin karaya tayi ba, Jin yadda Jikin Angel ya yi zafi sosai, tasan dole taji raɗaɗin a cikin zuciyarta,’ ƙara ƙanƙameta ta yi a jikinta, hannayenta asaman sumar kanta, A hankali take shafa sumar Angel tana lallashinta, zuciyarta tamkar ta fashe saboda ƙunar da ta ke yi mata, gudun kada ta zauce ta rasa madafa, yasa ta soma furta duk wasu addu’o’i da tasan zasu kwantar mata da hankalinta.

A yayin da ta ke yin addu’o’in idanuwanta suna arufe, sosai ta matse su, tana jiyo muryar Yasmin tana faɗin

“Angel Kin yi shiru baki bamu amsa ba, har yaushe ne zamu tsara Jiran taimako daga wurin Allah! Kina ganin mun fara mutuwa, tsoro da firgici kaɗai kaɗai sun isa su sa mu zauce, Mun yi tunanin cewa idan muka kar6i addinin ki, Mu ka yi Imani da Allah, komai zaizo mana da sauƙi, Amma shiru sai ma ƙara shiga tashin hankali da mu ke yi, lokacin da kika zo cikin rayuwar mu Ba ki ji daɗin da mu ka ji ba, saboda alƙawarurrukan da kika ɗaukar mana na cewa Zaki taimaka mana wurin ganin mun ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddarar nan, Ki ka sanya mana kwaɗayin son yin rayuwar ƴan ci kalar wadda ki ka yi awaje, Meyasa angel muke ganin ba dai dai ba? Idan da ace kinsan ba zaki iya taimakon mu ba, meyasa kika sanar damu hakan? Kuma kika bamu labarin rayuwarki har muka sanya rai da yin irinta……..”

Yasmin bata ƙarasa maganar ba, ta rushe da kuka, Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi, Dama fa dole ta fuskanci wannan matsalar, cos itace mutun ta farko data fara sanar dasu komai agame da mahaliccin su, Nauyin komai ya rataya akan wuyanta! Duk idan su ka ji ba daɗi dole ita zasu tunkara, to ayanzu dai mutuwar Unaiza da Majnoon ta kwance notikan kawunansu, sun fara tsorota shiyasa su ke waɗannan maganganun.

“Angel idan har akwai abunda ya rage mana wanda ba mu yi ba dangane da addinin ki, to ki faɗa mana shi don muyi wata’ƙil Allah zai ji ƙanmu ya tausaya mana, ya dube mu da idon rahama ko mun samu mu tsira da ranmu!” Eve ce ta yi maganar, Duk sun mimmiƙe tsaitsaye Agaban Batul da ke a rungume da ita, sai ƙara tighting ɗinta ta ke yi a jikinta, ita kanta batul ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta, cigaba da ambaton sunan Allah ta yi acikin zuciyarta, tana roƙonshi akan ya basu bafita kada yasa su ga gazawarta.

“Angel Mun san kina sauraron mu, kin yi shiru ba ki ce komai ba, kada ki sanya mana kokwanto A cikin zukatan mu, Mun yarda dake, Munsan kina ƙaunarmu, kuma kina son Farin Cikin mu, don haka Muna jiran amsar ki me ya rage mana wanda ba muyi ba a cikin addininmu wanda zaisa Allah ya jiƙan mu……” Cikin rauni na murya Hibba ta yi maganar, daga ganin fuskokin su a matuƙar tsorace suke.

Angel tana a cikin tsaka mai wuya, ta kasa ɗago da idonta ta dube su, saboda bata da ƙwarin gwiwar yi masu magana, to me zata ce masu? Itama fa A tsoroce take da abunda ya faru na mutuwarsu Unaiza.

Muryar Rubina a hargitse tace”Babban abunda nake jimawa, Ƴan uwan mu da aka kwashe Shin suna araye ko sun mutu, bamusan a wani hali su ke aciki ba, Tun da yanzu mun fahimci cewa kashe mu ake yi, Lalata rayuwarmu ake yi a kwashe wani sashe na jikin mu! Kamar yarda aka yi ma Unaiza, Da Majnoon…….” Bugun zuciyar Angel ne ya ƙaru tunawa da Mazan su da aka kwashe, ba ita ba Hatta su Deeja damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Tabbas Suna fuskantar barazana a cikin rayuwarsu.

“baƙin Cikin da mu ke ƙunsa da barazanar da muke fuskanta sun isa su sa zuciyoyin mu su buga mu mutu” Eve ce tayi maganar tana faman huci, idanuwanta a zazzare, ruwan hawaye ne kwance a cikinsu. Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, mutun biyar ne basu tanka ba, sai da su ka yi mai isar su tukunna Deeja ta miƙe cikin kakkausar murya ta soma magana tana duban kowan nan su.

“Na yi mamakin jin maganganun da harsunan ku su ke furtawa, saboda abun da ya faru ne yasa ku ke kokwanto Akan Addinin da Angel tazo mana dashi, Kun bani kunya duk da na fahimci cewa ba’a cikin hayyacin ku kuke ba, banaso mu yi abunda zamuyi danasani acikin rayuwar mu, Angel ba ita bace silar halin da muka shiga ba, Akan me za ku dinga ɗaura mata nauyin komai akanta! Yarinyar nan fa ƙanwar mu ce, babu wanda bai girmeta ba a cikin mu….”

Numfasawa Deeja ta yi a yayin da take bin fuskokin su da kallo.

“Ya ku ke so tayi da ranta ne? Kalaman ku zasu iya sanyawa ta zauce, itama fa tana jin raɗaɗin da mu ke ji, saboda ta ɗaurawa kanta nauyin kula da rayuwar mu, so ku ke ku ƙara sanya mata damuwa har zuciyarta ta buga mu rasa ta? Meyasa za ku yi kokwanto akan addinin da tazo mana dashi? Saboda kun ji shiru har yau Allah bai kawo mana ɗauki ba? Ƙaddarar mu ce tazo a haka, ba lallai bane mu moriya rayuwar duniyar nan ba, amma ku tuna abunda Angel ta faɗa mana, ko kun manta ne, zai iya yiwuwa namu jin daɗin ba anan yake ba, sai ranar da muka koma ga mahaliccin mu! Itafa wannan rayuwar duniyar ƙanƙanuwa ce jin daɗinta na wucin gadi ne, kowa zai mutu ne, damu da wanda ke rayuwa awajen kurkukun nan da waɗanda suka azabtar da rayuwar mu, kaf zamu koma agare shi ne, mutuwa dole ce, zamu mutu zamu koma ga Allah, za’ayi mana hisabi tsakanin mu dasu! Allah zai bi mana haƙƙin mu, zasu ɗanɗani kuɗarsu, Ai mu abun farin ciki ne agare mu, Haƙƙinmu ya rataya akan wuyan waɗanda suke sarrafa rayuwar mu, don haka daga yau bana son wani ya ƙara yin kukan mutuwa acikin mu, Mu sanya wa ranmu cewa dole mu rasa wani acikin mu, ko muna so ko ba mu so, dole mu mutu, Mu zama masu tawakkali kada mu butulce wa Ubangijinmu, Abun da na fahimta wanda ba lallai bane ku fahince shiba, Allah shine ya ƙaddara zuwan Angel a gidan kurkukun nan donta sanar damu komai agame dashi, yanzu mu musulmai ne, kuma munyi imani da Allah, don haka babu gudu babu ja da baya, Duk runtsi duk wuya kada mu kuskura Mu rasa ƙwarin giwar da mu ke da shi, tsakanin mu da Angel sai godiya, Allah ya saka mata alkhairi, Allah ya bata ikon cigaba da taimakon mu….”

Kalaman Deeja sun sanyaya zuciyar Angel, Jikin kowan nan su Ya yi sanyi, sun yi danasanin maganganun da suka soma gaya mata, kusan atare suka haɗa baki suna bata haƙuri haɗi da lallashinta, hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalinta yayi ba, har lokacin bata ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul ba’

Deeja tace masu su share hawayensu, Su yi rayuwar su tamkar babu abunda ya faru dasu, suka masa mata da toh, Duk da sun san abune mai wuya su dawo kamar yarda suke ada, A ranar sun ɗan samu sunci abincin Da Jamimah ta ajiye masu a cikin kwando, Bayan sun kammala ci, Kowan nan su ya yi wanka, A saman gadajen su suka kwakkwanta, zuciyoyin su a ƙuntace.

Rayuwar prisoners ta zama abun tausayi Cikin kwanakin nan, jimamin rashin ƴan uwansu ya hanasu sakat, Babu wasa babu dariya, kullum fuskokin su a bushe su ke, abu ɗaya ne su ke yi su ji daɗin shi, su kuma samu natsuwa da kwanciyar Hankali, Karatun qur’ani da Angel ta ke yi masu tsakar dare, a lokacin da take samun damar yin shi murya abuɗe ba tare da ta samu targarɗa ba, tasha ware kanta ita kaɗai, Ta ke6e a sashen toilet ɗinsu, ta ɗaga hannayenta sama hawaye nabin fuskarta, ta dinga roƙon Allah akan ya taimaka mata, kada yasa taji kunya a idanuwansu, ya agaza masu yajiƙan su, Ya kawo masu mafita ko dan taci ka masu alƙawarin data ɗaukar masu na ku6utar dasu daga Cikin kurkukun ƙaddara!

Ta zama abun tausayi, ga duk mai imani idan yaga yadda ta ke roƙon Allah sai ya matse mata ƙwalla. dukkan wasu ladubban yin addu’a ta iyasu, Saboda an koyar da ita, mutun biyun nan sun bata gudummuwa a cikin rayuwarta, shiyasa bazata ta6a mantawa dasu ba, mutun na farko Mahaifinta Tajuddeen, nagartaccen uba wanda ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, lokacin da Unaiza ta bata labarin nata uban daya tarwatsa rayuwarta, sai taji ta ƙara ƙaunar daddynta, kuma har aranta taji cewa Mahaifinta bazai ta6a iya sadaukar da ita ba, ɗan adam ba abun yarda bane, amma ita ta yarda dashi har cikin ranta, saboda tasan halin daddynta ita shaida ce akan shi, ko dabba bazai Iya sadaukar ba balle ita da ya ɗauke ta tamkar ranshi! Mutum na biyu da bazata ta6a mantawa ba, ANEELERH CE, matsayin da ta bata a cikin zuciyarta na mahaifiyarta ne data gudu tabarta, Aneelerh uwace ta gari agare ta, dayawa wasu abubuwan da Angel ta iya da suka shafi addini da rayuwar duniya, Aneelerh ce ta koyar da ita su, hatta karatun makaranta idan aka yi mata, Aneelerh ce ke ƙara koya mata shi idan daddynta bai nan, Tana matuƙar son aunty aneelerh, kuma bata zarginta cikin waɗanda su ka sadaukar da ita! bayan aunty aneelerh da daddynta babu wani shege da take tunanin zata ɗaga ma ƙafa, muddin ta fita daga cikin kurkukun nan sun shiga uku, Hatta hajiya Adama da uncle Abdallah, da Alhaji ubaid kakanta, da maigadin gidansu, da abokan dadynta na wurin aiki, da makwabtan dake a kusa da gidansu kaf ɗinsu abun zargine awurinta, Ba wanda ta cire a cikinsu, dama kawai take jira ta samu, duk wani mai hannu acikin sadaukar da su, sai ta binciko su, alwashine ta ɗaukarwa kanta, shiyasa bata son ta dawwama agidan kurkukun saboda idan har tana aciki bazata ta6a Iya gano su wanene shuwagabannin kurkukun ba, Dole sai tana awaje zata samu damar gano munafukan, ta ci buri akan su, musamman mahaifin Unaiza JAN WUYA, wannan ɗan tahalikin duk ranar daya bari Angel ta dira ƙafarta daga cikin kurkuku, sunanshi matacce, muddin ta gano shi.

Tuntuni Angel ta ɗauko Jotter ɗin unaiza da ta ajiye mata a cikin toilet ɗinsu, tare da pant ɗin data bata kyauta, tana matuƙar son pant ɗin musamman da ya fito daga hannun Unaiza, yanzu haka pant ɗin yana sanye a jikinta ko wanke shi ba ta yi ba, saboda ta shaida tsaftar da ke a jikin shi, daga gani ranar da za’a kawota kurkukun ta sanya shi a jikinta, saboda sabuntakar shi. a cikin backpact ɗin Unaiza ta sanya jotter ɗin tare da biro din duka ta tura su ciki ta zage zip ɗinta, tana fatan Allah ya bata damar isar da wasiyyarta.

Bayin Allah sun zubama sarautar Allah ido, almost two month Yau, babu labarin su Haris, Danish kuwa yafi kowa daɗewa don Yana acikin wata na uku da aka tafi dashi, tsakaninsu dasu addu’ace wadda ba fashi, kullum ne sai sunyi masu ita tare da waɗan da su ka rasu.

💔PRISONERS💔

Wuraren marece, Angel tana kwance saman gadonta, ta rungume pillow a ƙirjinta, ba zaka ta6a gane awani hali ta ke a ciki ba, ta lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci, Azeeza ce kwance a gefenta saman gadonta, Jamimah tana asaman bayanta ta haye ta ɗaura kanta, sun zamar mata alaƙaƙai, Kullum suna atare da ita, tana matuƙar son jinsu a tare da ita, babu mai yin magana a cikinsu, Parveen tana a kuɗundune cikin bargo saman gadon majnoon, kullum nan take kwana, da hannunta ta wanke jinin da ke abargon shi, ta gyara gadon taci gaba da kwana saman shi, saboda ƙaunar da ta ke yiwa majnoon ɗinta, wani lokacin har pillown shi ta ke yi ma wasa a matsayin majnoon kamar mai ta6in hankali.

Sarah na a zaune saman shimfiɗarta tare da Hibba da eve sai yasmin da rubina, babu mai magana acikin su duk sun yi zugudum, Deeja tana a kwance saman gadon Haris idonta na fuskantar ceilling, kowa dai da abunda ke damun shi, itama Hanna tana a naɗe saman gadonta.

Saukowa batul ta yi daga saman gadonta, Ta nufi sashen toilet ɗinsu, ba tare da kowa Ya ankara da ita ba, shigarta ke da wuya Angel ta buɗe idanuwanta muryarta asanyaye tace da jimamah ta sauka zata miƙe, zame jikinta ta yi daga na jamimah ta sauko daga saman gadon, Jikin ta duk ba ƙwari ga ramar da ta yi.

Sashen toilet ɗinsu ta nufa, tana shiga ta soma jin shessheƙar kukan batul, Hankalinta yai mugun tashi, bata zo da niyar tabi bayanta ba, tunawa da furennin dake a cikin tukunyar fulawar nan ne yasa ta zo sashen makewayin nasu, tun bayan rasuwar Unaiza babu wanda ke ba furennin ruwa saboda halin da su ka shiga, Cikin sanɗa ta nufi ƙopar toilet ɗin da batul ta shiga, A hankali ta tura ƙopar tare da Leƙa kanta ciki, karaf idanuwanta su ka sauka akan Batul da ke ta faman leƙa cikin wandonta da ta zame kamar wani abu ta ke dubawa,

Jin motsin shigowar mutun yasa ta firgice ta ɗago da idanuwanta fuskarta sharkaf da hawaye suna haɗa ido da Angel tasha jinin jikinta, da sauri ta gyara zaman wandon jikin ta.

“Batul me ya ke damun ki? Na jiyo shessheƙar kukan ki ne,” wahalallan yawu ta haɗi, ba tare data furta mata komai ba.

Hakan ba ƙaramin ɗaga ma Angel hankali yai ba, fargabarta kar ace wani abu ne ya sami gabanta shiyasa ta ke kuka

“Ƴar uwata rabin raina, dan Allah ki faɗamin meke damun ki, Na yi maki alƙawarin bazan faɗama kowa ba, Hankalina ya tashi dana ga kina duba wandon Jikin ki, ina tsoron ace wani abu ne ke damun ki”

Ta ƙarasa maganar yayin da take nufar batul, girgiza mata kai ta dinga yi muryarta Ƙasa ƙasa take faɗin”Kada ki matso kusa dani Angel, babu abunda ke damuna, lafiyata qalau…..” adabarbarce ta yi maganar.

“ƙarya ki ke yi min batul! Wai har ni zaki 6oye ma abunda ke damun ki? Me ki ka ɗauke ni ne? Nifa ƴar uwarkice, idan baki faɗamin ba wa zaki faɗa mawa, ni dama tun da aka dawo mana dake ban yarda dake ba, meyasa zaki 6oye min abunda su ka yi maki”? Fuskarta a ɗaure ta yi maganar, kafin taci gaba da cewa”Allah yajiƙan unaiza ba ta mutu ba sai da ta sanar dani komai daya faru da ita, don haka ki daina 6oye min, idan har kina son zaman lafiya to ki faɗamin me aka yi maki!! Cikin shessheƙar kuka batul tace”nifa ba abunda ya faru dani, ki daina tambayata bana so ki tafi kawai,” Jinjina kai Angel tayi tare da sassauta muryarta”Its ok xan tafi batul tun da baki so in sani,” Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi ƙopar fita, ajiyar zuciya batul ta sauke duk a tunaninta Angel tafiya zata yi tabar toilet ɗin ashe ƙopa ta je ta rufe don kada sauti Ya fita, jamlock Ta sanya ta datse ƙopar da kyau, fuskarta a ɗauke ta juyo ta kalli batul dake manne jikin bango, jikinta sai kerma yake yi

“Zaki Faɗamin meke damun ki ko kuwa kin fi so in bi ta ƙarfi”! Shiru batul bata tanka mata ba, sai faman zazzare mata idanuwanta take Yi, Cizon le6e Angel tayi tare da naɗe hannun rigarta, gadan gadan ta nufi batul, ganin tana tunkarota yasa batul ta bar jikin bangon ta watsa da gudu da niyar ta fuce, Cikin rashin sa’a Angel ta cafko Sumar kanta, ta janyota da ƙarfi ta maka ta jikin bango ta yadda bazata ji zafi ba, Faɗane ya kaure a tsakanin su, Sai nishi su ke yi sun cakumi juna, ga jikin nasu duk ba ƙwari, tuni sun haɗa uban gumi, ƙarfi Angel ta sanya wurin kada batul ƙasa, tare da sanya hannu ta damƙi wandon jikinta ta soma kiciniyar zame mata shi daga jikinta, duk don ta gane ma idonta abunda batul ke 6oye mata………”

Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08169856268 ko 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button