Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 6 Hausa Novel

    WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

~Unique Barakancy~

        SIX📍

     Kallon gefe Deen yayi,yaga farar mota a gefenshi,daga ganin glass din motar kasan tint ne amma wani ikon Allah baa zuge glass din ba. Bin wacce ke cikin motar yayi da kallo ganin ta juya gefe,ga niqab a hannunta dake dauke da gloves,hakanan bugun zuciyarsa ya changa,ya farajin irin abinda yakeyi a duk sanda yake kusa da ita,zuciyarsa ce ta cigaba da tabbatar masa da lallai itace,kasa hakuri yayi ya fita daga motar domin ya tabbatarwa kansa dukda be taba ganin fuskarta ba,gabadaya ya manta ma a traffic suke,karasawa yayi yana addu’ar Allah yasa ta juyo kafin ya karasa,kawai sai yaga wayam,harta figi motar ta tafi,chan kuma sai yaji horn na tashi a cikin kunnensa,bin motarta ya cigaba dayi da kallo ko kula da masu horn din bayayi,saida wasu suka fito suna mishi magana sannan absent mindedly yashiga motarshi ya bar wajan………….  

   Driving yake amma gabadaya hankalinshi baya jikinshi,danasani yake meyasa ya koreta daga class ranar daya fara ganinta,dayasani ya kyaleta yaga gudun ruwanta,yaga meta karaso yi,da maybe ya samu damar jin muryarta,kila ko yayi saurin ganeta,dan yanzu bashida abinda yake ganeta dashi illa bugun zuciyarsa ,akwai wani weird bugu da zuciyarsa take masa aduk sanda take wajen da yake,kuma ya yadda da zuciyarsa dari bisa dari bazata masa karya ba,tabbas duk sanda yaji hakan it means tana nan…. Wani tinani ne ya fado masa ya daki steering motar yace “damn it” da karfi sannan ya sake cewa “How was I stupid not to think of going back to that school again,it’s the easiest way for me to locate the damn demon!”……….. Tuno warning din dad yayi yace “I don’t care what the damn old may will say,dole ma inyi accepting new invitation din school dinnan,I need to lecture their class”…….. “Yeah for fun” ya sake fadi yana fashewa da dariya kamar wanda ya zare,sai kuma yaga kamar yana hango motarta a chan nisa,wani over speeding yayi ya bita a guje……..

         Lalubo niqab dinta tayi dukda ba sawa zatayi yanzu,sai ta kai destination dinta,rikeshi ta cigaba dayi tana Allah Allah traffic light ya nuna green,haka take bata da hakuri sam sam,kawai saita farajin footsteps daga gefenta,ko baa fadamata ba tasan meshi is walking towards her,batareda ta jira an basu hannu ba ta taka motar a guje…. Ko zaa kasheta batasan dalilin yin hakan ba,haka kawai taji koma waye bataso su hadu,dama da niqab a fuskarta zata iya tsayawa tayiwa meshi tass,in this case kawai sai taji gwara ta gudu……………..

Kula tayi da ana binta,wani ajiyar zuciya ta sauke ganin me kiranta,picking tayi da sauri cikin muryarta me sanyi tace “Ana bina”….. Murmushi yayi daga dayan barin yace “Yeah I know,kiyi tafiyarki a nitse,I’ll handle that now…….. numfashi ta sauke saita cigaba da driving a nitsen kamar yanda yace mata,dan tasan tabbas zeyi handling komai kamar yadda ya fada……….

         Shiko Deen sai binta yake kamar wanda aka aiko,a bazata yaga wata mota ta tawo kamar zata bugeshi,da sauri ya kauce,unfortunately ya daki wani  gini,a take ya zube akan steering a sume……….

      Cigaba da tafiya tayi a nitse kamar yanda yace,ganin ta dena ganin motar dake binta yasa tayi smiling,a hankali ta furta “weldone man”…… Sannan ta kunna Qur’ani a motar tana cigaba da tafiya a nitse……. 

     Yan gurinne suka taso da sauri ganin motar da tayi causing accident tajuya a guje ta gudu,ba wanda yabi takan motar ganin wanda ke cikin motar data daki gini ko motsi bayayi,gurin maza biyarne suka kakkamasa aka fito dashi da kyar,asibiti aka nufa dashi,ana zuwa ko akayi rushing dinshi emergency….. Sai muce Allah ya bawa Deen lfy……

            

             After a week

        Taku take kamar wata hawainiya,duk inda tabi a airport din binta kawai ake da kallo,sanye take da lifaya me shegen kyau daya zagayeta ya kuma rufe komai na surar jikinta,hannayenta dauke suke da gloves,sannan kafafuwanta na sanye da safa,nose mask ne a fuskarsa,sai wani black shades daya boye idanunta sosai,shi kanshi nadin lifayar ta janyoshi har goshinta yanda ko gashin gaban goshinta baa gani….. Bawai ana kallonta bane dan ana ganin wani abu a jikinta a’a saidan yanayin takunta,taku take komai nata yana kadawa,yanda ko mutum bega fuskarta ba yasan Allah yayi halitta anan,barinma faffadan ugunta da tin daga nesa zaga hangoshi yana juyawa kamar tarwatsa,wani saiya dauka ma da ganga ta keyi,saidai sam ba haka bane,hasalima haka salon takunta yake,komai zakaga yana kadawa,hijab din da take sawa ne ke boye komai…… Aiko duk wanda yazo wucewa ya kalleta sai yace ‘masha Allah’ baga matan ba baga mazan ba,dan tabbas takai a kalleta. Wasuma cewa suke daga gani mijintane ya sata shigarnan dukda basuga fuskarta ba,toh Fisabilillahi ya baze boye kamar wannan ba…….. 

Suna boarding ta mishi text message sannan ta kashe wayarta,lumshe ido tayi tana tinanin manufar tafiyarnan,sai kuma ta fara tinanin irin dagar da suka sha da daddy kafin ya kawo mata visa da ticket,nacewa yayi akan zasu fara exam be kamata tayi tafiya wata kasar ba,kuma yasan tsap zata iya cewa zata biya ta wata kasar,rufe ido tayi tace masa in shi baze mata ba saitasa danshi ya mata dan dole (dukda badan shi zata ba) amma wlh kudinta bazeyi kuka ba,kuma tanada kudin da zata yiwa kanta komai saidai batayi niya ba,da daddy yaga dai ta dage sai taje,kuma yasan yanzu sai Khaleel ya farajin haushinshi akan hakan,yace baya sonshi tinda zai hana abincin ruhinshi zuwa gareshi,kawai sai ya hakura ya mata komai,kafin one week ko visa da ticket din ya fito abunka da masu shi…  Daddy da kansa ya kira khaleel ya sanar masa da zuwanta,dan yasan duk wannan abun da akeyi khaleel be sani ba,daya sani ko da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba,aiko ba karamin farinciki khaleel yayi ba da daddy ya sanar masa da zuwanta…….. 

Chan kuma sai text message din da mama ta mata ya fado mata wai”zaki san koni wacece,in ni bansan ke wacece ba,mu zuba nidake mugani fatima zainab!”….. Sosai message din ya bawa fatima zainab dariya,dan tasan ita she’s unshakable,dubun mama ma sun buga sun barta…. Sai kawai taji wani bacci ya kwasheta,hakan kuma baya rasa nasaba da abinda tasha kafin ta shiga airpot………. 

         Shiryeshirye khaleel yake na gani na fada,duk wanda yaga irin shirin daya keyi sai ya dauka biki zaayi,bazai iya kirga irin kyautar dayayi from three days back da aka mishi breaking good news din zuwa yau ba,ji yayi kamar anyi filling duk wani empty space dake zuciyarsa,wani irin walwala yakeyi naban mamaki,duk wanda yake tare dashi saida ya tambayesa ko yayi winning jackpot ne,dariya kawai yakeyi yace abinda yayi winning ai yafi karfin jackpot. Yadai ki fadawa kowa dalilin farincikinsa sbd yasan in dai ya fada toh ya gama yawo a gurin mutane don kowa cewa zeyi ze ganta,tinda duk wanda yake taredashi yasan itace damurwarsa da farincikinsa,shiko da wani ya gane masa ita gwara Allah ya dau ransa kawai dan ya dade yana sanarwa kansa danshi aka halicceta,haka itama dan ita aka haliccesa,shiyasa yake kap kap da duk wani abu daya shafeta…. Wani abinda yake hura masa hutar abinda yakeji gama da ita shine yayi believing duk wanda yaganta will definitely fall for her shiyasa yake boye ta sosai,inda Allah ya taimakesa kuma itama tana tayasa boye kanta,dukda bata taba cemasa danshi takeyi ba amma ko kokwanto bayayi saboda shine…..Har spa saida yaje aka gyara mishi fuska da komai ma,kada ma coily hair dinshi yaji labari……

            A hankali take nufar exit din arrival hall din,nan ma kamar Nigeria sai binta ake da kallo,sai kuma kallon yazama biyu ganin yadda baa ganin komai na jikinta ,har wasu sunfara tinanin ko criminal ce,alerting securities din akayi da su kamata,suka ko nufota da sauri da niyar zagaye ta,sai kuma suka kasa karasowa kamar wanda aka daure,itako bata masan sunayi ba harta fice daga airport din……..

Nufoshi tayi ganin sai juye juye yake kuma ya kasa ganinta.Kokarin hugging dinta yayi kuma sai yaja ya tsaya yana binta da kallo,sai chan kuma ya daki kumatunshi yace “Ya rabb if I’m dreaming don’t wake me up,wifey is that you”…. Cikin muryar sabon baccin da takeji tace “I’m exhausted!”………. “Sorry wifey,you’re highly welcome,words enough can’t express how excited I am to see you,can’t wait to take off those masks and see you vividly,you may enter the ride”…. Yayi bowing kamar yanda akeyiwa sarakuna sannan ya bude mata motar…. Shiga tayi batace komai ba,yana jan motar ko ta cigaba da bacci………..,,,

      Sakkowa yayi ya zagaya side din da take,ya bude murfin motar,sunkuyowa yayi ya shiga binta da kallo,undressing her with his eyes,bacci take hankali kwance,kuma ko kaffara baze yiba wani abu tasha,ya rasa ya zaiyi da ita akan shan abunnan amma kullum  saidai yata fadawa kansa ‘there’s time’,da zaran sunyi aure zeyi exploring dinta to something very sweeeter than what she’s taking,saita gane shayeshayenma bashida dadi………..

       “Alhamdulillahil-lazee ahyaanaa ba’ada ma amaa tanaa wa ilayhin-nushoor” ya jiyota tana fadin hakan chanchan kasa,badanma ya sunkuyo kanta sosai baze jiba,da sauri ya janye daga jikinta jin tana addu’ar tashi daga bacci,mamakinta na kara kasheshi,she’s just an absolute definition of ‘ustaziya ko yar duniya?’,akwai fadin Allah a baki kamar me,meanwhile in tayi wani abun ko wanda be taba zuwa islamiyya bazeyiba,gata kuma mahaddaciyar alqur’ani amma fa saita yini tanajin waka chan kuma sai kaji ankoma qur’ani,in akwai abinda ze shede ta dashi kuma shine ibada,kome tasha zata tashi tayi sallah a ko wani yanayi kuwa,sam bata fashin azkar da zikirin safe,ga nafilfili kamar me,saita raba dare akan sallaya hakan kuma bazesa taki shan abinda ze bugar da ita ba……. She’s just bipolar,sam baka gane kanta,in kace zaka shedeta yanzu saita baka kunya,in  kamata shedar banza kuma saita baka mamaki yanzu,shiyasa tintini yawa kanshi fada ya kuma hakura da san sanin “WACECE ITA”………..

           Phillimore Gardens Street unguwa ce me shegen kyau a UK,sannan sai wane da wane ke zama a cikinta,ko wani gida a unguwar haka zaka sameshi hadadde kamar bazaa mutu ba,haka ‘2 story cottage house’ din khaleel keda bala’in kyau,ba wani me girma bane amma tin daga wajan gidan abin kallo ne balle akaiga cikin………. Karasawa ciki sukayi sai gasu a wani hadadden parlourn da kyauwunsa ma baze faduba,wasu hadaddun flowers masu shegen kamshi ne suka fara zubowa akan Fatima Zainab wanda suka sata wassakewar dole,sai kuma ta hango wani designed  ‘I love you wifey’ glitters me daukan ido da aka manna a jikin bango,sai abun kuma ya fara voicing I love you wifey,ga wani katon table da aka cikashi da duk wani nau’in kayan ciyeciye irinsu cakes da akasa different sweet names a jiki,su chocolate boxes,frames,gold jewelries and many more. In takaice muku dai babu wani abun more rayuwa dana jin dadi da babu a table dinnan…….     

      Indai a gurin khaleel ne tasaba ganin fiyeda haka so batayi wani mamaki ba,juyowa tayi tana cire nose mask da shades dinta,tana duba ta ina zata ganshi,hangoshi tayi rike da guitar a hannu,while he stares at her like his life depend on it,dauke kai tayi ganin ya fara miming favorite wakarshi na tems titled ‘higher’,duk sanda suka hadu baya gajiya da mata wakar,da tayi complain kuma yace it’s just for affirmation……….. 

‘If the world was ending,would you cry or try to get me?’

‘Tell me now I want you to be clear,yeah’. 

‘Tell me now I need you to be clear,yeah’

‘I will wait for you,for you’

‘I will wait for you’

    A hankali taji kamar ana zare mata wani abu a jiki,this is the reason bataso yana mata wakarnan,har cikin jikinta takeji,ji take kamar yana hitting soft botton nata,dan smiling tayi sannan ta haura sama……….

    Bin takunta yayi da kallo yana admiring every step nata,ko bata ce komai ba yasan wakar na tabata,gane effect din da wakar kedashi akanta ne yasa yake mata duk sanda suka hadu….. Zama yayi a parlourn yana tinaninta kamar ba yanzu tabar gurin ba,jiran fitowarta ya shigayi yasan she went to freshen up and pray……… A hankali shedan ya fara kitsa masa wani abu,da kuma kwadaita masa da yayi amfani da damarsa ganin yanda tayi laushi sosai,atleast he has waited for long,Afterall shine ze aureta,kuma kilama abun yayi triggering yin aurensu da wurwuri,kokarin yakice abun ya shigayi amma ina zuciyarsa ta fara rinjayarsa,haka shedan yacigaba da kunnashi,hutar abinda yakeji game da ita na kara huruwa,tashi yayi ya shiga wani bedroom dake kasa inda friend dinshi sameer ke kwana idan yazo sleepover ,if he can recall a bedside drawern dakin ya taba ganin drugs din,harya karanta content din yana mamakin me sameer keyi dashi,amma be tambayeshi ba,dauka yayi yanajin dadin ganin liquid ne,for “easy dilution” Ya fada yana smirking …. Fitowa parlour yayi yana kalle kalle gudun karta fito ta kamashi,ganin ko alamarta babu yasa ya nufi kitchen,bude fridge yayi ya dauko chilled Greek yoghurt sannan ya juye duka arousal drug din a ciki,ya jijjiga sosai ya tabbatar yayi diluting sosai sannan ya rufe,yana sane yasa a yoghurt saboda yasan ko baza tasha komai ba zatasha yoghurt din….. Dawowa parlour yayi ya zauna yana dokin fitowarta………

           A yangance take takowa sanya da hijab har kasa da sabon handgloves da safar datasa,kyakkyawar fuskarta ce kawai a bude,karasowa tayi ta zauna a kujerar dake facing dinshi,kallonshi tayi da lumsassun idanunta masu daukan ido,sannan tabi kayan dake table din da kallo ta tabe baki tace“I can only take yoghurt”….. Zuciyarsa har wani tsallen murna ta dingayi dukda yayi expecting hakan,kwata kwata yasan dama she’s not a foodie…….. Da sauri ya mike ya shiga kitchen,bude fridge yayi ya dauko yoghurt din dayayi isolating saboda ma karsu hade da sauran,ya hado da glass cup sannan ya fito. Yi yayi kamar a lokacin yake budewa,bayan a bude yake,zuba mata yayi cikin glass cup sannan ya mika mata,karba tayi ta kafa kai tashanye saboda wani yunwa dake taso mata,sai kuma ta dago ta kalleshi,saida gabanshi ya fadi abunka da mara gaskiya,dauke kai tayi daga kallonshi sannan tace ya kara mata jin yanda yoghurt din yamata wani extra ordinary dadi,kara mata ko ya sakeyi yanajin wani nishadi a ransa,ji yake kamarma anyi angama…… Haka ta dinga sashi yana kara mata har ta shanye robar tass sannan ta hakura……. Kamar a mafarki taji idonta na rufewa sannan system din jikinta na chanjawa…………

   

 Toh jamaa gadai khaleel na shirin yin abinda zeyi triggering marriage dinsu da wuriwuri shida Fatima Zainab🌚….. Alamu kuma sun nuna ta hau network itama🌚….. 

Ina labarin Deen toh,ko ya mutu ma?🌚…..

 Toh mu hadu a next page for all this🚶‍♀️

Unique Barakancy Ce😁

Back to top button