Uncategorized

Tsatsuba Book 6 Littafin Yaki Na Abdulaziz Sank M/Gini

 

Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.

   

TSATSUBA

Littafi Na Shida (6)

Part A.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Lokacin da sarki Hulbasu ya zo nan a zancensa sai Hailur ya jinjina kai gami da yin murmushi sannan ya tattara hankalinsa gaba daya kan sarki hulbasu yace ina saurarenku yakai abokina , koda jin wannan batu.sai shima sarki Hulbasu ya mayar masa da martanin murmushin da yayi masa sannan ya fara bashi labarin kamar haka….

”KIMANIN SHEKARU GOMA SHA DAYA DA SUKA SHUDE, Sa adda satki shardas ke nahiyar nan yana cinsu da yaki sai ya zama dodon maza kuma ki gudu sa gudu domin kuwa duk kasar da ya durfafa sai ya sami nasara akanta, a wannan lokaci mahaifina ne akan karagar mulki ni kuwa nine sarkin yakinsa, kuma nine kadai dansa a duniya kuma nima dana guda daya ne tal a duniya wato YARIMA HUZEIN.

.

Lokacin da labari ya riski mahaifina cewar sarki shardas yaci kasashe guda ashirin da daya da yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi da farko yayi shiri ya dauki matakin yin yaki da sarki shardas don har ya bami umarni na tara gaba dayan mayakanmu mu tanadi abinci da kayan yaki da nufin mu yi riga kafi muje mu tari sarki shardas da yaki tun gabanin yazo ya yakemu amma sai wani tunani ya zo masa ya dakatar da fita yakin yayi shiri ya tafi izuwa gidan wani mashahurin boka wanda ake kira ZAMARANU IBINI KALBIYA,, boka zamaranu na zaune a cikin wani daji ne dake gabam iyakar wannan birni namu kuma masana tarihi da bincike sun tabbatar da cewar boka zamaranu yafi shekara dari zaune a ciki wannan daji shi kadai, babu wanda yasan abinda yake yi a cikin dajin ko kuma dalilin zamansa amma dai an tabbatar da cewar da shi da bukkar da yake zaune a cikinta kwai rana guda aka gansu sun wanzu ba a san mafarinsu ba, mahaifina Ya durfafi dajin DANYUL shi kadai kai tsaye ba tare da fargabar komai ba alhalin tsawon bayyanar boka zamaranu a dajin babu wani mahaluki daya sake shigarsa walau MUTUM KO ALJAN ba don komai ba kuwa face sai don mugayen bakaken aljanun dake cikinsa, AA Misau Sunana, Komai gawurtar ayari na fatake basa iya ratsa dajin duk tsautsayin da ya sa suka shiga kuwa shi ke nan sun bata har abada ba za a sake jin duriyarsu na a tsawon shekara dari da baiyanar boka zamaranu a cikin dajin Danyul fatake ko yan fashi ba sa sake shigarsa ba, don haka nema ake yiwa dajin lakani da BIRNIN FATALWA.

.

Duk da sanin tsananin hadarin dake cikin wannan dajin haka mahaifina ya kunna kai cikinsa, kai da ganin yanayin fuskar mahaifina a lokacin da yake tafiya bisa dokinsa a cikin dajin ka san cewa babu batun tsoron mutuwa a ransa, in da ma mutuwar zata zo masa to zai marhaban da ita

ai kuwa tunda ya shigo cikin dajin ya rinka yin arba da wadansu irin mugayen bakaken aljanu masu tsananin muni da ban tsoro, duk sa adda wadannan mugayen aljanu ska tasamma mahaiina da nufin su dasa masa wawa sai su ga ko gezau baiyi ba alhalin duk bil adaman da yayi arba dasu take yake zaucewa ko sumewa haka dai Aljanin suka yi ta kokarin firgita mahaifina da razanashi amma ko kadan yaki razana wani lokacin ma sai yayi kamar bai gansu ba ko baijisu ba, sai da ya shafe kwana tara yana tafiya kuma baya yarda ya yada zango a ko ina ko barci zaiyi akan dokinsa yake yi, kuma a tsawon kwana taran.baiyi bawali ba ko bayan gida, kuma baya tsayawa da tafiya face idan dokin nasa ya gaji

ya tsaya don kansa yana hutawa, a ranar kwana na tara ne ya iso kofar bukkar boka zamaranu wacce ke tsakiyar dokar dajin Danyul.

++  ++

ACAN BIRNIN ASKANDARIYYA KUWA, hankalina dana yan majalisar sarki ya dugunzuma ainun, domin mun nemi sarki sama da kasa a cikin birnin nan mun rasa babu wanda ya san cewa ya tafi izuwa dajin Danyul, Ashe cikin tsakiyar dare ya sulale ya fice daga cikin birnin ta hanyar batar da kamanninsa.

++  ++

MAHAIFINA NA isa can kofar bukkar boka zamaranu sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak ! Kafin ya sauko daga kan dokin nasa ne yaji an  da dariya kuma sai yaji sautin dariyar yana fitowa daga kowanne bangare wato gabas da yamma, kudu da arewa sarki ya leka cikin wannan bukka sai yaga wayam babu kowa a ciki kawai sai yaji an dafa kafadarsa ta baya, a firgice  ya juya da sauri yayi arba da abinda ya dafa kafadarsa boka zamaranu ne!

.

Boka zamaranu ya kasance dogon mutum kuma siriri mai kwala kwalan idanuwa kunnuwansa wasu iri ne kamar ba na mutum ba domin a tsaye suke tamkar na zomo yana da tarin gashin girar ido mai kauri da tsawo kuma yana da dogon hanci tamkar alkalami, Gaba daya gashin kansa gemunsa da sajensa fari ne saboda tsufa

ga masana ilimin karanta shekarun dan adam ta hanyar lura da yanayinsa za su iya bashi shekaru dari biyu da yaya na haihuwarsa, domin gaba daya fatar jikinsa ma ta yankwane ta bushe kai kace ma ba mutum bane.

.

Siffofinsa gaba daya sun juye sun zama abin tsoro koda

sarki yayi arba da boka zamaranu sai yaja da baya a tsorace a karon farko tunda ya shigo cikin dajin Danyul,

koda ganin haka sai boka zamaranu ya sake bushewa da dariya a karo na biyu yace haba yakai sarki mai birnin askandariyya akan wani dalili Zakaji tsorona alhalin ka wuce abubuwan tsoro sama da guda dubu a baya wadanda suka fini firgitarwa?

.

Ka sani cewa kaine kadai mahalukin da ya ratso wannan daji ya iso har nan a raye tsawon shekara dari da suka gabata kuma kaima din bawai jarumtakarka ko sihirinka bane suka kwaceka ba face cire tsoron da kayi a cikin ranka rashin tsoro a cikin zuciyar mutum shine sirrin shigowa cikin wannan daji na Danyul har mutum ya cimma burin da yake dashi  dashi acikin dajin ba tare da ya hallaka ba, shin zaka iya gaya mini dalilin da ya saka siyar da ranka ka shigo wannan daji alhalin ga mutanenka can sunyi shirin yin yaki da sarki shardas ?

.

Lokacin da boka zamaranu yazo nan a zancensa sai sarki yayi ajiyar zuciya ya kasa cewa komai domin a sannan ne yaji bawali ya matse shi kuma wata irin azababbiyar yunwa da kishirwa sun kamashi, saboda dama tun a kwana na takwas da tahowarsa dajin danyul guzurinsa ya kare, da yunwa da kishirwa ya kwana.

.

Kwatsam! Sai sarki yaji boka zamaranu ya sake bushewa da dariya sannan yayi nuni da cikin bukkar sa yace da sarki sauko daga kan dokinka ka shiga cikin bukkata ka kawar da bukatarka duk abinda kake so zaka samu a ciki koda jin wannan batu sai sarki ya sauko daga kan dokin nasa da sauri ya ruga izuwa cikin bukkar.

.

Yana shiga sai kansa ya juye ya firgita ainun domin ba a dakin bukka ya tsinci kansa ba, cikin wata makekiyar fada ya tsinci kansa wacce ta kawatu ainun fice da tasa

take kofar wani makewayi ta bayyana tare da bude kanta

ba tare da wata fargabar komai ba sarki ya ruga izuwa ciikinta ya kawar da bukatarsa, yana fitowa daga cikin kewayen kuma saiga Abinci da abin sha iri-iri akan wani dogon tebur na alfarma sarki ya karasa kan wannan tebur jikinsa na tsuma zuciyarsa cike da tunani da mamaki domin sa adda ya shigo fadar babu wannan teburi bare abincin dake kansa ba tare da fargabar komai ba mahaifina ya zauna yaci gaba da sha sai da yayi gyatsa mai nuni da alamar Ya koshi faruwar hakan keda wuya sai boka zamaranu ya baiyyana tsulum a gabansa yace yauwa tun da yanzu ka sami nutsuwa saika bani amsar tambayata ?

.

Mahaifina yayi gyaran murya yace yakai wannan boka mai daraja kayi sani cewa ba komai ne ya sa na sai da raina na shigo cikin wannan daji ba alhalin na san cewa duk wanda ya shigeshi sai ya mutu face sai domin gudun kada nayi garaje na zuwa yakar sarki shardas saboda masu iya magana sunce mai laya ya kiyaye mai zamani

.

A iya sanina ban taba ganin sarkin da ya yaki kasashe ashirin da daya ba a wannan nahiya tamu har ya sami nasara a kansu face sarki shardas duk da na san cewa a nahiyar nan tamu kaf babu wata kasa mai yawan dakarun yakina, amma duk da hakan sai da zuciyata ta buga kuma tsoro ya darsu a cikin raina bisa al amarin sarki shardas, naji daga bakin bokaye da yawa cewa kaine kadai zaka iya gaya mini wani abu akan sarki shardas bisa wannan daliline yasa nazo gareka domin ka sanar dani shin idan nayi yaki da sarki shardas zan samu nasara a kansa? Baya ga wannan ina so nayi maka wata tambaya  guda daya ? Tambayar kuwa itace wai shin menene ya zaunar dakai a cikin wannan daji har tsawon shekaru dari ??

.

Lokacin da boka zamaranu yaji wadannan tambayoyi sai yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa kamar ba zai ce komai ba, daga can kuma sai ya dago kansa ya dubi mahaifina cikin nutuwa yace yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wani jarumi ko matsafi daga jinsin MUTUM KO ALJAN wanda zai iya kashe sarki shardas a  yanzu domin kuwa yana kan sharafinsa ne kuma zamaninsa ne, ina tabbatar maka da cewa idan har ka ce zaka yakeshi sai gaba dayan dakarunka sun kare, kuma sai ya shigo har cikin birninka ya yi maka KISAN GILLA idan kana son ka tsira daga sharrinsa sai dai ka shirya masa kyauta ta dukiya da bayi mai yawa ka aika masa kuma ka tambayeshi duk abinda yake bukata daga gareka domin kai da jama arka ku zauna lafiya, dangane da tambayar dakayi mini kuwa ta karshe amsar tambayar ka itace yau shekarata dubu biyu ina jiran zuwan ranar da wata hula zata bayyana wacce ake kira da suna HULAR LAMSARA Zamana a cikin wannan daji ba na komai bane face na binciken gano inda hular lamsara take da kuma yadda zan iya mallakarta amma har yanzu na kasa gano hakan sa adda boka zamaranu yazo nan a zancensa sai mamaki ya kara kama mahaifina yace, yakai wannan boka mai daraja da abin al ajabi an ce shekaranka dari a cikin wannan daji kuma gashi a yanzu da bakinka ka gaya mini cewa yanzu shekararka dubu biyu kana jiran bayyanar hular lamsara to waishin anya kuwa kai mutum ne ?

.

Ko a a zamanin baya sosai na kakannin kakanninmu mutane basa yin shekaru dubu biyu a doron kasa, sannan kuma ita wannan hula ta lamsara yaushe ne za ta bayyana kuma me kake so kayi da ita da har ka shafe shekaru dari a cikin wannan daji saboda ita?

.

Koda jin wannan tambayoyi sai boka zamaranu ya bushe da dariya mai karfi har Dariyar ta kama amsa kuwwa ta cika fadar gaba daya, mahaifina yaji kamar kunnuwansa zasu dode ba shiri ya sa hannayansa ya toshe kunnuwan nasa har sai da ya daina dariyar sannan ya dago ya kalleshi, boka zamaranu ya mike tsaye yayi tafiyar taku biyar sannan ya juyo ya fuskanci sarki yace ni mutum ne kamar kai ba aljan ba amma na fito daga cikin mutanen da suka fi kowanne kabila dadewa a duniya domin a yanzu haka da kake ganina shekarun haihuwata sun kai dubu biyu da dari hudu da arba’in, nine kadai mutum da ya rage a duniya daga cikin jinsinmu kuma nine kadai na san sirrin kayan yakin MAZAN JIYA guda hudu makaman yakin da babu kamarsu a duk fadin wannan duniyar gaba daya, idan na mallaki hular lamsara sai na mallaki duniyar nan gaba dayanta, kuma a sannan ne kadai zan iya yin aure har na haifi irina wanda a gaba zaiyi shekara dubu takwas yana mulkin duniya Jikana kuma zai karbi karagar a hannunsa ya ninka shekarunsa haka dai zuri ata zata ci gaba da mulkin duniya har abada ba zan taba cika wannan burin nawa ba face na mallaki hular lamsara yakai wannan sarki kayi sani cewa babu wanda zai iya hallaka sarki shardas face wanda ya fara mallakar wannan hular ta lamsara, da wannan furuci nake yi maka bankwana kuma ina mai shawartarka daka gaggauta barin dajin nan  ka koma izuwa ga kasarka domin idan ka kara dakika arba in anan zaka iya rasa rayuwarka duk amsar da baka ji ba daga tambayoyinka ba zan iya sanar dakai bane gama fadin hakan keda wuya sai boka zamaranu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen, koda ganin haka sai mahaifina ya mike zumbur ya fice da gudu daga cikin fadar sai gashi ya bayyana a gaban wannan bukka a dimauce ya karasa inda dokinsa yake ya daka tsalle ya haye kansa sannan ya sakar masa linzami ya kama gudu ba sassauci sai da mahaifina ya sake shafe kwana tara yana tafiya sannan ya dawo gida, yana isowa ya bayar da umarnin a janye batun yaki nan take aka sallami kowa mayakan suka koma izuwa ga gidajensu tare da kwance damarar yakin da suka daura suna cike da dumbin mamakin dalilin da ya sa aka fasa zuwa yakin, kashe gari kuwa, da sassafe sarki ya tashi ayari na dakaru dubu uku dauke da bayi dubu ashirin da kuma dukiya mai dumbin yawa ta dinare, lu’u lu’u da murjani cikin akwati dubu suka tafi izuwa ga birnin sarki shardas da kuma wasika.

.

Lokacin da wannan ayari suka riski sarki shardas yaga dukiyar da mahaifina ya aiko masa kuma ya karanta wasikarsa wacce ke nuna mubaya a gami da neman zaman lafiya sai ya bushe da dariyar mugunta sannan yace’ tabbas na cika zaki uban dawa a wannan nahiya kuma dole ne sarakuna su durkusa a gabana su nemi tsira da jaddada muba ya arsu gareni nan take sarki shardas ya sa aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da ita bayanin dake cikin wasikar shine kamar haka………..

Danjin wani bayani ne sarki shardas ya aiko sai ku tarbeni a Post na gobe ehem Dafatan wannan labarin yana kayatar daku Idan hakane kawai ku sauke mun comments dinku gami da likes kafinnan Nidinne Dai Abubakar Saleh AlQuyraemey.

TSATSUBA

Littafi Na Shida (6)

Part B.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Nan take sarki Shardas ya aka rubuto amsar wasikar mahaifina aka maido masa da ita, bayanin dake cikin wasikar shine…

Yakai mai birnin askandariyya kayi sani cewa sakonka

na bayi da dukiya ya riskemu, kuma mun gode da wannan karramawa da kayi mana gami da mubaya’a, amma ka sani cewa ba mu karbi mubaya’arka ba har saika zo da kanka fadata ka zube kasa a gabana ka kwashi gaisuwa sannan zamu aminta da mubaya’arka a garemu, sharadi na biyu kuma shine dole ne duk shekara ka rinka kawo mini irin wannan kyauta daka kawo mini ta bayi dubu ashirin da dukiya akwati dubu sharadi na uku shine dolene ka baiwa wakilina matsayi da mazauni a kasarka domin su dinga kawo mini rahoto duk abin dake gudana a cikin birninka da kauyukan kasarka, sako daga sarki mai cikakken iko kuma sarki dodon maza gallabar sarakuna sarki shardas.

**   **

Lokacin da wannan wasika ta riski mahaifina aka karanta a tsakiyar fada sai hankalin kowa ya dugunzuma ni kuwa sai raina ya baci jikina ya kama tsuma, cikin tsananin fishi na mike tsaye ina mai zare takobina na dubi sarki nace yakai abbana kayi sani cewa idan muka bi wannan sharadi na sarki tamkar mun zamo bayin sane domin zamu rike masa saniyar tatsa ne ya rinka tatsar nononta zamu zamo bamu da wani sirri na kanmu a cikin kasarmu kuma tattalin arzikin mu zai raunana mutanenmu zasu iya fuskantar fatara da talauci kafin na gama rufe bakina tuni sarki ya daka min tsawa yana mai tarar numfashina ya ce, idan muka ki bin umarnin sarki shardas sai ya kashe kowa a kasar nan ya mallake komai namu idan mukace zamu yakeshi komai yawan nan namu sai ya karar damu saboda yana kan sharafinsa abin da boka zamaranu ya gaya mini kenan.

.

A matsayinka na dana kuma yarima mai jiran gado ya kamata ka zamo mai kishin kasarka da jama arka, abinda sarki shardas ke bukata kawai shine na kaskanta kaina a gareshi kuma mu bashi dukiya kada ka dubi matsayina da kimata a wannan nahiya, zan iya sallama rayuwata ma gaba daya don kare jama ata da kasata dukiya kuwa shirme ce idan ka rasata zaka iya samun wata, ina mai dada ja maka kunne babu batun yaki tsakaninmu da sarki shardas kuma kada ka kuskura ka yi wani abu wanda zai jefa kasarmu ko jama armu cikin hadari ina mai umartarka da ma za kaje kasa a shirya mana tafiya gobe gobe zamu durfafi birnin sarki shardas don amsa kiransa, kuma dakarun da zasu yi mana rakiya kada su wuce su dari biyu don samun kariyar hanya daga sharrin yan fashi da dabbobin daji, koda gama fadin hakan sai sarki ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya shige cikin gidan sarautarsa, ni kuwa sai bakin ciki ya lullube ni na sunkui da kaina kasa a lokacin da idanuna suka ciko da kwallar takaici a wannan lokaci ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa aka barni ni kadai a zaune babban abin da ya kona zuciyata shine idan na tuna cewa mahaifina zaije gaban sarki shardas ya durkusa masa alhali a nahiyar mu gaba daya babu wata masarauta mai tsohon tarihi da daukaka sama da tamu idan har sarki ya durkusawa sarki shardas shikenan darajarsa da kwarjininsa a idanun jama a sun zube har abada kuma ba za su kara dawowa ba.

.

Ina zaune cikin wannan halina bakin ciki dana yarima huzein ya zo gareni ya dafa kafadata koda na dago kai nayi arba dashi sai naga shima yana zubar da hawaye, cikin sanyin murya huzein ya dubeni yace yakai abbana

ka zamo mai hakuri da juriya bisa wannan kaddara data same mu ina so ka sani cewa komai nisan jifa kasa zai fado don haka komai dadewa akwai ranar da sarki shardas zai fadi duk wulakancin da zamu fuskanta daga gareshi yanzu yana da iyaka wataran sai labari, ina mai tabbatar maka da cewa idan sarki shardas ya kuntata mana a yanzu da zamaninka to nan gaba namu zamanin

sai komai ya sauya sa adda huzein yazo nan a zancensa sai na cika da mamaki bisa dalilin yin wannan jawabi tamkar wanda ya jiyo wani abu daga wajen bokaye nan take na rungume huzein iana kuka nace yakai dana zan kasance mai fatan ganin ranar da sarki shardas zai fadi

kafin mutuwata.

.

Koda jin wannan batu sai huzein ya janye jikinsa daga cikin nawa ya dubeni cikin murna da murmushi yace yakai abbana ina neman alfarma guda daya a wajenka cikin mamaki  na dubeshi nace yakai dana kai kuwa wacce irin alfarma kake nema a wajena? 

.

Huzein yace ina son kuyi wannan tafiya tare dani gobe zuwa birnin sarki shardas, koda jin haka sai idanuna suka zazzaro na dubeshi cikin alamun damuwa nace haba yakai dana ka tuna cewa idan sarki baya nan

nima bana nan kuma babu kai babu wanda zai gajemu kenan koda tsautsayi yasa mun hallaka wannan tafiya da zamuyi mai hadari ce komai zai iya faruwa a garemu ko akan hanya ko kuma a can birnin sarki shardas, bugu da kari a halin yanzu mahaifiyarka na dauke da tsohon juna biyu haihuwarta yau ko gobe idan babu ni babu kai a kusa da ita wa zata kalla taji dadi?

.

Sa adda yarima huzin yaji wannan batu nawa sai jikinsa yayi sanyi amma duk da haka sai yaci gaba da rokona akan na Rarrashi sarki ya amince ayi wannan tafiya tare dashi, muna cikin wannan hali ne muka ji takun sawu a bayanmu cikin sauri muka waiga mukayi arba dashi, ba wani bane face mahaifina fuskarsa cike da annuri kawai sai ya karaso garemu ya zauna a tsakiyarmu sarki ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yayi murmushi yace naji duk abinda kuka tattauna, kuma na amince zamu tafi tare dakai gobe koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube yarima huzein ya rungume sarki yana mai sumbatar goshinsa kawai sai sarki ya janye jikinsa daga cikin na huzein ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace yakai jikana kayi sani cewa na amince muyi wannan tafiya tare dakai ne saboda dalili daya rak dalilin kuwa shine nima sa adda na taso a wannan gidan sarauta daga san da aka haifeni zuwa lokacin dana kai shekarunka wato shekaru bakwai a duniya sau daya rak aka taba barina na fita wajen birnin na, bai kamata ace yarima guda wanda zai mulki al umma da yawa ba ya kasance kifin rijiya yana da kyau ka shiga duniya kaga yadda talakawa ke rayuwa kuma kayi gwagwarmaya kasha wahala sosai domin ka san menene rayuwa amma ka sani cewa akwai sharadi guda uku a kanka daga ranar da muka fita daga cikin garin nan,

sharadina farko shine ba ka da ikon zuwa ko ina walau a cikin daji ko a cikin gari face da izinina ko na mahaifina sharadi na biyu shine duk abinda zakayi saika shawarcemu sharadi na uku kuwa shine ba zaka ci ko ka sha wani abu ba face wanda muka baka da hannunmu, shin ka amince da wannan sharadai guda uku.

.

Ko dajin wannan tambaya sai yarima huzein yayi murmushi kuma ya zube kasa a gaban sarki ya kama godiya cikin farin ciki tare da tabbatar da amincewarsa

ga wadannan sharudda.

.

Kashe gari kuwa da sassafe aka yi shirin tafiya dakaru dari biyu ne suka yi mana rakiya dauke da isashshen guzuri sai kuma kuyangi goma wadanda za su rinka yi mana hidima tsakanin yan fashi da mugayen dabbobin daji sai da mukayi karo da rukuni rukuni har guda bakwai kafin mu isa birnin sarki shardas amma sai da muka tarwatsa su muka kashe na kashewa masu gudu suka tsere dakaru guda arba in kacal muka rasa a cikin wannan gumurzu da la asar sakaliya muka iso birnin sarki shardas koda muka tsaya a bakin kofar gidan sarautar akaje akayi mana iso sai sarki shardas yaki fitowa saboda jin izzarsa da takamarsa kawai sai ya turo wani hadiminsa aka kaimu masauki bayan mun zauna munci abinci muna hutawa sai tunanin gida ya fado min inda na tuno lokacin da muke yin bankwana da matata luzuraina wacce ke dauke da tsohon juna biyu.

.

Sa dda ta rungumeni mu biyu ni da yarima huzein ta fashe da kuka tana mai cewa yakai mijina kayi sani cewa bana son wannan tafiya da zakuyi domin ina bukatarku a kusa dani a yanzu fiye da ko yaushe ba don komai ba sai don saboda ita haihuwa bata da tabbas zan iya rasa rayuwata a wannan tafarki ko kuma na rasa abinda na ke dauke dashi haka zan iya rasaku tunda kuma tafiya zakuyi mai hadari tun a jiya da sarki ya shirya wannan tafiya sai naji zuciyata ta kama bugawa yadda naga rana haka naga dare ina mai tabbatar muku da cewa ba zan taba samun sukuni da kwanciyar hankali ba face naga dawowarku lafiya, koda luzuraina ta zo nan a zancenta sai ni da huzein muka kamu da tsananin tausayinta muka kara kankameta a jikinmu mukaci gaba da kuka kamar ba zamu daina ba, daga can sai na janye jikina daga cikin nasu na dubi luzuraina cikin nutsuwa da murmushin karfin hali nace yake matata kiyi sani cewa bana son nayi wannan tafiya saboda rashin sanin halin da zaki iya shiga amma kuma idan har na bar sarki yayi wannan tafiya shi kadai zan shiga cikin tashin hankali da wasi wasi akan halin da shima zai iya shiga don haka dole ne na bishi ko don na bashi kariya ina son ki kwantar da hankalinki ki sani cewa nayi miki alkawari duk wuya duk tsananin sai na dawo gareki a raye kuma na dawo miki da yarima huzein cikin koshin lafiya gama fadin hakan keda wuya sai ga babban hadimina ya shigo cikin falon nawa ya risina gareni yace ya shugabana sarki ya fto ku kadai ake jira.

.

Koda jin haka sai ni da yarima huzein muka mike tsaye da sauri muka nufi kofar fita, a guje luzuraina ta sha gabanmu tana kuka ta sake rungumemu sannan ta janye

jikinta ta dubeni tace idan na haihu baka nan wanne suna za a sakawa abinda na haifa ka sani cewa yarima huzein zai samu kani koda jin wannan batu sai mamaki ya kamani na dubeta nace yaya aka yi kika san cewa da namiji zaki haifa luzuraina ta ce sau uku ina yin mafarkin na haifi da namiji don haka ina ji a jikina cewar lallai da namiji zan haifa, sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi sannan na dubi yarima huzein na ce na baka dama ka zabi sunan da za a sawa kaninka yayin da yazo duniya cikin murna yarima huzein ya daga kansa sama yayi dan tunani sannan ya dubi mahaifiyata yace ki sawa kanina suna YARIMA BASMAR, kuma kiyi masa bushara da cewa ya jira yayansa yazo suyi wasa. Lallai nine zan koya masa yadda ake sarrafa doki da takobi.

.

Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa luzuraina ta sake rungume yarima huzein tana mai sake fashewa da

wani sabon kukan. A dai dai wannan lokaci ne muka jiyo muryar sarki yana mai kwala mana kira cikin hanzari na fisge yarima huzein daga cikin luzuraina na ja shi da gudu muka fice daga cikin falon huzein na waigen mahaifiyasa yana hawaye itama tana kuka lokacin da na zo dai dai nan a tunanina sai yarima huzein ya dafa kafadata na dawo cikin hayyacina yarima huzein ya dubeni cikin alamun damuwa yace yakai abbana anya kuwa babu wani mugun nufi a zuciyar sarki shardas a kanmu ?

.

Yakamata ace ya fito ya tarbemu a bisa irin matsayin mahaifinka da daukakarsa a wannan nahiya amma kuma sai kawai ya aiko da hadimi aka taho damu nan masauki

sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi nace kada ka damu ya kai dana duk wannan ba komai bane, babu wani mugun abu da sarki shardas zai yi mana, kawai dai wulakanci ne irin nasa da son nuna isa, koma menene ai da zarar mun isa gabansa za a yita ta kare yaz sallame mu mu koma izuwa kasarmu burina kawai shine mu koma gida mu iske mahaifiyarka ta haihu lafiya kafin na rufe bakina saiga sarki ya shigo cikin dakin namu kuyanginsa guda hudu na biye dashi dauke da abinci cikin hanzari muka zube kasa muka kwashi gaisuwa su kuwa wadannan kuyangi sai suka ajiye wannan abincin

da abinshan a gabanmu suka juya da baya suka fice sarki ya zauna a gabanmu ya dubemu cikin annashuwa yace na kasa cin abincina shi yasa na yanke shawarar na zo har nan dominku muci tare.

.

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kamamu na dubi sarki nace yakai abbana kai kuwa menene dalilin daya hanaka cin abinci? Sarki ya yi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kasa sannan yace tun da muka shigo cikin  garin na naji zuciyata tana bugawa abu ne mawuyaci mu bar garin nan lafiya cikin farin ciki musamman idan muka yi duba da irin karbar da sarki shardas mana ta wulakanci da rashin nuna muhimmancina a gareshi ya yinda sarki yazo nan a zancensa sai nayi dariya nace haba yakai abbana akan wane dalili zakayi irin wannan tunanin alhali mun kasance masu biyayya ga sarki shardas gami da bin umarninsa, ni na san cewa babu wani tsautsayi da zai same mu lafiya kalau zamu koma gida kawai mu jira muga yadda zata kasance tsakaninmu da sarki shardas

koda jin wannan batu sai sarki ya saki ransa hankalinsa ya kwanta nan take muka kama cin abinci  cikin raha da nishadi muna ta hira da ban dariya har sai da muka koshi……

.

Wow littafi fa yanzu ya fara tafiya domin yanzu ne zaku san an fara karanta TSATSUBA zakuji yadda zata kaya tsakaninsu da yadda Ake tsantsan yaudara da cin amana gami da rashin imani.

.

Kafinnan dai Nidinne

Abubakar Saleh AlQuyraemey

Ke cewa Ku huta Lafiya…

TSATSUBA

Littafi Na Shida (6)

Part C.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Nan take muka kama cin abinci ikin raha d nishadi muna masu hira ta ban dariya har saida muka koshi.

.

A wannan rana sarki bai koma dakinsa ba anan dakinmu ya kwana saboda ko kadan baya son nisanta damu sai da muka kwana uku a cikin gidan sarautar sarki shardas amma wai har tsawon wadannan kwanaki sarki shardas bai kirawo mu ba duk da cewa kullum yana zama a fada, duk sa adda ya bukaci ya gana da shi sai yace a gaya masa cewa ya kara sauraro a ranar kwana na ukun ne da safe bayan mun gama kalaci  sai ga hadimin sarki shardas yazo mana take hadimin ya shaidawa  mahaifina cewar sarki yace muje mu riskeshi a fada cikin farinciki muka mike tsaye muka yi shiri sarki ya taramu gaba  dayanmu dakarunsa da kuyanginsa sannan aka debo wadannan bayi guda dubu ashirin gami da akwatunan dukiya guda dubu muka wuce izuwa fadar sarki shardas fadar ta cika makil ta batse da mutane ko ina ka duba saikaga fadawa dakaru da manyan attajirai  da sauran masu fada aji a kasar.

.

A gefe daya kuma mutanen gari ne maza da mata a durkushe a kas babu wani mutum guda daya a tsaye ko akan kujera face sarki shardas wanda ke kan karagarsa ta mulki, koda muka shigo cikin fadar mahaifina na kan gaba muna biye dashi gaba dayanmu sai naga  an zubawa mahaifina idanu kawai mutane so suke su gani shin zai iya durkusawa a gaban sarki shardas ya kaskantar da kansa? Babu abin takaici sama da ganin yadda mahaifina yayi gagarumar shiga ta alfarma mai tsananin tsada wacce ta ninka ta jikin sarki shardas sau uku amma kuma gashi zai kaskanta a gaban dubunnan talakawa a wannan lokaci ina rike da hannun yarima huzein muma munci ado na kwatance domin ko a cikin fadawan sarki shardas da duk jama arsa babu wanda ya sa suturar data kai tamu daraja ni da huzein ke bin bayan sarki sai kuma kuyangi da sauran dakarun da muka taho dasu daga birninmu don yi mana rakiya lokacin da ya rage saura baifi taku goma ba tsakanin mahaifina da karagar mulkin da sarki shardas ke zaune a kai sai yaja da baya cak muma da muke bayansa sai dukkanmu muka ja muka tsaya cak a bayansa nan take mahaifina da sarki shardas suka fara kallon kallo fuskar sarki shardas a murtuke take ko kadan babu annuri kuma jikinsa ya kama tsuma har fuskar tasa na yin gatsine saboda fishi bisa tunanin cewa ko mahaifina ba zai durkusa masa ba kawai sai akaga mahaifina ya durkushe kasa bisa guiwarsa guda ya risina yana mai dukar da kansa ga sarki shardas cikin murya mai dauke da ladabi yace gaisuwa gareka ya shubana a madadina da al umar kasata nazo domin mu jaddaja mubaya armu a gareka ya sarkin duniya kuma na amsa kiranka, gani nazo da duk abinda ka bukata.

.

Koda mahaifina yazo nan a zancensa sai fuskar sarki shardas ta fadada da murmushi ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin matukar murna sannan ya tako yazo har inda mahaifina ke durkushe

ya kama kafaduna ya tashe shi tsaye suka fuskanci juna yace lale marhaban da sarki mai birnin Askandariyya lallai ka tsira daga dukkan fishinmu kuma daga yau ka zama amintaccenmu nan take fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki shardas jinjina da kirari bisa ganin yadda sarki mai daraja da cikakken iko kamar mahaifina ya mika wuya a gareshi a wannan lokaci takaicida bakinciki suka lullubeni har idanuna suka ciko da kwallah ban sani ba, sarki shardas ya daga hannu sama sai fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta , A sannan ne sarki shardas ya bushe da dariyar farinciki ya kirawo wani hadimi nasa mai dauke da tambulan na ruwan giya gami da kofi guda biyu da zuwan hadimin sai sarki shardas ya dauki kofi guda hadimin ya tsiyaya masa ruwan giyar sannan ya dubi mahaifina yayi masa tayi, batare da fargabar komai ba mahaifina ya dauki daya kofin shima aka tsiyaya masa ruwan giyar amma sai yaki yasha.

.

Koda ganin haka sai sarki shardas ya bushe da dariya sannan ya kurbi ruwan giyar har sau biyu ya dubi mahaifina yace kwantar da hankalinka

abokina ai ba zan shayar dakai guba ba, saboda me kake tsoron shan wannan giya mai albarka wacce nasa aka yi ta musamma don tarbarka?

Koda jin wannan batu sai mahaifina yayi murmushi yace ai ba komai bane yasa naki sha ba sai don yin ladabi a gareka kada na rigaka dandana dadinta dajin haka sai sarki shardas ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya kamo kafadar mahaifina ya juyo dashi suka fuskancemu sarki shardas ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yace wannan danka ne yarima hulbasu mai jiran gado tare da dansa yarima huzein ko ?

.

Mahaifina ya gyada kai yace kwarai kuwa sune sannan ya dubemu yace kuyi gaisuwa ga.sarkin duniya, da farko sai na dan noke a lokacin da huzein tuni ya duka kasa ai kuwa sai nan da nan fuskar sarki shardas ta juye izuwa fishi har sai da nima na durkusa na gaisheshi sannan yayi murmushi yazo ya dafani  ta yadda har muna iya jin numfashin juna ya budi baki cikin karamar murya yadda babu mai iya jinmu ba sannan yace, Samari nasan abinda kake ji a ranka bisa kaskantar da kan da mahaifinka yayi a gareni domin jaddada min mubaya arsa amma ina mai shawartarka da ka zamo mai biyayya idan har baka son daular birnin Askandariyya ta fadi, yana gama fadin hakan sai ya wuce gabana ya shiga duba bayin da aka kawo masa guda dubu ashirin har sai da ya tabbatar da cewa gaba dayansu lafiyayyune sannan yaje kan akwatunan dukiya guda dubu sai da aka bude gaba dayan akwatunan yaga dukiyar dake cikinta nan take sarki shardas ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dawo wajen mahaifina ya kama hannunsa ya jashi har zuwa kan karagar mulkinsa suka zauna tare a wannan lokaci fadar tayi tsit ko tsinke ne ya fadi kasa sai an ji kararsa.

.

Sarki shardas ya dubi mahaifina cikin nutsuwa ya ce ya.batun sharadin da muka gindaya maka a cikin wasikarmu?

Shin ka amince zaka yi abinda muke so ko kuwa ba zaka bi ba ? 

.

Sa adda mahaifina yaji wannan tambaya sai ya risina cikin biyayya yace ya sarkin duniya na amince da duk bukatarka amma ina neman wata alfarma guda daya, alfarmar kuwa itace ina son ka rage yawan bayin da zan rinka kawo maka duk shekara da kuma yawan akwatunan dukiya su koma rabin wadanda na kawo maka yanzu ba don komai ba sai saboda hakan zai iya kawo karyewar tattalin arzikin kasata domin a halin yanzu bayi sunyi karanci a kasata kuma bayin nan sune suke yi mana aikin noma a gonakinmu noman kuma shine yake kawo mana dukiyar da zamu tara mu kawo maka koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata ya dakawa mahaifina tsawa yace babu ruwanmu da wannan matsala domin kai ta shafa bamu ba don haka sai ka san hanyar da zaka bi ka nemi bayi koda kuwa sai kayi farautarsu ne a sauran kasashen da ke kusa daku ka sani cewa gobe goben nan zan hadaka da wakilina mutum uku wadanda zaka tafi dasu izuwa fadarka a dinga gabatar da harkokin mulki tare da su domin su rinka kawo mini

rahoton duk abubuwan dake gudana, a karshe ina mai gargadinka da cewa digon jini daya na wadannan wakilai nawa dai dai yake da digon jinin saba in na jama arka don haka a kula da su da kyau kuma a basu

duk abinda suke bukata. 

.

sa adda sarki shardas yazo nan a zancensa sai nayi wuf na matso gaba kusa da karagar mulkin sa na dubeshi nace yakai wannan sarki

ka yi sani cewa idan ka hadamu da wadannan wakilai naka tamkar ka rushe karfin mulkin mahaifina ne gaba daya tunda ba shi da ikon yin wani sirri a cikin harkokinsa na mulki kuma ba shi da ikon zartar da komai sai da saninka da  amincewarka, wannan ba adalci bane zalunci ne da kaskantarwa……. Kafin na gama wannan jawabi tuni jikin sarki shardas ya kama tsuma saboda fishi har gumi ya fara tsatstsafowa daga fuskarsa shi kuwa mahaifina a wannan lokaci ya firhita ainun so yake ya hanani ci gaba da magana amma ya kasa, kawai sai sarki shardas ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ya zo daf dani ya zare takobinsa ya dora kaifinta akan wuyana yana mai ci gaba da tsuma ni kuwa ko gezau ban yi ba.

.

A lokacin gaba dayan mutanen dake fadar sun firgita ainun kowa ka kalla sai kaga jikinsa na bari don gudun kada laifin wani ya shafeshi, sarki shardas ya daka min tsawa ya ce kai dan samari kaine mahaluki na farko wanda ya taba shigowa har cikin fadata yayi mini bakar, don haka yanzu zan kasheka domin na gusar da kishirwar karya wannan lago nawa da kayi, koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya daga takobinsa sama da nufin ya sareni amma sai mahaifina yayi wuf ya janyeni daga gabansa sannan yayi sujjada a gareshi ya dago kai yace ya sarkin duniya ina nemawa dana afuwa ka san cewa har yanzu akwai kuriciya a tare da shi.

.

Koda jin wannan batu sai sarki shardas ya sake bushewa da dariyar  mugunta sannan ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dafa kafadata yace samari ka tsira daga kaifin takobina yau, amma ka sani cewa idan ka sake aikata kuskure irin wannan ba zaka taba tsira ba yana gama fadin hakan sai ya juya ya fuskanci fadawansa ya kirawo wadansu mutane uku daga cikin dan uwansa wanda ake kira MUHAIRU wanda ya kasance dan yayarsa sarki shardas ya dubi muhairu ya ce yakai dan uwana daga yau na cireka daga matsayin gwamnan birnin DAILUFA a yanzu kaine shugaban wakilaina na birnin Askandariyya saboda haka kaje ka fara shirin binsu gobe amma kafin goben ina so ka zauna da yarima hulbasu ya sanar dakai iya adadin biranensu da kauyukansu da kuma duk harajin da suke tarawa a kowacce shekara ka rubuta komai ka kawo min.

.

Muhairu ya risina yace an gama ya shugabana kawai sai sarki shardas ya juya ya fice daga fadar ya wuce izuwa cikin gidan sarautarsa, shi kuwa muhairu sai ya zo gabana ya tsaya yana mana wani irin murmushi na mugunta da raini ya dubeni yace ka saurari zuwana nan da lokaci kankani yana gama fadin hakan sai ya kyalkyale da dariyar mugunta  ya wuce abunsa sauran wakilai guda biyu na take masa baya suma suna kyalkyala mana dariya.

.

Nan take dakarun sarki shardas suka ingiza keyar bayin da muka kawo guda dubu ashirin aka wuce dasu izuwa can wani bangare na gidan sarautar sarki shardas, kuma aka kwashe Wadannan akwatunan dukiyar da muka kawo , A sannan ne fadar ta watse ya zamana cewa daga mu sai jama armu kacal a tsaye cikin tsananin bakin ciki da takaici.

.

A dai dai wannan lokaci ne zuciyata ta kama tafarfasa kamar zata kone ban san sa adda na kurma uban ihu ba mai tsananin firgitarwa na durkushe kasa ina mai fashewa da matsanancin kukan bakin ciki.

.

Al amarin daya janyo hankalin dakarun sarki shardas kenan suka zare takubba suka rugo izuwa kanmu, koda suka ganni durkushe a kasa ina

kuka sai suka kama dariya suka tafi suka barni a wannan lokaci ne mahaifina da yarima huzein suka durkusa a gabana sa adda suma suka fara zubar da hawayen bakinciki kawai sai sarki ya rungumeni tare da fashewa da kuka sosai mu duka sai muka kama kukan, sai da muka dan jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan muka mike tsaye muka tafi izuwa masaukinmu…….

.

Wow Zan dakata A wannan guri saikuma Allah ya kaimu Gobe

zan cigaba daga nan. Amma kafinnan Nidinne Dai Abubakar Saleh AlQuyraemey Angon farar mace alkabbar mata.

TSATSUBA

Littafi Na Shida (6)

Part D.

Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

08138873799 For More Littattafan Yaƙi 

.

Sai da muka dan jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan ka mike tsaye muka tafi izuwa masaukinmu.

…Bayan mun isa masaukinmu mun zauna cikin bakinciki muna tunanin wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki na takaici da wulakanci, sai sarki ya dubeni a lokacin da hawaye ya zubo masa yace yakai dana ka yi sani cewa wadannan sharadai da sarki ya gindaya mana sai sun janyo fari da talauci a kasarmu kuma wannan shine lokacin da na dade ina tsoron gani a rayuwata fadin hakan keda wuya sai sarki ya fara wani irin tari mai karfi kafin a jima kuwa sai ya kama aman jini cikin rudewa na kwallah ihu ina mai kiran likitan sarkiwanda muka taho tare dashi tun daga birninmu domin duba lafiyarmu, nan da nan wata kuyanga  ta ruga taje ta kirawo likitan yazo ya shiga duba mahaifina dan ceto rayuwarsa da kyar likitan ya samu ya shawo kan cutar sarki ya tsayar da jinin dake zuba a bakinsa sannan kuma ya bashi magani ya sha faruwar hakan keda wuya cikin dakika kadan nannauyan barci mai karfi ya sace sarki a wannan lokaci ne ni da huzein  muka dawo cikin hayyacinmu na dubi likitan sarki cikin alamun mamaki nace yakai likita wannan wane irin ciwo ne ya sami mahaifina alhalin ina tare dashi tsawon shekaru amma ban taba ganinsa a cikin irin wannan hali ba sai yau.

.

Koda jin wannan batu sai likitan ya sunkui da kansa kasa yayi shiru kamar ba zaice komai ba har sai da na daka masa tsawa sannan ya dago kai ya dubeni a tsorace bakinsa na rawa yace ka gafarceni ya shugabana ka sani cewa sarki ya haneni da na sanar da kai komai dangane da rashin lafiyarsa, sa add anaji wannan batu sai na sake fusata na zare takobina na dora kaifinta akan wuyan likitan nace na rantse da darajar sarki idan baka sanar dani wannan al amari ba yanzun zan kashe ka.

.

Koda jin haka sai jikin likitan ya kama tsuma ya budi b baki cikin in ina ya ce tun ranar da wasikar sarki shardas ta iso birninmu na askandariyya  fadar mahaifinka yaji sakon da ta kunsa a  lokacin ya kamu da ciwon zuciya ina mai sanar dakai cewa wannan ciwo yana da tsananin hadari domin zai iya zama sanadin ajalinsa a ko yaushe cikin kankanin lokaci muddin zai rinka fuskantar abinda zai bata masa rai  koda likita yazo nan a zancensa sai na durkusa kasa na fashe da matsanancin kuka.

.

Al amarin da ya karya zuciyar yarima huzein kenan, shima ya fashe da kuka nan take naji na tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma na kudurce a raina cewar in dai wannan ciwo ya zamo sanadin ajalin mahaifina sai na yaki sarki shardas gaba da gaba duk da na san cewa hallaka zanyi muna cikin wannan haline muka ji an kwankwasa mana kofa sai ga wakilin sarki shardas kuma  dan uwansa mubairu ya shigo cikin dakin da muke, koda ya ganmu muna kuka kuma ya ga sarki a kwance a gefe daya yana barci ga likita zaune a kusa dashi sai yayi dan guntun murmushi sannan ya dubeni yace yakai yarima hulbasu ka sani cewa nazo ne gareka domin ka sanar dani abubuwan da sarkina ya umarceka daka sanar dani domin na rubutasu nakai masa,  koda jin haka sai na dago kai na dubeshi cikin tsananin fishi nace ashe baka da hankali da nutsuwa?

.

Kana ganin halin da mahaifina yake ciki ne zaka zo min da wannan maganar banzar ? Ta yaya kake tsammanin zan iya maka bayani a yanzu bayan ina cikin tashin hankali da damuwa, koda jin haka sai ran mubairu ya baci ya daka min tsawa mai karfi tare da nunani da dan yatsa yace babu ruwana da batun halin da mahaifinka yake ciki domin kuwa umarnin sarkina na gaba dashi maza ka sanar dani abinda nazo sani kafin fishin sarki ya tabbata a kanka yana gama fadin hakan sai ya zauna a kusa da ni ya fiddo littafi, tawada da alkalami domin yin rubutu

ni kuwa sai na tattare hannun rigata kamar zan zauna a gabansa amma sai na shammaceshi na gabza masa wawan naushi a fuska sabo da karfin naushin sai da ya wuntsila da baya sau uku a lokacin da jini yai feshi daga cikin bakinsa, ai kuwa sai ya taso da alkafira yai tsalle ya doki tawa fuskar da kafarsa, nima na gwaru da bango na fasa baki kafin na mike tsaye ya danneni kuma ya zaro wata wuka zai caka min a kirjina sainayi wuf na rike hannunsa, a sannan ne likita da sauran

hadimanmu suka kurma uban ihu suka ruga waje da gudu suna kiran dakaru domin su kawo dauki, yarima huzein ne kadai tsaye a gabana yana kallon abinda ke faruwa jikinsa na karkarwa sabo da tsananin razana mubairu yaci gaba da kokarin dannan  wukarsa a cikin kirjina, ni kuma naci gaba da kokarin hanashi samun nasara, amma sai karfinsa ya rinjayi nawa har wukar tasa ta dan sokeni na kwalla ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da naji, a lokacin da jini ya fara bulbulowa daga cikin kirjina duk wannan abu dake faruwa sarki na kwance a gefe daya yana shara barci bai sani ba.

.

Koda yarima huzein yaga saura kiris mubairu ya sami nasarar hallakani sai yai wuf ya zare wuka a jikinsa ya dako tsalle sama ya sokawa mubairu a wuya take wukar ta lume ta faso makogwaronsa ya sulale

kasa matacce huzein ya sunkuya a rikice ya kama Wukar tasa domin ya zareta daga cikin wuyan mubairu.

.

A dai dai wannan lokaci ne dakaru sarki shardas suka rugo izuwa cikin dakin su da yawa rike da makamai, koda suka ga yarima huzein yana zare wuka a cikin wuyan muhairu kuma gashi ya zama gawa sai suka yi caraf suka daureshi ni kuwa sai na taso da sauri izuwa kansu na hausu da sara da suka domin na kwaci dana a hannunsu duk da cewa suna da yawa amma sai da na tarwatsa su na kashe sama da mutum arba in ina cikin tsakiyar yin yaki dasu ne naji anyi min wani wawan duka a kirji saboda karfin dukan sai da nayi sama na gwaru a jikin katangar dakin na fado kasa a galabaice lokacin dana farfado sai na tsinci kaina a tsakiyar fadar sarki shardas kwance a kasa.

.

A gefen damata yarima huzein ne a daure cikin sarka a haguna kuma mahaifina ne tare da dukkan dakarunmu da kuyanginmu suma duk a daure cikin sarka zaune akan karagar mulki sarki shardas ne rungume da gawar dan uwansa muhairu yana ta faman rusa kuka, nan take zuciyata ta buga da karfin gaske na kamu da tsananin tsoro irin wanda ban taba jinsa ba a rayuwata ba komai ne ya sa ni jin wannan tsoro ba face tunanin cewa sarki zai kashe mune gaba dayanmu, idan ya kashemu kuma matata luzuraina ta mutu a wajen haihuwa shike nan fa duk burinmu ya tarwatse kuma lokacin faduwar kasarmu yazo a dai dai wannan lokaci ne yarima huzein ya dubeni a lokacin da hawaye ya zubo masa yace yakai abba na ka gafarceni domin na janyo mana abinda zai kawo karshen mu gaba daya.

.

Sa adda naji wannan batu sai hawayen takaici ya zubo min na dubeshi nace yakai dana baka bukatar rokona gafara domin baka aikata laifin komai ba tabbas ka kashe muhairu ne domin ka ceci rayuwata babu wani da da zai bari a kashe mahaifinsa a gaban idanunsa muddin zai iya hanawa.

.

Koda jin wannan batu sai mahaifina ya dubi yarima huzein cikin alamun tsananin tausayi a lokacin da shima hawaye ya zubo masa yace yakai jikana huzein hakika kayi babban kuskure daka ceci rayuwar mahaifinka a hannun muhairu  domin hakan zai janyo asarar da babu abin da zai biyata gama fadin hakan ke da wuya sai sarki shardas ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya ajiye gawar muhairu akan  karagar sannan ya share hawayansa ya dubi mahaifina fuskarsa a murtuke sannan ya dubeni kuma ya dubi huzein yace yaro ka kashe mini dan uwa wanda shi kadai ne ya rage mini a duniya inda zan kashe gaba dayan mutanen kasarku mazanku da matanku jininku ba zai goge bakincikin abinda na rasa ba zan dasawa mahaifinka bakin cikin da har ya mutu ba zai manta da ni ba domin hakan ne kadai zai sa zuciyata ta lafa daga ruruwar wutar bakinciki.

.

Koda gama fadin haka sai sarki shardas ya sa aka kwanceni daga cikin sarkoki sannan ya zare wata sharbebiyar wuka ya cillo mini ita na cafe kuma ya zare takobinsa yace nine na doki kirjinka dazu ka suma sa adda kake  kashe dakaruna.

.

Koda ka manta cewa na gaya maka cewa digon jinin daya na wakilaina da zan tura birninku dai dai yake da digon jinin mutanenku saba in to ku sani cewa a yanzu jinin mutum saba in ba zai zamo fansar dan uwana ba abinda nake bukata shine ina son  uba ya yanka dansa da hannunsa yanzu a gabana ko kuma na kashe ka da dukkanin jama arsa gaba daya.

.

Koda jin wannan batu sai mahaifina ya fashe da kuka ya risina ga sarki shardas kuma ya zube kasa gaba daya ya yi masa sujjada sannan ya dago kai ya dubeshi a lokacin da hawaye ke shatata bisa kumatunsa ya kuma dubi gaba dayan fadawan sarki shardas da mutanan gari yace yakai sarkin duniya ka dubi yadda na kaskanta kuma na wulakanta haka a gaban talakawanka a matsayina na sarkin da ya gawurta  a wannan  nahiya tamu ka dubi darajarr sarauta ka canja wannan nufi naka, koda jin haka sai sarki shardas ya girgiza kai yace ai bana yin magana biyu na gama yanke hukunci ko danka ya yanka nasa dan yanzu take ko kuma na kasheka a gaban idansa  kuma na kashe gaba dayan dakarunka da kuyanginka da duk hadimanka, mahaifina ya fashe da kuka yace yanzu jinina ni kadai ba zai fanshi jinin dan uwanka ba ? 

.

Sarki shardas ya dubi katon badakarensa mai rike da wata katuwar gudumar danko yace dashi yakai KALBAN ka buga gangarka sau goma idan yarima hulbasu bai yanka dansa ba kafin bugu na goma zan kashe mahaifinsa da duk jama arsa.

.

Koda jin wannan umarni sai kalban ya daga gudumarsa ya doki wata katuwar ganga dake rataye a jikin wani dogon karfe take sautin gangar ya cika birnin gaba daya a dai dai wannan lokaci ne huzein ya kama jan guiwarsa kasancewar a daure yake cikin sarka ya iso gabana ya kwanta kasa ya dubeni yana mai murmushi gami da zubar da hawaye yace yakai abbana ma za ka yankani domin ka  kubutar da mahaifinka da jama armu.

.

Ka sani cewa zan mutu a cikin farin ciki tunda da jinina ya zama fansa ga rayuka masu yawa a wannan lokaci kalban yaci gaba da buga gangarsa har yayi bugu na biyar, sa adda naji wannan batu na dana huzein sai hawaye ya zubo mini na dubeshi nace ka gafarceni yakai dana kayi sani cewa zan yanka ka ne ba don na ceci rayuwata ba ko ta ubana ba sai don Rayuwar jama armu ga su can wadanda suka sallama rayuwarsu don biyayya a garemu lallai ina son su koma gida a raye domin su rungumi iyalinsu………

.

BABBAR MAGANA KENAN

.

SHIN HULBASU ZAI YARDA YA YANKA DANSA YARIMA HUZEIN ?

.

IDAN YA KASHE SHI  IDAN YA KOMA BIRNIN ASKANDARIYYA MAI ZAICE DA MAHAIFIYARSA ?

.

SHIM MAHAIFIYAR YARIMA HUZEIN TANA HAIHUWA LAFIYA?

.

INA LABARIN JARUMA SIYAMA DASU YARIMA HULKAS ?

.

Marubucin Littafin Yace Mu Hadu A Littafin Tsatsuba Na gaba Don Jin Ci Gaban Wannan Kasaitaccen Labari.

Marubucin Littafin Wato

The King Of Adventure Story

Malam Abdul aziz Sani M/Gini

Saikuma Ni Abubakar Saleh AlQuyraemey wanda nake jagorancin typing din wannan littafi nake cewa Mu zama lafiya saimun hadu a littafi na bakwai….

Dont Forget My Name

Back to top button