Ajiya A Duhu Book 1 Page 18 Complete Novel
🅿️➖1️⃣8️⃣…….“Ban gane ba Usman, kamin bayani yanda zan gane da ƙyau”. Kai Daddy ya jinjinama Baba Kallah. Kafin ya gyara zamansa da ƙyau ya shiga zayyano masa abinda ya sani. Kuma ma duk ita Hajiya Yaya ce ta kirashi a waya ta sanar masa. Daga ƙarshe ya dora da faɗin, “Gasu nan baba ka tambayesu daga Asia ɗin har Basariyya akwai wanda na zaunar naima magana akan batun? Na barsu ne har sanda yarinyar zata samu lafiya dan shine mafi muhimmanci. Amma sai ita ta nuna min ban isa ba. Nace taje ta duba yarinyar ita da yara sashenta tace ban isa ba ita kuma Basariyya taje, hakan yasa na dakatar da ita da shigowa wajena…..” “Dolene to sai naje. Itama Basariyyan ai munafunci da gulma ne ya kaita badan ALLAH ba”. Hajiya Yaya ta faɗa cikin katse Daddy. Tsawa Babanta ya daka mata shima, dole tai shiru tana kumbura fuska. “Usman kamin dai-dai, dan abinda kayi ɗin shine mazantaka.” baba Kalla ya faɗa, sai kuma ya juya ga Hajiya Yaya yana mai kiran sunanta. “Sadiyy! Dukkan abinda Usman ya faɗa haka akai?”. Babu musu ta jin jina kanta. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Baba nifa tsakanina da ALLAH koda aurena zai ƙare ne tsakanina da Usman sai dai ya ƙare a yau. Dan haka ku zama shaida ban amince Yazeed ya auri ƴar Asiya ba. Idan kuma ba hakaba a shirye nake na fiddashi a cikin ƴaƴana na barma Asiya tunda haka naga yake buƙata. Na gaya masa na masa faɗa amma yana maidani ban san abinda nake ba, to tunda haka ne dai ya zaɓa ko ni ko yarinyar”. Hankali tashe Yazeed ke duban mahaifiyar tasa. Zai yi magana Baba Kalla ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu. Dole Yazeed yay shiru. “Sadiyya miyyasa baki son shi haɗin nasu? Yarinyar nada wata illane da musulunci ya hanamu auren irinsu?”. “Illoli da yawa kuwa Baba. Ciwuwwuka sun gama zagaye rayuwarta. Sannan mu har yanzu bamu da tabbacin ma suna da uba tunda mudai bamu taɓa ganin dangin uban nasu ba balle mu shaida, har bikin yayunta akai a gidan nan mudai bamuga kowa ba, wama ya sani ko basu da uban ne shiyyasa sam ni jinina bai wani haɗu da nata ba dan bana ƙaunar yarinyar nan, ba kuma na ƙaunar uwarta gata nan”. Ta ƙare maganar da nuna Ammie babu nauyi ko kara. Kai baba Kalla ya girgiza da faɗin, “Ashsha Sadiyya, wannan magana tayi tsauri da yawa. Kiyi ƙoƙari ki dinga gyara harshenki yayin magana. Dan haka karna sake jin irin wannan zancen banzar ya fito. Munji baki son wannan haɗin, wacece kika fidda masa ke a matsayin matar?”. “Baba Nazeefar Sabuwa. Idan har Yazeed yana son yaga farin cikina to ya aurenta dan ita nasa tushenta. Idan ko ba haka ba ya shirya rayuwar auren ƙunci da baƙin ciki, sannan duk abinda zata haifa babu ruwana da su kamar yanda shima na ciresa daga cikin ƴaƴana…..” Cikin takaicinta da harzuƙa Daddy ya ce, “Aiko baki isaba wlhy, Maanal na zaɓama yarona matsayin matarsa ko kina so ko baki so, kuma wlhy first and last da zaki sake sheganta yaran nan idan ba hakaba kuwa sai ranki ya ɓaci fiye da yanda kike zato….” “Kaima kuwa baka isaba Usman, dan yanda kake jin kai uban Yazeed ne nima nice mahaifiyarsa. Nina ɗauki cikinsa na tsawon wata tara, nai naƙudarsa na kumayi rainonsa haɗe da tarbiyya har yakai girman da wata banza a banza daka kawo gidan ka kake ɗaukar ta a mutum ta isa ta mallake min shi, kai wlhy duk abinda kake ji ka iya na iya fiye da iyawarka Usman, dan…. “Sadiyya!!!”. Babanta ya katseta a tsawace. Shiru tai amma a ranta tana ƙunƙuni, dan ta ɗau aniyar koma miza’ayi sai dai ayi amma Yazeed bazai auri ɗiyar Asiya ba dan ita zuwa yanzu ma ta fara tunanin basu da uban. Ganin ran baba ya kai ƙolokuwar ɓaci hakama Daddy da ita Hajiya Yayan Ammie dake saurarensu kawai ziciyarta na mata ƙuna cike da girmamawa ta kalla Baba. “Baba dan ALLAH ina neman alfarma”. “Faɗi ko minene ɗiyata in dai ina da shi zan miki”. Wani takaici ne ya lulluɓe zuciyar Hajiya Yaya ganin yanda Babanta ke bama Ammie muhimmanci a zaman fiye da ita. Baki ta buɗe zatai magana ya harareta. Dole tai shiru ta cigaba da hare-harenta. Ammie bata nuna ta damu ba ta cigaba da faɗin, “Baba dan ALLAH ku barta ta aura masa wadda take so. Domin gaskiya ta faɗa Maanal bata dako isashiyar lafiya ma. A yanzu haka likitocin ma sunce tana matuƙar buƙatar hutu ta yanda al’amuranta zasu dai-daita. Shi kuma Yazeed za’a cigaba da tauyesa babu aurene saboda hakan. Bayan UBANGIJI ya halatta masa auren mata har uku ne. Idan har Maanal matarsa ce ko zuwa nan gaba sai ayi……” “Allah ya kiyaye, har abada bako za’ayi ba idan abinda kike tunani kenan ki ciresa kuwa….” Hajiya Yaya ta katse Ammie a harzuƙe. Shima Daddy a harzuƙen ya katseta da faɗin, “Ashe kuwa zaki mutu bayan anyi, dan Maanal ita na zaɓama Yazeed kuma shima itace zaɓinsa aure tsakaninsu babu fashi da izinin UBANGIJI ko da Asiya data haifeta bata yardaba kuwa. Baba ku ƙyaleta, tunda ita bata san masalaha ba dan ALLAH mu zuba aga ni da ita waye keda ƙarfin iko akan Yazeed ɗin…..” “A’a Usman duk baza’a kai ga haka ba”. Baba Kalla ya faɗa. Batare da ya jira cewarsu ba ya cigaba da faɗin, “Ku duka ku kwantar da hankalinku kuji. A matsayinku na iyayen Yazeedu duk kuna da iko a kansa, amma fa ku sani shima yanada hakki a kanku. Aure dai ba wasa bane, ba kuma jeka ka dawo bane ba. Dan haka ku masa adalci ku barshi ya zaɓi wadda ransa ya kwanta da ita koda a cikin zaɓin naku ne. Idan kuma babu a cikinsu itace ma babbar masalaha ya auro daga can gefe shike nan matsala ta kare. Saboda haka kai Yazeedu kana da wadda kake so ne?”. A hankali kuma karo na farko Yazeed ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur saboda damuwa. Cikin danne ƙuncin daya mamaye masa zuciya ya ce, “Baba idan har auren duka zaɓin nasu zai zama masalaha na karɓa. Zan auri Maanal ɗin da Nazeefa….” “Baka isa ba sai dai ka auri Nazeefa ita kaɗai….” Hajiya yaya ta katsesa cikin daka tsawa. Babanta ne shima ya katseta a tsawacen. “Sadiyya bana son shashanci fa. Yaro ya kawo mafita kinama mutane rashin hankali, ko kunyar idona baƙyaji bare nauyi. Shin kokin manta mune a gabanki bashi mijin naki kaɗai da kika raina ba. Ana binki ta lalama kina wani botsarewa saboda wulakanci. To wlhy ki shiga hankalinki. Idan kuma ba hakaba zan hanashi auren Zazeefa ɗin naga yaya zakiyi. Shashancin banza kai”. Haƙuri ta fara bashi ranta a matuƙar dagule. Tayi hakanne kawai dan ganin yanda ransa ya ɓaci, ta kuma san halin mahaifin nata idan yay magana baya canjawa. Gara ta lallaɓashi suje a haka ita tasan duk ma hanyar da zatabi dan ganin ta tarwatsa wannan aure…. Shima Daddy haƙurin yaba baban, dan haka ya cigaba da faɗin, “Shike nan magana ta ƙare zai auresu su dukan. Dan haka sai kuje ku fara shiri dan nan da watanni biyu za’ayi a wuce wajan. Rana ɗaya za’a ɗaura auren.” Wani irin motsawa zuciyar Ammie tayi da ƙarfi. Hakama Hajiya Basariyya da tun da aka zauna bata tofa komai ba zuciyarta wani irin raɗaɗi take mata. Ina bazai yiwu ta bari ai wannan haɗin ba, sannan bazata taɓa yarda aima Yazeed auren gata shi kaɗai ba wlhy, Gara a cigaba da wannan fitinar hakan yafi sakata nishaɗi, zai kuma fi bada armashi idan yazam anyi auren Nazeefa da Yazeed ne farko. Ammie zatai magana tai saurin katseta ta hanyar fara yi. “Baba mun gode ALLAH ya saka da alkairi ya kuma sanya albarka a al’amarin. Sai dai nakega maganar ɗaura auren rana ɗaya kamar akwai damuwa musamman ga ita Maanal. Tunda likitoci sunce abarta ta ɗan huta mizai hana a fara yin na Yazeed da Nazeefa daga baya sai ayi da ita Maanal. Komai ma zaifi tafiya a cikin masalaha ni dai anawa ganin, zuwa lokacin itama Maanal ta murmure dan yarinyar ta fyaɗu sosai a wannan karon, wlhy abin tausayi kamar bazata rayuba ma. Sai itama Huznah ta samu miji, Inaga sai a haɗa dana Yazeed ɗin kawai ko yaya kukace”. A maganar farko Hajiya Yaya wani irin daɗi da godema Hajiya Basariyya ta shigayi a zuciyarta. Daga ƙarshe kuma sai taji zafi danta fahimci hassada Hajiya Basariyya ke son nunawa. Amma zata bita a hakan dan itama ta ribantu. Itama dai Ammie har ranta taji daɗin zancen Hajiya Basariyya, duk da tasan tayi hakanne badan ALLAH ba sai wata manufa tata. Shiko Daddy wani irin ƙuna zuciyarsa ta shigayi, saboda ya jima da fuskantar wacece matar tasa. Cikin takaici kawai yake mata wani kallo mai kama da harara. A ɓangaren Yazeed kuwa wani irin tsanar matar uban tashi ya fara ji a karo na farko a rayuwarsa. Duk da ya jima da fahimtar halinta na munafunci dan ta sha haɗashi da Daddy a baya bai taɓa maida hankali ko damuwa da lamarinta ba. Amma a yau ji yake kamar ya maketa dan baƙin ciki. Shifa ya amshi auren Nazeefa ne kawai dan ya samu dai Mamma ta haƙura ya auri Maanal. Amma shine munafukar matar nan zata kawo wannan ƙauli da ba’adin. Kasa daurewa yayi cikin sanyin murya ya ce, “Ummi anawa tunanin ai ba komai bane. Idan ta dawo ƙarƙashina zama tafi samun kwanciyar hankalin da su likitocin ke buƙata. Maanal na buƙatar hutu ne da kulawa. Kuma ina sha ALLAHU duk bazan gaza yin hakan akansu su duka ba”. Ganin kamar zancen ya shigi baba yasa Ammie saurin tare numfashinsa. “Hakane Yazeed, amma dan ALLAH nima ina roƙonka da abi shawarar Hajiya. Saboda ya kamata aje neman auren Maanal wajen dangin mahaifinta. Ita kanta kuma sake samun nutsuwar zaisa komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata. Idan akayi na Nazeefar kamar da wata biyar haka itama sai ayi natan. Kamar yau ne ai ka kwantar da hankalinka kaji Yazeed”. Ji Yazeed yay kamar ya fashe da ihu. Dan idanunsa har wani ɗan tara ƙwalla sukayi. Baba Kalla ne ya ce, “To da gaskiyarsu kuma ta wani fanin idan muka kalla. Tabbas mai irin wannan ciwo mai haɗari ya kamata abi dokar likitocin domin samar mata da nutsuwa. Sannan kamar yanda mahaifiyarta ta faɗa yana da ƙyau aje neman aurenta wa mahaifinta. Dan haka kayi haƙuri Yazeedu kamar yau ne in sha ALLAHU. Kaima idan akai haka zaifi baka nutsuwa da kwanciyar hankali. Ai rabon baima zoba ballantana ya wuce”. Albarka duk suka saka da fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Sai dai a ɓangaren Yazeed zuciyarsa a matuƙar ƙuntace take. Haka shima Daddy sam wannan tsarin bai masa ba. Kawai dai dan anfi ƙarfinsa ne. Amma ya ƙullaci Ammie da Hajiya Basariyya. Da haka dai taron ya watse….. _________★ Bayan wucewar su Baba Ammie ta samu Daddy akan zataje gaishe da Nene tai mata godiya da ban gajiya. Amma sai yace bai yarda ba. Abin ya bata mamaki, saboda a fusace yay maganar. Zata roƙesa kuma ya ɗaga mata hannu da nuna mata ƙofa alamar ta fita. Tsantsar biyyarta garesa yasa bataja zancen ba ta fitan, dan ta fahimci a fusace yake da ita ne, sai dai bata san ainahin laifin nata ba ita kam. Koda ta kira Nene ta sanar mata ya hana, sai tace ta jirata gata nan zuwa ita…. ________★ Hajiya Basariyya kam dariya ta dinga sheƙawa. Sai kuma tai kiran aminiyarta ta lambarta mata komai. Dariyar suka haɗu sukayi tayi su duka. Sai da sukai mai isarsu cike da zolaya Hajiya Kamila daga can tace, “Aminiyata ke kwalba ce wlhy uwar sharri. Cikin ƙanƙanin lokaci kinsa dole anbi yanda kike so. Ho tawajena kina wuta fa”. “To ni ɗin ta wasa ce aminiya ai idan sun san wata basu san wata ba. Idan har ina raye Asiya bata isa samun abinda ni ban samu ba. Ita kanta Hajiya Sadiyya da take ganin kamar na mata aiki ne ta saurari shirina akanta.” “Kai ta wajena mi kike shirya mata ita kuma?”. “hhhhh karki damu sai mun haɗu zaki ji komai da komai. Ke dai yanzu kice da Malam Nagode. Zuwa gobe kuma zan turo miki Huznah ya mata dukkan abinda yace dan ina son shap-shap yaron nan ya kawo kasa tunda har na gumtsa musu zancen kada a fara ɗaukata maƙaryaciya”. “An gama ai karki wani damu kanki”. “To shike nan sai tazo.”Daga haka sukai sallama kowa ya yanke wayar. Hajiya Basariyya ta faɗa saman gado tana mai jin kanta a sama can ƙolokuwa da tabbatar ma da kanta yau sa’a tata ce……..✍️
