Hausa novels

Mejo Najeeb Page 12 By Autar Alheri

“Dukkansu da kallon mamaki sukabita musamman general aliyu da captain Jameel nakiran Sunan mejo najeeb datayi kenan Hakan nanufin tasanshine kome? Sukaɗai keyiwa kansu wannan tambayar dabame basu amsarta, suna cikin wannan tinanin Sega maah tafito riƙeda wani gaye ahannunta cikin bada umurni tamiƙawa Isseta shi tace “imaza maryama karanta ayatushifa,ihilas, nasi, da falaq ajikin wannan gayen kishafa masa a ƙirji yanzu karki soma bari tasha iska bakiyiba mazayi da azama…jikina rawa Isseta takarɓa cikin bin umurnin mahaifiyar tata tashiga karantowa cikin sexy voice ɗinta meratsa zuciyar mesauraro…da mamaki sosai su general aliyu ke kallonta ganin gasu maza ƴan uwanshi kuma sune sukazo dashi amma bata basuba tabawa bawa mace komihakan kenufi oho? Itako maahh sarai tagano abunda suke nufi Hakan yasa tayi murmushi kana tace”kudena mamakin nabawa mace bayan kuna maza tabbas maryama mace ce amma ba kamar kowacce mace ba awurin wasu mazajen zata iya zama mace kamar kowa amma Banda agun NAJEEBULLAH..ido suka zaro atare cikin matuƙar mamakin data ƙara basu domin kalamanta idan bacikin chakwakiyar mamakiba babu abinda suke sakasu….suna cikin wannan yanayinne Isseta tagama karatun Hakan yasa tamatse ruwan gayen asaman faffaɗan ƙirjinshi kamar yadda maah ta umurceta bayan general aliyu yabuɗe maɓallan rigarsa taredayi sama da tacikin, tana zuba ruwan gayen suna shigewa cikin kusafen sumardake kwance akan faffaɗan ƙirjin nashi, seda tagama matsewa tass cikin azama taɗora lallausar Fatar tafin hannunta akai kamar yadda maahh tafaɗa ayanzu nacewa tamurza mishi ruwan su shiga jikinshi sosai, seda duk suka zabura alokacinda hannunta yasauka akan lallausar Fatar jikinshi, wanda ba maryama dake garauba shikanshi dabesan waye akanshiba seda wani mugun shuck yajashi..natsuwarta ta tattaro dudda haryanzu jikinta rawa yakeyi kamar mazari tafara shafa mishi ruwan maganin tanayi tana murza sumar ƙirjinshi tinda akwance take wurin doline kuwa inta murza tamurza hadda ita….shikuwa tin zaburar dayayi tafarko alokacin da hannunta yasauka akanshi beƙara ko motsiba har karkarwarda jikinshi keyi kamar zesuma yadena…itako taɗauki kusan minti 4 tana murza maganin kamun suga yafara motsa kafarshi daganan yafara yunƙurin buɗe golden eyes ɗinshi ahankali yasaukesu akan kyakkyawar fuskarta data gama jiƙiwa sharkaf da hawaye duk sunbishe mata..wata irin zabura yayi yana ingijeta tareda Banka mata muguwar harara..cikin sauri maah tatareta tafaɗo jikinta tana murmushi. Kwaɓe fuska Isseta tayi kamar zatayi kuka itama tana Banka mishi hararar kamar yadda yayi mata.”Miye Hakanne mejo? Inda kajimata raunifa ? Miyasa kakeda saurin fishinewai? tukunnama kasan miyakawota jikinka dahar zaka mata Hakan? General aliyu yafaɗa cikin hasala da abinda mejo ɗin yayi.”Aa kabarshi airashin sanine amma ba yadda za’ayi najeebullah ya cutarmun da Maryama, cewar maah tana murmushi ga dukkan alamu yin murmushi ɗabi’artane…aɗan razane yaɗago yana kallonta jin muryarda baze taɓa mantawa da itaba dudda acikin mafarki yakejinta amma tabbas idan yajita ze iya ganewa koma a’inane, bakinshi narawa yashiga harhaɗo kalamanshi daƙyar yabuɗe bakin yace “maahhh. “Ƙuttt😱 badai najeeb ɗinma yasan maah ba?? Nafaɗa araina, domindai nikam yau ina ganin abubuwan mamaki awurinnan kar Brain na tatushe nakasa fahimtar mikeshirin faruwa balle naɗauko muku rahotofa masu karatu..🤔🤫Sumadai su general aliyu kallonda suke mishi kenan ta ina yasan wannan aljanar dahar zekirata yadda yaji wannan yarinyar na kiranta…basugama tantance amsarsuba sukaji ta’amsa mishi da “na’am najeebullah…idonshi yaruntse daƙarfi yana tasbihi ga ubangiji tabbas wannan maah ce wadda yake gani a mafalkinshi duk kwanan duniya tokodai mafalkinne yake ƙarayi ayanzu darana tsaka? Zuwan wannan tambayar a ƙwaƙwalwarshi ne yasakashi buɗe dara daran idanuwanshi tareda ɗauke kanshi da mari domin ko mafalkinne ya falka…cikin sauri general aliyu yariƙe hannunshi yana faɗar “innalillahi mikakeyine Hakan mejo? Kanacikin hankalinka kuwa? Muryar maah ce takatse mishi zancenshi inda take cewa “kadena dukan kanka najeebullah wannan zahirine ba mafarki ba domin Allah yayi azahiri zan ƙarasa cika alƙawarina agareka.LagosWata mata ce kezaune bedroom d’inta tarufe ko ina afuskarta. Wata irin zabura naga tayi alokacin da take kallon madubin dakinta inda take ganin mejo najeeb kwance tareda su general aliyu gakuma wani haske ataredashi har biyu kuma gaya tana kallo yamiƙe daga cutarda yakeyi dudda bawarkewa ne yayi gabaki ɗaya ba…cikin mugun ɓacin rai tabud’e baki daƙarfin gaske tace “whatt??? mihakan kenufi? Badai zakurusamun shiri bane wanda Nasha matuƙar wahala wurin yinshi, Humm tab ɗijam ai wlh baku isa. Tana gama faɗar Hakan tafice daga bedroom ɗin kamar zata tashi sama tanufi wani ɗakin.GombeWani irin ajiyar zuciya mejo najeeb yasauke kamar ɗan dakejin yunwa yana neman mah’mah yasha kuma yasamu, dararrafe yazo gun maah tareda riƙo dukkanin hannayenta biyu cikin muryar tausayi yace “maah narasata narasata tarufe fuskarta kuma tajeda wannan abunda bansan komineneba inaso tadawo dagareni maah inaso nakarɓi wannan abin daga hannunta domin inaji ajikina abune me matuƙar mahimmanci agareni..shiru yayi yana haɗiye wani abun daya tokare mishi maƙoshi kana yacigabada faɗar “maah suwaye waƴannan mutanen? Misuke nema ataredani suke bibiyata? Wacece wannan yarinyar? Miyasa sukesan yimuna…ya’isa najeebullah maah tamatseshi batareda tabashi damar ƙarasa abunda yakesan faɗa ba kana tace “duk abinda kagani amafalkinka isharace daga uban gijinka yanuna maka abinda zefaru dakai tinkamu yafaru kuma yanuna maka abinda yafaru bayan faruwarshi ko ganina dakayi Ayanzu ya’isa ya tabbatar maka dahakan, babu abinda zancema Ayanzu domin koma minene lokaci shine ze bayyana kansa zaka ga komai kuma kafassara abunka batareda wani ya fassarama ba sedai inaso kasani. Shiru taɗanyi kafin yacigabada faɗar”ita wannan dakake faɗar karasata to bazaka taɓa rasataba har abada, sedai idan wanin kune baya raye aduniya kuma tabbas wannan abun dake hannunta baka faɗi ƙaryaba yanada matuƙar mahimmanci agareka domin shine giɓin daka rasa arayuwarka sedai kasani bazata taɓa mallakamakashi kaikaɗaiba domin itama tanada buƙartarshi atata rayuwar sedai kuyi anfani dashi ku biyu yadda zecike muku wannan giɓin dukkanku.Shiru wurin yaɗauka kowada tinanin dayakeyi akan wannan lamarin musamman su general aliyu da captain Jameel awanan karon harmada Isseta. “Tofa awannan karon nikaina nashiga kwakulushin iyimuku hausar mutanen garincan🙈 amma bara muyi ɗanta ƙyaitaccen bayani akan waye mejo najeeb dakuma haɗinshi da maah konace inda yasanta.”Shin wanene mejo najeeb??????Mejo Najeeb ɗa ne agun Alhaji Khamis sahabi shine ɗanshi nafari.. Alhaji Khamis sahabi yanada mata biyu salamatu itace babba wato Hajiya Umma sekuma murjanatu itace ta biyu wato Hajiya mama.Alhaji Khamis sahabi haifaffen ƙasar Niger ne acikin garin maraɗi inda yataso amatsayin maraya domin tinyana ƙaramin yaro iyayenshi suka rasu Hakan yasa yataso ahannun abokin babanshi Alhaji idirisu inda yariƙe Khamis amana shida yaronshi namuji wanda ya kasance tsaran Khamis ɗinne wato Abdussalam atare sukayi karatunsu har suka girma suka mallaki hankalin kansu…bayan sun girmane Alhaji idirisu ya aurawa Khamis yarshi inda shiko nashi yaron wato Abdussalam yanemi wata bazuwa ya’aura yar wani attajirin me kuɗi agarin yamai…Hakan kayi hidimar biki lpy aka ƙare. bayan wannan auren da shekara ɗaya aka haifi najeeb kuma haihuwar najeeb befida wata ukku ba Alhaji idirisu yarasu mutuwar data girgiza gaba ɗaya ilahirin garin maraɗi bama iya ahalinshiba. Bayan rasuwar Alhaji idirisu da wata 5 wani abun tashin hankalin yaƙara faruwa a wannan ahalin Hakan yasa Alhaji Khamis kasa zama a ƙasar tasu ta haihuwa yadawo Nigeria da zama yafara kasuwancinshi da kuɗaɗenda Alhaji idirisu yabashi kafin yarasu domin ko wanensu seda yabashi wadataccen jari ahannunshi kamin Allah yayi masa cikawa…to kobayan dawowar Alhaji Khamis Nigeria bedena waiwayar Niger ba kuma suna zumunci sosai shida Abdussalam sedai waƴannan shekarunne na baya’bayannan komi yataɓarɓare.Alhaji Khamis yana zaune ne agarin Lagos da iyalanshi, inda Ayanzu Hajiya Umma takeda yara ukku najeeb, Munir, sekuma Siyana, mansura kuwa ƴar ƙanwarta ce take riƙo. Hajiya mama kuwa yaranta biyu sajad kusan sa’ar Munir ne wanda Ayanzu yanacan wurin training ɗin soja acewarshi yayanshi zegada, sekuma naja’atu wadda suke kirada ummi.Najeeb tin tasowarshi yatasone shiru’shiru kuma bayasan hayaniya gazafin zuciya wanda baya ɗaukar reni kokaɗan agun ƙannenshi Hakan yasa suka mafi tsoronshi akan dadynsu…najeeb tinyana yaro ƙarami suke tareda Aliyu Haidar kasancewar Aliyu yaron abokin dady ne Hakan yasa shaƙuwarsu ƙaruwa inda sukayi makaranta tare tindaga matakin farko harkawo yanzu da suka zama manyan sojoji aƙasar Nigeria da temakon Abban Aliyu domin shine yadafa musu kasancewar shi menistan tsaro.Najeeb tinda girma yakamashi yazama cikakken saurayi lafiya tafara ƙaurace mishi idan ranshi yaɓace seya azabtu kamar zebar duniya kuma ko ankaishi asibiti basa gane komai akan abinda kedamunshi wannan ciwon nashi yayi bala’in ɗaga hankalin iyayenshi domin babu abinda suke so a duniya sama dashi musamman Alhaji Khamis domin jiyakeyi ko rayuwarshi ze iya bawa najeeb sabida muguwar soyayyar dayake yiwa yaron kamin tarikiɗe takoma ƙiyayya…Hajiya mama mahakan abun yake awurinta domin tafison najeeb duk acikin yaranta bata ƙaunar abinda ze taɓashi sedai gaya wannan ciwon yayimusu illa arayuwarshi….anacikin wannan badaƙalar tacinwon nashi sekuma gawata sabuwa taƙara ɓullowa ta tsanar mata dayayi domin najeeb yayi bala’in tsanar mace arayuwarshi wanda ada kuma bahaka abin yakeba daga bayane yajuye yazama Hakan, kuma abun har ƙannenshi mata yashafa ummi ce kawai keɗan ganin rahamarshi,,,itako auta Siyana ƙaramace batakai budurwa ba shiyasa yake sake mata domin yanajin son yarinyar sosai aranshi.Bayan Hakan kuma wani abun yasake bayyana wanda bakowane yasan dashiba seshi kaɗai wanda abin yashafa wato najeeb ɗin…wannan abun kuwa bakomai bane face aduk kwanan duniya idan yakwanta bacci seyayi wani mummunan mafalki na wasu muta nabinshi sunaso sujefashi cikin wuta kuma matanesu ba maza ba sedai dukkansu fuskarsu arufe take, daga gefe ɗaya kuma yaga wata yarinya rungume da wani abun tana nuna mishi amma taƙi bashi kuma koya bita baya taddata seta ɓace mishi gaya kuma sosai yakejin son abunda ke hannunta ɗin, idan taɓace mishi bayadda zeyi dole se yadawo yana kuka dawowarshi keda wuya sekuma yaganta da wata ƙatuwar dorina duk takore waƴannan dake neman hallakashi idan takoresu seatazo tana mishi murmushi tana rarrashinshi..to kuma acikin wannan mafalkinne yafara ganin maah inda yabi wannan yarinyar tace yadawo ya ƙyaleta zata kawo mishi abin, dayatambeta ita ɗin wacece setace mishi sunanta maah kuma tabashi wani abun yasha wanda yasakashi ƙara nisanta da waƴannan matan masu bibiyarshi domin ada idan suka bishi sesun kusa makamashi sutura yana cikin tsoro da fargaba sannan wannan yarinyar kezuwa ta tarwatsasu amma da maah tabashi wannan abin yasha seyakoma musu killace acikin wani glass duk yadda sukaso surusa glass ɗin sukamashi sesu kasa har wannan yarinyar tazo takaɗasu sedai sukoma gefe suyita kuka. Itako maah tana kallo sedai tace yabarsu babu abinda zasu iya yimishi, ahakan haryasaba da maah sosai acikin mafalkinshi inda razame mishi uwa me rarrashin ɗanta domin sosai maah tasakashi ajikinta tana bashi dukkan kulawa inda kowata damuwarce dashi daya kwanta bacci acikin mafalkinshi zegayawa maahh kuma tabashi shawara kota rarrasheshi kuma koda zefarka wannan abun yafita akanshi domin yasamu mafita agun Allah daƙarin ilimi agun maah ɗinshi…To awannan karon yayi mafalkin sun fasa wannan katangar glass ɗinda maah tayi mishi kuma suna ƙoƙarin cutardasu shida wannan yarinyar wanda bebari naga menene suke ƙoƙarin yimusuba ya hafalka gashi maahh tahana yafaɗa mana Ayanzu😢 to mudai cigabada bibiyarsu aide zamu sani agaba koma minene🤩.To kunjidai wanene mejo najeeb dakuma tsaƙaninshi da maah sabida Hakan mukoma cikin labarinmu kaitsaye 💃Sedai kuma anan zan dakata domin alƙalamina yaɗan huta semun haɗu a Page nagaba zamu ɗora daga inda muka tsaya…!

Back to top button