Gargadar So Chapter 76 By M Shakur
Baba yayi shiru yace “Ibrahima bai riga yace wani abu kan aikin ki ba koda nan gaba zai nuna ki barsa, ki barsa aure yafi aiki Hawwa, Allah yamiki albarka yabaku zaman lafiya, yabaku yara masu albarka, Hawwa ina sonki ina sonki amman yaune ranan barin gidan Baba zuwa gidanki Hawwa” wani kuka Hawwa taji yataso mata, she always wish tai aure tagaji da gidan Baba, takoma nata gidan but yau saitaji bata gaji da gidan Babanta ba bataso tabar gidan Babanta, Ammi ta sharemata hawaye tace “ya isa stop crying now, Allah yabaku zaman lafiya, banson dan kinyi aure gidan hutu ki sangarce Hawwa, ba ruwanki da yan aiki sai when necessary only when necessary, Hawwa ki dafa abincin mijinki da kanki ki basa yaci da kanki, ki gyara makwancinsa karki yarda kiba yan aiki daman gyara dakin mai gidanki, turaren wuta kullum ki kona agidanki safe dare Munnawara tamiki masu kyau duk an kai, ki zama mai tsafta komin aikin office ki dafama mijinki abinci kusan shine first kafin komi, ki tausasa muryanki a inda yake, idan yayi fushi ke karkiyi idan yana fada ki shiru Hawwa take care of yourself ki rike mijinki da kyau yanzu da Allah yabaki don’t let him go ko let him loose ki kamashi da abubuwan da kika iya na koyamiki, keba yarinya bane kinsan menake gaya, idan mijinki yakiraki ga shinfidarsa duk wani kalan gajiya dakikayi daga aiki ki amsashi kije gareshi Allah mimi albarka tashi kije da ni da mahaifinki mun sakeki lafiya mun yafe miki duk wani abu dakika mana jeki fara sabuwar rayuwanki cikeda albarka mu dakuma fatan alkhairin mu” zuciyan Hawwa har wani tsuma take takasa motsi sai kuka atare Baba da Ammi suka tashi sukazo inda take ko Wanne ya tsaya a side nata suka dagota gyaramata lullubi Ammi tayi sannan suka bude kofa sukai waje da ita Hawwa na kuka lokacin around 6 har zuwa kofar gida inda Jama’a suke jiranta, gaban wata sanuwan jeep dal da aka zagaye da flowers suka kaita tashiga kawia ta rungume Ammi da Baba da kyar suka zareta suka sata Ummu tareda Noor tashiga motan, Daddo tashiga gaba aka ja motan, kanninta suka shiga sauran motocin da yan unguwa kowa na so yaje yaga gidan Hawwa aka wuce.Wuraren 7:30 sukakai gidan motan Amarya ne kawai ba’ayi scanning ba sauran motocin saida akai scanning incase wani yadauki mugun makami compound din suka shiga da akai decorating irin na masu kudi ga jama’a acike ga abinci da drinks.Parking motan Amarya akayi gaban wani red flower carpet da aka shimfida body guard suka bude motan daidai Mom Sam da Hajiya Daraja da wasu tawagan manyan classic matan nera biyeda su faram faram suka gaisa da Daddo da Umma sukace afito da Amaryanmu tazo tafara gaida Maman Mijinta kafin akaita barayintaJuyawa sukayi suka fito da Hawwa ahankali wani sanyi Hawwa taji tana tuna memories nata na gidan nan which first one din is kidnapping na Noor second one din is rannan datazo daukan motanta taga wata na kissing Khaleel tako’ina Mom Sam tace “Masha Allah our beautiful bride” suka rike Hawwa da kanta ke kasa cikin lullubi aka wuce tawagan Hawwa na wucewa suna binsu har Side na Mom.Mom na zaune kan wata hamshakiyan kujera tayi gayu harda makeup na bala’i ta zuba gwalagwalai awuya da hannu hannunta rike da bowl na fruits spa workers nata guda biyu sanye da uniform na matsa mata kafa aka shigo da Hawwa Hajiya Daraja tace “ga yarki an kawo miki Hajjaju” Daddo tace “kibiya kudin ganin fuska” aka kwashe da dariya Mom tabisu dawani irin kallon takaici but tuna maganan Khaleel ta daure takalli PA ta tace “basu konawa sukeso in any currency” bude wani jaka dake hannunta PA tayi tazo gaban Daddo tashiga zuba mata bandır bandır Daddo tace “ke ya isa” Mom Sam tace “bari mubude fuskanta” Yaye lullubin tayi fuskan Hawwa ya bayyana Mom ta tsareta da kallo kan Hawwa na kasa bayabo ba fallasa tace “welcome home” kan Hawwa akasa tace “akaita side nata” aka buga ayiriri aka fita Mom tabisu da mugun kallo taja mugun tsaki alwala aka.Alwala aka farasa Hawwa tayi sannan aka shigar da ita side nata dake kamshin sababbin abubuwa babban mansion ne da dakunan ciki dasukai 10, duplex ne akwai elevator ga staircase gidan yahadu akwai falo kusan uku but main falon kayan designer na Khaleel ne, sama aka wuce da ita wasu yan kauye suna shiga lift yakaisu sama Hawwa aka bi bene da ita, wani daki suka bude wanda furnitures nasu ne aciki kuma yayi kyau sosai dan sun sai mata kaya mai kyau a all this turkish furnitures company bawai na Nigeria ba zaunar da ita Umma tayi kan gado Munnawara data biyosu tace “tashi kiyi salla zan baki magunguna” share fuskanta tayi tawuce tashiga bayi ya Allah bata taba ganin bayi mai kyauAlwala tayi su Hafsa suka shiga kunna turaren wuta kowa murna yake cikinsu Yayarsu tasami gidan hutu jibi kalan gidan da Hawwa take ciki,Abinci aka shiga kawo musu ma’aikata da uniform kawai ke safa da marwa a flat din, salla Hawwa tayi wata makeup artist tashigo tazo mata makeup akwai event Hawwa kawai tahau kuka wai tagaji da kyar su Umma suka lallashi ta aka mata makeup ta tashi tai sallan isha’i sannan aka shiryata cikin wani lafayan yan maiduguri ashe Excellency dan maiduguri ne, wai wushe wushe za’ayi welcoming nata around 10 akace sufito kan Hawwa na kasa kunya takeji suka fito an cika compound din ga Khaleel zaune gaban stage din cikin wani malum malum sai kallonta yake kaman yayi shekara bai ganta ba yaga duktai zuru zuru and she looks tired and even scared yanzu ne ta yarda sunyi aure sosai, kawota sukayi har wajensa yatashi ya karbeta yana murmushi murya chan kasa yace “you look so sad sabida baki ganni tunda kikazo bane” dan hararanshi tayi yasake mata murmushi kawai yaja hancinta yace “smile ita sunna” akahau ihu da sauri yakalli crowd din yama manta suna gaban mutane zama sukayi aka fara event din sai around 1 aka gama Khaleel yarike hannunta yace “tunda zasu kwana muje side dina mu kwana” fizge hannunta tayi daga nashi tace “don’t even go there” tsayawa yayi yana kallonta yace “to muje namiki massage saiki dawo kin gaji” makemai kafada tayi agajiye duk yana kallonta saikuma yace “marowaciya” kin kulashi tayi daidai su Hafsa sunzo wajen kawia tabisu suka tafi side nasu yana kallonta Sam yazo wajen yace “munafuki you’ve fallen deeply kasa amaidasu gıda kayi amarcinka mana” kaman zaiyi kuka yace “kunyansu nake lemme just be patient gobe kowa zai tafi ahhhhh”.Wankan ruwan turare akasa Hawwa tayi kawai ta chanza kaya tabi gado ahaka tai bacci tanajin hayaniyan yan uwanta sama sama washe gari da safe suka tashi aka shiga aiki ana kara gyara komi ana turara ko Hawwa gabanta sai fadi yake tuna yanda zasu tafi anjima.



