Hausa novels

Halysaah Page 68 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 68…Khaleesat dake karatu da Laptop dinta ta juya tana kallonsa, a takaice yace “Don’t look at me that way, ki dau duk wani abinda zaki bukata yanxu zaki koma dakin Jay don muna da baki a gidan….” Ko rufe baki bai yi ba aka bude kofar dakin, ta madubin dakin yake kallonta don tsayuwa tayi bakin kofa tana kallon Khaleesat with mouth agape, Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “Ina yini….” Aunty ta karaso cikin dakin da mamaki tana kallon Ajay tace “Junaid? Wacece wannan kuma?” Ba tare da Ajay ya juya ya kalli inda take ba a takaice yace “Kanwar Salem” da wani expression Aunty tace “Kanwar Salem? Me take yi a gidan nan? Kuma a cikin daki zaune a saman gado?” Sai a sannan Ajay ya juya, looking at her in the eyes yace “The apartment she was staying was sold out yesterday, and she is homeless, so she is here for today before moving to her new apartment tomorrow….” Aunty tace “Da iznin wa kayi hakan? Dama gidan ka ne nan din da zaka yanke hukunci kanka tsaye kamar me gidan? I can’t remember his Highness saying this house is urs in anyway Junaid, baka da right, sannan iyayenta da suka turota karatu basu nema mata wani alternative ba sai kai sarkin Hausawan Nigeria dake Baltimore? Beside ban ga ta inda take kama da Salem ba, Salem da yake baki me ya hadasa da wannan farar yarinyar? karya kake yi daya daga matan banzan da kake iskancin ka da su ne a kasar nan, ka zata duk bamu san abinda kake yi ba ne?” Calmly Ajay yace “You can say whatever, kawai dai ni dai i also can’t remember Abba saying we are to share this house with you and ur visitors, saboda ni da Jawwad Abba ya siya gida a garin nan ba don kowa ba, don haka ban ga dalilin da za ki dinga zuwa da wasu mutane can babu notice ba ki maida mana gida gidan saukan baki, kaf Massachusetts babu hotels da dole sai kin taho Maryland za ki samu masauki? Beside all this… u are not even in the rightful place to tell me what to do and what not don da sunana da na Jawwad Abba ya siya gidan nan, don haka babu ruwanki da duk wanda zan kawo gidan, since you can’t do without intruding, ki zo kiyi intrusion dinki in peace kiyi tafiyarki without questioning me….” Aunty da ta bude baki tana kallonsa tace “Zagin nawa da ka saba zaka yi Junaid? Ni kake gaya ma bakaken magana? Rashin kunyan da ka saba yi min zaka yi a nan ma?” Ajay yace “Whatever, all i know is that u can’t just be appearing in here without notice tare da wasu mutane can kina inconveniencing din mu kina sa mana ido” Wani murmushi kawai tayi ta kalli Khaleesat sannan ta juya ta fita daga dakin, gaba daya jikin Khaleesat yayi sanyi ta kasa motsi a inda take, after few seconds ta sauka daga kan gadon tana kallon Ajay da ya kafe ma dressing mirror ido yasan fitar da tayi Abba zata je ta kira, cikin sanyin murya Khaleesat tace “Why will u speak to her that way Ya Junaid?” Ya dakatar da ita fuska daure yace “Ba ruwanki Malama, kin san ta ne?” Khaleesat ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, ya juya ya fice daga dakin yana birkita gashin kansa, ga wani zafi da yake ji, where is he even going to start explaining this to his dad for the second time, gashi Jay baya gidan just him and the lady in the house, wani bayani zai yi ma Abba da zai yarda da shi? ɓangarensa ya nufa ya zauna gefen gado ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi, in mahaifiyarsa ce ai sai dai su kashe su rufe tare da ita without her involving his dad in this issue, infact baza ma ta so wani yaji ba, he felt soo emotional, Aunty na komawa downstairs ta zauna kan kujera ta jawo jakarta ta ciro wayarta, Hajiya Usaina dake kallonta tace “Ya naga ranki a bace Fulani?” Aunty tayi wani murmushin takaici tace “Bari dai inyi waya da mai martaba tukunna Usaina” Tana fadin haka ta tafi dakin da take sauka ta tarar da jakadiyarta a ciki tana ta faman goge goge duk da dakin fess yake, zata fita Aunty ta mata alamar ta ci gaba da abinda take, sannan ta zauna kan kujera tayi dialing number mai martaba tana girgiza kafa at the same time tana fatan Allah ya sa ya samu damar daga kiran don zuwa yanxu dai tasan yana ɓangarensa shi kadai, ai ko babu jimawa ya daga kiran, bayan sun gaisa cikin ladabi da kwantar da murya tace “Allah ya taimake ka ya ja zamaninka, mun iso Maryland babu dadewa yanxu” Daga daya bangaren yace “To maa sha Allah fulani…” Ta kara yin kasa da murya tace “Amma Allah ya ja zamaninka ban ji dadin abinda na zo na tarar a gidan nan ba” Shiru Mai martaba yayi bayan yaji me tace, don tana fadin haka babu abinda ya fado masa sai abinda ya gani dakin Ajay kwanaki da ya sauka Baltimore, Jin Mai martaba yayi shiru Aunty tace “Ko kana tare da baki ne ranka shi dade babu sararin mu yi magana?” Calmly Abba yace “Ina sauraron ki” Aunty ta gyara zama tace “Mace na zo na tarar a dakin Yarima cikin wani yanayi mara dadin fade, hankalina yayi matukar tashi ranka shi dade, na dimauce ba kadan ba da abinda idona ya gane min, ban ji dadin hakan ba ko kadan wallahi, kuma da alama ba wannan bane karo na farko, ya saba yin hakan, Allah Ubangiji ya shirya mana su kawai” Mai martaba yayi shiru don sosai yaji abinda ta fada ya dake sa don har sai da ya jingina kansa da kujeran da yake zaune, tayi kasa da murya tace “Amma ba komai ranka shi dade kar hakan ya sa kaji babu dadi a ranka ko kuma ka damu, in sha Allahu idan na dawo sai mu san abun yi, mu san inda za mu billo ma lamarin don baza mu zuba ido a ci gaba a haka ba, kaga wannan big slap to our faces ne idan aka samu labarin abinda yake yi a kasar nan, hakan zai zubar mana da reputation din masarautarmu ne kawai, shi yasa kwanaki nace maka a samu yarinya me hankali da nutsuwa er manya a aura masa ko da kuwa ba er gidan sarauta bace, sai naga kamar hakan bai gamshe ka ba tunda baka ba maganar tawa muhimmanci ba na lura baka son yi masa dole ne, ni kuma abinda yasa na kawo wannan shawaran shi ne saboda shi Yarima ba kula yan matan yake ba a gida Nigeria” Cikin nutsuwa mai martaba yace “Bangaren nasa kika je?” Aunty ta ɗan fara kame kame tace “Ehh can na je ranka shi dade, gani nayi tunda muka shigo gidan ga dai motarsa amma shiru bamu gan sa ba, da yake kwanaki ai ya ɗan yi zazzabi saboda weather sai nayi tunanin to ko baya jin dadi ne, sai na karasa bangaren nasa, shi ne fa idona yayi mummunan gamon nan” Mai martaba yace “If possible try conversing with the lady u saw ki ji er wace jaha ce a Nigeria, ina son sanin background dinta, just Converse with her Fulani….” Aunty tayi shiru bayan taji me Mai martaba yace, can tace “Ranka shi dade ai ba er Nigeria bace matar, baturiya ce fa, kuma irin tsofaffin turawan nan, da kyar ma in bata haifesa ba” Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace “Na fahimta” Aunty tace “Yanxu dai idan na dawo za mu tsara komai ur Highness, ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu anyi na karshe, we will put a stop to this soon, kuma ko makusantan ka na fada don Allah kar ka gaya ma wannan magana, don ba magana bace da ya kamata ace ya fita” Mai martaba was quite, don tunanin da yake yi ma shi daban, daga karshe Aunty tayi masa sallama ya katse wayar, tana kallon jakadiyarta dake zaune kasa tayi murmushi tace “Mace na samu a dakin baƙi, amma ban san tun yaushe take zaune gidan ba ya dai ce min jiya ta zo gidan, sannan babu cin mutuncin da ya mance bai min ba” Jakadiya ta kara bajewa a kasa tace “Ja’iri, gaskiya ya kamata wannan karan ki dau mummunan mataki akan sa ranki shi dade kar ki dau lamarin da wasa, abubuwan da yake maki sun isa haka, duk baya ganin mutuncin ki kuma wannan abu na saka ni damuwa uwar gijiyata, yanxu dai kamata yayi ki kira daya daga ma’aikatan gidan ku kebe ki tambayesa ki ji tun yaushe ya ajiye yarinyar a gidan nan…” Aunty tayi wani murmushi tace “Kin kawo shawara kuwa….” Mikewa tayi ta fita daga dakin Jakadiya na jero mata kirari…. Bayan wani lokaci Ajay ya fito dakinsa ya tafi dakin da Khaleesat take, without looking at her yace “Ina jiran ki downstairs” Daga haka ya fita daga dakin, har zai sauka kasa ganin su Aunty a parlon ga uban kayan ciye ciyen da aka baje masu a tsakar parlon, sai kawai ya tsaya a corridor, a hankali Khaleesat ta mike tsaye ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fito, yana jin alamar ta fito ba tare da ya juya ba yace “Mu je, kuma ban ce ki ce zaki gaida kowa Downstairs ba” Daga haka ya fara sauka kasa tana biye da shi a baya jiki a sanyaya, tun da suka sauko Aunty da kawarta da Afrah ke kallon Khaleesat, Ajay dai ko kallonsu bai yi ba ya nufi kofa Khaleesat na biye da shi ita ma bata yarda ta kalli direction din su ba, gun motarsa taga ya nufa ya bude ya shiga, ta karaso gun motar ganin bata shigo ba ya daure fuska yace “Baza ki shigo ba?” A hankali ta bude seat din ta shiga, yana kallonta yace “Haka kika fito baki dauko komai ba?” Tayi shiru, sai kuma tace “Ai baka ce min in dau komai ba” Tsaki ya ja ya bude motar ya fita ya koma cikin gidan, ita dai ta bi sa da kallo, dakin da take ya koma ya dau laptop dinta da charger sai wayarta shima da Chargern sa sannan ya fita daga dakin yayi locking kofar yanda ba wanda zai bude ya sauka downstairs, nan ma su Aunty suka bi sa da kallo, Afrah kamar idanuwanta za su bi sa har compound din…. Har Ajay ya isa apartment din Khaleesat bai ce mata komai ba, ita ma dai tayi shiru da tunani iri iri a ranta, kana ganinta kasan duk a sanyaye take, bayan sun sauka motar ya nufi entrance din shiga apartment din ya ciro makullin a aljihunsa ya bude ya shiga parlon, ta bi bayansa. Jay na zaune gaban mai martaba kansa a kasa yana jin duk abinda yake cewa, Cikin nutsuwa mai martaba ya ci gaba da cewa “I am so disappointed in you Ahmad, kana kallon abinda ɗan uwan ka ke yi amma ka kasa gaya min, i am really disappointed, even if you can’t tell me directly there are other ways to approach me and i will understand you, to yanxu kana tunanin rufa masa asiri kake yi yana aikata sabo kenan?” Jay ya dago kansa a hankali, after few seconds murya can kasa yace “Abba ba abinda ku ke tunani bane, i promise you Junaid is doing nothing that is against the teaching of Islam, ba ma shi da lokacin da yake kula mata balle har yayi wani doguwar mu’amala da su, ka yarda da ni Abba bazan maka karya ba” Mai martaba dake kallonsa yace “Na je Maryland na ga mace a dakinsa, Auntynku ta je jiya and same thing happened, ta yaya zan yarda da maganar ka Ahmad? What sort of silly coincidence is that?” Jay yace “A gafarce ni Abba, amma nasan ba a dakinsa Aunty ta ga mace ba sai dai a dakin baki, shi Junaid wani irin mutum ne wanda idan yaga mutum stranded be it namiji ko mace bai ki ya ajiye ko ma waye a gidan ba har zuwa sanda mutumin zai yi sorting kansa out, you can confirm this from the workers of the house, wallahi halinsa kenan ba wai don ya hada komai da wa enda yake taimaka ba, Abba kasan bazan maka karya ba wai don in rufe laifin da kake tunanin Ajay ya aikata don in nayi hakan nima Allah bazai bar ni ba, Billah i am telling you nothing but the truth Junaid ba shi da hadi da koma wacece Aunty ta gani a gidan nan” Abba yayi shiru, after a while yace “Na ji, kuma na yarda, but i am afraid hukuncin da na tsara a kansa bazai masa dadi ba, but he still have to accept it cause hakan kadai ne zai sa in samu nutsuwa da kwanciyar hankali” Jay sai kallon Abba yake, a hankali yace “Wani hukunci kenan Abba?” Abba yace “Na yanke hukunci zan masa aure and he just have to accept ko ma wacece matar, you are not excluded also, duk da kai akwai maganar ka da Hadiyah…..” Jay ya kwantar da murya yace “Don Allah kayi hakuri Abba, we have just few months remaining da muke saka ran za mu gama karatun nan da muke yi, bamu yi tunanin za mu kawo har warhaka bamu gama ba, plss Abba a saurare mu har zuwa sanda za mu gama, in just 2 to 3 months” Abba yace “Kwanaki ma haka ku ka min dadin bakin nan, kun maida ni kakan ku” Jay yace “Kayi hakuri Abba, mun san ka bamu dama sosai and this will be the last in sha Allah” Murmushi kawai Mai martaba yayi yana kallonsa, kowa yasan sa a mutum mai magana daya, amma ga yara sai juyasa suke yanda su ke so, after a while Abba yace “Yaushe zaka koma Amurkan?” Jay ya sunkuyar da kansa yace “Watan da za mu shiga in sha Allah” Abba yace “Allah ya kai mu” Khaleesat na zaune saman darduma wajen karfe shidda na yamma, tun da tayi sallan la’asar take zaune kan darduman take karatu a laptop dinta don in a month and few days time za su fara Spring semester exams din su, wayarta taji yayi vibrate alamar shigowar text, ta jawo wayar tana duba text din taga number Ajay, “Come out” iya abinda ya tura mata kenan, ta ajiye wayar ta mike ta dau Hijab dinta ta saka, tunda ta dawo apartment din nata kusan kullum zai zo wani lkcn ya gama zamansa a motarsa da yake parking a garage sai kuma yayi ordering ride ya bar motar tasa a garage din ya tafi, wani lkci kuma ya shigo parlon nata bazai dai dade ba zai fita, kuma ba wai magana yake yi mata ba, da ta lura bai son magana iyaka kawai ta gaishesa ta koma ta ci gaba da abinda take, wani lkcn ma sai ta dawo school zata ga alamar ya zo apartment din idan taji kamshinsa a parlor, duk ta lura for security purpose yake hakan, har ma da barin motarsa da yake yi a garage din apartment din, don ko da ya zo da safe ya dau motar ya tafi inda za shi to zai maida nan yayi parking da yamma sannan yayi ordering ride da zai kai sa gida, and she really appreciate all this that he is doing for her safety, don farko da ta dawo gidan kusan kullum sai tayi kuka gashi bata iya bacci da daddare don gani take kamar at anytime Aymaan zai iya zuwa gidan, gradually kuma ta hakura barin da ta ga Ajay na yawan zuwa gidan, amma fa duk wannan abubuwan ba shi ne yasa bata tunanin Housemate dinta ba, babu ranan da zai zo ya fadi bata yi tunaninsa ba, wani lkcn har da kukanta ta rasa dalilin hakan, zuwa yanxu kam ta ma hakura ta dena masa magana ta WhatsApp din tana ganin kamar takurasa take maganar da take masa duba da yanda yake amsa mata kamar baya so, tana bude kofar apartment din bayan ta sauka downstairs taga ledojin dake ajiye bakin kofar, sai kuma ta kalli garage ta gan sa zaune cikin motarsa, sai da ta fara shiga da ledojin parlor sannan ta fito ta nufi gun motarsa tana kallonsa ta gaishesa, ya bude motar ya sauka ya amsa without looking at her ya kulle motarsa, sai kuma taga ya nufi lyft din da ke jiran sa, tana tsaye tana kallo har ya shiga sannan ta juya ta koma apartment dinta ta kulle kofar da makulli, kayan shayi ta gani a ledojin da ya kawo mata, gwangwanin madara manya biyu, milo biyu, kwalayen sugar, Lipton, coffee powder, da kuma chocolate, har da bread manya uku da cookies iri iri, kilan ya shiga kitchen ne yaga babu madara shi ne ya siyo mata, kuma lokaci ne bata samu ba tana ta son zuwa taje tayi shopping din kayan shayin…. Bayan kwana biyu Khaleesat na isa school Safiyyah dake zaune lecture hall ta dinga mata wani kallo tace “Wai don Allah baza ki dena yafa manyan mayafan nan ba kina kunyata ni Khaleesat, kin fa gama wannan kadararren iddan ba wai baki gama ba, ko sau biyu za ki yi masa iddan ne?” Murmushi kawai Khaleesat tayi tana kallonta tace “Ni na ce maki na gama?” Safiyyah tace “Ai shi yasa na tambaya ko sau biyu za kiyi don ina nan ina taya ki lissafi wallahi kin gama, duk na kagu inga kin fara cin gayu kina zuba zawarcin ki son ranki, ai yanxu kuma ba da bane kin shiga wani level daban” Khaleesat tace “To bakya lissafi dai dai kuwa…” Safiyyah tace “Wallahi ina yi sai dai in kece bakya lissafin” Khaleesat bata tanka ta ba ta nemi waje ta zauna don yanxu wani sabon gayu Safiyyah ke ji a makarantar ita ga final year student, ko ta zo da mayafi sai ta saka a jaka tayi ta yawo da hula kawai kamar er Enugu, ko kuma tayi azababben English dressing ta daura karamin dankwali a kai, ita dai har ta gaji da yi mata magana ta zuba mata ido, a tare suka koma apartment din Khaleesat ranan don danwake Safiyyah tace zata masu, sai kusan yamma likis Safiyyah ta bar gidan shi ma Mustapha ne ya isheta da kira, Khaleesat na kitchen ta gama wanke duk Utensils din da Safiyyah taki wanke mata tana goge gogen kitchen din taji an bude kofar apartment din, dama tasan dole zai zo tun da taga ya mance charger dinsa a parlor alamar da taje school ya zo apartment din daxu, a hankali take wanke hannunta a pampon kitchen din trying to be sure of what she is perceiving, gently tayi patting hannunta jikin towel din kitchen din tana goge ruwan hannunta, sai kuma ta juya, sai da numfashinta ya tsaya for some seconds tsabar yanda gabanta ya fadi, yana jingine jikin bango kusa da kofar shiga kitchen din ya rungume hannu yana kallonta, ta sunkuyar da kanta, sai kuma ta nufi kofar kitchen din zata fita zuwa parlor, hannunta ya kamo yana kallonta with smile on his face, bata san sanda ta fashe da kuka ba zata kwace hannunta ya jawota kusa da shi murya can kasa yace “Halysaah” Hawaye kawai ke zuba idonta ta kasa kallonsa, slowly ya rungumota jikinsa murya can kasa yace “I am sorry” Bude kofar parlon aka yi, Jay yayi saurin saketa amma tuni Ajay ya shigo, sau daya ya kallesu sai kuma ya sauke idonsa ya tafi ya dau charger dinsa ya juya ya fita daga parlon….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button