Ruwan Zuma Page 47 Hausa Novel
(47) K’arfe hud’u da rabi Sheikh Nafi’u Kano ya fara wa’azi wanda ake kallo Live a gidan television d’in Nagari na kowa, wanda wa’azi ne game da hukunce-hukuncen sallah yana had’awa da misalai. K’arfe shida tana cika ya dakata akan cewa wata sati zai k’arisa sannan a shiga wani babin. Alaramman shi ne ya fara karanta tambayoyi shi kuma yana amsawa. Tambaya ta uku aka fara karantawa kamar haka, ‘Assalamu alaikum, Allah ya biya Mallam da alkhairi ya kuma bamu ikon gyara halinmu da ibadunmu Amin. Mallam ni na kasance babbar mace wacce ta bawa shekara arba’in baya, hakan yasa da mijina ya nemi in haihu na k’i amincewa har Allah ya nufeni da samun ciki na kuma nemi in zubar, naje asibiti da niyyar a zubar amma Allah ya canja mini ra’ayina naji ina son cikin. Mijina ya zo asibitin ya samu ana mini scanning sai ya d’auka zubar da cikin nayi yayi fushi ya tafi bayan ya sakeni saki d’aya, Mallam don Allah a rok’eshi ya dawo gareni don wallahi har yanzu cikin yana jikina ban cire ba. Mallam shi almajirinka ne saboda wa’azinka baya wuceshi kowanne sati. Nagode.’ “Wato Mallam wasu matan basa amfani da hankalinsu.” Wannan shine abunda Mallam Nafi’u ya fara fad’a fuskarsa babu alamun wasa. Mutanen da suke cikin masallacin suka kaure da cewa, “Allah ya bada lada. Allah ya gafarci Mallam. Allahu Akbar.” “To gaskiya ne mana. Ina hankali a cikin maganar k’in haihuwa don kawai kin fi shekara arba’in? Rashin lafiya ne zai hanaki haihuwa ko kuma don tsabar raina Rahamar Allah ne? Gashi nan kina gani wasu neman haihuwar suke yi amma har su mutu Allah baya basu, amma ke saboda rashin godiya da jan ido shine kike neman kashe halittarsa daya baki ba tare da ikonki ko taimakonki ko na sisi ba! Ba zan ce ya dawo ba, kuma ko ya dawo ni ina bashi shawaran ya k’ara aure tunda ke cikinki bana haihuwa bane sai na tara abinci.” “Allahu Akbar.” Aka k’ara tada kabbara. “Yanzu kuma sai kaji tace bata son kishiya.” Fad’in Mallam Nafi’u yana kallon mutanen masallacin. “To bakya son kishiya, bakya son haihuwa wa zai zauna dake a haka? Mata kuji tsoron Allah domin wata mijin baya sani take zuwa take zubar da cikin, da ke da mai kashe mutum da wuk’a wallahi duk hukuncinku d’aya kuma zaku gane baku da wayo idan kuka tsaya a gaban Allah ranar gobe k’iyama. Kuma shin kina da tabbacin yaran da kika tara zasu rayu ne? Wallahi komin yawansu Allah zai iya d’aukansu a lokaci guda idan ya so. Sau nawa kike jin iyali miji, mata da ‘yayansu sun mutu a dalilin hatsari, gobara, 6arayi masu fashi da makami da sauransu? Kin tabbatar ke da iyalin naki kun tsira daga dukkan wad’annan jarabawar ne? Kar ku bari rud’in duniya da wasu dalilai marasa kan gado su jawo muku fushin Allah. Wallahi kuji tsoron Allah ku sani cewa yana sane da duk abunda kuke yi na 6oye da kuma na sarari. Alaramma karanta tambaya ta gaba.” Laila da take zaune a falonta tana jin wa’azin jikinta yayi matuk’ar sanyi game da kalaman Mallam Nafi’u. Ita yara biyu gareta wanda d’ayan hanyar daya d’auka bata tunanin ko ta mutu zai mata addu’a, sannan ina take da tabbacin Sabrin zata kai har tsufanta ko kuma zata ci moriyarta? Wato Allah yana sonta kuma yana mata Rahama da tanadi amma ita duk bata gani sai neman fushinsa da take yi a kanta. Hawaye ne ya taru a idanunta tana istigfari tare da addu’ar Allah yasa shirin su da Alhaji Abdul yayi aiki, wato Haydar yaji wannan sak’on ya dawo gida. Tana ji a ranta cewa daga yau asabar zuwa gobe lahadi zai iya dawowa a kowanne lokaci matuk’ar ya saurari wa’azin. Tana zaune har aka gama aka fara kiran sallah magrib ta tashi tayi alwala tayi sallah ta k’ara gyara fuskarta domin har kwalliya tayi domin dawowar Haydar, a falo ta k’ara zama tana waya da Sabrin wacce duk nauyin Laila Beauty ya dawo kafad’unta, “Mama yaushe su Ummii zasu tafi Maiduguri? Kwanaki Uncle Mas’ud ya zo dubani yake bani labari.” “Ina ganin nan da kwana uku ne, ranar Tuesday ko Wednesday. Zaki bisu ne?” Laila ta mata tambayar cikin tsokana. “Ina son ganin Yaya Abul ne Mama. Kullum idan na tunashi sai naji babu dad’i a zuciyata.” Tayi maganar cikin sanyin murya cike da damuwa. “Kici gaba da mishi addu’a ki kuma rage damuwa a ranki. Insha Allah komai zai zo ya wuce tamkar ba’ayi ba. Batun zuwanki kuma ki bari sai na tashi zuwa mu je tare. Wannan zuwan su Ummii daban ne ba wai na duba Abul bane.” “Kaala Abdi zai rasa inda zai da kanshi idan ya ganta.” Sabrin ta fad’a cikin farin ciki. “Don Allah waya fad’a miki?” Laila ta tambayeta cikin mamaki domin sun 6oye bayyanar Ammi ga mutane da dama bayan Ammin tace haka take so. “Uncle Mas’ud ne ya fad’a mini tunda ke baki yarda dani ba kin 6oye mini. Mama hankalina ya k’ara kwanciya akan aurenki da Uncle Haydar tunda naji cewa su jininmu ne. Allah ya bayyanashi ya kuma shiryi Yaya Abul.” Laila kasa cewa komai tayi illah, “Amin.” Suka yi sallama ta kashe wayarta tana cewa inama Abul ya yarda da aurenta da Haydar kamar yanda Sabrin ma ta yarda dashi, ai da matsalolin su da dama basu faru ba. Har aka idar da sallah isha Laila na zaune ta kasa motsi domin kar Haydar ya dawo ya buga k’ofa bata kusa. ‘To in kuma a wani gari can nisan duniya yake fa?’ Wata zuciyar ta raya mata wanda ta samu amsarta nan take wato, in dai a wani gari yake zai yi wuya ya iso yau sai dai gobe ko kuma jibi. Zata jirashi, zata kuma cigaba da addu’a har ya bayyana ta nuna mishi soyayyar da bata ta6a mishi irinta ba. Tana tashi zata shiga d’aki tayi sallah taji ana kwankwasa k’ofa wanda yasa tayi saurin isa ta bud’e tana fatan Haydar d’inta ne. Ganin Mas’ud da tayi yasa jikinta yayi sanyi tace, “Kai ne?” “Dama waye kike tsammani?” Ya mayar mata da tambaya yana shigowa cikin falon bayan ta bashi hanya. Bata ce komai ba har ta zauna shima ya bita ya zauna yana karantar yanayinta. “Wa kike jira Kalti? Sannan yau na ganki different.” “Ka ga nayi kwalliya ko?” Ta tambayeshi tana murmushin dole wanda iyakarsa fatar baki. “Yes, kin yi kwalliya.” Ya amsa babu 6oye-6oye. “Ina son in fad’a maka wani abu amma kar kaga laifina domin ni d’in mai nema da lalu6e ne a cikin duhu.” Gyad’a kanshi kawai yayi yana kallonta kwakwalwarsa ta kasa bashi abu d’aya da take son fad’a mishi. Ko dai tafiyan Haydar ya fara rud’ata ne? A nan Laila ta bashi labarin yanda ta kira Alhaji Abdul da kuma tambayar da suka aika ga Mallam Nafi’u, aka karantashi ana uku bayan dubbannin tambayoyin da ake jiran amsarsu tun na wancan satin. Shiru yayi bai ce komai ba har na tsawon minti d’aya yana kallon gefe yana tunani. Ganin shirun yayi yawa yasa ta dubeshi fuskarta cike da damuwa tace, “Nayi kuskure ko?” “Ko kad’an. Duk wanda yake cikin hali makamancin naki abunda zai yi kenan, zai kar6i duk wani opportunity da yazo gurinshi don ganin ya cimma nasara. Allah yasa hakan ya zama sanadiyyar samun shi.” Ya fad’i hakan yana kallonta fuskarsa babu alamun 6acin rai ko kad’an. “You are not mad at me?” Ta k’ara tambayarshi domin kamar bata yarda da furucinshi ba. “Why would I be mad at you Kalti? All you are trying to do is to bring your husband back. Sai dai nan gaba duk abunda zaki yi let me know muyi shawara tare, kuma ba zan hanaki duk hukuncin da kika yanke ba, ko na nuna shawaran naki bai mini ba I will support you a yi yanda kike so.” “I’m sorry ban fad’a maka da wuri ba, naga yanda ka d’auki Alhaji Abdul da fushi yasa nayi tunanin baza ka ta6a yarda in yi magana dashi ba.” “You are right, na tsaneshi.” Shiru suka yi na wani lokaci sannan Mas’ud ya dubeta yana cewa, “Dama nazo miki sallama ne gobe zamu tafi Maiduguri dasu Ummii, sannan jiya an kama Madu akan kud’in marayun daya cinye. K’arshenta gidan da yake ciki da wasu k’adarorinshi za’a sayar a biya marayun kud’in gadonsu, wannan labarin da Ummii taji yasa ta nemi tafiya gobe saboda bata son cigaba da zama a gidan haram ana ciyar da ita da haram.” “Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un. Abun har ya kai haka?” Laila shiga cikin rud’u lokaci guda. Gyad’a kai Mas’ud yayi kana yace, “Hajja ma ta kwashi yaran ta tafi dasu gidan iyayenta shekaran jiya.” “Ita kuma menene ya had’asu?” Laila ta tambaya cikin mamaki sanin halin Hajja na hak’uri. “Tun lokacin da ya gane Alhaji Abdul ya nemi Jamila ya kasa zama a gidanshi ya kuma daina basu kulawa, hatta kud’in cefene da wani buk’atunsu na rayuwa ni nake basu idan naje gaishe da Ummii. Dalilin da yasa aka kamashi kuma yaje sayar da shagon daya ragewa marayun ne suka kaishi k’ara aka rufeshi. Abun dai babu dad’in ji kawai don wasu abubuwan ma babu amfanin fad’a.” Dafe kai Laila tayi tana jin bak’in ciki a ranta don ko babu komai Madu yayanta ne, uwa d’aya uba d’aya take dashi. Ko a baya da Hajiya Shatu take kawo mata k’orafin abunda Madu yake yi da kud’in marayun bata san yakai har haka ba. “Yanzu wa zai tsaya mishi tunda kai zaka tafi Maiduguri gobe?” “Abokansa da suka ci kud’in tare kuma suke mara mishi baya su suke kanshi.” Ya bata amsa yana tashi tsaye. “Amma Mas’ud bai kamata mu watsar dashi ba, yana buk’atar taimakonmu.” “Idan zaki yi bazan hanaki ba amma Ummii tace in fad’a miki bata yarda ki fita ba sai da dalili mai k’arfi na rashin lafiya ko neman abinci wanda nasan bazaki nema ba har inje in dawo, kwana biyu kad’ai ni zan yi. Idan Haydar ya dawo kiyi saurin sanar dani don Allah, komin dare zan zo.” Gyad’a kai Laila tayi tana murmusawa don ta lura hatta shi Mas’ud d’in yana d’okin ganin Haydar, ashe ba ita d’aya bace wacce take kewanshi. “Allah yasa ya dawo d’in. Idan ka dawo ka d’auko mini motar Haydar a ajiye a nan.” Ta fad’a tana binshi a baya. Bud’e k’ofa yayi yace, “Shikenan. Ina ganin kafin mu wuce su Ummii zasu zo su dubaki, kiyi tsammaninsu da safe.” Da haka suka yi sallama Laila ta rufe k’ofar ta shiga d’akinta don gabatar da sallan isha. Bayan ta idar ta k’ara dawowa falo ta zauna zaman jiran tsammani, har ta fara gyangyad’i daga zaune bata hak’ura ba. K’arfe sha d’aya da rabi ta farka daga baccin da tayi a gurin zuciyarta na bugawa cikin sauri domin bata san tayi baccin ba, duba agogo ta fara yi tayi salati kana ta mik’e jiki a sanyaye ta rufe falon ta shige d’akinta. Washe gari da safe k’arfe bakwai su Ummii da Ammi suka sauk’a a gidan Laila don mata sallama. Bayan sun gaisa Laila ke cewa, “In kun tafi sai yaushe kenan zaku dawo.” “Sai Mas’ud ya nema mana gurin zama, sauran kayana da suke cikin gidan Madu kuwa zai kai store d’in gidanshi idan ya dawo.” Ummii ta bata amsa. “Ummii wai ke kika hana a bi sawunshi?” Laila ta sake mata wata tambayar don bata so hukuncin da Ummiin ta d’auka ba. “Ni ce, kuma ban yarda wani ya sa6a ba. Suwaiba tashi mu tafi.” Ta fad’i hakan tana mik’ewa tsaye. Ammi da take ta kallon Laila tun shigowarta tayi zamanta tana cewa, “Kuyi gaba zan d’an yi magana da ita.” Sai da su Ummii suka fita sannan Ammi ta dubi Laila wacce kanta ke k’asa ta k’i su had’a ido tace, “Yanda na zo na sameki na kuma lura dake kina cikin damuwa, nasan dole zaki damu amma karki bari yayi yawan da zai jawo miki matsala ke da d’an cikinki. Babu abunda zai fi yiwa Haydar dad’i irin yaji kin lura da cikin nan tamkar yana nan, ki dinga kula da cin abinci domin naga kin rame kamar ba ke ba. Don Allah ki kula ki kuma lura da kanki, Allah ya rabaku lafiya. Wata nawa ne cikin?” Laila kunya taji kamar ta nitse k’asa domin bata yi tsammanin maganar da Ammi zata mata ba kenan. Daburcewa tayi ta fara murmushi nervously tace, “Ya shiga na uku.” “Ikon Allah. Kuma duk wannan lokacin baki sani ba?” Ammi tayi tambayar cikin mamaki domin ai ciki yana k’arami yafi sauk’in cirewa, kenan Laila bata san dashi ba sai yanzu. Wannan karon shiru Laila tayi tana jin nauyin tambayar da Ammi ta mata, wanda ta lura ita kwata-kwata abun bai bata kunya ba. “Tsakanina dake babu kunya ko surkunta Hajiya Laila, ni a matsayin yayarki nake kuma abokiyar wasanki. Kina jina.” “To Ammi.” Kawai Laila ta iya fad’a amma har cikin zuciyarta bata tunanin zata iya daina jin kunyar Ammi. Sannan ta yaya zata iya bud’an baki ta fad’a mata cewa period d’inta bai daina zuwa ba sai wannan watan? Ai abun da kunya wallahi. Sallama Ammi ta mata data lura Lailan ta kasa sakin jiki da ita. Har bakin mota ta rakasu suka tafi tana jin kamar ta bisu itama. Can da rana misalin k’arfe biyu da kwata Alhaji Abdul ya kira Laila ta d’auka tace, “Bai dawo ba.” “Na sani, don Allah karki kashe wayar magana nake son yi dake.” Yayi saurin fad’a daya lura tana son kashe wayar. “Akan me kenan?” Ta tambayeshi tana jin wayar na gundurarta. “Akan Ammi ce. Wallahi tun da ta dawo rayuwar mahaifina ya kasa sukuni yana zuwa gidan Ummii don su gana amma ta k’i sauraransa. Nasan tana mishi hakane duk akan abun da na yiwa Haydar d’anta. Ki fahimtar da ita cewa na canja, wallahi na canja bana yiwa Haydar mugun fata ko mugunta. Ko wani ne ya ta6ashi a yanzu wallahi sai inda k’arfina ya k’are. Ki bata hak’uri kar ta mishi hukunci akan laifin da ba nashi ba, laifin da bai ma san anyi ba sai ranar data bayyana. Don girman Allah ki taimaka mini kar abun ya mini yawa, yana fushi dani don abun da na yiwa Haydar yanzu kuma ya k’aru da cewa Ammi ta k’i sauraronshi.” Ajiyar zuciya Laila ta sauke kana tace, “Yanzu kam Ammi bata nan yau ta tafi Maiduguri don ganawa da mahaifinta. Magana a waya kuma ba zai yiwu ba sai dai idan sun dawo.” “Shikenan, zan fad’awa Baban kawai yaje ya sameta a can gaban iyayenta zai fi mutunci.” “Kar ka kuskura kace ni na fad’a maka.” Tayi warning d’inshi domin bata son koda wasa a san tana waya dashi. “Insha Allah bazan fad’a ba, nagode.” Yana fad’in hakan ta kashe wayarta tana jin zullumi a ranta kan wannan al’amari. Shin ya Haydar zai d’auki wannan maganan wai cewa Alhaji Abdul Yayanshi ne wanda suke uba d’aya? Sannan ya matsayin auren Baba da Ammi yake a yanzu da yake neman ta dawo gidanshi a matsayin matarsa? Yaya Haydar zai yi? Sai da Mas’ud ya dawo daga Maiduguri Laila ta samu labarin duk abunda ya faru a can. Wato Kaala Abdi duk tsufansa sai da yayi kuka yana shafa fuskar Ammi yana cewa ta yafe mishi, itama kukan take yi tana neman yafiyarsa ana basu hak’uri. Sai da ka nitsu ta basu tarihin rayuwarta ta kuma fad’a musu d’anta Haydar shi yake auren Laila, ‘yan uwa sun yi mamakin wannan abun domin shi Kaala Abdi tun had’uwarshi da Haydar lokacin da suka kawo Abul yaji yaron ya kwanta mishi, ganin irin yanda yake k’ok’ari a kan d’an Laila, ashe jikanshi ne bai sani ba. Murmusawa kawai Laila take yi har Mas’ud ya gama bata labari, ya k’arisa da cewa, “Sai dai Abul ne da aka bashi labarin muka kasa sanin halin daya shiga. Daa yana mayar da martani ga mutane cikin rashin kunya amma yanzu duk abunda aka fad’a mishi baya tankawa, kai ko kallonka ba zai yi ba.” Cikin firgici Laila tace, “Don meyasa zaku fad’a mishi? Sannan me hakan yake nufi kenan? Kar duk wahalan da aka sha ya dawo sabo fa!” “Kaala Abdi ne da kanshi yace a fad’a mishi, kuma yace mu rabu dashi kar mu damu.” Gyad’a kai kawai Laila tayi amma zuciyarta na waswasin wannan mataki da Kaala Abdi ya d’auka. Ita a ganinta yafi a ce an bari sai ya nitsu sai a fad’a mishi duk abunda yayi missing na rayuwarsu. Zama gida ya fara damun Laila domin yau wata d’aya da sati biyu kenan Haydar baya nan, a lokacin da suka bayar ta tambaya mai d’auke da cigiya gurin Mallam Nafi’u tayi tsammanin baza a kwana biyu ba zai dawo, amma gashi har yau babu shi babu labarinshi. Alhaji Abdul na yawan kiranta yana tambayar ko Haydar ya dawo, kullum dai amsar d’aya ce. Karshenta cewa tayi ya daina kiranta akan idan Haydar d’in ya bayyana ita da kanta zata kirashi. A daren ranar Laila ce kwance a d’akinta misalin k’arfe takwas da rabi na dare, a yanzu har ta daina hira mai tsawo domin ta hak’ura da jiran Haydar a falo wai ko zai dawo. Sai kuma yanzu ta fara laulayin ciki amma nata na kwad’ayi ne da bacci da kuma son kasancewa tare da mijinta, wanda kullum bata iya bacci sai ta da tufafinsa a hancinta. Kiran wayar Haydar tayi a karo na ba adadi taji an ce wayar a kashe take kamar kullum, cikin saduda ta kira wayan Kaala Abdi tace tana son magana da Abul wanda ta dad’e bata nemi hakan ba. Babu musu Kaala Abdi ya bada wayar aka kai sashen da aka rufe Abul aka mik’a mishi wayar ya k’arba ba tare daya tambayi waye bane. “Abul.” Ta kira sunanshi cikin sanyin murya. “Mama.” Shima ya kirata amma bai k’ara cewa komai ba. “Ya kake? “Gani nan dai.” “Ina fatan ka daina tsanata don na kaika gurin da zaka shiryu?” Shiru yayi na wasu sakanni sannan yace, “Ina mijinki?” Murmusawa tayi wanda aka ce yafi kuka ciwo tace, “Ya tafi ya barni Abul. Nasan zaka ce ‘I told you so’ amma laifi nayi ya yanke wannan hukuncin.” “Na san komai Mama. Duk abunda ake ciki na sani an fad’a mini. Mijinki jikan Kaala Abdi ne sannan k’anin Alhaji Abdul ne. Yaushe zaki fad’a mini wannan babban al’amarin Mama? Shin har yanzu baki yarda dani bane kamar yadda kika kasa yarda dani a baya? Zaki iya tuna abunda ya fara tunzurani na bar gidanki? Saboda kin mini k’azafin d’aukanki a hoto ne tare dashi wanda wallahi wallahi bani nake yi ba. Idan nace kin tsaneni sai kice karya nake yi amma gaskiya ne bakya sona tunda har yanzu baki yi trusting d’ina ba.” Tashi zaune Laila tayi domin rabon da Abul ya mata magana irinta masu hankali har ta manta. Wai yau itace take magana da Abul babu zagi babu bak’ar magana? “I’m so sorry Abul, amma nayi hakan ne don karka sake tunzura tunda bana gane me yake pushing d’inka. Sannan zan k’ara baka hak’uri kan d’aura maka laifin da nayi alhali ba laifinka bane duk na Alhaji Abdul ne.” A nan Laila ta bashi labarin komai bata 6oye mishi ba saboda tana son gaining trust d’insa. Shiru yayi yana sauraranta har ta ida aya sannan ya fara magana cikin tsananin fushi har yana huci yace, “Basu fad’a mini cewa duk makircin Alhaji Abdul bane Mama, ki fad’awa Kaala Abdi ya sakeni in dawo in kasheshi. He dared used me as a bait don ya sameki, na zama tamkar pawn a wasansa. Wallahi sai na kasheshi.” Ya k’arisa maganan cikin k’araji yana hawaye. Tsoro sosai ya bawa Laila wacce ta fara kiran sunansa tana cewa ya nitsu yayi shiru amma inaa! Sai hauka ya k’ara yi k’arshe wanda aka aikan ya kwace wayar ya fita ya kulleshi yaje kiran Kaala Abdi wanda shi kad’ai yake saisaitashi in ya fara wannan abun. Kafin Kaala Abdi ya zo Abul ya yiwa kanshi rauni da jikin k’ofa domin buga kanshi yayi har sai da ya fashe. Sai da aka wanke mishi ciwon ya nitsu yayi bacci sannan Kaala Abdi ya kira Laila wacce dama tun d’azu take kiran wayarsu amma basu d’auka ba yace, “Me kika fad’a mishi?” “Mas’ud ya fad’a mini kun labarta mishi komai akan abunda yake faruwa shine na k’ara maimaita mishi, na kuma sanar mishi cewa duk makircin Alhaji Abdul ne wanda ashe ku baku fad’a mishi ba.” “Shikenan sai da safe.” “Kaala Abdi na 6ata muku shiri ko?” Ta tambayeshi hawaye na taruwa a idanunta. “Babu komai, kawai abun ne yazo mishi a bazata. Kafin gobe da safe zai dawo yanda yake.” Da haka suka yi sallama tana addu’a a ranta Allah yasa bata 6ata abun da suka dad’e suna gyarawa ba. A haka tayi bacci cike da mafarkan Haydar wanda ya zame mata d’abia, wannan karon mafarkin yafi mata dad’i domin kwanciya yayi a bayanta ya rungumeta sosai yana shafa cikinta yana kuma kiran sunanta a kunnenta. A haka ta farka tana murmushi amma jin mutum da tayi a bayanta yasa zuciyarta ta fara bugawa da k’arfin gaske tace, “Haydar!!!” “Shhhh, kiyi shiru karki tayar da Babyn Haydar.”
Mum Fateey 👌

