Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 42 Hausa Novel

Washegari ya kama ranar asabar ce don haka yara basu da makaranta; ko da ya dawo daga masallaci a kan dadduma ya sami Khadeeja a dakinta tana azkar, bayan ta idar ta gaisheshi sannan tace ‘Mantawa fa nayi jiya ban gaya maka yau ne bikin su Fatin Baba Sani wanda na nuna maka invitation din last week.’Ya gyara pillow ya kashingide a kan gadon yana cewa ‘Ok, Allah ya sanya alkhairi. Ai in sha Allahu nima zani daurin aure don Baffa da kansa ya turo min kati.’‘Ok. Ni sai wajen azahar zan tafi don ka ga ban je yawon arba’in ba sai na hada gaba daya, idan na kwana biyu a gidan Mommy ranar litinin sai na dawo.’Ya dan bata fuska ‘Kuma shine har kwana biyu? Ai na zata a gidan bikin zaki ga duk wani wanda ya kamata kije masa yawon.’Tayi ‘yar dariya sanna tace ‘Kada fa ka manta bikin na dangin Baffa ne, ‘yan uwan Mommy su kuma ai sai dai naje musu gida yawon arba’n din ko? Hajiya Nana dama ban kai mata baby ba ga su Anti Halima da Baba Usman. Ka ga yau a gidan biki zan wuni, gobe kuma tun safe zamu fara da Nabila; dama zamu kai musu katin bikinta tunda ka ga an fara rabo duk da dai bikin saura sati uku.’‘Uhm, sai kun dawo.’‘Mun dawo kuma? Ni kadai fa zan tafi, Hafsa kawai zan dauka saboda Hammad.’Ya tashi zaune yana fuskantarta ‘Na zata ke da yara zaki tafi kamar yanda kuka saba.’Ta jijjiga kai tana dariya ‘Haba dai, yawon arba’in din na kwashi yara har hudu? Dama saboda babu mai kula da su ne yanzu kuma ka ga Antinsu tana nan. Ni kadai zan tafi.’Duk yanda ya so ta tafi da yaran nan haka ya hakura ya kyaleta domin ta ci alwashin ba zata sake tafiya da su danginta ba tunda yanzu suna da uwar dakin da zasu dinga kawowa gulma.A kan lokaci ta gama abincin safe, sai dai da yake yana nan babu yanda ta iya haka ta jera a dining table din parlor dinsa. Dankalin bature ta soya da ragowar sauce din jiya da aka ci abincin dare sannan kuma da soyayyen kwai. Kowa a plate dinsa ta zuba masa har shi Mustaphan ta saka sauce a gefe da kuma soyayyen kwai. Nashi ta fara ajiye masa tare da na Shukra sannan ta juya ta koma kitchen din.Tana shigewa kitchen din ya dubi Afaf yace ‘Jeki kasa ki kirwo Antinki ta zo muyi breakfast.’Nan da na ta mike ta fice, ya dubi Habib ya mike yana shirin ya bi Khadeeja kitchen ya karbo nashi abincin yace ‘Shiga parlor din Anti ka daukowa kujerar dinin guda daya a kara.’Don haka yabi bayan Khadeejan. A hanya ta hadu da shi ta riko plate biyu, tana kokarin mika masa yace ‘Abba ne yace na daukowa Anti Naja kujera tare za ayi breakfast din da ita.’Kafin ta gama fahimtar abinda ya fada ya wuceta ya nufi dining; tana karasowa ta ajiye farantan hannunta daya a gaban Nasreen ta zagayo da dayan zata ajiye a kujerar da take kusa da Mustaphan a daidai lokacin da Afaf ta shigo tare da Naja suna tafe suna hira. Kafin tayi magana ta zauna a kujerar da take kusa da Mustapha daga damansa a daidai lokacin da Khadeejan take shirin ajiye nata abincin a wajen. Tayi cak ta dauke farantin da take niyyar ajiyewa ta dubi Habib tace ‘Yaya kaje kitchen ka dauko naka abincin ke kuma Afaf ungo wannan ni sai na dauko wani.’Cike da fara’a Naja tace ‘Ina kwana Umman Hammad.’Itama nan da nan ta saki fara’a ‘Lafiya kalau amarya ba kya laifi, ya gajiya.’‘Alhamdulillah. Sannu da aiki.’‘Yauwa.’Har cikin ransa yaji dadin yanda suka gaisa, haka yake son iyalansa ko da dai idan baya nan ba zasu hadu suyi hira ba to idan yana nan a zauna duka kamar haka a ci abinci tare; ya dubi Khadeeja yace ‘Yauwa itama ki taho mata da abincin ko?’‘Ok.’ Ta amsa a gajarce sanna ta juya ta nufi kitchen dinta.Kafn ta karasa kitchen din zuciyarta ta gama tunzura; Mustapha so yake yayi mata dole kenan? Ta gaya masa ba zata yi abinci da matarsa ba amma shine zai saka a kirawota harda zama a kujerarta. Lokacin da ita Najan take girki ai bai taba kiran Khadeejan yace tazo suci abinci ba shine sai yanzu don ya tabbatar mata Naja itace matar da yake kauna shine zai ce ta bata abinci.Nan take ta juye ragowar dankalin wanda dama ba yawa ne da shi ba ta ajiye ne saboda Shukra, ta hada da wanda da ta zubawa Afaf ta zuba sauce da kwai. Ta hada shayinta mai kauri ta dauka ta wuce dakinta ta bar Hafsa a kitchen tana cin nata abincin.Shiru Khadeeja bata fito ba, kowa yana ta cin abinci yayinda Naja take shan shayinta wanda ta hada. Shirun yayi yawa ya dubi Habib yace ‘Je ka dubo ko Antinka dankalin ta tsaya soyawa?’Bai dade da shiga ba ya dawo yace ‘Abba bata kitchen din, tana dakinta kuma ta kulle kofar.’ Ya zauna ya cigaba da cin abincinsa ba tare da wata damuwa ba.Ajiye fork din dake hannunsa yayi yayi shiru saboda takaici; mantawa ma yayi ya bawa Khadeeja mukullin dakinta saboda a da yayi alkawarin ba zai sake bata mukullin dakinta ba saboda yanda take kulle kanta a ciki tayi burus da kowa.Ya ture kwanonsa ya mike, itama Naja ta mike a lokacin. Ya kalli plate dinsa; ya riga ya ci da yawa sannan kuma sauran duk ya dame da sauce. Cike da damuwa ya cewa Naja ‘Ko wannan zaki ci naje na dubo.’‘No, kada ka damu. Ku ci abincinku akwai bread a kasa zan je na ci.’ Ta juya ta fice daga parlor din ba tare da ta surareshi ba.A fusace ya nufi dakin Khadija, tuna kafin ya fara buga kofar ya kirawo sunanta. Ba tare da bata lokacin ba ta amsa sannan ta taso ta bude masa kofar, ko a fuska bata nuna masa ta san tayi laifi. Ya shige cikin daki ya kalli abincin da take ci a gefen dadduma yace ‘Ya zaki taho nan ki kama cin abinci ki bar mutane? Kuma kina ji nace ki bata abincin itama.’Duk yanda ta so abi maganar a hankali bai samu ba, domin yanda yayi mata wannan tambayar da isa da gadara take taji duk wata kara da zata iya yi masa ta bushe. Ta kalleshi ta kawar da kai sanna ta wuceshi ta koma ta zauna a gaban abincinta inda ta taso sannan tace ‘Gani nayi kun cike table din, abincin kuma babu tunda ni ban soya dankali da ita ba. Me kake so na bata?’‘Ai tun jiya nace ki dinga saka abincin a can don kowa ya ci kuma kika amsa ko? Me yasa ne kike so ki dinga raina ni a gaban mutane? Saboda me nace ki bata abinci ba zaki bata ba zaki shigo nan ki bar mutane?’Ta kula dai duk wani zille-zille ba zai yi mata ba, ta kalleshi suka hada ido tayi murmushin yake mai dauke da takaici sannan tace ‘Kwana kusan talatin tayi a gidan nan tana girki bata taba bani ba, kuma tare kuke cin abinci kai da ita da yara baka taba cewa a kirawoni naci abinci ba; ko da yake ko ka kirawoni ma ba ci zan yiba tunda nima na iya girkawa. Kayi hakuri ba zan hada girki da matarka ba itama kar ta hada dani, duk wanda ya girka yaci shi da maigida da yara kawai.’Ta mika hannunta ta dauki fork a kan plate din da yake gabanta ta fara wasa da shi tana kokarin tokare takaicin da yake taso mata yana neman ya sakata kuka.‘Wai ke me yasa ban isa na gaya miki magana kiji bane Khadija? Ko..’‘Ita da ka gaya mata ai ta ji har ta bani abincin, ko da yake ita ka dauka mutum shi yasa kake nema mata abinda zata ci. Ni da babu wanda ya damu da rayuwata ina nan kake fita ka siyo muku abinci ka sakata a gaba ita da yaranka ku cinye ba tare da ko rabona an bani ba. Ban yi magana ba, shine kuma yanzu za ace ni zan bata abinci; to ta cigaba da jirana taga idan zata ci abinci.’ Ta gyara zama ta jingina da bango ta kawar da kai.Ya rasa abinda zai gaya mata saboda tabbas ya san duk abinda ta fada gaskiya ne, sai dai a wancan lokacin ai laifi tayi masa na kin amincewa ta kula da yara don haka bai ga dalilin da zai sa ya bata abincin da ya siyo ba bayan taki ta girka. Ba tare ya ce mata komai ba ya fice daga dakin don a yanda ya san Khadija da taurin kai sai dai ya datse igiyar auren nan amma ba zata yi abinda yake so ba. Sai dai tabbas idan ta cigaba da gwada masa taurin kai irin wannan zai datse igiyar auren ya huta, taje can gidansu ta cigaba da taurin kan.………..Haka ya karasa shiryawa zuciyarsa babu dadi, don ko dakin Najan ma bai shiga ba suka fice tare da Habib suka tafi daurin aure.Yana ficewa itama ta gama shiryawa, ta kulle dakinta da parlor dinta gaba daya. Ta hada mukullanta da wanda ta cire daga jikin nashi keys din duka ta jefa a jaka don bata so ko shi ya bude mata waje idan bata nan. Ta goya Hammad ta tasa Hafsa a gaba, suna saukowa kasa ta shiga parlor din Naja inda ta jiyo hayaniyar yaran, ta dubeta da fara’a tace ‘To Anti ni na fita, zan je gidanmu ne in sha Allahu zan kwana biyu. Sai ranar litnin zan dawo.’Ta juyo ta yi mata wani kallo na raina sanna tace ‘A dawo lafiya.’Shukra ta tashi da gudu ta kama hannunta tace ‘Anti gidan Mommy zaki je?’Ta shafa kanta ‘Can zan je Shukra, sai ranar Monday zan dawo.’Ta langabe kai tana cewa ‘Kai Anti ina son zuwa fa, kwana biyu ban je wajen Anti nabila ba fa.’‘Ai kin ga Monday akwai school ko? Shi yasa ba zan tafi dake ba. Amma idan zan koma ranar da babu makaranta zan tafi dake kin ji.’Haka ta tsaya ta lallabata sannan ta wuce…

Back to top button