Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 30 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                                  THIRTY📍

         In banda innalillahi babu abinda Mami da Umm ke maimaitawa, ko masifar da Deen yake basaji burinsu kawai a gano inda take, abun mamaki kuma mai gadi ya tabbatar ko nan da chan be motsa ba bare ace ko ta fita be saniba, bama wannan ba duk uban securities din dake gidan ba yanda zaayi ta fita wani be ganta ba…….

      “Waya turoku gidannan?”…. 

Mami suka juyo muryar Deen rai a bace yana tambayar su eesha…..

     “Mekakeyi hakane? Aisha ce fah yar gidan Hajiya saratu, dayar kuma kawartace”…..

Umm ta katseta……

    “Banyarda dasu ba!”….

  “Kaji abinda na fadamaka kuwa? Eesha fa yar gidan aminiyar mami, baka ganeta ba?”…..

   “Nagane but they’re still among my suspects!”….

       “Why?!”…..

   “Akanme daga zuwa zasuyi hugging dinta and I’m very sure basu santa ba!”……

     “Is that so?”…..

Mami ta tambayesu…..

    “Mun santa she’s our roommate, itace wacce nake baki labari mami, that unknown girl that is always covered”…..

    “Really? Toh amma taya kuka gane itace bayan baku taba ganin fuskarta ba”…..

   “Recently munga fuskarta mami, abinda naketa so nazo na fadamiki kenan, wallahi itace wannan din”…

Tsaki Deen yaja yace;

     “Duk wannan sa idon na menene? Meye damuwarku da ita harda wani so kizo ki fadawa mami gaki gulma na cinki ko!”……..

    “Toh sarkin masifa, bakaji tace she’s their roommate ba dole ko su damu ai”……

    “Yanzu Umm kawai dan tana roommate dinsu shikenan sai susa mata ido, how sure are you itace wannan dinma?”……

      “All this isn’t necessary, yanzu dai ta ina zaa fara neman yarinyar shine!”…….

         A hankali Khaleel ya bude idonsa after almost three days of unconsciousness, sosai ya rame fuskarsa tayi fayau kamar bashi ba saidai babu abunda ya ragu daga kyannan nasa me ruda yan mata, ga mamakinsa sai gashi ya mike tsaye akan kafafunsa wanda rabonsa da tashi batareda an taimaka masa ba harya manta, toh shi in banda abinsa me kwanciya a asibiti ya kara masa? Wacce yakeyi domin ita kilama batasan yana kwance a asibiti ba, in akwai abu daya daze iya chanjawa a rayuwarnan toh tabbas weakness dinsa ne, kwata kwata be iya facing challenges ba, abu kadan sai yayi breaking down memakon yayi man up and fight for it, amma Insha Allah daga yanzu ya zama jarumi, he’ll fight for her love with all his soul, a take yaji wani strength yazo masa ya kuma kudirta a ransa this time around ba gudu baja da baya harsai ya mallaketa a matsayin mata……..

       Zaune yake a katafaren parlournsa hannunsa dauke da newspaper daga dan gefensa kuma coffee ne me zafi sai tiri yake daga cikin kofin, a zahirin gsky idan ka kallesa zaka dauka karatu yake a newspaper amma ba hakan take ba dan ya dade da fadawa duniyar tinani… Besan meyasa ba kwanannan maslaha yake nema tsakaninsa da hajiya fatima amma taki bada hadin kai, in banda provoking dinsa babu abinda takeyi, yanzu gashi yace zeyiwa dansa aure tace tariga ta masa mata kamar ita keda alhakin aurar dashi, idan tana wasu abubuwan har mamaki take bashi dan shi shedane ba haka take ba saidai besan meya chanjata haka ba dan tsakina da Allah shi ta cuta amma yaga harta fishi daukan zafi akan abun alhalin itace batada gsky….. Gashi ya bata zabi akan Deen ya auri duka zabinta da nasa amma taki yarda, shikuma idan ya bari Deen ya auri zabinta ai ya zama looser kenan!…. Abun haushi kuma da yacewa Deen ya bisa su koma gida saice masa yayi akwai important abinda yake son clearing a hospital dinsa na abuja so baze iya binsa ba amma ya masa alkawarin zezo in the next three days, tsabar renin hankali harda fadamasa sudaina fada da mahaifiyarsa tunda sunki gayamasa dalilin fadansu, maganar datasa ransa ya baci kenan har yace masa karya zo masa gida tinda bayan uwarsa yakebi suje chan su karata… Gashi yanzu ya dawo abun na mugun damunsa……

Yana cikin wannan hali Mom tashigo, kamar ko yaushe murmushi dauke akan fuskarta, karasowa tayi ta zauna a hannun kujerar da yake, cikin kwantar da murya tace;

    “Alhajina ni kadai!”……

Shiru yayi kamar bejitaba dan so yake tabashi space yanda ze samu damar yanke abinda ya kamata yayi…

     “Kasan yanda nakeji a raina idan na ganka a cikin damuwa kuwa? Dan Allah ka tausayamin ka fadamin damuwarka kona samu salama a zuciyata, da yarda Allah kuma in tayaka nemo mafita”……

Sosai ya danji kalamanta sun sanyaya masa zuciya, shiyasa take da wani guri me girma a zuciyarsa saboda gwana ce wajan kwantarwa da mutum hankali, ko yanaso ya boye mata damuwarsa saiya kasa shiyasa babu abinda bata sani ba akansa har wanda be kamata ya fadamata ba saiya samu kansa da fadamata………

     “It’s about Deen!!”…….

Kara matsowa kusa dashi tayi cikin kwantar da murya kamar yanda ta saba tace;

     “Allah ya huci xuciyarka yallabai, but what about my son?”…..

     “Aure nakeso namasa very soon!”…..

    “Nagane, toh amma meye abin damuwa tinda yasan da maganar dama?”……

   “Mahaifiyarsa ce tashigo da wani abu!”……

Ya fada wani bari na zuciyarsa najin kamar be kamata yayi hirar da ita ba…….

Gabanta ne yayi wani mugun faduwa jin abinda yace wai mahaifiyarsa, yaushe suka hadu har sukayi magana har tashigo da wani abu? Ashe tana zaune gaho abubuwa nata faruwa bata sani ba?…. Cikin basarwa tace;

     “In banda abinta ai gwara yayi auren zefi samun nitsuwa, ita da kanta hankalinta sai yafi kwanciya da yawace yawacen daya keyi, adai bi abun a sannu”…..

     “Ba auren bane bataso, wai tana da wacce takeso ya aura”……

     “What?!”…..

Ta fada da karfi unknowingly…..

Juyowa yayi ya kalleta cike da mamakin yanda tayi maganar…. 

Ganin irin kallon dayake mata yasata saurin gyara maganarta da fadin;

     “I mean ba kariga ka masa mata ba kuma yasan da maganar?”…..

    “Yes!”…..

   “Toh ka fadamata mana tinda shima Deen din yasan da maganar”……

   “Na fadamata!”……

Nan ya kwashe duka yanda sukayi da Mami ya gayamata da yanda suka kare da shima Deen din har yace karya sake yazo masa gida gashin yanzu abun ya damesa…….

     “Yallabai in banda abinka ai hannunka baya rubewa ka yar, be kamata kacewa son kar yazo ba kamata yayi ka bishi a hankali tinda yasan da maganar Hamida a kasa, kuma tinda tace saidai ya auri daya ai zabinka ya kamata ya aura tinda uba keda alhakin aurar da dansa, yanzu gashi ka kara bata damar da zata janyeshi sosai, tsap saita masa auren baka saniba ma!”……..

Dafe goshinsa yayi yana harhada maganganunta, tabbas abinda ta fada gsky ne, yin zuciyar da yayi kamar ya kara bata damane taci galaba akansa….

     “Yanzu menene abunyi?”……

Murmushi tayi ganin ta fara samun kansa tace;

     “Ta inda aka hau tanan zaa sauka!”….

    “Me kike nufi?”……

   “Ka kira Deen, kace masa ya tawo kawai, ni kuma na maka alkawarin indai yazo zanyi convincing dinsa kawai sai a daura auren!”…….

    “Anya zaki iya kuwa samira?”….

   “Just trust me alhajina, yanzu ka kirashi kace ya tawo”……..

Daukan wayarsa yayi ya shiga dialing number Deen, kira uku ya masa be dauka ba…..

Deen da suke cikin tashin hankalin neman fatima zainab wayarshi na jikinsa amma ko ringing bejiba……

Sosai ran dad ya baci yana ganin kamar Mami ce ta hanashi daukan wayarsa, wato tin baaje ko ina ba maganar sameera ta fito na janyeshi kenan?…. Dukda haka sai ya kasa hakura ya cigaba da kiransa,

Sai a kira na biyar sannan Deen yaji wayarsa na ringing, kamar ya share kawai ya fito da wayar, ganin Dad ne yasasa daukan wayar da sauri……

Tinda ya dauka yake zazzaga masa masifa akan rashin daukan wayarsa da wuri, yana sauraransa amma bece komai ba saboda abinda yake damunsa yafi karfin masifar da Dad yake, shiko jin abinda yake cewa bayayi dan hankalinsa baya wajan……

      “Kana jina kuwa?!”……

    “Ina ji”…

Sai a lokacin Deen yayi magana…..

    “Duk abinda kakeyi ka barshi ka tawo yanzu yanzu!”……

    “But Dad I told you I have some issues to settle, zuwa jibi zanzo Insha Allah”…

    “My friend shut up! Bakaji abinda na fadamaka ba? Nace duk abinda kakeyi ka barsa kazo! Umarni nake baka ba shawara ba!”……

    “Naji!”….

Yana fadin haka ya kashe wayar yanajin kamar zuciyarsa zata fado tsabar bacin rai, yana fama da nemanta kawai zece ya tawo, rasa abinda zeyi yaji dadi yayi kawai ya rotsa wayarsa a kasa, a take ta fashe into pieces, ko a jikinsa ya fasa Samsung din million plus sai neman ma abunda ze kara fasawa yake ko zeji dadi……

 Baki sake suke kallonsa ganin ya fasa waya haka kawai dan sudai basuji yayi wata magana me tsawo a wayar dayayi ba hasalima su mami basu gane dawa yake waya ba, eesha ce tayi kokarin zuwa ta dauke masa wayar Umm ta rukota da sauri tana fadin;

    “Kar kije, ku koma ciki”….

Dan tasan tsap taje saiya iya ball da ita be saniba yanda yayi fushin nan haka…..

Hanyar gate ya nufa ze fita daga gidan, mai gadi ya taso da sauri yana tambayarsa baze fita da mota bane……

Wani wawan mari ya daukesa dashi sannan ya hankadesa ya bude gate ya fita……..

Har ya danyi nisa da gidan zuciyarsa ta shiga saka masa abu akan batan yarinyar dukda bacin dan da yake ciki, juyawa yayi ya koma ya nufi gidan, saidai ba main gate yayi ba zagayawa yayi ta gate din baya, rike kansa yayi sosai yanajin kamar ya buga kansa a bango ko zai samu salama, haka kawai zuciyarsa taki amince masa ya wuce be duba gate din baya ba, gashi kuwa alamu sun nuna tanan tabi ta fita, wato ta gane ba zaa barta ta fita ta main gate ba kenan, amma abun tambaya anan shine ya akayi ta samu key din gate din?….. 

Juyawa kawai yayi ya cigaba da tafiya ko sanin insa yake jefa kafarsa bayayi……

    Da sauri su Umm sukayi kan mai gadi da bakinsa yake fitar da jini ga goshinsa daya fashe shima… 

A take akasa driver da wasu securities biyu sukayi rushing dinsa to the nearest hospital kafin su mami su karaso……

Bayan fitarsu Umm ta sauke ajiyar zuciya, hankali tashe ta kalli Mami tace;

    “Dama Saif be daina wannan mugun zuciyar ba?”….

      “Wallahi nima na dauka ya dena, especially yanda naga yana tolerating yarinyar chan, normal him nasan tuni yayi zuciya da lamarinta koda yayi niyar taimakonta”…..

     “Nima dai abinda nagani kenan naga ko sau daya betaba nuna mata bacin ransa ba, har ina godewa Allah ya chanja, ashe halinnasa na nan”…..

    “Wannan halin nasa na damuna Umm, kullum addu’a ta akan Allah ya yaye masa wannan muguwar zuciya gashi yanzu ya jiwa bawan Allah ciwo, daga baya yazo yanajin ba dadi kuma”…….

    “Ameen ya Allah, Insha Allah ze dena, kawai muciga da masa addu’a, yanzu meya bata masa rai? Kuma ina ya nufa?”…….

     “Abinda naketa tinani kenan, ko dawa yayi waya haka?….Allah ya karesa a duk inda yake, Allah karya hadasa da wannan ze shiga sabgarsa bare ya masa illa”…….

     “Ameen ya hayyu ya kayyum, ki kwantar da hankalinki yaya Insha Allah he’ll be fine”…..

     “Allah yasa Jamila, muna fama da batan yarinya ga wani abu kuma, ni narasa tinanin da zanyi ma”….

    “All is well Insha Allah, karki tada hankalinki, mushiga ciki musan abinyi”……..

       Ba karamin shock fatima zainab tashiga ba ganin su eesha da har yasa ta kasa ture billy data wani rukunkumeta, tariga ta kudirta aranta kome zaayi nunawa zatayi batasan su ba, haka idan ta koma hostel nunawa zatayi ba ita suka gani ba, tana cikin wannan lissafi taji tsawar daya daka musu, ba shiri ta mike tsaye ta koma chan gefe, tana tsaye harya haura sama bayan su Umm sun fito, ganin hankalinsu baya kanta ya sata ficewa da sauri dama mayafinta na hannunta…….

Bata nufi ko ina ba sai kofar baya, idan da zaa tambayeta batasan ya akayi tasan da gate a baya ba kawai jitayi kamar ana janta ta fita daga gidan, tana zuwa kuma taga wani key a kasa, dauka tayi batada tabbacin key din gate dinne kuma batasan ya akayi yazo gurin ba, tana zirawa gate ya bude, luckily tana fita taga wani cab ta tsaidashi da sauri tashiga…..

    Suna zaune a parlourn daddy har lokacin babu wanda ya motsa ko nan da chan, jira kawai suke suga zuwanta dan boss ya fadamusu su saurari zuwanta any moment, sai tattattaunawa suke akan yanda abun ze kasance da kuma wasu abubuwansu daban da suke shiryawa… Har malamin da ze daura auren sunzo dashi ita kawai suke jira tazo a daura auren a parlourn…..

Suna cikin wannan halin sukaji knocking, da sauri daddy ya tafi ya bude ko wannensu na addu’ar Allah yasa itace….. Ilai kuwa itace, murmushi yayi sosai yana mata sannu da zuwa, batace komai ba tabi bayansa suka shiga parlourn……

Guri daddy ya nuna mata ta zauna ya shiga tambayarta ina tashiga sunata jiranta……

      “Ina school”….

Haka kawai taji batasan gayamasa daga inda take dukda yanda takejin bazata iya masa karya….

     “Kin tabbata daga school kike kuwa?”….

   “Yes!”…

   “Yayi kyau, yanzu kin shirya a daura auren?”…..

       “Eh”….

Murmushi duka yana parlourn sukayi, daddy ya gyada kai yana fadin;

    “Nawa kikeso a baki a matsayin sadaki?”…..

  “Ko nawa!”….

  “Kidai fada, daga million har billion duk abinda kikeso zan bayar”…

       “Just any amount kawai!”….

     “Shikenan yanzu zabi wanda kikeso ya zama waliyinki anan”….

Kallonsu tashiga yi daya bayan daya har idonta ya sauka akan alhaji habibu, nunashi tayi akan shi takeso ya mata waliyyi……

Gyada kai mallamin yayi nan daurin aure yashiga gudana a cikin parlourn!!…….

Domin sauke cikakken Littafin ku dannan bulun Rubutun dake kasa 👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2023/01/wace-ce-ita-chapter-25-complete-novel.html

~Uniquebarakancy~

Back to top button