Ruwan Zuma Page 39 Hausa Novel
(39) A bakin gate Haydar ya samu Mas’ud yana kaiwa da komowa, yana parking Mas’ud yayi saurin isa gurinshi yana masa tambayoyi. Ka shigo cikin mota muyi magana, don daga nan Abuja nake son muyi babu 6ata lokaci. Mas’ud yayi jimm kad’an kana ya gyad’a kanshi ya shiga gefen Haydar ya zauna yana mai juyowa gareshi da kuma bashi hakalinshi duka. “Ya aka yi ka samu Abul har ka barshi a can duk tsawon wannan lokacin?�? Haydar ya dafa steering kana ya fara magana. “Naje Abuja da niyyar yin kwana hud’u, ana washegari zan dawo na shiga kasuwa kan wani aika da zan kar6owa Alhaji Abdul cikin ikon Allah na had’u da Abul yana d’aukan kaya yana sakawa a wata pick up, wato dai aikin dako yake yi. Da farko ban ganeshi ba dalilin ramewa da kuma bak’in da yayi. Ko da na ganeshi sai ban tunkareshi ba na shiga kantin da zan kar6i aikan sannan na koma can nesa dashi na tsaya ina kallonshi ba tare dana bari ya 6ace mini ba. Bayan kusan minti sha biyar da haka suka gama loda kayan aka basu kud’i shi da wasu samari guda biyu. A nan ne nabi bayanshi ba tare daya sani ba har zuwa makwancinsa domin nasan zai iya guduwa idan na mishi magana cikin jama’a. Ganina da yayi ya razana ba kad’an ba it’s like bai ma yarda ni yake kallo ba. Da kyar wani abokinsa da naji yana kira Banney ya rok’esa sannan ya tsaya ya saurareni amma daa niyyarsa guduwa zai yi ya bar unguwar. Duk rok’onsa da nayi kan yayi hak’uri ya biyoni mu koma gida bai shiga kunnenshi ba. Karshe ya mini barazanan k’ara 6acewa idan na takura masa, a dolena na hak’ura na barshi domin har ya fara tara mana jama’a suna tambayar ba’asi. Kafin in bar gurin na kira wani da muka had’u a nan Abuja gurin aikin namu ya sama mini wanda zai kula da motsin Abul 24/7, dabara nayi a kan idan ya sake jiki da cewa bazan fad’awa kowa na ganshi ba sai in fad’a muku muje mu d’aukeshi ba tare da yayi tsammani ba. I’m sorry na k’i fad’a muku da wuri, saboda nasan da zarar kun san inda yake zaku yi gaggawan d’aukoshi wanda hakan zai k’ara janyo gaba tsakaninmu. This is what happened a tak’aice.�? “Kalti tana da masaniya kuwa?�? Mas’ud ya tambayi Haydar bayan ya d’auki tsawon minti d’aya yana tunani. “Ban fad’awa kowa ba sai kai yanzu. And na fad’a maka plan d’ina.�? “Bari in shiga gida inyi sallama da Naana, ina zuwa yanzu.�? Fad’in Mas’ud yana fita daga motar. Bai jima ba ya dawo ya shiga motar ya samu Haydar na waya da mai bashi rahoto a kan Abul. Bayan ya gama ne Mas’ud ya kalleshi yana jiran yaji me kuma ya faru. “An kaisu asibiti ana dubasu. Thou an hanashi ko isa ward d’in da aka ajiyesu.�? “Kalti na had’uwa da k’addara a rayuwarta, amma kuma Alhamdulillah da aka sameshi, sai dai wannan karon baza ayi wasa ba za’a kaishi gurin Kaala Abdi a Maiduguri. Insha Allah.�? “Allah ya yarda.�? Fad’in Haydar yana kunna motar suka fara tafiya. “Amin Amin. Amma baza kabi gida ka d’auki kaya bane? Don zai yi wuya mu dawo a yau sanin halin hukumar Abuja baza su sakeshi cikin sauk’i ba.�? Mas’ud ya amsa kana ya had’a da tambaya. “Ina ajiye extra set a mota idan emergency irin haka ya tashi.�? “Kace dai kana ajiye wanda kake sakawa idan zaka je hira. Yayar tawa ta sani kuwa?�? Mas’ud ya fad’a cikin zolaya duk da tension d’in da suke ciki. Murmusawa Haydar yayi amma idonsa da hankalinshi na kan titi yana tuk’asu. “Ita ta fad’a maka ina neman aure?�? Shima ya mayar masa da tambaya. “Ko d’aya, amma nasan nan gaba zaka buk’aci hakan. Kai dai duk abunda zaka yi karka wulak’anta mini ‘yar uwa please.�? “Laila ta wuce wulak’anci a gurina, ka mana addu’a Allah yasa ta bani abunda nake so tunda naga kamar kasan me yake faruwa.�? Gyad’a kai Mas’ud yayi kana ya dubi Haydar cikin tausayawa yace, “Do what makes you happy, haihuwa ba k’aramar magana bace.�? “Insha Allah komai zai wuce kamar ba’a yi ba.�? Haydar yayi maganar cikin dakewa. Awanni bakwai ya isar dasu cikin garin Abuja, daga nan suka d’unguma zuwa Police Station d’in da aka kai su Abul kafin a kaisu hospital daga baya. Bayan sun gabatar da kansu da kuma fad’in wa suka zo bailing sai ya kasance an fara tamke musu fuska nan take. K’arshe suka k’i fad’a musu komai akan Abul suna cewa sai sun taho da Lawyer d’inshi. Ganin haka yasa Mas’ud da Haydar suka kalli juna tare da excusing kansu zuwa wajen police station d’in. Mas’ud ne ya fara magana cikin d’aurewar kai. “Kace me su Abul suka yi?�? “Sata suka yiwa mai sayar musu da kayan maye sai ya musu duka ya kuma kawo k’ararsu nan.�? “But ka duba yanda suke treating d’inmu kamar kisa suka yi. Anya kuwa abun bai fi haka ba?�? Haydar ya kama kanshi da hannunsa biyu yana tunani sannan can yace, “Haka dai ya fad’a mini, amma mu shiga mu ga yanda Allah zai yi. Watakila so suke su 6ata mana lokaci kamar yanda ka fad’a mini tun kafin mu zo.�? Da haka suka k’ara shiga suka samu police officer da suka yiwa magana tun farko. Duk yanda suka yi dashi ya fad’a musu laifin Abul da kuma bailing d’inshi da zasu yi yak’i sauraransu. Suna nan tsaye har aka yi sallah azahar amma babu wani cigaba, hakan yasa Mas’ud ya dubi Haydar yace, “Muje.�? “Ina zamu je bamu gane inda suka dosa ba? Ban gane me suke nufi da k’in fad’a mana laifin da yayi ba. Kisa suka yi ko satar mutum da har suka cancanci treatment kamar terrorist? I don’t understand.�? Mas’ud ya dubi Haydar yaga ranshi ya 6aci sosai yana magana muryarsa a sama har jijiyoyin wuyansa na fitowa. “Haydar kake ko? Baza mu lamunci kazo gurin aikinmu kana d’aga mana murya ba saboda nan ba kasuwa bane. Kuje ku d’auko Lawyer yazo da kansa muyi maganan dashi domin za’a yi gaba da k’arar tasu zuwa kotu nan da kwana biyu.�? “Fuck me.�? Haydar ya fad’a k’asan mak’oshinsa kana ya fita daga police station d’in kamar zai tashi sama. Mas’ud yabi bayanshi ya sameshi yayi kira a wayarsa yana jira a d’auka. Bai mishi magana ba ya tsaya a gefenshi yana jiran ya gama wayar. “Jibril kace me yaran nan suka yi?�? Abunda a fad’a masa tun farko shi ya k’ara nanata mishi babu maganar daya canja. “To meyasa suka k’i fad’a mana komai har suna ik’irarin kai case d’in kotu? Sun masa sata ya dakesu har gadon asibiti, shine zai kawo k’ararsu a kaisu kotu zuwa prison kenan? Bayan ya d’auki mataki da hannunsa kuma meya rage?�? “Wallahi Yalla6ai nima abun yana d’aure mini kai domin in kaga tsaron da aka saka a asibitin zaka yi tsammanin wasu masu fashi da makami aka kama. Inaga abun nasu ba banza ba, watakila Ima yana da d’aurin gindi a sama shine yake son bada misali a kansu. Gasu nan sun fito za’a dawo dasu station.�? Ya k’arisa maganan cikin gaggawa kamar yana tafiya. “Shikenan.�? “Wai a d’auko Lawyer in this lawless country.�? Fad’in Mas’ud cikin rashin fahimtar abunda ke faruwa. Daga nan masallacin dake kusa da police station d’in suka isa suka yi alwala. Suna gamawa motar police biyu suka iso station d’in, hakan yasa Mas’ud da Haydar saurin isa gurinsu ganin an fito da Abul da abokinsa Banney. Ko kusa dashi basu sami isa ba aka shigar dashi ciki tare da rakiyar police hud’u. Mas’ud da sai wannan lokacin ya samu damar ganin Abul tun bayan guduwanshi sai daya zubar da hawaye ganin yanda yaron ya jeme yayi bak’i kamar bashi ne mai gata a daa ba. Haydar ne ya jashi suka shiga masallaci yana bashi baki, “Ranar dana ganshi nima sai dana ji d’aci a raina, da yardar Allah komai zai zo k’arshe.�? Mas’ud ya share hawayen fuskarsa cikin dakewa tamkar bashi yayi hawaye yanzu ba kana yace, “Ina tausayinshi dalilin halin daya jefa rayuwarsa, sannan ina tausayin uwarsa data d’auki son duniya ta d’aura musu. Ni nasan Kalti ba k’aramin dauriya take nunawa mutane game da zancen Abul ba, baya tausaya mata shiyasa shima duniya take garari dashi.�? Da haka suka yi sallah suka tashi da niyyar fita daga masallacin wani police da yayi sallah a bayansu ya musu magana cikin k’asa da murya tare da mik’a musu wayarshi. Cikin d’aurewar kai Mas’ud yasa hannu ya kar6i wayar yana karanta rubutun da akayi a cikinta ta text message. Yana gama karantawa ya bawa Haydar wanda shi kuma bayan ya karanta ya mayarwa police d’in wayarsa cikin d’aurewar kai duk da cewa ya gane me ke k’unshe a cikin rubutun. “Mun gode, Allah ya biyaka.�? Fad’in Haydar. Police d’in ya gyad’a kai tare da fita daga cikin masallacin ba tare da ya k’ara kallon inda suke ba. “Nasan ba haka banza suke treating d’in yaron nan kamar babban terrorist ba. Me ya kamata muyi?�? Mas’ud ya nemi shawarar Haydar. “Abunda wancan ya musu shi zamu yi, hakan kad’ai zai sa su bamu shi cikin ruwan sanyi.�? “Shikenan, ka jirani a can bari in shiga cikin gari in dawo.�? Mas’ud ya tashi tsaye zai fita daga masallacin Haydar ya dafa kafad’arshi yace, “I want to contribute too. Muje.�? “A’a Haydar, k’ok’arin da kayi a baya ma ya isa, just ka barni da wannan.�? Kafin Haydar yayi magana wayarsa ta fara k’ara ya cirota daga cikin aljihunshi ya duba, Laila ce ke kiranshi. “Yan mata.�? Shine abunda ya fara fad’a bayan ya amsa kiran. “Hmm, yau kuma? Ya kake ya aiki?�? Ta tambayeshi. “Lafiya kalau Alhamdulillah. Kefa?�? A nan Mas’ud ya gaji da tsayuwa ya kar6i makullin hannun Haydar yayi gaba abunsa. “Hamdallah. Nace k’arfe nawa zaka dawo kuma me kake sha’awa a dafa maka?�? “Ohh, na manta ban fad’a miki na tafi Abuja ba ko? Zai yi wuya yau na dawo sai gobe Insha Allah.�? Shiru Laila tayi na wasu seconds sannan tace, “Allah ya tsare hanya.�? Kana ta kashe wayarta. Bin wayar yayi da kallo yana murmushi domin ya gane ranta ne ya 6aci da bai fad’a mata zai yi tafiya har ya kwana ba. Mayar da wayar yayi cikin aljihunshi ya fara tafiya zuwa gurin da suka yi parking motarsu amma ya samu har Mas’ud ya tafi. Kad’a kai yayi kana ya koma cikin police station d’in don gwada sa’arsa. Cell d’in da aka gark’ame Abul ya hango a can lungu amma yasan baza su barshi ya isa ba, da haka ya isa gurinsu yace, “Ina son yi magana da DPO naku.�? “Ka jira idan ya nemi magana da kai zamu kira ka.�? D’aya daga cikinsu ya bashi amsa. “Yanzu nake son yin magana dashi, ina so ka fad’a masa cewa zan iya yin komai don yaron nan ya fito.�? Police d’in yayi jimm yana kallon Haydar wanda shima shi yake kallo fuskarsa babu alamun wasa kuma da alama sak’onshi ya isa kwakwalwar police d’in. “Zamu mishi magana amma ka matsa daga nan ka koma can ka zauna kafin ya nemi ganawa da kai.�? Ba musu Haydar ya juya ya fita daga cikin police station d’in ya tsaya a waje yana jiran kiran da suka ce zasu mishi ko kuma Mas’ud ya dawo. Minti biyar da haka Mas’ud yayi parking a gefenshi kana ya fito ya iso gurin Haydar d’in. “Ya aka yi bayana?�? “Na nemi magana da DPO, zasu kiramu anjima kad’an.�? Mas’ud ya gyad’a kanshi kana suka shiga tare suka samu guri suka zauna, basu yi minti biyu da zama ba aka kirasu suka shiga office d’insa. Bayan sun gaisa suka fad’i wanda suka zo bailing tare da son sanin laifinsa. A nan ne DPO ya gyara zamanshi yace, “Na d’auka an wuce wannan wajen. Ba haka wanda kuka aiko ya fad’a mini ba.�? Mas’ud na jin haka ya ciro wata leda a aljihunshi ya d’aura bisa table d’in dake tsakaninsu tare da turawa gaban DPO. A hankali DPO ya saka hannu ya bud’e ledar kana ya bud’e drawer d’inshi ya jefa a ciki ya d’ago ido yana murmushi kamar bashi ba. “Sun yi satan magani a chemist d’in wani mutum mai suna Ima, a garin kare dukiyarsa suka yi kokawa dashi har ya ji musu ciwo, saboda a kwato mishi hak’k’inshi yasa ya kawo k’ararsu nan gurin hukuma.�? Haydar da tun lokacin da DPO ya fara magana zuciyarsa na tafarfasa dalilin rashin yarda da duk kalamansa yace, “Ya aka yi mutane biyu marasa k’arfi zasu iya yiwa Ima sata har suyi k’ok’arin fad’a dashi?�? D’age kafad’a DPO yayi kana yace, “Idan an je kotu zaka ji duk abunda ya faru daga bakinsu gabad’aya.�? A nan ne Mas’ud ya tari numfashin Haydar yace, “Yalla6oi abun bai kai haka ba, kasan yara masu shaye-shaye ba hankali ne dasu ba da har za’a d’auki k’arar zuwa kotu. In zai yiwu shi wanda yayi k’arar a had’amu dashi mu bashi hak’uri ya janye k’arar.�? Sai da DPO ya gama jan ransu wanda sai da Mas’ud ya k’ara ajiye masa wani damin kud’in sannan ya amince. Tare suka fito daga office d’in kana DPO ya kira wani police ya had’ashi dasu Haydar kan zasu cika wasu forms. Minti goma da haka aka ciro Abul yana d’ingishi hannunsa d’aure da handcuffs, fuskarsa tayi futu-futu kamar wanda ya shekara bai ga ruwa ba, ga kuma ciwoka a jikinshi da aka rufe da bandage. “Ina d’ayan yaron?�? Haydar ya tambaya ganin ba’a fito da Banney ba. “Har dashi ne?�? DPO ya tambaya. “Ehh har dashi.�? Ya bashi amsa kana ya maida hankalinshi kan Mas’ud da Abul wanda yake tausayawa. Mas’ud ido kawai ya zubawa Abul idanunshi sun tara hawaye amma fuskarsa a dake take tamkar babu abunda yake damunshi. Shi kuma Abul 6acin rai ne k’arara a fuskarsa yana danna musu harara dukansu da alama bai ji dad’in bailing d’inshi da suka yi ba. Suna tsaye aka fito da Banney wanda shi rauninsa yafi na Abul dalilin Ima ya buga shi da gini har kanshi ya kumbura. Babu 6ata lokaci aka cire musu handcuffs d’in Mas’ud ya k’ara yiwa DPO godiya kana suka yi saurin fita daga gurin. Suna isa bakin mota Abul yaja tunga ya tsaya yana kalle-kalle inda zai gudu, Haydar yana ganin haka ya gane ai kuwa yayi saurin bud’e motar ya sakashi a baya, shi kuma Banney da kanshi ya shiga motar ta d’ayan gefen. Da haka Haydar ya dawo gaba ya shiga mazaunin driver da Mas’ud a gefenshi, bai fara tafiya ba sai daga saka lock a motar yanda Abul bazai iya bud’ewa ba balle ya samu damar gudu. “Ina zamu yi?�? Haydar ya tambayi Mas’ud wanda ya kama kanshi da hannu d’aya yana rufe da idanunsa. “Mu wuce gida kawai.�? Ya amsa a sanyaye kamar wanda bashi da lafiya. “Babu gidan uwar da zanje wallahi, ku sauk’eni in tafi.�? Babu wanda ya kulashi sai Banney dake kallonshi yana mishi ido alamar yayi shiru. “Banney kake da suna ko waye? Ina ne gidanku mu sauk’eka?�? Haydar ya tambayeshi yana juyo da kanshi kad’an. “Oga ba’a nan garin nake ba, ni mutumin Adamawa ne.�? “Yanzu idan na sauk’eka a tasha zaka koma gidanku?�? Haydar ya k’ara tambayarshi. “Zan koma.�? Shine kad’ai abunda Banney ya fad’a. Mas’ud ya bud’e idanunsa a hankali ya kalli Haydar, bai ce mishi komai ba amma ya fahimci me yake nufi. “You promise zaka daina shaye-shaye ka nitsu ka zama mutumin kwarai?�? Wannan Mas’ud ne yayi tambayar. “Idan na koma na samu yanayin gidan namu ya canja nima I’ll change, but if suna nan yanda suke zan k’ara barin musu gidan in tafi. God knows I’m tired of this life.�? “Uncle Mas’ud ku sauk’eni in tafi.�? Fad’in Abul cikin 6acin rai ganin an shareshi kamar bai yi magana ba. Mas’ud ne ya juyo cikin 6acin rai ya nuna Abul da yatsa yana cewa, “Wallahi in ka sake magana sai na tsitstsinka maka mari mara mutunci kawai wawan yaro. Idan aka sauk’eka gidan uban waye zaka je? Ka zama jaki abun tausayi kamar mara galihu. Dubeka yanda ka dawo kamar mahaukaci ka 6ata rayuwarka a banza, wallahi kafi yiwa kanka illa akan kowa. Rayuwarka ka lalata bata wani ba. Idiot.�? Daga nan motar tayi tsitt har suka iso tasha, a nan ne idanun Abul suka ciko da hawaye ya dubi Banney yace, “Yanzu komawa gidan zaka yi? Ba munce duk wuya duk rintsi bazamu koma ba?�? “I’m tired man, na yiwa rayuwata illah akan wani abu da aka yi mini na 6atanci, maimakon in k’ara gyara rayuwata in yi proving nasu wrong sai na fad’a wata rayuwa makamanciyar tasu. Kai kanka kasan bariki bata da dad’i tunda ka kusan losing rayuwarka sau biyu, it’s not worth it. I will try and change ko don kaina da k’anwata, and idan na kasa ka tayani da addu’a Allah ya shiryeni. Lokaci yayi da zan koma gida in fuskanci demons d’ina. I hope you’ll try and change too.�? Yana gama fad’in hakan ya fita daga motar ya bar Abul na cije le6e cikin takaicin rabuwa dashi da Banney yayi. Haydar bai bar k’ofar a bud’e ba duk da cewa Mas’ud na ciki ya raka Banney har motar da zata tafi Adamawa, sai da Banney ya shiga mota sannan ya mik’a mishi kud’i masu d’an dama kana yace, “Allah babu ruwansa da dalilin da yasa ka 6ata rayuwarka, duk abunda kaga ya faru dakai ka d’auka yasan zaka iya cinye k’addaran shiyasa ya d’aura maka, hakan na nufin shaye-shaye is never an option. Ba zai yiwu ka sa6awa Allah sannan kayi tsammanin zai gyara rayuwarka ba. Ban san labarinka ba amma na samu labari daga sources d’ina cewa kaima fushi kayi irin Abul har ka tsoma rayuwarka cikin garari. And as you said; it’s not worth it. Idan kana buk’atar wani abu ka kirani a waya in bai fi k’arfina ba Insha Allah zan maka. Allah ya kiyaye hanya and make sure kana komawa gida kaga likita, domin kanka kamar k’ara kumbura yake yi.�? Haydar Ya juya ya tafi ya bar Banney wanda ke murmushi a hankali amma idanunsa cike suke taff da hawaye. Haydar yana komawa mota ya samu Abul yayi kicin-kicin da fuska tamkar zai mari mutum, a nan ya raya a ranshi cewa Mas’ud ne ya fad’a masa abunda bai mishi dad’i ba. Da bismillah ya kunna motarshi kana ya fita daga tashan suka doshi Kanon dabo domin had’a uwa da d’anta. K’arfe tara na dare suka isa garin Kano wanda kai tsaye wani private hospital suka kai Abul domin a duba jikinshi dalilin Mas’ud yace bai yarda da lafiyar yaron ba. Duk yanda Abul yayi k’ok’arin guduwa bai samu ba dalilin takunkumi da suka saka masa yanda duk wani motsinsa na idonsu, duk bandage d’in jikinshi sai da aka d’aye aka sake wankewa saboda Doctor yace bai yarda da wanda aka mishi ba. Abul yaga wahala, sai ‘wash wash�? kawai yake fad’a yana shanye hawayensa da suke son zuba. Tests kuwa an masa har dana HIV akan washegari result zai fito. Sune basu bar asibitin ba sai k’arfe sha d’aya da rabi na dare, Haydar ya sauk’e Mas’ud a gida sannan shima ya wuce gidansa yana tunanin yanda zai samu Laila wacce ke fushi dashi. A gajiye ya fito daga motarsa ya fito da abunda ya saya zai ci kana ya shiga sashensa. Kai tsaye d’akinsa ya wuce domin bashi da niyyar dawowa falo sai washegari dalilin gajiyan daya kwaso. Bai yi tsammanin ganin Laila kwance akan gadonshi ba, sai dai hakan ba k’aramin dad’i ya mishi ba saboda yasan kewarsa da sonshi da take yi ne yasa tazo d’akinsa ta kwanta. A hankali ya mayar da k’ofar ya rufe sannan ya ajiye abun hannunsa a k’asa ya fara cire kayan jikinshi, daga nan kuwa ya shiga band’aki yayi wanka ya fito sannan ya zauna ya fara cin abinci yana kallon Laila wacce bata ma san ya shigo ba sai baccinta take yi hankalinta kwance. Singlet d’insa da gajeran wandonsa ne a jikinta kamar wacce ta rasa kayan sakawa, sai dai a idanun Haydar ta mishi kyau sosai tare da tayar mishi da wani kewarta na daban. Yana gama cin abincin ya tattara gurin ya kashe wutan wayarsa kana ya isa bakin katifar ya kwanta. Addu’a yayi ya shafa a jikinshi tare da nata, jin hannun mutum a jikinta yasa Laila ta farka zuciyarta na dukan uku uku. Tsabar rud’ewa har numfashinta ta d’age domin bata san mutum ko aljan ne ya ta6ata ba. Haydar da bashi da masaniyar ta farka ya gyara kwanciyarsa hakan kuma yasa Laila ta k’ara firgita domin wanda ya ta6ata yana kan gado kusa da ita. Wani irin ihu tayi ta mik’e tsaye cikin sauri tana lalu6ar abunda zata yi masa lahani dashi, Haydar a tsorice shima ya tashi tsaye yana kiran sunanta tare da yin kanta don yaji meya sameta. “Laila lafiyanki? Meya sameki? Laila.�? “Waye ne kai? Me kake yi a gidana?�? “Nine Haydar, ki kwantar da hankalinki. Kalli nan.�? Ya d’auki wayarsa ya kunna haske ya ganta rungume da takalminsa wanda zata kare kanta dashi. Wani wawan ajiyar zuciya tayi tana dafe k’irjinta domin ba k’aramin tsoritata yayi ba. Abun ya bashi dariya ya kamo hannunta yana cewa, “Yanzu da saceki za’a yi da sai dai ki farka ki ganki a cikin buhu. Tun d’azu fa na dawo nayi wanka naci abinci sannan nazo na kwanta, duk baki ji ba? Yaushe kika fara bacci mai nauyi haka?�? “Dan Allah ka sakeni.�? Ta fad’a tana mai kwace hannunta domin har lokacin bata dawo saiti ba. “I’m sorry I scared you like this.�? Ya bata hak’uri ba tare da yayi gigin ta6ata ba. Sai data k’ara minti biyu sannan zuciyarta ta fara normal bugawa, hakan yasa ta zauna a bakin katifar ta dubeshi tace, “Kace kwana zaka yi.�? “Yes, na gama abunda ya kaini da wuri ne shiyasa.�? “Sannu da dawowa. Ya hanya?�? “Lafiya kalau. Ya kike?�? “Hamdallah.�? Ta bashi amsa tana kwanciya. Tana son tambayarshi me yaje yi Abuja kuma a cikin kwana d’aya amma bata so yayi tsammanin bincikensa take yi. Shima Haydar kwanciyar yayi tare da kashe hasken wayar a karo na biyu. “Me kayi a Abuja?�? Ta tambayeshi duk k’ok’arinta na k’in son tambayar nashi. “Wani abu muka d’auko.�? Ya bata half answer. “Ba kai kad’ai bane kenan?�? “Ni da Mas’ud ne.�? A nan ne Laila tayi wata wawiyar ajiyar zuciya domin har ta fara jin d’aci a ranta da tayi tunanin ko gurin mace yaje. Watak’ila a wancan zuwan nashi ya had’u da ita shine yau tace tana son ganinshi ya kuma je. Kenan duk tunaninta ba haka bane? “Nikam Abul yana kiranki ne kwana biyun nan?�? Haydar ya tambayi Laila. “Bai fi sati ba ya kirani amma yak’i magana kamar mai jiran in fad’i wani abu. Da yaji bazan ce komai ba sai ya tambayeni wai ina kake.�? “Uhm, sai kika ce masa me?�? “Nace kana lafiya.�? “Then?�? “Shikenan sai ya kashe wayarsa. Ban gane me yake nufi ba, har na fara tsoron ko wani abun zai maka sai na tuna rashin hankalinshi bai kai haka ba.�? “Zai yi wuya kam.�? “Lafiya dai ko?�? “Lau. Ki kwanta, I’m sorry na katse miki baccinki.�? Bata ce komai ba ta gyara kwanciyarta sai dai idanunta kek’au babu alamar bacci. Shima Haydar ya nemi gajiya da baccin da yake ji ya rasa, babu abunda yafi so a yanzu kamar yaji Laila a jikinshi. Minti biyar da haka ta mirgina ta shiga jikinshi tana ajiyar zuciya. Hannunsa yasa ya gyara mata kwanciyar sannan ya ruk’unk’umeta tsam a jikinshi yana cewa, “I have missed you.�? “Me too. Please mu daina yawan fad’a mu ba yara bane Haydar.�? “Zamu kiyaye.�? “I need you.�? Ta furta a hankali tana kai hannunta jikinshi inda tasan ba zai iya resisting d’inta ba. Kafin ta k’ara cewa komai ya kar6i jagorancin a matsayinsa na head of the house. “I need you too like crazy Laila.
Mun Fateey 👌



