Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 8 Complete Hausa Novel

 

Kallonta Jalal yayi da mamaki ya kalli inda Ilham ta tarwatsa masa waya ya dawo da dubansa kanta 

“Baze yiwu ba Yaya Jalal, kana wahal dani kana garani kawai dan nace inasonka amma kalli yadda wata take bayyana maka soyayyarta baka dau wani mataki ba amma ni kalli yadda kake wulakantani sau daya baka taba kallona da idon tausayiba

Meye laifina dan nace ina Sonka?”

Shi mamakima ya hana shi magana be ce mata kala ba ya durkusa yana tattara pieces din wayarasa, ya tattara ya nufi waje ze bata guri tazo ta sha gabansa 

“Magana fa nake maka Yaya Jalal, let me tell you something wallahi kai nawane ni kadai babu wata Jaka data isa tayi takara dani wallahi kowace sena kauda ita gefe”

Hawayene ke fitowa daga Idonta wani irin kallon baki da hankali yayi mata ya kuma zagayeta da niyyar ya fita

Janyo shi tayi takuma tsayawa a gabansa ta kalleshi ido cikin ido cikin masifa tace

“Jalal baka isaba ina magana ka maidani mahaukaciya zaka tafi ka barni, I mean what I said wallahi, zan iya komai akan cinma burina, gara tun wuri ka gargadi zuciyarka kattayi gangancin fara soyayya kaidin nawane”

Bata rufe baki ba ya sauke mata maruka biyu masu kyau, 

“Har kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin maganganun dakika ga Dama, kin fasamin waya na kyaleki be isheki ba shine zaki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama ko yaushe ma nafara wasa dake, da kika iya tsayawa kina gayamin wannan haukan,”

“Wallahi kozaka kasheni na dena boye soyayyata a gareka koni ko ita wallahi”

Hannu yadaga ze kuma marinta

“Jalal meye haka kakeyi”

Jawwad ya karaso da sauri ya rike shi 

“Haba Jawwad ba girmanka bane dukan mace, me tayi maka haka, kake dukanta”

Dawo da kallonsa yayi kan Ilham

“Ilham koma cikin Gida yi hakuri banni da shi tashi kikoma Gida”

Wani mugun kallo tayiwa Jawwad a ranta tace munafiki ai kasan komai amma a zahiri ta mike ta nufi cikin Gida tana kuka

“Haba Jalal me kayi hakane abunda kakewa Ilham yafara yawa gaskiya, koba komai kanwarka ce kuma mace ce, kadena dukanta hakan baze canza komai ba Fa”

Nunawa Jawwad wayarsa yayi

Download>>>  Saran Boye Complete Document

“Kalli abunda tayimin be isheta ba, ta tsaya a gabana tanamin hauka”

“Dukda haka kadinga hakuri, halin mata sekana hakuri, kasan shi so makahone waima tukuna, waima ya akayi wayarka taje hannunta har hakan tafaru?”

“Mtseww manta kawai”

Shine abunda Jalal ya fada kawai ya bi hanyar fita waje

Itakuwa Ilham tana zuwa cikin gida taga mummy a palour jikin mummy tafada tana kuka

“Ilham lafiyarki kuwa me akayi miki kike kuka,?”

“Mummy Yaya ne baya sona kwata² ya tsaneni, ni kadai nake sonshi mummy kiyi wani abu akai Dan Allah, zuciyata zata fashe”

Tausayinta ne Yakama mummy

“Is OK my dear, yi hakuri kidena kukan, Insha Allah Jalal bashi da matar data wuceki insha Allah, komai ze wuce”

“Mummy me nayiwa Yaya Jalal ne dabaya kaunata baya so naje inda yake”

“Bikiyi masa komai ba Ilham, haka dai halinsa yake na rashin son mutane, ya za ayi yace baya son mace kamarki, karya yakeyi, kidena kukan haka kar kanki yayi ciwo”

Haka mummy tai ta kwantarwa da Ilham Hankali

Maman Hanan ce hakimce akan kujera dauke da remote a hannunta, yayinda Hanan ta kwanta akan cinyarta tana kallon TV

Sallama Abdallah yayi yayan Hanan 

Sannan yasamu guri ya zauna

“Da girman kujerarki mum barka da Gida”

Ya mutsa fuska tayi ta nisa

” “Yar uban waye ta dakarmin yarinya kunje kaida daddyn Ku amma ba wani mataki daya dauka, waye ubanta a garin nan”

Kallonta Abdallah yayi da mamaki

“Ohh I think dad has already closed this case, meyasa kike kokarin dawo da maganar nan, an sulhunta komai”

“Dalla yimin shiru, a gurina be wuce ba tambayarka kawai nayi Yar inace waye ubanta?”

Tai maganar cikin fushi

“Amm Mum Dan Allah kiyi hakuri zancen nan ya wuce wallahi kanwar abokina CE, kuma mum dinta tabada hakuri sosai, tundaga kano Wan babanta ya taho yau duk Dan subada hakuri fa, to mu suwaye daba zamu hakura ba”

“In kaga ma yimin nasihar tashi kabarmin parlour”

Be kuma cewa komaiba ya fice

Hanan ce takuma fashewa da kuka “mummy ciwon zafi yakemin kaina se ciwo yake wallahi ni ban hakura ba”

Tayi maganar tana kuka

“Yi shiru mana sannu, nima ba hakuran nayiba ai, ai jininki baze zuba a banza ba nasan matakin dazan dauka”

Abbane ya fito ze tafi, Jalila tafito da sauri daga dakinta tana kallonsa domin jin wani hukunci aka yanke akanta 

Siyama ce tabiyo bayanta itama

“To se yadda ta yuwu, ummu Jalila ki hada mata kayanta in Allah ya kaimu sati me zuwa koni ko Jawwad zamuzo mu tafi da ita, tunda bata jin magana”

Abban Jawwad yayi maganar yana kallon Ummi

Kuma fashewa da kuka Jalila tayi

“Ummi nace na dena fa bazan kuma ba Dan Allah kiyi hakuri”

Girgiza kai Abba yayi

“A a senaga kindena din tukuna, a yanzu dai ban yaddaba zuwa sati me zuwa insha Allah in kin canza halinki, shikenan ta fiya kano bayan zuba”

Gyada kai tayi tana goge hawaye itakam Ummi banza tayi mata taki kulata 

“Abba insha Allah bazata karaba ta dena”

Cewar siyama

“Anya kuwa wannan kawar taki batta kawai akwai rashin ji”

Abba yafada yana nuna Jalila

Haka Jalila ta cigaba da kuka tana magiya akan suyi hakuri

Abba yayi musu sallama ya koma, kano yayinda still Ummi taki kula Jalila 

Abun duniya ya ishi Jalila, Jalila tayi trying lambar Jawwad har tagaji amma akashe 

“Haba Yaya Jawwad kaima Fushin kake dani haka, shikenan kowa ya tsaneni”

Haka dai Jalila ta cigaba da sake² aranta tana kuka

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

Hannah ce take ta trying lambar Jalal taki shiga tayi messages din ba adadi amma shiru

Layin Jeje ta kira 

“Da girman kujerarki, gimbiya sarautar mata farar mace Alkyabbar mata, Zara acikin mata, daya tamkar da goma, tauraruwa me wutsiya ganinki ba alheri ba”

Murmushi Hannah tayi da jin wannan kirari da jeje yake mata

“Jeje ya akayi ne dazu muna cikin waya da Jalal naji ta dauke nayi trying tun dazu wayar bata shiga”

“Wow har ya fara yadda ya amsa wayarki kice tarkon ya fara kamashi”

“Ina fa da sauran aiki Ja wallahi, shammatarsa kawai nake naji ya daga wayar, yanzu dai yana ina ne?”

“Nima bansan inda yake ba rabona dashi tun last week, wannan mayen ya hanashi zuwa inda nake”

“Allah sarki simple dashi abokin nasa da akansa zanyi aikin nan da yanzu nakusa nasara, shikam taurin Kaine dashi”

Dariya jeje yayi

“Lallai baki San Jawwad ba zahirinsa kika gani, tsawon shekaru shiya hana aikinmu tafiya yadda ya kamata anyi masa barazanar amma, bashi da niyyar hakura duk abunda kikayiwa Jalal, kai tsaye kamar kinyiwa zuciyar Jawwad ne”

“Tab amma gaskiya yana kaunar JALAL, yanzu dai ka bincikomin inda Jalal yake, inason zuwa”

“To bari in jarraba”

Jawwad ne yabi bayan Jalal

“Yanzu dai kayi hakuri zomuje se a siyo wata wayar”

Bece komaiba yabi Jawwad sukaje suka siyo sabon waya, yabada wadda Ilham ta tarwatsa aka gyara, domin ya kwashe abubuwansa masu mahimmanci na kan wayar, wayar ta daku, Dan karfinta Ilham tasaka ta buga wayar,

  Jawwad ne ya dakko wayarsa don kiran Abba yaji koya dawo, seyaga wayar tasa akashe, be tunanin komaiba ya kunnata Abba ya kira yaji ko yakaraso, yace masa yana hanya.

Ya kashe kiran kenan message ya shigo wayarsa

Jalila ce ta turomasa message,

   “Yaya kaima fushi kake dani  

     Shikenan kowa yatsaneni

     Abba yayi fushi, Ummi ta      

     Dena kulani, Dan Allah kai

      Kar kayi fushi dani”

“Allah sarki sisyna ni Sam bana fushi dake”

Jawwad yai maganar a fili Jalal da yake driving ya Dan kalleshi ya basar

Jawwad ne yaketa kokarin kiran Jalila amma taki dagawa, be fushiba haka ya dinga kiranta har daga karshe ta daga tana daga wayar sautin kukanta yaji

“Yaya  Jawwad kaima fushi kake dani ko? Nakiraka dazu ka daga kaki magana daga baya kuma ka kashe wayarka”

“Nidin Jalila? Ni na isa in miki haka sedai matsalar network, a duniya banga laifin dazakiyi min in ki daga wayarki ba baby”

“Yaya Jawwad Ummi sunyi fushi dani wai se sun dawo dani kano, Dan Allah kabawa Abba hakuri,”

“Kai sisy to meye a ciki kinga seki dawo kusa damu naji dadin hakan”

Cikin shagwaba tace

“Ni wallahi, Yaya bana son zaman kano, ni nafi son zama a gurin Ummi”

“Hmm mune ba kyason zama damu ko”?

“A a Yaya nifa bahaka nake nufi ba, Ummi tace wai in na dawo kano garinsu zata koma”

“No, calm down sisy, dena kuka nan is OK ko so kike nima kisani kukan, bana son kukan nan”

Jalal da haushi ya isheshi Hannu yasaka ya fizge wayar daga hannun Jawwad

“Kana ta shirme da yarinya ko kunya bakaji, se wani shagwaba take kana lallabata”

Jawwad ne ya bishi da kallon mamaki

“To ina ruwanka dani so kake in kyaleta taita kuka in kanta yayi ciwo fa?”

“A’a bindiga kan nata zeyi ba ciwo ba, kukan dadi take da sojoji basu karairayota sun zubowa Abba a boot ba yakawo maka”

“To naji ban wayata”

Kashe wayar Jalal yayi,

“Na hana in munkoma Gida idan nabar gurin seka cigaba, kokuma in baka wayarka in tsaya ka sauka, seka samu gurin zama a titi, ka cigaba da shiriritar”

“Yanzu kiri² bazaka bani wayata ba”?

“Eh bazan bayar ba”

“Allah sarki baby, nasan kukan zata cigaba, Dan Allah kabani in rarrasheta”

“Aiko sedai ta mutu, in seka rarrasheta zata dena”

“Shikenan zan ramane”

Haka suka tafi Gida suna tafe suna fad’a

Memakon  Jalal ya kaisu Gida se ya canza hanya

“Ina kuma zamuje”

Jawwad ya tambayeshi

“Yunwa nakeji ice-cream kawai zan siyo ko fura”

“Kwadayayye kawai”

“Eh naji kwadayayyen ne nasan duk haushina kake ji Dan na hanaka waya, kuma bazan bayarba”

Yasa hannu ya dau wayar Jawwad, ya bar wayoyinsa sabuwa da tsohuwar a cikin mota ya bude motar ya fita

Dan murmushi Jawwad yayi

Jalal kaima ai rigimammen ne

Jawwad ya furta hankali

Jeje tun dazu se trying lambar JALAL yake amma baya shiga

Yanzun ma kuma trying yayi by luck wayar ta shiga

Jawwad dake kashingide a cikin mota yaji wayar Jalal tana ringing da ya duba ba suna ya daga yasa a kunnensa ba sallama ba komai Jeje yafara magana

“Ina ka shigane tun dazu nake kiran wayarka amma yaki shiga”

“Sorry ba shi baneba wayarsa ce ta Dan samu matsala”

Jeje yagane muryar Jawwad amma alamu ya nuna shi Jawwad be gane shiba Dan da ya ganeshi baze daga wayarba ma

“OK Dan Allah yana ina yanzu”

“Mun Dan fita dashi, yanzu muna kabuga ya Dan fita ne yanzu zamu karasa Gida insha Allah”

“OK nagode”

“Wa zance masa?”

“No bakomai zan kuma kira”

“OK”

Jawwad ya katse kiran

Jeje ne ya kira Hannah a waya

Bugu biyu ta dauka

“Ya”?

” ke kin ban wahala gaskiya tun dazu nake kiransa a waya se yanzu na same  shi a waya, shima ba shi ya daga ba mayensa ne ya daga wai wayar Jalal dince ta lalace, sun Dan fita yanzu zasu koma Gida”

“Au nice ma nasaka wahala kamanta aikin naka ne?”

“Hakane fa tuba nake me idon zinari”

Murmusawa Hannah tayi

“Weldon yanzu kuma zanyi nawa aikin, zan Dan jefa masa fargaba a zuciyarsa”

“Meye shirin naki?”

“Ba ruwanka kai dai zuba ido”

Jawwad yafara gajiya da zaman jiran Jalal 

“Kome ya tsaya yi oho”

Jawwad yai maganar tareda duba wayar Jalal don ganin lokaci message ne yake shigowa wayar

Download>>> Dangin Rabi Complete Document

  “Yau kaki daga wayata, ka jefa Zuciyata cikin matsala, ko Abinci nakasa ci dan haka Kaima zan saka taka zuciyar a damuwa Ina hanyar zuwa gidanku

Zakazo ka sameni a gidanku

Cikin dakinka, kuma komai 

Ze iya faruwa in aka ganni a

Dakinka, in baka son hakan

Ya kasance mu hadu a   

Restaurant din damuka hadu 

Da farko mintuna goma sha 

Biyar kawai kake dashi

          From your lovely bae

           (Hannah)

Wannan wace irin jaraba ce, haka Jalal yai maganar hankalinsa a tashe, bayaso sunan Jalal ya kuma baci, da sauri yayi dialing number da aka turo message din da ita amma taki dagawa, 

Yasalam Jalal ina ka tafine ana shirin jefaka cikin matsala

Daren ranar ma Jalila batayi ishashen bacci ba ko abinci taki sakin jiki taci, Ummi se rayuwarta take ita kadai ba tare da ta shiga sabgar Jalila ba dukda a cikin zuciyarta bata jin dadin abinda takewa Jalilan amma yazama dole ta nuna mata bacin ranta akan abunda Jalilan takeyi

   Washe gari da safe Jalila haka Jalila ta shirya ta tafi makaranta, tana zuwa yan ajinsu yan son jin gulma sun so su tambayeta yadda akayi amma ba fuska ta hade rai se muzurai take, suna tsoron su tambayeta suma ta juye musu kwandon bala’i

Mummy Hanan dakanta tare da wasu sojoi Guda biyu suka kawo Hanan makaranta cikin wata CRV me tint glass, sojoji guda biyu na gaban motar, sun dan jima a kofar makarantar koza suga wucewar Jalila amma basu ganta ba daga baya, mummy tace Hanan ta shiga school ita tasan abunyi 

Tsakanin Jalila da Hanan ba Wanda ya kula wani, duk yanda yan aji sukaso jin gulma basu samu dama baa

bayan tafiyar Hanan ba dadewa sega malama ramatu an sauketa a napep zata shiga cikin makarantar 

Dan sauke glass mummy Hanan tayi 

“Sannu dai”

Mummy Hanan tafada cikin ISA da iyayi

Malama ramatu na ganin mota

Ta washe baki da durkusa

“Yawwa sannu madam ina kwana”

A dan wulakance mum Hanan ta amsa

“Yawwa lafiya, if u don’t mind please I have an issue to discuss with you”

“A a ba wata damuwa, madam ina jinki”

Alama tayiwa malama ramatu data shigo cikin mota

Ba tayi tunanin komai ba ta shiga 

Mummyn Hanan ta numfasa

“Da alama kema staff ce a school din nan ko?”

“Yea of course”

“Good, kinsan case din da akayi a school din nan da akayi fada tsakanin dalibai biyu aka daki yarinya Yar gidan captain rasheed “

Se a lokacin malama ramatu ta kalli suwaye a gaban motar taga sojoji nan take ta sha jinin jikinta

“Emm…e..eh nasani madam amma wallahi bana gurin akay….”

“Inma kina gurin ke kikasani tambayarki zanyi kikamin karya, zaki gane kurenki ne”

“Zanma fadi gaskiya wallahi”

“Wacece Jalila Aliyu Imam Yar uban waye ita?”

Nan take malama ramatu ta karkace ta dinga rattaba bayanin karya da gaskiya 

“Ba Yar uban kowa bace ba, a sanina ma bata da uba, amma naji ana wai ya mutu ko karya akema ohoo, daga  ita se uwattta suke zaune baata da wani gata, se tsabar iskanci da Neman rigima”

Haka taita zuba, kaman ruwa ba comma ba full stop

“Ke surutun ya isa haka bani address din gidan su”

Malama ramatu ta bata address

Maman Hanan Tabawa malama ramatu 5k a wulakance sukaja mota sukayi gaba

Kuma trying lambar Hanna Jawwad yayi da wayar Jalal

seda taja aji, azatonta Jalal ne sannan ta daga cikin yanga tafara magana

“Baby lokacinka ya fara karka dauka da wasa nake wallahi dagaske nake in samu haduba gidanku zanje”

“Amm Hanna ba  JALAL bane nine Jawwad dan Allah karkiyiwa Jalal haka, dama yan anguwa sun samasa ido, yanzu in kikayi haka zaki kara bata masa suna kisa akuma tsanarsa dan Allah karkiyi haka duk abun Jalal baya bin mata kuma mahaifinsa yana gari in ya ganki bazeji dadi ba”

Nisawa Hannah tayi

“Jawwad dan uwanka yafiye taurin kai yaki karbar bukata ta, gara in biyo masa ta inda yakamata, mintuna sha biyar ne kacal daku, in bakuzoba wallahi zanyi shigar danaga dama ince karuwarsa ce ni kuma har Gida xanje, ko dayake nasan hakan ba lallai yabata masa ba but at least ze gane da gaske nake, ganinsa kawai nakeso nayi in samu sauki a raina, zabi ya rage naku dan uwa na gari”

Ta kashe wayar 

“yasalam wannan wane irin abune, Allah ya fidda kai sharrin wannan yarinyar Jalal, ohhh gara muje mu sameta karta bishi Gida daddy bazeji dadi ba dama ga yan unguwa sunsawa Jalal ido, inaga kuma aga karuwa taje gurinsa “

Jawwad ne Ya bude motar da sauri ya fita Neman Jalal

Ko islamiyya Jalila ba taje ba, kuma Ummi batace ta shirya taje ba, ta kyaleta idonta duk ya kumbura saboda kuka

“Allah sarki baby na banajin dadin ganinki a haka amma kedin ce Zuma seda wuta, gara in horaki” Ummi tayi maganar a zuciyarta

Da yamma likis su Jalila sukaji tsayuwar mota a kofar Gida, Jalila tana tsakar Gida ta zurawa Ummi ido kaman bata Santa ba, Ummi tanaa shan fura,

Cikin izza sukaji sallama

Ummi ce ta amsa sallamar tare da jiran shigowar Wanda yayi sallama

Jalila tana zaune bata amsa sallamar ba balle ta motsa daga inda take, 

“Sannu da zuwa shigo”

Ummi tayi maganar tana mikewa tsaye bata gane matar ba tayi zaton irin customers dinta ne

“Ba zamane ya kawoni ba”

“To lafiya meyafaru?”

Ummi ta tambaya

Download>>> Yaro Ne Complete Document


“Nasan baki sanni ba nice Hajiya Safiyya Mrs. Captain Rasheed “

Da sauri Jalila ta daga kai tayi arba da Hanan da mamanta 

Maman Hanan ce ta janyo hannun Hanan

“Kalli duba ta’addancin da y”arki tayi kina tunanin kunci bulus ne?”

Gaban ummine ya fadi da taga Hanan.

Wani mugun kama Ummi taga Hanan tanayi da Jalila, ciwon goshin Hanan ta kalla

“Eyya kiyi hakuri ai munje makaranta akan case din, mun bada hakuri, babanta yace komai ya wuce kiyi hakuri Dan Allah”

“Keda kinsan da bada hakurin kika haifi Yar da bata da tarbiyya, kika haifi yarinyar Datafi karfinki ni na dauka ma Yar wata hamshakin ce Ashe ba Yar uban kowa bace face Mara galihu?”

“Duk me ya kawo wannan maganar, haba ke kuwa Jalila tana da tarbiyya rashin ji ne kawai na yara, kuma batun gata kowa gatansa Allah,”

Wani abune yakawo wa Jalila iya wuya motsa baki tayi da niyyar rashin mutunci cikin tsiwa sukayi ido hudu da Ummi seta hadiye maganarta tayi shiru

“Da wallahi niyyata ubanta zansa akoyawa hankali in yaso gobe yabawa yarsa tarbiyya ya banbance mata matsayin yayan gata da marasa galihu”

“Kar a kuma sakomin uba, a barshi ya kwanta cikin aminci a kabarinsa, ni nayi laifi ba shiba”

Jalila tayi maganar tana jujjuya idanu

“U see mummy wannan yarinyar bazata yi nadama ba memakon tabaki hakuri rashin kunya zatayi miki, in bakiyi Sa a bama zaginki zatayi, kawai kisa a dauketa a je a horata”

Hanan tayi maganar tana kallon Jalila

Da yarabanci Ummi tayiwa Jalila magana, Jalila ta yamutsa fuska ta Dan kara hade rai

“Naji yata ba Yar uban kowa bace bamu da gata se Allah mu bamu su arziki bane, amma kiyi hakuri batun a dauki Jalila a horata be taso ba, bazata karaba”

“Tsiyar talaka kenan ko ince matsiyaci, ya dakko abunda yafi karfinsa, karshe yazo yana karya murya,”

Ta maida idonta kan Jalila

“Kekuma kinci Sa a da ubanki zan Sa akama, wannan uwataki ce ma tabani tausayi, ba dan haka ba da sena Sa an sauya miki halittu, kibari kitaka wani matsayi kisamu me tsaya miki in kinyi rashin mutunci, a yanzu dabaki da galihun nan wahala zaki sha Mara tarbiyya kawai”

“Nice ma ke saboda rashin tarbiyya kuma kar……

Jalila ce tafara magana ummi ta dakatar da ita

Ummi ta kalli mummy Hanan sannan tace, 

” nace kiyi hakuri ko, se magana kike akan gata se dai ko nan gaba amma a yanzu dai banajin kinsamu gatan dana samu a rayuwata, sannan yata ba Mara galihu bace ba, da gatan ta, daliline yasa kiga ganmu a haka, amma bazan gazaba Allah yabaki hakuri”

Tsaki mum Hanan tayi taja Hanan suka fita, ga magana fal abakin Jalila amma Ummi ta hanata magana,

Wata kwallar bakin ciki ce ta taru a idon Jalila, meyasa Ummi ta hanata magana daki ta wuce ta kyale Ummi a tsakar Gida

Jawwad Yana ta duba ta inda Jalal ze taho ya hangoshi yana nufo inda motarsu take da ledoji a hannunsa da sauri Jawwad ya karaso 

“Ina ka tsaya daga siyen abu”

“Au fitowa kayi nemana, da nasani kulleka nayi a cikin mortar”

“Bar wannan maganar ban mukullin mota ni zanyi driving dinmu”

“Me yasa?”

Jalal ya tambayi Jawwad da mamaki, be bashi amsaba yasa hannu ya karbi key din daga hannun Jalal, suka shiga suka tada mota

Jalal ne ya kalli Jawwad

“Nifa bangane wannan abun da kakeyiba, ina kuma zamuyi , ba gida zamu tafi ba?”

“No wani guri zaka rakani”

“Ina kenan?”

“Just watch” inda sukayi zasu hadu da Hannah ya kaisu, ya kulle Jalal a motar ya fita da wayar Jalal kaman yadda shima yayi masa dazu lambar Hanna ya kira

“Kina dai² ina gamu munzo restaurant din”

“Nabar nan gurin ina bayan layinku rukunin sababbin gidajen nan”

“Haba Hannah amma ba haka mukayi da farko ba”

“Na canza ra ayine ina daf da zuwa gidansu Jalal in bakuyi Sauri ba” katse kiran yayi ya koma motar da sauri ya kunna ya ja motar ya bar gurin

“Nikam naksa gane ma’anar abunda kakeyi Jawwad wai meye haka?”

“Zaka gane ma’anar abunda nake yanzun nan”

Inda Hanna tayiwa Jawwad kwantace nan Jawwad ya kaisu ya kirata yace gasu sunzo, sannan yacewa Jalal ya fito daga motar, ba musu ya fito daga motar yana kallon Jawwad, daga cikin tata motar Hannah ta fito tana wani taku cike da iyayi da isa wata shedaniyar rigace a jikinta straight found ce amma yadin roba² ya kwanta a jikinta yakamata tsam se Dan kwali data daure kanta dashi ta fito da Wig’s dinta ya bazu a gadon bayanta,

Da mamaki Jalal ya kalli Jawwad cike da tuhuma da sauri Hannah ta karaso domin rungume Jalal amma yayi saurin matsawa baya

“Meye haka wannan wane irin shirmene baki da hankali niza ki hugging? Meye ma anar hakan daka kawoni nan gurin Jawwad?

Yai maganar a fusace yana kallon Jawwad, Jawwad bece masa komaiba 

” ba laifinsa bane, ni nace yakawomin kai ko in maka ba dai² ba kuma Dan na rungumeka ai ba laifi bane,  Jalal why are you avoiding me? do you thinks am Jocking danace ina sonka, se wulakanci kake min haba Jalal kalleni sama da kasa banyi kama da irin matar daza a wulakanta ba meye aibuna”

Kallon Jawwad yayi

“You see, meye amfanin hakan dakayi, ka dakkoni ka kawoni gurin wannan mahaukaciyar yarinyar, kalleta kalli jikinta, dan ta rainamin hankali kuma tace tana sona, koda nake shan giya nasan abunda ya dace dani”

Jalal se fada yakeyiwa Jawwad duk yadda Jawwad yaso ya kwantar da hankalinsa yayi masa bayani yaki yadda se fada yakeyi, murmushi Hannah tayi sannan tace

“Masoyina naji kana kasan abunda ya dace da kai, ai babu wani abu me kyau da yadace da kai babyna, nidin dai nina dace da kai, kai duba da yanayin taka rayuuwar, da kuma tawa suna kamanceceniya babancin kadanne kawai”

Kurawa Jawwad ido Jalal yayi”kagani ko ka kyauta” shine abunda Jalal yafada Yakama hanyar tafiya, da sauri Jawwad ya bishi “Dan uwa Dan Allah ka saurareni”

“Nika rabu dani babu abinda zaka gayamin, wallahi in kayi wasa sena Sa an batarmin da yarinyar nan, Dan me zaka dinga cusamin ita dolene sena dinga shiga sabgar matan, I hate her”

Ya juya yayi tafiyarsa yabar Jawwad a nan gurin a tsaye Hannah kuwa dariyar farin ciki tayi saboda tayi nasara, so take dama ta Dan janye Jawwad daga jikin Jalal don tasamu damar gudanar da abinda tayi niyya, tayi nasara tunda Jalal har yayi fushi haka

Jawwad ne ya dawo inda yabar Hannah cikin damuwa ya dubeta

“Haba Hannah baki kyautamin ba kalli yadda yayi fushi, ba  haka mukayi dake ba, anya son gaskiya kike masa?”

“Kwarai kuwa son gaskiya nake masa, kayi kokari nagode daka yi dalilin dayasa naganshi at least dukda yaji haushi amma ka faranta min”

“Dan Allah ina rokonki, karki je gidansu Jalal a hakan ma fama ake akan ya canza halayensa, in kika kuma sanadin lalacewarsa biki kyauta ba, Hannah ke mace ce baza kiso ace Jalal danki ne ko yayankine a haka ba”

Yadda Jawwad yai maganar abun tausayi har Hannah taji yana nema ya kashe mata gwiwa Dan haka da sauri tace

“Thank you, ni na tafi semun kuma haduwa”

Ta juya tai shige motarta, bashi dazabin da ya wuce shima ya tafi, Dan haka ya hau motar da sukazo ya tafi

Bayan sallar magariba Jalila durkushe agaban Ummi tana kuka”Ummi Dan Allah kiyi hakuri, najanyo anzo har Gida anci zarafinki nasan laifinane amma insha Allah bazan kuma ba kiyi hakuri Dan Allah “

Hannu Ummi tasaka tana gogewa Jalila hawaye”ya wuce baby amma ki canza halinki ki rike maraicinki ki dena dakko mana magana”

“Ummi na dena insha Allah”” yawwa baby nima ba a son rains name fushi dake ba” rungume Ummi Jalila tayi”nagode Ummina Allah yabaki tsawon rai me amfani”

“Ameen, Allah ya shiryamin me yabaki miji nagari” shiru Jalila tayi tareda kuma gyara kwanciyarta a jikin Ummi

“Ummi amma kinfasa maidani kano ko?

” tafiyarki kano tana nan”

“Ummi meyasa?”

“Haka mahaifinki yace kafin ya rasu” dagowa tayi ta kalli Ummi

“To amma ai yanzu baban nawa baya nan,”

“Zaki kumako ai bazaki canza halinki ba dagani ni”

Mikewa tayi daga jikin Ummi taje ta samu guri ta zauna tana tunani

Duk yadda Jawwad yaso ya shawo kan Jalal ya nuna masa dalilin dayasa ya kaishi gurin Hannah amma Jalal yaki saurarensa

Haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi gida, yaje yayi salla sannan ya shiga cikin Gida bangaren Abba, ya tarar dashi yana kallon labarai

“Sannu da zuwa Abba ya kabarosu ya hanya”

“Lafiya kalau Jawwad, ai tun dazu na dawo naita zuba ido in ganka, amma banganka ba”

“Mun Dan fitane da Jalal, Abba ya akayi da case din, munyi ways da wani Dan ajinmu yacemin ai ita yarinyar kanwarasa CE”

“Eh kam mun hadu yace ya sanka, ajinku data, Ai Allah ya temakemu abun yazo da sauri,”

Abba ya labartawa Jawwad abunda ya faru

Jinjina kai Jawwad yayi”amma Abba Jalila takirani a waya tana kuka, tace kunce nan zata dawo, zama tare damu”

Murmushi Abba yayi

“Hakane amma Dan mu tsorata ta ne mun yanke seta kammala wannan ajin da take, sannan zata dawo nan, kasan wasiyyar kanina kenan, gara ta dawo nan maybe sekaga ta nutsu”

“Hakane, to Abba ita ummin fa haka zata cigaba da zama ita ka dai”

“A a Jawwad itama zata koma gurin iyayenta ne, intaje insun karbeta se akai Jalila taga dangin mahaifiyarta, ina ganin in Jalila ta dawo nan bata ganin idon umminta zata dena fitina”

“Hakan yayi kyau Abba Allah yasa mudace,” 

“Ameen Jawwad”

Download>>> Yaro Ne Complete Document


Haka suka cigaba da tadi daga baya Jawwad ya fito ya koma gurin Jalal amma da yaje baya nan ya kirashi a waya amma baya dagawa,

Girgiza kai Jawwad, yayi yasan ba makawa Jalal ya tafi mashaya

Aikuwa hasashen Jawwad yazama gaskiya domin kuwa don kuwa bayan abunda yafaru tsakaninsa da Hannah da Jawwad, Jalal yakoma Gida yaji ransa yakiyi masa dadi, ransa yagama baci Dan haka ya fita ya tafi mashaya

Aikuwa Jeje ya takewa Jalal cikinsa da giya yayi mankas ya fita hayyacinsa sannan ya kalli Jalal

“Mutumina wai me yabata maka raine haka naganka some how”

Cike da maye Jalal yafara magana yana tangadi

“Wata usless creature ce take son takurawa rayuwa ta, ga Jawwad shima ya bata min rai mtseww, wai meyasa mata suke da matsala kasan mene ma”?

Murmushi Jeje yayi

“sekafada nawan”

“Kasan wannan kanwar tawa ko? Ilham itama fa hadamin zafi tayi da safe so nayi in tattakata amma Jawwad ya hanani kaga itama wannan banzar da take takuramin wallahi so nake inyi maganinta”

Seda Jeje yakuma banka masa giya sannan yace

“To meye a ciki man Hannah ta kai macen daza a sota she’s so beautiful fa” Jeje ya dakko waya yana nuna masa hotunan Hannah da wasu irin kaya a jikinta me bayyana surarta

Ture hannunsa Jaalal yayi yana tsaki

“Kai jeje ni bana sonta bana son shirme aikin banza kaima batamin rai zakayi meye hakane kakeyi”

Jalal Ya mike yana tangadi yana shirin tafiya 

Jeje a ransa yace lallai gayen nan akwai taurin kai a bugen ma yana da lissafi amma muje zuwa zaka gane kuskuren ka 

A zahiri kuma mikewa Jeje yayi ya riko Jalal in bahakaba ze iya faduwa, Dan baze iya tuki ba Dan sosai yake tangadi

Ilham ce take ta kaiwa tana kawowa a dakinta tana tunanin me yakamata tayine, dan tayi Alkawarin fitinar Jalal tako ina bazata bari yafara soyayya da wata banza ba, ba itaba Dan hakan dai² yake da rushewar shirinmu ana samun kuskure komai ze lalace, dabara ce ta fado mata

Dan haka gaban mudubi taje ta zauna, ta fara shafa mayuka a jikinta, tareda fara tsara simple make up a fuskarta, dogon wando tasaka skin tied se wata karamar Riga body hook, ta dakko wannan turaren ta shafe jikinta da shi, parking din gashinta tayi ta Dan Dora mayafi akanta ta nufi hanyar fita 

Jeje ne yakawo Jalal gida a buge part dinsa ya kaishi ya kwantar da shi

Jawwad da yake kofar gida yaga wucewar motar Jalal koba a gaya masa ba yasan Jeje ne yakawo Jalal, kuma ba makawa a buge yake, girgiza kai Jawwad yayi cikin bacin rai yakoma cikin gida

Bayan jeje ya kwantar da Jalal ne yazo fitowa daga part din Jalal sukayi clashing da Ilham

“Wow so cute, common beb u look so beautiful”

Jeje yai maganar yana mata wani shedanin kallo

“Kai kashiga hankalinka, ka kiyayeni, bani hanya”

“Meyasa kikeso in baki hanya me zakije kiyi masa? Gaskiya na kyasa ya za ayine?”

Wani mugun kallo Ilham tayi masa

“Eh kaman ba gidan ubanka bane nan, meye na tambayata me zanyi masa kai me kayi masa, ka kiyayeni ka fita hanyata, niba Sa arka bace sakarai kawai”

Ta hankade Jeje ta wuce ajiyar zuciya Jeje yayi “gaskiya yarinyar nan ta hadu I have to do something”

Yasa kai ya fice, Ilham har cikin bedroom din Jalal ta shiga ta ganshi kwance yayi dai² akan gado yana bacci. Murmushi Ilham tayi ta shiga cikin dakin ta samu gefen Jalal ta zauna hannu tasa ta Dan shafa sajensa zuwa cikin sumarsa

Dan jijjigashi take

“Yaya Jalal wake up please”

A hankali ya bude idonsa da sukayi jawur, saboda buguwa ya mayar ya lumshe sannan ya fara magana a cikin mayae

“Ni wannan yarinyar bana sonta, narasa meyasa Jawwad yayi min hakane, nace masa bana so amma shi……se wani”

Sekuma yayi shiru, Ajiyar zuciya Ilham tayi tace”munafukan banza daga Jawwad har kanwar tasa, zasu gane kurensu

Matsawa takuma yi ta kwanta a jikinsa sannan ta Dan dago ta kalleshi

“Meyasa baka sonta”

“Mtseww nifa bana son tambaya, bana sonta kawai bata da hankali,” ya Dan girgiza kai ya yamusta fuska warin turaren nan yaji da yabaya so

“Itakuma Ilham meyasa baka sonta?”

Dan bude ido yayi ya mayar ya lumshe”wannan fa kanwata ce, meyasa zanyi wani soyayya da ita, kanwata ce kawai”

Shigewa jikinsa ta kumayi sosai 

“But I love you, karkayi soyayya da wata bayan ni, Ilham ce kawai take sonka, sauran duk bamasu kaunarka bane, Ilham tana sonka kaima kasota kaman yadda take sonka”

Dukda yana cikin maye setaga yayi murmushi”ka yadda zakaso Ilham”

“Bacci nakeji ki kyaleni da wannan mafarkin”

“Mafarki kake?”

Ya gyda mata kai “ya kusa faruwa a zahiri” 

Tai maganar tana shafa gashin kirjinsa ya mutsa fuska yayi ya rike mata hannu”kidena bana so”

“Meyasa bakaso?”

Shiru yayi be ce mata komai ba

“Shikenan tunda bacci zakayi bari in tafi,”

Durkusowa tayi da nufin tayi kissing dinsa se ya juyad da kansa alamun baya so, kallonsa tayi

“Why?”

“Ki tashi ki bani guri nace miki bacci zanyi”

Gabanta ne ya fadi dataji yayai normal magana ba tare da maye ba, kallonsa tayi taga ya bude idonsa fes akanta, sekuma ya mayar ya lumshe yacigaba da bacci Ajiyar zuciya tayi tare da fading”Allah ya temakeni na dauka giyar tasakeshi ne”

Kissing dinshi tayi akan lips dinsa sannan ta mike ta fita ta nufi cikin Gida, me gadi ya hango fitowarta daga part din Jalal

“Kai me yarinyar nan take a bangaren yaron nan a wannan tsohon daren,

Allah ya kyauta bayan shan giya kuma yafara biye² mata, abun kunya kuma da kanwarsa Allah ya shirya”

Da safe Jalila tanata shirin makaranta, wata makwabciyarsu bata  wuce sa ar Jalila ba ta shigo tacewa Ummi Dan Allah ta sammata abunda ta girka ita tayi girkin takasa ci dayake tsohon ciki ne da ita 

“Allah sarki hawwa’u Allah yaraba lafiya bari azuba miki

Jalila zubomata abinci”

Jalila kam zuwa yanzu Hawwa haushi take bata gani take tsabar kwadayine da iskanci komai bazata iya Ciba sena gurin ummi, Ummi kuma bata taba hanata ba ko kyararta

Jalila tana zumbura baki taje ta zubomata dataga ummi bata kallonta ta dungurar mata da kwanon da kayan tea

“Gashi nan kwadayayyiya seki hada Sa kanki niba Yar aikinki bace”

“Eh naji kwadayaiyiyyar ce ke in naki yazo maga yadda zakiyi”

“Bawani nan komai kidorawa ciki, dayana da baki se yace karya kike masa”

Dariya Hawwa tayi ta hada abincinta ta fara ci suna hira da ummi tana gama ci ta kama aman abincin nan dataci seda ta amayar tsaf

“Kai kekam kin banu sekace akanki aka fara ciki ga rakin tsiya ni bari in bar gidan nan tun kafin nima kisani aman”

Jalila tai maganar tareda daukar jakar makarantarta tayi waje

Girgiza kai ummi tayi indai Jalila ce bazata canza ba

Download>>> Yar Harka Complete Document

Wajen karfe Tara sannan Jalal ya tashi daga nannauyan baccin da yayi kansa yana ciwo, jiyayi yana warin turaren Ilham tsaki yaja yafara tunanin abunda yafaru wannan wane irin sha³ mafarki yayi kuma ma da Ilham (shi a zatonsa abunda yafaru mafarkine)

Mikewa yayi yaje yai wanka ya fito yayi sallar asuba karfe Tara na safe

Jalila tana kokarin shiga makaranta taji ana tayimata horn bata waiga ba ta koma gefe akakuma tahowa inda take a fusace tajiyo tana masifa

“Wai meye hakane anyi Horn na canza hanya ankuma biyoni if you like bi ta kaina komawaye”

Bude motar yayi ya fito tana dariya Allah yabaki hakuri Yar baba,

Yayan Hanan ne Abdallah yakawo Hanan makaranta murmushi Jalila tayi

“Au ai bansan kai bane ina kwana”

“Lafiya kalau ya mamanki”

“Tana lafiya”

Juyawa yayi ya kalli motar yace”ke Hanan fito mana kin wani Zauna a cikin mota”

Sannan ya dawo da kallonsa kan Jalila “Yar baba kaman kuwa kinsan daddy yace agaisheki har yabada sako abaki”

Hanan ya kalla wadda se wani cika take tana batsewa 

“Hanan bani sakon nan”

A wulakance ta bude Jakarta ta miko masa wata Leda

Ya karba yabawa Jalila

“Kai amma nagode sosai Yaya Abdallah ka cewa baba Yar baba ta gode, Allah yasaka masa da Alkhairi yabashi abunda yake nema duniya da lahira, Allah yabashi ladan kyautatawa marainiya”

Ba Karamun burge Abdallah tayi ba,”zangaya masa insha Allah”

Tsaki Hanan tayi ta wuce abunta cikin school, Jalila ma cikin makaranta ta shige, duk zafin kan Hanan bata kuma kallon seat din Jalila ba balle takuma sha awar zama a gurin, 

Zama Jalila tayi ta dakko abunda akabata chocolates ne kala² a ciki murmushi tayi gaskiya mutumin nan yana da kirki

Bayan anfita break Jalila taje seat din Hanan ta zauna a kusa da ita kawata ya kike

Wani mugun kallo Hanan tayi mata ta dauke kai, bude chocolate dinta tayi tafara sha sannan ta kalli Hanan kawas

“Bismillah”

“Abun ya fito daga gidanmu sannan kice insha ke dai da kike kwadayaiyiyya seki sha dama Dan talaka akwai iya shishshigi,”

Murmushi Jalila tayi sannan tace “duba ajin nan akwai yayan Wanda sukafi mahaifinki dukiya, amma abun be baki mamaki ba ina Yar talaka amma nake makarantar yayan attajirai kaman Hanan rasheed, ashema Baku wani Tara ba tunda har Yar matsiyata kamar Jalila Aliyu take a irin makarantar Ku”

Mike kafa Jalila tayi ta Dora a saman bencin 

“In ana batun gata Hanan, be kamata kisaka baki ba, Dan baki da gatan da Jalila take dashi”

Jalila se gayamata bakaken maganganu take tana shan chocolate dinta, Hanan tana fargabar ramawa saboda gani take Jalila bata Risina ba zata iya maimaita mata abunda tai mata amma duk da haka ta dake tana ramawa

Jawwad ne yakuma dawowa gurin Jalal amma Jalal yayi masa banza yaki kulashi, haka ya hakura ya tafi ya kyaleshi

Bayan an tashi daga makaranta Jalila ta dawo Gida amma ummi bata nan wani bakin ciki Jalila taji ta tsani ta dawo Gida taga ummi bata nan 

Waya ta dakko ta kira ummi

“Ummi ina kika tafi ne?”

“Kinganmu a asibiti Hawwa muka kawo ta haihu Dan ba rai yanzuma Karin jini ake mata”

Zaro ido Jalila tayi 

“Wace hawwan dazu fa da safe tazo”

“Bayan tafiyarki tafara nakuda”

“To meyasa akayimata aure yanzu se wahala takesha?”

“Aa seki bari in danginta sunzo ki tambayesu”

“Allah yabaki hakuri itakuma Allah yabata lafiya amma Dan Allah ki dawo Gida”

“Bazan dawo ba din a can zan zauna”

Ummi ta kashe wayar

Seda Jalal ya shafe sati baya kula Jawwad, sekuma daga baya Dan kansa ya sakko, suka shirya

yayinda kullum se Jalal yaje mashaya, Hannah tasamu damar cigaba da cusa kanta, a gefe daya itama Ilham tanata nata kokarin, sunsaka Jalal a gaba, Jalal dai se kara shirircewa yake

Alhamdilillah Neman maganar Jalila daga Islamiyya har boko yayi sauki, ta fara nutsuwa, yayinda mahaifin Hanan keta kyautatawa Jalila, amma Jalila ta takurawa Hanan, kullum tana manne da ita, Hanan ta zageta ta gaya mata bakaken maganganu amma Jalila batajin haushi takance mata”Hanan mahaifinki yana da karamci, yana kyautata min, komai zakiyi min bazanji haushi ba, shiya hadamu kawance kuma ni na karba”

Hanan mulkinta take zubawa a cikin makarantar daga malamai har dalibai shakkata sukeyi,amma banda queen J

Watarana anayiwa wata Yar ajinsu Jalila birthday a aji, kunsan yayan masu kudi aka dinga jijjiga champaign suna sakinta a sama, suka dauki turare suka dinga fesawa a ajin sun ware kida suna cashewa

Hanan ce ta nufo ajin ta shiga tana shiga wannan kamshin turaren da akasaka ta shaka nan take ta fadi kasa dama tanada asthma, da sauri Jalila taje kanta tana jijjiga ta

Yan ajin tsayawa sukayi suna kallon Hanan data ke ta fama da numfashi, 

Jalila ta dinga jijjigata “Hanan meyafaru, ki tashi”

Jalila taga hakan bazeyiba tasa ta dago Hanan ta rungumeta zata fita da ita amma jikinta yariga ya saki yan ajin suna kallo ba Wanda yabi takan Hanan saboda rashin mutuncinta balle ayi tunanin me temakamata

Jalila ce kawai taketa kici² da hanan, ana haka Sega siyama 

“Jalila meyasameta?”

“Nima bansaniba amma kaman asthma ne,”

Jalila da siyama ne suka kama Hanan suka kaita school clinic akaimata abunda yakamata amma babu wani cigaba duk ta fita hayyacinta 

Aka kira gidansu hanan aka sanar dasu, sukace akaita wani asibiti private anan likitan dayake duba hanan yake, 

a motar makaranta aka saka hanan Jalila tana rungume da ita tana mata fifita

Suna zuwa aka karbeta aka fara yimata abunda yakamata har tasamu bacci 

“Likitan ya kalli Jalila yace sister din kice”

Gyada masa kai tayi 

“Ya akayi bansanki ba kuna kama sosai”

Banza  Jalila tayi masa tacigaba da kallon hanan har cikin zuciyarta ta kejin ba dadi halin da hanan ta shiga, saboda bata manta lokacin da hakan yafaru da ita a kanoba lokacin da Jalal ya duramata sigari, ta sha wahala amma condition din Hanan yafi worst 

DOWNLOAD: “HARIJI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT”

Se da baccin Hanan yayi nisa sosai, ga lokacin ta shi yayi Dan haka Jalila ta mike ta tafi Gida aka bar Hanan da wata malama a harabar asibitin taga daya daga cikin motocin gidansu Hanan ta shigo,

Ba ta tsyaba tayi tafiyarta Gida,

Ummi ke tambayarta ina ta tsaya tagaya mata abunda yafaru

Dan kallonta ummi tayi taga duk ta damu a ranta tace Allah sarki baby halinki halin abbanki ba kya riko sam,

“To Allah ya sawwake yabata lafiya”

“Ummi zakije dubata?”

Hararar Jalila tayi ta cigaba da aikin ta,

Washe gari da safe Jalila ta shirya ta dama kunun gyada ta zuba a flask ta tafi asibitin da aka kwantar da hanan, room din da Hanan take taje ta bude kofar ta shiga, mum Hanan ce a zaune tana ta fama da Hanan taci abinci taki, “ina kwana”

Jalila ta gaida Maman Hanan

“Ke mekikazo yi nan”?

“Hanan nazo dubawa”

“Waya nemeki, munji mungode, jeki Allah yabada lada”

“A a mummy dubanifa tazo, shigo kawata”

Hanan tayi maganar tana kallon Jalila,mikewa Jalila tayi taje gefen gadon Hanan ta zauna

“Sannu Hanan ya jikin baki”?

” da sauki Jalila, yau za a sallamemu ma”

“Allah yabaki lafiya, ga kunun gyada na kawomiki ni zan tafi makaranta”

“Jalila nagode sosai da abunda kikayimin jiya,”

“Bakomai manta kawata, Allah yabaki lafiya”

Jalila ta mike ta kalli mummy Hanan

“Mummy se anjima”

Dauke kai mummy tayi batace komai ba, Jalila na waigowa zata fita taci karo da Abdallah abakin kofa a tsaye, yaga duk abunda yafaru gaisawa sukayi ta ratseshi ta wuce

Bakin gadon Hanan yaje ya zauna”sannu autar mummy “

“Yaya kasan wani ABU?”

“A a sekin fada”

“Yanzu nakejin ban kyautaba abunda na dingayiwa Jalila a baya ba, bakaga yadda ta dinga kula dani jiyaba, kaman Yar uwata, ban tabajin naji babu dadi ba saboda na wulakanta mutum ba se akan Jalila”

Murmushi yayi”auta kinga illar wulakanta mutum ba, yanzu dai kwanta ki huta”

Tsaki mummy tayi ta tashi tabar dakin 

  Tundaga wannan ranar Hanan ta sake da Jalila har ziyara take kaiwa Jalila, ga kyautatawa da mahaifin Hanan yake yiwa Jalila, a sanadin Jalila Hanan ta dena wasu daga cikin halayenta marasa kyau

Haka lokacin ya dinga tafiya Jalal ya cigaba da fuskantar barazana a cikin rayuwarsa ga Hannah tasashi gaba, gefe ga Ilham da itama take uzzurawa rayuwarsa danma ita Ilham yanacin kaniyarta, ga Jeje da yake ta kuma rusa rayuwar Jalal, lalacewa har tafi baya, danma Jawwad yana kokari akan Jalal

Lokaci² Jalila takan yi miyagun mafarkan data sabayi da Jalal

Abun yana damunta sosai a rai,

Duk mafarkan da take dashi se dai taganshi a mawuyacin hali.

Yaune ake taron iyaye da yan uwa na kimanin dalibai arba’in na set dinsu Jalila, taron ya kunshi manyan mutane da iyayen dalibai, taro yayi taro inda aka karrama dalibai da dama, can na hango Jalila cikin graduation gound tayi kyau matuka takara girma tayi wani irin kyau, Jalila tana cikin dalibai naga ba da aka karrama da iyayenta, ta karbi kyautuka da dama sunyi hotuna da malamai da dalibai yan uwanta, mussaman Hanan da siyama ga Jawwad da Abba gefe ga ummi sunji dadin yadda sukaga ana ji da Jalila a cikin dalibai, a matsayinta na shugabar dalibai tayi speech me matukar ma’ana, ta birge mutane da dama, sunyi kukan rabuwa da dalibai sakamakon shakuwa da sukayi, haka taro ya tashi farin ciki fal zukatan dalibai

  Bayan sunkoma gidane Jalila da Jawwad suka tafi yawo cikin garin Kaduna yayinda Abba da ummi suke tattaunawa akan makomar rayuwar Jalila, Jalila taji dadin fitar da sukayi da Yaya Jawwad sunsha yawo sosai tare da hira 

“Baby naji dadin ganin yadda aka karrama ki gashi kinkara kyau kin girma u look so beautiful”

Murmushi Jalila tayi

“Yayana na kaina, jajircewar Abba ce tasa na taka duk wani matsayi a yanzu bazan manta karamcin Abba ba Allah yasaka masa da alkhairi”

“Ameen baby?”

“Amma Yaya Jawwad,Ina Jalal?”

Subucewa maganar tayi taji ta fito ba tare da ta shirya ba

Kallonta Jawwad yayi

“Meyasa kike tambayarsa bayan ba kyayimasa addua”

“Kawai tambaya nayi amma ina yimasa addu’a”

Gyada kai Jawwad yayi

“Jalila al amuran Jawwad se a hankali abun nasa sedai addu a kawai 

Yana nan yadda kika sanshi, yama fida”

“Kuma har yanzu kana tareda shi?”

“Eh muna tare Jalila bazan iya rabuwa da shiba”

“Amma meyasa?”

“Kin manta alkawarinmu sekinzo kano zan gaya miki”

Gyada kai Jalila tayi sannan suka nufo Gida

Bayan sunkoma ne Abba da Jawwad suka tafi, tun bayan tafiyarsu Jalila ta fuskanci ummi bata da walwala tana cikin damuwa sosai lokaci² takan share hawaye

“Ummi wai meya farune me akayi miki, meyasa ki damuwa haka, kona bata miki Raine?”

“A a Jalila lokacine yayi daza a cika wasiyyar mahaifinki, zaki koma gurin wan mahaifinki, nima zanje ganawa dangin, munyi magana da Abba sati me zuwa insha Allah zezo ya tafi dake”

Ummi tayi maganar cikin kuka

“Gaskiya ummi ni ba inda zani ina tare dake, bazan iya zuwa wani guri in rayu ba tare da ke ba,”

“Am sorry baby wannan karon dole kiyi hakuri, nima zani inga iyayena, komawarki kano ba yana nufin mun rabu baneba”

“No ummi seda na rayu da soyayyarki for all this years lokaci daya acemin wai sena barki dama dagaske kike, ummi dama uwa zata iya Barin yarta?”

“Baby illa ne ga ratuwarki a matsayin ya mace ace kin girma an ta shi aurenki amma ace babu namiji tsayayye akanki, kiyi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa,

Zankoma ahalina kicigaba da zama a dangin mahaifinki ya aurar dake”

Kuka sosai Jalila ta dingayi ranar da take ta farinciki a gareta ta koma mata ta bakin ciki tayi kuka har ta gaji, haka nan yan kwanakin nan ta dinga yinsu ba kuzari se aikin kuka kawai ummi kuma se rarrashinta take tare dayi mata nasiha

“Baby duk inda kika samu kanki kizama me tsoron Allah, ki rike mutuncinki, kizama me tsoron Allah ki rike amanar tarbiyyar danayi miki, ina kaunarki baby nima ba a son raina hakan zata farm r̃

Ita dai Jalila jin ummi kawai takeyi 

Saura kwana biyu tafiyar Jalila taje yiwa Siyama sallama sun sha kuka sosai Maman Siyama tai ta bata hakuri tayiwa Jalila alheri 

Siyama ta tafi raka Jalila gidansu Hanan, Hanan rudewa tayi 

“Jalila meyasa zaki tafi Zuwanmu Kaduna na kiyi abubuwa da yawa a gurin ki, meyasa zaki tafi bani da wata Yar uwa sama dake”

Duk yadda Jalila taso dakewa kasawa tayi suka dinga kuka Hanan tai musu jagora har gurin daddy, haka nan yaji ba dadi mussaman yadda yaga sunata kuka

Jalila tasoyi masa godiya kan alkhairan da ya dinga yimata amma kuka ya hanata nasiha yayi mata shima sannan yace insha Allah har kano zasu dinga kawo mata ziyara

Haka ta koma Gida ummi ta hada mata kayanta cif, data kalli kayan seta kuma fashewa da kuka

“Baby kukan nan ya isa haka, kirike abubuwan danake gaya miki, kizama me hakuri da rayuwa duk inda kika tsinci kanki, ki zauna da kowa lafiya, ki rikemin amanar kanki da tarbiyyar danayi miki,

Baby duk mijin da Allah yabaki ki masa biyayya, kiyi hakuri dashi”

“Ummi wai ya kikemin magana kamar me wasiyya”

Murmushi kawai ummi tayi tanaji a jikinta akwai wani abu daze faru da Jalila a kano amma ta dake taketa kokarin kwantar da hankalinta 

Download>>> Babban Yaya Complete Document

To kome ze kasance in ummi ta koma garinsu?

Wace rayuwa Jalila zatayi a kano?

Ya makomar rayuwar Jalal?

Waye Jalal ?

Meze faru da Jalila zamanta a kano?

Meye alakar Jalila da Hanan da suke kama?

Tskanin Jeje dasu Ilham suwa ke nasara akan Jalal

Dama sauran tarin tambayoyinku Ku cigaba da bina sannu a hankali domin samun amsoshinku

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Daga alkalamin (daddy’s girl)

Back to top button