Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 10 Complete Hausa Novel

BAYAN KWANA BIYU

Mama ce zaune tana tattare kayan da zainab za ta tafi da su gidan miji

Duk wani abu da ba dashi zata tafi ba ta ware shi a gefe

Zuguɗi Zainab tayi tana kallon mama, 

Tunda aka kawo lefe mood ɗin ta ya canza gaba ɗaya, ta ƙara tabbatar da lallai tafia fa zata yi

Tas mama ta gama haɗa kayan a ƙatuwar jaka ta aje a gefe, waigowa tayi ta kalle ta, tace

“kinga shikenan an huta, wanda suka je jere se su jera miki su”

Shiru zainab tayi bata ce komi ba, gaf da maman zata fita zainab ɗin tace

“Dan Allah mama baza’a ƙara kwanakin ba?”

Dawo tayi ta zauna a kusa da ita, dafa kafaɗar ta tayi ta ɗan kwanto da ita kaɗan jikin ta, sannan ta fara magana a tausashe

“Banda abinki zainab, a ina ma kika taɓa ganin an ɗaura auren budurwa kuma an barta a  gida na tsawon kwanaki?”

Batace komi ba, maman taci gaba

“Ki saki ranki, ki ci gaba da walwalar ki kamar yarda kika saba, 

Ƴa mace dama komin daɗewar ta indai da rabo dole wata rana ta tashi daga gaban iyayen ta, itama taje can ta haɗa nata iyalan, haka rayuwar take, 

Bana son ko kaɗan naga rauni ko damuwa a idanun ki zainab, 

Ba kiga muma duk an rabomu da iyayen mu ba? kuma gashi har nazo na haife ku,kuma bani da inda yafi nan?to kema kisa hakan a ranki kinji?”

Gyaɗa kai zainab tayi, sannan tace

“Mama, amma dai harda ke zamu tafi ko?”

Dariya mama tayi tana miƙewa, sannan tace “Allah dai ya kaimu jibin lafia”

Bayan mama ta fita daga ɗakin, komawa zainab tayi tai kwanciyar ta duk da hayaniyar surutun mutane da suka ɗan fara zuwa ana ta kwasan shafta besa ta fita ba

Tana nan a kwancen yaya Abida(matar yaya Abubakar)  ta shigo ɗakin, hannun ta ɗauke da manyan ledoji guda biyu

A nan gefen gadon ta aje itama ta zauna.

kallon zainab tayi da ta rufe ido, tace

“nasan ba bacci kike ba, tashi ga kayan nan ki duba ki gani”

Banza tayi da ita, bata tashin ba bakuma ta ce komi ba

Ɗaka mata duka tai a baya, 

Zumbur zainab ta miƙe zaune tana sosa wajen, cuno baki tayi tace

“Kai yaya Abida, ai se ki saka mutum ciwon kai wallahi”

Banza tai da ita, taci gaba da firfito da kayan dake cikin ɗayar ledar tana dudduba sunan da aka rubuta ajikin kowacce

Riga ɗaya zainab ta ɗaga, baki buɗe tace

“wai dan Allah da gaske seda kukayi ankon nan?”

Can ta ƙaracewa “wallahi kuna da aiki kam”

Yaya Abida tace “Ba ruwan mutum, ɗayar ledar kayan ki ne na walima da wanda zaki shigar biki, anjima yayan ki yace ze tawo da hijaban”

“Humm” zainab tace, ta koma tai kwanciyar ta.

Gaba ɗaya yaya Abida ta gama fitar ma da kowa na shi, ta aje anan, 

Har ta juya zata fita, ta dawo ta ɗauki na IYA sannan ta fice.

IYA na zaune cikin ƴan’uwa da suka fara yo gaba ana ta fira da nishaɗi, 

Yaya Abida ta tsallaka  inda suke zaune ta aje ma IYA tata ledar a gaban ta, tace “ga naki kema hajiya IYA”

Buɗe ledar tayi ta ciro kayan, 

Kallon Abida tayi tace 

“Abida wannan fa, name ne?”

“Ankon ki ne kema, ɗazu baban Amir ya kawo yace hada naki”

Da sauri IYA ta wancakalar da kayan gefe, murya ƙasa-ƙasa tace

“kiyi ta kanki wallahi Abida, ni nace muku ina da ra’ayin saka anko?, to wallahi bance ba, ku ɗauki abun ku, ku da kuka ga  zaku iya saka kanku a masifa ba se kuyi ta yi ba, ni kam ba ruwana”

Mama dake can gefe tace

“Waye yace ayi da IYA, ɗauka kikai ɗaki na ai ba nata bane dama”  Mama ta yi maganar tana ƙyaftawa Abida ido.

Ajiyar zuciya Iya ta sauke, sannan tace “har na ɗan samu nutsuwa wallahi”.

***Ta ɓangaren su Abdul ma ba zama sam, Duk da dai anyi ɗaurin aure, kuma ba wasu abokai ke gare shi ba

Su Amal ne ma suka dame shi da se anyi dinner

Ba abunda ya fito bakin Abdul, se cewa yayi

“Abie ze ƙwace ƴar shi kenan yara”

Ba wanda be dara ba a wajen, abokan wasa na ta tsokana

Daddare bayan ya dawo yake ce ma su Amal ɗin, 

“ku shirya, gobe zasuyi walima a gidan su se mu kai ku”

Da murnar su suka haɗa baki wajen faɗin  “yauwa yaya Abdul”

Amal da ta ɗan fi fauza rawar kai, ta kalle ta tace  “wani irin shiga zamuyi?”

Kafin Fauza ta yi magana, Abdul yace

“Wallahi ku zumbuɗa hijabai, gidan malamai zaku je”

RANA BATA ƘARYA….

Ga zainab dai durƙushe gaban Abie lulluɓe cikin babban hijabi

Gaba ɗaya yayun su shida duk suna zaune a palon, ga Mama zaune ga Iya, se ƙannen Abie su biyu

Zainab na zaune a tsakiyar su, palon ya ɗauki shiru baka jin komi se shashshekan kukan zaiinab dake nukurƙusar Abie da mama a can cikin ransu.

gyaran murya Abie yayi, ya maida idon shi a kan IYA dake ta matsar ƴan ƙananun ƙwalla, yace

“Bisimillah IYA, kar a ɓata musu lokaci”

Banza Iya tayi da shi ta kalli gefe, seda ya ƙara magana, tukun tace

“ka kiyaye ni wallahi, ka tufa mata abinda zaka tofa mata aje a kaita kawai, wani gulman ne zaka wani ce “IYA bisimillah” ai sarai ka san bani da abin cewa”

Shiru ɗakin ya sake ɗauka, Abie ya sake yin gyaran murya, sannan ya ɗora da

“Inallahamdulillah, yayi godiya ga ubangiji sannan ya fara ma ɗiyar shi nasiha da kuma jan hankali game da zamantakewar aure, 

Ya kai lokaci me ɗan dama yana yi kafin daga baya ya rufe da addu’a”

Ɗaya bayan ɗaya Abie ya tambayi yaran na shi ba wani abu da zasu ce? 

Duk a’a suka ce, sedai addu’ar zaman lafia

Mama da aka tambaye ta, cewa tayi

“mun gama da wannan inshaAllahu, Allah yasa mutuwa ce zata raba su”

IYA da tace ba ruwan ta, kamar warce aka mintsila tace

“Har angama banji wanda yace ba ruwan ta da kishiyar ta ba”

Ba wanda yace komi, sarai kowa yasan inda IYA ta dosa, 

Ganin ba wanda ya tanka mata yasa taci gaba da magana

“Wallahi kibi a hankali, tun da dai iyayen ki sun ji kuma sun gani suka haɗa ki KISHI DA ALJANA, to se kin cire naki kishin kin kwantar da kai, 

Ki zama kamar doluwa in kina son ki tsira da mutuncin ki, in da hali ma zaki iya barmata mijin duk dan a zauna lafia, hanyar lafia akace abita da shekara ko?”

Ba dauɓi wanda ya ce uffan, ta ɗora

“Nasan a al’adance raba kwana ake, to ki sani in ranar girkin ta ne, ki tabbatar kafin naki ya fita kin shiga ɗakin ki da komi gudun matsala, sann

Kafin ta sake cewa komi, Babban ɗan Abie ya miƙe, kama hannun zainab ɗin yafi ya tayar da ita, sannan yace

“angode IYA, faɗan ya isa haka”

Taɓe baki IYA tayi tace

“Koma ba’a gode ba ai dai na faɗi gaskiya, Zainabu na ko ba ke kika ce min Allah ya na son me faɗin gaskiya ba?, kuma ai ciki da gaskiya wuƙa baya taɓa huda shi”

Kusa da Abie zainab ta matsa ta rungume shi, 

Murya cikin kuka tace

“Ina neman yafiyar ka akan laifin da nasan nayi da kuma wanda ban san da shi ba Abie na”

Nan da nan zuciyar Abie ta karye, idanuwan shi suka kaɗa sukai jaaa, murya a sanyaye yace

“Na yafe miki Zainab, Allah yayi miki albarka ya shiga lamuran ki”

Da “Amin” ta amsa sannan ta sake shi, ta taka ta tafi wajen mama

Rungume ta tayi itama, kuka na ƙoƙarin cin ƙarfin ta tace

“Mamana kema ki yafe min dik rashin jin da na rinƙa miki da bakya jin daɗi”

Kasa magana mama tayi, kuka na ƙwace mata

Da ƙyar ta iya faɗin “Allah yayi miki albarka”

Abie da ƙiris ya rage shima ƙwalla ta fito mishi ya, 

“ku tafi da ita muhammad, kaima ubane a gareta, Allah ya bada sa’a”

Yayun faba ɗaya suma jikin su yayi sanyi, a tsakiya suka saka ta, 

Har ta kai ƙofa, suka haɗa ido da IYA da itama gaba ɗaya idanun ta sunyi jaa

Fasa fita tayi, taje ta rungume ta, murya cikin kuka tace

“IYA ta kema ki yafe ni, ina son ki sosai, sannan bazan taɓa yin fushi da duk abinda kika ce ba, abu ɗaya nake so in gaya miki 

In bawa ya riƙe Allah, ba wani halitta da ya isa ya cutar da shi, “addu’ao saiful mu’i’min” ma’ana, addu’a makamin mumini ce.

Kema kici gaba da taya ni addu’a, Allah ya bani nasara akan abinda zan tunkara a yanzu”.

Su kansu yayun ta duk dauriyar su seda kowa ya karkace yana shawarar ƙwalla

Mama kam barin ɗakin tayi, dan bazata iya tsayawa ba, tasan kukan ta ze ƙara karya ma zainab gwiwa ne.

Abie ma toilet ɗin palon shi ya shige, sam shima ya kasa riƙe nashi hawayen.

Gam IYA ta riƙe zainab, suka fara takawa a tare,

Shauƙin tausayin da ta shiga ne yasa har ta saka ƙafar ta a mota bata ankare ba

Zainab na rungume a ƙirjin ta, tana sharar hawaye

Motocin da suka zo ɗaukan amarya suka fara ɗagawa.

Motoci ne guda goma sha biyu reras,

goma warce su Abdul suka kawo, biyi kuma motar gidan Abie ne, haka suka jera reras gunin ban sha’awa suka hau titi.

****Gidan ummie shima damƙam yake da jama’a,

mutane da yawa suka fara haramar zuwa ganin gidan amarya

Suma ba laifi an kawo musu motaci uku, irin manyan bus ɗin nan, wasu kuma suka tafi a tasu.

Motar da aka ɗakko zainab a cikin tace kawai ta shiga cikin gidan

Sauran duk a waje sukai parcking.

IYA na rungume da zainab suka shiga cikin gidan, kai tsaye sama aka haura da ita, 

IYA na rungume da ita, suka shiga har cikin ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake saman

Da bisimillah Zainab ta zauna a gefen gadon ta, sannan iya ta zauna itama a kusa da ita.

A hankali wasu daga cikin dangin Abdul suka fara ragewa saboda gabatowar sallar magrib.

Haka ma wasu daga ƴan’uwan zainab ɗin ma suka fara rarragewa

Wanda sukai saura, duk na jiki ne, an baje ana ta shan drinks da abinci kala-kala da aka kawo

Dukkan su suna a palon ƙasa, banda IYA da zainab dake sama su uku

Zainab ɗin, se iya, se kuma Amal data maƙale, kusa da amarya zainab.

Wasu sun idar da sallah ana zazzaune, basu kai ga yi ba,

ƙiftawa da bisimillah suka ji ɗiff, an ɗauke wuta, ga wata iska me ƙarfin gaske data fara kaɗawa

Nan da nan yara suka fara tsuwar ganin duhu

IYA ma da sam bata ƙaunar duhu ta fara ƙorafi

Kafun iya ta rufe baki suka ji gamm, gammm, windows sun kullo kansu, ƙofofi ma sun kullu kansu

Daga can ƙasa suka fara jiyo salati da innalillahi na muryoyi mabanban ta.

Da sauri Amal ta kunna fitilar wayar ta, zainab ma ta miƙe, kafin kowa ya tashi tsaye, IYA ta riga kowa tashi tana rarraba idanu.

Da hanzari suka nufi ƙofa, dan ihun su ƙara yawa yake, 

Gam-gam suka ji ƙofar a rufe, zainab ma ta gwada buɗewa, amma inaaa taƙi buɗewa

Jiki na rawa Amal ta fara ƙoƙarin dialing number Abdul, 

Wani wawan wulli akai da wayar ta tarwatse a wajen, duhu ya mamaye ɗakin gaba ɗaya, ga kuma razanannen ihun da suke jiyowa daga ƙasa.

Da ƙarfi Amal ta ce

“Innalillahi wa’inna ilahirraji’un, wallahi jana ake yi, kuna ina? ku riƙe ni dan Allah!”

A cikin duhun nan, ba wanda ke iya ganin wani a cikin su

A ruɗe Zainab tace

“Kina ta ina Amal? bana ganin ki”

Ɗif suka ji shiru ba muryar Amal ba kuma motsin ta.

IYA da tai mutuwar tsaye ta ƙanƙame idanun ta, 

takasa cewa uffan, seda taji itama an fara janta, ta kware baki ta zunduma wani ihun da seda ya razana zainab da itama ƙarfin halin jurewa kawai take

“Zainabu, jana ake nima, shikenan mun kawo kanmu gidan da ya zama haramun gare mu, wayyo!”

Zainab da gaba ɗaya ji take kamar an riƙe mata maƙogoro, magana ma na neman ta gagareta

Riƙe IYA tayi gam-gam, amma ina, ƙarfin su da nata ba ɗaya ba

Da ƙarfi da yaji, tana ji aka ɓanɓare hannun IYA daga nata, 

a hankali zainab ta sulale a wajen, ɗif, ta dena motsi.

Kamar ƙiftawar ido, aka dawo da wuta, iskar dake kaɗawa tana jijjiga komi na gidan ta tsaya, 

IYA da Amal, basu san ta yarda akai ba, sedai suka gan su an sakko da su palo inda sauran suke an haɗe su.

jajayen Jemagu da fararen mujiyoyi ne birjit suka cika palon dam, 

Ba wurin da zaka raɓa ka wuce, 

ko miƙewa baza ka iyayi ba saboda yarda suka buɗe fukafukin su suka zagaye ko ina a palon

Sunyi sahu-sahu, suna ta raba idanu, su kalli wancan su kalli wannan

In ka kalli zubin jemagun da kyau, zaka ga fuskar su yayi daban da asalin jemage, 

wani fuska ne kamar na mutum hakan, kamar kuma na wani halittar daban.

Tunda IYA ta ƙyallara ido ta ganta a ƙasa kuma cikin wasu halittu

 bayan ta san da ƙafafuwanta ta haura sama, tace

“Shikenan, lukutar masifar yau akan mu zata ƙare”

Tunda hasken ya dawo, sukai arba da wannan halittu ihun wasu daga ciki ya ƙara ƙarfi

Wanda aka lura a cikin su suna da ƙarfin halin yin addu’a, duk aka bugar da su

Da gudu ɗaya daga cikin ƙannen mama tai hanyar kitchen, 

Cak aka ɗage ta sama, aka dawo da ita inda ta tashi

Tunda Iya taga yarda aka ɗakko ta, ta sake ɓarkewa da kuka, tana toshe baki da hannayen ta dan kar sautin kukan ya fito waje

Gaba ɗayan su sukusan goma sha biyar ɗin dake palon kuka suke, 

Kuka me sauti da kururuwa na tashin hankali

Kaɗan daga cikin su ne ke kiran sunan Allah shima haɗe da kuka

Yaya Abida da ta san duhun garin ta kware yanshareren bakin ta tafara karanto ayatulkursiyu

Ko nisa ba tayi ba, taji an fara zumbuɗa mata bulala a gadon bayan ta, Iya dake gefen ta se da taji saukar ƙarar dukan

Idon ta ƙam a rufe ta rarrafa ta matsa daga kusa da yaya Abida, 

Memakon taci gaba da yi, inaaa se ihune ya maye gurbin ayatulkursiyun.

IYA da ta baje a ƙasa ta ɗan buɗe ido kaɗan ta kalli yarda yaya Abida ke tare dukan da take sha, tace

“ya kikai shiru ƴarnan?, kici gaba ko mun samu sauƙi”

Ihu take tana faɗin “IYA duka na suke, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Tunda IYA taji kalmar dukan ta ake ɗin da gaske, taja bakin ta tai shiru, 

tunanin addu’ar data fara shima ta kawar da shi, 

a tunanin ta gara mutum yayi ta ɗirka ashariya, da kayi addu’ar kuma asamu wani narkeken aljani ya narke ka a banza a wofi.

Suna a wannan yanayi na firgice da dimuwa

Mujiyar da tafi kowace mujiya a cikin su girma ta bayyana, 

daƙwa-daƙwan idanunta ta zuba musu, 

Daga can kusurwar da zaka fita daga palon suka ji murya mara daɗi amo tace

“Duk ku tashi zaune munafukai!”

Da gudun su, har suna gware da junan su suka tashi, 

Dunƙulewa sukai a waje ɗaya, 

Gaba ɗaya galabaita ya bayyana a fuskokin su

Bama kamar fauza, tunda ta buɗe idon ta so ɗaya taga waɗan nan jemagu da mujiyoyin bata sake buɗewa ba, fuskar nan tata tai jajir tsabar yarda ta runtse ta da ƙarfi.

****Duk wainar da ake toyawa a gidan Abdul bashi da masaniya, amma can ƙasan ranshi ya kasa samun sukuni da nutsuwar zuciya

Gab da za’a je ɗakko zainab, sarauniya Aziza ta kai mishi ziyara lokacin ya shiga wanka a toilet ɗin ɗakin muslim

Tunda ya fara jin sarewar nan tata gaban shi ya yanke ya faɗi, 

ga harshen shi yai mishi nauyin gaske, wankan da yake ma sedai ya haƙura ya zauna, saboda bashi da kuzarin da ze iya ƙarasawa, ga muslim da wasu abokan su biyu da suke jiran shi ya fito su tafi ɗaukan amarya.

Yana ji yana gani, suffar shi sak ta fita daga toilet ɗin.

Can ya jiyo suna ma siffar tashi tsiyar daɗewar da yayi a toilet ɗin

Murya irin tashi sak yaji tace

“ai gara na wanke lungu da saƙo,”

A lokacin da muslim yaji haka, seda ya waiga ya kalli siffar Abdul ɗin da ɗan mamaki a fuskar shi, dan ya san halinn Abdul sarai be fiya sakin baki yana magana anyhow ba,

 basar wa yayi suka fice, sannan ya saka key ya kulle ɗakin Abdul na a toilet zaune.

Yunƙurin duniyar nan Abdul yayi shi, amma a banza, ba wanda ke jin shi.

Seda Aziza ta tabbatar da sun tafi tukun, tace

“Kaɗan daga cikin abinda zan iya kenan, 

“Ku bil’adama kuna da manta alkairi, sannan baku san me ƙaunar ku tsakani da Allah ba”

Ba jira daman take yace komi ba ta ɗora da

“Na haɗaka da Allah akan kar ka yarda da haɗin nan, amma kai kunnen uwar shegu dani ka mayar dani sakara, har ka iya wanke ƙafar ka kaje wajen ta, sannan ka saka sakaran uban ta ya jimin ciwon da har seda na kwanta jinya na ƴankwanaki, ko da dai har yanzu ba warkewa nayi ba, ƙarfin so da ƙaunar da nake maka ne kawai ya fito da ni”

Cikin amon muryar ta sake cewa

“wallahi, se na rama duk wani ciwo da ubanta yaji min akan duk wanda tsautsayi yasa ya taka ƙafar shi a cikin gidana, kuma zan ɓatar da ita warda ka ke tutiya da cewa matar ka ce”

“AZIZ” ta ƙira sunan shi da kakkausar muryar ta mara daɗi tace

“A yau ɗin nan nake so in ɗauki cikin ɗanka ko ƴarka!

Duk jarumta irin na Abdul, se ga shi yana tsiyayar da ƙwalla, idon shi sun kaɗa sunyi jajir, ga shi ƙiri-ƙiri yana so ya yunƙura ya tashi, amma kamar ansaka igiya an ɗaɗɗaure shi.

Kamar da wasa yaji hannayen ta bila’adadin suna yawo a jikin shi, 

Cak ta ɗaga shi ta maida shi ƙasan shower ta fara wanke mishi kumfar jikin shi, tun daga kan shi har izuwa yatsun shi.

Tas ta wanke shi, kuma ta naɗoshi a towel sannan ta fito da shi

Sam baya ganin ta, amma yana jinshi a jikin wani abu rungume kamar bishiya.

Abdul na zaune, amma kamar a cikin tarko yake zaune, gaba ɗaya hankalin shi yayi masifar tashi tunawa da yayi da lallai iyanzu ankai Zainab ɗakin shi, kuma yasan halin Aziza tsaf zata aikata abinda tace ɗin.

A hankali maganganun da sukai da zainab jiya da daddare bayan an tashi daga walima suka faɗo mishi a rai

“Da zaran ka fara jin haka ka rinƙa daurewa ka ambaci sunan Allah, in har ka karanta wannan addu’ar ba wata halitta data isa ta cutar da kai ‘A’UZUBIKALIMATILLAHI TAAMAT MIN SHARRI MA KALAƘ’

Da ƙarfin gaske Abdul ya ambaci addu’ar yana miƙewa tsaye

Da sauri ya ɗauki towel ɗin da ya fita daga jikin shi ya ɗaura

Duk addu’ar data zo bakin shi yinta yake, ya karanta ayatulkursiyu ba adadi

Yana karantawa yana saka kaya, jikin shi ko ta ina rawa yake, Allah-Allah yake ya cimma su muslim kar ta cutar dasu ko taje ta cutar mishi da mata.

A dai-dai lokacin da Abdul ya kori Aziza da ƙarfin ayar Allah, a wannan lokacin an riga da an kai zainab, ba daɗewa, zafin korar da Abdul yayi mata yasa, ta dirar musu ba shiru.

Abinda ya ɗaure ma muslim kai shine, neman da yayi ma Abdul ya rasa lokaci guda, 

Ga kuma wayoyin shi kaf da suke a hannun shi

Shiyasa suka bar gidan amaryar suka koma can gidan Abbah, su duk a tunanin su Abdul ɗin can yayi.

Shiru muslim yayi yana tuna wasu alamomi da ya gani a tare da waccan siffar, kafin kace me tsiga jikin shi ta fara tashi, a ranshi yace

“Allah kasa tunani na ba dai-dai bane”

Sun fitowa gidan Abbah ke nan se ga Abdul ya sauka a acaɓa

Ƙuri Muslin yayi yana kallon Abdul ɗin da gaba ɗaya jijiyoyin kan shi sun fito sunyi ruɗu-ruɗu, yace

“ina ka shige ina ta neman ka?, akwai fa sauran mutane da ba’a maida su gida ba suna can”

Huci me zafi Abdul ya fesar, ƙasa yayi da murya dan baya so sauran abokan suji yace

“Daga unguwar nake fa guy, na kasa gane gidan, kuma wallahi jiki na yana bani akwai wani abu a ƙasa”

Shiru muslim yayi yana haɗiye miyau da ƙyar, 

Yace

“Ban fahimce ka ba guru, ba yanzu muka dawo daga can tare ba, juyawan da zanyi ban gan ka ba, shine nace ko kana nan, amma zaka kawo wani zance na daban?”

Jan hannun shi Abdul yayi suka ɗan matsa gefe yace

“look guy, ka fahimce ni, ba nine wanda kuka fito daga gidan ku tare ba……… tas Abdul ya bashi labarin abinda ya faru a ɗazun”

Kafin Abdul ya rufe baki, muslim ya kwasa da wani mahaukacin gudu yayi cikin gidan su Abdul ɗin

Mutanen dake a wajen ma suka hau runtumawa a guje cikin gidan

Wasu suna zazzaune a harabar gidan suka ga maza sun antayo ciki da gudu, ba wanda ya zauna a cikin su, suma suka ari na kare sukai ciki da gudu

Wasa-wasa dai, gidan ya kacame da guje-guje, kaf a cikin su ba wanda yasan gudun me ɗan’uwan shi keyi.

Abdul na nan waje a tsaye ya saki baki da hanci yana kallon ikon Allah, Abbah da isowar shi kenan yayi parcking

Kafin ya buɗe baki yai ma Abdul magana ya jiyo hayaniya me ƙarfi daga cikin gidan nashi

Kusan a tare suka shiga gidan, 

Wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan

Kowa tambayar na kusa da shi yake “me ya faru”

Ba wani amsa, tunda ba wanda yasani ɗin.

Firfitowa mutanen da suka nemi wajen ɓuya suka fara yi, kowa na baza idanu.

Abbah da shima zuciyar shi ke tsinkewa ya kalli ɗayan abokin Abdul da shima ke ta maida numfashi ya tambaye shi

“Meke faruwa ne nura?”

Wanda aka kira da nura ya shafa ƙeyar shi yana kallon ƙasa yace

“wallahi bamu sani ba Abbah, kawai dai muna tsaye muka ji muslim ya kurma ihu, kuma ya kwaso da gudu ya shigo nan, shine muma muka shigo dan bamu san abinda ya gani ba”

Kowa tsaki ya fara ja, wasu suka hau dariyar gudun da suka kwasa ba gaira ba dalili

Suna a haka muslim ya fito daga can cikin mata, hannun shi riƙe da malum malum ɗin shi ya haɗa wata uwar zufa da tasa shi nason maiƙo

A ɗarare ya miƙa ma Abbah wayoyin Abdul, yace 

“Gashi Abbah, in na gaskiyar ya dawo ka bashi”   

Yana gaba faɗar haka ya ƙarashe ficewa a guje.

Tun daga sama har ƙasa Abbah ke kallon Abdul da ya rumtse idon shi tam

Da yawa a cikin mutanen dake wajen sun san da problem ɗin Abdul

Ɗaya bayn ɗaya aka rinƙa saɓewa, wanda ke kusa suka fara tafiya, wasu na nesan ma duk sun ɗau jakkunan su sun aza 

Shi kanshi Abbahn ranar da Aziza tazo mishi a siffar Abdul ɗin ce ta dawo mishi a rai

Ƙarfin hali yayi ya kama hannun shi ya kutsa, yayi cikin palon shi da shi.

Har Abdul ya zauna, ya tashi zumbur yana laluban key, da sauri Abbah ya riƙe shi yace

“meye haka kake yi Abdul?”

Cikin tashin hankali Abdul yace

“zata tafin min da mata Abbah, na kuma kasa gane gidan balle in kai mata agaji”

A kiɗime Abbah ya miƙe tsaye, yana lalubar inda wayar shi take

Gam ya riƙe Abdul ɗin waya na kare a kunnen shi suka sake fitowa, 

Bugu biyu Abie ya ɗaga dan shima sam hankalin shi ya kasa kwanciya tunda aka tafi da zainab yake jin faɗuwar gaba

Bayanin da Abdul yayi mishi, shima yayi mishi

Abie yace “kuje gamu nan zuwa muma”.

Abbah da kanshi ya saka shi a mota, sannan shima ya zagaya ya shiga, ya fice layin a ɗari.

***GIDAN AMARYA

Sannun ku da zuwa ƴan kawo amarya, kuyi haƙuri fa, ban fara da muku sannu da zuwa ba.

Ba wanda ya ɗaga kai a cikin su balle ya amsa,

Can suka ƙara jin muryar ta mara daɗin amo tace

“Tsitu, jariri, ku ɗakko musu kayan da muka tanada domin baƙin Aziz”

Kuka suka ƙara ɓarkewa da shi, suna ƙanƙame idanuwan su da junan su.

ƙiftawa da bisimillah seka wasu manya manyan mazubi an aje a tsakiyar palon

A tsawace tace

“ku rabu da junan ku, ku marmatso kuci abinci”

Kafin ma ta ƙarasa faɗin su rabu, suka rabu ɗin

Kusan dukan su sun fitsare zannuwan sh,

 Fauza  kam ta daɗe a sume ita da ƙanwar mama

A kan idon su murafen kwanikan suka ɗaɗɗaga, wani mahaukacin wari ya daki hancin su, nan da nan wasu suka fara kwara amai a wajen suna toshe hancin su.

Tunda IYA tai ido biyu da abinda ke cikin kwanukan ta aza hannuwa a kai ta ɓare baki, tana kuka tana faɗin

“Mun shiga uku, Yau wannan ita ake kira da danƙareriyar lukutar masifa ni jikar dije, ina mu bil’adama da iya cin farfesun tsutsotsi da kyankyasai, yau kam ranar mutuwar muce ta zo, innalillahi wa’inna ilahirraji’un!!!”

IYA na a cikin wannan sambatu suka ji kukan wata mujiya daga waje.

kamar da wasa, ɗaya bayan ɗaya suka rinƙa fita da sauri, 

A dai-dai nan Abie da yaran shi biyu suka iso, se Abbah da Abdul suma suka iso kusan a tare

Akan idon su ƙatuwar farar mujiyar ta fito tabi ta saman su da gudu

Kusan da gudu suka ƙarasa shigowa gidan,  Abdul na taɓa ƙofar ta buɗe duk suka shigo

Amal ce ta fara ganin su, ta tashi a firgice tai kan Abbah, tana kiran sunan shi

Sunan shin data kira yasa sauran da suke a mammaƙe suka buɗe idanun su suma suna tashi

IYA kam tana yin ido biyu da Abie ta sake ɓarkewa da kuka, fuskar nan tata tai jaga-jaga da hawaye ga majina

Da sauri Abie ya zo ya kamata dan ta kasa tashi, 

Da kallon mamaki duka suka fara bin manyan kwanonin dake ajiye da kallon mamaki

Abdul sarkin ƙyama, yana kallon kyankyasai da suka sha romo ya kwasa da gudu ya shiga toilet ɗin dake nan manne a jikin palon, amai sosai yake yi kamar ze amayar da ƴan hanjin shi.

Murmushi me ciwo Abie yayi, dan tsaf ya gane kwanan zancen.

Sauran matan da abun ya ritsa da su, suna ganin sararin ƙofar ko wacce ta kwasa tai waje da gudu ta saɓi hanya

duk da sunyi ƙoƙarin tsayar da su, amma ƙememe suka ƙi tsayawa, ɗaya daga cikin su tace

“Tunda Allah ya cece mu, ai ba wani amfanin tsayawa”

IYA da har yanzu ta kasa tsaida kukan ta tace

“Ku dubo Zainab jama’a, ƙila ita ta window aka fice da ita, ko kuma tana can tana kwasan romon tsutsotsi ba”

Abie da shima ke ta baza ido yaga ta ina zega ɗiyar ta shi yace

“kamar ya ta window IYA?”

Sharce hawayen ta tayi tace

“Eh mana, mu kam ni da warcan ƴar farar ta bango aka ratso da mu aka dire mu a nan wajen, tunda aka kwakuso mu ita bamu sake jin ɗuriyar ta ba”.

Yaya muhammad ya saurin faɗin, “ta bango fa kika ce IYA?”

Seda ta fyace hancin ta sannan tace

“ai mu kam munga jalala iri-iri a yau ɗin nan, tunda na fara tafiya ba’a sake ɗauka ta ba se yau da aka sa wani narkeken aljani yai sama da ni, yazo ya dankwafar dani anan”

Can sabon kuka yazo mata tace

“Badan Allah yasa na tuna addu’ar da Zainab ta koya mun ba, da tuni mun cika tumbin mu da abincin da bana jinsin mu ba”

“Kai, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un yanzu saboda rashin imani da haka nan zata danne mu ƙila taita ɗirka mana wannan kayan ƙazan tar, mutum yaƙi ci a samu wasu su shirge shi kamar yarda suka shirgi Abida”

Tunda Abdul yaji abinda IYA tace, ya haura saman ba tare da kowa ya ankare ba

Ɗayan ɗakin ya fara dubawa yaga wayam ba kowa, kai tsaye ya wuce ɗayan, yana buɗewa ya ganta kwance a ƙasa tana sharar baccin ta hankali kwance ba irin tashin hankalin da yagani a fuskokin mutanen ƙasan.

Seda ya ɗagota jikin shi ya rungume ta ƙamm, tukun yace “ALHAMDULILLAH” a bayyane yana jin wata nutsuwa da kwanciyar hankali na ratsa shi.

Rungumar da yayi mata da ɗan ƙarfi ce ya sa ta buɗe idanun ta, da sunan Iya da Amal a bakin ta 

Jinta a jikin mutum yasa ta sauri ture shi ta ja da baya tana raba idanu.

Tsayawa yayi yana kallon yarda take ta waige-waige kamar wata mara gaskiya

Kamar yasan me take neme yace 

“suna ƙasa dukan su”

Batace mishi komi ba ta miƙe tsaye tana gyara hijabin ta da ya ɗan karkace

har ta kai ƙofa taji yace

“Jirani mu tafi”

Tsayawa tayi ya ƙaraso,

Jerowa sukai a tare, kafaɗar su suna gogan juna, ƙara matsawa tayi kusa da kyau shi tana gogar kafaɗar shi

Abin yaso bashi mamaki amma dai ya basar.

Ta sama zainab ta hango Abie a tsugunne gaban fauza yana tofa mata addu’a, dan gaba ɗaya hankalin ta ya ɓace a jikin ta.

Da sauri-sauri ta fara sauka ƙasan har tana cin tuntuɓe kamar zata faɗi

Da sauri Abdul ya cimmata ya kamota yace

“Bi a hankali fa”.

“Abie, kaine?, me ya faru” tai tambayar duk a kusan tare

Da sauri Amal ta bar jikin Abbah taje ta rungume Zainab dake ta kallon mutanen palon ɗaya bayan ɗaya, tace

“Aunty zee, badai suyi miki komi ba ko?”

Da mamaki zainab ke kallon Amal, can dai tace

“su wa?”

Shiru Amal tayi tace “bakomai”

Fyace hanci IYA tayi tace

“Ba zancen bakomai, a dai gaya mata muguntar da akai mana ba wani ɗigon imani a ciki”

Da sauri zainab ta juya inda taji maganar Iya, ita sam bama ta lura da ita ba

Wajenta ta nufa, tana kallon yarda zanin Iya ya jiƙe sharkaf da fitsari

Zama tayi tana kamo hannun ta da aza bisa kan ta tace

“Iya, jiƙewa kika yi haka? garin yaya?”

Bata bata amsa ba, se cewa tayi

“Zainabu, ya naji hannuwan ki kamar itace?”

Jin Zainab ta zauna  kusa da Iya, Abie dake tsugunne gaban fauza yayi sauri ya jiyo, ba zato ba tsammani suka ga Abie ya damƙi bayan hijabin zainab da ƙarfi.

Wata razananniyar ƙara ta saki da ta firgita duk wani mahaluki dake cikin palon, 

Ba ma kamar Iya da kusan rabin zainab ɗin a jikin ta take

Akan idon su, zainab ta fara rikiɗewa tana zama firɗeɗiyar  mujiya

Tunda idanun Iya sukai tozali da abinda ta kasa gasgatawa, ko ƙwaƙƙwaran motsi bata sake yi ba ta sume a wajen.

yaya Abida kam wata jijjiga ta fara yi kamar me farfaɗiya, 

Duk da jarumtar mazan dake palon suma seda hankalin su yayi masifar tashi, 

Abbah da shima babu inda baya rawa a jikin shi yace

“Abubakar, ɗauki iyalin ka da su Amal ka maida su gida”

Abubakar ɗin ya kalli Abie dake riƙe da fiffiken mujiyar yace

“ya za’ai da IYA Abie?”

Abie da shima kanshi ya ɗau zafi, gashi da ƙarfi da yaji mujiyar nan neman gudu take daga hannun shi yace

“zasu maka yawa, kawai kaje da su, in ka dawo se mu wuce da Iya itama”

Da ƙyar aka saka su Amal, fauza da yaya abida a mota, sannan suka tafi.

Shi ba’a maganar Abdul dama, tun kafin Iya ta sume ya rigata kaiwa ƙasa, dan gaba ɗaya yafi su sanin wacece Aziza, da abinda zata iya aikatawa

Firgicin ganin matar da ya ƙwallafa rai a sonta ta zama mujiya ya kaishi ƙasa a ƙanƙanin lokaci.

Rai a ɓace Abie yace, 

“Ko ki gaya min inda kika kaita ko kuma wallahi in yanka ki a wajen nan!”

Ƙwalalo idanu kawai mujiyar keyi, amma shiru ba alamun zasu ji magana daga wajen ta.

Maganar duniyar nan Abie yayi, amma taƙi cewa uffan

A fusace Abie ya kalli yaya muhammad yace

“shiga kitchen ɗin nan ka samo min wuƙa”

Da sauri yaya muhammad ya shiga kitchen, Abie kuma ya gyara zama yana riƙe da ita gam yayi bisimillah ya fara karatun Alƙur’ani me girma.

Tunda Abie ya fara karatun nan mujiyar nan ke kuka da kururuwa,

Farko ainihin kukan mujiya ta fara, daga baya kuma ta saki sautin ainihin muryar ta 

“Wallahi bani na ɗauke ta ba, ka tsaya zan faɗa maka, ni saka ni akayi nayi suffar ta amma wallahi ba da son rai na ba”

Banza Abie yayi da shi ya ci gaba da kwararo ayoyin ubangiji da in ka riƙe su bazaka taɓa danasani ba.

Seda Abie ya tabbatar da ko a yanzu ya dakata yasan yayi mishi illa ba ƴar ƙarama ba, sannan yace

“ina kuka kaita?”

“Tana nan a ɗakin da take, waje kawai na sauya mata, in ma kace naje na ɗakko ta zan ɗakko ta”

Dai-dai nan yaya Abubakar ya dawo  daga kai su Amal gida, 

Kallon su shi da yaya muhammad Abie yayi yace

“Ku shiga saman ku duba min in da gaske tana nan”

Ilai kuwa, suna shiga suka ganta kwance a can saƙon lungun gado a takure 

Da bisimillah yaya Abubakar ya ɗagota, yana kiran sunan ta

A hankali zainab ta buɗe idanun ta da suka kaɗa sukai jajir kamar jan gauta, hannu biyu ta sa ta dafe gefen kanta data ji yana sara mata

Murya ƙasa-ƙasa tace

“yaya Abubakar, sun ɗauke Iya da Amal, sun haɗa da mutanen palon gaba ɗaya sun tafi da su”

Tausayin ta gaba ɗaya ya hanasu cewa komi, 

Ɗaga ta sukai, sannan  suka sakota a tsakiya suka sakko ƙasan.

Da mamaki Zainab ke bin su Abie da kallo, 

Mujiyar data gani a hannun shi ma yafi bata mamaki

Kafin tace komi, suka ji muryar ɗan saƙon Aziza yace

“kai mun rai ka sakeni intafi, wallahi ba abunda nai mata, garin turab kawai na shaƙa mata, shine ya sakata bacci, shima ɗan kusantar ta da nayi ba ƙaramar ƙuna na samu ba a gefen hannu na,

Dan Allah ka barni na tafi, naje naji da jinyar da na samu yanzu”.

Rai ɓace Abie yace

“Zan sakeka ka tafi, amma ko kusa da gidan nan ka sake raɓa da sunan cutarwa gare su, wallahi zan baka mamaki, marasa tsoron Allah kawai”

“wallahi ko wucewa ce ta kama ni ta nan, to zan zagaye gidan nan ko ta saman kan shi ba zan bi ba”

Abie be sake cewa komi ba, ya saki mujiyar,

Ta  kai kusan second talatin, kafin ta tashi da ƙyar ta fice ta ƙofa.

Tana fita, Abbah da Abie suka yo kan Iya dake sume, 

Ruwa akai ta shafa mata kafin ta kawo numfashi me tafe da kuka da salati.

Abdul da aka samu ya farfaɗo, shi kam da sunan zainab ya farko,  faɗi yake

“Allah kasa mafarki nake ba zainab bace ta zama mujiya”

Murmushi Abie yayi ya shafa kanshi

Yana buɗe idon shi a kan ta ya fara saukewa

Tana zaune kusa da Iya da ta rufe fuskar ta da ɗankwalin ta, ita duk a tunanin ta in ta buɗe idon, zata ga abinda ta gani ɗazu, bata san Zainab ɗin na a kusa da ita ba tunda ta farko daga suman da tai

Gyaran murya Abie yayi yace, 

“Ku zauna lafia da junan ku, sannn ku riƙe addu’a, kar kuyi wasa da ita”

Idon shi ya maida ga yaya Abubakar yace mishi

“Ka duba a mota akwai wasu ƙullin magani guda biyu ka ɗakko min”

Fita yayi ya ɗakko su ya kawo

Kai tsaye zainab ya miƙa ma maganin yace

“Ki rinƙa turara gidan, ko a cikin bunner ne”

Duk maganar da Abie yakeyi, idanun Iya a rufe ne, amma tsab tana sauraron shi.

Jin muryar Zainab a kusa da ita ta amsa da “inshaAllah Abie” yasa iya buɗe idanun ta da sauri tana kallon ta

Sake fashewa da kuka tayi tace

“Ni kam in ba kun gaji da ganin motsina a doron ƙasa ba kuzo ku raba nibda gidan nan

Wallahi zuciya ta na gab da tarwatsewa”

Kawar da kanta tayi daga saitin zainab ta maida ɗayan ɓangaren, nan ma da sauri ta kauda kanta ganin sun yi ido huɗu da Abdul.

“Shikenan gasu nan sun saka ni a tsakiya, nidai Allah ya fitar dani daga gidan nan lafia kar nima na zama mujiya”

A gurguje Abie ya ƙarasa maganar da yake yi, 

Abbah ma ya ɗora da nashi, sannan suka miƙe 

Abie da kanshi ya kama iya da taƙi yarda sam ta shiga ciki ta wanke jikin ta

Dukan su suka ɗunguma suka fito waje, 

Abbah ne ya fara shiga tashi motar yayi musu sallama ya tafi.

Sannan suma su Abie suka shishshiga mota

Tunda Iya taji ta zauna kuma a rufe motar, ta leƙo da kanta waje saitin inda zainab ke tsaye tana sharar ƙwalla tace

“Kukan ki baze ƙara tasiri a zuciya ta ba in gaya miki

 ban fitar da rai ba ma, ƙila kishiyar ki na kamo ɗazu ba ke ba,  ta wani langaɓe dan ta kawo ni inda zata birkita mani ƙwaƙwalwa da mugun tar ta

Humm, yanzun ma bani da tabbasa, dan al’amarin ku bagane mishi ake ba,

a yanzu a ganku a mutane, anjima kaɗan ku rikiɗe ku zama wasu halittun,

Na barku da dangin ku na ɗayan jinsin”

Yaya muhammad da ranshi ke ɓace yace

“Haba Iya, in baki kwantar mata da hankali ba ai ba kya ƙara tasar mata da shi ba dan Allah”

Taɓe baki Iya tayi tace

“yanzun ne nake da ƴancin magana, inda kaga lukutar masifar da muka shiga a ɗazu da baza ka ma fara wannan maganar ba, kuma baka isa ka hana ni faɗin abunda ke cikin raina ba ehe”

Shiru yaya muhammad yayi ganin kallon da Abie ke mishi.

Juyawa Abie yayi ya kalli Iya cikin girmamawa yace, “zamu iya tafia kin gama?”

Ƙara taɓe baki tayi tace “saura kalma ɗaya zuwa biyu”

Kanta ta ƙara leƙawa waje, bata yarda ta kalli Abdul dake tsaye kusa da zainab ɗin ba,  

idonta akan zainab ɗin ya tsaye tace

“Ko na yanke zumunci dake zainabu ai Allah baze kamani ba ko?”

Banza zainab tayi da ita, bata ce komi ba

Taɓe baki Iya ta sake yi tace

“kada Allah yasa ki kula ni,

Se mun haɗu a aljanna in mun mutu, amma ni da anguwar nan bama gidan ki ba, har abada”

Maida kanta cikin motar tayi tace “muje na gama”.

Ba wanda yace mata komi, yaya Abubakar yaja motar suka tafi.

Fashewa da kuka zainab tayi, tana jin wani baƙin ciki na tokare mata maƙogoro.

Shi kanshi tausayin ta ya kama shi, ji yake ina ma shine ze iya kukan nan da take yi da ya ji daɗi.

A hankali ya matsa kusa da ita, ya haɗe ta da jikin shi yana shafa bayan ta alamar rarrashi

Ganin suna ta tsayuwa a waje, ga kuma dare sosai ya fara yi yasa ya kamota  suka shiga gidan

Sakin ta yayi, ya juya ya rufe ƙofar sannan yace

“muje”

Kallon shi tayi ta galla mishi harara, duk da kukan da take, ta buɗe baki ta ce

“Lallai ma, a haka kake so mu shiga ciki?” ai baka rufe gidan ba, salon azo a maida mu agwagi”

Ta ƙarashe maganar tana kafe shi da idanuwan ta.

Kallon ƙofar yayi, sannan ya sake kallon ta da mamaki a fuskar shi

Can dai yace

“Na rufe fa, zo ki duba ki gani”

“Bafa ka rufe ba malam”

Da zuciya ɗaya yace 

“zo ki rufe to, ƙila idon nawa ya fara taɓuwa ne shima”

Sakato tayi tana kallon shi, wani tausayin shi na rufe ta

Matsawa tayi jikin ƙofar, sannan ta buɗe baki dai-dai yarda ze iya jinta, ta fara karanta

BISMILLAHILLAZI LAA YA DURRU MA’AISMIHI SHAI’UN FIL ARDI WALA FISSAMA’I WA HUWAL SAMI’UL ALIM”

Sannan ta karanta ayatulkursiyu da amanarrasulu har ƙarshe, ta tofa a ƙofar

Yana tsaye yana kallon ta, Ammah ce kawai ta faɗo mishi a rai

Kallon shi ta yi tace

“na rufe muje”.

Suna shiga ƙofar palon taga ya rufota, sannan ya tsaya, murya ƙasa-ƙasa taji muryar shi me daɗi yana karanto abin da yaji ta karanta a warcen ƙofar.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke.

Kallon yarda palon yai kaca-kaca tai tace

“anzo wajen fa”.

Ƙarasowa yayi shima yana kallon yarda wajen ya yi kaca-kaca,

 tashi zuciyar shi ta hau yi, amma haka nan ya daure yace

“Ki je ki zauna, zan gyara wajen”

Kallon shi tai da kumburarrun idanun ta tace

“kaine zaka zauna dai, kaje ka huta zan gyara”

Gaddamar suka hau yi, wannan yace shi zeyi, itama tace ita zatayi.

Kowa yaƙi yarda ɗan’uwan shi yayi, daga ƙarshe ganin suna ɓata lokaci, Abdul yace

“Naji to, zo mu gyara a tare”

Ba dai wata hira a tsakani, haka suka gyara wajen tsab suka goge

A daren zainab ta jona bunner ta tirniƙe gidan da garin maganin da Abie ya bata ɗazu.

Tunda Zainab ta gama abunda ya kamata, ta haura sama ɗakin da aka fara kaita.

Seda ta saki labule windos ta saka key a ƙofar sannn ta cire hijabin jikin ta

Gaba ɗaya jin jikin ta take wani iri, ga gajiyar taro ga kuma gajiyar gyaran gidan da suka yi.

Wanka kawai take da buƙata a wannan lokacin.

Yana kallonta ta haura sama, bata ce mishi uffan ba shima bece mata ba

Seda ta ƙule ma ganin shi tukun yace a hankali

“Anan zata barni to?”

daga ƙasan zuciyar shi yaji tace

“Haba dai, kaine mijin fa”

Murmushi ne ya suɓuce mishi yana shafe ƙeyar shi

Har ya miƙe tsaye da niyar bin bayan ta, ya koma ya zauna

A hankali yace

“Tabɗijan, ai ba haka ake shiga ɗakin amarya hannu na gugan cinya ba, ni sam ba da shiri na tawo ba wallahi”

Shi kaɗai yake kiɗan shi yayi rawar shi.

Wasa-wasa tun Abdul na cewa bari dai ya tashi, bari dai ya tashi, har bacci ɓarawo yazo yayi awon gaba da shi.

Zainab kam tunda ta samu ta watsa ruwa masu ɗumi, tai shafa’i da wutiri a daddafe, 

 sannan tabi lafiyar gado bayan tayi addu’o’in da annabi ya koyar da mu.

MAFARKI

zuro hannuwa  ta ko’ina suke, amma sun kasa ɗaukan shi

Ɗakine gajera mara yalwa ga duhu a cikin sa, 

ƙofofi ne birjit a ɗakin, yana zaune a tsakiyar ɗakin jikin shi nata kyarma, tsorata shi ake ta ko wani kusurwa

Ga zaƙo-zaƙon hannayen su da suke sakowa, kallon su kaɗai abin firgici ne gare shi

Da ya yunƙura ze guda ta ƙofar da yaga basu a wajen, kafin ya ƙarasa ƙofar sun ƙara yayyaɓe wajen suna so su damƙe shi

Ɗayar ƙaramar ƙofar dake ta gefen shi na dama ya waiga yaga ko ze iya fita, 

abinda ya ƙara firgita shi shine ganin hannayen su suna ƙwaƙular ginin da in suka fasa shi to tabbas kashin shi ya bushe.

Da ƙarfi yace “ki rabu dani! na gaji!”

A daidai lokacin da Abdul ke wannan mafarkin, a daidai lokacin kuma ƙishi ya addabi zainab data farka ta kasa komawa sobada ƙishin.

sakkowa tayi daga kan gadon, ta ɗauki hijabi ta saka, a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito

Kallon ɗayar ƙofar dake kallon ɗakin ta tayi ta galla mata harara, duk a tunanin ta Abdul na cikin ɗakin

Kanta a ƙasa ta sakko ƙasan tana shaƙar ƙauri-ƙaurin turaren maganin da ta saka da haryanzu akwai saura be tafi ba

Wutar ko’ina a kunne ba’a kashe ba, kanta tsaye ta wuce kitchen ɗin 

Roba biyu na ruwa ta ɗakko, ɗaya na riƙe a hannunn ta, ɗayar kuma ta buɗe tana sha

Tana tafe tana sha har ta fito palon

Wurwurga idanu ta fara yi taga ta’ina zata ga inda makunnin wutar ya ke ta kashe, 

Hango shi tayi kwance akan kunjera ya haɗa zufa sharkaf yana wani mutsu-mutsu kamar ze faɗo daga kan kujerar

Da mamaki zainab ta ƙarasa shiga palon tana kallon yarda ya haɗa zufa sharkaf ya jiƙe

A ranta tace “mafarki yake”

A kan shi ta tsaya tana ƙare mishi kallo tundaga sama har ƙasa

Murmushi tayi, a bayyane tace

“kyakkyawa ne fa, amma sauran aljana”🙄

Ta ƙarashe maganar tana murguɗa baki.

 Abdul na faɗin “ki rabu dani” a cikin mafarkin

Dai-dai sun gama ƙwaƙulan bango sun shigo inda yake, amma sun kasa ƙarasowa saboda wani haske me kashe idanu da ya zagaye shi,

Shi kanshi hasken kashe mishi ido yake

A fili kuma gani kawai zainab tayi ya ɗaga hannayen shi yana ƙare fuskar shi, at the same time kuma yana faɗin “karki matso kusa dani”

Da sauri zainab ta saka hannu ta ɗaka mishi duka a cinya tace

“Tashi!”

Firgigit, Abdul ya buɗe idon shi ya tashi zaune da sauri yana shafa wajen da ta ɗala mishi duka

Ɗayan hannun shi  ya sa ya shafo fuskar shi da yake jin kamar an mishi sharkaf da ruwa

Kafe shi da kallo zainab tayi, murya a sanyaye kamar ba ita bace ta ɗala mishi duka yanzu ba, tace

“Bakayi addu’a ba ko?”  

Bece mata komi ba, kuma be ɗauke idon shi a kan ta ba, itama bata ɗauke nata idon ba

Sun kai kusan minti ɗaya suna kallon juna

Gira ɗaya ta ɗaga mishi tana kauda idon ta, sannan ta samu waje daga gefen shi ta zauna.

“Inda kayi addu’a bazata taɓa zuwar maka ba zawj”

Yarrr haka Abdul yaji tsiga jikin shi ta tashi jin salon yarda ta kira shi da “zawj”

Ya mai-maita suna “Zawj” a cikin ranshi yafi a ƙirga

Zunguro shi ta sake yi da ƙafa, kallon ta yayi shima ya ɗaga mata gira ɗaya kamar yarda ta yi mishi ɗazu

A tare suka kwashe da dariya, kamar sabbin kamu

Kafe ta da ido yayi yana jin ta a duk wasu ƙofofin jikin shi da zuciyar shi

A ranshi yace 

“Zuciyar ta tsarkakkace, Alhamdulillahi ya rabbi”

Seda tayi dariyar me isar ta tukun ta tsaya, 

Miƙewa tsaye tayi tace

“Ni na tafi, ka rinƙa kashe haske in zaka kwanta dai”

Jin tace zata tafi yasa gaba ɗaya mood ɗin shi ya sauya, fuskar shi ta koma kalar tausayi

Juyawa ta yi zata tafi, da saurin shi ya riƙo hijabin ta, ƙiris ya hana ta kai ƙasa

Waigowa da sauri tayi, tana waigowa ya saki hijabin ya fara kame-kame, ya rasa me zece mata

Shi kanshi be san yarda akai ya riƙo hijabin nata ba.

“Da matsala ne?”

Ji yayi bakin shi ya furta “wallahi tsoro nake ji”

Me zainab zatayi in ba dariya ba, 

A nan kan matakalar benen ta zauna tai ta kwasar dariya, shi kuma ya tsaya yana kallon ta kamar sakarai.

*A wannan daren su Abbah na can na fama da fauza, gaba ɗaya an kasa gane kanta,

Da bacci ya ɗan fizgeta zata farka da ihu da buge-buge, abu kamar wasa komi ya rikice akan ta suka kwana a wannan daren.

Ta ɓangaren Iya kuwa, tunda ta samu suka isa gida, ta shige toilet,

Gaba ɗaya kayan jikin ta tacire ta haɗa ruwa tai wanka

Tana wanka tana ƙorafin abubuwa, Allah ya isa kam tayi ta tafi cikin toilet ɗin nan

Seda ta gama wankan tsaf ta naɗo kayan da ta cire taji suna bugawa,

Ajesu tai ta warware, ilai kuwa abinda take tunani ne, guntun zawo ne faca-faca a jikin zanin

Tana gani ta rafka salati, sam ta mance a cikin banɗaki take, Tana ɗauraye wa tana ƙorafi

“Banda ma Allah yasa kwanan mu na a gaba, banjin zan kawo wannan lokacin ba, Allah nagode maka da yasa a iyakacin zawo na tsaya”

Haka tai ta ƙorafin ta har ta gama ɗauraye kayan sannan ta fito ta baza su a kan igiya tai cikin ɗakin mama da ƴan’uwan ta ke ta jajan ta abinda ya faru.

Mama na ganin IYa ta taso, fuskar ta da ka gani a cikin damuwa take,

Tace “Nasa an gyara miki can ɗakin ai”

Ido waje Iya ke kallon mama, tace “badai ɗakin zainabu zan kwana ba?”

Mama tace “can mana Iya, ai naga a can kika sauka kuma kayan ki duk suna a can”

Taɓe baki Iya tayi tace

“Ko a daren nan na mutu, ban yarda akai gawata can ba wallahi, maza kisa a ɗakko min kaya na, ai ba ace dole se na zauna anan gidan ba, daɗin abun ina da nawa gidan”

Murmushi mama tayi tace “abun be kai nan ba Iya, zo muje, in buɗe miki wancan ɗakin, shi dai babu bayan gida a cikin sa”

“Yo ai gara shi ɗin da ɗakin zainabu”.

Tas aka kwashe kayan Iya aka maida wancan ɗakin, sannan ta Iya shiga ta kwanta.

Data rufe ido zainab take kallo a suffar mujiya, 

Da sauri ta buɗe ido a karo na kusan biyar kenan ta tashi zaune ta zabga uban tagumi

Bugun duniya tayi-tayi ta tuna addu’ar da zainab ta koya mata, amma inaa, ta ɓace mata (HAKA ABUN YAKE, IN BAKA SAMU DAMAR YIN KARATU TUN DA ƘURUCIYA BA, KA BARI SE GIRMA YA KAMA KA, YA KAN ZAMAR WA MUTUM WAHALA MATUƘA WAJEN RIƘEWA, ALLAH YASA MU DACE.)

*** Dare ya raba sosai, baka jin motsin kowa, mama data kasa bacci, tunanin autar ta sam ya hana ta sukuni tun da taji abinda ya faru, kuma aka baro ɓata ƴa a can ta rasa sukunin ta.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin Abie ta shiga, ilai, yarda ta kasa bacci haka shima yake zaune ido biyu, kallo ɗaya zakai mishi ka ga damuwar dake kwance a ran shi.

Ɗaga ido yayi ya kalli mama da taƙi ƙarasowa ciki ta tsaya a bakin ƙofa

A hankali yace “shigo mana, me ya hana ki bacci?”

Kamar jira take, ta fara share hawaye, nan da nan jikin Abie ya ƙara yin sanyi, da kan shi ya tashi ya kamo mama ya zaunar da ita a gefen shi

Kanta da aza a kafaɗar shi, bata ce komi ba, amma shi kan shi yasan damuwar matar shi

Cikin hikima da fikira ya dunga nusar da ita abubuwa da dama, har ya samu ya shawo kanta, suka raya wannan dare da nafiloli da kuma neman kariya da tsarin ubangiji ga ɗiyar tasu da kuma abokin rayuwar ta.

*** Kayi addu’a ka kwanta, inshaAllah ba wani abu da ze sake faruwa.

luf Abdul yayi bisa gadon zainab, tun yana satar kallon ta har wani bacci me cike da nutsuwa da daɗi yayi awon gaba da shi, 

Bacci yake irin wanda ya jima be yi shi a rayuwar shi ba.

WASHE GARI

Kayan gara da aka haɗa za’a kai gidan amarya, ƙiri-ƙiri kowa ya saɓar yayi gaba abinshi

Abun ba ƙaramin ƙona wa mama rai yayi ba, ta tashi taje ta samu Iya da maganar

Shiru Iya tayi har seda mama ta kai aya tukun tace

“Humm, Binta kenan, kin san kuwa irin danƙareriyar lukutar masifar da muka shiga kuwa jiya?”

IYA ta kafe ta da idanu  tana jiran taji me maman zata ce

Kan mama a ƙasa tace “ai naga ranar naka se naka IYA, kuma mutum in ya riƙe Allah baze ji shakkar komi a ran shi ba”

Taɓe baki Iya tai sannan tace “Hakane Binta, ki saka hijabi ku tafi ke da Hamza ku kai, ai naga ba haramun bane”

Shiru mama tayi, bata sake cewa komi ba ta tashi ta fita daga ɗakin idon ta fal da ƙwalla.

Abie da kan shi ya lallashe ta yace ” anjima zan saka Abubakar ya kai komi, ba komai ai, munyi komi saboda Allah ne, kuma ladan mu yana gare shi”.

Mama tace “Ban tari numfashin ka ba malam, ana kai amare gidan sirikai fa, sannan a tafar musu da ƙore”

Shafa kanta Abie yayi yace

“wannan duk ba addini bane, al’adace, in komi ya lafa ayi daga baya”.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU

TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!”

INA MATA ƳAN ƘWALISA?

A.A.G COMPLEX YA ZO MUKU DA NAGARTATTUN KAYA, WRAPPERS, LACES, SHADDA, SHOES, BAGS, KAYAN KITCHEN, ROBOBI PLASTIC AND MORE.

A FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA, MUNA MARABA DA KOWA DA KOWA

DOMIN ƘARIN BAYANI, ZAKU IYA TUNTUƁAR MU TA WANNAN NUMBER

07035046805.

Back to top button