Health

Amfanin Zogale Guda Sha Takwas (18) A Jikin Dan Adam

AMFANIN ZOGALE GOMA SHA
TAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM
==========================


Ana Bukatar Jama’a su yada wannan Post zuwag Sauran Al’umma domin Qaruwa da Juna.

1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a
sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).

2- Ana shafa danyen ganyen zogale
akan goshi domin maganin ciwon kai.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko
wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale in sha Allah jinin zai tsaya.

4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya
hada garin zogale da man zaitun ya shafa.

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Kanki Kafin Aure Da Bayan Aure

5- Ana sanya garin zogale akan wani
rauni ko gembo domin saurin warkewa.

6- Sanya garin zogale a cikin abinci
yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa
kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon
shawara.

8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga
ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.

10- Wanda ke fama da yawan fitsari
wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

11- Idan aka tafasa furen zogale da
albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.

12- Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.

Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure

13- Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.

14- Ga mai fama da sanyin kashi ko
wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su  sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

15-A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.

16- A daka saiwar zogale da ‘ya’yan
kankana a  sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

17- Haka kuma idan mutum yana
fama da ciwon Aids zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.

18- Haka kuma mai fama da Typhoid da
malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.

Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata

Back to top button