Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 46 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                             FORTY-SIX📍

      Mami da fitowarta kenan jin sabon hayaniya taga mata ta sume, ruwa ta kawo da sauri aka zubama ammy, bude ido ammy tayi ta mike tsaye still idonta akan fatima zainab tace;

     “ku fadamin WACECE ITA?”

Wani irin kallo fatima zainab ta mata tace;

     “ina ruwanki da wacece ni?”

 Ihu ammy ta saki tace;

       “wayyo Allah shikenan tayi magana wallahi itace!”…..

Sai kuma ta sake nuna fatima zainab kamar zararriya tace;

      “kunganta ko wallahi baby tee dinku ce! Itace! Itace!”

Mami ce tace:

    “bamu gane baby tee dinmu bace? Wannan ai basa kama kwata kwata da umm,baby tee da take carbon copy na umm, hala idonki na miki ciwo ne?”….

Dariya ta fashe dashi ta kalli fatima zainab tace;

    “kina shayeshaye ko? Maza nawa kika bawa kanki? Nasan yanzu kinyi degree a karuwanci ko? Koba fatima zainab bace?! Hahaha ko yanzu na mutu nasan na gama da rayuwarki data uwarki da danginku! Ke har ubanki saidai yayi hakuri duk da ina sansa, ko a yanzu nasan naci galaba akanku hahaha”….

Ai gabadaya sai kowa yayi shock even though basu yarda da abinda take fada ba amma maganganunta sun daga musu hankali musamman data ambaci sunanta……..

Deen ne ya daka mata tsawa cikin dakakkiyar murya yace;

    “dalla mallama ki mana bayanin haukar da kike fada ba wai ki samu a gaba kina mana dariya kamar wasu gayyar yan iska ba!!”

Dariyar data fi ta dazun ta sakeyi tace;

    “kwantar da hankalinka yaro, dole zan fada muku komai tinda kwalliya ta biya kudin sabulu hahaha”……

     Anan asalin labarin WACECE ITA ya fara…..

     Alhaji suleim haroun shuwa shine cikekken sunan bappa sai matarsa zulaiha abdoul shuwa da suke kira anna , sosai suke ji da kyau a familyn kasancewarsu shuwa arab din maiduguri, hakan yasa ko auren bare basayi dole ku sasanta kanku a cikin family dan gani suke kamar in suka auri wani familyn zaa haifo mummuna, su kuma gashi sun bawa kyau mahimmanci sosai har gani suke kamar sunfi kowani kabila kyau a duniya, gasu kuma yan boko sosai ga arziki tin na iyaye  da kakanni shiyasa basu so wani ya rabe su da sunan aure inba a dangi ba, har ta kai ta kawo idan akaga kunki sasanta kanku sai kawai ayi meeting a sanar da auren wane da wace nan da lokaci kaza, shiyasa kowa ke kokarin sansanta kansa da wani gudun kar kaji announcement daga sama, duk da yanda suke auren hadi a hakan kuma basu yarda da kara aure ba koda zaku shekara nawa baku haihu ba, gashi baa saki haka zaayi ta sasantawa ace suyi hakuri, ada bappa yana ganin baiken wannan tsattsauran tsari na gidansu har yayi planning breaking rules din ya auro wata kabilar, saidai kash yana dawowa daga wani course a Europe idonsa ya sauka akan zulaiha wacce ta kasance yar kanin mahaifinsa, yaji inaa ga abu nan a gida ina shi ina tsallakawa wani wajan ai gwara kawai yabi yarima asha kida shima yayi auren dangi, ba bata lokaci ya sameta da maganar dan still be yarda da auren hadi ba ya fiso ya nemi soyayyarta suyi auren soyayya, ba bata lokaci ta amince dan itama tana crushing akansa, nan suka dasa ingantacciyar soyayya me tsafta data kaisu ga aure……

Shekararsu daya da aure akayima bappa transfer zuwa garin abuja, haka suka tattara suka koma shida yar matarsa anna, shekararsu biyu da komawa abuja Allah ya azirtasu da samun haihuwar ya mace, ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar anna wato fatima zahrah(mami), sosai haihuwar tazo musu da budi kala kala acikin haka harda appointment na vc din university of abuja aka bawa bappa, a shekarar da bappa ya gama tenure dinsa na vc wato after four years Allah ya sake azurtasu da samun haihuwar jamila(umm), a kuma lokacin aka bawa bappa ambassador na Nigeria…..

Haka umm da mami suka taso cikin gata da kulawar iyayensu, gasu kyawawa san kowa kin wanda ya rasa saboda sun gado kyau ta ko ina dan iyayensu na kama ma, sam basu san wani abu wai shi talauci ba gasu kuma da tarbiyya me kyau da suka samu a gurin iyayensu…..

Kamar yanda shekara hudu ke tsakanin mami da umm haka bayan shekara hudu anna ta sake haihuwa, abun farin ciki kuma Allah sai ya azurtasu da samun da’ namiji, ba karamin murna mami da umm sukayi ba na samun kani, haka yan maiduguri suka zo aka sha suna kamar yanda suka saba duk sanda wani abun ya taso, suma su bappa haka suke zuwa maiduguri duk sanda wani abu ya taso….

Haka bappa ya dinga samun karin matsayi hakan yasa dole ya maida abuja permanent residence dinsa…….

Haduwar umm da muhammad(abby) ya faru ne tin tana jss1 shi kuma ya gama ss3 at that time, lokacin anyi wani gagarumin conference na manyan mutanen kasar, mahaifin abby daya kasance delegate a lokacin ya halarci taron da babban dansa wato abby, tashin farko jininsu ya hadu da umm kasancewarsu duka marasa hayaniya gasu kuma very jovial, hira sukayi tayi kamar sun dade da sanin juna…..

Ana tashi daga taro Abby ya rike wuta sai sun bisu gidansu, ba musu mahaifinsa ya yarda dan yanaji dashi sosai a matsayinsa na dansa na fari…. Daga wannan rana Abby ya maida gidansu umm gidan zuwa sannan alakarsu ta kara karfi sosai shida umm a matsayinsu na yaya da kanwa, tin baayi nisa ba Abby ya gane san umm yake dukda karancin shekarunta amma sai ya basar, boddi da yake ce mata ya samo asali ne tun ranar da suka fara haduwa, ta tambayesa menene ma’anar sunan yace mata kyakkyawa kenan da yaransa wato fulani, daga ranar kuma ko fada suke baze fasa kiran wannan sunan ba dan ya riga yabi bakinsa……..

    Lokacin da Abby ya samu admission a oxford university England ba karamin daru akasha dashi ba kafin ya amince yaje dan rike wuta yayi shi a Nigeria yakeso yayi karatunsa bayan da kansa ya zabi school din, babu wanda yasan dalili kuma baa tambayesa ba saima lallabasa da akayi, haka yanaji yana gani ya tafi ya bar umm bayan duk abinda yakeyi saboda itane, gani yake kamar ze rasata idan ya tafi kuma fa  a jss1 take har lokacin…..

Mami ce ta zama barrier of communication dinsu bayan ya tafi dan umm batada waya lokacin saidai tab, dokar bappa ce sai ka kai jss3 sannan zaka fara rike waya regardless ko mace ko namiji…….. 

Shekarar Abby hudu a England, a shekara hudun nan kuma ze iya kirga so nawa yayi fashin waya da umm dan kullum suna makale da juna a waya dukda mami kadai ce ta sani, sosai soyayya me karfi ya shiga tsakanin umm da Abby tin umm batasan menene so ba, akanshi ta fara sanin menene soyayya tun bata gane ba harta gane……

   Saida ya gama degree dinsa ya dawo lokacin zata shiga ss2, ba karamin farin cikin ganin juna sukayi ba sanda yazo gidan kadama Abby yaji labari dan sai yaga gabadaya an chanzata kamar ba boddinsa ba ta girma ta zama budurwar abinta, itama haka take a gareta sai taga ya kara zama handsome sosai fiyeda kyakkyawan bafulatanin data fara gani a conference din da akayi, rudewa yayi yaje ya gayama mahaifinsa shi fa ya gani yanaso kuma yanzu yake so a daura musu aure ya tafi da ita inyaso saita cigaba da karatun achan while yana masters dinsa, ba bata lokaci mahaifinsa ya amince ya kuma ce masa zeje har embassy na mahaifinta suyi maganar dan sun kai a hada iri dasu dan babu wanda be musu shedan tarbiyya ba dukda kudin mahaifinsu…..

Kamar yanda ya masa alkawari washe gari yaje, babu wani appointment aka masa iso da bappa kasancewarsa babban mutum shima kuma good friend din bappa, kai tsaye ya gayawa bappa abinda ke tafe dashi, sosai bappa ya nuna jindadinsa akan hakan sannan shima ya yaba da tarbiyyan yaron dan har hira yake zuwa suyi in yazo gidan amma shi baze iya aurar da yarsa bata gama degree ba balle wannan da ko secondary school bata gama ba, amma tinda yaga sun matsu idan kuma ze iya jira zeyi magana da mahaifiyar yarinyar da kuma ita yarinyar yaji, indai tanaso ta babu shakka ze basu dama su turo asan da maganar a kasa shi kuma ya musu alkawarin baze bari yarinyar ta kula kowa ba, godiya mahaifin abby ya masa sosai sannan sukayi sallama cikin mutunci ya kuma ce masa ze kirasa a waya yau duk yanda sukayi da dan nasa….

Yana zuwa gida ya sanar da Abby yanda sukayi da mahaifinta, daga masa hankali Abby yayi wai lokacin yayi yawa, ya zaayi ace har sai ta gama degree dan Allah ya taimakeshi ya gayawa mahaifinta shi zeyi supporting dinta in every way tayi achieving duk abinda takeso tayi achieving a gidansa, kin yarda yayi saboda basa haka da bappa sannan kuma bappa man of his word ne, da wuya kaga ya fadi abu ya chanja, ganin haka  yasa yaga kar yayi saki na dafe ya cewa mahaifinsa ya amince akai komai inyaso sai ya tafi yayi masters dinsa ya dawo…..

  Shima bappa yana zuwa gida ya gayawa anna abinda ake ciki, nuna masa tayi tana jin tsoron abunda ze biyo baya tinda familyn su basu yarda da auren bare ba, kai tsaye ya nuna mata ba ruwansa da wannan shirmen as long as ya’yansa suna so, da kansa ya kira umm ya tambayeta, bata bashi amsa ba amma yanda takeyi ya gane itama tanaso, to be sure ya kira mami ya tambayeta alakar dake tsakanin umm da abby ya kuma fada mata yanda sukayi da mahaifin abby, ba bata lokaci mami ta fadamasa eh suna san junansu, mamaki ne ya kama bappa ace Umm tana soyayya tin yanzu be sani ba amma sai yayi la’akari da tarbiyyar abby sai yaji hankalinsa be wani tashi akan hakan ba, nan ya basu dama aka turo…..

Haka kuwa akayi suka kai kudi me mugun yawa har saida bappa yace a rage dan albarkar abun akeso ba bidi’a ba, sun so ma sukai harda sadaki nan ma bappa yace inaa ba yanzu ba, saida aka gama komai sannan Abby ya koma England yin masters cike da kewar umm….

   Kiri kiri umm ta koma art student tin a ss2 ita da take da burin yin medicine, bappa bece komai ba dan yace kowa yayi abinda yakeso tinda ba wani ne ze masa karatun ba, nan ko lissafi tayi taga bazata iya kara shekaru me yawa basuyi aure ba itada Abby shiyasa kawai ta zabi 4 years course, data tashi kuma ta dau law…… 

   Ko bayan Abby ya gama masters be dawo ba dan lokacin umm tashiga level 2, yasan kuma in yazo ya ganta hankalinsa kara tashi zeyi gashi mahaifinta yace dole saita gama degree, yace ko wacce da kwalinta ze kaita yanda babu me rena masa ya’ya, lokacin shekarar mami daya da aure ita da dad, sai kawai ya fara PhD dinsa…….

    Akace ko min nisan dare dole ne gari ya waye, sai aka wayi gari su umm na call to bar, a kuma ranar Abby ya dawo Nigeria, lokacin bikinsu saura sati daya, haka yan uwa da abokan arziki sukazo taya umm murna, har yan maiduguri baa barsu a baya ba dan gabadaya sukazo da shirin biki…….

Shagulgula iri iri akasha lokacin bikinsu meanwhile amarya da ango naji kamar su chinye juna saboda so…… 

Ana daura aure suka bar kasar as planned dan Abby yace bazasu zauna a Nigeria ba tinda karatu yake itama kuma zata cigaba in suka tafi……..

    Babu irin soyayyar da Abby be nunawa Umm ba har takejin kamar bazata iya rayuwa babu shi ba, watansu shida da aure lokacin anyi honeymoon har an kaji ya zaunar da ita suyi magana akan plan dinta base on career wise dan yasan mahaifinta ido kawai ya zuba musu yaga gudun ruwansu dan sunyi da wajewa zata cigaba da karatu, ce mishi tayi kawai zatayi masters ko kuma tayi wani course din based on law, Abby ne ya bata shawara akan why not tayi medicine dinta tinda dama chan shi takeso, aurensu ne yasata chanja course sai tayi using law dinta as supplement that’s idan tanaso tayi aiki dashi ma, sosai taji dadin shawarar amma tayi mamakin yanda yasan saboda shi takiyin medicine, dariya yayi yace in banda abinki boddi na da bakinki kika fadamin fa, dagewa tayi saidai in wani ne ya fadamasa amma wallahi ita bata fada ba, murmushi yayi sosai ya gaya mata gaskiya, mami ce ta fadamasa kasancewarta straight forward mutum kamar bappa, ta kuma masa kashedi akan ya bar kamwarta tayi medicine dinta in sunyi aure tinda ya hure mata kunne ta fada abinda tayi niya……

Dariya sosai Umm tayi tace Allah sarki dan uwa me dadi…….

Haka Abby ya shiga ya fita har saida umm ta samu admission na medicine a oxford, babu dadewa ta fara karatu cikin kulawa da kyautatawar mijinta……..

    Shekararsu biyar da aure ta gama medicine dinta kuma har lokacin Allah be basu haihuwa, amma saboda soyayyar dake tsakaninsu ko maganar basayi dukda yanda kowannensu keso, abu daya kawai sukayi lokacin shekararsu uku da aure Umm ta dage sai sunje asibiti an duba lafiyarsu, they are both fertile haka aka sanar musu a asibiti kawai haihuwar ce Allah be kawo ba, jin haka yasa abby ya watsar da zancen ko umm ta dauko masa sai yace bayaso, har dan misunderstanding suka samu wani lokacin yace in ta dena sonsa ne ta gayamasa akan kullum tana nuna masa haihuwa takeso kamar sune zasu bawa kansu haihuwar, sosai tashiga taitayinta ganin yanda ya hau sama abinda ko murya be taba daga mata ba tinda sukayi aure, sai itama ta tattara zancen ta watsar dukda abin yana makale aranta……

Haka abby ya cigaba da zama the most supportive husband ever, komai tazo dashi ko bayaso baya nuna mata, kullum kuma jinta yake kamar sabuwa……

    Shekararsu bakwai da aure mahaifiyar Abby ta bullo da wani abu, wai sai Abby ya kara aure saboda basu haihuwa ba har shekara bakwai ita kuma gaskiya tana san jika, karya Abby ya mata akan shine baya haihuwa fisabilillahi kawai umm ke zaune dashi, jikinta ne yayi sanyi jin wannan dake nata ne akace ba lafiya amma dake yar wata ce tace a karo mata kishiya(Allah ya kyauta)…….

    A ranar da sukayi gagarumin celebration na ten years da aure suka gano umm na dauke da ciki, sai celebration ya zama biyu abinda har sun fidda rai…. Ba karamin farin ciki sukayi ba kamar cewa akayi ta haihu, amma basu fadawa kowa ba suka rike abun iya su biyu….

Sai da umm tashiga second trimester sannan suka fadawa iyayensu, sabon kura mahaifiyar Abby ta sake tadawa wai sunce Abby baya haihuwa toh yanzu waya mata ciki, ganin ana nema a chanja zance yasa Abby ya gaya mata gaskiya dama baace baya haihuwa ba kawai bayason kara auren ne, bacin rai ta nuna sosai wai Abby ya rena mata hankali saboda matarsa ta mallakesa kuma taji labarin cewa familyn su umm basu da saurin haihuwa, amma da yake asararre ne ya makale mata a haka harda mata karya wai baya haihuwa, toh wallahi saiya kara aure, hakuri ya hau bata dan gaskiya baze iya kara aure ba saboda yasan bazeyi adalci ba dan baze iya hada soyayyar umm data wata ba, da kuma mala’iku suna tsine masa akan rashin adalci gwara beyi ba kawai, ita kuma tace batasan wannan zancen ba dole sai ya kara aure, sai kawai abby ya dena daukan wayarta ya cigaba da bawa matarsa da cikinta ya shiga wata shida kulawa me kyau…..

Ganin haka yasa mahaifiyar Abby kiran mami taci mata mutunci wai dama buzaye an sansu da asiri, toh wallahi ta sakar mata yaro gashi yanzu ko maganarta bayaji komai yace matarsa matarsa kamar akansa aka fara aure, tasan kuma in banda aikin asiri babu yanda zaayi namiji ya zauna dakai shekara goma baka haihu ba sannan dole Abby ya kara aure ko tanaso ko bataso…..

Umm batace mata komai ba harta kashe wayar, daidai nan Abby ya shigo ashe duk yaji komai, hakuri ya shiga bata yace karta damu kanta dan babu wanda ya isa yasasa kara aure, kar kuma tasa tinanin komai aranta yayi affecting condition dinta, daurewa tayi ta nuna masa gwara ya kara auren tinda mahaifiyarsa naso, yanzu idan be kara ba zaana ganin kamar ita ta hanashi, ce mata yayi kawai su bar maganar bayaso……..

    Lokacin da cikin umm yakai wata takwas wata rana Abby na zaune a office kaninsa ya kirasa a waya wai an daura masa aure da wata cousin dinsa, sosai hankalinsa ya tashi ya kira mahaifinsa direct dan be yarda da wannan mummunan labarin ba, tabbatar masa mahaifinsa yayi ya kuma gaya masa shi wallahi babu hannunsa a ciki mahaifiyarsa ce tayi komai itada kaninta, labari kawai aka basa a yanzu haka ma case din sukeyi da ita…….. 

Zubewa a kasa Abby yayi cikin tashin hankali, taimakonsa daya baa gida wannan abu ya samesa ba yasan da umm taji komai itada yake lallabawa saboda cikin jikinta daya tsufa, yafi hour biyu a haka kafin ya daure ya mike saboda wani tinani dayayi kar suje su kira umm su daga mata hankali gwara yaje ya kashe wayarta ya boye tin yanzu, yana zuwa gida ya sameta sleeping peacefully, sosai ta bashi tausayi ya shafi gefen fuskarta yace my one and only boddi, daga ke ba kari a zuciyata…… Daukan wayarta yayi yana dubawa yaga missed calls din mahaifiyarsa, call log dinta ya shiga yaga batayi waya da yan gidansu ba, ajiyar zuciya ya sauke ya kashe wayar sannan ya boye……

Ko data tashi bata tambayi wayarta ba dan ta kanta take, sai daga baya taga ta nemi waya ta rasa, wayarshi ya bata yace tayi wayar da zatayi da yan gidansu, har ce mata yayi suje tayi register sabon SIM card a siya wani wayar tace kawai ya barshi inta haihu saje dan bata wannan take ba…… 

Haka abby ya share duk kiran yan gidansu har umm ta haifo tsaleliyar kyakkyawar yarinyarta me kama da ita sak kamar an tsaga kara an karya, saidai kuma a fizge tana yanayi da Abby shima, sosai suka sha shagalin suna harda mutane arziki daga Nigeria amma banda familyn Abby ko daya dan kin gaya musu yayi saboda har yau baya daga wayarsu, har mami dake Cyprus tana wani course saida tazo, kamar yanda sukayi planning idan namiji Umm ta haifa Abby ne ze zabi suna, idan mace ce ya bata zabi, tashin farko tace asama yarinyar sunan yar’uwarta wato fatima saboda ba karamin soyayya ne a tsakaninsu da mami..

Haka mami tayiwa namesake dinta shopping nagani na fada har Deen saida tasa aka kawo lokacin yana kusan 12 years, zuwan da umm ta hana deen komawa kenan ta rikesa a gurinta, sosai deen yake san yarinyar koda yaushe yana makale da ita kuma shi yasa mata baby tee shikenan kowa yake kiranta haka…… 

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

Har baby tee ta kai 1year Abby be dena abandoning family dinsa ba har lokacin kuma Umm batasan da labarin auren da aka masa ba kawai suka wayi gari da zuwan mahaifiyar Abby da kuma matar da aka aura masa, wai tinda matarsa ta sashi dena daukan wayarsu ita gashi tazo da kanta ta kuma kawo masa matar daya banzatar, hakuri Abby ya hau bata ya kuma ce mata ba ruwan matarsa dan har yau batasan da zancen auren ba, bata saurareshi ba tayiwa umm tatass sannan ta gaya mata ga kishiya nan an kawo mata ruwanta ta zauna lafiya da ita ruwanta taki kuma daidai take da ita, umm batace komai ba har tagama masifarta ta sunkuci yarta taja hannun deen suka shige ciki, binta da sauri Abby yayi yana bata hakuri, bata kulashi ba tashige toilet ta fashe da kuka, yana jinta tana kuka amma taki saurarensa, bugun duniya kuma taki budewa, haka ya koma parlour gurinsu, hakuri ya hau bawa mahaifiyarsa akan rashin daukar wayarsu da bayayi, cewa tayi bazata yafe ba har sai ya yadda ya zauna da huraira(ammy) a matsayin mata, kiri kiri ya nuna mata shifa baze iya zama da mata biyu ba tayi hakuri kawai ta yafe masa, ganin ya kafe akan hakan yasata cewa koya hakura ya zauna da huraira kota tsine masa, yanaji yana gani yace mata ya amince badan ze iya adalci ba amma ze kwatanta, albarka ta hau shi masa sannan tace a bawa huraira masauki dan ba zama zatayi ba so take ta koma, kai tsaye ya nuna mata baze hadasu gida daya ba ze kama mata gidanta daban, bata musa ba tinda ya riga ya amince ze zauna da ita saima cewa da tayi aje a kama gidan tana nan karta wuce a kama mata gida mara kyau, dake kota online mutum yana iya duba gida sai yaje yagani yasa Abby duba available gida dake nisa dasu kadan ya bawa mahaifiyarsa ta zaba, a take sukaje aka ga gidan dukda hankalin Abby nakan Umm amma babu yanda ya iya, kuma saida ya sake dubata kafin su tafi amma taki bude kofar, ba bata lokaci ya biya kudin gida dan huraira na ganin gidan tace ya mata….

Dawowar huraira sai ya bude musu wani sabon phase na rayuwa, tabbas Abby yasha wahala kafin ya shawo kan Umm dan har cewa tayi sai ya saketa saboda abun ba karamin tabata yayi ba, ace lokaci daya azo maka da kishiya har gida wai gata nan miji ya kara aure, saida yayi iya bakin kokarinsa sannan Umm ta kwantar da hankalinta har takai ita take masa nasiha akan yin adalci dan sai ta tirsasashi yake zuwa gidan huraira, abinda bata sani ba kuma hotel yake tafiya yayi kwanansa washegari ya dawo yace mata yaje, saida baby tee ta kai shekara uku lokacin tayi wayo sosai ga surutu kamar me, haka deen ze dagata sama yayita mata wasa tana zuba masa surutu kafin Abby ya daure ya dan fara zuwa gurin huraira bayan takai kararsa akan kudi kawai yake turo mata amma baya zuwa….

Ranar daya fara cin abinci a gidan huraira komai ya chanja masa, yaji kamar an chanzasa, umm na zaune taga kamar an jewo mutum, bece mata komai ba ya rubuta mata saki daya ya mika mata ba duka ba zagi, babu kalan magiyar da bata masa ba akan ya mayar da ita dan tana sansa kuma ita batasan meta masa ba, be kulata ba ya dauke yarsa ya nufi kofa, kafafuwansa ta ruko tana bashi hakuri akan ya bar mata koda yarta ne amma be saurareta ba yayi tafiyarsa, shima Deen kuka ya dingayi yabi abby har waje yana basa hakuri karya tafi masa da babynsa amma ko kallonshi abby beyi ba ya shige mota ya tafi, daga wannan rana bata kara jin koda labarinsa bane bare na yarta, tayi kuka tayi kuka har saida ta fita hayyacinta, duk wannan abun da take Deen na tare da ita dukda bakomai ya fahimta sosai ba, kiran mami yayi a waya ya gayamata umm nata kuka kuma Abby ya tafi da baby tee, da sauri mami ta biyo flight ta tawo, koda tazo Umm harta sume, ita tayi rushing dinta hospital itama sai kuka take tana ta tambayar Deen abinda ya faru, iya abinda ya gani shi ya sake maimaita mata, kwanansu uku a asibiti kafin su samu suyi magana da umm lokacin har bappa da anna sunzo dan mami ta gaya musu abinda ta tarar, sosai ran bappa ya baci dukda besan abinda ya faru ba amma yasan tabbas ita da Abby ne tinda deen yace ya tafi da baby tee, tinda umm ta farka take musu sambatu tana fadin ya sake ni, nashiga uku ya sakeni, wallahi ban masa komai ba, Anna ce tace ta nitsu tayi musu bayani sunsan batayi komai ba, nan ta kwashe komai ta fada musu har auren da aka masa data boye musu dan tasan halin familynta ba’a yin injustice a zauna lafiya shiyasa taki gayamusu maganr auren, fada sosai bappa ya mata akan boye musu da tayi a tinaninta zaa ce ta rabu dashi ne kome? Inda ta fada musu da ba tini ya kafa masa dokoki ba, hakuri ta hau basu ta kuma rantse musu basu taba samun sabani da Abby ba ko bayan auren, ko ranar daya saketa lafiya suka rabu da safe, kiranshi a waya bappa yayi saidai numbersa taki shiga, kwantar mata da hankali suka dingayi har ta dan sake tace musu ita kawai ya bata yarta ta hakura da auren, lallashinta sukayi tayi har ta dan ci abinci, satinsu daya aka sallami umm daga asibiti, ba karamin making effort bappa yayi na ganin Abby ba saidai abun yaci tura dan ya yanke duk wata hanyar da zata sadasa dasu,mafita dayace shine su koma Nigeria su sami iyayensa, direct suka wuce kuma bayan an sallamesu daga hospital, suna zuwa bappa ya kira mahaifin Abby a waya ya fadamasa yana san ganinsa, cewa yayi ya bari kawai yazo dan su basu masan anyi saki ba, a ranar kuwa yazo bappa ya kwashe komai ya fada masa sannan yace masa ya gayawa dansa ya bata yarta tinda yarinya ce karama idan ta kara wayo sai a bashi yarsa, sosai ya shiga shock dan be taba tinanin Abby ze iya rabuwa da umm ba ko a mafarki, hakuri ya shiga bashi ya kuma dau waya ya kira Abby a take, amma haka wayar taki shiga kamar yanda bappa ya fada, hakuri ya basa yace Insha Allah zeyi magana da Abby kuma zaa sasanta dan yasan da hankalinsa baze saki Jamila ba……..

Amma shiru haka kowa ya dena jin labarin su abby kamar wanda suka bace, harta huraira anyi kiran duniya itama baa sameta ba, mahaifiyar Abby data hada aure sai tafi kowa shiga damuwa dan kowa na zuwa sai yace ai ita ta janyo suna zamansu lafiya da matarsa ta bijiro da aurensa da huraira bayan tasan bayaso gashi yanzu an nemesu an rasa……..

Suko yan uwan Umm kowa nan nan yake da ita, ko zama ita kadai baa bari tayi, har sai tayi bacci kafin a watse, har kaninsu alameen da shima yayi aure lokacin kuma kusan lokaci daya matarsa suka haihu da umm saidai ita twins ta haifa kuma Umm ta riga haihuwa, haka ya kwaso iyalinsa daga dubai inda suke zaune duk suka hadu ake taya umm jimami….. 

A hankali itama ta fara moving  on saboda yanda kowa ke bata kulawa saidai ko so daya baby tee bata taba fita daga ranta ba, shiko Abby neutral kawai takeji akansa, bata sansa kuma bata tsanesa ba…… 

After one year har lokacin babu wani labari akan su Abby, dole tasa umm komawa bakin aikinta dan sun dameta saidai tayi requesting transfer dan bazata iya zama a England with all this memories ba, a take suka amince dan rashin irinta akusa dasu ba karamin asara bane, haka aka wayi gari umm ta cewa bappa zata koma uk, be hanata ba dan shima yafiso tayi moving on ta manta da Abby, haka ta koma uk ita da Deen daya dage sai ya bita, mahaifinsa yaso ya hana wai an rena masa hankali daga zuwa ya dan gaishesu sai a tafi dashi wani kasar, bappa ne da kansa ya nemi alfarmar ya barta su tafi kona shekara dayane dan yasan Deen ze debe mata kewa ya kuma hanata tinani, haka suka koma ta sashi a school ita kuma ta cigaba da aikinta at the same time tana taking wani courses, sosai suka shaku da deen dan bawanda yasan ba ita ta haifesa ba saboda har kama sukeyi dan yana kama da mami…..

     Saida tayi shekara biyar lokacin ta samu karin matsayi sosai kafin ta dawo Nigeria lokacin ana yiwa mami wani karin matsayi kuma har lokacin babu labarin su abby, komawa uk umm ta sakeyi bayan angama taro saidai wannan karan bata koma da deen ba dan mahaifinsa yaki yarda, babu kalan borin da deen beyi ba amma haka dole ya hakura ya zauna badan yanaso ba, bata dade da komawa ba mami ta koma Nigeria permanently…

   After 5 years ta sake komawa Nigeria lokacin da zaa bawa mami chief Justice, sosai bappa da anna sukaji dadin yanda sukayi making dinsu proud dan saida sukasa bappa yin retire dan dolensa, Anna ko dama ta dade da retire dan lecturer ce dama, har petrol station suka hada hannu suka ginawa bappa, anna kuma suka bude mata company ana yin abayas, sannan suka bude foundation na marayu da niyar Allah ya kare musu baby tee a duk inda suke……

Umm na komawa da shekara biyu itama aka bata highest rank a medical aspect wato attending physician, haka su mami da bappa da anna harda kaninsu ameen sukazo da iyalinsa suka tayata murna, bata kara zuwa Nigeria ba tin bayan komawarsu, saidai time to time suzo su kawo mata ziyara, da bappa ya musu maganar aure duk sai suka waske karshe ma kuka Umm tasa masa ta fara dawo masa da abinda Abby ya mata gashi har yau batasan inda yarta take ba, dole ya hakura ya kyalesu da zancen, sai randa mami ta kirata tace mata Deen yayi accident shine ta tawo ba shiri……..

         Bayan Abby ya bar gidan umm direct gidan huraira ya tafi da baby tee, wayarsa ta dauka tayi flushing sannan ta basa shawara su bar kasar, ba musu ya shirya musu tafiya suka koma Sweden, tinda sukaje yana rungume da yarsa yanata mata wasa, koda tace ya bata ya dauketa kin zuwa gurinta tayi, data dage sai ta dauketa sai tasa kuka, karshe ma sai tace ita a kaita gurin mamanta da yayanta, lallabata Abby yayitayi dan ba karamin san yarinyar yake ba, da tace akaita gurin mamanta kuma sai yaji wani iri amma sai yaji kamar besan wacce take magana akai ba, huraira da take ganin duniya ta mata dadi ta rabashi da matarsa saita fara samun challenge akan rashin kulata da bayayi kullum yana tare da yarshi yana mata wasa kamar akansa aka fara haihuwa, sosai ta tsani yarinyar harji take kamar ta kasheta, ba karamin damunta abun yake ba har take fadawa aminiyarta da suka hadu a airport wani lokaci wato samira(mom), ita data koyawa harkar sai taga tana nema ta fita iyawa dan shawara ta bata akan ta raba uban da yar kawai tasa a mata aiki me zafi yar tashiga duniya ya zamana ita kadai yake gani kuma yasota dan dole…….

    Kasancewarta kwararriya akan harkar mugunta saita zauna ta sake sabon shawara akan yanda zata billowa alamarin sai taga gwara ta batar da yarinyar daga duniya yanda har abada ba zaa kara ganinta ba, koda an ganta kuma kar a ganeta,sai ta fara takan sunanta, haka ta dagawa Abby hankali akan sai an canzamata suna, yanaji yana gani badan yaso ba,yasa akamata saban yanka aka canzamata suna zuwa zainab wanda ra’ayin huraira ne dan saida ta hanga ta dubo suna da tasan babushi a danginsu yanda ba zaayi saurin gane yarinyar ba, kwatsam yarinya taji ana cemata zainab bayan ita sunanta fatima,duk da abby kadai ne yake kiranta da fatima sauran mutan gidan kuma baby tee suke ce mata amma hakan baisa umm tabbatar da cewa tasan sunanta fatima ba,  sai yarinya tadauka an kara mata suna akan sunanta ne, shikenan duk wanda ya tambayeta ya sunanta sai tace ‘fatima zainab’ …… 

Tin tana tambayar mahaifiyarta harta hakura ta dena, karshe ma saita dauka ammy ce mamanta, a haka kuma babu kalar azabar da bata gallaza mata, tun tana shekara biyar ta fara koya mata shan codeine, tin bataso har taji yana mata dadi, abby kuma besan abinda akeyi ba dan kullum kafin ya dawo tayi bacci, har cewa yake a tasota saboda su gana da juna amma kememe ammy sai tace be kamata a tashe taba saboda zataje school da huri gobe, yana ji yana gani ganin yarsa ya gagaresa, saidai ko sau daya soyayyar da yake mata be ragu ba….  Babu kalan dukan da ammy bata mata ba dukda kankatar shekarunta, haka kawai inta kalleta taga fuskar uwarta ta kuma tina irin wulakancin da abby ya mata akan uwar sai taji wani bacin rai ya kamata sai ta hau marinta daga karshe tayi ball da ita dan har yau ta kasa samun kan abby, wani zubin ma sai taji yana ce mata boddi kuma tasan umm yake kira da haka, da dakin yarinya da komanta amma take kaita dakin megadi duk dare sai tace masa gatanan ta kawo ta yayi duk abinda yaga dama da ita kuma kar ya sake ya gayawa ubanta inba hakaba kashesa zatayi, shiko bawan Allah har daura mata net yake tayi bacci akan katifarsa shi kuma ya kwana a kasa, haka ze bita da kallo cikin tausayawa yana mamakin anya ammy ce ta haifi yarinyar dan babu uwar da zatayiwa yar cikinta haka, haka tasa akazo aka koya mata shan sigari saidai kememe takasa koya kamar na codeine, har giya saida ta bata tasha, yarinya tayi high harda suma, sai ga abu ya danganasu har gadon asibiti, nan likitoci suka tabbatarwa mahaifinta abinda tasha maybe by mistake ta dauka lemu ne, iya bincike abby yayi be gane taya akayi ta samu giya tasha ba, karshe haka yabar zancen yasa aka chanza duka kalolin juice din dake gidan, shidai yayi mamakin ganin yanda yarinya ta kanjame ta rame amma sai ammy tace masa ciwon kwana daya ne ya maida ita haka….. 

Ko bayan an sallamesu sun dawo gida ammy bata fasa azabtar da ita ba saidai bata kara bata giya ba ganin hakan na neman tona mata asiri dan sosai abby yasa tsaro akan lemukan gidan…

    Basu farga da sunan da take amfani dashi ba saida aka kawowa abby result din common entrance dinta kasancewar ammy ake kaiwa duk wani result nata, ita kuma shashashar bata taba dubawa ba saidai ta karba ta yaga ta watsasu a shara, sosai abby ya zama confused akan hakan gashi iya fatima zainab dinne akan sunan ko nashi babu, yayi niyar biyan kudi a chanza mata sunan amma yana gayawa ammy tace ya barshi kawai ai ba wani babban matsala bane, haka ya biye mata dukda zuciyarsa bata so, nan kuwa dadi ne ya kama ammy ganin yarinya ta saukaka mata lamari tinda ta cire sunan ubanta a sunanta, yanzu duk inda zata shiga bame ganeta dan ita kadai tasan irin tanadin datake mata, lokaci kadan kawai take jira ta aiwatar da abinda tayi niya, haka yarinya ta cigaba da amfani da sunanta a haka ko mutum ze shekara yana gayamata babu suna haka ba zata taba yarda ba, saboda codeine din da ammy take bata yasa takoma very silent yarinya mai surutu hakan yasa karatun natama da taimakon Allah kawai takeyi amma ba wani ganewa takeyi sosai ba..

Lokacin data kai jss2 ammy ta damu abby akan sudawo Nigeria, babu yadda ya iya haka suka tattara suka koma Nigeria, basu sauka a ko ina ba sai a Abuja dake dama yana da gidaje a abuja, ammy dakanta tazabi inda takeso su zauna, haka sake enrolling fatima zainab a school tacigaba da amfani da sunanta guda biyu, haka ammy ta dora daga inda ta tsaya akan azabar da take ganawa yar mutane, babu kalar azabar da fatima zainab bata fuskanta ba a hannun ammy dan akwai ranar da ammy ta lakawa fatima zainab sharrin sata a gurin abby, gabadaya yaji hankalinsa ya tashi zuciyarsa ta kasa gasgata hakan, amma dayake ammy juyashi takeyi baisan sanda ya dinga dukan fatima zainab kamar zai kasheta ba ammy sai tsallen murna take aranta, sai kuma daga baya yazo yana dana sani har yayita bata hakuri yana fadin baze kara dukanta ba dama wannan shine na farko, haka ammy ta cigaba da mata sharri kala kala idan ta fadawa abby kuma ya mata dan banzan duka sai daga baya yazo yana bata hakuri….. 

Kamar yanda take kaita ta kwana a gurin mai gadinsu na Sweden hakan nan ma tacigaba dayi a abuja, saidai bawan Allah yaji yanajin shaawar yarinya dan ta fara girma lokacin amma tsakani da Allah bayaso ya lalatata, kai tsaye yaje ya samu mahaifinta ya gayamasa dukda kashedi me tsauri da ammy ta masa, da farko kin yarda abby yayi sai yace masa ya fito kamar sha biyu saura ya labe zega ta fito da yarinyar, haka kuwa akayi abun aljabi abby na tsaye ammy ta kawota gurin mai gadi, kashedi ta masa kamar yanda ta saba sannan ta bar gurin, wannan rana har kuka abby saida yayi tsabar tashin hankali ace yarsa kwalli daya ake nema a lalatawa rayuwa ba shiri ya bankawa ammy saki daya dukda karfin asirin data masa na tasiri a jikinsa saidai san yarsa ya danne asirin ranar, tana ji tana gani yace wallahi saita bar masa gida, rasa yanda zatayi tayi ta kira kawarta samira dama da ita kadai suke waya dan ta watsar da dangi da kowa,  ce mata tayi kawai ta tawo gidanta sai su sake sabon shiri yanda zata dawo da zafinta, mayafinta kawai ta zara ta tafi gidan samira, washegari da sassafe suka fita itada samira zuwa gurin wani mallami da suke jindadin aikinsa, bayani ya musu sosai akan abinda ke tafe dasu kamar yanda ya sabayi duk sanda suka zo saidai ya bubbuga kasa yace gashi gashi, nan da nan ammy ta fadamasa tanaso ayi duk abinda zaayi ta koma dakin mijinta, sannan tanaso ayima yarinyar abinda zesa tabar rayuwarsu har abada sannan a mantar da kowa nata ita har ubanta dake fifitata akan kowa ya kasa ganeta idan sun hadu, sannan da kansa takeso ya kori yarinyar daga gidan, kuma tanaso rayuwar yarinyar ya wulakanta ta zama rikakkiyar yar shaye shaye sannan kuma karuwa me zaman kanta, haka kuwa akayi ya hada mata abubuwa kala kala ya kuma gayamata yanda zatayi amfani da kowanne, wani a abinci wani a karkashin gado zata binneshi, batasha wahalar shiga gidan ta binne na karkashin gadan ba dan ma’aikatan gidan babu wanda yasan abby ya saketa, zama ta cigaba dayi harya dawo, yana dawowa yace ya mayar da ita alamun aikin da akayi akansa yaci kenan, sauran ma duk haka ta barbade musu a abinci, a take abby yaji wani mugun tsanar fatima zainab ta kamashi, kullum yaganta in banda zagi da hantara babu abinda yake hadasu, wani zubin harda duka ma in bataci saa ba har ta kai ss1….. 

      On one faithful day! Ranar da abby yake kira da bakar rana, dawowarsa kenan daga office ya tarar da ammy na jibgarta, daya tambayi baasi kuma ammy tace kamata akayi suna lalata da wani saurayinta a cikin mota harda cewa idan be yardaba ya tambayi me gadi, wani irin sarawa kan abby yayi ba shiri ya nemi guri ya zauna dan ba karamin dakarshi maganar tayi ba, yaza ayi ace yarinyar da batafi 14 years ba ace an kamata da saurayi, kiran me gadi yayi dan ya yarda da me gadin dari bisa dari tinda ze iya gayamasa abinda ake mata na kawota dakinsa ai baze masa karya ba, haka me gadi da ammy ta wure wa kunne yazo ya bada shedar zir, ba karamin baci ran abby yayi ba jin maganar daga bakin trusted me gadinsa, ba shiri yace mata ta tashi suje su ammy aka baza ido da hanci ana jira aga abinda ze faru, saida ya sadata da kofar gida ammy na biye dashi sannan ya cillata bakin titi yace daga yau bashi ba ita! Ta nemi wani uban bashi ba!……

Daganan wani sabon phase na rayuwarta ya bude, ta dade a durkushe a gurin tana kuka har saida taji hawayenta sun kafe kap sannan ta mike ta miki layin taje ta samu uncompleted building ta zauna, har daga baya taje ta roki me taba sigari ta dawo ta zauna tana shan abinta, anan kuma daddy ya dauketa lokacin kuma yanada appointment da mahaifinta batareda yasan yar shi bace, appointment din dayayi losing kenan har abada saboda tausayinta daya kamasa a lokacin…….

Kamar kar dare yayi abby ya birkice musu a nemo masa yarsa shi be koreta ba kome tayi kuma yana santa a haka, kiri kiri ammy ta nuna masa ai shi ya koreta dakansa be nemi shawararta ba saboda haka babu ruwanta, sosai ya daga hankalinsa kamar wani zararre ya hau yawon nemanta a daren ranar dan zuciyarshi bazata iya jurewa ba, ammy na ganin haka ta kira mallaminta da sauri ta gayamasa zazzafan aikin da takeso a mata akan abby yanda ze manta da yarinyar gabadaya……

Haka ya gama shatale tale amma ko alamunta be gani ba, daurewa yayi ya dawo gidan da niyar gobe da sassafe ze fita nemanta ya kuma bada sanarwa a gidan radio da television, saidai me? Yana tashi da safe yaji kamar an masa formatting brain dinsa, yaji ya manta da duk wani abu daya shafi fatima zainab, shi ko zaa tambayesa ma cewa zeyi be taba jin sunan ba amma dake abun a zuci yake baayi sati daya da batanta  ba jininsa ya hau sosai hakanne kuma yayi leading to paralysis dinsa, ba shiri aka shirya masa tafiya dubai inda yake medical check up, saidai ammy bata bishi ba tace mishi tazo daga baya dan akwai abubuwan da take sonyi, shi kuma yana zuwa yaji bayasan kowa a kusa dashi har ita din shiyasa yaki gayamata taka meme asibitin da yake, tin tana damuwa tana mita akan abun kawai ta kwantar da hankalinta ta shiga spending kudinsa san ranta dan ba karamin attajiri bane abby…….

Haka yayi jinya for more than 5 years har Allah yasa ya hadu da deen a asibitin, cikin ikon Allah kuma yagane shi sannan irin sakin da yayiwa umm ya dawo masa, a take yaji babu wanda yakesan gani sama da umm kodan ya nemi yafiyarta, saida deen ya tambayesa baby tee ya tina yanada wata ya’ mai irin sunan amma dayake baya cikin hankalinsa ya koreta sai ya dauka tana gida tare da ammy…………

Kamar yanda yayi expecting suna haduwa da umm yarta ta fara tambaya, shi kuma hankali kwance yace aje a daukota dan har lokacin ya manta da shi ya koreta da kansa, abun mamaki kuma ammy tazo ita kadai, shine Allah ya matsi bakinta tayi duk wannan confession din!!!…….

    Tin kafin takai karshen labarin umm ta kifa kanta akan kujera, ashe ta suma babu wanda ya sani, Abby ko yana zaune a kasa sai raba ido yake amma babu abinda yake tinawa sai irin azabar da ya bawa yarsa da hannunsa sannan ya koreta daga gidansa da kansa…..

     Tana gama bada labarin fatima zainab ta tafi luuu zata fadi, da sauri deen ya tareta suka fada kan kujera tare daidai nan deen yayi ido hudu da khaleel da basu san sanda ya shigo ba!!….

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button