Harijin Sarki Page 29 Romantic Hausa Novel
Tsakar dare ne. Sarautar ta nutsu, amma iska tana motsi cikin hasumiyoyi kamar tana ɗauke da saƙo daga duniyar da ba a gani.Fitilun dake haske a fadar sarki sun fara rawa, haskensu ya ɗan dusashe alamar cewa wani abu yana tashi daga ƙasa.A cikin ɗakinsa, Sarki Rashid ya farka daga barci mai nauyin mafarki ya kalli Samha dake gefensa.Numfashinsa ya yi nauyi, jikinsa yana zufa.Ya ɗaga hannunsa, ya ga hatimin da ke gefen kirjinsa yana walƙiya da hasken baki da ja, kamar wuta da jini suna haduwa.Ba zai yiwu ba…” ya furta cikin murya mai rauni.“Na riga na kulle wannan ikon… me yasa yake dawo da kansa?”Wata murya mai sanyi, mai kama da iska, ta amsa daga cikin duhu:“Saboda kana ƙoƙarin gujewa ƙaddara, Rashid… Ba zaka iya tserewa ba.”Ya tsaya cak tabbas yasan wannan murya, murya ce ta Sarkin duhu, wadda ake cewa ita ce asalin hatimin sarautar Zirkan.”Kada ka manta da alkawarin jini,” muryar ta ci gaba. “Duhu ne ke kare masarautarka. Idan hasken mace ya mamaye zuciyarka, to sarki zai zama marar iko.” Sultan Rashid ya ɗauki wuƙar tsafinsa, ya nufi madubi mai siffar tauraro, ya faɗa da ƙarfi “Ni ba bawan duhu ba ne! Ni sarkin Zirkan ne! Inada Ikon yin abinda nakeso dole a barni na rayu da wacce zata iya dan, Samha eh ina nufin samha Ni na zama bawanta”Haske ya karye, madubin ya nuna hoton Samha tana barci a ɗakinta a kusa da ita, wata inuwa mai siffar mutum tana tsaye tana kallonta.Rashid ya ɗan ja baya, idanunsa suka kaɗa yace “A’a… ba za ki kusanceta ba!” Ya ɗaga wukar, ya furta kalmomin da baya furta su sai cikin gaggawa:“Bi ismu’l-nur al-maknun, aƙrimni bi ƙarfin haske!”A nan take, haske mai ƙarfi ya fito daga wukar, ya nufi hoton madubin.Sai dai kafin ya isa, muryar ta sake cewa cikin dariyar mugunta:“Haske ba zai iya rayuwa idan zuciyar mai ɗauke da shi tana da duhu ba”Take madubin ya fashe Sultan ya shiga cikin tashin hankali baison wani abu ya samu Samha to wai dama ba tare suka kwanta da ita bane? Kallon gadonsa yayi yaga babu kowa sai shi ɗaya ya cika da tsoro zullumin da mamakin wannan lamari, meyesa tun shekaran jiya da Samha ta furta rabuwa dashi abubuwa suke rikicewa a ɓangarensa ne?.A gefe guda kuwa, Samha ta farka cikin firgici.Idanunta suka zazzaro, jikinta yana rawa.Ta ga ƙaramar alama ja a gefen wuyanta — kamar an latsa mata hatimi.“Subhanallah…” ta furta da razank.“Wani abu yana faruwa da shi…….”Ta miƙe da sauri, ta ɗauki mayafinta, ta nufi hanyar turakar Sultan itama tana rayo ai tare suka kwanta ya akayi suka rabu cikin dare? Masu gadi suka yi ƙoƙarin dakatar da ita, ta kallesu ɗaya bayan ɗaya tace “inada muhimmanci a yanzu gareshi Ku faɗa masa ni ce Samha. Likitarsa. Idan bai gan ni yanzu ba, zai rasa ransa!”Jin wannan, suka buɗe mata.Da ta shiga ɗakin Sultan Rashid yana tsaye a tsakiyar ɗaki, jikinsa yana rawa, haske da duhu suna haɗuwa a kansa.Idanunsa sun ɗauki launin ja, muryarsa ta canza.“Ki koma, Samha! Ki barni!”Bata koma ba kuma bata daina takawa ta matsa kusa, tana ajiyar zuciya tace “Ba zan bar ka ba! Duk abin da ke faruwa, sai mun fuskance shi tare!”Ta riƙe hannunsa.Zafin jikinsa kamar wuta haka ta ƙara riƙe hannunsa “Samha…” Sultan ya furta cikin rauni.“Ki barni kafin ki ƙone. Ki barni kafin wutar ta ci gaba da wanzuwa Ni kaɗai nasan abinda nakeji a jikina ki barni ku rayu keda ɗana banason na rasaku” share hawayenta, ta ce cikin ƙarfin hali:“Idan zan ƙone, ka barni na ƙone a tare da kai.”A lokacin da ta faɗa haka, hatimin duhu na ƙirjinsaya fara haske sosai, saɓanin hasken ja wanna wani sabon haske ne, haske mai launin fari ya fara fitowa daga hannunta.Wutar ta haɗu da haske, dakin ya cika da ƙarar da ta girgiza masarauta ƙasar birnin ta cika da wani irin gunji mutane suka farka suna tambayar “Menene wannan yake ƙara daga fadar sarki?” cikin ɗakin kuwa Rashid ya faɗi a ƙasa jikinsa babu motsi.Samha ta durƙusa, tana riƙe da hannunsa cikin kuka take girgiza shi tana cewa “Ya Allah… kar ka ɗauke shi… kar ka bar ni cikin duhu…”Hawayenta ne ya sauka bisa hatiminsa, haske ya sake bayyana ya shiga jikinsa nan take Numfashinsa ya dawo sannu a hankali.Ya buɗe ido, idanunsa sun koma fari.“Samha…” ya faɗa cikin sanyi. “Kinyi nasara… duhu ya fara ja baya.”Ta murmusa cikin hawaye. “Ba ni ba… Imani ne.” Sultan rashin imani da Allah ɗaya duk shine Ummul aba’isin wannan halin da muka tsinci kanmu babu shiri”….

