Gwamnatin Najeriya ta fitar da sunayen mutum 15 waɗanda ta ce ana zargin su da taimakawa ta’addanci a ƙasar.
Hakan na kunshe ne cikin rahoton da hukumar tattara bayanan sirri kan sha’anin kuɗi a ƙasar (NFIU) ta fitar a ranar Talata.
Ta ce waɗanda ake zargi da taimakawa ta’addancin sun kunshi mutum tara da kuma masu kamfanonin canji.
Rahoton na NFIU ya nuna cewa kwamitin sa ido kan takunkumi a Najeriya ta zauna ranar 18 ga watan Maris, inda aka bayar da shawarar saka takunkumi kan wasu mutane da kuma kamfanoni saboda hannu a tallafawa ta’addanci.
“Babban Attoni Janar na Ƙasa, tare da amincewar shugaban ƙasa, ta ayyana waɗannan mutane da kamfanoni don a saka su a jerin waɗanda aka saka wa takunkumi,” kamar yadda raoton ya bayyana.
Cikin jerin mutanen har da Tukur Mamu, wanda ake ci gaba da shari’arsa kan zargin taimakawa ƴan bindiga waɗanda suka kai hari kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a watan Maris ɗin 2022.
A cewar kundin da NFIU ta fitar, ta ce Mamu ya tallafawa ta’addanci ta hanyar karɓar kuɗi da ya kai $200,000 daga hannun waɗanda aka yi garkuwa da ƴan uwansu da kai wa masu garkuwa, don sakin fasinjojin jirgin ƙasan na Abuja-Kaduna.
Har ila yau, rahoton ya ce ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi shi ne wanda ya kai hari kan cocin Katalika na St. Francis da ke Owo, a jihar Ondo ranar 5 ga watan Yulin, 2022.
An bayyana ɗaya daga cikin mutane a matsayin mamban ƙungiyar Ansarul Ansarul Muslimina Fi Biladissudam, wadda ke alaƙa da Al-Qaeda da ke yankin Maghreb.
Akwai kuma wani babban kwamandan ƙungiyar ISIS a Afrika ta Yamma, wanda shi ma ake zargi da taimakawa ta’addanci a Najeriya.
Source: bbc Hausa