Uncategorized

Mahaifin wata ‘yar TikTok ya kwanta dama bayan ganin bidiyonta tana rawar wakar batsa

 

Mahaifin wata ‘yar TikTok ya kwanta dama bayan ganin bidiyonta tana rawar wakar batsa

Wata ‘yar TikTok ta yi sanadiyyar ajalin mahaifinta bayan ya ga bidiyonta tana rawa da wakokin batsa da zage-zage a kafar.

Ganin bidiyon nata ke da wuya, wanda dama shi malami ne na addini, ciwonsa ya tashi yace ga garinku.

Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito bidiyon wani mutum yana bayani, ya ce wani malamin addini ne ya ga diyarsa tana rawar TikTok wanda hakan ya yi ajalinsa.

Kamar yadda mutumin ya bayyana, daya daga cikin daliban malamin ya dade yana ganin diyarsa tana rawar amma sai yana kokwanton idan diyar malamin ce.

Ya ci gaba da shaida cewa watarana ya ga yarinyar ta saki wani bidiyo na rashin kyautawa, sai ya dauka ya nunawa mahaifinta bayan sun gama karatu.

Babbar matsalar Kannywood shi ne karancin ilimi a masana’antar, Aminu Sharif (Momo)

Video Amarya Ummi Rahab Tana Cin Abinci Abin Burgewa

Ya bayyana cewa an nuna masa bidiyoyi fiye da hamsin na diyarsa wadanda take nuna tsiraicinta da kuma rashin tarbiyya.

Ya bayyana cewa bayan ya tsare diyar da matarsa akan yadda su ka ci amanarsa yayin da su ka yi cirko-cirko, ya yanke jiki ya fadi kasancewar yana da hawan jini.

Ya ce bayan ya yi kwanaki a asibiti ya mutu sanadiyyar wannan takaici da bakin cikin da diyarsa ta sanya sa a ciki.

Buhari ya umarci TikTok da sauran kafafe su cire duk wata wallafar tsiraici ciki awanni 24

Gwamnatin Tarayya karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bai wa duk manyan kafafen sada zumuntar zamani kamar Instagram, Facebook, Twitter, WhatsApp da TikTok umarnin cire duk wata wallafa mai dauke da tsiraici, lalata ko kuma wani abu na rashin da’a cikin awanni 24, Instablog9ja ta ruwaito.

An samu wannan bayanin ne cikin sabbin dokokin amfani da kafafen sada zumunta ko yanar gizo da aka saki.

Kamar yadda dokar ta nuna:

“Duk wadannan kafafen na yanar gizo su yi gaggawar cire duk wasu wallafe-wallafe da ke dauke da tsiraici, lalata da sauransu wadanda aka shirya don tozarta mutane.

“Wajibi ne kafafen su dinga kula da korafi wurin sauke duk makamanciyar wallafar tsiraici cikin awanni 24.”

Dokar ta kuma bayar da umarnin a cire duk wata wallafa da ke kalubalantar wani ko kuma hukumar da ke karkashin gwamnatin tarayya.

Har ila yau gwamnati ta umarci kafafen da su tabbatar ba a sake wata wallafa makamanciyar hakan ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: aihausanovels@gmail.com

Back to top button