Gargadar So Chapter 113 By M Shakur
Gaban Ammi faduwa yashigayi jin abinda Baba yafadi tace “Subhanallahi meya faru? Maisa kace haka Malam? Ko jiya saida mukai waya tagayamini taje park kallon ganye haka da iri” dasauri Baba yace “nikuma Ibrahima cemin yayi tana gida ya akayi suke fadin abu daban daban” dasauri Ammi tace “ohh Allah na, fadamin kaimene kalura Malam“ daga abinda yafaru jiya zuwa yanzu da asuban nan dayakira Khaleel Baba ya sanar da Ammi yace “wlh Zainabu wani babban abu nafaruwa tsakaninsu ki gwada kiran Hawwa muji dan ni banda hakuri zan iya duramata ashar akan Ibrahima kin sanni, haba yaro na fama da kanshi halakashi takeson yi” zuciyan Ammi ba dadi tace “bari nakirata” kashe wayan tayi tashiga kiran wayan Hawwa kusan sau biyar duk bai shigaba not reachable yake gayamata, ijiye wayan tayi tace “anjima na kirata back”.Girki Hawwa tayi just pasta tai making da tea takai komi dinning ta ijiye tafito takoma sama tana kallon dakinshi tashiga ciki, dayake tai wanka sai tawuce closet nata tashiga shiryawa even though basaita saka uniform ba kawai saita shiga shiryawa cikin uniform tsaf tai kyau sosai around 8:00 dot na sage tabude kofa tafito daidai shima Khaleel yafito yana sanye da jean dawata shirt daya bude boturan gaba ya makala dark shade a idanu yana kamshi sosai, sai kamshi yake hada ido sukayi ta dauke kai tanajin haushin yanda taga yayi kyau kawai tawuce staircase tashiga sauka Khaleel ya tsaya yana kallonta kaman taji wani abu saikuma ta tsaya bayan takai last staircase din ba yabo ba fallasa tace “I’m resuming work today!” Tana maganan tawucetai wajen kofa tasa hannu zata bude kofan Khaleel yace “Hawwa!” Chak ta tsaya sabida yanda taji da kakkausan murya yakirata but bata juyoba yace “kinsan I’m the one that married you! Bake kika aureni ba ko?” Juyowa Hawwa tayi ta watsamai kallon rashin mutunci jin maganan day mata yana tsaye a sama, strictly yace “get back inside and remove that uniform and stay at home, my wife can’t be working awani police station or as a police woman never!” Sosai Hawwa ke kallonshi bata tabajin bacinrai a tone na Khaleel yana mata magana ba sai yanzu, kallonshi tayi from head to toe tace “which wife are you talking about? And wani husband? Auren da banso? Mijin dana tsana? Find matan dazakai controlling not me!” Tana maganan tajuya tareda bude kofa tafice Khaleel yaji kirjinshi nawani tafarfasa sosai, yahau wani kalan nishi ranshi yabaci kanshi kawai yashiga sarawa sosai bana wasaba yakasa motsi yafara ganin jiri jiri dasauri yashiga dukawa yana breathing fast fast yana kokarin saita kanshi yana taking deep breath.Hawwa na fita taji tama kasa gudu sosai but dai still tacigaba da gudu zuciyanta yashiga mata ba dadi wlh hakanan taji bazata iya zuwa aikin ba tunda yahana kawai dai tafito ne bamatasan mesa ba kodan ta nunamai batajin magana ne oho,Wayanta ne taji yana ringing dasauri tai slowing down ta gangara gefen hanya tadauki wayan tana ganin number ne batasan number ba ko daga office nasu ne, amsa wayan tayi takai kunnenta kai tsaye cikin muryanta mai dadi tace “hello!” Kaman daga sama taji muryan Baban Yaseer yace “Assalamu Alaykum Hawwa nine Baban Yaseer, Aliyu ne!” Wani kalan faduwa gaban Hawwa yayi batasan sanda tazare wayan daga kunnenta takalli call din tama kasa maida wayan kunnenta ba Baban Yaseer yace “Hawwa Hawwa sorry na kiraki impromptu, I just tried layinki banma dauka zai shiga ba cus I thought kin chanza layi bayan aure, daman i called naji yaya kike ne? And how are you holding up with the divorce?” Da farko da Hawwa bataso ta maida wayan kunnenta but jin maganan da Baban Yaseer yayi dasauri ta maida wayan kunnen kai tsaye tace “did I tell you am divorcing anyone ne?” Dasauri Baban Yaseer yace “ohh not really but nasanki sosai to know what is going on in your head, I know u are not happy, don’t get me wrong Hawwa I’m on your side like I said yesterday I just called to check on you” ran Hawwa abace tace “Baban Yaseer karka kara kirana again please! I don’t appreciate that! Ni da mijina are fine okay” dasauri yace “Wlh karya kike you are not fine!” Wani irin mamaki abin yabama Hawwa data fara tunanin kodai yasami tabin hankaline mutumin nan cus this is not the Baban Yaseer she knows, Baban Yaseer yawani rage murya yace “I know you cried severally yesterday, I know he’s hurting you, I know he is not treating you right!” Yawani kara rage murya yace “nobody can treat you better than me! Nida har matana na saka sabida ke, I love you Hawwa!” Bala’in faduwa gaban Hawwa yayi jin da aurenta tana sauraron wani na gayamata he loves her batasan sanda tacire wayan daga kunnenta ba tana kokarin kashe wayan wayan yashiga speaker daidai Baban Yaseer yace “I will wait for you alkali na baku saki I will marry you..” “saidai ka auri uwarka jaki! Mahaukaci!” Hawwa tafadi loosing all respects for him jin abinda yake gayamata da aurenta akanta tace “ka sake kirana wlh I will drop duk mutunci naci uban mai garinku”takatse wayan daga kunnenta kawai Baban Yaseer yashiga kiranta tana katse wayan yana kira tana katse wayan ahaka ganin yaki daina kira kawai saita saka wayan a flight mode tama jefar da wayan ta kifa kanta not knowing wat to do gajiya tayi kawai ta kunna motan tai reverse takoma gidan tai parking tafito tawuce side nasu taga Khaleel bayanan wajen abinci taje ta bude taga bai taba komiba taji abu ya tsayamata awuya.Uniform tacire ta kwanta she’s not happy babu abinda ke mata dadı aryuwanta ahaka har tayi la’asar tasauko falo zata wuce tashiga kitchen kawai taji landline na falon na ringing saida tadan firgita cus ta dauka decoration ne kawai dasauri ta wuce wajen Khaleel ne ke kiranta dauka tayi ahankali taji muryan namiji yace “Good Evening Ma this is security 067 at the gate, we have a guest here that claim to be your Mom, she said her name is Zainab all the way from zaria!” Atsorace Hawwa tace “Ammi” “did you know her”? Dasauri Hawwa tace “yes yes she’s my Mom”?.

