Fatalwar Delu Part 10
🤡 FATALWAR DELU 🤡
Part 10
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Baki na saki na bishi da kallo har ya gama wucewa daga shagon, ko da yake ba abinda ya kamata ya bani mamaki bane dan Bukar yaki zuwa kiran fatalwa idan nayi la’akari da shegen tsoron da yake da shi. Tunani na shiga yi a raina, shin ta wace hanya zan iya lallaba Bukar ya yarda muje wajen Fatalwar nan yau da dare ta yafe masa ayita ta kare, su kansu yan garin ma da sun sama lafiya ai. Na kare duk tunanina ko kusa ban hango dabara ko wayo da zan iya yiwa Bukar ya yarda ya fito tsakar dare bama balle har ya yarda ya bini wajen fatalwa. Ina tsaka da tunanin ne wayata ta fara kara na dauka na sa a kunne da sallama. Mahaifiyata ce bayan mun gaisa take tambaya lafiya ban karaso gida ba bayan tun shekaran jiya na taho. Nan nake tuna mata tsayawa da nayi garin su abokina Bukar domin mu gaisa. Fatan alkhairi tayi mun kana ta ce ya dai kamata in taho gida dan mahaifinmu ma na tambayata yace ban kirashi ba. Na ce eh na kirashi da zan taso a nan garin ne ban kira ba saboda wayata ba kati amma yanzu in na fita zan saya in kira. Da haka mukayi sallama tana tambayata yaushe zan taho nayi saurin katse kiran saboda bansan abinda zance ba kuma.
Ni kaina ina son tafiya to amma wannan fatalwar Surayyah na tabbata ba zata barni in tafi cikin sauki ba. Yanzu ma tunanin ya fado min na rasa dalilin da yasa na kasa yin karatun neman tsari ga fatalwar nan haduwar da mukayi da ita jiya da kuma yau. Amma na kudiri aniyar idan har ta sake ta bayyana a gabana yau sai na konata da addu’a fitar dare dai ba fasawa zanyi ba, saboda ba tsoronsu nake ji ba daga ita har uwarta Delu. Jin cikina yana murdawa na tuna ko karyawa banyi ba don haka na fito na kulle dakin ina ta waige-waige inda zan ga Bukar amma ban hangosa ba. Don haka nayi sallama gidan ina tambayar ko yana nan daga ciki naji ance baya nan, ni kuma yunwar da nake ji ba zata bari na tsaya jiransa ba don haka na dauki hanya nayi cikin gari domin neman abinda zanci. Na dade ina yawo banga inda ake sayarda abinci ba, don haka na samu wani matashi na tambayeshi inda zan samu abincin sayarwa. Nan yake fada min wai ba zan sama abincin sayarwa yanzu ba sai karfe biyu tayi ‘yar mai gari Hamsa’u tana kawo tallar shinkafa da wake a majalissa. Ido na zaro waje domin na tabbata yanzu ko karfe sha biyu batayi ba, yunwar da nake ji ba zan iya hakura har karfe 2 ba tukun in karya.
Cikin sa’a na samu ya kwatanta min wani kanti inda yace zan iya samun lemu da biredi a can. Haka kuwa akayi dake kauyen ba yawa gareshi ba, bansha wahala ba na je shagon na saya biredi da lemun roba na karya tukun na koma. Har lokacin Bukar bai dawo ba, don haka na shiga daki na jona wayata a fawa bank na hau latse-latsen waya. Da rana bayan munyi sallah ni da Bukar muka nufi wajen Hamsa’u mai abinci, da yace mu tsaya mu jira a gama abinci a gidansu na nuna ina ba zan iya jira ba. Bayan mun karyo kwana tun daga nesa na fara hangota zaune a gaban kular abinci, sai gyare-gyaran rubobi da chokula take, ga wasu yara da suka zagayeta suna mika mata kwano da alama masu saya ne. Haka ya nuna bata dade da zuwa ba, yarinyar ba fara ba ita ba baka ba, amma kyakykyawa ce matuka, don tun kan mu karaso na gane hankan. Duk da tana yar kauye amma na ga kwalliyar fuskarta ba kalar ta yan kauye bane, har muka karasa wajen ban dauke idona daga kanta ba, Bukar na ta surutu amma ni ba ko wanne nake amsa masa ba, domin tuni zuciyata tayi gaba.
Ni sai da na karasa mukayi sallama ta amsa, ai sai muryarta ta karashe saye zuciyata baki daya. Don haka ba bata lokaci na bata wajen zama a farfajiyar zuciyata, ni bansan a gidan ubanwa na koyi iya tsara kalaman soyayya ba, amma ina da tabbacin na iya dai-dai gwargwado. Don haka na shiga yakin nemo soyayya da kalaman bakina, tun ina furta kalaman tana bata fuskar har ta dawo tana murmushi. Bukar sai kwabata yake amma naki kulashi haka na shiga tsara yarinyar mutane, daga karshe bayan mun gama cin abincinma Bukar ya ce in ta so mu tafi ni kuwa na ce ina nan ya je sai na taho. Haka kuwa akayi ya barni nan, ina ta zuba mata surutu wasu ta amsa wasu tayi dariya ko ba komai dai na gane na samu karbuwa, ban baro wajen ba sai da tayi min kwatancen gidansu duk da kuwa naji ance yar mai gari ce, na ce mata da yamma zan shigo hira shima bata musa ba. Haka kuwa yamma nayi na je na aika aka kirata ta fito na kara zazzage mata irin kaunar da nake mata, ta kuwa amsa domin ta furta min kalmar so naji dadi sosai nima.
Sai wajejen magariba na baro wajenta na taho gida ina ta sake-saken zuci tabbas da gaske nake son Hamsa’u ni tuni ma na manta da batun wata Surayyah fatalwa, ko da yake ita dama babu ita a lissafi tunda ba mutum bace. Da na zo gida na tarar da Bukar bayan magariba ba irin bakin da ban basa ba a kan ya yarda ya biyo ni muje ya ba Fatalwar nan hakuri ta shafawa mutane lafiya amma bawan Allahn nan yaki. Daga karshe kallon mahaukaci ya fara yi min ma, a cewarsa idan ba karen hauka ya cijesa ba me zai sa ya fito yaje wajen fatalwar wai da sunan neman afuwa. Ina ji ina gani bayan munyi sallar isha’i a gaggauce muka ci abinci, domin yana sauri ya gudu can shagon abokinsa Musa inda ya kwana jiya. Bayan mun gama ni da kaina na rakashi har shagon lokacin karfe tara ta kusa sun nemi in tsaya kar tara tayi min a hanya in hadu da fatalwa nayi murmushi hade da cewa su ne suke tsoronta. Nan na barsu Bukar yana ba Musa labarin da na bashi, harda batun gayyatarsa da nayi domin neman afuwa wajen Fatalwa. Kamar jiya yau ma waje nayi shimfidata na kwanta, ina jin jama’ar garin suna guje-gujen shiga gida amma ni ko a kwalata, don kallo ma nake a waya. Nine har karfe 12 na dare a waje ina kallo, garin yayi shiru baka jin motsin komai sai kukan gyare da na tsuntsaye sama-sama, lokacin film india hausa da nake kallo ya kare, don haka na kwashi tabarmar na shiga shago na rufe.
Daga zaman da nayi a waje har zuwa shigowata nayi zaton waccan fatalwar zata zo, ganin bamuje da Bukar ba amma sai gashi shiru banga alamarta ba don haka na kwanta na fara bacci hankalina kwance, don dama ni banyi niyar zuwa ba tunda Bukar suka bukaci yaje ya basu hakuri ba ni ba. Cikin bacci na ji ana kwankwasa kofar daki, na farka ina tsaki, na aza ma asuba ce tayi don haka na danna wayata domin kallon agogo bisa mamaki sai na ga karfe 2:30. Don haka na ce “Waye!”. Cikin daga murya, amma sai naji shiru ba’ayi magana ba an sake kwankwasawa. Nan kara fadin waye still dai ba magana, don haka na tashi a fusace na zare kubobin kofar shagon na haska waje amma sai gani nayi babu kowa. Na ja tsaki na tura kofar na sake saka sakata amma tun kafin na idasa sakawa na ji an sake kwankwasa kofar. Hakan yasa na bude raina a bace na fita waje ina haskawa, ina tambayar waye. Ba zato ba tsammani sai ji nayi an sharara min wani wawan mari a fuska, nan take na dafe fuskar ina mai sunkuyawa kadan domin naji zafi sosai, amma ina dagowa sai ji nayi an sake falla min wani sabon marin wanda ya fi na farko zafi.
Ai bansan lokacin da nayi wata uwar ashar ba, wacce ni kaina bansan cewa na iya irin wannan zagi ba, kana na bi baya da fadin, “Wane shege ne yake labewa cikin duhu yana marina. Idan kin isa ko ka isa kai shege ne ka fito fili muyi gaba da gaba mana”. Ko gama maganar banyi ba daga bayana naji ance “Gani nan ni ce nan nake marinka”. Tun kafin in juya tabbas na gane muryar sarai ba kowa bace fatalwa Surayyah ce. Ina juyawa ban tsaya wata-wata ba nima na dauketa da mari, duk da a juyowar da nayi fitala ta hasko min a mummunar fuskar da ta bayyana da ita irin ta dodanni. Dafe kumatu da hannunta mai cike da zankala-zankalan yatsu da farata tayi tana kallona, kana sai ji nayi ta bushe da dariya abinda banyi tsammani ba. Ni kuwa zuciyata shawara take bani a kan in kara sharara mata wani marin tunda nima mari biyu tayi mun. Cikin masifa na fara fadin, “Ke wace irin muguwa ce, me nayi miki da zaki mareni haka kawai tsakar dare, irin wannan mari mai zafi haka hala so kike ki kurumtani? To wallahi ba zan lamunci wannan cin mutuncin ba, ni ba irin yan adam din da irinku iskokai suke wulakantawa bane su ci bati, domin da karatu a kan nan nawa na sauke, yanzu sai in toyaki kurmus”.
Duk maganar da nake bata ce kala ba, sai dariyar da take marar dadin saurare, lokaci daya kuma sai naga ta tsayar da dariyar ta bata rai matuka, ina cikin haskata tuni naga kanta ya fara yin ja ko ba’a fadi ba na tabbata ranta ne yayi mummunar baci. Zuwa yanzu ya kamata ace na arce duk kuwa rashin tsorona ai mutum da aljan karfinsu ba daya bane, amma sanin da nayi ina dauke da ayyatul kursiyyu, da wattaba’u, ga wassafati a kaina shiyasa nake jin cewa duk fitsarar aljani bai isa yayi mun komai ba, asalima wannan shine dalilin da yasa bani da tsoro ko kadan. Magana ta farayi cikin wata irin murya mai ban tsoro, tunda na zo duniya ban taba jin kalarta ba, yanayin yadda sautin amon muryar ke fita uku-uku na tabbata iya maganar kadai ta isa ta sa mutum ya saki fitsari a wando cewa take, “Wato tsaurin idonka har ya kai ka sa hannu ka mareni duk da kasan cewa ni ba mutum bace? Lalai yau ka kwaso ruwan dafa kanka, domin kuwa a yau son da nake yi ma ba zai hana in karyama hannuwa ba sannan in kwakule ma idanu, kaga daga nan ko ance kayiwa wani rashin kunya ba zaka samu damar yi ba”. Duk da kasancewar na tsorata matuka, amma sai na boye tsoron a zuciyata hade da cewa, “Kamar ya, wannan ai rashin adalci ne, idan da gaske kina sona ai a tashin farko ma ba zaki mareni ba, ballema mari biyu kikayi min ni kuma daya kacal nayi miki”.
Ba zato ba tsammani sai ji nayi ta daka min tsawa cikin fadin, “Yi mun shiru, laifin da ka aikata ka cancanci hukuncin tashin farko ma in raba kanka da gangar jikinka. Marin da nayi maka gargadi ne kawai amma sai gashi ka kara wani laifin a kan wani ta hanyar marina, to bari kaji in fada maka, kayi kadan ka hada soyayyata da ta wata ‘ya mace a wannan rayuwar. Yanzu ka fada min zaka fita daga harkar waccan yarinyar bil adama da kuka hadu dazun ko ba zaka fita ba yanzun nan in kasheka kowa ma ya huta?”. Ko da jin haka sai gabana ya fadi, wato da gaske kenan wannan fatalwar ta zame min tamkar CCTV camera duk abinda nake tana kallona kenan ko da rana ne? Lalai aiki ya ganni ashe ba ma karami ba kuwa. Sanin ina da addu’o’i a bakina yasa na kauda tsoro na ce, “In dai game da Hamsa’u kike magana bari kiji in fada miki yanzu ma na fara sonta, tunda itama ta amsa tana sona, kuma ba abinda kika isa kiyi”. Ko da gama fadin haka sai ji nayi ta daka min tsawa, sannan ta fara kurma wani uban ihu mai firgitarwa, a duk sanda tayi ihun sai in ga wani iska mai karfi ya fito daga bakinta har yana yunkurin jana baya. Gani kawai nayi ta tashi sama cikin iska, ranta a matukar bace, “Yanzu ta tabbata babu wani dalilin da zaisa na barka a raye, laifukanka uku ne, na farko na ce kaje kai da Bukar amma ka zo ka kwanta kana bacci, na biyu ka mareni sannan mafi muni ka hada soyayyata da ta wata a zuciyarka”.
Tana gama fadin haka nan take ta daga hannayenta sama, ni dai ina nan tsaye ina haskata da wayar hannuna, ba zato ba tsammani sai gani nayi wani irin iska mai karfin gaske tamkar guguwa ya tunkaro mu ta bayanta, na kuwa tabbata ita ta jawo iskan zuwa kaina. Don haka na fara yunkurin karanto addu’a domin nuna mata ba ita kadai Allah ya ba baiwa ba. Amma me ga addua ina ji a kwakwalwata amma na kasa kawota zuciya balle ma baki ya furta, kusan karo uku ina yunkurin karanta addu’a amma bakina ya kasa furta ko kalma guda. Ai nan take naji wani irin tsoro da ban taba jin kalarsa ba ya ziyarci zuciyata. Cikin gajeren lokaci tuni zuciyata ta gama bani shawarar da nayi amana da ita kuma na karba hannu bibiyu, shawarar kuwa itace in gudu. Don haka na juya na nufi hanyar cikin gari a guje, ina iya cewa gudun da nake ban taba yin kalarsa ba, ko ba komai dai wannan gudun kalarsa ne ake cewa gudun ceton rai………
Yau ma fa ba wutar ta dawo ba, kawai dai masu yi min magana a kan cigaba ne suka yawaita, 🤣 na ji ya kamata ko da na yau ne in rubuta, kunsan idan mutum bashi da isasshen caji duk jinsa yake a takure