Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 44 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                            FORTY-FOUR📍

   Daka mata tsawa dad yayi yace;

     “Me kika binne?”…..

Jiki na rawa tace;

    “Ni na rabaku! Ni ce! A bayan gidan na binne”….

Wani tsawan dad ya sake daka mata yace;

     “Zaki mana bayani ko kuwa?”…..

Dankwalin kanta ta fizge tana fadin;

    “Zanyi zanyi!”……

   Kanin labari;

    Fatima(mami) da samira(mom) sun kasance kawaye ne tin suna yara kanana kasancewarsu makota, haka suka taso tare gwanin ban sha’awa babu wanda besan kawancensu ba, shakuwa tayi shakuwa har suka zarce aminai suka zama tamkar yan uwa, idan har zakaga mami tabbas mom ma tana nan, harta islamiyya da boko iri daya suke zuwa, kuma tare suke zuwa, haka gurin zama ma tare suke zama, kawancensu saida ta kai ta kawo har kaya iri daya suke sawa, har ta kai idan zaa siya musu abu a gida guda biyu ake siya, sai da suka fara zama yan mata shedan ya fara shiga zuciyar mom, abun ya samo asali ne daga yanda mami take da farin jini kasancewarta kyakkyawa kuma su dama haka yan gidansu suke kyawawa, itama mom tana da nata kyan daidai gwargwado saidai rashin godiyar Allah dake dawainiya da ita, babu abinda yake daga mata hankali irin yanda kullum in suka fita sai an biyosu kuma kowa yazo yace mami in kaga tayi saurayi toh ita kadai ta fita, sosai hankalinta yake tashi akan hakan harta kai ta kawo tana bata mami a boye a gurin masu sonta, ba karamin yaki tayi ba gurin boye bakin cikinta a fili har suka shiga university ko so daya bata taba bari wani ya gane ba… Sannan mom bata kara rena kanta ba saida suka shiga university, gashi dama sun nemi admission na law mami ta samu ita bata samu ba, ga masoya da suke kara yiwa mami yawa, sai hassadar da takeyi yaci uban na da….. Saidai ko a haka suna makale a tare in sun gama lectures, kuma ko daya bata da lectures zata rako yar uwarta…..

Suna level two wata rana sun fito daga cafeteria zasu shiga mota su wuce gida Abubakar(dad)  ya hangonsu lokacin yazo gurin wani abokinsa lecturer, tinda idonsa ya sauka akan mami yaji notikan kansa sun kwance yaji kamar an zuba masa zazzafar soyayyarta lokaci guda, yana kallonsu har mami taja motar suka bar gurin, ba bata lokaci ya fasa abinda ya kawo shi ya bi bayansu, saida ya bari suka shiga gidan sannan yasa ayi masa sallama da me gidan dan dagaske yazo  ba da wasa ba shiyasa kawai ya zabi yabi ta sama, har parlourn baffa aka kaisa bayan an masa izinin shiga, gaisawa sukayi cikin mutunci kamar sun san juna, ba boye boye dad ya masa bayanin abinda ya kawosa da kuma inda ya ganta, nan da nan baffa ya gane mami yake nufi dan Umm tana senior secondary school a lokacin, sosai baffa ya yaba da hankalinsa da tinaninsa na yadda ya fara tinkarar iyayenta kafin ita, saidai ya sanar masa shi baze aurar da yayansa ba sai sun gama degree kasancewarsa rikekken dan boko daya rike muka mai kala kala yake kuma matsayin ambassador na nigeria gabadaya, in yaga ze iya jiranta ze bashi dama su sasanta kansu, ba bata lokaci dad yace ya amince, ya kuma nemi a bashi izini iyayansa suzo suyi gaisawa idan sun sasanta da ita dan a tabbatar dagaske yake sannan asan da zamansa karta gama a mishi take over, ce masa baffa yayi wannan ba matsala bane in har sun sasanta kuma tana so, godiya ya shigayi sosai kamar ance masa an basa ne, fita baffa yayi yasa aka turo masa mami………

 Dad besha wahala gurin samun soyayyar mami ba kasancewarsa mutum gwanin iya tsara kalamai, ga kyau gashi kuma dan babban gida kamar yanda itama take dan lokacin mahaifinsa ne gwamnan kano shiyasa shima ya taso cike da san harkar siyasa, soyayya me karfi ce tashiga tsakaninsu cikin lokaci kankani har takai suna jin kamar a daura musu aure basai anjira ta gama ba saidai dole suyi hakuri ta gama………

A lokacin da mom tayi finding out suna soyayya ba karamin bakin ciki bane ya kamata saboda dad ya kai a kira shi saurayi na kece raini gashi kyakkyawa dan gwamna kuma, sai ta fara zuga mami akan dad batareda mami ta sani ba, haka zasuyita samun sabani su rasa me yake janyo hakan, da badan jajircewa da nacin dad ba da tini basu kai haka ba dan mami tasha cewa su rabu idan mom ta zugata cikin siyasa dama mom gwanar iya tsara magana ce tin suna yara saidai dad yaki yarda yace soyayyarsu mutu ka raba ne babu rabuwa…..

Haka rikici kala kala suka dinga shiga tsakanin mami da dad, shi kuma ya dage sai ita har Allah yasa sukayi graduating akasa aurensu nan da one month, ba karamin tashin hankali mom tashiga ba lokacin da akace itama saita fito da miji a aurar dasu tare, a kuma lokacin tagane lallai san dad take dagaske, tayi kokarin bin duk yanda zatabi ta rabasu amma Allah beyi ba har takai dad ya gane ya kuma fita sabgarta gabadaya, yayita cewa mami tayi hankula da kawarta ita kuma ta nuna mishi ko zancen bataso dan mom tafi karfin kawa a gurinta saidai yar uwa, kyaleta yayi ya cigaba da shirye shiryen aurensu, babu yanda mom ta iya hakan ya sata fito da wani a cikin samarinta badan tana so ba, lefe nagani na fada dad ya kawo hakan ba karamin tadawa mom hankali ya sakeyi ba dan wanda ta aura be kama ko kafar dad a arziki ba, haka aka sha shagulgulan biki na kece raina musamman ta bangarensu mami da dad sannan aka mika ko wacce dakinta…….. 

Sosai mamaki ya kama mami da dad ganin yanda suke balakin zaman lafiya kamar basu bane koda yaushe cikin fada lokacin courtship hakan kuma baya rasa nasaba da yanda dad yake nitsar da mami akan boye sirrin gidanta ma kowa har mom, haka mom zatayita bugar ruwan cikin mami akan zamanta da dad itako tayita ce mata Alhamdulillah daga nan ba kari, ganin kamar baza tayi nasara ba ya sata hakura tajira sanda opportunity ze zo mata dan ta riga taci alwashin raba su…..

Wani abu daya fara dagawa mom hankali shine rashin haihuwa, ace antafi shekara biyu da aure amma shiru kakeji, ita ko mami watansu tara da aure ta samu ciki, wata tara na zagayowa kuma ta haifo santalelan yaronta son kowa kin wanda ya rasa, ranar suna yaro yaci suna Saifuddeen…….. 

Haka yaro ya taso cikin gata da kulawar iyayensa, gashi da farin jini da shiga rai kowa yanaso ya daukeshi, gashi kuma kyakkyawa bubulbul dashi gwanin sha’awa…….. 

Saida Deen ya shekara biyar sannan Allah ya azurta su mom da samun haihuwa, ta haifo yar ta mace dataci sunan mahaifiyarta hameeda, sosai mami ke san hameeda har takai tace hameeda bata da wani miji sai Deen tin suna yara, haka deen da hamida suka taso cike da kaunar juna gwanin sha’awa….

Lokacin da deen ya kai shekara goma mom ta sake bullo da wani abu, taso tayi hakuri ta share kawai saidai zuciyarta ta kasa tinda shaidan ya riga ya buga mata ganga…. Wata kawa ta hadu da ita data zama musabbabin fara bin bokanta, aiki na farko da aka fara mata shine akan mahaifin hameeda ya zamana ko ce mishi tayi karya fita na sati haka ze zauna be fita ba, sosai taji dadin harkar ganin yanda take juya baban hameeda da komai nasa, abu na biyu data sa aka mata shine hargitsa zaman lafiyan dad da mami da ze kaisu ga rabuwa, shiru shiru taji mami batace mata koma ba, sai ta hau bugar ruwan cikinta akan babu abinda yake faruwa tsakaninta da dad ne, ita kuma mami tace babu, a lokacin kuma ta fara fuskantar chanji sosai daga gurin dad saidai sam bata bari abun ya dameta ba, in ya fara fada babu gaira ba dalili ko kulasa batayi……..

Abu ne ya isa mom ta sake komawa a mata sabon aiki akan su mami dan bataga alamun na farko yaci ba, ba bata lokaci aka sake wani aikin akansu dayafi wanchan sai ga mami tana kuka tana gayamata itafa ta kasa gane kan dad kwana biyunnan gabadaya ya chanja mata, magana kadan fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba gashi ko dansa be kyale ba, wani irin farin ciki mom taji a ranta kamar ta tashi ta taka rawa, saidai ta daure ta shiga bawa mami shawara cikin tausayawa akan tace ya saketa kawai, amsa mata kawai mami tayi badan zata iya ba……. 

Haka suka cigaba da zaman wahala na tsawon shekaru biyu batareda kowa ya sani ba in banda mom, har a lokacin kuma maganar saki bata taba shiga tsakaninsu ba…….

Ita kuma mom ji take kamar tayi hauka dan bata da wani buri illa taga sun rabu amma kamar mayu sunki rabuwa gashi sun riga sungama plan ita da kawarta kan yadda zatasa baban hameeda ya saketa ita kuma ta auri dad idan ta rabasu da mami……

Ganin lokaci na kara gudu ba wani maganar rabuwa tsakanin mami da dad yasa suka sake shawara ita da sabuwar kawarta, set up suka yiwa mami sukasa daddy ya kamata da wani a daki, nan rikici me karfi ya barke tsakanin mami da dad, kullum bashi da aiki sai ci mata mutunci akan ta kawo masa kwarto gida, ya dena cin abincinta ya dena kwana da ita amma kuma yaki sakinta, mami da taga she’s dying in silence tace wallahi sai ya saketa, shi kuma ya dage baze saketa ba saboda yasan karuwanci takeso taje tayi gwara suyita zama a haka  har su mutu dan shi ko aure baze iya karawa ba saboda gani yake kamar duka mata haka suke………..

Mami data rame ta lalace saboda damuwa taga bazata iya jurewa ba taje ta fadama iyayenta, ba bata lokaci baffa yasa a kirasa ya tarasu duka su biyun ya musu fada sosai, sannan yace dad ya saketa kawai saboda aure baya yiwuwa da zargi tinda tace ita bata aikata ba shi kuma yace da idonsa ya gani, sai cewa yayi shi yana sonta baze iya sakinta ba, baffa kuma yace be isaba dan baze yarda yarsa ta cigaba da zama cikin wahala ba da sunan aure, hakuri yayita basa wai ya hakura koda tayi din dagaske ya yafe mata kuma insha Allah ze gyara baze kara mata cin mutunci ba, ganin ya dage yasa baffa sake musu nasiha me ratsa jiki sannan yace su tashi su tafi………

Saidai inaa dad be chanja zani ba dukda yayi kokarin ganin yayi hakan amma kamar zugashi ake sai yaji ya kasa, haka mami ta sake jurewa na tsawon wani shekarar lokacin deen na sha uku ya kuma fara gane akwai sabani sosai tsakanin iyayensa……….

Wata rana mami taje gida dad yazo daukarsu mami bata fito ba ya shigo ya tasata a gaba su tafi, baffa ne ya fito daga part dinshi ze fita yaji irin munanan kalaman da dad ke jefar mom dashi, yi yayi kamar bejiba ya wuce, daga sama kawai dad yaji sammaci daga kotu washegari, shi da mami suka shirya suka tafi, suna zuwa suka tarar da baffa da mahaifiyar su mami a kotu suna zaune, a take aka sake tambayar mami abinda yake faruwa ta fada bata boye komai ba, aka tambayi dad shima ya tabbatar da hakan amma ya nemi a masa afuwa, nan iyayen mami sukace basusan zancen ba itama mami tace wallahi saiya saketa dama ta gaji, dad naji na gani badan ransa yazo ba ya mata saki daya yana kuka, tin a gurin baffa ya masa kashedi akan karya sake ya tako masa gidansa biko dan shi kuma ga dan shi chan yaje ya rike tinda ba yaro bane, haka suka tafi suka barsa a gurin yanaji kamar yayi hauka….

Mom bata taba farin ciki ba irin na ranar dukda ta nuna alhininta a fili saidai sam ba haka take a ranta ba, har wani dan celebration suka hada ita da sabuwar kawarta suka sha shagali abunsu……..

Bayan wata daya da sakin mom ta sake komawa gurin bokanta aka mata aiki akan mjinta da kuma dad, tin a ranar ta fara ganin aikin kuwa dan tana dawowa mahaifin hameeda ya bata takardarta, washegari tana tashi kuma taga missed call din dad….…

Nan tarayyarsu ta samo asali, dad ya rikice yace sai ita kodan ya rama abinda mami ta masa, ace ya kamata tana zina da wani a gadon aurensu amma ita zatace sai ya saketa bayan shida aka zalinta ya yarda ze zauna da ita a haka, da kyar ya daure ta gama idda sannan aka daura musu aure suka tare cike da begen juna, mami was so heartbroken da taji labarin auren Umm ce ta dinga tausarta akan kartace mata komai kawai ta rabu da ita kowa yayi da kyau zega da kyau sannan tayi kokarin gani mami da dad sun sasanta ana mutunci koda ba aure amma suka nuna mata basa so, haka mami ta rabu dasu tayi focusing on building kanta baffa kuma yayi supporting dinta sosai har ta kai matsayin da take kai a yau, maganar aure kuma tace ta shafeshi a babin rayuwarta………

Da farko deen yaso ya bawa mom matsala saboda yanada wayan da yake ganin bata kyauta ba na auren mahaifinsa a matsayinta na aminiyar mahaifiyarsa, sawa tayi shima a mayar dashi sai yanda tayi dashi, be koma yanda take so ba saidai ya zama kamar wani psychopath be damu da kowa ba har iyayensa, harkar gabansa kawai yake, shigowar fatima zainab rayuwarsa ne yasa ya fara sanin damuwa, kasancewar be saba ba yasa besan yanda ake bin abu a hankali ba shidai burinsa kawai ya illata duk wanda ya masa abu, sannan yafi rashin kula mami ma saboda lokacin ta bar abuja gashi dad yace karta sake ta kara tako masa gida bisa ga umarnin mom, ita kuma tayi hakane saboda sharadin da boka ya bata idan suka hadu su duka hudun ma’ana mami dad deen da ita toh asirin ya karye kuma zata haukace, amma dake rana dubu ta barawo rana daya tak ta mai kaya sai gashi ta manta ta biyo dad ko tinanin zasu iya haduwa gabadaya batayi ba…….

Tana gama bada labarin ta zube a kasa tana birgima, deen da jijiyoyin kansa suka firfito tsabar bakin ciki da takaici besan sanda ya dagota ya hau bubbugata da bango, fuzgota daga hannun deen dad yayi ya shiga dukanta yana kuka yana fadin;

    “Kin cucemu! Kin cuceni! Allah ya isa sakani na dake! Kin rabani da abinda iyalina abar kaunata! Kin cuceni!”…..

Fizgewa tayi daga hannun dad ta tashi tayi wani ihu ta fita a guje, binta deen yayi ya zare belt dinsa ya shiga zuga mata tana gudu yana binta, har a lokacin bata daina bada labarin wasu abubuwan da tayi daban ba, daga karshe ma saita fara kokarin cire kayanta alamun hauka ta kamata, sawa deen yayi aka bude kofa ya cigaba da zuga mata belt din harta fita daga gidan, tana fita tayi tsirara ta ruga a guje tana ihu tana kara bada labarin abinda ta aikata……….

     (Gareku masu bin bokaye da kuma mallamai; wallahi ku tuba tin yanzu dan babu yanda zaayi kuyi kyakkyawan karshe, inaso kusani kuma rana dubu ta barowa rana daya tak tame kaya amma rana dayan nan yafi tsawon ranakun dubun nan sau goma, sannan duk nisan jifa kasa ze dawo, kina ganin kamar komai yana tafiya yanda boka ya miki ko mallami toh wallahi wallahi asirinki ze tonu ko badade ko ba jima, Allah yasa mudace ya doramu akan tafarkin gsky)…………

        

      Dawowa ciki deen yayi lokacin mami ta bar parlorn cuz tana bukatar tayi digesting abinda ya faru yanzu so bazata iya saurarar dad dake neman afuwarta ba, Umm ce tabi bayanta amma ko kafin ta karasa mami ta rufe kofa, dawowa tayi daidai lokacin da deen ya shigo……

Abby ne ya taso ya dawo inda take kamar zeyi kuka yace;

     “Boddi na(kyakkyawata) dan Allah ki saurareni”….

Hannu ta daga masa da dakatar dashi da fadin;

    “Babu abinda zesa in saurareka inba ganin ya’ta nayi a kusa dani ba!!”…….

Gyada kai yayi yace;

     “Yanzu zansa a kawota ki ganta boddi!”…..

Bata ce komai ba ya kira securities dinsa yasa suje su tawo da baby tee da ammy yanzu!!”……

Back to top button