Ruwan Zuma Page 35 Hausa Novel
(35) Bayan Abul ya fakaici idon Mas’ud da yaran shagonsu sai ya fara d’aukan kud’i ba tare da sun gane ba. A ranar daya shirya gudu, ya d’auki jakarsa ta Laptop ya sanya kayansa kala uku a ciki da kud’in daya sata sannan suka tafi shago shi da Mas’ud kamar kullum. Mas’ud bai kawo komai a ranshi ba game da jakar Abul saboda ya san shi mayen Computer ne kuma yana fita da ita kullum. Lokacin sallar azahar yana kawowa ya bud’e Laptop d’in ya fara danne-danne mutanen gurin na tsokanarsa wai Computer Guru yana murmushi. Har suka yi alwala domin gabatar da sallar azahar shi yana zaune bai daina aikin da yake yi ba. Hakan yasa Mas’ud da sauran suka tafi suka barshi a kan in ya tashi ya rufe shagon su sun wuce masallaci. Sai daya tabbatar sun isa masallacin sannan ya bud’e jakarsa ya juye kaf cinikin da aka yi a ranar ya fita daga shagon a hankali kamar ba wanda yayi 6arna ba. Daga nan bai nufi tasha ba domin yasan zasu iya bin kadinshi su gane motar ina ya shiga. Babban titi na k’arshen gari ya nufa ya tsaya can motoci manya da k’anana na zuwa suna wuceshi ba tare da sun tsaya kamar yanda yake d’aga musu hannu ba. A nan ne ya kira Laila da sabuwar sim d’in daya saya ta d’auka yace, “Nine Abul. Kuma ina miki albishir da cewa na bar garin Kano da zama kwata-kwata har sai kin kashe aurenki da wannan matsiyacin yaron sannan zan dawo. Kar kusha wahalar nemana domin ba zaku ta6a sanin ina nayi ba.�? “Allah ubangiji ya shiryeka.�? Shine kad’ai abunda Laila ta samu fad’a ya kashe wayarsa. SIM card d’in ya cire ya karya sannan ya watsar a cikin ciyawin bakin hanyar. Daga nan ya kai awa biyu tsaye sannan da kyar ya samu wata Sharon da zata je Abuja ta tsaya aka d’aukeshi. A takure ya isa Abuja domin motar cike take da Lawashi da Albasa a bayan booth da kuma seat d’in baya. Seat d’in tsakiya ne kad’ai mai d’auke da mutane hud’u sai shi da Driver a gaban motar. Suna isa tasha ya d’auki jakarshi sannan ya sanya wata sabuwar Sim Card ya kira abokinsa Faisal d’an wani hamshak’in mai kud’i a nan Abuja. Mota zugegiya aka zo aka d’aukeshi da ita wanda Faisal na bayanta yana busa Shisha yana sauraron wak’ar Naira Marley. Suna ganin juna suka tafa kowannensu d’auke da murmushi domin wannan ne karo na farko da suka ta6a had’uwa. “Sai gaka a Abuja. I’m glad you come Man.�? Fad’in Faisal yana komawa cikin motar. Daga nan suka wuce gidansu Faisal a wata unguwar masu ji da kud’in Nigeria, gida ne babba wanda daga gani zaka gane na wani hamshak’in mai kud’i ne wanda baya jin zafin kasheta. Faisal d’a babba a gidan Cabin house aka gina masa a can lambun gidan wanda babu mai zuwa gurin sai shi da kuma wad’anda ya gayyata. A can aka sauk’e Abul wanda yake bin tsari da kyawun gurin. Living room ne babba guda d’aya sai d’akuna biyu da toilet guda d’aya dake tsakanin d’akunan. Furnitures d’in da suke ciki masu kyau da tsada wanda basu cika yawa a ba dalilin mai Cabin d’in baya son hayaniya a tsarin gurin zamansa. “You live here?�? Abul ya tambayeshi yana zama kan Sofa dake cikin falon. “Ina son zama a secluded area shiyasa Babana ya gina mini nan, sometimes na kan manta a cikin gari nake domin bishiyoyin da suke zagaye dani kan sa in d’auka a real forest nake. Bana son damuwa da hayaniya, bird chirps sun fi mini dad’in sauraro akan maganan mutane. Da fatan baka da surutu? Domin bazan shirya da kai ba.�? “No. Nima bana son yawan magana nafi son zama a gaban Computer like you.�? “Yeah.�? Da haka Faisal ya isa gurin wani cabinet dake falon ya d’auki wata wayar hannu ya nunawa Abul. “Duk abunda kake son ci ko kake buk’ata na rayuwa ka rubuta ka tura a nan za’a kawo maka a lokacin da kake so, zasu ajiye maka a bakin k’ofa domin na hanasu shigowa gurina in ba weekly cleaning ba. Ina da bak’uwa a d’akina, don’t disturb us.�? Da haka ya fara takawa ya isa bakin d’aya daga cikin rooms d’in kana ya juyo yace, “Next room is your as long as you want.�? Ya shige ciki. Haydar tashi yayi ya isa gurin da wayar take ya rubuta abunda yake so da time d’in da yake son a kawo mishi kana ya tura. D’aukan jakarshi yayi ya shiga d’akin da aka ce nashi ne, sai dai yana shiga ya fara jiyo muryoyin Faisal da budurwarsa a wani hali na intimacy wanda hakan ya takurashi nan take. Yana ajiye jakar bai ko tsaya k’arewa d’akin kallo ba ya fice cikin sauri saboda irin kalaman da suke amfani dashi ya girmi kwakwalwarshi. Minti sha biyar da haka yaji alamar an ajiye abu a bakin k’ofar ya tashi ya bud’e ya shigo da kwandon abincin. Kamar yanda ya fad’a haka aka masa chips da scrambled egg sai black coffee wanda babu cream babu sugar. Yana gama cin abincin ya tattara ya kai kitchen island da yake wani gefe a falon kamar kitchen. Bayan ya dawo ya zauna ya kunna Netflix yana kallo amma hankalinshi na kan Mamanshi wacce ya tabbatar yanzu tana cikin zullumi da kuma dana sanin auren da tayi. Kwafa yayi a zuciyarsa kuma murna yake yi da Allah ya had’ashi da Faisal a Dark Web d’insu har suka bayyanawa junansu suna da kuma inda suke, wanda ba’a cika hakan ba a duniyarsu. Yana zaune Faisal ya fito gefenshi wata yarinya ce da bazata wuce shekaru sha shida ba tana shafa k’irjinsa. Wata riga ce iya cinya a jikinta shara-shara da bata 6oye komai ba na jikinta. Kai tsaye gurin da wayar take suka yi Faisal na rubuta musu abunda suke buk’ata, Abul kuma daya lura da shigan yarinyar sai ya kawar da kanshi, a lokacin ne ya rage murnarsa domin da alama haka zai dinga ganin ‘yan matan Faisal and zasu takurashi. “Abul this is Beeba my girlfriend.�? Faisal ya fad’i hakan yana zama a sofa dake kallon Abul ita kuma Beeba ta hau cinyarshi tana shafa kanshi da kunnuwanshi. Abul da bai ta6a kallon hakan a zahiri ba sai ya tsorita zuciyarsa ta fara bugawa yayi saurin kawar da kanshi gefe yace, “Hey Beeba.�? Juyowa tayi ta masa kallon sama da k’asa sannan ta sanya yatsanta a bakinta tace, “Hey Bull.�? “It’s Abul not Bull.�? Faisal ya gyara mata yana sanya hannunshi cikin rigarta. “I prefer to call him that.�? Abul da yaji haushin had’ashi da tayi da Shanu sai ya tashi ya koma d’akin da aka bashi domin ya lura kamar basu gama abunda suke yi ba. Sai daya tabbatar sun fita daga gidan sannan ya fito ya shiga band’aki yayi wanka da alwala kana ya koma yayi sallah. Yana zaune a kan sallayar yaji yana buk’atar abunda zai kawar da hankalinshi. Jakarsa ya jawo ya fara bincike ko zai samu sauran kwayarsa, yana binciken ya samu wata kwayar da sau d’aya Micheal ya ta6a bashi yasha saboda k’arfinta da tsadarta. Waye ya iya sayan mai yawa haka har ya sanya mishi a cikin jakarsa? Ya gama kaf tunaninshi bai tuna lokacin daya saya ko aka bashi ba. Ganin zai 6ata lokacinsa yasa ya d’auki biyu ya harba kana ya kawar da duk abunda zai iya yiwa kanshi illa dashi ya kwanta a kan gado yana jiran ta fara aikinta ta kaishi duniyar da babu damuwa sai farin ciki da jindad’i. Bai iya komai ba bayan ta fara wargaza masa kwakwalwa illa bud’e bakinsa da yake yi yana rufewa, can kuma sai ya rufe idanunsa sai ya bud’e yana murmushin jindadi shi kad’ai. Wani lokaci kuma zai gwada tashi amma daya duba k’arkashin gadonsa sai yaga rami ne mai duhu babu gurin takawa. Hakan yasa yayi kwanciyarsa akan gadon har bacci ya kwasheshi mai cike da mafarkai iri daban-daban. Haka rayuwarsa a gidan Faisal ta kasance, da safe kafin su tashi zai rigasu tashi yayi amfani da band’aki ya kuma yi order d’in abinci a kawo masa yaci. Daga nan kuma zai shige d’akinsa yana danna Laptop d’insa inda yake samun labarin duk wani motsi na uwarsa da mijinta. Yamma tana yi zai sha kwayarsa yayi mankas ya kwanta a kan gado yana zaro harshensa waje har bacci ya d’aukeshi. Faisal bai damu da sanin ina Abul yake ba domin shima harkar gabansa kawai yake yi da Beeba budurwarsa. Idan kuma suka had’u falo in dai ba wata babbar magana ba basa kula juna. Beeba na yawan kallon Abul tana kuma jan hankalinsa idan Faisal baya ganinta, Abul daya lura ta fara seducing d’inshi sai yayi saurin gama abunda yake yi ya bar musu falon. Yau satinsa biyu a gidan, a nan ne kuma kwayarsa mai kwantar masa da hankali da sakashi nishad’i ta k’are. Kud’insa da yake dashi ya fitar ya fito falo ya samu Faisal da Beeba a wani hali da bai so gani ba. Ya kai seconds goma yana kallonsu sannan ya kira sunan Faisal ya juyo. “What bro?�? Faisal ya amsa masa ba tare daya daina abunda yake yi ba. “Ina son fita supplies d’ina sun k’are.�? “Go to my Driver.�? Daga nan ya maida hankalinshi kan abunda yake yi ya rufe idanunsa yana cije fuska. Abul hanyar k’ofa yayi amma bai san dalilin da yasa ya juyo ba hankalinshi na kan Beeba dake k’asan Faisal tana aiko masa da kallo mai cike da fassara iri-iri. Shi ba gwanki bane koda yana shan kwaya yana buk’atar mace a rayuwarsa, ganinsu da yayi kuma cikin wannan halin yasa yaji shima yana buk’atar hakan. Sai dai wa zai samu? A yanzu daya 6ata rayuwarsa ma baya buk’atar k’arin yin zina. Zai sha kwaya amma ba zai yi zina ba, da haka ya isa gurin da motocin Faisal suke Driver ya d’aukeshi suka fita daga gidan. Babu inda bai zaga ba amma bai samu inda ake sayar da kwaya ba, Pharmacy babba ko k’arami sun hanashi magani sunce sai da prescription. Ya fito a wani Chemist na shida da suka je ne wani ya biyoshi ya masa kwatancen shagon Imaa dake can kwararon unguwar ‘yan iskan garin marasa galihu. Da k’afarshi ya k’arasa shagon domin Driver yace motar baza ta iya shiga unguwar ba, a bakin shagon ya samu samari hud’u zaune suna busa sigari, daka gansu zaka san suna shan wahalar rayuwa. Duk abunda yake buk’ata ya saya a shagon Imaa na murna domin yayi ciniki sosai ba kad’an ba. Sai dai bai samu kwayarsa da yake sha tun zuwanshi Abuja ba. Bayan ya fito ya bawa samarin kud’i wanda ciki har da Banney dake binshi da kallo yana tuna gatanshi na da kamar Abul d’in. Godiya suka masa kana ya koma mota suka tafi gida. Abinci ya fara aikawa a kawo mishi yaci sannan ya har6a kwayoyinsa ya kwanta yana jiran ta fara aiki ta sakashi bacci. Sai dai wannan karon jinshi yayi garau babu alamun bacci a idanunsa balle nishad’i nishad’in da yake ji idan yasha waccar kwayar, wannan hauka yaji yake son yi ya wargaza komai daya shiga gabanshi. Yana zaune akan gadonsa ya fara wurgi da duk abunda hannunsa ta kama, yana tsaka da haka Beeba ta shigo d’akinsa tsirararta tana masa murmushi. Rufe k’ofar tayi ta iso gurinshi tare da zama akan cinyarsa tana tura masa k’irjinta. Hakan yasa hankalinsa ya k’ara barin jikinshi ya biye mata tana k’ok’arin rabashi da kayan jikinshi. Sai dai bata kai ga cimma burinta ba Faisal ya band’ako k’ofar ya ja gashin kanta ya had’ata da gini goshinta ya fara zubar da jini, Abul kuma daya fara gane inda hankalinsa yake yaji an naushi hancinsa ya gigice ya rasa gane a ina yake. Dukan hauka Faisal ya yiwa Abul ba tare daya ce komai ba sai furzar da iska da yake yi ta bakinshi da hancinsa. Jina-jina ya yiwa Abul sannan ya jawo kwalar rigarsa ya fitar dashi k’ofar Cabin d’in ya jefar. Komawa ciki yayi ya d’auki wayarsa ya kira wani mutum wanda a cikin minti uku ya iso yace, “Ka kaishi d’akin karnuka, kar ka bari su kasheshi amma ka tabbata sun masa illar da har abada ya gani sai yasan yaci amanata.�? Yana fad’in hakan ya koma d’akin Abul ya samu Beeba na tsugunne a gurin tana kuka, gashinta ya k’ara kamowa ya kaita zuwa d’akinsu yana cewa, “You want to fuck with him? Then fuck yourself with this.�? Ya nuna mata kwalbar barasa dake gefenta. Hak’uri ta fara bashi ya girgiza kanshi yana mai zama a kan kujerar dake d’akin yana fitar da numfashi cikin 6acin rai. “Na sayeki gurin ubanki da kud’ina don ki zama mallakina ni d’aya zuwa lokacin da zan gaji dake in freeing d’inki. But you want to be a real bad bitch kinyi seducing my only friend dana ta6a kawowa gidana. You ruined him for me, nima kuma zan lalataki yanda babu wani d’a namiji da zai k’ara morarki, you ungrateful bitch.�? Fad’in abunda ya faru da Beeba ba’a magananshi domin sai daya tabbatar yayi ruining d’inta sannan yasa aka fitar da ita daga gidan aka je aka watsar da ita a cikin jeji wanda zata yi kwana biyu a ciki bata fito kan titi ba, that’s is in tayi rai kenan. Faisal ya cika sunansa ‘Sadistic�? wanda shine Handle d’insa a Dark Web. Kwanan Abul biyu ana turashi d’akin karnuka, sai sunyi kamar zasu kasheshi sai a fitar dashi a barshi a waje yana ihu yana kukan raunin da suka ji mishi, wanda har sun karya mishi k’afarshi baya takata. A kwana na biyun Faisal ya zo gurin da ake mishi horon ya sameshi a waje tare da fresh wounds wanda karnukan suka mishi. Tsugunnawa yayi a gabanshi kana ya zare sunglasses d’in idanunsa ya dubi Abul wanda idanunsa suka kumbura baya iya bud’esu da kyau. “I liked you Man, but sai ka nemi budurwata bayan ni mutum ne da bana sharing sex doll d’ina. I still like you shiyasa zan barka da rai but waccar tsinanniyar ta mutu babu ita babu k’ara nanewa wani namijin. Na san ita tayi seducing d’inka domin ina ganin lokacin data shiga d’akina bayan tayi tunanin na fita daga gidan ne, I have cctv cameras da babu mai ganinsu sai ni d’aya. Na d’auka ba zaka biye mata ba, na d’auka you’ll push her away ashe kaima jiranta kake yi kana muradin kasancewa da ita. Shiyasa ban ta6a trusting kowa ba sai kai, kuma you showed me yarda da mutane gangancine. You’ll live but ba yanda kake so ba. Danny ka masa allura ka kaishi can k’arshen gari ka jefar wannan shine alfarma da kuma tausayawa da zan iya maka.�? Abul dake durk’ushe a gurin ya kasa koda magana saboda irin ciwo da zogin da jikinshi ke mishi. Da haka Faisal ya mik’e ya saka glasses d’insa yana cewa, “Zan je Sex doll hunting wish me luck.�? Abul na jin k’arar sawayensa har ya shiga mota suka fita daga gidan. Danny da zai mishi alluran sai da ya naushi k’afarsa wacce ta karye sannan yana dariyar mugunta ya danna masa allurar wacce a take ta sakashi fita daga hayyacinsa gaba d’aya. A wata pick up da Faisal ke 6adda kama in yana son fita shi d’aya suka sakashi, sannan suka nemi abun rufe mota suka d’aura a kanshi suka fita daga gidan. Driver dake tuk’a motar shi yaji tausayin Abul ya fasa kaishi bayan gari, don haka ya kaishi unguwar daya ta6a kawoshi sayan magani wato gurin su Imaa. Duk da cewa ba tare suka je ba amma ya gane gurin da zai kaishi wanann karon har k’ofar shagon Imaa yayi parking kana ya isa gurinsu ya musu magana. Banney da bai manta alherin da Abul ya musu ba ya d’auki nauyin kula dashi bayan ya nemi kud’i gurin Drivern. Babu musu ya ciro kud’i mai yawa ya bawa Banney yana cewa, “Ban san meyasa nake tausayinsa ba, but take care of him kuma kace ya koma gidan iyayensa inji ni.�? Yana fad’in hakan ya koma mota da taimakonsu suka ciro Abul wanda yake kamar matacce. “Wooo ya zaka kawo mana gawa? So kake ka d’aura mana sharrin kisa?�? Fad’in Imaa yana fitowa daga shagonshi bayan yaga abun nasu bana k’arewa bane. “He is not dead but unconscious.�? Fad’in Banney yana sauk’ar da Abul kan simintin bakin shagon Imaa. “Ku d’age mini wannan abun daga bakin shagona kafin ni in k’arisashi.�? Imaa yayi maganar cikin zafin rai. Banney yasa baki sauran suka taimaka mishi suka d’auki Abul zuwa shagon da yake kwana suka yasar dashi a nan suka yi tafiyarsu suna cewa, “Idan ya mutu a gurinka babu ruwanmu.�? Sai da suka tafi sannan ya 6arka kayan jikin Abul ya fara duba meya sameshi. Duk jikinshi ciwuka ne wanda wasu sunyi zurfin da suna buk’atar stitches yayinda wani gurin kuma fatar ta d’aye sai nama kad’ai ake gani. “You fought with a Lion Nigga?�? Banney ya tambayi unconscious Abul. Fita yayi daga shagon ya isa shagon Imaa yana fad’a masa abubuwan da yake so don treating Abul. “Kud’in double zaka bayar don baka da prescribtion.�? Fad’in Imaa bayan ya gama kawo masa abunda yake buk’ata. “Don’t do this Imaa, mutumin nan ya maka alheri a baya karka mishi haka a lokacin da yake buk’atar taimakonka.�? “I don’t give a damn. Ka bada kud’i ko kuma kaje ka nemi wani gurin.�? Banney yasan idan ba shagon Imaa ba babu inda zai je a bashi abunda yake buk’ata. Don haka dolenshi ya kirga kud’in da Drivern ya bashi ya bawa Imaa nashi. A nan ya rage Saura dubu biyar cikin abunda aka bashi wanda yake zaton dubu sha biyar ne duka. Yana komawa shagon da Abul yake kwance ya samu ya farka yana hawaye kawai baya iya ko motsi. “Ka farka kenan? Gashi bani da alluran da zan maka hankalinki ya 6ace saboda abunda zan maka will hurt like a bitch.�? Banney da kanshi ya wankewa Abul ciwokanshi ya saka antiseptic kana yayi stiching wand’anda suke bukatar hakan. Duk abunda ake yi Abul in banda ihu babu abunda yake yi amma ya kasa motsa jikinshi dalilin allurar da aka mishi bata gama sakeshi ba. A cikin unguwar tasu Banney ya kira wani dattijo mai d’aurin kafa ya d’aurewa Abul kafarshi wacce yace gocewa tayi. Da sauran kud’in yake ciyar dasu har Abul ya fara tashi da kanshi yana zuwa bola inda suke Bahaya ba kamar daa da yake yi a leda Banney na kaiwa ya jefar ba. Satinsa biyu ya warware sai dai har lokacin yana d’ingisa k’afarsa wacce mai gyaran yace zai yi wuya ta dawo daidai in ba Bature ne ya gyara ba. Ko da ya samu lafiya sai ya koma harkar shaye-shayensa inda yake zuwa kasuwa da Banney suyi kwadago sannan su samu na shan kayen maye, wanda sun gwammace su sha kwaya akan suci abinci. Wannan shine tak’aitaccen tarihin Abul a Abuja bayan ya tsira da rayuwarsa da kyar.
Mum Fateey 👌


