Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 10

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

Daga alƙalamin Boss Bature writer of Abban sojoji

E10

Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon a zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan.

Yana cikin wannan halin ha’ula’in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, “Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku.” Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face Æ´arsa É—aya tilo da ya mallaka wato Angel.

A matuÆ™ar ruÉ—e ya miÆ™e, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key É—in motarsa ya É—auko saboda tsabar ruÉ—u wardrobe ya dosa zai buÉ—e a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin Æ™ofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom É—insa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiÉ—ime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko’ina ba sai É—akin Angel, bugu É—aya ya yi ma Æ™ofar ta buÉ—e, ko’ina duhu, kunna hasken É—akin ya yi, nan take haske ya gauraye ko’ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke Æ™unshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya Æ™arasa shiga É—akin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, “Angel, Angle my daughter!Azeezaty!” Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaÉ—arsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, Sam baya a cikin hayyacin shi, balle ya iya tunawa da aneelerh dake a cikin mawuyacin halin na rashin dawowar mijin ta gida,

kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, É—aya daga cikinsu ya buÉ—e Æ™irar Range Rover, back seat ya buÉ—e ya kwantar da Angel tukunna ya buÉ—e diver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buÉ—e gate É—in, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danÆ™ara-danÆ™aran motoci gudan shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka daga gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba Æ™aramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror É—in motar, hakan yasa shi Æ™ara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La’ila’ha’illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheÆ™ar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.

A ruÉ—e take furta,”Daddy…What’s happening, where are u going in this darkness night?”

Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.

“Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba.” Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheÆ™ar kuka ta kuma cewa, “Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaÉ—aya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daÉ—i. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.

Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faÉ—a wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruÉ—e ya yi parking É—in motar ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya É—auko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yavyi cikin dajin da ita yayin da take sa6e avsaman kafaÉ—arshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare davya ankara ba, ya É—aura kafarsa saman wani Æ™arfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin Æ™asa, kaifinsa tamkar na wuÆ™a, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin Æ™afar ya 6ulo ta sama, wani irin raÉ—aÉ—in azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke Æ™afarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, “Innalallahi wa’inna ilaihir raji’un.” Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, “Dad let’s go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?” Ta yi tambayar still tana shassheÆ™ar kuka.

Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, “Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne.” Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, “Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji.” Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,

A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin davya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan dacta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.

Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa.

Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faÉ—i a mace.

A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.

Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.

Guntun tsaki É—aya daga cikinsu ya ja, “Mala’ika ya riga mu É—aukar ransa, ba haka na so ba.”

Na gefensa ya ce, “Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir.”

Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka É—aure fuskokinsu. ÆŠaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan É—aya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, “MiÆ™o mini galon É—in fetur tare da lighter.” A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.

“Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abuvne mai sauÆ™i.” Bai kai Æ™arshen maganar ba, aka miÆ™o masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur É—in a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.
Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.

Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus.

In the Morning

Hasken rana ne ya haske fuskarta, sakamakon windown bedroom ɗinta da ta bari a buɗe, dogon numfashi ta ja tare da buɗe kumburarrun idanuwanta waɗanda suka yi luhu-luhu da su sun ƙanƙance saboda kukan da ta sha a daren Jiya. Kwance take a saman gadonsu, jikinta duk ya yi nauyi sam ta kasa motsawa, gefe da gefe na gadon ta kalla don ta ga ko Uzair ya dawo. Ras ta ji gabanta ya faɗi ganin still bai dawo gidan ba, hankali a tashe ta yunƙura ta miƙe zaune tare da wurga idanuwanta kan agogon bangon, ƙarfe tara na safe ko sallar Asubahi ba ta samu ta yi ba, saboda nauyin barcin da ya ɗauke ta.

Siraran hawaye ne suka gangaro daga cikin kwarmin idanuwanta har izuwa saman kuncinta, masu É—umi, harshenta ta sanya ta É—an lashi gefen bakinta inda ruwan hawayen ya gifta.

DaÆ™yar ta samu ta lalla6a ta sauko daga saman gadon, still riga da wandon jiya ne a jikinta, kanta babu mayafi, sumar kanta ce da ta zubo mata ta ko’ina ta yamutse.

A hankali take tafiya harta shige toilet, after some minutes ta fito daga cikin toilet É—inta, da alama alwala ta yi, lemar ruwa ce a fuskarta da hannayenta.

Cikin wani irin yanayi na jin faduwar gaba, da tsinkewar zuciya, ta nufi closet É—in kayan su, buÉ—ewa ta yi tare da zura hannu ta É—auki hijab É—inta, ta sanya a jikinta.

Saman dardumar dake shimfiÉ—e ta tsaya, a tsanake ta kabbara sallah, cikin nutsuwa ta soma yin ibadarta.

Bayan ta kammala, zama tayi saman dardumar tare da É—aga hannayenta Cikin harshen larabci ta soma yin addu’o’inta daga Æ™arshe ta rushe da matsanancin kuka tana faÉ—in. “Ya Allah Ka dawo mun da mijina lafiya,Ya Allah ka karemun shi aduk inda yake! inaji araina kamar wani mummunan abu ne ya faru da shi, Uzair bai ta6a tafiya batare da sanina ba. Amma jiya ya tafi ya barni in the midnight without my knowledge,” Sosai take yin kukan ta jima, kafin ta yanke shawarar zuwa Wurin taj donta tambaye shi idan Sunyi waya da Uzair.”

Miƙewa tayi da sauri, ta fito daga Cikin bedroom ɗinta, ta nufi hanyar fita daga falon, a bakin gate ta samu maigadin gidanta zaune saman benci yana sauraron radio.

Tunda ya hango ta ya yi saurin ajiye radio É—in saman bencin ya mike ya tunkare ta, “Barka da safiya hajiya, kun tashi lafiya.”Ba ta amsa mashi sallamarshi ba, saboda ba ta acikin natsuwarta,

“Inaso zanje wurin taj ne, may be sunyi waya da uzair, wlh nadamu sosai nakasa samun natsuwa baba, inaji kamar wani abu ya faru da shi,” Tana magana hawaye na fita daga cikin idanuwanta.

Tsananin tausayinta ya kama baba maigadi, tunda yake bai ta6a ganin hawayen Aneelerh ba, sai a daren jiya da kuma yau, ya lura da tashin hankalin dake akan fuskarta.

Cikin sanyin murya yace”Kiyi haÆ™uri ki kwantar da hankalinki, in sha Allah uzair yana cikin Æ™oshin lafiya, babu abin da zai faru da shi.”

Gyaɗa mashi kai ta yi tare da wuce shi ta nufi gate ɗin, Hannu tasa ta buɗe ƙopar jikin shi ta fuce daga cikin gidan.

Girgiza kai maigadi ya yi ji yake da a ce yana da halin da zai iya taimakon Aneelerh a yau daya taimaketa, abin da ciwo ka ga mutumin daya saba kyautata maka a cikin wani ƙunci na rayuwa kuma baka da yadda za ka iya taimakon shi, komawa yayi jiki asanyaye ya zauna saman bencin.

Bayan fitar Aneelerh, kai tsaye ta nufi gidan Taj dake a jikin gidansu, tun abakin gate ta hango maigadin gidanshi a tsaye ya jingina bayan shi jikin gate É—in, fuskar shi duk a harmutse da alamun damuwa atattare da shi, hakanan taji gabanta yayi wani irin mugun bugu ras!

Ƙarasawa inda yake tsaye tayi muryarta da fargaba atattare da ita ta ce, “Assalamu alaikum”

Tunkan takai Æ™arshen maganar taga ya É—an firgita, sai daya kalleta tukunna YaÉ—an saki fuskarshi yace”wa’alaikum salam, malama Aneelerh, in ce ko lafiya?”

Hawaye ne suka sake wanke fuskarta, cikin shessheÆ™ar kuka ta ce, “Har yanzu uzair bai dawo ba, yanzu ma zuwa nayi wurin taj, don inji idan ya kira shi awaya,” Tana kai Æ™arshen maganarta baba maigadi ya ce, “Innallahi Wa’inna Ilaihir raji’un!”

A ruÉ—e ta ce, “Baba lafiya?” Cikin tashin hankali ya ce, “Æ´ar nan tun jiya na gaza samun kwanciya hankali, ko runtsawa ban yi ba, saboda damuwa, jiya bayan kin zo neman Taj, kin tafi na shiga daga Cikin É—akina na kwanta, har bacci na fara bacci sama sama, can cikin dare wuraren Æ™arfe É—aya da rabi, ina kwance na ji fitar mota daga cikin gidan nan. A firgice na farka na fito daga É—akina, koda na fito naga gate a wangale, na leÆ™e banga komai ba, na dawo na duba naga babu motar taj da yake yawan fita da ita, a nan na gane cewa shine ya fita cikin motarshi.”

Tunda ya soma magana Aneelerh ta dafe ƙirjinta da tafin hannunta, ta zazzare ido tana kallon shi,

“Na yi mamakin ina Taj ya tafi batare daya sanar dani ba! domin kuwa tunda nake aiki a Æ™arkashin shi bai ta6a lekawa koda Æ™ofar gida batare da sanina ba, amma sai gashi jiya tsakar dare ya fuce, kuma abun da ya É—aure mun kai, ba shi kaÉ—ai ya tafi ba. Hada ANGEL!” A gigice Aneelerh ta shiga ambaton Innallahi Wa’inna Ilahir raji’in! Na shiga Uku! Wai meke faruwa ne? Wayyo Allahna!” GabaÉ—aya ta bi ta ruÉ—e, shi kan shi baba maigadi da ya sanar mata, sai da yayi danasani ganin yadda ta daura hannayenta a saman kanta tana zabga salati.

Juyawa tayi da gudun gaske Ta koma Cikin gidanta, A lokacin malam Garba maigadinta Yana zaune saman bencin yaga shigowarta a guje, har yana tambayarta lafiya, amma bata saurare shi ba.

Hankalinshi ya ƙi kwanciya, Miƙewa ya yi da nufin yaje su yi magana da tajo,yana ƙokarin fita daga cikin gidan, baba maigadin gidan Tajo, ya tura kofar gate ɗin, suka yi kicibus da juna.

“Wai meke faruwane É—an ladi”malam garbane yayi mashi tambayar fuskarshi a yamutse.

Baba maigadi ya ce, “Tun É—azu naso in zo mu yi magana. Amma damuwa ta hana ni, lamarin dai babu daÉ—in ji.” Nan ya kwashe duk abin da ya faru na tafiyar Tajo tsakar dare ya sanar da shi.”

Malam Garba ya hauyin sallallami, hankalinshi duk ya tashi a rude ya ce, “Indai kuwa haka ne akwai matsala. Ya kamata a sanar ma Ƴan sanda don a san abin yi tun kafin lokaci ya Æ™ure mana”!!

Jinjina kai baba maigadi ya yi” ni ma abun da nake tunani kenan, amma mu É—an Æ™ara jira kaÉ—an zuwa anjima”

“Shikenan zan koma bakin aikina, zuwa anjima idan ba wani labari game dasu sai muje police station É—in” a cewar É—an ladi, daga haka suka yi sallama da juna. Ya koma gidan da sauri don ya barshi a buÉ—e bakowa

Aneelerh kuwa bayan shigarta Cikin gidan. Afujajen ta nufi bedroom É—inta ta shige, jikinta na kerma ta É—auki wayarta dake ajiye saman bedside drawer,

Call logs ta shiga ta dannawa numbar da tayi saving da Abie kira,Tana fara Ringing, Aka É—aga wayar, muryar babban mutuncine mai cike da kamala Ta karade kunnuwanta, “Assslamu Alaikum daughter…” Tun kafin ya kai Æ™arshen maganar, Aneelerh ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita…”

Muryar Abie a ruÉ—e ya shiga kwala mata kira.” Aneelerh lafiya kike kuka meya faru? Waya ta6a mun ke? ki buÉ—e baki ki yi mun magana!”

Sai da ta yi kukan mai isarta, sannan ta soma magana cikin shessheÆ™ar kuka”a…Abie..Uzair da Taj..” katse ta ya yi da cewa.”me ya faru dasu? Wani ya rasu ne’
“A’a, tun daren jiya Uzair ya bar gida wuraren Æ™arfe tara, shi kuma Taj ya bar gidansa karfe É—aya da rabi na dare, kuma ya tafi tare da Angel. Babu wanda yasan meya faru dasu, kuma dukansu layinkan wayoyinsu akashe, Abie ina cikin matsanancin tashin hankali.”

Lamarin ya girgiza abie sosai,”
Muryarshi cikin sigar lallashi ya ce, “ki kwantar da hankalin ki aneelerh, In sha Allah babu abun da ya faru da su, yanzu zan yi waya da uncle É—inki, ki É—an Æ™ara haÆ™uri.” Cikin shessheÆ™ar kuka ta ce”To Daddy, saina jika “ya ce” ki daure ki ci abinci, na san ba ki ci komai ba” Amsa mashi ta yi da to kafin suka yi sallama ta kashe wayar. Saman gado ta koma ta zauna zugudun cikin zullumi, salla kadai ke tada ta.

Wuraren Æ™arfe huÉ—u na marece, tana kwance magashiyan fuskarta ta kumbura tayi suntum, tunda tayi sallar la’asar bata cire hijabin jikinta ba,

jiniyar motor Æ´an sanda tajiyo daga waje Wii! wiii! ras! taji gabanta ya faÉ—i, fargabarta kada ace gawar Uzair kota taj suka kawo Cikin gidan,

A hanzarce ta miƙe, da gudu ta fito daga cikin bedroom tana sauko ƙafarta cikin falon, adai dai wannan Lokacin mahaifinta Alhaji Muhammad falgore ya doko sallama, Yana sanye Cikin shiga ta alfarma, Shaddace fara tass taji guga, tare da malun malun, kanshi Na sanye Cikin hula, Bayan shi kuma Ƴan sanda ne su huɗu sanye cikin kakin su, ɗaya daga Cikinsu Uncle dinta ne kaninta mahaifinta me ruƙe da muƙamin dco(Divisional Crime Officer),Atare dashi akwai Ic (inspector crime) sai kuma Ipo(Investigation Police Officers) Su biyu ne ɗaya mace ɗaya Namiji masu tsayi da jiki ba laifi a launin fata baƙake ne,

Zuba masu ido aneelerh tayi tana kallonsu batare da kiftawa ba, tasan aikin mahaifinta ne, mutunne mai É—aukar abu da mahimmanci babu wasa a lamarinshi, Sam ba ta yi tsammanin zai yi report din case din wurin Æ´an sanda ba, Sai gashi É—ungurugum ya taho dasu Gidan,

Ganin ta yi tsaye tana kallonsu yasa Shi yi mata gyaran murya yace”Daughter Kece kika koma haka”? jin haka yasa ta nufe shi da sauri, tunkafin ta Æ™araso ya buÉ—e mata hannayen shi ta faÉ—a a kirjin shi, ta fashe ma shi da kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Hannu yasa yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kafin ya kalli uncle din nata yace dashi Bismillah su zauna”wuri suka samu kowa ya zauna saman sofa, Bayan ya raba jikinshi daga na aneelerh yace itama ta zauna, atare dashi suka zauna,

Uncle Bash Æ™usa yace”Aneelerh Why tun daren jiya daya fita baki sanar damu ba”?

Cikin shessheÆ™ar tace”Ae nayi tunanin zai dawo kafin da safe”

Jinjina kai yayi”okey, yanzu ki natsu ki faÉ—a mana taya akai yabar gidan without your knowledge”?

Ƙoƙarin buɗe baki tayi donta kora masu jawabi kamar yadda suka buƙata, nan take Wani irin yunƙurin amai yazo mata, da sauri ta miƙe daga saman sofa din ta watsa aguje zuwa bedroom ɗinta,

Dco ya kalli Ramlat Jami’ar binciken da suka zo da ita yace da ita tabi bayan aneelerh, amsa mashi tayi da Okey sir, Kafin ta miÆ™e ta bi bayan aneelerh cikin bedroom É—inta,

Tana shiga tajiyo Sautin ƙaƙarin aman da aneelerh keyi acikin toilet, kaitsaye ta taka izuwa cikin toilet ɗin, Agaban Sink ta samu aneelerh tana ta kwara amai tamkar ƴar hanjin cikinta zasu fito waje,

Ƙarasawa tayi har zuwa bayanta, ta sanya hannunta tana ɗan bubbuga bayanta, Tana yi mata sannu,

Bayan ta kammala yin aman, Ramlat ta kunna mata fanfo, ta wanke bakinta tass, Takai hannu jikin tissue holder ta yago kaɗan ta miƙa ma aneelerh ta goge mouth ɗinta, daga haka ta ruƙo hannunta suka fito daga Cikin toilet ɗinta
“Sorry dear ki kwantar da hankalinki, in sha Allah we will try our very best wurin ganin mun gano inda mijinki ya ke,”acewar Jami’ar binciken,

Aneelerh dake ta faman fitar da numfashi mai É—umi tace”Bana jin daÉ—in jikina, tun jiya banci komai ba, kuma bana jin zan iya cin wani abu,”

Ramlat tace”Ki daure kici, lafiyar ki muke buÆ™ata, domin kuwa idan ba lafiya atare dake taya zamu iya samun haÉ—in kanki wurin yin investigation É—inmu”?

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

(Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i layina 08103884440, Kurkukun ƙaddara Book one free ne,

Yawan Likes da comment yawan update.

Back to top button