Gargadar So Chapter 34 By M Shakur
Shiga cikin hospital din Baban Yaseer yayi anan reception yaga Baba zaune dasauri yayi wajenshi adan rude yace “Baba” dasauri Baba yajuyo jin muryan Baban Yaseer yace “na’am Aliyu harkazo? Ga dakin nan likitoci na ciki cewa sukai na fito, ina Ni’ima”? Boye komi yayi yace “tana asibiti, nariga na gayamata zatazo da zaran tasami chance” Baba yace “Allah sarki Ni’ima nasan tashiga cikin tashin hankali” Baban Yaseer yace “Baba an ina tayi hatsarin”? Tagumi Baba yayi ahankali yace “wlh bansani ba ko inda motanta yake ma bansani ba ta lafiyanta nake yanzu, kwananta biyu batada lafiya tun ranan litinin da yamma, yauma cewa tayı bari taje asibitin su Ni’ima adubata saidai aka kira su Ammi wai me waya tayi hatsari nikuma suka kirani su Ammin suka sanar dani” anatse Baban Yaseer yace “kada kadamu Baba zan kira wani Abokina dake aiki da road safety naji idan zan sami any details na hatsarin da inda motarta yake” Baba yasauke ijiyan zuciya yace “tom shikenan” Baban Yaseer yadaga wayanshi yakira yadan matsa daga inda Baba yake kusan 20min yayi sannan yadawo yace “Baba ance motoci biyar ta deba ta hada da trailer amman Alhamdulillah babu any casualty babu wanda yarasu saidai sunji ciwo, ance wanda yakawota asibiti yasa agent ne ko PA wani dai nasa yasaka yabiya duka masu motocin har trailer kudin gyara motan su da kudin zuwa asibiti” Baba yakama baki da mamaki yace “iyye awannan zamanin abiya kalan kudin nan? Wannan bawan Allah akwai kyan zuciya da imani dakuma adalci da taimako” Baban Yaseer yace “ba shakka, kowaye gaskiya yayi kokari Allah sakamai da Alhairi”.Duk suna zauna awajen dan an hanasu shiga dakinta har around 12 na rana saiga Ammi tashigo reception din tareda Ramla dake goye da katuwar jaka abayanta dukansu idanunsu ja, Baba na ganinta yashiga kokarin mikewa hakama Baban Yaseer Ammi ta taho wajen dasauri Baba yayi wajenta hankalin Ammi atashe tace “ina Hawwan Malam? Ina Hawwa na? Ina tak….” Sai kuka kaman ba Baba ba yace “ya isa ya isa, gatachan adaki ance kar adameta kar a shiga saita farka, zauna, Ramla kema zauna” ahankali Baban Yaseer yace “ina yini Ammi” gyadamai kai tayi tana goge fuskanta da bakin hijabi tace “lafiya lau Aliyu sannu, bazakaje aiki ba ka zauna anan” adan hankali yace “bari mugani zuwa ta farka yanzu banda natsuwan yin aiki” ijiyan zuciya Ammi tasauke wlh har ranta batason zamanshi anan, cikeda hikima tace “to dan Allah tayani kai Ramla gida ta ijiye kayanmu tadafo wani abu takawo incase Hawwa ta tashi tanason abinci, Ramla dakin Antyn ku zaki ijiye kayanmu” Dasauri Baba yace “dakin nata abude yake, kaita Aliyu akwai kazanta adaki zaki iya dumama mata shi Ramla” hannunshi Baban Yaseer yasa ya karbi jakan dake hannun Ramla yace “muje” binshi tayi suka fice wajen yarage daga Ammi sai Baba.Aliyu na ijiye Ramla yajuyo cus bazai iya jiranta tayi wani girki ba ayanda yadamu din nan tsayawa yayi yay salla yafito yana ciro wayanshi daga aljihu inda yaga Ni’ima tamai sama da 20 miss calls thank God wayan na silent maida wayan yayi back yashiga mota yatada.Shigowa reception din Baba yayi dan yafita yaje masallaci sallan azahar yadawo inda Ammi take zaune tana kallon gaban dakin da Hawwa tayi yace “likitan dana bari ya shiga yafito”? Ahankali Ammi tace “a’a baifito ba tukunna Malam gabana sai faduwa yake sunki fadamana komi har yanzu” shima Baba cikeda damuwa yace “karki damu in sha Allahu alkhairi zamuji” suna zaune awajen Dr yafito tareda Nurses yakalli su Baba yace “Alhamdulillah yarku ta farfado” harwani rige rigen tashi tsaye ake tsakanin Baba da Ammi but Ammi tariga Baba tashi dasauri tace “Dr zan iya ganinta”? Gyadamusu kai yayi yace “eh zaku iya ganinta amman kafin nan inaso kubini office inada magana daku” faduwa gaban Baba da Ammi sukayi, gaban Baba nafadi sosai yace “to Allah yasa lafiya, muje Zainabu” itama Ammi gabanta na faduwa ta gyadamai kai tabi Baba sukabi bayan Dr. Office din suka shiga suka zazzauna Dr ma ya zauna ganin yanda suke zazzaro idanu yasa yace “ku kwantar da hankalinku bawai wani abu bane dalili yasa nakiraku, na farko dai banda ciwukan data samu daga accident din nan yarku batada lafiya, mun gano tanada Hypertension wato hawan jini” daga Baba har Ammi atare sukace “hawan jini!”? Gyadamusu kai Dr yayi yace “yes BP yayi high sosai shinema dalilin dayasa na kiraku tunda nasan kune iyayenta in tambayeku ko akwai wani tunani da yarku keyi ko akwai takamaiman abinda ke damunta?” Shiru daga Baba har Ammi sukayi cus they know amsan tambayan Dr, abinda ke damun Hawwa is rashin aure da yawan tunanin dalilin, Ammi kuma tasan harda fadanta da Ni’ima yahadun mata but bata taba sanin Hawwa nada hawan jini ba, and she’s sure Hawwa ma batasan tanada shi ba danda zata gayamata, ganin sunki magana yasa Dr yace “I guess kunsan abinda kesa yarku damuwa dakuma tunanin datakeyi, banson na shiga family issue dinku dan haka bazan tambaya ba, amman dai kusani hakkin iyaye ne su kauda duk wata matsala da damuwa daga jikin yaran su especially idan damuwan yasoma haifar musu da cuta ajikinsu, arayuwan nan there’s nothing like yarona yayi girma he can take care of kanshi, naga kasa shekaranta 29 da 10months haka karubuta mana, Baba yaro ko shekaransa dari yana bukatan iyayensa su kula dashi, ku kula da ita dan Allah, ku taimakama yarku cus BP ta yayi high sosai, ku bata farin ciki, ku kauda mata damuwan and support her, BP yatashi yasa tai loosing control kanta tana tuki harta hada hatsari, hawan jini muguwan cuta ce da tashi daya takan dauki ran mutum, dan Allah akiyaye, babu maganin dayafi aiki kaman maganin iyaye a rayuwan yaransu, menene maganin nan danake magana akai? Shine support na iyaye da love da mantar da yaransu damuwa da bama yaran farin ciki da natsuwa……” Dr yaciga da advising Ammi da Baba sosai……Around 1:30 yashigo asibitin parking yayi yasauko yawuce ciki, ganin baiga Baba ko Ammi wajen ba yasa yayi wajen dakin da Hawwa keciki ya leka ta glass na kofan idanunta biyu amman idanun sun kankance sosai irin na mara lafiya tana kallon waje guda tai shiru tana tunani, daga ita sai dogon ringan jikinta ga gyalenta an rataya wajen bag hanger dake gefen wardrobe na dakin gashin gaban goshinta dukya kwanta luplup ansa bandage a goshinta hakama hannuwanta duk bandage wani kalan sonta da bala’in tausayinta ne ya mamayeshi kaman ya shiga ya karbe ciwon daga jikinta, hannunshi yakai yabude kofan gently yana shiga ciki, ahankali Hawwa ke juyo da kanta kadan da kadan dan har yanzu kanta na banging saidai ba kaman dazu ba so da kyar take juya kan kallo kofan dataji an bude tayi tahada idanu da Baban Yaseer daya shigo yana mata kallon tsantsan so kaman zai hadiyeta, faduwa gaban Hawwa yayi kaman taga dodo tashiga mikewa tana tashi daga kwance dasauri ya yunkuro zai taho yace “don’t move Hawwa ina zaki”? Da muryanta da baya fita sosai cikin rashin lafiya tace “karkazo nan!” Chak ya tsaya daidai tana tashi zaune da kyar idanunta har layi suke kanta yafara kwankwatsa sabida yanda ta tashi, dafe kanta tayi da hannunta da drip ke makale tana damtse idanunta cus her head is pounding kaman ana daka a turmi da kyar tace “kafita Baban Yaseer!” Cus bamata kaunan ganinshi arayuwanta, kallonta Baban Yaseer yake kaman yau yafara ganinta ahankali yace “Hawwa nafita kuma why? Nine fa? It’s Aliyu, Kinsan yanda nake cikin damuwa kuwa?” Ganin yanda yake wani irin kallonta zuwa kirjinta dan andan zage zip na bayan dogon rigan, tashin datayi yasa gaban rigan ya zazzago sama saman kirjinta na showing, da sauri tarike gaban rigan da hannu daya dayan hannun takai bayanta taja zip da mugu karfin hali Hawwa ta sauko da kafafunta daga gadon adan tsorace Baban Hawwa yakara yunkuro wa zai taho yace “ina zaki Hawwa sit please you’re not well, me kikeso ki dauka? I can give it to you”hannunta daya akai dayan ta daga ta nunashi tana haki tace “kafita I don’t want to see you! Stay away from me Baban Yaseer” yana kallonta gently and softly yace “har abada bazan taba ita staying away from you ba Hawwa” ganin yacigaba da kallonta yasa Hawwa ta diro daga gadon danta dauki gyalenta datagani a hanger kawai ta zube akasa babu karfi ajikinta ko digi kaman kafafunta basa aiki tai wani kara tana kama kanta da duka hannun biyu tace. “Kainaaa uhnnnnnn”Dagudu Baban Yaseer yayi wajenta without having a second thought sabida tsabagen yanda yarude kawai yakai hannunshi yadauki Hawwa dake kasa idanunta a kulle takama kanta da duka hannuwa biyun jin an dauketa yasa Hawwa tabude idanunta da kyar dan kadan suka hada ido da Baban Yaseer hawaye masu zafi ne suka fito daga idanunta cikin muryan da baya fita bamata da karfi sosai tace “Baban Yaseer kaji tausayina kafita daga rayuwana! Ka ijiyeni! Stop touching me, ka ijiyeni nace” tai maganan tana lumshe idanu ta rirrike kanta, yanda hawaye ke fita daga idanunta tana magana kasa kasa kaman yar baby ya kashema Baban Yaseer zuciyan he just wants to kiss her and hug her so damn tight, kofa yakalla ganin babu kowa dake tahowa yasa ahankali yashiga sauke fuskanshi zuwa daidai fuskan Hawwa he just love Hawwa and feels like kissing her baimasan meyake ba, fuskanshi na dab da sauka anata akai mahaukacin bugokofan dakin dayasa yadago kanshi da gudu Hawwa tabude jajayen idanunta da kyar suka kalli kofan suna hada idanu da Ni’ima data bugo kofan tana sanye da abaya idanunta sunyi matsiyacin ja tana kallon Baban Yaseer daya dauki Hawwa ajikinshi kaman yanda yake daukan su Yaseer da Yasmeen, adaidai lokacin kuma Baba da Ammi na zuwa wajen duk sukaci tura suka tsaya abayan Ni’ima duk suna kallon Baban Yaseer, yanda gaban Hawwa yahau bugawa ganin Ni’ima ta dauka kirjinta zai fashene da sauri ta shiga kokarin kwace kanta batama da karfin motsi abin gwanin ban tausayi tana kallon Ni’ima Baban Yaseer kuma yariketa gam ajikinshi yana kallon Ni’ima, wani kalan mosti fuskan Ni’ima yafara tana huci tace “ba kiss zakuyi ba”? Tayi mahaukacin ihu tana daukan kujeran datagani adakin tayi kansu tace “ka sumbace ta mana Aliyu…….”

