Fentin Zina Page 24 Hausa Novel
π ββοΈ *FENTIN ZINπ °οΈ* πββοΈπ ββοΈ *EESHERT ADAMU* *PAGE 24.* *Wannan page din kyauta ne kuma sadaukarwa ga masoyiya abar qaunata farin cikin rayuwata ‘yar kanwata kwallin kwal kuma auta _AMEENA BUNKAU_ much love my sister Allah ya kare mun ke a duk inda kike* .*****Suka gama ci fateema ta tattare kwanukan takai wajen wanke-wanke Ameena ta tashi zatayi shara mama rabi tace barshi zan tashi inyi.Ta girgiza kai tace bazan iya ganin kina aiki ina zaune ba alhalin babu wata lalura a tare dani.Eh toh ga dai lalura kam sai dai fatan Allah ya raba lafiya.Shiru Ameena tayi ta dauki tsintsiyar ta ci gaba da sharan ta gama ta kwashe ta fita ta zubar bata komo ciki ba ta samu fateema a inda take wanke-wanke ta ja karamin turmin karfen data gani ta zauna suka kafa hira.Wayar fateema dake ajiye a gefe tayi kara tace adda dan Allah duba mun wa ke kira.Mikewa tayi ta dauki wayar taga SWEET MOM ta Kali fateema da itama take kallonta tana son jin mai kiran tace inna ce ke kira.Fateema tace ki daga kawai.Girgiza kai tayi tace kin san inna bata kaunata yanzu shiyasa nike kiyayar duk abunda zai hada ni da ita na dan lokaci nasan zata huce a hankali.Gyada kai tayi ta karbi wayar ta danna received tasa a kunne tana cewa.Inna ina kwana ya aiki dama yanzu idan na kammala wanke-wanke nike tunanin kiranki.Eh lafiya kalau ya hanyan kun isa lafiya.Lafiya kalau inna.Ya ita Rabi’iatu din kun same ta lafiya ko.Eh inna lafiya kalau ya baba malam.Lafiya yake.Inna ki gaida mun shi.Zaiji ina ita isassiyar renon saurayi take tafi karfin tayi kirana ta gaishe ni ko?A’a inna ina ganin kamar wayar tace babu charge.Kada ki nemi kare ta ke meya hana wayar taki rashin charge din idan taga dama kada ta kirani har abada kinji ko, tunda ta mayar da kanta shashasha.Inna dan Allah kiyi hakuri wallahi duk ba yadda kika dauka bane insha Allah idan tayi charge zata kira ki.Kada ma ta kira din, inna ta fada tana jin radadin dake cikin ranta na karuwa so take ta durawa Ameena ashariya sosai koda hakan zaisa ta huce saidai kuma hakan ba dabi’arta bace tun asali shiyasa take jin nauyi a kirjinta sosai tunda bata samu fitar da abunda ke ranta ba.Kiyi hakuri inna. Fateema ta fada.Bata ce komai ba ta kashe wayar fateema tabi wayar dake hannunta da kallo tana kada kai ta kalli Ameena da bata san meke wakana ba tunda wayar ba’a jin me na Cikin ke cewa. Ta fitar da huci hadi da ajiyan zuciya tace adda inna ta dau zafi da yawa ranta ya baci sosai na rashin kiranta da bakiyi ba.Juya idanu Ameena tayi tace fateema kenan inna dai neman dalili kawai takeyi amma ai kema baki kirata ba itace tayi ta kiran ki kinga bata yi korafin naki ba sai ni. Ta karashe cikin rashin kwarin gwiwa.Hakane amma kinsan yanzu sai kin hada da hakuri kan duk abunda zaki ji daga bakinta domin cikin fushi take kuma ba domin hakan take so ba a’a kawai tana ganin hakan shine kadai zaisa ranta ya huce.Babu komai ai na riga da na dau kaddara.Allah ya kara miki dangana amma ya kamata zuwa anjima ki kirata koda zaginki zatayi.Kira kam ya zama dole ai fateema. Daga haka suka rufe zancen har ta kammala wanke-wanken suka shiga ciki suka yada zango a falo har saida Ameena ta fara hamma alamun zatayi bacci ta tashi ta shige ciki bata jima da kwanciya ba bacci ya dauke ta.Fateema ko hira sukeyi da mama rabi inda cikin hirar ne ta sako mata zancen da sukayi da inna ta kara da cewa mama dan Allah ko zaki fadawa inna cikin hikima ta daina jifan adda da irin wadannan kalaman wallahi basu da kyau.Kada ki damu zan mata magana amma ba yanzu ba domin idan na fada mata yanzu zata sake dora laifin akan Ameena ne cewa zatayi karar ta kuka kawo kinga kuwa abu baiyi kyau ba madadin ayi gyara sai ayi barna.Hakane mama domin kwarai inna zata kara kullatar addata kuma bazan so hakan ba ada nakan dauka cewar inna tafi baba malam saukin kai sai bayan faruwar al’amarin nan ne na fahimci kuskuren hasashe nayi domin baba da fari yadau fushi sosai har baya kallon inda adda take bare ya amsa gaisuwar ta amma daga baya nasiha yazo yana mata akan ta kiyaye gaba kuma ya nuna mata kuskurenta sosai ta hanyar nasiha da tausasan kalamai sabanin inna da duk abunda zai fito daga bakinta kausasan kalamai ne kawai na aibatawa da kuma Allah wadai.Hmm fateema ke yarinyace bazaki fahimta ba amma barin dan pincila miki. Ita uwace dole tafi jin ciwon abun fiye da yadda shi zaiji domin kuwa tarbiyyar tace wani ya gurbata sannan uwa tafi kaunar danta fiye da ninkin yadda uba zaiso dan dole kuma duk abunda zai samu wannan dan na farin ciki ko akasin hakan uwa tafi jin shi.Na fahimta mama amma duk da haka bai kamata bacin rai yayi nasara akan ta ba har ta furta kalmomin da zasu zama tamkar barazana ga rayuwar yarinyarta ba.Akwai kuskure kam an riga anyi gaskiya kuma kamar yadda kika fada din ne bai kamata ta aikata hakan ba amma ku bani lokaci mudan bata space kafin nayi mata magana ina fatan kafin lokacin ta huce.Allah yasa.Ameen.*****Ameena ba ita ta farka ba sai karfe daya da rabi tana tashi ta duba agogo taga yadda lokaci ya tafi ta ayyana a ranta lallai tayi bacci sosai.Fateema bata dakin don basu yi bacci ba girki suka dora ita da mama rabi.Sauka tayi daga kan gadon ta shiga ban daki ta dauro alwala ta fito ta shimfida sallaya ta tada sallah tana idarwa tayi addu’ah sannan ta jawo wayarta ta danna kiran inna.Bata daga ba harta tsinke bata damu ba ta kara kira sai data kusan tsinkewa kafin ta daga kamin tayi magana inna ta tare ta da cewa ke isassa bazaki kirani ba wato sai na bada sako ko?Kiyi hakuri inna don girman Allah wallahi ba nufina haka bane ina yini.Da ban yini ba ai bazaki jini ba kuma dayake na saba karya dole kice haka yo wacce ma ta iya bawa saurayi jikinta har ya mata ciki ai komai ma akace zata aikata.Kuka Ameena ta fashe dashi domin kalaman inna suna matukar razana tunaninta dama duka duniyarta.Kuka ma zaki mun? Toh dana miki me?. Saurin hadiye kukan tayi ta koma ajiyan zuciya.Inna ta cigaba da cewa kin bani mamaki yadda har kika iya budewa na miji kafa ya miki ciki hakan yana nufin duk saurayin daya zo domin soyayya dake irin abunda zaki mishi kenan? Ban taba jin kunci ba duk tsayin rayuwata sai wannan karon wallahi sam bana jin kaunar ki a yanzu cikin raina, a da idan naji ana cewa mutum na tsanar dan daya haifa zan karyata amma yanzu na fahimci wannan karatun domin bana jin zan ci gaba da ajiye ki a matsayi daya da sauran yara na, kin wulakanta ni kin ci mutumci na kinci amanar yardata akan na miji kinsa ni bakin ciki kin hana mun walwala, a yanzu bana jin ko digon soyayyarki bare tausayinki.Tana kaiwa nan ta kashe wayarta.Numfashin Ameena ne ya soma hawa da sauka da sauri da sauri numfashinta na nema ya bar gangar jikinta amma cikin karfin hali take karanto duk addu’ahr data zo bakinta tana kokarin daidaita numfashinta tana cikin haka ne fateema ta shigo da nufin ta gabatar da sallah sai kuma ta tarar da addanta cikin halin neman taimako tayo kanta da gudu tana kiran sunanta.Karfin hali kawai Ameena takeyi ta daga hannunta tana mikawa fateema. Da sauri ta kama hannun tana cewa cikin damuwa.Adda meya same ki?.Magana ta somayi cikin sarkewar numfashi.Bayan rai ya tsinke daga gangar jikina ki rokar mun inna gafara domin ba…. bazan samu rahama ba muddin na tafi tana fushi dani ki mun wannan…. wannan alfarmar kinji kanwata. Ta karasa hawaye na tsiyayowa daga cikin idanunta lokaci daya kuma numfashinta ya kara sama sosai jikinta ya soma wani irin jijjiga daga baya kuma komai ya tsaya cak………….. **DAN ALLAH KUYI HAKURI WALLAHI DOMIN FARIN CIKIN KU NE YASA NAYI TYPING AMMA BANDA LFY DAGA NI HAR DIYATA A KWANCE MUKA YINI SAI BAYAN MAGRIB NE DANA SAMU KAINA NACE BARIN DAN YI MUKU KODA KADAN NE* *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* βοΈ

