Hausa novels

Ruwan Zuma Page 15 Hausa Novel

(15) Har suka kusa isa asibitin babu wanda yayi magana domin kowa da tunanin da yake yi a ransa na wannan al’amari da suke ciki. Laila ce tayi parking a bakin hanya ta kalli Haydar tace, “Ina Ammin take?�? “Tana cikin emergency.�? Ya bata amsa ta fice daga motar ba tare data kallesu ba. Da sauri suma suka fito Haydar na rik’e da hannun Nasir suka yi gaba Laila na binsu a baya. “Haydar don girman Allah ka sakemin hannuna in tafi.�? Fad’in Nasir kenan yana neman hanyar guduwa kar laifin Haydar ya shefeshi. Suna isa bakin d’akin da Ammi take Haydar yaja tunga ya tsaya yana ta juyar da kansa baya son had’a ido da Laila don wani kwarjini ta masa har yana jin shakkarta. “Me yake damunta sannan me ake buk’ata?�? Ta tambayeshi tana mai tsura masa ido har yaso ya bata dariya ganin yanda yake kallon ko’ina amma banda ita. Amma tuno da risk d’in data d’auka na taimakonshi sai taji babu dariyar ta k’ara had’e fuskarta tamau. A aljihunsa ya ciro takardar da aka bashi d’azu na maganin ya mik’a mata yana cewa, “Ga abunda suka rubuta sannan sun ce inyi sauri in kawo.�? Laila ta kar6i takardar tana karantawa lokaci d’aya fuskarta ta k’ara had’ewa ta dubi Haydar kamar ta dakeshi tace, “Amma ina hankalinka yake da aka ce kayi sauri ka kawo amma ka bari muka shigo asibitin ba tare da mun saya ba?�? “Kiyi hak’uri Hajiya.�? Ya k’ara k’asa da kanshi don bai san ma dalilin da ya hanashi nuna mata ba tun farko. Tsaki ta ja mai sauti kana tayi hanyar fita daga asibitin yana binta a baya don bai san me zai yi ba. A bakin motarta ta tsaya tana kallonshi cikin mamaki, “Ina zaka je?�? Shiru yayi yana sosa kai don bashi da amsa yace, “Na’am.�? “Ka koma ciki ka zauna kusa da d’akin Incase suna buk’atar wani abun sai ka mini waya.�? Gyad’a kai yayi ya koma ciki amma ranshi na k’una don yanda Laila ke kad’ashi kamar ba d’azu ya gama cewa yana sonta ba. In ya gane da kyau kamar so take ta nuna masa cewa bata d’auki maganarsa a ta masu hankali ba, sai ma titsiyeshi da tace zata yi nan gaba kad’an don taji wa ya aikesa furta mata haka. Alk’awari yayi zai fad’a mata gaskiya ko da kuwa kasheshi zata yi. Pharmacy d’in da ta mallaka ita da Mas’ud taje don ta tabbatar a nan zata samu duk abunda aka lissafa na Ammi. Bata yi tsammanin ganin Mas’ud a gurin ba domin bayan ya mari Haydar ta daina masa magana duk da cewa bata hanashi aikata hakan, ko kuma ta nuna mishi yayi ba daidai ba. Yaran shagon su biyu suka gaisheta cikin girmamawa ta amsa cikin gaggawa sannan ta mik’awa d’aya daga cikinsu takardar hannunta ya fara d’auko maganin yana ajiyewa a counter da ta d’aura hannunta akai. Duk abun nan da suke yi idon Mas’ud na kanta amma tayi kamar bata ganshi ba, k’arshe shi da kanshi ya taso yazo gurinta yace, “Kalti waye ba lafiya?�? Yasan tana fushi dashi don fad’an da suka yi d’azu amma bashi zai hana yak’i mata magana ba. Baya iya fushi da ita mai tsawo sanin ita d’in rayuwarsa ce. “Wata ce.�? Shine kad’ai amsar da ta bashi kana ta dubi wanda ya gama had’o mata maganin tace, “Nawa ne kud’in.�?Lissafi ya fara yi da calculator Mas’ud kuma ya fara sakawa a leda. “Baki fad’amin wacece bata da lafiya ba, and naga kamar rashin lafiyar na zuciya ce.�? “Wata ce.�? Ta k’ara fad’a tana k’arban ledar a hannunsa. Bayan yaron shagon ya fad’a mata yawan kud’in tace, “Zan turo kud’in ta bank account d’in Pharmacy.�? “Duk yanda kika yi Hajiya.�? Ya koma ga wani customer daya shigo a lokacin. Waje ta fita tana danna wayarta wanda kafin ta shiga motarta Mas’ud yaji alert d’in shigowar kud’i a wayarsa. Bin bayanta yayi yana kiran sunanta ta tsaya ta juyo suka fuskanci juna. “Laifin me na miki Kalti kike k’in mini magana? Me na miki?�? Yayi mata tambayar cikin sanyin murya gudun kar ya k’ara 6ata mata rai duk da ma bai san tak’amammen laifin da yayi ba. “Babu komai, kawai sauri nake yi.�? Ta bashi amsa ta shige motarta. Mas’ud ya iso gurinta ya rik’e marfin motar ya cigaba da magana. “A gida fa?�? “Ban gane a gida ba!�? “Ina nufin a gida da kike shareni saurin kike yi?�? “Mas’ud kaga mu bar maganan nan domin banida lokacin yinta. Idan ka dawo gida zamu tattauna.�? Ta ja murfin motar ta rufe. “Shikenan, muje zan rakaki gurin da zaki kai maganin.�? Yana fad’in hakan ya juya zuwa inda yake ajiye motarsa ba tare da Laila taji maganar rakata da yace zai yi ba. Tana fita a haraban Pharmacy shi kuma ya kunna tashi motar kana yabi bayanta ba tare da ta sani ba. A yanda take sauri sai ta 6acewa Mas’ud wanda dama sai da tayi nisa yabi bayanta. Kiran wayarta yayi amma har ta gama ringing bata d’auka ba. Da ya gaji da kiranta shima ranshi a 6ace ya koma gida in da ya tarar da abun tashin hankalin da bai yi tsammani ba. Laila kuwa tana komawa asibiti ta samu Haydar tsaye shi da wani Likita wanda yake kula da Ammi. Tana isowa ta mik’awa Haydar maganin shi kuma ya bawa Likitan ya shige cikin d’akin da Ammi take kwance. Bayan shigarsa Laila ta dubi Haydar tace, “Sai kuma me kuke buk’ata?�? “Sai kud’in test d’in da za’a mata.�? Ya bata amsa wannan karon yayi bajintar d’ago ido ya kalleta. Ganin fuskarta a murtuk’e yasa ya k’ara kawar da kanshi, zuciyarsa kuwa bugawa take yi wanda ya kasa tantance na tsoro ne ko kuma na sonta da yake tunanin yana yi. “Muje in biya.�? Bayan an biya ta mik’a mishi receipt tace, “Idan wani abun ya tashi ka mini text kawai, karka kirani. Sannan gobe zan shigo in duba jikin nata.�? Godiya ya mata sosai wanda bata amsa ba ta fita ta barshi a gurin shi kad’ai, dama tun fitanta siyo magani Nasir kam ya gudu. Gida ta nufa tana jin zuciyarta a cunkushe kamar bata ta6a samun kanta a halin walwala ba. Horn tayi maigadi ya bud’e mata gate ta kutsa hancin motar cikin gidan. Tana shiga falonta ta tsaya cak ganin Mas’ud, Abul, Sabrin da kuma mutumin da bata yi tsammanin k’ara kallonshi ba a gidanta wato Yayanta Madu. Mas’ud ne ya fara takowa gurinta idanunshi sun yi jaja zur ya mik’a mata hotunan dake hannunsa yana cewa, “A ina kika k’ara had’uwa da yaron nan bayan fitanki?�? Bata amsa ba ta k’arbi hoton dake hannunshi tana dubawa mamaki k’arara a fuskarta duk da cewa d’azu an aiko musu makamancin haka. Hotuna ne guda biyu wanda ciki ita ce da Haydar a bakin motarta a wani hotel, sai kuma d’ayan still ita dashi a cikin mota amma fuskarsu bai fito sosai ba dalilin duhun dare. “Waye ya kawo?�? Shine tambayar data fara yi tana kallon mutanen d’akin. Sabrin da sai a yau taji labarin abunda yake faruwa ta tako zuwa gurin mamanta tana kuka, “Mama menene yake faruwa? Waye wannan d’in da kuke zuwa Hotel tare?�? Tass!! Sabrin taji sauk’ar mari a fuskarta wanda ya gigitata na sakanni goma kafin ta dawo cikin ruwan hankalinta. Madu dake gefe da sauri ya iso gurinsu yaja Sabrin kusa dashi ya fara magana tamkar zai tada gidan tsabar 6acin rai. “Tambayar da ke bakin kowa ta miki Laila, meyasa kike zuwa hotel da yaron nan? Kar kiga laifinta domin taga uwarta na son kaucewa kan hanya ne. Me ya kaiki hotel da yaron?�? Laila tsabar 6acin rai ta watsar da hotunan a k’asa ta kalli ‘yan d’akin kaff tace, “A tunani kai Mas’ud, Abul da kuma Sabrin bazaku ta6a yarda da cewa ni Laila zan iya aikata alfasha ba, sannan kuyi amfanin da hankalin kanku da kuma ilimi da kuke dashi na zamani, shin wad’annan hotunan gaskiya ne ko dai editing d’insu aka yi? Bazan ce bani da Haydar bane a cikin hoton sai dai an canja mana background, a maimakon asibitin Murtala aka mayar dashi hotel. Kuma kai Mas’ud ka ganni a Pharmacy naje siyan magani, ko a nan kwakwalwarka bata maka lissafin cewa hoton nan k’arya bane? Yaushe na fita? Yaushe muka je hotel? Yaushe kuma muka fito har naje pharmacy na siyo magani na dawo gida? Duk a ciki awa d’aya? Anya kuna aiki da hankalinku ko kuma dai tsabar neman laifina yasa kuka kasa tunani mai kyau?�? Da haka tayi hanyar d’akinta sai dai taji muryar Abul na cewa, “Meyasa kika d’aukeshi a motarki bayan duk abunda ya faru da yamman Mama?�? “Saboda mahaifiyarsa ce bata da lafiya, ita ke kwance a emergency tana buk’atar taimakon gaggawa dalilin ciwon zuciyarta. Idan har yanzu baka yarda ba kaje asibitin Murtala a emergency ka tambayi sunan Lu’alu’a Aliyu Haydar za’a kaika d’akin da take.�? Tayi shigewarta d’aki ta bar Madu na fad’a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Kwanciya Laila tayi bayan ta kulle d’akinta da key tana jin komai na duniyar ya fita a ranta. Tasan tabbas akwai wanda yake son ganin bayanta yana neman ya zubar mata da kimarta. Idanunta ne ya ciko da hawaye amma ta dannesu, a ranta kuma cewa take yi baza tayi kuka akan abunda take da gaskiya ba. Ita ba fasik’a bace. A nan ne kuma ta tuna abunda ya faru ranar litinin d’in da zata kai Haydar neman aiki har rana mai kamar ta yau. Ta gama shiryawa kenan ta fito falo, a nan ta tarar da Mas’ud zaune a kan dinning table yana karyawa. Bayan sun gaisa itama aka kawo mata tea kamar yanda ta buk’ata ta dubeshi tayi dariya ganin yanda ya tsura mata ido yana kallonta. “Nayi kyau ne?�? Ta tambayeshi kana ta kur6i tea d’in nata. “Kamar kullum. Amma ina zaki je da sassafe haka?�? Ya tambayeta yana mai kawar da abincinsa gefe alamar ya k’oshi. Sauran abinci nasa ta jawo gabanta ta d’auki cokali ta kai loma d’aya na d’umamen tuwon alkama miyar ku6ewa d’anye. “Yaron nan zan nemawa aiki a office d’in Alhaji Abdul.�? “Amma Kalti kina ganin baza a samu wata matsala ba idan aka ga yaron nan na sintiri a gidan nan sannan kuma ana ganinku tare ba?�? Nan take taji abincin ya fita a ranta sanin hakan na iya faruwa, tun bayan rasuwar mijinta take kaffa-kaffa da mutanen da take huld’a dasu ta kuma kori duk zawarawanta tana fad’a musu cewa ba aure bane a gabanta. Amma yanzu a yanda Haydar ya samu kar6uwa a zuciyarta bata tunanin maganar mutane zai sa ta rabu dashi wai don gudun zargi. In bata manta ba a bata kula kowa d’in ma wasu na zarginta ciki kuwa har da shak’ik’inta wato Madu. “Bazan tsara miki yanda zaki tafiyar da rayuwarki a yanzu ba kamar yadda ba nine na tsara miki na baya ba, shawara ce kawai zan baki shine kisan yanda zakiyi ki rabu da yaron nan domin haka kawai naji bai kwanta mini ba.�? Bata yi musu dashi ba a wannan lokacin hasalima cewa tayi zata k’ok’arta ta rabu dashi tunda zata sama mishi aiki. Tunanin yanda zata rabu dashi ne yasa ta fito fuskarta babu walwala har ta kaishi office d’in ya samu aiki kamar yanda taci buri. Sai dai bayan tafiyar mahaifiyarsa ta fara mafarki tare dashi wanda ya sanyata cikin rud’u da zullumi har bata son rufe idonta da niyyar bacci. Ana haka kuma sai gashi yau da yamma ya zo mata da wata banzar magana wai yana sonta! Taimakonshi da take yi ne yasa yayi tunanin sonshi take yi ko kuma tsabar ya raina mata wayo ne ya aikata hakan? Kenan sakin fuskar da yaga take masa shi yasa ya iya bud’e baki yayi maganar a gaban d’anta da kuma k’aninta? Marin da Mas’ud ya yiwa Haydar tajishi har cikin zuciyarta amma tasan ya cancanci hakan, ko ba komai zai dawo cikin hankalinsa ya gane da waye yake magana, itace Laila uwar d’akinsa ba ‘yan matan da suke soyayya a titi ba, kuma Haydar ba tsarinta bane wannan a rubuce yake shi kanshi ya sani. Bayan Mas’ud ya fitar dashi har waje ta kwalar rigarsa ya dawo falon yana bambami yana cewa, “Ga irinta nan Kalti, ki duba yaron da ko k’oshi bai gama yi ba wai shi zai dubi tsabar idonki yace yana sonki? Ina zai kaiki ko ke sa’arshi ce? Wani irin raini ne ya shiga tsakaninku haka?�? Abul ma zai fara magana ta d’aga masa hannu tace, “Ka fita ka bani waje kar inji bakinka.�? Hakan kuma akayi amma a yanda ya fita a zuciye tasan cewa ta aikata kuskure na korashi da tayi a wannan halin da yake ciki. Bata san me zai iya aikatawa ba bayan nan, tana tsoron zuciyar Abul. Fad’a sosai suka yi da Mas’ud wanda ita kanta tasan gaskiya yake fad’a mata amma ta runtse ido tana nuna masa cewa ba abunda yake so zata yi ba, itama tana da nata tunanin kuma dashi zata yi amfani bana wani ba. Suna tsaka da wannan sa’insar maigadi yayi sallama ya shigo hannunsa d’auke da envelope da ya mik’awa Mas’ud wai wani yace a bashi. “Wai ance ka duba yanzu-yanzu.�? Fad’in Maigadin yana fita waje. Mas’ud da mamaki ya kamashi ya dakatar dashi yace, “Waya kawo?�? “Wallahi nima banga wanda ya kawo ba, domin an kwankwasa k’ofa na tambayi wayene sai aka turomin envelope d’in ta k’asa ana cewa in baka kuma ka gani yanzu. Kafin ma in bud’e k’ofar naji k’arar mashin ya tafi.�? “Shikenan.�? Bayan maigadin ya tafi Mas’ud ya bud’e envelope d’in inda yaga hotunan Laila ce da Haydar kala daban-daban har shida. Kowanne kuma an d’aukesu a yayin da suke kusa da juna ne suna dariya ko kuma suna murmushi. Wanda yafi d’aga masa hankali shine wanda aka d’aukesu a ma’aikatar su Alhaji Abdul Laila na gaba Haydar na tafiya a bayanta tamkar zai take mata dunduniya kuma idonsa na kallon bayanta. “Na fad’a miki ban yarda da yaron nan ba Kalti.�? Fad’in Mas’ud yana takowa gurin Laila zufa na taruwa a goshinsa duk da sanyin dake falon. Laila da take tunanin sun gama hargowar har ta zauna tana dafe da kanta ta d’ago ido ta kalleshi cikin mamaki. Me kuma ya gani game da Haydar da zai ce haka? Hotunan ya mik’a mata ta fara kallonsu hannunta na karkarwa, bata mishi magana ba ta shige d’akinta ta kulle ta zauna kan gado tana mai cigaba da gani tana mamakin wanda ya iya d’aukan hoton cikin sirri ba tare da sun ankara dashi ba. Tunani guda d’aya ta kasayi amma tana da tabbacin lallai behind all these akwai mutum ko mutanen da suke son bak’antata a idon duniya. Su waye? Shine bata sani ba amma zata yi bincike kuma baza ta zauna har su zami galaba akanta ba. Sai dai wannan karon tasan ta fita zuwa gurin Haydar ne don Amminsa ba don shi ba, a yanda taga soyayyar dake tsakaninsu ba zai iya yin k’arya da lafiyarta don ta saurareshi ba. Ashe duk saurin da tace su Haydar suyi su shiga motarta bai hana mai d’aukansu a hoton ya samu chance d’in d’auka ba. Waye ne? Me yake nema? Kuma menene manufarsa? Har safiya tayi Haydar bai mata text kamar yanda tayi tsammani ba. Tana na zaune a cikin d’akinta har k’arfe tara babu wanda ya buga mata kamar yanda a daa suke mata idan wani abu ya faru tak’i fitowa. Kenan duk fushi suke yi da ita sun barta da halinta? K’arfe goma daidai ta fito tana sauraron d’akin Sabrin dake kusa da nata amma bata ji alamar tana nan ba. Bud’ewa tayi taga babu kowa a ciki sannan an gyara d’akin tsaf tamkar bata kwana a ciki ba. Kitchen ta shiga inda mai aikinta ke wanke-wanke suka gaisa, Laila ta tambayeta ina mutanen gidan. “Wallahi Hajiya nima tun tashina ban gansu ba, kamar da sassafe suka fita.�? Gyad’a kai Laila tayi kana tayi hanya fita daga kitchen d’in. “Hajiya a kawo miki karyawa ne?�? Mai aikin ta tambaya tana goge hannunta a jikin zaninta. “A’a bana jin cin abinci amma ki daina goge hannunki da zaninki, ga kitchen towel nan da nace kina amfani dasu.�? Fita tayi a motarta ta nufi asibiti don duba jikin Ammi kamar yanda tayiwa Haydar alk’awari. Tana isa ta nufi emergency ward inda aka kwantar da Ammi, ko da ta shiga sai ta samu bata nan sannan bata ga Haydar a bakin gurin ba. A gurguje ta d’auko wayarta dake cikin jakarta ta kira Haydar, ringing biyu ya d’auka yana sallama. Bata amsa sallamar ba tace, “Ina kuke? Ina Ammi?�? Don a tunaninta wani abun ne ya faru da Ammi. “Muna female ward, yau da safe aka maida ita can bayan sun ga jikin nata yayi sauk’i.�? Da haka yayi mata kwatancen inda suke har ta isa. Abunda ya fara bata mamaki shine yanda aka yi Haydar ya samu kud’i ya kamawa Ammi side room ita d’aya. Mamakinta bai tsaya a nan ba domin wasu mutane biyu da ta gani tare da Haydar kowannensu tsaye a gefen kad’arsa d’aya shi kuma yana zaune a akan kujera yayi tsuru-tsuru yana kallonta.

Mum Fateey 👌

Back to top button