Hausa novels

Ruwan Zuma Page 16 Hausa Novel

(16) “Sannu da zuwa Gimbiya Laila.�? D’aya daga cikin mutanen yace da ita yana barin bayan Haydar ya tako zuwa gurinta. Sake k’ofar Laila tayi ta rufe ruff kana ta kallesu da tsantsan mamaki a fuskarta tace, “Alhaji Abdul, Mas’ud, me kuke yi a nan?�? A nan ta mayar da dubanta ga Haydar wanda ya mik’e tsam ya isa bakin gado inda Ammi take bacci ya tsaya a nan. Gaisheta suka yi dukansu tana amsawa tana musu kallon rashin yarda. Ganin haka yasa Mas’ud ya isa bakin window ya tsaya yana kallon waje ba tare da yace da ita komai ba. “Yau da safe na shigo nan asibitin yin wani taimako na hango ma’aikacina Haydar a bakin emergency room, a nan yake fad’a mini mamarshi ce bata da lafiya kuma har kin biya komai ni kuma na k’arisa sauran. Da fatan ban muku katsalandan akan harkar family ba? Duk da cewa Mas’ud ya fad’a mini baku had’a jini da Haydar ba. Ko ba haka ba Mas’ud?�? Mas’ud yayi kamar bai ji me ake maganan ba yaci gaba da kallon waje. Runtse ido Laila tayi na sakanni biyar sannan ta bud’e ta sauk’esu kan Alhaji Abdul. Tun ba yau ba tasan shi mai bin asibitoci ne yana taimakawa masu neman taimako na kud’in magani, aikin tiyata ko kud’in gado da suka kasa biya. To shi kuma Mas’ud me ya kawoshi? “Haydar ya jikin Ammi.�? Ta isa gadon da Ammi ke kwance tana kallon fuskarta wacce tayi haske irin ta mara lafiya. “Da sauk’i. D’azu ma da kanta ta tashi tayi sallah, bayan ta karya ne ta k’ara komawa bacci.�? Ya bata amsa yana mai russunawa kad’an. “To! Ni zan tafi. Aliyu Haydar idan kuna buk’atar wani abu ka kirani, kaji ko? Allah ya bata lafiya.�? Fad’in Alhaji Abdul kana ya juyo da dubansa gurin Laila yace, “Gimbiya Laila sai gani na biyu. Take care.�? “Nagode Alhaji Abdul. Kana k’ok’arin taimakawa bayin Allah, Allah ya saka da alkhairi.�? Murmushi yayi har hakwaransa na bayyana cikin farin ciki kamar wanda aka yiwa kyauta yace, “Ameen Gimbiya Laila.�? Da haka ya gyara garen dake jikinsa ya fice daga d’akin bayan ya musu sallama duka. “Da fatan babu wata matsala ko?�? Ta tambayi Haydar amma kuma Mas’ud take kallo. Shima idonta ya bi ya had’iye yawu mai kauri yace, “A’a babu komai Hajiya.�? “Mas’ud ka fito muyi magana a waje.�? Tana fad’in hakan ta fice waje. Minti uku Mas’ud ya d’auka kafin ya fito ya sameta tana kaiwa da kawowa, a ranta kuma tana fad’in tayi garajen barin Haydar shi kad’ai tare da Mas’ud. Daa taso komawa cikin d’akin amma idan tayi haka zata nunawa Mas’ud ta damu da Haydar, wanda kuma hakan zai k’ara jawo mata wani zargin. “Gani.�? Ya tsaya a gefenta yana karantar yanayinta. “Me ka zo yi a nan Mas’ud?�? “Ke kika bani address d’in da suke, wanda Allah ya taimaka nazo dubasu da safe na samu an rik’e Abul yana cewa zai lahanta Haydar. Tare muka shigo da Abdul wanda dama ya fad’a miki dalilin zuwansa, so shi ya lalla6i Abul yasa drivernsa ya kaishi gidan gonarsa wai ya huce a can. Daga nan kuma ya biya kud’in gado aka shigo da ita nan shine har kika zo kika samemu.�? “Alhaji Abdul yaji me yake faruwa?�? “No, amma idan ya koma gidan gonarsa zai iya samun labarin komai.�? Da sauri Laila ta kira Abul ya d’auka amma yak’i yayi magana, tace, “Ka dawo gida yanzu sannan kar kowacce magana ta had’aka da Alhaji Abdul.�? Abul ya kashe wayarsa ba tare da yace komai ba Laila runtse ido tana addu’a a ranta. “Mas’ud ko nayi wauta da nak’i yin aure tun daa? Ka duba Abul yana nema yafi k’arfina. Shin na musu adalci kuwa da nak’i yin aure suka rasa tarbiyyar uba.�? Mas’ud da tun zuwanta fuskarsa a turnuk’e take ya sassauto ya matso kusa da ita yana bata baki. “Kinyi iya bakin k’ok’arinki wajen bawa yaran nan tarbiyya, so baki da wani laifi. Sannan tun tashin Abul haka Allah ya yishi da zuciya da taurin rai. Kici gaba da mishi addu’a zai canja Insha Allah.�? Kad’a kai kawai take yi har ya gama ta share hawayen fuskarta. “A yanzu ka yadda babu wata alak’a a tsakanina da Haydar? Kai kad’ai ne mai fahimtata a koyaushe amma na rasa gane dalilin da yasa wannan karon ka juya mini baya Mas’ud.�? Juyar da kanshi yayi kana ya fara tafiya a hankali yana cewa, “Ki rabu dashi kawai Kalti. Please.�? Da haka ya barta a gurin baki bud’e har ya 6ace mata da gani. Ta jima tsaye a gurin tana tunani barkatai a ranta, wayarta ta d’auko ta kira Sabrin wacce har lokacin bata nemeta ba. “Ina kwana Mama.�? “Lafiya. Kina ina ne?�? “Ina shago.�? Ta bata amsa amsa. Da haka suka yi sallama bayan Laila ta fad’a mata cewa itama gata nan tana zuwa. In su basu fahimceta ba tasan Sabrin baza ta juya mata baya ba, wannan a zaune yake. Haydar ta kira a waya ya fito ya tsaya a gefenta. “Ka fad’a mini gaskiya, kai kake turo mini hotona ko kana da wata alak’a da hakan?�? Haydar ya girgiza kanshi cikin takaici yace, “Wallahi bani bane, kuma ban ma san da ana miki haka ba sai da kika fad’a mini. Kuma Hajiya bazan saka miki da haka ba duk tarin alkhairinki gareni.�? Kad’a kanta tayi tana son yarda da zancensa kana ta dubeshi, sai taga kamar ya fad’a kad’an sannan rigarshi ta jiya itace a jikinshi har yanzu. Tausayinshi taji ya kamata don haka ta sassauto da fuskarta tace, “Kayi wanka kaci abinci kuwa?�? Girgiza kai yayi yana kallonta kamar maraya wanda hakan yasa Laila ta k’ara jin tausayinsa a zuciyarta. “A nan na kwana ban koma gida ba.�? Ya bata amsa yana saka hannunsa cikin aljihun wandonsa. Murmushi ne ya su6uce a fuskarta da taga yayi hakan kana ta d’ago idanunta ta zubasu cikin nashi, tana jin kamar damuwarta na tafiya a hankali a hankali. “Ka koma gida kayi wanka zan zauna da ita kafin ka dawo.�?“Are you sure? I mean bazan takuraki ba?�? Yayi gaggawan canja maganarshi. Kud’i ta ciro a jakarta ta mik’a mishi tana cewa,“Gashi ka hau mashin.�? Girgiza kai yayi ya zaro kud’i masu yawa a aljihunsa yana cewa, “Oga Abdul ya bani dubu ashirin yace in rik’e a hannuna incase wani abun ya tashi.�? Laila ta zagaye bakinta yayi ‘o�?, alamar mamaki, a ranta kuma dariya take yi yanda Haydar bai san cewa kud’in tsohon saurayinta ya k’ar6a ba duk da cewa bata d’auki maganarshi a bakin komai ba sai shirme da yarinta. Shi kuma Alhaji Abdul daa yasan cewa Haydar ya furta mata kalmar so da ya koreshi a aiki. Shiyasa take son Abul ya dawo gida kafin su ke6ance da Alhaji Abdul d’in ya bashi labarin komai. Bata k’ara magana ba ta shige d’akin da Ammi take ta samu guri ta zauna tana kiran layin Abul. Sai da ya kusa tsinkewa ya d’auka yana cewa, “Gani a hanya.�? Ya kashe wayarshi. Runtse ido tayi cikin takaici kana ta fara yi masa addu’a a ranta, yayinda lokaci d’aya kuma taji kamar da bata k’ara taimakon Haydar ko ta kulashi ba. Sai dai wata zuciyar a gefe ta kwa6eta da cewa, ‘Don mutum na nufinki da sharri bashi zai hanaki aikata alkhairi ba. Ki barshi da Allah domin shi kad’ai zai miki sakayya ya kuma wankeki daga zargi. Tunda aka iya zargin uwar muminai wato Aisha (RA) ke wacece da zaki iya kaucewa hakan? Ki bar komai ga Allah.�? Wannan tunanin da tayi yasa taji sauk’i a ranta ba don damurta ya yaye ba, sai dai ta sani duk wuya duk rintsi Allah bazai bari ta wulakanta ba domin bata bi hanyar fasikanci ba balle har ta aikatashi ba. Bayan awa d’aya Haydar ya dawo yayi wanka ya canja kaya sai k’amshi yake zubawa kamar bashi yayi kwanan asibiti ba. “Na dawo Hajiya, Allah ya saka miki da alkhairi.�? Ya mata godiya. Laila ta mik’e tsaye tana sak’ala jakarta tace, “Yau baza ka kirani da sunana Laila ba kenan? Dama ranar baka cikin hankalinka ko?�? Kunya yaji ta kamashi amma ya dake ya k’i sauk’e idonsa k’asa. “Ka kula da me kake yi a rayuwa Haydar, don ina wasa da kai bashi zai sa ka bud’i baki a gaban d’ana da k’anina ka furta mini cewa kana sona ba. That was rubbish and unacceptable kuma bazan lamunci hakan a gaba ba. Ka kiyaye harshenka ka kuma san wace magana zaka iya furta mini. Sannan daga yau bana son k’ara jin wannan maganar ta k’ara tashi. Kana jina ko?�? Ta k’arishe maganan tana nunashi da yatsa kamar mai magana da d’an cikinta. Bai gyad’a kai kamar yanda tayi tsammanin zai yi ba, illa sanya hannayensa da yayi a aljihun wandonsa ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai cinyeta. Zuciyarta ce ta buga ganin yanda halin Haydar ke canjawa lokaci guda kamar mutum biyu ne a gangan jiki d’aya. Hanyar waje tayi ta bud’e k’ofa zata fita taji ya fara magana a hankali yana cewa, “Ni na gani, naji ina sonki kuma na furta miki da fatar bakina. Ko menene zai faru bazan daina sonki ba kuma bazan fasa fad’i ba sai dai in kasheni za’a yi a kasheni. KI SA A RANKI HAYDAR YANA SONKI NE DA DUKKAN ZUCIYARSA.�? Rufe k’ofar tayi ta fita cikin sauri tana nanata kalmomin da yayi amfani dasu musamman ma na k’arshen. Tabbas ta ta6a jin wannan maganar a gurin masoyinta kuma uban ‘yayanta. Me yake faruwa ne? Bayan kwana d’aya ranar lahadi kenan aka sallami Ammi wacce ta samu sauk’i sosai sai dai abunda ba’a rasa ba. Sosai Haydar yake kaffa-kaffa da ita yana kula da ita baya son 6acin ranta. Ko da litinin tazo cewa yayi ba zai je aiki ba domin baya son barinta. “Bana son shirme, ni d’in yarinya ce da zaka tasani a gaba kana raino? Maza tashi ka shirya ka tafi kafin kayi sanadin aikinka. Ji mini maganar banza.�? Ganin zai 6ata mata rai yasa ya tashi ya shirya ya tafi, a ransa kuma yana tunanin watak’ila Laila tasa an koreshi bayan abunda ya furta mata a had’uwarsu ta k’arshe, wanda har yau bata sake kiranshi ta tambayi jikin Ammi ba. Sai dai har aka tashi daga aiki bai ga takardar sallama ba sai ma Alhaji Abdul da ya kirashi ya tambayeshi jikin Ammi kana ya k’ara damk’a mishi dubu goma wai na sayan magani. Da fara’arsa ya dawo gida bayan ya tsaya ya sayawa Ammi kayan marmarin da aka ce tana yawan ci don gyaran zuciya. Sai da ya tabbatar ta fara ci sannan ya shiga d’akinshi ya tu6e kayan jikinshi ya kwanta bacci. Dama shi haka yake, duk sanyi kuma duk zafi bazai kwanta da riga a jikinsa ba, idan kuma ya saka bazai iya bacci ba. La’asar sakaliya ya farka ya lalu6o wayarsa zai duba lokaci. “Ali wai bada kai nake magana ba? Ali!�? Ya jiyo muryar Ammi a tsakar gida, zuciyarsa ce ta tsinke ya fita cikin saurin domin yasan ciwonta ne ya tashi. Abunda ya gani ne ya bashi mamaki ainun, domin Ammi ya gani zaune a kan kujera sai kuma uwar d’akinsa kuma masoyiyarsa Laila a kan tabarma ga k’ofin silver a gabanta wanda aka kawo mata ruwa a ciki. “Ammi…�? Yama rasa me zai ce sai kallon Laila da yake yi wacce ta kawar da kanta gefe kamar bata ganshi ba. “Kai dai baka da kunya wallahi, na rasa wani irin hali ne da kai.�? Ammi ta fad’a tana jefa mishi harara. Komawa yayi d’akinsa yana ji suka cigaba da magana ta yaren Shuwa wanda ko kad’an baya ji. Sai dai yaji Ammi na yawan kiran sunanshi a cikin maganarta. Ko me take fad’a mata shine bai sani ba, a zuciyarsa kuma yaji haushi da Ammi bata koya masa yarensa ya tashi dashi ba. Sai dai wannan mai sauk’i ne akan k’in sanar dashi tushensa da tayi, wanda yayi alk’awarin ba zai sake tambayarta ba har sai taga damar fad’a mishi. Ba zai k’ara tayar mata da hankali ba balle ya rasata ita kwalli d’aya da yake gani yaji dad’i. Yana fitowa yayi sallama suka amsa masa wannan karon Laila na binshi da murmushi tamkar yanda take mishi a daa kafin yace yana sonta. Cikin girmawa ya gaisheta ta amsa kamar kullum har tana tsokanarshi wai ya cika bacci. Murmushi kawai yayi amma a zuciyarsa bai yarda da ita ba, fara’arta yayi yawa ko dai ta amince da soyayyarshi ce zata aureshi? Wannan tunanin ne yasa ya shima fuskarsa ta washe yace, “Hajiya ya aka yi kika gane gidanmu?�? “Ai gidanku bashi da wahalar ganewa, abokinka Nasir ne ya mini kwatance.�? “Mun gode da ziyara da kuma kulawa Hajiya.�? “Sai ka k’ara mata godiya ba don shi zai saka mata da abunda take shirin yi maka ba Ali. Samun irinta a duniya sai an tona, domin ban ta6a ganin mai farar zuciya da kuma son taimakon na k’asa da ita ba sai Hajiya Laila. Allah ya biyaki da aljanna ya kuma biya miki buk’atunki na alkhairi.�? “Ameen Ameen Ammi.�? Laila ta amsa tana dariya kad’an kad’an tana kallon Haydar. Ganin haka yasa yaji wata kunya ta rufesa ya gane cewa Laila tayi na’am ne da soyayyarsa, yau ina zai sa kanshi don farinciki? Akwai farin rana kuwa irin ta yau? Wani irin aikin mai kyau yayi da Allah ya saka masa da samun Laila. Wannan karon k’ara washe hakwaransa yayi wanda suke a jere kamar na yara yace, “Ammi kema yanzu kin ji kenan?�? “Dama kin fad’a masa ne?�? Ammi ta tambayi Laila cikin murna. “Anya kuwa?�? Ammi ta juya ta dubeshi farin ciki fal a fuskarta tace, “Ka k’ara godewa Allah da yake kawo masu taimaka maka a rayuwarka Ali. Hajiya Laila ta zo mini da wata magana wacce ta sakani cikin farin ciki mara misaltuwa kuma cikar burina na biyu; wato kayi aure ka hayayyafa ka tara mini jikoki. Tace ka fitar da mata nan da wata d’aya zata maka aure kuma ta d’auki nauyin komai da komai hatta gidan da zaka zauna a ciki kai da iyalinka. Yau ina zan sa kaina? Farin ciki ya mini yawa.�? Ammi ta fashe da kuka tana goge hawaye da zaninta ba tare da ta lura da halin data saka Haydar a ciki ba. “Ka shirya nan da wata d’aya zan aurar dakai da kuma Sabrin a rana d’aya. Da fatan dama kana da budurwa?�? Wani tuk’ukin bak’in ciki ne yazo ya tsaya a makwogoron Haydar, tuni idanunsa ya tara ruwa wanda ya bawa Laila dariya, sai dai maganar da yayi ne yasa ta gimtse fuskarta tamkar bata ta6a yin dariyar ba. “Ina dashi amma bazawara ce mai ‘yaya biyu.�? Ammi dake share hawaye da zaninta ta sakeshi ta fara salallamai tana tafa hannu. “Ina zaka kai bazawara Ali? Kuma ma mai ‘yaya biyu? Duk ‘yan matan Kano kaff ka rasa wacce zaka aura sai bazawara? To ba’a nan gidan ba. Ga yarinya nan mai hankali Minat, tun ba yau ba na lura da sonka take yi amma baka son kulata. Hajiya ki yiwa yaron nan fad’a, ya fita a idona.�? “Zan masa Ammi. Giyar samartaka ke d’ibanshi.�? Fad’in Laila ba tare data kalleshi ba. Hakan kuwa data fad’a ya k’ona masa rai domin d’aukanshi take yi kamar d’an cikinta. Wai ko bata san cewa shi ba yaro bane? Shekararsa ashirin da tara babu watanni biyu. “Anjima da dare ka shirya kaje gidansu ku fahimci juna.�? Bai ce komai ba ya tashi tsaye yayi hanyar fita daga gidan Ammi na kiran sunanshi. “Laa ki barshi Ammi nima haka nake fama da Abul, yaro ne ai, sai gaba zai yi hankali.�? Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta girarsa d’aya a sama kana ya fice daga gidan, a ransa kuma yana cewa zai nuna mata shi ba yaro bane komin daren dad’ewa.

Mum Fateey 👌

Back to top button