Hausa novels

Matar Hariji Page 23 Romantic Hausa Novel

Rufe Mata baki yayi yace “karki wani damu ki barni zanji da komai nidai fatana ki haifamin yarona lfy” bata kuma cewa komai ba ta kwanta ya shige jikinta yana yamutsa mata lissafi tabbas yau da bambamci da kullum.Lameer ya bata kashi taji a jikinta yaji dadin da tunda yake a duniya baitabajin irinsa ba, ya samu nutsuwar da baisan akwai irinta a duniyar bani adamu ba, Hauwah kasa motsawa tayi saboda mamakin yanayin daren nasu na yau.A cikin shekaru biyun tasu da rabi da sukayi matsayin ma’aurata bata tabajin ta kwanta da namiji ba sai yau bata taba sanin dadin shigar namiji jikin mace ba sai yau da kanta ta tambayi kanta dama haka akeji idan namiji ya dade yana sex da mace?Da wannan tunanin bacci ya dauketa tana rungume a jikinsa wannan rana makara sukayi saboda sunyi abinda basu tabayi ba a ratuwarsu sex sau biyu a dare daya kuma kowanne yabada citta yanda ya kamata.Da safe suna tashi wanka sukayi ya kalleta cikin faduwar gaba yace “zamuje ki duba Hajiya a asibiti ne?” Dagowa tayi da sauri tace “meye yake damun Hajiyan?” Numfashi ya sauke yace “kusan wata guda kenan tana asibiti nima ban sani ba sai shekaran jiya dana dawo” kwantar da kanta tayi tace “Allah sarki bansani ba wlh kuma ko Aunty Zulaiha batayimin mgnr ba”Da wannan suka tashi suka fita yajasu a mota suka tafi gdansu suka nufa gabanta na tsananta faduwa saboda takasa mantawa da ranakun nan guda biyu ranar da Muneef ya zagayo ta bayanta ya taba Mata nono da ranar da yabita kitchen a gidan mijinta zaiyi Mata fyade.Wadannan abubuwan sun cake Mata a qahon zuciya har tanajin tsoro da fargabar zuwa gidan gani take abinda zai faru kenan a gaba hakadai yayi parking ya juyo ya kalleta tare da Kama hannunta yayi kissing kuncinta ya sake mata murmushin qarfafa gwiwa yace “idan kina dari dari da parents house dinmu sai na rinqajin kamar baki yarda duk abinda ya shafeni ya shafeki ba my Hauwah”Numfashi ta sauke a kasalance tace “inajin tsoron kada abinda ya faru last zuwana ya sake faruwa ne Babe” idonta ne ya ciko da qwallah yasa harshensa ya lashe yace “babu abinda zai faru sai alkhairi kinji” daga masa kai tayi suka fita yana riqe da hannunta suka shiga cikin gdan tana kwance a jikinsa ya bude qofar parlourn tayi saurin janyewa daga jikinsa ganin Alhajinsa a parlourn da sauran iyalansa gabadaya.A kunyace ta zube a parlourn Zulaiha da da Aunty Zainab suka kalleta sukayi murmushi ita kuwa Hajiya kunya ce tasata yin qasa da kanta, Alh ne ya Kira sunanta yace “uwata” sunan da yake kiranta kenan ta dago tace “nan…naam Alh Ina kwa…na” yanda muryarta take rawa yaba Lameer dariya komai nata burgesa yakeyi musamman kunyarta.Amsawa Alh yayi yace “uwata tafi ta kowa uwata sarkin kunya taso ki dawo kusa da danki kinji “sake qunshe kanta tayi Lameer yayi murmushi yace “yar qauye da ita” dagata yayi cak ya direta gaban Alh itadai kamar qasa ta tsage ta shige Alh ya kamo hannunta yace “Alfarma zan nema a gurinki uwata kinji?” Kada kanta tayi yayi murmushi yace “zamu riqe Muftahu a gurinmu tunda qaddara ta dora mana nasan idan nace Lameer ya riqe dinma zai riqeshi amma hakan ba adalci bane gara mu rabashi da ganin abinda zaike tuna masa da baqin cikin baya ya shiga sabuwar rayuwa me tsafta da iyalansa da suke dolensa”Shiru Alh yayi inda kowa ya kasa kunne yanason jin abinda ya faru wani murmushi me ciwo Alh yayi yaci gaba da cewa “Abubuwa da dama sun faru marasa dadi wanda suka samu daurin gindin sakaliyar uwarku Lameer, nayi iyakar qoqarina akanku da tarbiyyarku alhmdllh na samu uku Mukhtar yayanka da kuma kai Lameer sai Zulaiha Zainab kuwa da Muneef dama na dade da sallama Mata su domin hudubarta sukebi ba tawaba.Wannan dalilin sakacin da sakalcin na uwarku ya kawo mana wannan gagarumar barakar nasani tun farkon aurenka da Mubaraka baka soba amma kayiwa mahaifiyarka biyayya bisa tursasawata saboda tsayin lkcn daka dauka baka tabayi mana mgnr aure ba tabbas da nasan abinda ka dade kana fada mini kenan akan yarinyar nan da dakaina zan kashe aurenku kafin zuwan wannan ranar.Ka aureta bazawara ka riqeta baka taba kawo mana matsalarta ba saidai ita ta kawo mana taka mun matsa maka mun takura maka a lkcn da kaso auro muradinka kazo ka sanar damu kanason zaka sauwaqe Mata saboda zuciyarka ta kasa nutsuwa da ita.Amma muka hanaka mukace saidai ka zauna dasu a haka to yaudai qarshen tukatukin tik mun gane abinda ka dade kanaji a ranka cin amanarka da qaninka uwa daya uba daya, cin amanarka da abokin qaninka, cin amanarka da mazan kwararo, abubuwan sun munana sun qazanta har takai anyi ciki da qaninka an liqa maka wanda Allah ya sani tun ranar dana fara ganin yaron nan Muftahu har kawo yanzu da binciken likitoci ya tabbatar da Fadwah itace jininka Muftahu ba naka bane na Muneef ne idan na kalleshi gabana faduwa yakeyi saboda tsananin kamarsu ta munana.Abisa wannan dalilin yasa na yanke shawarar baku Fadwah ku riqe a hannunku shikuma wannan zai zauna a hannunmu alhmdllh naji dadin datse igiyoyin aurenka akanta.Bullet ya shige ta gabanta a lkcn da aka harbi abokin barnar Tata qafa zaayi Mata aiki cikin satinnan idan taji sauqi ta gama iddarka zan daura musu aure suje su qarata su riqe shegen dansu a tsakaninsu…”Wata zabura Hajiya tayi tace “aa Alh kadama ka fara iri me kyau akeson yayi yado a cikin zuri’a wannan mummunan irin bana fatan cigaba da wanzuwarsa cikin zuri’ata don Allah ka qyaleta ta koma Jalingo akwai Amina me tallan awara ta gidan Idi dillali wlh gara ka aura masa ita da wannan baqar kadarar Alh kada kace aa yarinyar tafi wannan tarbiyya”Shidai Alh baice komai ba saima miqewa da yayi yace “Lameer ka rufe taron da addu’a ka dauki iyalinka ku wucce” gdy yayi masa ya rufe musu taron da addu’a sannan suka gaisa itadai Hauwah sai quqqunshe cikinta takeyi a haukanta bataso su gane cikin jikinta amma saiji tayi Hajiya tace.“Ashe matar taka ma takusa haihuwa?” Shafa kansa yayi yace “eh wlh nan da wata uku insha Allahu banmasan ya abin zai kasance ba idan na gama karbar magani qarshen watannan nakeson wuccewa America na samu aiki a Flight Emirate kuma inason tafiya dasu” Kallon Hauwah Hajiya tayi cikin kunya tace “idan ta amince sai kabarta anan idan ta haihu lfy sunyi arba’in saikazo ka tafi dasu…” Wani gumine yake karyowa Hauwah ya zuba mata ido tare dayin murmushin yaqe yace “karki damu Hajiya zan kaita gidansu ina ganin zatafi nutsuwa naga kamar ta tsorata daku”Zulaiha ce ta matso jikin Hauwah tace “don Allah kiyi zamanki damu anan Hajiya tayi nadama kuma zata baki kulawa sosai” Sakeyin qasa tayi da idonta Zainab ta matso tace “idan bazata zauna anan ba ni kabani kwangilar kula maka da ita….” Wata uwar harara daya zuba Mata tasata tsuke bakinta ya miqe yace “tashi muje duk yanda mukayi da ita zakuji” Dama kamar akan qaya take ta miqe ta zari Jakarta ta fice murmushin nadama Hajiya tayi dakanta akan wannan makirar yarinyar tasa surukarta ta arziqi tana gudunta.Yana driving din yana kallonta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin sit har sukaje wani shopping Mall suka shiga ya rinqa lodar masu kayan baby har saida ta riqe hannunsa tace “don Allah ya isa haka babe komai munadashi fa ni wani abinma bansan amfaninsa ba” zame hannunta yayi yaci gabada abinda yakeyi Saida ya gama suka fita suka nufi gda.Daqyar ya samu ya shawo kanta ta koma gurin Hajiya lkcn da zai tafi America shima saida yace Mata ai Muneef bayanan yana England ana kula da qafarsa data fara rubewa saboda Harbin da akayi masa.Haka watannin suka yita turawa kulawa ta musamman Hajiya ke bawa surukarta Alh ma komai ya gani uwarsa wannan dalilin yasa ta saki jikinta tana boffidonta a hannun surukanta, Ranar wata Laraba suna parlour Hajiya nayi Mata tsifar dogon gashinta tanata yimata surutu sunata dariya Hajiyan taji ta dauke wuta, shiru na dan lkc can kuma taga ta muskuta zata miqe Hajiya tayi saurin riqeta tace “menene Hauwah?” Qanqame qafar Hajiya tayi cikin fitar hayyaci tace “ci…cikina Hajiya wayyohh bayan….” Kamata tayi suka shiga daki ta sake durqushewa jikinta yana karkarwa tana kuka kafin Hajiya ta nemo Mata hijjab me afkuwa ta afku yaron ya sawo kai tayi kanta da sauri kafinma tazo ya fado gabadaya Hajiya tasa hannu ta dauko yaron ta yanke masa cibiya.A towel ta nadeshi ta dawo ta fara gyara Hauwah kafin wani lkc ta gama gyarasu tsaf sunkucecen yaron me masifar kama da ubansa yanata wawurar hannunsa da alamun abinci yake nema.Kiran Alh tayi ta fada masa abinda yake faruwa ya turo musu likita tazo ta dubata tayi Mata dinki saboda qaruwar da tayi ta bata magunguna sannan Hajiya ta hada Mata shayi ta fara bata tanasha a hankali tana kallon yaron hawaye na zuba a idonta so qauna da tausayin iyayenta na qara narkar da zuciyarta.Nadamar watsin da tayi da iyayenta tana nuqurqusar zuciyarta ashe irin wahalar da Goggonta Tasha kenan ta kawota duniya amma ta zabi mijinta akanta wani kuka ya qwace mata ta kwantar da kanta a kafadar Hajiya daidai lkcn da Lameer ya kira wayarta.Hajiya ce ta dauko ta daga ta miqa Mata ta miqe ta fice, ajiyar zuciya yayi yace “Yau Ina cikin farin cikin da bantabajin irinsa ba Hauwah nasan baby na baiyi kama dakeba dani yake kama saboda nasha wahala a daren da zan bakishi alhmdllh alhmdllh alhmdllh Hauwah don Allah ki shafamin kansa kiyimin kissing lips dinsa kafin nazo insha Allahu jibi zan taho” shassheqar kukanta yasashi yin shiru da kalamansa yace “meye kikeyiwa kuka?” Cikin shassheqa tace “yau… Yaushe zaka kaini gurin Goggona?” Dariya yayi sosai yace “sai yanzu kika tuna da ita da kikaji abinda akeji ko?”………….

Back to top button