Hausa novels

Gargadar So Chapter 72 By M Shakur

Har dare party akeyi bamatasan yaushe aka sai generator agidan ba, itafa komi yi akeyi batasan ya aka samu ba dan su Ammi sun daina sata a lissafi maybe Khaleel yakawo, wanka tayi Munawwarah ta turareta ganin su kadaine adakin tace “Ibrahima yadan rage miki jaraban ko”? Kunya kama Hawwa tayi ta sauke kai kasa da gangan taba Hawwa wani magani a cup dudda Ammi tace adakata a daina bata haka Hawwa tasha tana tane baki suka gama komi tawuce taje gado, yau su Ramla ma sun sauka kasa daga ita sai Noor, Noor is so happy kaman ba yar gidan masu kudi ba, Ramla sun mata wanka tasa kayan bacci suna wasa kowa na son yarinyar she’s so sweet, abubuwan da aka samata a box ma bataci ba, tuwo da miyan kuka da aka dafa agidan taci cikinta kaman zai fashe saida Hawwa tama hanata ci ta hakura.Kiranta Khaleel yahauyi awaya taki dauka, tai lamo tana sauraron su Hafsa dake planning dan gobe bridal shower kanninta sai planning suke tana kallonsu ita yar kallo ce kawai.Washe gari Alhamis aka fara baki yan uwa da abokan arziki, yan uwan su Baba daga kauye sunzo wayanda ko bikin su Hafsa ma basu zo ba amman anzo na Hawwa, yan uwan su Ammi ma haka sunzo yan Bauchi kuma sun nunama Hawwa tanada dangi, sun kawo waina tundaga Bauchi, ga yan uwan Baffa ma mijin Ammi duk ya gayyacesu duk anzoma Ammi biki, gida ya kachame abubuwa kawai ake kawowa drinks, menene, menene, banda girkin dasu sukayi Juzzyfabevent suma sunyo abinci cus they also handle catering services, babu kalan abincin da babu, kowa dazaizo yanada gifts, ko yaushe akai wannan planning din oho yan uwanta suma kowa ya gayyaci mutanensa da friends nasa, Aminu ma ya gayyaci abokansa na school dudda babu daurin aure akwai event.Wuraren 4 aka shiryata makeup artist tazo Hawwa sai kallon ikon Allah take dan batasan daga ina takeba kowa yaturota akama Hawwa makeup aka shiryata cikin gold gown kunga Hawwa aka fara rawa kawayen kannenta ne kawayenta dan batada kowa ga DJ, ga masu hoto ga MC, ga jama’a ga abinci akai wasa akai quiz akan amarya aka gama games na balloons, it was fun, Hawwa tagaji still taki waya da Khaleel.Yau Friday budan kai a hall za’ayi tun around 1 motoci luxurious bus na yan gayu sukai layi a unguwan kai mutane zuwa venue ga kaya an kawoma duka kanninta ashobe harda su Noor ga kayan Ammi na yan gayu, kasa daurewa Hawwa tayi tace “waya muku kayan nan”? Doddo tace “mijinki duka harda kayan ranan asabar yama kowa da takalma da jaka, wasu ma’aikata sukazo suka aunamu muma mu zama yan gayu” shiru Hawwa tayi aka shiryata cikin wani traditional clothes na atampa blue light and dark daya mata bala’in kyau ga katon lullubin atampa da aka dauramata akai, da Ammi tashigo taga Hawwa sai hawaye yataru a idanunta duk yanda taso ta daure saita fashe da kuka Hawwa tafashe da kuka itama Ammi tace “inama Mamanki na raye taganki Hawwa kinyi kyau Allah miki albarka, Allah sanya albarka a aurenki” kankame Ammi tayi da kyar aka hanata kuka aka gyara makeup din kafin finally aje asata awani arnen sabon jeep gal aka tattafi Umma kawai aka bari agida da Baba, Event aka fara harda yan uwan su Khaleel but banda Mom but Maman Sam da Hajiya Daraja na wajen, duk wanda yazo daga side na Khaleel dadan korafinshi Khaleel na auren yar gidan talakawa ya auro da akaga Hawwa sai ayi shiru cus Hawwa ta hadu ba karya, Khaleel carry better eye go market, chan akai annoucing zuwan ango yaye lullubi, waka aka saka na burina by Hamisu breaker saiga Khaleel yashigo yana sanye da dark blue yard da babban riga dayamai kyau na bala’i yasa hula ga manyan abokanshi Moh da Sam da sauran abokanan all in white da black huluna kana ganinsu ka ga big boys, mic yarike yana murmushi yana kallon Hawwa yafara mata wakan yana nunata da hannu filled with love ba kunyan iyaye yace.Babban burina ki kasanche dab da niIn za ki kirga masoya ne ki sanyo daniKi duba kan ki ana kallo na majanuniNi kuma nace indai kai naki ne ban fadi baSako ya bayyana ni tun daga zuciyaSannan kaunar ki tana kaman zuciyaKin kama mini kurwa ta tun jiyaHar ya kai matsayin bana samun lafiya….. yawani nuna kirjinshi yace Kin shiga rainaKin zauna dan kin sami guriNaji kirankiNa amsa kuma nazo da wuriKece farko kuma kece karsheBishiyar nan tai girma wadda kikayi mini dashe daidai ya iso gabanta yawani duka yana kallon fuskanta yanuna kanshi yace Bana ji bani gani bana son mai kusheBuri na rayu dake har numfashin karsheKin rikita duka tunani naTaimaka ki bani gurin kwanaSon ki ya hana mini bacci naIna ganin ki har a mafarki naSon ki yanai mini dadi ban son mu rabuKi jaddada jarumta ta ki nadan kambuBani da komai sai keIna tafe ya wa wani falkeIna duhu ki kunnan haskeIna na je dake?Ihu akahau yi na bala’i awajen na Khaleel is super romantic, he’s just madly in love da Hawwa, yamika hannu Moh yabude jakan LV dasuke rikeda shi yafara zubama Hawwa dollars Mom Sam tarike baki da sauran kawayen Mom like dama Khaleel ya iya soyayya haka? Ya iya wakan hausa haka wat? Rufe Hawwa sukayi da manni shida abokanshi, MC tace “abudemai fuskan amarya” Babban Aminiyan Ammi Anty Lami ta zo tabudemai fuskan Hawwa fuskan Hawwa da Khaleel yagani kawai saiya rungumeta baimasan meyake ba zokaji ihu DJ yasaka musu kida MC tace “Ango fito da amarya ku taka” dayake kamu ne wakokin hausa ake sawa komawa baya su Moh sukayi Hawwa bataso ta tashi amman haka Khaleel yadagata yana rungume da ita kunya ya gama kasheta, yafito da ita dance floor kanta akasa daidai DJ na sakin beat yasaka wakan Mai kishina na Sadiq Saleh kaman Khaleel aka samawa kawai kama hannun Hawwa yayi yawani jawota jikinshi yakama waist nata ko kadan baida kunyan iyaye, Hawwa namai wani irin kallo da jama’a ke gani na soyayya ne but shi yasan na haushi ne dana mehaka, yawani lumshe mata idanu yana daga mata gira daidai anfara wakan yace”uhm UhmmmmmmmmmmmmmmUhmmmmmmmmmmmmmmUhmmmmmmmmmmmmmmkunga inajin dadiinajin dadi na samu muradin raina tana kishi na nidaikunga inajin dadi inajin dadi na samu muradin raina ya na kishi na nimaUhmmmmmmmmmmmmmmUhmmmmmmmmmmmmmmsonki ya fattatakenii harna durkusa shiya addabeni haryasa na fallasa Ni Dake mu raini so takai mu kyankyansa nayi binciken kamarki babu na rasa” woooo haukacewa akayi a hall din kawayen Mom su Hajiya Daraja da Mom Sam suka taso ana ciro bundle na kudi dan Khaleel da Hawwa sunyi kyau, abokannan shi suka taso su Ammi da Jama’anta suka taso dan Khaleel yabama Ammi sababbin kudi dayawa bana wasaba tai manni cus itace Maman Amarya, Khaleel ganin an tattaso za’azo kawai yawani bude babban riganshi yajawo Hawwa cikin jikinsa yarufe babban rigan da ita yana rawa.Tundaga kan Abokan Khaleel da family shi babu wanda yataba ganin Khaleel this happy, su Moh at first sun dauka this marraige is just to teach the police girl a lesson but yau different abu suke gani a idanun Khaleel cus this is love! Khaleel has never been this happy, sosai Hawwa take kallon Khaleel ganin farin cikin dayakeyi and he looks damn handsome bata taba ganinshi da manyan kayaba sai yau.

Back to top button