Zakuna Biyar Page 13 By Princess Teema
Jim kaɗan ya fito daga toilet ɗaure da towel, a nan ya ji jiniya ta karaɗe ko’ina a hotel ɗin, alamar jami’an tsaro sun ninka yawansu kenan. Body lotion na kamfanin STARS BODY LUSH da hotel ɗin ke amfani da shi ya shafa tare da buɗe drawer, ya ɗauko wasu kaya tamkar shi ya ajiye. Shirinsa ya yi a natse, gabaɗaya ya canza tamkar ba shi ba, ya cire pChinese face ɗinsa, yanzu ya fito da fuskan European, still dai nose mask na face ɗinsa. Kayan da ya ɗauko ɗin tail coat ne masu balain kyau da ɗaukar hankali launin white, ya yi kyau matuƙa, kai kace meeting zai shiga da shugaban WORLD SYSTEM.Bayan ya kammala ya ɗauki jacket ya mayar jikinsa, sai tashin fitinannen kamshi yake yi, sannan ya fito, kai tsaye ya nufi elevator, ƙasa ya sauƙo, nan fa ya ga jami’ai ta ko’ina, already an buɗe hanya saboda jami’an da suka zo sun tsinci hankey ɗinsa mai ɗauke da tambarin IRON FIST, dan haka an san su ne suka yi kissan, ba sai an wahalar da shari’a ba, already an san ba zasu kamu ba, shiyasa kawai aka buɗe hotel ɗin.Motarsa ya ɗauka ya fito daga hotel ɗin cike da kwarin gwiwa. Ya ɗan yi tafiya kamar na mintuna biyar, sai ya dakata a saman wata babbar gada kusa da wata bene da ake ginawa ba’a gama ba. Fitowa ya yi daga cikin motar hannunsa rike da jakar guitar mai shegen kyau. Saman benen kololuwa ya haura, bene ce mai hawa goma. A nan ya zauna tare da fito da drinks ƴar karama a kwalba, ya ɓalle bakinta, kaɗan ya yi sipping tare da ajiyeta a jefe jikin window ɗin da yake tsaye. Zuge zip ɗin jakar ƙasa ya yi, a maimakon ya fito da guitar sai ya fito da dalleliyar sniper gun, shegiyar bindiga da bata saɓa saiti, yawancin manyan terrorists sun fi amfani da ita, kat ce ita, ta kware a iya harbin nesa, bullet ɗinta na da mugun gudu, dan bullet ɗinta na gudun 1000km a kowani second ɗaya, shiyasa ba’a iya kauce mata, in an harba sai ta sama ne kawai, dan rufe ido a sake buɗewa ya fi bullet ɗin sniper ɗaukar lokaci.Tsabar Lion ya yarda da kansa da kwarewarsa a aiki, bullet ɗaya ne a cikin bindigar, kafa bindigar ya yi a jikin window ɗin da yake tsaye, yana facing babban hanya ne, amma ta gaban in da ya baro motarsa, motarsa na baya saman gada, shi kuma sai ya tsaya ta gaba, hanyar kamar round haka take.Gyara bindigar tsab ya yi, intently ya ɗauki drinks ɗinsa ya ɗan yi sipping tare da ajiyewa kafin ya sanya kansa a mahangar bindigar, ya ɗana kunamarta, after kamar 20 second ya saki harbi wanda ya tafi kai tsaye sai tsakiyar gidan baya na motar jami’an da suka baro star hotel a yanzu, motoci biyar ne a wajen, biyu a gaba biyu a baya sai ɗaya a tsakiya, to na tsakiyar ya harba, wanda kuma ba kowa bane a ciki face IG na ƴan’sanda.Mayun saiti ake magana, su Lion basu taɓa harbi an saɓa saiti ba, idan suka yi fa dole a tafi! Kwakwalwar kan IG ya tarwatsa, kuma motocin jami’an suna gudu sosai fa, amma ya harta ta fasa kan IG. Yana harbin ya naɗe kafar bindigar ya ɗauketa ya maida cikin jaka, tsabar yarda da kai bai tsaya tantance bullet ɗin ta samu abin hari ko bata samu ba? Shin abin harin ya mutu ne ko da sauran numfashinsa? Dik bai bi ta kan wannan ba, dan yasan in dai ɗaya daga cikin IRON FIST suka yi harbi fa to an gama ne.Ɗaukar jakar ya yi, ya bar ɗrink ɗinsa a wajen ya nufi ƙasa. Daidai zai sauƙa ya dannawa su Champions alamar ja zubar jini kenan. Ya gama aiki ba. A daidai lokacin da suka samu saƙon nan suna ƙoƙarin shiga wani gida na shaggun tantiran karuwai, idan kuna ji ana karuwai to daga kan wannan gida an rufe kofa. Suma sun canza fuska daga na korea da suka sanya ɗazun zuwa na Asia, cike da takun jarumta suka shiga wajen, sai tashi sauti ake yi ta ko’ina, maza da mata an sha an bugu sai rawa ake yi. Ai suna shigowa mata suka fara tururuwan zuwa jikinsu. Sai dai dik wacce ta dimfarosu sai ta ja da baya, domin kuwa kwarjininsu firgita zuƙata suke yi, bare yadda suka ɗaure fuskan nan, dik wacce take a cikin maye sai da ta wastsake idan ta nufosu. Ko sau ɗaya basu ɗaga ido sun ga kowa ba, suka nufi sama, dan karuwan dake ƙasa ma ai iskancinsu kaɗan ne tin da da kaya masu ɗan nauyi a jininsu, karuwan dake saman daga pant sai bran da iya nipples ɗinsu ya rufe suka sanya. A farko haurawa sama suka tsaya suka kama ɗaki ɗaya a zuwan zasu kwana da ƙaruwai, tsabar sun shahara har da yin oder karuwai guda shidda, guru uku Champion uku kenan, watau mace ɗaya ta masu kaɗa. Tsala-tsalan ƴan’mata suka zaɓa tare da bada lokacinsu, wai karfe 1 na dare matan su samesu a ɗakin. Daga nan suka karɓi card suka wuce room ɗin bayan an basu farashi sun biya. Suna shiga suka fara rage kayan jikinsu, guru ya hau fito da wasu chemical daga aljihun jacket ɗin jikinsa, cikin kwarewa ya fara haɗa Chemical ɗin, shi kuma Champion ya wuce ya shiga toilet. Yana shiga ya haye sama, wajen fan da ake yi a tsakiyar pop dake baiwa toilet iska ba irin iskan Ac ba, kun san iskar Ac bata kaɗe warin abu sai dai zuba sanyi, shiyasa a manyan wurare basa amfani da ita, sun fi yin amfani da wata sabuwar technology na wannan fanka da ake yinta a tsakiyar pop, tamkar babban bolb na wutar lantarki haka, kuma idan kuka kallah in ba kun lura ba zaku zaci Ac karama ce, da tsari dai suke yinta. Ita Champion ya hau kwancewa bayan ya kasheta. Daga kan yadda yake aiki zaku san ba yau bane farau a kwance irin wannan fanka, ya kware, dan a take ya ware notikanta dikka ya ajiye, sannan ya buɗeta, a hankali ya sauketa ƙasa, ya cireta gabaɗaya, sai ga hanya ya huda a wajen tamkar in an cire cilling ɗaya a ɗaki.Yana sauƙeta sai ga guru ya shigo rike da Chemical ɗin a hannunsa, miƙawa Champion ya yi. Karɓa ya yi tare da matsawa ya bashi hanya. Hayewa sama guru ya yi, cike da kwarewa da yarda da kai ya shige ta cikin wajen, sannan ya zuro hannunsa ya karɓi chemical ɗin tare da wata ƴar karamar kwalbar acid, daga nan ya fara jan jiki cikin cilling ɗin ya tafi. Shi kuma Champion ya dawo cikin ɗakin ya kwanta a saman bed ɗinsu yana jiran dawowar guru.To mu ɗan yi duba kan yadda aka yi Lion ya kashe Minister. A daidai lokacin da ya buge wannan jami’i, in baku manta ba ai ya ware hannunsa dan bawa jami’in hakuri ko? Bayan ya bashi hakuri sun juya zasu wuce ne hannunsu ya gogi na juna, da gangan Lion ya ɗan matsa ya shafi hannun jami’in. A lokacin da suka kaiwa Minister abinci wannan jami’i shi ya sauke kayan abincin daga saman plate, ya jerewa minister a gabansa, sannan shi ya fito mashi da spoon daga kwali, da wannan hannu nasa da suka shafi juna da Lion. Karfin gubar da Lion ya yi amfani da shi ko taɓa cup aka yi da hannun da aka taɓa gubar aka goge hannun, idan wani ya sha abu da cup ɗin sai ya mutu, dan balain karfi gareta, a shegen kaifin kwakwalwarsa ya auna cewa wannan jami’in idan sun isa wajen Minister shi ne yake ta hannun dama, dan haka shi zai yi serving Minister, shiyasa ya bugesa da gangan.Minister na karɓar wannan cokali da aka fitar mashi daga kwali ya fara cin abinci kenan gubar ta ratsa jininsa, dan gubar tana da karfin gudu ne fiye da yadda kuke zato, cikin ƙanƙanin lokaci ta kewaye jininsa gabaɗaya har ya fasa ɓargon ƙashi, spoon biyu ya ci bai kai na uku ba ya fara aman jini. To kun ji yadda aka yi, shi kansa jami’in da ya yi serving abincin ya mutu, saboda ya tattaɓa sassar jikinsa da hannun, musamman fuska, ya shafi fuskansa, a take gubar ta huda jikinsa shi ma. —————————— Kwanciyar 5 mins Champion ya yi sai ga guru ya dawo. Miƙewa Champion ɗin ya yi, ya dawo cikin toilet ɗin, a natse ya mayar da fankar ya ɗaure, suka wanke hannayensu a toilet ɗin tare da shiryawa suka fito waje. Reception suka nufa, card ɗin suka miƙa masu tare da cewa akwai sayayyar da zasu je su yi, zasu dawo nan da 30 mins.Manager ya amsa da to tare da karɓar card ɗin. Daga nan suka wuce suka fita. Basu zame ko’ina ba sai gida, dan sun gama aikin da zasu yi a wannan waje, wasu manyan mutum suka shirya aiki a kansu. Kun san manyan mutane idan zasu yi meeting suna samun wajen da ba za’a taɓa zaton suna wajen bane, koda ace mutanen kirki ne mutanen, suna ɓadda kama dan meeting, yanzu kunga ai babu wanda zai zargi mutumin kwarai zuwa gidan karuwai! Kunga zasu samu damar yin meeting ɗinsu a natse.Wasu manya ne su uku suke zaman tattaunawa kan yadda za’a kawo karshe IRON FIST, manyan ɗaya daga ciki ma babban soja ne, sai Minister na tsaro da wakilin shugaban ƙasa. Shi ne fa suka shiga ta cilling ɗin nan, a tab fankarsu na toilet ɗin ɗakin da suke meeting ɗin guru ya zuba acid a cikin wannan chemical ɗin, take hayaki kaɗan-kaɗan ya fara fita, shi ne ya dawo suka tafi, wannan hayaki nan da mintuna goma zata kewaye ɗakin nasu, kafin su farga ta kewayesu, in kuma suka shaƙa ko sau ɗaya ne zasu fara aman jini, daga nan minti uku ya yi yawa su wuce lahira. Su guru suna kula da dik motsin gwamnati a kansu fiye da yadda gwamnatin ke nemansu, dik wani take-taken jami’ai a tafin hannunsu suke, dik wata ƙullah-ƙullah da shirya yadda za’a yakesu da ake yi suna sane, wannan meeting ɗin sun san da za’ayi shiyasa suka fito da shirin gamawa da su, wai a hakan gwamnatin ta yi dabara, sun zo gidan karuwai meeting, a tinaninsu ai babu wanda zai zaci suna wajen, har da ɓadda kama na sanya fuskan boge dik dan kada a ganesu, basu san a tafin hannun su Lion suke ba.Shiyasa hankulansu a kwance da suka haɗa komai suka fita, nan da 10 mins dai gidan karuwan ma zai rikice.A yayin da dik wannan yake faruwa ƙasa na can ta rikice, dik wani babba ana kiransa da ya koma gidansa yanzu, saboda IRIN FIST sun fita aiki. Suna ɗaukar lokaci kafin su fita aiki, idan kuma suka fita fa to a tashi ɗaya suke zubar da mutane 10 zuwa 15, in sun gama suka lafa zasu ɗauki lokaci basu yi wani aikin ba.Kwance a gida suka isko Lion, ya yi wanka yana shirye cikin sleeping dress, dogon wando da riga mai dogon hannu saboda sanyi, yana kwance saman katafaren bed ɗinsh mai girman gaske wanda suke kwana su uku ɗin. Hannunsa rike da waya yana latsawa, while makeken TV dake manne a bangon room ɗin nasu na magana, labarai ne na yadda ƙasa ta rikice a ƙasa da mintina 10, an rasa babban IG na ƙasa, anrasa babban baƙonsu daga India, ga babban soja da minister ɗin tsaro da aka rasa, uwa uba wakilin shugaban ƙasa, kunga kuwa dole ƙasa ta rikice, dare ya zama tamkar rana, hankula sun tashi.Abin da zai baku mamaki kuma dik wani Camera dake babban hanya su Lion suna da shi a computers ɗinsu, sun datsi camerorin gwamnati ba tare da sun sani ba, yanzu haka manyan ambulance sai gudun cetan rai suke yi a birnin, kuma suna ganin dik abin da yake faruwa, su kaɗai sun girgiza ƙasa bakiɗaya, suna nan cikin kwanciyar hankali su kuma. Kai su Lion fa basu fito ba sai da suka shirya!. Suna shigowa guru ya nufi toilet dan yin wanka, Champion kuma ya nufo in da Lion yake kwance. Yana zuwa ya kwanta kusa da shi tare da ciro wayansa, a sanyaye ya ce. “Yanzu nike samun wannan sako ta email”.Ya faɗa yana nuna mashi hoton da ya gigitani, hoton daddyn Noor dake tsaye a bakin ruwa shi yake nunawa Lion.Kallo ɗaya Lion ya yi wa hoton ya ɗauke kansa ba tare da ya yi magana ba. A dake Champion ya ce. “ARM company ne suka buƙaci da a kashe masu wannan mutumi, amma ni ina ganin wannan matsala ce tasu ta cikin gida, kasan kayan kamfanin BODY LUSH ta samu karɓuwa matuƙa a duniya, ta buge kowani product, shiyasa hankulan sauran Company ya tashi suke son a kawar masu da shi!”……. Kai daddyn Noor ɗin namu ake farauta fa! Ko da yake dama yadda kayan kamfaninsa ta yi suna dole ya samu makiya ta ko’ina bawan ALLAH.Shiru wajen ya ɗan yi for almost 2 mins, in a cool way Lion ya ce. “Ba zamu yi wani aiki yanzu ba, sai nan da 2 years, sai duniya ta ɗan yi shiru an manta da labarinmu, dan haka ka mayar masu da aikinsu”…….. Sanin cewa basa magana biyu yasa Champion ya yi cancel wannan aiki, ya mayar da saƙon cewa ba su da lokaci yanzu, daga nan ya toshe wannan email ɗin nasu, dik da cewa su ba’a isa a bibiyi email ɗinsu ba saboda mayun computer ne su, amma suna toshewa time to time saboda tsaro.Shiru suka kwanta kowa yana latsa wayansa, gabaɗaya hankalin Champion ya koma kan tinanin Seraph, ya fara kewanta, ya kwana biyu bai je ba. While shi kuma Lion ba zaka taɓa sanin a wani hali ma yake ciki ba, ga shi dai yana ta latsa waya.A haka guru ya fito sanye da bathrobe fara tas a jikinsa, a tsakiyar room ɗin ya tsaya yana ƙoƙarin goge gashin kansa da karamar towel fara dake hannunsa. Miƙewa Champion ya yi ya sauƙo ƙasa, toilet ɗin ya shige dan yin wanka shi ma.Ganin Lion ya kura mashi idanu yasa guru cewa. “Ya dai my guy? Na maka kyau ne yau kuma?”…… Hararansa Lion ya yi ba tare da ya yi magana ba, kuma bai ɗauke kallonsa ba. “Wai ka kyasa ne ka biya sadaki?”. Guru ya faɗa cike da iskanci da tsiya a maganar tasa.Wani irin mugun kallo Lion ya dallah mashi bai dai ce komai ba, kuma babu alamar zai yi magana……. Towel dake hannunsa ya jefawa Lion a kan fuska, ya nufi gaban closet ɗinsu yana faɗin. “Idan ranka ya biya ka faɗa mun”.Intently Lion ya same towel ɗin daga face ɗinsa tare da cigaba da kallon guru ta glass wall da ya raba room ɗin nasu da wajen closet ɗinsu, babu dai alamar zai yi magana. Shiru ɗakin ya yi, jim kaɗan guru ya fito sanye da sleeping dress irin na jikin Lion ɗin, sai tashin kamshi yake yi, kai tsaye ya nufo bed ya zo ya kwanta tare da jawo wayarsa dake gefen Lion ɗin. Sai a lokacin Lion ya ɗauke kallonsa daga kan guru ya mayar kan Champion da ya fito yanzu, shi ma yana sanye da bathrobe fari tas, hannunsa rike da towel yana goge gashin kansa.Wai kun san wani abin mamaki da su Lion ne? Tsananin son juna suke yi, ba zasu iya juran rasa mutum ɗaya daga cikinsu ba, amma kuma su sun iya raba mutane da ƴan uwansu, a lokacin da Lion bashi da lafiya hauka ne kawai guru da Champion basu yi ba, basa iya juran ko ciwo ɗayansu ya ji, kuma abokai ne fa kawai, sai dai abotarsu ta zarce kawai! Sun zama tamkar jinin jikin juna.(Su waye suka ga trailer ɗin labarin nan da na saki kafin fara posting ɗinsa? Kun tuna na ce maku abokai da ba’a taɓa ganin irin abotarsu ba?)Champion bai lura da Lion na kallonsa ba, ya wuce ya shirya cikin irin kayan jikinsu, sannan ya dawo in da suke. Yana isowa wajen ya ɗauki remote ya kashe Tv dake magana. A tare guru da Lion suka miƙe. Ƙasa suka sauƙo, jerawa suka yi izuwa parlo dan yin dinner. Tamkar ba kisa suka yi ba fa, suka ci abincinsu a natse, babu mai magana a cikinsu kamar kurame. Bayan sun kammala suka miƙe sai ɗakin da zakinsu yake a kwance. Sai da suka duba lafiyansa sannan suka wuce zuwa room nasu, suka yi amfani da light control suka kashe wutar gidan, sannan suka kwanta. Asuba ta gari. ————————🔥STAR LADYKwance take a saman bed a room ɗinsu, yanzu ba jimawa suka dawo daga class, da yake suna exams ne sai suke tashi da wuri. Ta afka duniyar tinani da damuwar sun kusa yin hutu, shikenan zata rabu da Rimsha, za kuma ta koma wannan kuntataccen gida da Champion yake kaita ita kaɗai tana rayuwa kamar mayya, ta tsani a yi hutu wlh.Shafa fuskanta Rimsha da ta shigo yanzu ta yi, a ɗan firgice ta miƙe zaune, ganin Rimsha yasa ta saki ƙayataccen murmushin da ya kara fito da tsantsar kyanta, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. “Sis ina kika je?”…….. Rimsha dake zama a gefenta ne ta amsa da. “Tinanin me kike yi ke kuma?”……. “Tinanin ankusa hutu zamu rabu”. Ajiyar zuciya Rimsha ta sauƙe, idan akwai wacce bata so a yi hutu to tana ganin a biyo bayanta, ta tsani komawa gidansu wajen waɗan nan mugayen Uncles ɗin nata. Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Rimsha ta katse masu shirun da cewa. “Ina zanenki yake?”. Take murmushi ya ƙara bayyana a kan fuskan Seraph, har ƴan kyawawan hakwaranta suka bayyana a waje, farare kal dasu, tamkar bata taɓa cin wani abin ba, kamar audiga. Jawo school back ɗinta dake wajen drawer ta yi, nan ta fito da cardboard paper and pencil ɗinta. Ware shi ta yi, take wani kyakkyawan zane ya bayyana, zazzaro idanu a kan zanen Rimsha ta yi, cikin zolaya ta ce. “Da ace dik abin da muka zana shi zamu rayu da shi mana, da kin more over sis”. Ɗan dariya mara sauti Seraph ta yi kafin ta ce. “Da kuwa ni kam na more ba, ke me kika zana ne ma?”……… Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. “Ni waye na sani idan ba uncles ɗina ba, Uncle Faryan na zana”……. “Ban ga amfani sakamu zane ba”. Star lady ta faɗa tare da fara nannaɗe nata zanen.”Sister lady faɗa mun gaskiyar yadda aka yi kika yi wannan zane? Ban yarda dake ba, kina ga matashin da kika zana tamkar ba mutum ba!”. A cewar Rimsha da ta dakatar da ita daga ƙoƙarin naɗe paper ɗin….. Ɗago ido ta yi suka kalli juna, sai ta kuma ta sauke da cewa. “Kawai zanen ne ya zo mun kaina na zana”. “Wlh ban yarda ba, ko dai saurayinki ne?”…… “Saurayi kuma?”. Ta faɗa da alamar mamaki. “E mana, idan ba saurayinki ba kin manta ranar da uncle James ya ce mu yi zane a class wannan matashin kika zana, yanzu ma madam Rohisha ta sanyamu zane kin sake zana shi, dik yadda aka yi kuna da alaƙa”. Ɗan taɓe baki star lady ta yi kafin ta ce. “Ni ban san shi ba, kawai zanensa nike yi”…….. Karɓar zanen Rimsha ta yi, ta zuba mashi ido na ƴan sakanni kafin ta ce. “Dik yadda aka yi yarinyar nan kin saba zana wannan zane sosai, ki duba wannan bashi da banbanci da na uncle James da ya bamu muka zana ranar”…….. “Rimsha, ni fa ban iya wani zane bane sai wannan shiyasa kowani work na zane da za’a bamu shi zan zana in dai na mutane ne”. “Kenan yanzu tsakanina dake akwai ɓoye-ɓoye?”. Rimsha ta tambaya cike da rashin jin daɗi abin da star lady take yi mata, tana da zurfin ciki da ɓoye abubuwa sosai, har yau taki ɗaukarta a matsayin ɗaya suke. Ganin ta ɓata rai yasa star lady ta ce. “Sorry sis, for give me, zan faɗa maki waye shi to”.Rimsha yarinya mai sanyin hali, take ta sauko ta ɗan yi murmushi game da cewa to ina jinki. Gyara zama lady ta yi tare da cewa. “Wannan shi ne kaɗai Uncle ɗin da nike da shi a duniya, brother ɗin mammyna ne, ban ma san in da yake ba, kawai na taso ne da kaunarsa a zuciyata, tin ban iya magana ba nike kallon hotunansa a ɗakin mammyna, da na fara wayau ta ce mun shi ne kaɗai kanin da take da shi, kila watarana zan haɗu da shi, lallai in san cewa shi garkuwa ne a gareta da bi bakiɗaya, ya taimaka mata a lokacin da duniya dikka suka juya mata ba, shi ya zama silar zamanta komai da ta zama a yau, shiyasa kika ga na iya zanensa sosai, hotunansa a gidanmu sun 100, mammy tana son shi sosai, amma fa ba ainahin kaninta na uwa ɗaya uba ɗaya ba, kanin daddyna ne, zamansu ya yi kyau ne yasa ta ɗaukesa tamkar kani, ko an tambayeta kaninta take cewa ba kanin daddyna ba, shiyasa nike son shi matuƙa, ba zanensa ba kome zan iya yi a kansa”. Da iya gaskiyarta ta yi maganar. Siririn murmushi Rimsha ta saki tare da cewa. “Ko dai ko dai”…… “Ko dai me?”. Ta faɗa tana harararta. “Ko dai son shi ya kamaki?”. …….. “Brother ɗin daddyna ne fa, the same Father the same mother, aikin ga babu soyayya a tsakaninmu, da aka ce akwai damar yin soyayya to idan na girma zan yi aure shi kawai zan aura”.Yara da su sai manyance da iyayi ga shegen wayon tsiya.Note sunan Seraph ni na yanke sunan, ainahin sunan Seraphina ne, saboda saukin kira yasa nike sauƙaƙa maku ta hanyar yanke sunan.Murmushi Rimsha ta saki tare da kara ware zanen da kyau tana kallon kyakkyawan fuskansa, uhm batun haɗuwansa ba’a magana. Cikin zolaya Rimsha ta ce. “Har na ji zuciyata ta buga a kansa, ya haɗu sosai, shiyasa dik in kika yi zanensa sai kin cinye marking kin barmu a baya, dole in koyi zana shi ni ma ko dan samun marking, kuma ba karya ya haɗu, zan rinƙa zanensa in manna a bangon ɗakina a gida”. Harararta Seraph ta yi tare da kwace zanenta, a natse ta ce. “Uncle ɗina bai yi arha har haka ba, mutum ne mai tsada da darajar da ta fi lu’ulu’u, ba zan bari ki koyi zana mun shi ba, dan nasan har cikin toilet sai kin yi zanensa, yanzu fa shi ne uban da kawai nike da shi a duniya, ina fatan in haɗu da shi a nan kurkusa”…… Tana rufe baki sai ga Aana ta shigo room ɗin, gadonta ta nufa tana faɗin. “Seraphina daddy ɗinki ya zo, wai ki je”. Wani irin faɗuwar gaba ta ji, jikinta take ya yi sanyi saboda har yau tsoronsu take ji, dik da wancan zuwansa ya tausasa mata, ya kalleta da kulawa har da runguma, amma murɗaɗɗun mutane irin wannan ba’a gane in da suka dosa. Naɗe zanenta ta yi tare da maida shi cikin jaka, tana hararar Rimsha ta ce. “Mu je ki rakani”.Zazzaro ido Rimsha ta yi kafin ta ce. “Uncle ɗinki na jikin hoton nan ne?”… Kai ta girgiza alamar a’a tare da cewa. “Wannan wani ne, zan baki labari, mu je”……… Sauƙowa ƙasan bed ɗin ta yi, ta wuce gaba Rimsha ta rufa mata baya, kai tsaye suka nufi parking lot, dan yau ko office na director bai je ba, yana cikin mota a zaune. Excuse ta yi mashi tare da buɗe front side, ta shiga tana ƙoƙarin matsawa Rimsha ta shiga ya rufe kofar da kansa. Lokaci guda ta ji babu daɗi, dan ita tasa Rimsha ta rakota, wannan kamar cin fuska ne ai, sam bata ji daɗi ba. Baya Rimsha ta koma ita ma, cikin rashin jin daɗi ta juya ta koma hostel ɗinsu, da kallo Seraph ta bita har ta kurewa ganinta, da yake akwaita da saurin kuka sai idanunta suka cika tab da kwallah, take violet ɗin suka ciza sosai.Ƙasa-ƙasa ta ce. “Good afternoon daddy”. Ta faɗa a daidai lokacin da hawayen da ya cika mata ido ya hau zuba. Sai da ya ɗauki good 2 mins kafin ya amsa da. “How’s your day?”. Ya faɗa tare da juyo da kallonsa gabaɗaya a kanta. Shiru ta gagara amsawa. Intently ya miƙa hannunsa ya ɗago haɓarta, ya yi mamakin ganin tana kuka, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya kasa, dan ba zai iya shareta ba a yanzu da ya gane wacece ita, sake haɓarta ya yi ya kama hannayenta dikka biyu da hannunsa ɗaya, jawota jikinsa gabaɗaya ya yi, ya ɗagata cak ya ɗaura a saman laps ɗinsa tare da ciro hankey daga aljihunsa. Hawayen ya fara goge mata a natse kafin ya ce. “Why are you crying Seraphina?”…… Kai ta shiga girgiza mashi alamar babu wani dalili. Hannu yasa ya kwantar da kanta a saman faffaɗar kirjin nan nasa, ya ɗan yi shiru tamkar mai tinanin wani abu, ita ma shiru ta yi tana shaƙar daddaɗar kamshinsa. Almost 5 mins suna a haka kafin ya ce. “Ya school?”…….. “Lafiya”. Ta amsa. “Akwai abin da kike so ne?”. Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. “Please daddy idan an yi hutu kada ka kaini wancan gidan da kake kaini ni kaɗai ɗin, babu daɗin zama”…….. “Nima yanzu bana son in kaiki in da zaki yi nisa dani, zaki zauna a gida tare dani”……. Dik da tana balain tsoron gidansu, amma sau dubu gara shi a kan gidan da yake kaita ta zauna ita kaɗai, ko ba komai a gidansu zata ji motsin mutane. Dan haka sosai ta ji daɗi tare da ɗan rungumesa kafin ta ce. “Thank you daddy”. Yarinta fa kenan, har ta mance da ta taɓa jin tsanansa a ranta, kuma fa lokaci guda ita ma ta jisa a ranta, dik yadda aka yi suna da alaƙa ta jini mai karfi, irin wannan abu jini ne ke fusgarsu. Sun jima suna tattaunawa, dik da bashi da yawan magana, amma ya daure ɗaya biyu suka ɗan yi hira, sannan ya ɗauko cartoon-cartoon na su chocolate, biscuits, har da su sweet sosai ya bata. A ɗan shagwaɓe ta ce. “Daddy Madam ta hana mu cin kayan zaƙi fa, wai cikinmu zai yi ciwo”…….. Ɗan zuba mata ido ya yi, lokaci guda kwakwalwarsa ta fara tariyo mashi lokacin da take jaririya cikin towel a kwance, a ransa ya ce. “Ba zan taɓa manta lokacin da aka haifa mana ke ba, da hannunsa Lion ya ɗaukeki ya yi maki huɗuba da sunan da Seraphina ba, bayan tafiyansa Mammynki ta dage sai Seraphina take son a kiraki”. Katse mashi tinanin ta yi da cewa. “Daddy zaka koma da su sweet ɗin ko?”…….. Kai ya ɗan girgiza tare da cewa. “Ki je da su, babu wani ciwon da cikinki zai yi, ai baki girma ba”…… Shiru ta yi, a ranta ta ce to zancen waye zata ɗauka? Na Madam ko na daddyn nata?Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce. “Ki ce wa Madam daddynki ne ya ce ki zo da sweets ɗin”…….. Da okey ta amsa tare da kwasan kayan ta fito. Bayanta ya bi da kallo har ta kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya tada mota ya wuce, ita kuma tana shiga room ɗinsu kai tsaye wajen Rimsha ta nufa. A gefen bed ɗinta ta zauna tare da cewa. “Sorry sis”. Miƙewa zaune Rimsha ta yi tana faɗin. “Nevermind my lovely star lady, daddyn nan naki akwai zafin rai da faɗa, amma ba komai”……. One side smiling ta ɗan saki kafin ta ce. “Wannen kikeso a cikinsu, zaɓa zan baiwa su Aana saura”. “Ke fa to?”. Rimsha ta tambaya. “Waɗan da ya kawo mun last two weeks ma kinga basu kare ba, kawai wannan zan baku ne”…….. Hannu Rimsha ta sanya ta ɗauki guda biyu ta bar saura kwali huɗu, dama shidda ne….. “Daddyn nan naki yana sonki sosai”. Cewar Rimsha. Uhm kawai ta ce tare da kwasan saura ta baiwa su Aana, daga nan ta koma gefen bed ɗinta ta zauna tare da fito da littafanta zata fara karatu. —————————-🔥To ku zo mu bi kowani jami’i daga cikin matasan jami’an mu zuwa gidansu mu ga ya suka isa ne? Ya rayuwarsu a gida bayan horo kafin su koma barrack. Daɗin abin ma dai dukkansu a Crystal Palace suke except Zaynish, dan haka haɗa kayanmu zamu yi, zaman Crystal Palace yakamamu, dole in kama mana gida ɗaya haya dani daku masu karatu, kumu je mu bararraje a can, hawa gomar dik zan kama mana, kowacce ta zo mu haɗu ai an zama dangi, to na yi gaba sai kun zo. CRYSTAL PALACE. MUHAMMAD KHAIZA’AN’S HOUSE. Idan baku fahimtar gidansu Vash kenan ba. Gida ne mai ɗauke da family guda bakwai, Muhammad Khaiza’an, ƴaƴansa maza guda uku, Faryan, Dr Aryan da ya je ɗaukar Vash a barrack, sai Harleen, sai Vash da Rimsha. Vash mahaifinsa shi ne babban yayansu Dr Aryan, ya rasu ne, mai bi mashi shi ne mahaifin Rimsha wanda momyn Rimsha ta yi breaking heart ɗinsa ya rasu.Nasan yanzu kun game karatun, da Vash da Rimsha ƴaƴan wa da ƙani ne, mugun Uncle ɗinta da kuke ji tana ambatar nan ba kowa bane face Aryan, ya tsaneta saboda ya fi kowa shaƙuwa da daddynta kafin mom ɗinta ta shiga rayuwansu ta rabasu da shi na har abada. A dalilin rasa mahaifin Rimsha yasa Muhammad Khaiza’an ya karfafa dokar haramta soyayya a zuri’arsa, dama can ya haramta auren soyayya, a dokarsa sai dai shi ya zaɓa maka mata, a cewarsa auren soyayya dik yaudara ce, dik yadda aka yi a lokacin samartakansa an taɓa yaudaransa.Haka yaransa suka tashi basama soyayya, mahaifin Vash da Mahaifiyarsa ba auren soyayya suka yi ba, daddy Muhammad Khaiza’an ne ya haɗa auren, kuma suka zauna lafiya har ALLAH ya basu Vash, sun koma ga ALLAH sanadin haɗarin jirgin sama da ya yi sanadin rayuka da dama. Shi mahaifin Rimsha bijirewa mahaifinsa ya yi, suka kullah soyayya da mahaifiyarta tin a school, ya kafe lallai shi ita zai aura, ba yadda Abbansa bai yi ba, ya ce wlh idan ba ita ba kashe kansa zai yi, cikin fushi Abba ya amsa da ya je ya aureta amma shi babu ruwansa, kuma ba shi zai nema mashi aure ba.Sai da su Arya suka dinga rokansa, sannan ya hakura ya nema mashi aurenta, daga karshe dai ta ci amanarsa, ta haifi Rimsha tana jaririya ta ajiye mashi ita ta tafi bayan ta kwashe mashi makudan kuɗaɗe, ko shayar da yarinyar bata yi ba, Abba ya yi takaicin hakan, ya dinga faɗa, a lokacin kuma daddyn Rimsha ya yake jiki ya faɗi yana faɗin shi a kira mashi matarsa, har lokacin bai daina kukan sonta ba, daga nan Abba ya ce ko bayan ransa bai yafe ƴaƴansa su yi auren soyayya ba, wai sai auren haɗi, ya zaɓa maka da kansa, ya aura maka a kawo maka ita ɗaki kawai!A taƙaice dai soyayya haramunce ga ahalin Muhammad Khaiza’an…… Kun san me mutane na? Wani diraman da za’a buga a cikin wannan ahali ba? Uhm sai shiru kawai, ku dai mu je ciki, ahalin haramta soyayya kenan, ko ya za’a kaya? Ga su dai da zaratan maza, su Vash da auren haɗi, jama’a you will love this part and laugh over.Zaune Faryan and Harleen suke a parlo, kowannensu danna wayansa, matasa ne da basu rufe 30 years ba, yayansu Aryan shi ne mai 32 years. Sun yi nisa cikin abin da suke yi sai ga Rimsha ta sauƙo daga upstair, sanye take da silky pj’s a jikinta, a lokacin da su Vash suka dawo daga horo Rimsha tana gida kenan, sun dawo hutu suma, kada ku manta a ɓangaren rayuwarsu a makaranta da rayuwarsu Lion na koma baya ne dan in faɗa maku yadda suka rayu, dan haka iya rayuwarsu ta makaranta ce muke baya, bana son ku rikice shiyasa na sake yi maku bayani!.Ganin su Harleen a parlo yasa ta sha jinin jikinta, ta fasa zama tare da juyawa zata koma sama. A natse Faryan ya ce. “Rimsha lafiya zaki koma?”…… Idanunta a kan Harleen, muryanta na rawa ta ce. “Babu komai uncle”…….. “Zo nan”. Ya faɗa yana mata alama da hannu. In baku manta ba dama na faɗa maku uncle ɗinta Faryan ne kawai yake sonta. Jikinta na ɗan kerma ta karisa sauƙowa ta nufosu…… “Don’t come here!”. Muryan Harleen a kaifafe ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta kalli Faryan da ya kirata, narai-narai da ido ta yi tamkar zata yi kuka. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. “Zo abinki, rabu da uncle Harleen ɗin nan da mugun halinsa”. Gagara motsawa ta yi, dan tana tsoronsa sosai, a gidan daga Aryan a waɗan da take tsananin tsoro sai Harleen. A daidai lokacin wani dattijo ya sauƙo ƙasan, irin dattawa masu kwarin nan ne, da karfinsa, yana rike da wata sanda mai kama dana mulki yana ɗan dogarawa, kafarsa ɗaya a ɗan karkace ne, karaya har biyu ya taɓa samu a ƙafa shiyasa yake ɗan ɗingisa kafar yake kuma yawo da sanda.Hannunsa rike da wani littafi mai suna The Franklin scandal yana karantawa. Hannun Rimsha ya kama tare da nufar su Harleen, kun san da cewa shi ma a farko ya ki Rimsha? Ya ce sai dai a kaita gidan marayu, dan wlh Abba yana da mugun zafin zuciya, sai da Ammie ta dinga lallaɓasa, kun san uwa, ba zata so jinin ɗanta ya walaƙanta ba, ta dinga bashi hakuri tana tuna mashi faɗar ALLAH da yake cewa laifin wani baya shafar wani, sannan ne ya aminta ya yafe ya kuma rike Rimsha, da gidan marayu zai kaita.A saman sofa kusa da Harleen ya zauna yana faɗin. “Harleen wai ba zaka daina takurawa jikata a gidan nan ba ko?”……… Shiru Harleen bai yi magana ba, sai ma yunkurawa da ya yi zai miƙe ya bar wajen kenan suka ji alamar motsin buɗe kofa. Dikkansu kai kallonsu wajen suka yi. A natse Aryan ya shigo cikin parlon bakinsa a ɗauke da sallama, daga ɓangarensa ya fito, fuskan nan tasa tamkar hadari, a ɗaure tamau. Ai Rimsha na ganinsa ta watsa da gudu ta yi sama, dan ta san shi ko Abba baya iya dakatar da shi a kan tsanar ganinta da ya yi, a kan ya ja mata bala’i ya karyata gara mata ta gudu ai. Tana haurawa sama suka ci karo da Vash da ya tashi barci a yanzu, jiya basu taso da wuri ba sai mangrib suka baro AZURE, cikin dare suka iso, shi ne yake ta barcin gajiya, tin da ya yi sallar asuba ya mai da barci sai yanzu ya farka.Tsawa ya daka mata game da cewa. “Baki da hankali ne kike yi wa mutane gudu a cikin gida haka?”. Kara shiga ruɗu ta yi, sai kawai ta fashe da kuma mai tsuma zuciya. Abinku da soja, to shi da zuciyarsa kamar dutse ina zata tsumu? Wani tsawan ya sake daka mata kan ta wuce ta bashi waje ko ya yi ball da ita. Ai tin bai gama rufe baki ba ta wuce da gudun gaske ta nufi room ɗinta. Siririn tsaki ya ja tare da wucewa ya sauƙo ƙasa cikin zafin nama……. Jama’a a irin wannan gida ta ya za’ayi Rimsha ba zata fi son zaman school ba?.Saman gadonta ta faɗa tare da fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya, tana jin tsanar kanta na ratsata, sai ta ji yau dai ta tsani mom ɗinta da ta ja mata wannan tsana, ita me laifinta. Cikin kuka ta ce. “Ni me laifina? Me na yi maku? Ni ɗaya nike da mom ne?”. Daga bakin kofa Faryan ya amsa da. “Baki da laifin komai Rimsha, kuma ba ɗaya kuke da ita ba, kawai zafin zuciya ce da riko irin nasu Yah Aryan, amma ki kara hakuri everything is nearing its end”. Ya faɗa tare da shigowa ciki. A gefen bed ɗin ya zauna, da sauri ta tashi ya faɗo jikinsa tana rirriƙesa tare da fashewa da sabon kuka, cikin kuka take faɗin. “Uncle kai da Abba and Ammie ne kawai masu tausayi a gidan nan, su uncle Aryan har Yah Vash basu da tausayi, kowa baya sona, shi ma Yah Vash ba kamar da ba, a baya idan ina kuka yana rarrashina, amma yanzu sai faɗa da tsawa, haka da asuba da na bugesa ban sani ba kamar zai dokeni…….”. Kukan da ya ci karfinta ne yasa ta dakata da yin maganar. Cikin tausasawa ya ce. “Vash yanzu ya zama soja, dik wani sanyin halinsa ya tafi, sai kin yi hakuri da shi kin ji? Su Yah Aryan kuma watarana zasu gane baki da laifi su daina kyararki”. Cigaba da kukanta ta yi bata sake yin magana ba, dan jin zuciyarta take yi tamkar zai fashe ne.A can parlo kuwa, Abba ne ya ce. “Aryan zo nan”. Ba musu ya je ya zauna kusa da Abba, shi kansa Abban shakkar yi mashi magana a kan Rimsha yake yi, saboda ya san zuciyar Aryan shi ya gado, ga balain kafiya kamar kafurin farko, tin da ya furta ya tsani Rimsha fa dole su yi hakuri kawai su kyalesa, in ya juya baya juyuwa ne. “Ina son ka kaini asibiti anjuma a duba mun kafarunan dake kafata ɗin nan, dan na fara jin canji”. Abba ya faɗa ba wai dan hakan ya so faɗa ba, so yake yi ya taushesa ya ce ya rage tsanar Rimsha, amma kwarjinin ɗan nasa yasa ya canza maganar.STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥


