Uncategorized

Abban Sojoji Page 49 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

**********

zaune take agaban mirror ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar material blue colour mai kyan gaske, rigar tabi shape ɗin jikinta daga can ƙasa yayi ƴar baza tamkar mermaid haka shape ɗin ya bada,hoda ta ɗauka tana shafa ma fuskarta, bayan tagama ta ɗauki jan baki red colour ta murza, ba ƙaramin kyau tayi ba, set na brushes ɗinta ta ɗauko ta gyara eye brows ɗinta,bayan ta kammala gyara gashin giran, ta ɗauki ribbom ɗinta data ajiye saman mirror ɗin, tattara sumar kanta tayi tana kiciniyar ɗaure gashin amma sam tagaza saboda yawan da yayi,ita kanta tayi mamamkin yarda gashinta yake toho,ba ƙaramin tsayi yayi ba ga yawan gaske dami guda dashi,bakomai ya jawo hakan ba face mayukan da take amfani dasu na gyaran gashi sun amshi kanta sosai,

   Sakin gashin tayi ya tarwatse a bayanta,saboda gajiyar da tayi da ruƙon shi,hannu takai cikin jerin perfumes dinta ta dauki kwalbar turaren flower bomb wanda junaid ya ɗaukar mata a lokacin da suka je siyayya saboda shima yana da irin shi, shiyasa ya haɗa mata dashi don suyi anko, 

   feshe jikinta tayi da turaren ko’ina ya ji, nan take daddaɗan ƙamshinsa ya gaure ko’ina na ɗakin gaba ɗaya,mayar da kawalbar turaren tayi bayan ta kammala fesa wa, sannan ta zuba ma madubin ido tana kallon fuskarta,fuskar sgr ta dinga gani acikin mirror ɗin,nan take ta tuna lokacin da ta watsa a guje zata bar ɗakin ya biyota da gudun gaske tare da ruƙota a jikinshi,tafin hannunta tasa tare da rufe fuskarta tana faman sakin murmushi,sake tunawa tayi da lokacin da ya yage rigar jikinta kai tsaye ya afka mata,nan take taji wani irin sanyi da kasala sun rufar mata,gaba ɗaya fa sehrish ta shiga yanayi cike da shauƙi take tariyo duk wani abu da ya faru da ita a daren jiyan ta shagala sosai, taji knocking daga waje, muryarta cike da kasala tace”Wanene”? 

.muryar Azmee tajiyo tana cewa”Auntynki ce,” jin hakan yasa sehrish tashi tare da ƙarasawa ta buɗe mata ƙopar,tana a tsaye jikinta sanye da jallabiya ta mata maroon colour, ta yafa mayafi akanta ba ƙaramin kyau tayi ba,

  sakin baki tayi tana kallon Sehrish kafin tace”Masha Allah, irin wannan kyau haka? sai kace sabuwar amarya,kinyi kyau sosai,”murmushi kawai sehrish ke saki,

   matsa mata hanya tayi tare da cewa”Aunty azmee ki shigo daga ciki mana,” 

  “A’a basai nashigo ba, dama nazo naji ya kuka ƙare da Omar?ina fata kin sanar dashi gaskiya? 

   shiru sehrish tayi tana tunanin amsar da zata bata,ranta ne ya bata cewa kawai ta amsa mata da eh,saboda tana da tabbacin cewa muddin ta faɗa mata cewa takasa furta sunan haroon agaban Omar to tabbas azmeen zata iya cewa zata sanar dashi ita da kanta,idan kuma hakan ya faru to tabbas itama azmeen zata fuskanci irin abunda sehrish ta fuskanta wurin Furta sunan Haroon,kuma bazata so hakan ya faru ba don ba ƙaramin raɗaɗi taji ba,. 

  Sam ta tafi duniyar tunani taji muryar azmee ta katsa ta da cewa”Lafiya kuwa naji kinyi shiru baki ban amsa ba”?. 

   cikin sauri sehrish tace”aunty azmee na sanar dashi gaskiya kuma yace zaiyi bincike akan haroon ɗin,” 

  “Kin tabbata”? ɗaga kai sehrish tari alamar eh,

  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa”kayan sunyi maki kyau sosai Allah,” murmushi sehrish tayi tana sunnar dakai,

   Azmee ta kuma cewa”Munyi magana da junaid akan kayan nan naki da aka kai ɗinki,yace mun tailor din ya kammala ɗinki shi zaije ya amso maki kayan,” cike da farin ciki sehrish tace”ngde sosoe aunty azmee na,” 

  Murmushi azmee tayi tare da kai hannu taja kumatunta tace”bani zaki godemawa ba, ko kin manta waɗanda suka bada kuɗi akayi maki siyayyar ne”? 

  girgiza kai sehrish tayi tare da cewa”a’a ban manta ba,amma ina jin kunyar zuwa inyi masu godiya,”

   “Gaskiya yakamata kije kam,zasu ji daɗi sosai su son cewa kinji daɗin abunda sukayi maki,ki same su kiyi masu godiya,” 

  “Insha Allah zanje,” ta amsa mata, sakin kumatun nata tayi sannan ta juya zata futa, har ta ruƙe ƙopar zata buɗe ta jinkirta kamar mai tunanin wani abu, sake juyowa tayi tare da kallon Sehrish dake a tsaye tace”wai nikam akwai abunda nake taso in tambayeki tuntuni sai in ta mantawa,” 

  cike da kulawa sehrish take kallonta don jin me zata ce,

  Cigaba da cewa tayi “a kwanakin baya kinyimun magana akan cewa kinason zuwa garinku domin ki duba ƴan uwanki da basa lafiya ko”? ta tambaya tana kallonta,

   A ruɗe sehrish tace”ƴan uwana kuma aunty azmee? Su wa kenan ? ni ba muyi wannan maganar ba kodai kin manta ne”? 

  hararar wasa azmee tayi mata tare da cewa”banason wasa fa, kinsan me nake magana akai mana, nan kwanaki kikazomin kina kuka kina cewa in taimaka maki kije kiga ƴan uwanki shine kuma yanzu zaki ce mun har kin manta? 

  Hankali tashe sehrish tace”aunty azmee ni bani da wasu ƴan uwa, bani da kowa wlh, bansan akan me kike magana ba,” 

   mamaki ne ya kama azmee ganin yarda sehrish ta haƙiƙance akan cewa bata da wasu ƴan uwa kuma fuskarta babu alamun zolaya,bayan ita da kanta ta sanar da ita game dasu,

   ɗaure mata fuska tayi tare da cewa”banason rainin hankali sehrish!kina nufin dama baki da wasu ƴan uwa!ƙarya ce kawai kika shirga mun?tun farkon zuwanki gidan nan aiki, kika sanar dani cewa ƴan uwanki ne basu da lafiya shiyasa kikazo neman kuɗin da za’ayi masu aiki, har na ranta maki kuɗi dubu ɗari tara domin ayi masu aiki a amatsayin kuɗin aikin ki na shekara ɗaya da rabi, shima wannan duk plan ne kika tsara mun !!!!?  Rai a6ace azmee ke magana hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, tuni idonta suka soma zubar da hawaye saboda tagaza gane kan me azmeen ke magana akai,. 

   “Aunty azmee wlh ni duk bansan anyi wannan ba! Bamu ta6a magana dake akan cewa ina da wasu ƴan uwa ba,kuma ni ban amshi wasu kuɗi ba saboda ayi ma wasu aiki ba…..’ 

  tunkan ta ƙarasa maganar azmee ta kwatsa mata tsawa tare da cewa”Ya isa haka Sehrish!!ashe dama ke maƙaryaciya ce!! kin cuce ni kinyi mun karyar cewa kina da ƴan uwa,ashe duk tsara ni kikayi saboda ki samu kuɗi,danasan haka kike da tunfarko ban yarda dake ba, wlh sehrish kinban mamaki kuma na gama yarda dake…….’ tana kai ƙarshen maganarta, a fusace ta juya zata bar ɗakin cikin sauri sehrish ta ruƙo jallabiyar jikinta,muryarta na rawa cikin kuka tashiga cewa”wlh aunty azmee bansan komai game da abunda kike faɗa ba,na rantse maki da Allah wlh bani da wasu ƴan uwa aduniyar……’

Karanta>>> Taswirar Ƙaddara Complete Novel Document

  girgiza kai azmee tashi ga yi tana cewa”wlh kin ban mamaki sehrish,bansan haka kike ba ae da tun farko ban bari kin fara aiki agidan nan ba!!kin cuce ni kin rushe duk wata yarda da nayi maki,sai faman rantse rantse kikeyi mun ko tsoran Allah bakiji,” rai a6ace azmee tayi maganar tare da fusge rigarta daga riƙon da sehrish tayi mata, cikin sauri tasa kai ta fuce daga ɗakin,

  A wani irin yanayi sehrish ta zube saman guiwowinta tana faman sharara kuka,mutun ɗaya da ta yarda da ita aduniyar nan ayau ta juya mata baya akan abunda batasan dashi ba,har ga Allah ita gaskiyarta take faɗi amma azmee taƙi fahimtarta,tuni zazza6i ya fara hawa jikinta,sam tagaza tashi daga kneel down din da tayi 😭

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

    

Tun da azmee ta fuce daga ɗakin sehrish, kai tsaye ta wuce nata bedroom ɗin, shiga ciki tayi tana faman safa da marwa,ranta ba ƙaramin sosuwa yayi ba,gaba ɗaya taji sehrish tafara fitar mata arai,saboda ƙaryar da ta shirga mata,cikin ƙunar rai take cewa”kin cuce ni sehrish,banta6a tunanin zakiyi mun haka ba,natsani makaryaci arayuwata, me yasa tunfarko bata fito fili ta faɗamun cewa kuɗi takeso ba,don me za tayi mun ƙarya? 

  tuni idon azmee sun cicciko da kwalla saboda ƙululun baƙin cikin daya tsaya mata arai,daƙyar ta iya samun wuri ta zauna daga gefen gadonta tana cigaba da tunani acikin ranta,

  “ɗan adam kenan!yanzu duk yarda nake kyautatama yarinyar can sai da ta butulce mun,saboda farin cikinta nakeyin wasu abubuwan don na faranta mata,amma hakan bai hana tayi mun ƙarya ba!!idan har dagaske ne sehrish ba ta da wasu ƴan uwa ƙarya  ne tayimun,TO WAYE TASA NA TURA MA KUƊIN!!!!!!? miƙewa azmee tayi lokaci guda gabanta yashiga faɗuwa tuni taji zufa tasoma tsattsafo mata,hankali tashe tace”nashiga uku!! tabbas na tafka kuskuren yarda da yarinyar can!! meyasa tunfarko najata ajikina?kada fa ace da wata manufa tazo cikin gidan nan!!!

  abubuwa iri iri suka dinga zuwa mata acikin ranta game da SEHRISH,😥

Lamarin dae ba daɗin ji

💋BOSS BATURE💋

A 6angaren su hossana kuwa tun bayan da suka yi faɗan nan atsakaninsu,su kayi fushi da junansu,saman gado hossana ta haye tana baccin wahala bayan ta gama shan kukan nata,Jahad kuwa bayan sun gama faɗan toilet tashiga tayi wankanta,bayan ta fito ta shirya cikin riga fara off shoulder tare da dogon wando baƙi,ba ƙaramin kyau tayi ba,musamman gyaran gashin kanta wanda akayi masu a wurin saloon ya ƙara ƙawata ta sosai,

  komawa tayi ta zauna daga gefen gadon kusa da hossana, bin ta da kallo tayi sai faman sharar bacci takeyi tana jan minshari,haryanzu kayan baccin nan ne ajikinta tun na daren jiya,

   Hannu tasa tare da bubbuga bayanta a hankali tana cewa”hossana ki tashi!ko baki jin yunwa ne? 

   tsoki taja tare da juya mata ƙeya don karta takura mata, sake bugun bayanta jahad tayi tace”wai ba zaki tashi bane!? 

   buge hannunta hossana tayi tare da cewa”ki rabu dani, babu ruwanki dani,idan banyi wankan ba jikinki ne ko nawa?ko kin ta6a ganin zararre mara hankali yayi wanka ne? ni mahaukaciya ce kibarni inyi rayuwata…….’cikin kuka hossana ta ƙarasa maganar,da alama abun ya ta6a mata zuciya dama ta tsani akirata da zararriya,

  Cike da lallashi jahad tace”am really sorry hossana nasan ban kyauta ba,raina ne ya 6aci shiyasa har na gaya maki hakan,bazan ƙara ba insha Allah,” 

   tayi maganar tare da ruko hannun hossana donta tashi,fisge hannunta tayi daga cikin nata tace”pls jahad leave me alone,zuciyata ba ta mun daɗi,yaya Omar kawai nake jira yazo,”

   Murmushi jahad tayi tare da janyo gashin kan hossana tana wasa dashi a hannunta tace”faɗa mun gsky hossana kodae son yaya omar kike ne”? 

   juyowa hossana tayi tare da kallonta fuskarnan ɗauke da murmushi tace”eh ina son yaya omar sosai ke fa”? 

   jiki asanyaye jahad tace”Wani kalar so kike nufi? Na soyayya da aure? ta tambaya tana kallonta,

  hossana tace”shi nake nufi,jahad inason ya omar sosai,”

  shiru jahad tayi gabanta na faɗuwa tuni yanayin fuskarta ya canza izuwa matsananciyar damuwa,ganin hakan yasa hossana tashi zaune tana kallonta tace”jahad naga kamar fuskarki ta canza meya faru ne”? 

  cikin sauri ta basar tare da ƙaƙaro murmushi tace”bakomai hossana,ni zan wuce kitchen na shirya mana lunch,” tana faɗin hakan ta miƙe da hanzari tabar bedroom ɗin nasu,saukowa daga saman gadon hossana tayi tare da wuce wa cikin toilet don tayi bath,

   sam jahad tagaza jurewa tana fitowa daga bedroom ɗin ta wuce cikin falon tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna jiki amace,

  “dagaske ne hossana ya Omar take so?amma hossana ba ta da cikakken hankali bana tunanin tasan menene *SO* ya Allah kasa hakane saboda bazan iya jurewa ba……’ ta furta tare da kai hannunta saman goshinta,bakomai bane ya faɗo mata aranta ba face farkon haɗuwarsu dashi a asibiti,lokacin ba ƙaramin tafiya yayi da zuciyarta ba saboda yarda yake acting dinsa,kyawawan ɗabi’unsa da halayansa sune suka sa jahad faɗawa tarkon shi, ita kanta bata tashi tabbatar da hakan ba sai ranar daya sanya handkerchief dinsa yana goge mata hawayenta………..”

   tayi nisa cikin tunanin nata  muryar hossana ta katse ta da cewa”jahad nayi tunanin zanzo na sameki a kitchen ne ashe kina nan zaune,” firgit jahad tayi tana kallonta sai da ta dai²ta natsuwarta sannan tace”har kinyi wankan kenan,” ta faɗi tana kallon hossana dake nufota jikinta na sanye da gown black colour, ta saki curly hairs ɗinta ya barbazo mata abayanta, 

   Amsa mata tayi da cewa”Eh baki ga har na canza kaya ba,” ta faɗi tare da jujjuya mata donta gani,

  Murmushi jahad tayi tare da cewa”kinyi kyau sosai,” ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye tace”kizo muje kitchen ɗin atare saiki tayani aiki, muyi sauri mu kammala,”

  Amsa mata tayi da toh, sannan suka wuce atare kitchen ɗin atare,

  ***************

Zaune yake acikin motarsu Ƙirar mercedes S450,ash colour,jikin shi na sanye da kakin sojoji,sai faman duba wrist watch ɗin dake hannun shi yake lokaci zuwa lokaci,gajiyar da yayi da jira ne yasa shi ɗauko wayarshi daga cikin trouser pocket dinsa ya buga ma Jahan kira nan take kiran ya shiga bada jimawa ba Ya ɗaga kiran, tsoki ayaan yaja tare da cewa”Wai kuɗin sunƙi fidduwa ne? Nifa nagaji da jira wlh,” fuskarshi a yamutse yayi maganar,.  

  on the other hand jahan yace”Am sorry yanzu haka ma na fitowa daga bankin gani nan zuwa,”

   katse kiran ayaan yayi tare da mayar da wayar inda ya ɗaukota ya ajiye,

  Cikin ƴan mintuna saiga Jahan ya fito daga cikin bankin hannunshi ruƙe da jaka,

  Yana ƙarasawa gaban motar ya buɗe back seat dinta tare da yin wurgi da jakar ciki, sannan ya rufe ya kuma buɗe front seat ɗin ya shiga ya zauna a gefen Ayaan dake zaune a driver seat,

  “Yau dae zamu jefar da kwallon mangwaro mu huta da kuda,” acewar Jahan,murmushi ayaan ya saki yana kallon shi yace”baka ji daɗin da nakeji ba wlh,saboda a ƙagare nake da mu bashi kuɗin nan mu huta da shegen nacin nan nashi,ya takurama rayuwarmu gaba ɗaya,Haroon bai da imani jahan,” fuskarshi a yamutse yayi maganar. 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

    

   “har yau in na tuna abunda yayi mana zuciyata tafarfasa takeyi mun saboda 6acin rai,haroon ya wulaƙanta arayuwarmu,Allah bazai ta6a barin shi ba, Insha Allah ƙarshen shi bazaiyi kyau ba,” acewar jahan 

  Jinjina kai Ayaan yayi kafin yace”amma Jahan kana tunanin in muka bashi kuɗin nan zai goge video ɗin duka?am just doubting about it,don na lura ba ƙaramin shaiɗani bane,

   jahan yace “ae ba zamu bashi kuɗin ba har sai mun tabbatar daya goge videon agabanmu mun gani,” 

   “Duk da haka nidae ina fargaba wlh,” cike da damuwa ayaaan yayi maganar,

  Sun jima suna magana kafin daga bisani Ayaan ya tashi motar suka miƙi hanyar gida,babu wanda ke ma wani magana acikin motar saboda duk sun tafi duniyar tunani, gaba ɗaya zulluminsu akan haroon,

  Koda suka ƙarasa cikin gidan basu shiga da kuɗin ba,acikin motar suka barsu cikin jakar saboda tsaro, sun ajiyeta ne da nufin in dare yayi suzo su ɗauketa su kai mashi,

   Bayan sun fito daga motar kaitsaye suka shiga cikin gidan tare da wucewa bedroom ɗinsu don rage gajiyar da suka kwaso,

Sehrish

Tasha kuka kamar kamar me,har sai da zazza6i da ciwon kai mai tsanani suka rufar mata sannan ta lalla6a ta haye saman gadonta ta kwanta,ta jima tana roƙon Allah akan yasa mafarki ne ba gaske ba,abunda ya faru tsakaninta da Aunty azmeenta,gaba ɗaya jikinta baya mata daɗi saboda dama can akwai fargar haroon dake damunta ga kuma wani ciwon kan ya taso mata na Azmee,duk ita kaɗae😢

  ta jima tana juyi asaman gadon amma bacci yaƙi ɗaukarta sai ma ciwon nata dake ƙara gaba,fuskarta harta fara kumbura saboda kukan da tasha,dakyar ta lalla6a ta tashi jikinta na kerma ta wuce toilet jin an fara kiran sallar la’asar,bayan wasu ƴan mintina tafito daga ciki tana faman ƙanƙame jikinta saboda sanyin daya rufar mata gashi ta ta6a ruwa,

   wurin wardrobe ɗinta ta wuce tare da buɗeta, ta zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta ta zurata ajikinta sannan ta ɗauko carpet ta shimfiɗa,sam babu natsuwa ajikinta haka ta kabbara sallar tana karanta fatiha hawaye na wanko mata a fuskarta a haka ta kammala sallar tare da zama saman dardumar ta ɗaga hannayenta sama cikin shessheƙar kuka tashiga cewa”Ya Allah kasa aunty azmee tadawo cikin hayyacinta ta gane cewa ni ba ƙarya nake mata ba,bansan ya zanyi ba in ta juyamin baya,Ya Allah ka yayemun damuwar da nake ciki,ka kawomin sauƙi acikin rayuwata………’ sosai sehrish tashiga jera addu’o’i tana roƙon Allah akan abubuwan dake damunta,

Karanta>>> Kishi Da Aljan Complete Novel Document

   ta jima zaune saman dardumar tana tunanin maganganun aunty azmee,har lokacin tana kokwantan cewa anya Aunty azmee tana a cikin hayyacinta kuwa,

   Har kusan ƙarfe biyar sehrish bata motsa ba tana zaune zugudun,sai da biyar da rabi ta buga,sannan ta tashi jiki a mace ta cire hijabin tare da naɗe carpet ɗin duka ta haɗa ta jefa asaman gadonta,cikin toilet tashiga ta wanko fuskarta sannan ta fito ta ɗauki mayafi acikin wardrobe ɗinta ta yafa shi asaman kanta, sannan ta buɗe ƙopar ɗakin ta fito, 

  Kitchen ta wuce saboda sanin cewa suna da aikin dinner,lokacin da ta ƙarasa kitchen ɗin tuni Azmee har tayi nisa a aikin nata,shiga ciki sehrish tayi tare da tsayawa tana kallon azmee dake tsaye agaban kitchen sink tana wanke naman da ta ɗebo acikin roba,

Gabanta na faɗuwa tace”Sannu da aiki aunty azmee,” tamkar bata ji taba haka ta shareta, kusan sau uku sehrish na maimaita maganar amma taƙi amsawa,

   Jiki asanyaye sehrish ta ƙarasa gaban chopping board ganin ta jera vegetables ɗin da zata yayyanka,  hannu takai zata ɗauki wuƙa,muryar azmee ce ta katse ta da cewa”kada ki ta6amun komai! Zanyi aikina ni kaɗai kamar yadda nasaba yi lokacin da baki nan,don haka ki fuce kibarmun kitchen ɗin….’ fuska aɗaure tayi maganar batare da ta juyo ta kalli. sehrish ba,

.  cikin tashin hankali sehrish tace”meyasa kika ce haka aunty azmee?tare muka saba yin aiki amma yau ke da kanki kike korata!? 

   rai a6ace azmee ta ɗago tare da nuna mata hanyar fita tace”dan Allah sehrish ki fuce kiban wuri!aikine nace bana so ni zanyi kayana,bana buƙatar taimakon ki,

    ganin yarda azmee ke kwatsa mata tsawa yasata fashe wa da matsanancin kuka tana cewa”aunty azmee dan Allah kada kiyimun haka, nasaba dake na ɗauke ki tamkar mahaifiyata,wlh bazan iya yi maki ƙarya ba,ni bansan akan me kike magana ba,dan Allah kada kiyi fushi dani akan abunda banda masaniya akanshi,”!

  tunda tasoma magana azmee ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah,tamarasa me zatayi ma Sehrish ta huce,ƙiri ƙiri tana neman raina mata wayau,

   “Sehrish in har kinason na kuma yarda dake to ki faɗamun gaskiya waye  kika bani acct number dinsa na tura kuɗin dana baki naira dubu ɗari tara da kikayi mun ƙaryar cewa ƴan uwankine basa lafiya!!? 

  Jinkirtawa sehrish tayi daga kukan da takeyi tana tunanin wai ma ina takai kuɗin?bama wannan ba yaushe ta amshi kuɗin? 

   “Ina sauraronki”! Muryar azmee ce ta katse ta daga tunanin da ta tafi,

    girgiza kai tashiga yi tana cewa”aunty azmee kiyi haƙuri amma ni bansan me kike magana akai ba,”

   tabbas in taci gaba da sauraron Sehrish ranta zai cigaba da 6aci ne don haka tace”ki wuce kiban wuri banasan sake jin wata magana daga bakin ki,” jiki asanyaye sehrish ta juya tare da barin kitchen ɗin,

   a hankali take tafiya jikinta ba kwari,

  “Sehrish”! Muryar junaid ce ta katse ta,a hankali ta ɗago ta kalli gefen hagunta ta inda yake tunkarota,shigowar shi kenann cikin babban falon,

   tunkan ya ƙarasa ya lura da yanyinta,tsayawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta da tayi suntum saboda kukan data sha,

   Cikin sanyin murya yace”reeeesh! Meya faru ne kike kuka?

   ganin cewa bata da wanda zata faɗawa mawa face junaid tunda shine abokin shawararta, don haka ta sanar dashi dukkan abunda ya faru da ita, tsakaninta da aunty azmee

   Cike da mamaki junaid ke kallonta tamkar mai nazarin wani abu can dae yace”sehrish saboda me za kiyima aunty azmee ƙarya?meyasa zaki ce mata baki da wasu ƴan uwa? 

   gaba ɗaya sehrish tagama ruɗewa cikin tashin hankali tace”junaid wlh bani da ƴan uwa,ni bani da kowa ba ƙarya nayi mata ba,’

   harara yaɗan watsa mata kafin yace”idan har dagaske baki da ƴan uwa,to su wanene kike kira a wayata? Lokacin da kike ɗaukar mun phone ɗina batare da sani na ba?kin manta last time har na nuna maki message ɗin da ƴar uwarki ta turo a wayata?sannan har kika roƙeni akan na kaiki ki gansu? A lokacin nace maki ki bari sai babban yayanmu sun koma Us ni da kaina zan kaiki ki gansu ko shi ma duk kin manta? Ya ƙarasa maganar cike da tuhuma,

   wani irin jiri sehrish tadinga gani a indonta,a hankali tashiga furta “innalallahi wa’inna ilaihirraji’un!!!” ganin tana ƙoƙarin zubewa yasa shi yin saurin ruƙo shoulders ɗinta yana cewa”ko baki da lafiya ne”? Ya tambaya yana kallon eyes ɗinta dake a rufe,

…..daƙyar ta iya furta cewa”junaid inaso nashiga bedroom ɗina,inaso na kwanta,”

   gaba ɗaya sehrish tayi confusing ɗinshi lamarin ya ɗaure mashi kai,ruƙo hannunta yayi ya taimaka mata suka nufi bedroom ɗinta,buɗe mata yayi tashiga ciki, sai da yaga ta kwanta saman gadon sannan ya rufo mata ɗakin,

  Cikin sauri ya wuce kitchen wurin Azmee,da sallama yashiga kitchen ɗin a lokacin tana tsaye agaban gass tana motsa farfesun data ɗaura,jin muryarshi yasa ta juyo wa fuskarta babu fara saboda ruɗin da sehrish ta jefa ta aciki,

Amsa mashi sallamar tayi sannan tace”junaid kana buƙatar wani abune”? 

   girgiza kai yayi alamar a’a Sannan yace”dama kan maganar sehrish ne,ta faɗamun duk abunda ya faru,bansan meke damunta ba,ni kaina tayi confusing ɗina,” 

   “Junaid sehrish tayimun ƙarya,ban ta6a tunanin haka daga wurinta ba,meyasa za tayimun ƙaryar cewa tana da ƴan uwa,bayan ba haka bane saboda kawai ta cimma wani buri nata shine ta shiryamun plan,”! 

Karanta>>> Shakuwa Ce Complete Novel Document

   “Aunty azmee bana tunanin sehrish tana cikin hayyacinta ne!saboda nima nasan da maganar ƴan uwan nata,da wayata takeyin amfani wurin kiransu tun a lokacin baya,akwai ma last message da sister ɗinta ta turo mata a wayana,nacewa suna buƙatar taimakonta har a lokacin naso na tura masu kuɗi amma lokaci guda wayarsu tadaina shiga kwata kwata,sehrish da kanta ta nemi na kaita garinsu tagansu,nace mata Sai babban yayanmu ya koma Us sannan zan kaita amma yanzu kuma ace ta manta komai? Yyi tmbyar yana kallon azmee itama kallon nashi takeyi,

  Cikin mamaki tace”junaid naji kace tana amfani da wayarka wurin kiransu,kuma har message sun tura maka dan Allah idan wayar na’a kusa inason gani,’

   cikin sauri junaid ya zura hannu acikin aljihun wandon jeans ɗinshi ya curo wayar,dannata yashiga yi can cikin messages ɗin shi yashiga sai ga saƙon da Jahad ta tura mata,

  Ƙarasawa yayi dab da azmee ya miƙa matar wayar yana cewa”kin ganshi nan,”

  Hannu tasa ta kar6i wayar tashi ta zuba ma screen ɗin wayar ido tana karanta saƙon,

Jinjina kai azmee tayi tare da cewa”Tabbas ƴan uwanta ne,idan bazan mantaba ta ta6a ambaton sunan JAHAD da HOSSANA amatsayin ƴan uwanta na jini,amma meyasa sehrish take ƙoƙarin mantawa dasu?ko don saboda tana cikin wannan daular ne……’

  Junaid ne yayi hanzarin katse ta da cewa”i don’t think so!rishi bazata ta6a mantawa da ƴan uwanta ba saboda abun duniya,na yarda da sehrish sosai kuma nayi imanin cewa rishi bazata ta6a yi maki ƙaryaba!tabbas akwai wani abu dake faruwa ne!!amma rishi bata cikin hayyacinta!!,

.. azmee ta gamsu da bayanin shi amma har lokacin tana mamakin yarda akai hakan ta faru,

   jinjina kai kawai tayi tace”yanzu ya zamuyi da ita junaid?inaso ni nasan awane hali ƴan uwan nata suke ciki ne,saboda inaso na haɗata dasu tun a lokacin naci burin hakan,nayi alƙawarin zan haɗata da ƴan uwanta,saboda yarda naga tana shiga damuwa akansu,

   “Aunty azmee,yanzu babu halin yin wannan,in ma muka ce zamu cigaba dayi mata magana akansu to fa za’a samu matsala saboda zata iya samun ta6in hankali,amma in muka bi komai a hankali insha Allah dakanta zata dawo cikin hayyacinta wata rana,addu’armu kawai take buƙata,

   Ajiyar zuciya azmee tayi maganganun junaid sun sa ta fara saukowa daga fushin da tayi da ita,

   amsar wayarshi yayi daga hannunta sannan ya kuma cewa”pls aunty azmee karki ce zaki juya mata,ko kice zaki canza mata hakan zai iya haifar mata da damuwa,saboda ta saba dake sosai ta ɗauke ki tamkar mahaifiyarta,”

  murmushi azmee tayi tare da cewa”shikenan junaid romeo insha Allah hakan ma bazata ta6a faruwa ba,kana da hankali sosai junaid shiyasa kake shiga ran mutane,ni nagaza fahimtar rishi,amma kai gashinan ka fahimce ta,”

   murmushi shima yayi tare dasa kai ya fuce daga kitchen ɗin,

*************

Agalabaice Amal ta kammala wanke uban kayan da suka tula mata,kaf sai da ta wankesu,ba ita ta kammala wankin ba sai wuraren la’asar,da zazza6i taƙarasa shi,gaba ɗaya ga66an jikinta ciwo suke yi mata,

   ɗakinsu tashiga ganin babu kowa aciki saboda duk suna can ɗakin mamynsu hayaam da abra wadda bata jima da dawowa ba,tana jiyosu acikin ɗakin suna ta faman ciye ciyen kayan daɗin da abra tadawo masu dashi,babu wanda ya tuna da ita duk wannan uban aikin da tayi masu,shiga ciki tayi jikinta na kerma ta faɗa saman lumbutsetsiyar katifarsu,bargo taja ta lullu6e jikinta dashi,dakyar take numfashi,da wani irin hucin masassara numfashin ke fita,rayuwarta gwanin ban tausayi tun safe ko wanka batayi ba,saboda babu lokacin yin wanka,koda tayi niyyar yin wankan,sun riga da sun hanata amfani da sosonsu ko sabulun wankansu,wani lokacin in jikinta ya soma yi mata tsami,ruwa kawai take ɗiba tashiga ta watsa,daga bayane tayi dabarar yankar buhu tayi amfani dashi amatsayin soso, ba sabulu haka take gurje jikinta dashi,😭

  Cike take da tsoran karsu shigo su same ta acikin ɗakinsu,saboda sun hana ta shiga ko’ina na gidan in ba kitchen ba,shima ɗin in zatayi masu girki ne,

tana acikin wannan yanayin tajiyo murya abra tana cewa”ke!uban mi ya kawo ki cikin ɗakin mu?ba mamynmu ta hanaki shigar mana ɗaki ba!! A fadace tayi maganar,tana a tsaye bakin ƙopar ɗakin,yarda kasan photocopy ɗin aunty babba haka kamanninta suke,

  Shiru Amal tayi batace komai ba zuciyarta ce kawai ke ta faman bugawa,

  Rai a6ace abra tace”ko ki tashi kona zonan inyi wurgi dake ƙazama kawai,”

   har lokacin Amal tagaza motsawa saboda nauyin da jikinta yayi mata,jinjina kai abra tayi tare da shiga ciki azafafe don tayi wurgi da ita,har takai hannu zata fisgi bargon da ta lullu6e dashi,jin muryar hayaam yasa ta dakata daga ƙoƙarin cire mata bargon da take yi,

  Shigowa cikin ɗakin tayi tare da cewa”meya haɗaki da ita ne,naji kina ta faɗa,”?

   turo baki abra tayi tare da nuna Amal ɗin da hannu tana cewa”baki ga yarda ta haye mana katifarmu ba da wannan baƙin jikin nata duk dauda,” 

  Sai lokacin Amal tasamu damar buɗe bakinta daƙyar murya na rawa tace”dan Allah kuyi haƙuri bani da lafiya,banjin daɗin jikina,”😭

   

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

    

I need ur prayers🙏😭

Back to top button