Ruwan Zuma Page 41 Hausa Novel
(41) Washe gari k’arfe takwas na safe ya samu Laila a asibiti domin hankalinta bai kwanta cewa za’a iya hana Abul guduwa ba. Sai dai ganinshi da tayi yana bacci yasa taji sanyi a ranta ta samu guri ta zauna tana tofa mishi addu’a bayan ta sallami wanda ya kwana da Abul d’in. Kafin goma tayi ‘yan dubiya sun fara zuwa ciki har da Sabrin wacce ta taho da girkin da ta yiwa Abul. Duk wanda ya gaishe da Abul baya kulawa sai Sabrin ce itace kad’ai zata mishi magana kai tsaye ya amsa. Hakan yasa Laila ta bata breakfast d’insa da kuma maganinsa don kar yayi mata musu. Abul kuma haushin kowa yake ji a gurin domin yana ganin da bakinsu aka had’a uwarsa ta auri Haydar sannan suna goyan bayanta, duk kuma mai goyan bayan wannan aure ya tsaneshi. Ko da sun masa magana ko tambaya baya amsa musu, ko da kuwa Laila ta mishi fad’a baya ko kallonsu balle ya amsa har suka watse aka bar Laila da Sabrin kad’ai. Kamar wanda aka jeho suka ga Umma a d’akin tana kuka tayi kan Abul wanda yana ganinta ya ja tsaki. “Dama kana raye d’an nan? Ashe zan sake ganinka a duniyar nan? Yau ku duba yanda yaron nan ya zama. Hatsari kayi ne ko ‘yan fashi ne suka maka duka? Duk uwarka ce ta jawo maka wannan masifa data rabaka da ‘yan uwanka. Lamla kin cuceni kin gur6ata gudan jinina.” Maganar Umma kenan tana shafa jikin Abul kamar wacce taga ya mutu ya dawo. Sallamar Nazifi daga bakin k’ofa ce tasa Laila da Sabrin suka amsa ba tare da wani ya cewa Umma uffan ba. Bai ma fara gaisawa dasu ba ya fara yiwa Umma magana. “Umma kin mini alkawari bazaki tara mana jama’a ba, don Allah kiyi hakuri ki gaishe da yaron mu tafi.” Juyowa tayi ta kalleshi kamar zata kai masa hannu tace, “Ban san yaushe zaka yi zuciya ba Nazifi, rayuwar d’an d’an uwanka ne aka salwantar amma naga alamar kai bai dameka ba.” Kana ta juya gurin Abul wanda ke harararta dalilin ta6a mishi fuska da tayi da kuma hayaniyar da take yi tace, “Ka tashi mu tafi domin bazaka k’ara zaman gaban wannan matar ba.” “Ba gidan uwar da zan je, kuma ki daina ta6ani.” Yana fad’in hakan ya ja tsaki kana ya kwanta tare da juya mata baya domin yanzu haushin kowa yake ji gashi yana son kora kwaya ko zai samu sassauci a zuciyarsa. Baki a sake Umma ta tsaya tana kallon k’eyar Abul sannan ta juya ga Laila wacce ke gaisawa da Nazifi fad’an ya dawo kanta. “Duk laifinki ne da kika kasa bashi tarbiyya nagari, kuma kina ganin yana mini rasar kunya amma kika kasa kwa6arsa da alama murna ma kike yi…..” Bata kai ga k’arasa surutunta ba Laila ta d’aga mata gaisuwa wacce fuskarta bai nuna koda d’igon 6acin rai ba. “Umma ina kwana.” Nan ido ya dawo kan Umma wacce ta daburce tama rasa me zata yi dalilin tunda ta shigo babu wanda ya mata mummunan kallo balle maganar banza, kenan tun zuwanta ita kad’ai take masifarta babu wanda ya tanka mata. Nazifi da yake bayanta kuwa kunya game da takaici ne taff a ranshi wanda har yayi dana sanin zuwa da ita bayan Laila ta aika masa da sak’on an samu Abul jiya. “Lafiya.” Shine kad’ai abunda Umma ta fad’a kana ta zauna kan kujeran da Laila ta tashi ta bata. Daga nan Sabrin ta gaisheta tana amsawa sama-sama hankalinta na kan Abul daya juya musu baya. A nan ne Nazifi ke tambayar a ina aka samu Abul sannan me yake damunshi. Laila bata 6oye mishi komai ba ta fad’a mishi abunda ta sani, Umma dake gefe sai sharce majina take yi tana cewa, “Allah sarki marayan Allah, an lalata maka rayuwarka.” Bayan Laila ta gama magana Nazifi ya fita zuwa waje bayan yayi kiranta, a gaba da k’ofar d’akin suka tsaya ya fara bata hak’uri kan abunda Umma tayi musu. “In da sabo yaci ace na saba da halin Umma. Babu komai wallahi.” Ta bashi amsa. “Yanzu yaya ake ciki? Wace shawara kuka yanke kan yaron.” “To…. munyi akan cewa zamu kaishi Maiduguri ne gurin kawuna domin ana kai mishi fand’ararrun yara irin haka yana musu rubutu da kuma magani. Nan gaba kad’an dai idan cutan da yake damunshi yayi sauk’i zamu kaishi can d’in.” “Hakan yayi Allah ya shiryeshi. Amma idan kuna da buk’atar wani abun ku mini magana in bayar da daidai k’arfina. Halin da yaron nan ya samu kanshi a ciki nima sai in ga kamar da laifina dana kasa tsayawa a kanshi a matsayin uba. Ina jin takaicin hakan domin ubanshi bazai ji dad’in ganin yaron haka ba.” Tunda Laila take zata iya cewa wanann shine karo na farko data ta6a ganin nadama a idon Nazifi, in bata manta ba bayan rasuwar Marigayi Aliyu har dashi a shirin Umma wajen kwato su Abul, saboda yazo mata da zancen aure ta nuna bata so yayi k’ok’arin blackmailing d’inta cewa duk ranar data auri wani bashi ba zai kwace yaran saboda baza suyi agolanci a gidan wani ba. Allah mai juya lamarinsa, wai yau Nazifi ne ke bata hak’uri? “Komai ya wuce sai dai muyi addu’an Allah gyara mana na gaba. Amma ba sai ka kawo komai ba, idan aka tashi kaishi Maiduguri sai kuje tare kuga inda yake saboda kuma ku sauk’e hakkinsa dake kanku. Kuma nagode da k’ok’arinka Allah ya shige mana gaba.” “Amin Amin. To ni zan wuce gurin aiki, gobe Insha Allah zan zo in kara duba jikin nashi.” “To Allah ya kaim….” Laila bata k’arisa maganan ba suka jiyo ihu a d’akin da suka fito. Cikin firgici suka koma ciki Laila na fatan ba dai Abul bane ya mutu, ganin Umma a tsaye bakinta a bud’e ga kuma Abul zaune a kan gado ya tayar da jijiyar wuya yana huci yasa suka fara tambayar ba’asi. Sabrin wacce tun zuwan Umma ta kimtsa kanta guri d’aya dalilin bak’in halin da Umman take nuna mata tamkar ba jikarta ba ta fad’a musu yanda aka yi. Wai Umman ne take ta yiwa Abul tambayoyi shine yace ta barshi, data k’i shine yayi wannan k’aran kamar zai d’age musu d’akin. “Abul baka da hankali ne? Me amfanin hakan kenan? Maza ka bata hak’uri kuma bana son inji ka sake haka.” Laila ta kwa6i Abul tana jin bak’in ciki a ranta domin ta lura kamar kayan mayen ya fara ta6a mata kan d’anta. Umma kuwa tun kafin Sabrin ta gama bada labarin ta koma kusa da Nazifi don ba k’aramin girgiza tayi da ihun Abul ba, domin ta d’auka hannu zai kai mata irin yanda ya tashi yana mata ihu a fuska. Har lokacin hannunta bai daina rawa ba sannan ta kasa cewa komai. “Mu tafi Nazifi. An juye hankalin yaron nan, domin kamar har da aljanu aka tura masa.” Tana fad’in hakan ta fice da sauri kamar ba jikin girma gareta ba. Cikin sauri Nazifi ya musu sallama yabi bayanta yana rik’e mata hannu. Sai a lokacin hankalinsu ya dawo kan Abul wanda ya fara kuka yana sauk’owa daga kan gadon. “Don Allah Mama ki barni in tafi, ko bazaki barni ba ku bani abunda zan sha. Na gaji da zama a nan kuma duk na tsaneku.” Yana fad’in hakan yana k’ok’arin yin hanyar waje Laila na tareshi. Sai yanzu rashin kwayar ya fara nunawa a jikinshi, domin yawu ne yake dalala a bakinshi yana kuka yana ture Laila wacce itama hawaye take yi tana mayar dashi kan gado. Ganin haka yasa Sabrin d’aukan wayarta ta kira Mas’ud ta fad’a mishi halin da ake ciki itama tana kuka. Duk yanda suka kai ga nitsar da Abul abun ya gagara domin yaso yafi k’arfinsu saboda duk mata ne a gurin. K’arshe sai da aka had’a da ma’aikatan asibitin aka daure hannayensa da k’afafunsa a jikin gado. Duk abunda ake yi ihu yake yi yana fisge-fisge yana 6are ciwokansa da aka manne. A bakin d’akin Mas’ud yazo ya samu su Laila kowa yayi tagumi, “Ina yake? Meya faru?” Shine abunda ya fara tambaya yana shigewa d’akin. Doctor dake kan Abul tare da Nurses suka ce ya fita suna dubashi. Bayan ya fito ne Laila ke bashi labarin yanda aka yi ta k’arishe da cewa, “Anya kuwa kwakwalwar yaron nan bata ta6u ba? Duka fa yake kai mana da duk wanda yazo kusa dashi.” Idanunta cike da hawaye. “Bana tunanin abun ya kai har haka, bari Likitan ya fito muji ta bakinsa.” Yana fad’in hakan suka hango Haydar na takowa cikin sauri. Yana isowa ya fara tambayar me yake faruwa cikin tashin hankali yana cewa, “Naga missed call d’in Sabrin, na kirata ta d’auka kuma naji hayaniya da kuka ana kiran sunan Abul. Me yake faruwa ne?” Mas’ud ne wannan karon ya fad’a mishi halin da ake ciki amma hankalinshi na kan Laila wacce ke cizon yatsarta ta kasa tsayuwa guri d’aya tana lek’en d’akin da Abul yake. Takawa yayi ya isa gurinta ya fara bata baki gami da kwantar mata da hankali, hawaye ke tsiyaya a idanunta tana kad’a kai. “Nice silar faruwar hakan ko? Nice na jawo mishi hauka ko?” Ta dubi cikin idon Haydar ta mishi wannan tambayar. “Idan akwai wanda za’a bawa laifi to nine, sai dai k’addara ta riga fata Laila, idan Allah yayi hakan zai faru sai kiga ya faru ko babu mu. Kici gaba da mishi addu’a babu haukan da zai yi Insha Allah.” Suna tsaye Doctor ya fito yace su bishi office, sannan kar su damu da batun Abul a yanzu domin yana bacci. A can ne yake fad’a musu cewa, “Rashin samun kwaya ko abunda zai gusar da hankalinsa yasa yayi haka wanda dama dole hakan zai faru. Amma idan aka cigaba da tsareshi har kwayar da fita daga jinin jikinsa zai samu lafiya ya dawo hankalinsa. Sai dai daga yau zamu k’ar6i kula dashi babu mai zaman jinyarshi sai ma’aikatanmu kwararru. Amma zaku iya zuwa dubashi idan buk’atan hakan ya taso.” Haydar ne ya dafa kafad’ar Laila wacce ke zaune a kan kujera tana fuskantar Doctor shi kuma yana tsaye a kanta. “Zamu yi shawara Doctor. Mun gode.” Fad’in Mas’ud kenan yana tashi tsaye ya fita su Laila ma suka bi bayanshi, “Ina tsoron kar mu barshi a nan ya samu damar ku6ucewa ya gudu. Kawai mu kaishi Maiduguri gobe.” Laila ta fad’a tana jingina da bango cikin karayar zuciya. “Idan aka kaishi can tun yanzu zai katse treatment da ake mishi na typhoid d’insa wanda ke k’okarin mishi lahani. Mu duba yanayin kulan da zasu bashi, idan yayi sai mu barshi in kuma bai yi ba sai a kaishi can d’in.” Wannan Haydar ne ya bada shawarar. Mas’ud da ya tattare naman goshinsa cikin damuwa da kuma tunani yace, “Shawaran Haydar d’in yafi Kalti. Abul needs his medications before anything else.” Gyad’a kai kawai tayi tare da runtse idanunta tana cizon le6enta. Haydar ne ya matsa gefe shi da Mas’ud suka yi magana kana ya dawo gurin Laila yace, “Ki koma gida, we will take it from here.” Bud’e idanunta tayi ta zubasu cikin nashi yayi nodding kanshi yana cewa, “Trust me, zamu yi duk abunda ya dace.” “Ina Mas’ud d’in?” Ta tambaya tana neman wayarta a jakarta. “Yana office d’in Doctor.” Kiran Sabrin tayi a waya wacce ke bakin d’akin Abul tace mata ta sameta a harabar asibitin. A nan ne ta dubi Haydar tace, “Nagode da kokarinka a kaina da kuma iyalina. Kana shiga damuwar da bai kamata ka shiga ba Haydar, saboda kullum rayuwata d’auke take da sabbin shafi na tashin hankali. I’m sorry.” Ta k’arisa maganan hawaye na taruwa a idanunta. “Once I’m in, I’m in for good and for worse. So ki daina fad’in haka domin nima Abul ya zama part of my family.” Hawaye ne ya silalo a fuskarta yayinda zuciyarta tayi haske da jin kalmomin Haydar. Shi d’in ya cika jarumi kuma dattijo ba ba don ya tsufa ba. Sallama suka yi ta koma gida shi kuma ya shiga office d’in Doctor don shirya yanda za’a kula da Abul. ******* Satin Abul uku a asibitin ciwukanshi suka bushe saura su k’arisa warkewa, haukan da yayi kuma har ba’a cewa komai saboda rashin kwayar da yake muradi. Laila kuwa an hanata zuwa ganinshi dalilin idan taje bata kasa daurewa sai ta zubar masa da kwalla. Hakan yasa Mas’ud da Haydar hanata zuwa gudun kar itama ta jawowa kanta wani cutan. Alhaji Abdul yazo sau d’aya duba Abul, sai dai yanayin taryan daya samu daga Mas’ud yasa bai jima ba ya tafi. Haydar ne ke tambayar Mas’ud ko lafiya ganin shi ya kamata ace ya fishi k’in ganin Alhaji Abdul. “Na tsani halinsa ne. Sannan yaso ya munafurci Kalti Allah ya ku6utar da ita domin ita ba mazinaciya bace kamar sa.” Gyad’a kai Haydar yayi domin watarana idan ya tuna yanda ya samu auren Laila sai yaji kamar mafarki yake yi zai kuma farka nan bada jimawa ba, domin kuwa ya mallaketa ne a lokacin da ya gama fitar da ran cewa zai sameta har abada. A wannan yanayin ne aka fara shirye-shiryen kai Abul Maiduguri, a wannan lokacin ne kuma Haydar ya lura Laila na yawan zama guri d’aya tayi ta tunani. Yasan duk akan Abul ne take wannan damuwar don haka yake rarrashinta game da kwantar mata da hankali. A ranar da suka dawo daga Maiduguri, Haydar ne zaune a kan kujera yana danna wayarsa yayinda Laila ke fuskantarshi itama zaune a kujera daban. Tun da yayi wanka yaci abinci yake lura damuwar nata ya k’ara yawa akan na da, don haka ya tambayeta, “Ki fad’a mini gaskiya me yake damunki Laila. Idan akan Abul ne inaga yaci ace kin kwantar da hankalinki sanin cewa ya fita daga hatsari na ciwon da take yiwa rayuwarsa barazana, sannan kwayoyin da yake sha sun fita daga jinin jikinsa kuma a yanzu ke kanki kinsan yana hannu mai kyau, za’a kula dashi a kuma kawar da hankalinshi daga kwaya ta hanyar magani, addu’a da kuma nasiha. Shin duk wannan bai kai yasa hankalinki ya kwanta ba? Kenan baki ga alamun nasara a tattare da hakan ba? Tell me abunda ke ranki Laila, that’s the only way da zan san yanda zan magance miki.” Ajiyar zuciya Laila tayi kana ta tashi daga inda take ta dawo kan kujeran da Haydar ke zaune fuskarta zallan damuwa tace,“Haydar kamar ciki ne dani.” Bai iya furta komai ba illah ido daya zuba mata don yasan wasa take mishi ko kuma tana son 6ata mishi rai ne, saboda tunda ya lura bata son haihuwa dashi ya sakawa kanshi hak’uri da dangana yana neman za6in Allah a al’amuranshi ya kuma daina kawo mata maganan kwata-kwata. To don meyasa zata kawo mishi maganar a yanzu? “Baka ce komai ba ka tsaya kana kallona.” Ta fad’i hakan tana yarfe hannu wannan karon kamar hawaye ne zai taru a idanunta. Ganin haka yasa Haydar tunanin ko maganar gaskiya ne. “Kince ‘kamar cikine’ kenan baki tabbatar ba. Ya kuke ganewa?” “Wannan watan ban ga al’adata ba har na tsawon sati biyu kuma ban kai shekarun da mace zata daina ganin al’adarta ba. Sannan Ina tsoron zuwa asibiti ko kuma in duba in ga cikin ne da gaske. Haydar ya zanyi?” Wani malulun bak’in cikine yazo ya tokare mishi a wuya daya tuna wai gudan jininsa ne take tsoron tabbatuwarsa, that’s if akwaishi da gaske. Wani irin tsana Laila take gwada mishi? “Kije asibiti ki gwada, idan cikin ne sai kisan me zaki yi saboda ni ban isa in saki ki d’auki cikina ba. Sai dai ki sani Laila, wallahil azeem da zan iya d’aukan ciki dana d’auka don kawai in tara zuriyata, sai dai babu yanda na iya amma na barwa Allah komai.” Muryarshi ce ta fara rawa ya tashi ya fice daga falon cikin sauri, daga baya sai ji tayi ya kunna mota ya fita daga gidan gaba d’aya.
Mum Fateey 👌



