Halysaah Page 203 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH 203…Bayan Khaleesat ta gama girka masu breakfast ta fito daga kitchen taga babu kowa a parlor, gashi dai ba ita bace Hadiyah amma har ta gama girki a kunyace take a kitchen, tashi tayi ta wuce sama ta nufi part din Ajay, tana ganin takalmin Jay a bakin kofa ta ki shiga parlon, taji Ajay yana cewa “Malam kai dai zaka kira ta mu ji inda take, ta yaya zaka ce in kirata bayan ba ni na koreta ba, ni fa tunda na kwanta jiya bayan isha’i ban farka bacci ba sai asuba shima saboda sallah, kai dai da ka raba dare kana ibada kai ya kamata ka kira mana ita mu ji inda ta tafi cikin snow….” Jay dake ta kallon Ajay yace “Karya kake, ni idan raba dare nayi ina ibada kai kwana kayi kana yi…” Ajay yace “A’a gaskiya, ana idar da sallan isha’i nake bacci, ko sallan dare bana tashi yanxu, sau da yawa ba kai kake tashina sallan asuba ba, amma yau ko sallan asuban ma kai baka samu kayi ba, saboda ka samu sabon ibada, shi ne zaka zo kace sai ni zan kira ta, to ai ba ni ne babba a gidan ba” Wani kallo Jay ya dinga yi masa, Ajay yaki bari su hada ido, dariya suka ba Khaleesat ta juya kawai ta bar wajen tun basu yi noticing dinta ba, bedroom din Jay ta nufa tayi knocking sannan ta bude kofar a hankali tana kallon ciki, kwance ta ga Hadiyah tana danna wayarta, Khaleesat ta karasa ta zauna gefenta tana murmushi, tun kan ta ce mata komai Hadiyah ta mike zaune tayi kasa da murya tace “Don Allah Mami tasan ina dakin nan Halysaah?” Khaleesat tace “Wace Mami, Mami ai bata gidan nan, kuma babu akwatin ta a daki” Da mamaki Hadiyah tace “Why?” Khaleesat tayi tagumi ce “Uhmm how will I know, kawai na shiga dakin in gaisheta naga ta tafi, wa ya sani ko ke da ya Jawwad ku ka korata, don dai haka kawai Mami bazata fita babu sallama ba, kuma da sassafe ana snow for that matter” Hadiyah ta dinga kallon Khaleesat babu ko kiftawa jiki a sanyaye, a hankali tace “Ta yaya muka korata kuma?” Khaleesat tayi er dariya tace “How will I know, bayan ba nan side din na kwana ba” Hadiyah ta fara kokarin recalling abubuwan da suka faru tsakaninta da Jay daren jiya, but she was lost don fargaba yasa ta kasa recalling komai da ya faru, but Jay isn’t even the type that speak out while having intimacy, amma daren jiya kam tabbas taji yayi, Hadiyah ta marairaice tace “Wallahi Halysaah har ce masa nayi ni dai na yarda mu tafi hotel zan bi sa duk don ya kyaleni cause nasan Mami’s room is close to this room amma ya ki ya saurareni, to ni yanxu don Allah da wani idon zan kara kallon Mami? Don Allah ki gaya min yanda zan yi Halysaah, da wani ido zan kalli Mami” Khaleesat tayi wani dariya har da kyakyatawa tace “Da idon da kike kallona yanxu mana, why didn’t you cover his mouth da kika ga tonan asiri na neman shigowa cikin lamarin, cikin snow fa Mami ta tafi” Tana fadin haka ta mike da sauri zata bar wajen tana dariya, Hadiyah ta rikota tace “Dama haka kike Halysaah, ki dinga wani abu kamar warce bata san komai ba ashe ke crook ce” Khaleesat ta zaro ido har sannan bata dena dariya ba tace “Wallahi ba abinda na sani kar ki min sharri, i am very innocent, I just suggest what I don’t know” Hadiyah tace “Hmm, amma where did you get those aphrodisiac da kika bani jiya?” Khaleesat ta koma ta zauna tana murmushi tace “Yana da kyau ko?” Hadiyah ta wani harareta tace “Oho” Khaleesat tace “To shikenan tunda Oho” Mikewa tayi Hadiyah ta kara rikota da sauri tace “Don Allah ki gaya min” Khaleesat tace “A’a ai sai kin gaya min dalilin tambayar ki” Hadiyah dai kallonta kawai take, sai kuma tayi kasa da murya tace “Ai maganin ne yasa har Mami ta jiyosa kila fa, don ni dai ba ni ta jiyo ba” Khaleesat couldn’t stop laughing tace “Haba dama ni dai bazan boye maki ba na zargi haka, har ke din ma ta jiyo ki you can never convince me bata jiyo ki ba, ba yayana kawai zaki lafta ma sharri ba” Hadiyah ta wani harareta, Khaleesat ta dakatar da dariyar da take tace “To maganin da Mami ta bani ne a Nigeria na taho da sauran” A hankali Hadiyah tace “Bai taɓa min reacting yanda yayi jiya ba during all the period we were married, kin san jiya bai bar ni nayi wani baccin kirki ba, ya ban wahala sosai” Khaleesat na murmushi tace “Uhm ni dai ban tambaye ki duk wannan ba, kawai cewa za ki yi anjima in baki magani ki kara sha” Hadiyah bata san sanda ta zaro ido ba tace “Waa? To har yanxu i am still uncomfortable, kawai maganin da ya ban na sha ne daxu na relieve yasa naji ɗan sauki fa” Kamar zata yi kuka tace “Yau sai dai Ya Junaid yayi hakuri wallahi i am sleeping in ur room, nothing will stop me from sleeping in ur room…” Dariya ya taho ma Khaleesat ba tare da ta shirya ba ta dinga yi, Hadiyah ta wani harareta tace “Ai kema maganin da kika sha ne yasa kika je kika makale ma Ya Junaid, da muka zo gidan nan fa ina lura dake gudunsa kike, saboda zaki min mugunta shi yasa kika tarkato magungunan kika sha wai duk don kiyi convincing dina in sha nima, sai gashi kina ta makale ma miji” Bude kofar dakin aka yi duk suka juya da sauri, Khaleesat na hada ido da Jay ta mike kamar munafuka tana kallon Hadiyah tace “To ko kawai in maki oat meal sai ki dinga sha a hankali tunda baki son Irish din?” Sosai ta ba Hadiyah dariya amma ta gintse fuska bata ce komai ba, Khaleesat bata jira Hadiyah ta bata amsa ba tace “Bari in je in maki” Da sauri ta juya ta nufi kofa, taki yarda su sake hada ido da Jay ta fice daga dakin, Jay ya karasa yana kallon Hadiyah da taki kallon inda yake, ya zauna kusa da ita yana kallonta yayi kasa da murya yace “Gulmata ku ke yi da Halysaah ko, what did you tell her?” Hadiyah ta wani kauda kai taki basa amsa yace “Kin zauna kina tona min asiri a wajen ta kenan” Nan ma Hadiyah taki tanka sa, Ya kara yin kasa da murya yace “To kin kori Mami daga gidan nan hankalin ki ya kwanta” Hadiyah ta juya da sauri ta kallesa jin abinda yace, ya daga kafada yace “Rakin ki ya sa ta tattara ta tafi bata yi mana sallama ba” mikewa yayi ya nufi gaban mirror ya dauko takarda ya dawo ya zauna, Hadiyah ta dinga kallon takardan gabanta na faduwa don takardan da ta rubuta ma Halysaah styles ne, yana mata wani shu’umin kallo yace “Style number 4 will be next” Zata warce takardan ya mike ya bar wajen, nan da nan hankalinta ya tashi taji kamar ta fasa ihu, ko dai kasheta Ya Jawwad ke son yi ne. Sai da Khaleesat ta kai zuciyarta nesa bayan ta koma bangaren Ajay sannan ta iya kiran Mami don da gaske kunyarta take ji kamar ita ce Hadiyah, bayan sun gaisa Khaleesat tayi kasa da murya tace “Mami naje zan gaishe ki da safe naga bakya nan, kuma babu akwatin ki a daki” Mami tace “Ehh kawai nayi deciding ba sai nayi rescheduling ticket dina ba Halysaah, i left for Canada” Khaleesat ta ɗan kalli Ajay dake kusa da ita yana kallonta, sai kuma a hankali tace “Amma Mami yaushe za ki dawo” Mami ta ɗan yi murmushi tace “A’a Halysaah ni ban ce maku zan dawo America ba dama, ke dai kawai ki ci gaba da kula da mijin ki kamar yanda kika saba kin ji….” Cikin sanyin murya Khaleesat tace “Mami mu ma ai zamu koma Nigeria soon” Mami tace “To Allah ya kai mu lokaci lafiya, Allah ya maku albarka, sai ayi ta hakuri da juna, zaman aure dama zo mu zauna zo mu saɓa ne, kuma ku yi ta ma mazajen ku biyayya gaba dayan ku” Khaleesat taji wani kunya ya rufeta on behalf of Hadiyah, da gaske dai Hadiyah da Jay ne suka sa Mami tayi tafiyar ta, a haka Khaleesat suka yi sallama da Mami ta juya tana kallon Ajay dake murmushi don duk yana jin abinda Mami tace, Khaleesat ta hade rai tace “Ai duk kai ka jawo, da baka kai ta dakinsa ba ai da ba ayi haka ba” Tana fadin haka tayi saurin tashi zata bar wajen ya jawota ta fada jikinsa. Wajen karfe takwas na dare Khaleesat na zaune parlon Ajay tare da Hadiyah da ta makale a parlon tun da taga yamma tayi, har ranta take fargaban gamuwarta da Jay daren yau shi yasa ma taki barin part din Ajay tun daxu, Ajay ya shigo parlon for the second time, yana kallon Hadiyah yace “Kee, tashi ki tafi sai da safe, ko daren ki bai yi bane” Ta marairaice tace “Yaya kallo fa muke yi, ka bari a gama Film din plss” Yace “In 15 mins time za a gama bana son in dawo parlon nan in sake ganin ki” Ta gyada masa kai a hankali, ya juya ya fita daga parlon, nan da nan mood din Hadiyah ya canza, ta kalli Khaleesat a sanyaye tace “Wallahi Halysaah i am afraid of another encounter with Ya Jawwad, ya ban wahala jiya sosai wallahi, har yanxu ban gama recovering ba, kuma kinga duk kofofin gidan nan ba key duk inda na shiga nasan sai ya bi ni” Khaleesat tayi kasa da murya tace “To nace ki kara shan magungunan nan yau kin ki, it’s for your own good ai, da gaske in kika saki ranki bayan kin sha maganin baza kiji wahala ba” Khaleesat ta mike tace “Ki tashi mu tafi kitchen in baki, you won’t feel any discomfort trust me” Hadiyah tace “Ashe ma Ina son abun kenan idan na sha magani” Khaleesat tace “Ai ba wai kina so ba, wahalan da kike complain ne baza ki ji ba, it will really help you” It took Khaleesat almost 5 mins kafin tayi convincing Hadiyah suka fita daga parlon suka sauka downstairs, Ajay da Jay na zaune parlon suna kallon kwallo, daga Khaleesat har Hadiyah basu yarda sun kallesu ba har suka shiga kitchen, yau ma Khaleesat haka ta tula ma Hadiyah magungunan mata ta bata ta sha, ita kuwa taki sha cause tun da garin Allah ya waye har yanxu tana jin effect din wanda ta sha jiya a jikinta, ko kallonta Ajay yayi sai taji wani iri, ko kuma idan yana mata magana, ko da kuwa normal magana ne sai ta ji yanayinta ya canza, shi yasa ta rufa ma kanta asiri taki sha yau, Hadiyah ce ta fara fita daga kitchen din sannan Khaleesat ma ta fita suka koma upstairs a tare, duk tunanin Khaleesat a corridor za su rabu da Hadiyah amma sai taga Hadiyah na kokarin sake bin ta zuwa parlon Ajay, Khaleesat ta hade rai tace “Ba yace maki ki tafi dakin ku ba dare yayi wai” Hadiyah taki tankata ta wuceta zuwa parlon Ajay, murmushi Khaleesat tayi ta bi bayanta, a haka suka isa parlon ta nemi waje ta zauna, sun kusa another 1 hour a parlon, Khaleesat ta kalli Hadiyah da ta mike tace “Sai da safe na fara jin bacci Halysaah” Khaleesat tace “Tohm, better don’t suffer ur self ki ce zaki je wani daki, kawai kiyi tafiyarki dakin Ya jawwad daga nan cikin sauki” Hadiyah bata tanka ta ba ta fita daga parlon, ba wai don tana jin baccin da gaske ba sai don kawai reacting da jikinta ya fara yi saboda maganin da ta sha, a corridor ta hadu da Jay da ya hauro sama from downstairs, zata tafi wani bedroom din yayi saurin rikota ya ja ta zuwa dakinsa, tun Hadiyah na turje masa har daga karshe ta kasa, kawai ta bada kai bori ya hau, sosai magungunan nan suka yi contributing wajen basa hadin kai, and all her actions shows how much she misses her Man, bata taɓa ganin Jay ya saukar da girman kansa yanda yayi a wannan daren ba, ta sha kalamai masu makalewa a zuciya da narkar da zuciyar, ko kadan bata nuna ta gaji da shi ba, she made sure he was more than satisfied, daga karshe ta rungume abun ta kamar za a raba su. Tun da Hadiyah ta fita parlon Ajay Khaleesat ke kwance kan 3 sitter bacci ya dauketa, juyawa taje yi wanda hakan yasa saura kiris ta fada kasan carpet, ta mike zaune a firgice tana bin parlon da kallo tana murza idonta, agogo ta kalla taga karfe daya har da rabi, ta sake bin parlon da kallo taga alamar Ajay bai shigo ba tunda babu takalminsa a kofar bedroom dinsa, ta tashi ta fita zuwa downstairs, yana kan 3 seater shi ma yana bacci ga remote a hannunsa, alamar yana cikin kallon baccin ya daukesa, sosai parlon yayi dumi saboda heater da ya kunna, ta ɗan yi murmushi ta karasa kusa da shi ta duka, a hankali ya bude ido saboda kamshin turarenta da ya daki hancinsa, ya jawota ta fado jikinsa yayi kasa da murya yace “I love ur scent Slushie” Tayi murmushi tana kallonsa babu ko kiftawa, sai kuma ta turo baki zata sauka daga jikinsa tace “To da ban sakko ba fa, shi ne zaka wani kwanta a nan ka barni ni kadai a sama” Ya riketa don kar ta tashi yace “Ina gama baccina dama zan je in sameki ai” Lamo tayi a warm body dinsa ta lumshe ido, mikewa yayi ya maidata ya kwantar kan kujera suka canza position ya cire hijab dinta yana bin jikinta da kallo, jawosa tayi ya fado kanta ta fara shafa gashin kansa tayi kasa da murya tace “Ko dai kitso zan fara yi maka?” Kissing dinta ya fara yi yana cuddling kirjinta, Sun dade a parlon yana sarrafata, TV na ta aiki shi kadai, da Khaleesat taga abinda yake kokarin yi tuni ta maido da hankalinta jikinta tana kallonsa da idanuwanta kamar me jin bacci tayi kasa da murya tana girgiza masa kai tace “Noo plss, don Allah mu tafi sama, ba mu kadai ne a gidan ba fa….” Da kyar ya iya bude baki yace “No one is coming downstairs Slushie” Tace “Nooo, ni dai plss let go upstairs, Wallahi kunya nake ji” Kawai gani tayi ya dauketa sai Laundry room alamar upstairs is too far for him at this point, sosai Khaleesat ta saki jiki suka mori juna, ko ɗan zafin ma da take ji a farko yau sam bata ji sa ba, ta bar sa yayi yanda yaga dama da ita a wajen. Da safe wajen karfe bakwai da rabi Khaleesat na sanye da hijab har kasa ta sauko downstairs zata tafi kitchen ta hada ma Ajay coffee, tsaye tayi bata karasa kusa da kofar kitchen din ba bayan taji alamar akwai mutum a ciki, after some seconds ta ɗan leka kitchen din taga Hadiyah ce, bude ido tayi da mamaki ta karasa ciki taga lafiyayyen girki take yi, haka kawai Khaleesat taji dariya ya taho mata, ta dafa gwiwa ta dinga babbaka dariya, Hadiyah ta juya ta kalleta tace “Ke wai komai sai kin yi dariya, to meye abun dariya yanxu” Da kyar Khaleesat tace “To ke wa yace maki amarya na shiga kitchen da sassafe, what are you even cooking?” Hadiyah ta jingina jikin cabinet din kitchen din ta juya mata ido tace “My husband’s favorite” Buda baki Khaleesat tayi tana kallonta with shock, wani sabon dariyan ta fara yi tace “Kawai ki ce min yesterday night was splendid” Hadiyah ta harareta tace “Idan na gama zan dafa maku ruwan shayi in gasa maku bread a toaster da ke da Yaya in case za ku yi breakfast anjima” Khaleesat tace “Ai koma meye favourite din mijinki shi ne favourite dinsa shi ma, duk abinda Ya Jawwad ya ci shima sai ya ci….” Murmushi kawai Hadiyah tayi tace “Gaskiya bazai samu da yawa ba, dai dai mijina nayi”Some weeks laterAjay ya bude kofar bedroom dinsa ya karasa ciki yana kallon Khaleesat dake kwance kan gado tana bacci, ya duka kusa da ita ya sauke bargon jikinta, yayi kasa da murya yace “Jeeddah” Da kyar ta bude ido tana kallonsa with sleepy eyes, yace “Kin zama sleeping beauty yanxu ko, haka za mu tafi Airport anjima kina bacci wife….” Miƙa tayi a hankali ta kai hannunta cikin lallausan gashinsa tana birkitawa gently, sai kuma ta rungumosa zuwa kirjinta cike da shagwaba tace “Me yasa zaka tasheni bayan ina baccina me dadi” ya kai bakinsa kunnenta yayi mata rada, maƙe masa kafada tayi ta turo baki bayan taji abinda yace, ya dinga kallonta da lumsassun idonsa, sake rungumosa tayi murya can kasa tace “Bacci fa nake ji dear, kayi hakuri pls” Yace “To yi baccin ki my love” A hankali tace “Ka gama hada min kayan ne?” Yace “Na gama ranki shi dade” Ta turo baki tace “Ni dai wallahi idan ka mance min komai sai ka dawo kasar nan ka daukar min da gaske” Yana murmushi ya ja hancinta yace “Ban mance komai ba Slushie, idan ma na mance zan dawo in dauka wallahi” Tace “Akwai fa shoes dina a laundry room ka dauko?” Ya ɗan bude ido yace “To bari aje a dauko yanxu, me kike so a siyo maki for breakfast?” Slowly tace “Nasan Hadiyah zata yi girki ai” Ko rufe baki bata yi ba aka yi knocking kofar dakin, Ajay na kallonta ya shafa tummy dinta yayi kissing flat tummy din yana kallon cikin, ita dai sai kallonsa take ganin yanda yake kallon cikinta, sai kuma ya mike ya nufi kofa ya bude, Hadiyah ce tsaye bakin kofar ta koma gefe tace “Yaya ina kwana, Halysaah ta tashi ne?” Without looking at her yace “Morning” Fita yayi daga dakin, ta ɗan leka ciki sannan ta shiga, Khaleesat ta mike zaune tana kara wani miƙan don duk jikinta is weak, ta jawo hularta ta saka a gashinta, Hadiyah na murmushi ta zauna kusa da ita tace “Kwana biyu kin yi scarce a gidan nan daga bacci sai command din Yaya kawai kike….” Khaleesat ta zaro ido tace “Ban gane command dinsa ba, kuma jiya ba tare muka yi kallo da daddare downstairs ba?” Hadiyah tace “Ji mata, ko minti biyar bamu yi da fara kallon ba kika yi bacci kika bar ni da TV” Khaleesat tace “To ni ban ma san how manage na dawo part din nan ba, kawai tashi nayi cikin dare na gan ni kan gado fa” Hadiyah tayi er dariya tace “Mijinki kika hada da aiki, nima fitowa nayi daga kitchen ban gan ki ba a parlon daga zuwa in hado tea, yanxu dai me za ki ci tunda jiya kin ce baki son breakfast din da nayi, har sai da kika aiki yaya uwa duniya cikin sanyin nan ya siyo maki abinci, shi da baya son fita cikin sanyi, ai ko sai da yayi zazzaɓi da ya dawo kina nan kina ta bacci” Khaleesat ta dinga kallonta tace “Da gaske?” Hararanta Hadiyah tayi, a hankali Khaleesat tace “Yau da na tashi kawai naji ina sha’awar cin tuwo dama mu yi tuwon yau” Hadiyah ta wani kalleta tace “Dama inyi dai, ke yaushe rabon ki da girki a gidan nan, ko hanyar kitchen bakya bi matar nan” Khaleesat ta saki baki tace “Kin fiye sharri Hadiyah” Hadiyah tace “A takaice dai yau ɗan baba tuwo yake so ko?” Khaleesat tayi shiru tana kallon Hadiyah jin abinda tace, Hadiyah tayi er dariya tace “Ya kike kallona haka” Khaleesat tace “Waye kuma ɗan baba?” Hadiyah tace “Gashi makale cikin ki ya maida ki sleeping beauty a gidan nan” Mikewa tayi ta fita daga dakin tana murmushi, Khaleesat dai ta bi ta da kallo, daxu da Ajay ya shigo shi ma sleeping beauty yace mata, ta ɗan turo baki, ita dai tasan bata da komai don bata dade da gama period ba. Tun da Ajay ya shiga laundry room Jay dake zaune parlor ya bi sa da kallo, sai gashi ya fito da shoes din Khaleesat guda uku da gogaggun hijabs dinta biyu kuma da alama shi ya goge, Ajay na kallon Jay ganin kallon da yake masa yace “Ko kayi rescheduling flight ticket din ne kake kallona haka?” Jay yace “Kai kuma a haka fatherhood din ya zo maka, ana tsaka da controlling din ka sai kuma ga fatherhood ya shigo, kaga sai abinda kawai muka gani game da kai….” Ajay yace “Kai matsala ta da kai sa ido, daga safe har yamma sai dai ka wani hakikance a gida kana muzurai, idan dare yayi ka shige daki da yarinya kana er murya, yanxu takaicin ka bana taya ka zama during the day muna ma yaran mutane muzurai ko” Bai jira cewar Jay ba ya wuce sama, Jay dai ya bi sa da kallo, can ya girgiza kai yayi murmushi don har cikin ransa tausayi Ajay yake basa yanda Khaleesat ta maidasa a gidan sai yanda tayi da shi kamar ma tsoronta yake, yanxu kuma ga karamin ciki don yasan wannan baccin da take yi a duk inda ta samu ba na lafiya bane, wani lokacin takaici yake sa Jay baya zama duk inda suke zaune, idan suka fita titi sai Ajay ya dau miskilancinsa ya dora a kai kamar ba wanda mace take juyawa ba, suna dawowa gida a bakin gate yake cirewa ya ajiye kafin ya shiga ciki, Jay ya ga abubuwa iri iri zamansu a gidan nan wanda yana jin in shi ne bazai iya tolerating ba a dai yanda halinsa yake, bai taɓa zaton akwai ranan da zai zo Ajay ya sauke duk wani ji da kansa ya zama sai yanda mace tayi da shi ba, sam bai son ɓacin ran matarsa, lallabata yake kamar something that is so fragile, yanda yake bi da ita ko kwai albarka, don dai shi Hadiyah tasan halinsa ne banda haka da sai ta dinga jin haushin baya treating dinta yanda Ajay ke treating din Khaleesat a gidan, shi dai yasan duk son da yake ma mace bazai taɓa maida kansa zuwa level dinta ba yanda Ajay yayi, he will show her love saisa saisa but not stooping so low, har ya fara tunanin yanda zai ceto ɗan uwansa daga tarkon Khaleesat da ya fada, nan kuma bai san reverse is the case ba don yanda Ajay baya son bacin ranta ita ma haka, har tafi gudun ɓacin ransa ma da lallabasa, gashi bata rage sa da komai a wajen kwanciya ba yana samun yanda yake so dari bisa dari, wannan ne yasa ake ganin kamar tana controlling dinsa, kuma a ko ina bata iya boye son mijinta ga shagwaban da take masa da kukan ba gaira ba dalili a gaban ko waye, Ajay ya zama kamar rayuwarta, tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba, ko fita suka yi da Jay ta dinga kiran sa kenan ya dawo gida, a gaban Jay ma nuna son mijinta take yanxu, ga uban kishi idan taga ya bar ta for long yana wajen Jay. Karfe shidda da rabi na yammacin ranan suka tafi Airport don Flight din su zuwa Nigeria na karfe takwas ne, tafiyarsu Nigeria ma Khaleesat ce tace ma Ajay su tafi don gobe Friday ake daura auren Safiyyah da Ya Mustapha, ko musu Ajay bai mata ba duk da baya son komawa Nigeria, ita din ma tafi son zamansu a Maryland gashi tana jin dadin zama da Hadiyah, amma she just have to show up in Nigeria for her Besty, Ajay bai gaya ma Jay Khaleesat ce tace su tafi Nigeria ba, kawai ce masa yayi su je su gaida Mai martaba it’s been long.


