Hausa novels

Zakuna Biyar Page 12 By Princess Teema

Ɗan ɗauke wuta ya yi, ya gagara yi mata reply, a can kuma tana can cike da zulumi da fargabar jiran amsa daga garesa, shi kuwa ya rasa a wani point ma yake tukun nan. Gagara danna reply ya yi, dan ya shiga ruɗani.Wai na ce kun san me ake cewa GAT kuwa? To Nigeria ma bata da muƙamin GAT, sai a manyan ƙasashe ake bada irin wannan muƙami, amma bari in yi maku yadda zaku fi ganewa kila ku gane dalilin Noor na shiga ruɗani da tashin hankali. A Nigeria muƙamin General shi ne babban kuƙami, amma a lokacin da ƙasa zata shiga yaƙi akwai wani muƙami da ake bayarwa wanda ya ɗara General mai ɗauke da 5 stars, wannan muƙami ana kiransa da field marshal, ana bada shi ne kawai a lokacin da ƙasa zata shiga yaki da wata ƙasa, rundunar da zasu jagoranci ƙasar babban da aka fitar shi ake baiwa muƙamin field marshal, bayan yaki ana cire muƙamin dan ba’a amfani da shi. Dan haka Naija dik girmanta bata da GAT!. Irinsu US sau sauran manyan ƙasashe ke amfani da GENERAL OF THE ARMY.Bari in kara yi maku bayani dan ku fi ganewa da kyau, ku san muƙamin da ake magana a kai. General of the Army yana da 5 stars ne da eagle ɗaya, daga shi sai General mai 4 stars kawai, sai Lieutenant General mai star uku kawai ba wani rank, Sai Major General mai stars 2, Brigadier General mai star ɗaya, Colonel bashi da wani star, Lieutenant Colonel shi ma ba star ba eagle, Major shi ma ba wani star, Captain yana da stars 2 kamar Major General kenan, akwai First Lieutenant mai star ɗaya, Second Lieutenant bashi da star, Sergeant Major of the Army bashi da star, Command Sergeant Major bashi da stars shi ma, Sergeant Major, First Sergeant, Master Sergeant, Sergeant First Class, Staff Sergeant, Sergeant sune suke kasancewa drivers na manyansu ko masu baiwa wani babba tsaro! Corporal, Specialist, Private First Class, Private PV2, Private PV1 dik waɗan nan basu da star, waɗan nan sune muƙaman soja gabaɗaya, to dik waɗan nan da na kirga maku fa a ƙarƙashin GAT suke, kun ga kuwa dole dik wanda ya ji sunansa in yasan me suna take nufi dole ya girgiza!.”Are okey?”. Leo dake kwance rike da waya ne ya tambaya cike da mamaki. Da sauri Noor ya diro kasan bed ɗinsa, V ta yi mashi message ya kai 5 bai iya buɗewa ba bare amsawa. Da zafin nama ya haye bed ɗin Leo, dik hankalinsa a tashe, muryansa na ɗan rawa ya ce. “Bro tashi ka ji wani abu?”. Da ido Leo ya bisa ba tare da ya motsa ba. Sanin halinsa yasa ya fara bashi labari kawai ba tare da ya jira ya tashi ɗin ba. Sai da ya kammala har karshe cike da sa ran zai ga ruɗu a kan fuskan Leo, sai ya ga ya ja siririn tsaki yana dallah mashi harara. Take ya ji jikinsa ta ɗan saki, sai kuma ya ce. “Bro ko baka ji da kyau bane? Ɗiyar GAT fa na ce!”. “Then so?”. Leo ya faɗa yana cigaba da dallah mashi harara. Shiru Noor ya yi, kwakwalwansa ta shiga doubting, anya Leo yana kan saiti kuwa? Ana maganar GAT yana faɗin then so what? Anya lafiyansa lou kuwa?.Katse mashi tinani Leo y yi da cewa. “Bana hanaka jin tsoron wani ɗan adam ba? Baka ji ko?”. Leo ya faɗa tare da miƙewa zaune……. Kada ku manta Noor yana da cutar tsoro a cikin kwakwalwansa, dole ya yi wannan rikicewa, dik da ya zama soja ba wai cutar ta rabu da shi bane, time to time tana tashi, idan ta tashi kuma yana rikicewa ya dinga jin tsoron abu, haka idan ya firgita sosai abin yana motsa mashi.Sake maimaitwa Leo ya yi cewa. “Bro I’m talking about GAT ooooo”. ……. “GAT shi ba mutum bane? Ba haihuwarsa aka yi kamar sauran mutane bane? Ko shi faɗowa ya yi daga sama da yasa ya fita daban?”. With full confidence Leo ya faɗa, dan shi wlh baya tsoron wani abin halitta face ALLAHN da ya haliccesa, ga shi da saurin fusata, dan a yanzu haka ya fusata na ganin yadda Noor ya tsorata a kan wani halitta, ya sha faɗa mashi ALLAH kawai ake tsoro haka ba wai halittar ALLAH ba, amma Noor baya ganewa, ALLAH sarki bai san cewa ba laifin Noor bane, cuta ce. Gabaɗaya kan Noor ya shiga ruɗani, sai yake jin kamar shi ne kunnuwansa basa jiyo mashi abin da Leo yake faɗe da kyau, in ba haka ba yana ganin ba zai yiwu wani ya faɗa magana da ta saɓa ta girmamawa ga GAT ba!. Call da ta shigo wayar Noor a yanzu ne yasa Noor dawo daga duniyar tinanin da ya afka, kallon wayar hannun nasa ya yi, V ce take kira, da sauri ya ɗago ya kalli Leo, while shi ma Leo ɗin shi yake kallo. “Bro ina tsoron ɗaukar wayar……”. Ya faɗa a raunace. Wani irin kallo da Leo ya dallah mashi ne yasa ya gagara karisa maganar. A sanyaye Leo ya ce. “A ina ka taɓa ganin soja da tsoro ko fargaba? GAT da kake magana ka rikice daga jin sunansa ɗin sai da ya jajirce ya cire dik wani tsoron abin halitta kafin ya taka matsayin da yake, idan ka zage watarana kai zaka ɗaura 5 star with eagle a gaban rigarka da taken GAT ɗin”. Ya ɗan dakata saboda ɗan sara mashi da kansa yake yi, Noor yana son ja mashi dogon surutu. Still dai babu alamar Noor zai kwarara kan nan nasa, ganin haka yasa Leo ya jawosa jikinsa, cikin hikima da dabara ya fara karfafa mashi gwiwa yana gwada mashi lallai dikkan wani abin halitta bai isa ya yi maka komai ba matuƙar ka yarda da ALLAH, dan haka ba GAT ba ko bakin sniper or machine gun bai isa yai maka komai ba, dan haka ya karfafa kansa. One thing da na manta ban faɗa maku na, su Noor ba musulmai bane, nasan zaku ce Noor sunan musulmai ne ai, kada ku manta ni na yanke sunan nike ce mashi Noor, amma sunansa Nooriel, dan haka ba musulmai bane, shiyasa idan Leo yana ce mashi kada ya ji tsoron kowa face ALLAH baya wani ɗaukar abin serious, dan tin farko bai yi imani da ALLAH ɗin ba, amma zamansa da Leo a yanzu yasa sosai yana jin cewa zai iya musulunta, kuma yana jin cewa lallai ALLAH shi ne mahaliccin kowa da komai, Leo bai taɓa ce mashi ya musulunta ba, yana dai yin ibada a gabansa, a haka kuma abin take shiga ransa, kun san addinin musulunci da shegen daɗi, ba sai ance maka zoka shiga ba, in dai ana ibadar a gabanka dole ka yi sha’awarta sai dai in son zuciyarka zaka bi!. Sosai ya kwarara mashi gwiwa, bai rabu da shi ba har sai da ya tabbatar ya kore mashi wannan tsoro, sannan dan ma ya kara karfafasa sai yasa ya kira V a yanzu su yi magana, saboda a cewansa idan ya kirata zai kara kwarara kansa. With his full confidence ya danna mata kira, yanzu baya jin tsoron komai.Kira ɗaya ta ɗaga, har lokacin tana zaune a balcony, ta ci kuka har ta ƙoshi, dan a tinaninta shikenan ya ji cewa ita ƴar GAT ne ya rabu da ita, ta yi ta nadamar faɗa mashi gaskiya da ta yi, har idanunsa suka yi jajir suka ɗan kumbura.Tana ɗauka ta fashe mashi da wani sabon kukan, dan zuciyarta a kusa take. Ɗago eyes ɗinsa ya yi suka kalli juna da Leo, hararansa Leo ya yi kafin ya koma ya kwanta tare da jawo bargo ya rufe har kansa. Ajiyar zuciya Noor ya sauke, slowly ya sauƙa daga gadon, da sauri ya fita zuwa balcony wai kunyar Leo yake ji. Tsayuwa a wajen ya yi tare da manna wayar a kunnensa, ya zura hannunsa ɗaya a aljihu kafin a sanyaye ya ce. “I’m so so sorry for the delay in responding to your message, wani ɗan abu ne ya ɗauke hankalina”…… Haba lokaci guda ta ji tamkar an sauƙe mata dik wani nauyin dake kanta jin cewa ba daina yi mata magana zai yi ba, amma dik da haka sai ta cigaba da kukan dan ta kara ratsa zuciyansa da kyau. “Please stop crying! Yana taɓa mun zuciya”…….. Cikin kuka ta ce. “Ni dai ka rarrasheni in kana son in yi shiru”….. Yadda ta yi magana voice ɗinta ya huda zuciyansa sosai, har wani ɗan shock ya ji, one side smiling ya ɗan saki kafin a cikin ransa ya ce. “Yau ga shi a hannun rigimammiya, wai ya rarrasheta kawai, to shi ko ta ina ya iya rarrashin ne ma?”.A fili kuma sai ya ce. “Okey me kike son in yi yanzu kenan?”…… Tana turo baki tamkar tana a gabansa ta amsa da. “Ka mun kalamai masu daɗi”……. “That’s all?”……. Kai ta jinjina tare da cewa yeah. “Okey, get ready to accept my cool and sexy words”. Da sauri ta ce. “Done, I opened all my ear, I’m listening now!”. Ta faɗa har tana tuntuɓen harshe…… “See her, rigimamma kawai, wai I’m listening, har kina haɗe words, kece auta ko?”…. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Kamar kai ba, nasan kaima ai kai ne auta”…… “Who told you?”…….. “Aunty Lisa”. Ta bashi amsa a taƙaice. Ɗan girgiza kai ya yi cike da mamakin yadda lokaci guda Aunties ɗinsa suka aminta da ita, har da bata labari. Jin ya yi shiru yasa ta fara jansa da hira da salon soyayyarta mai melting heart har bai san time da ya saki jiki ya shiga biye mata ba, suka raba dare suna hira, dan ko da su Arya suka dawo room ɗin bata daina wayar ba, sai da daddynsu ya shigo ne ta ɓoye wayar ba tare da ta katse kiran ba, Noor na jin dik abin dake wakana. Yau da yake yana da baƙi bai zauna hira da su ba, sai ya yi masu goodnight ya fita kawai. Su Arya suka tattaro laptop ɗinsu suka shiga aiki dan gyara kwarewarsu, ita kuma V ta cigaba da wayarta da heartbeat ɗinta. Sai around 3 na dare sannan ya ce su kwanta dan da safe zai wuce US, akwai sammako kenan a gabansa. Kada ku manta tsakanin Avaris da US ba nisa, suna kusa sosai.Abin ku da sabon soyayya, sam bata so su yi sallama, ita ko kwana zasu yi a haka a shirye take, amma ta hakura dan girmama buƙatarsa, suka yi sallama ba tare da ya yarda ya furta mata kalmar so ba, dik hiran da suka yi bai yarda ya furta kalmar ba, ba wai dan bata yi mashi ba, no, kawai dai ya ce tukun nan, sai ya gama sanin wacece ita da yadda take gabaɗaya. Ita ma bata damu da ya furta mata ba, a cewarta a hankali zai furta ba sai an ce ya yi ba, dan haka da suka zo yin sallama ma ce mashi ta yi take care, goodnight and have a nice dream, bata kawo zancen love ba, amma tana kiransa da heartbeat. While shi ma abin da ya ce mata kenan, have a nice dream like your beautiful face. Ta dinga murmushi jin ya yaba kyanta, a haka dai suka yi sallama, ta kashe wayar ta kwanta. A yayin da dikka hakan ke faruwa shi kuwa GAT ya je sun sha hira da daddyn Noor dasu Aunty Lisa a room da aka baiwa daddy. Sai satar kallon Aunty Lisa yake yi, amma bai amayar da abin dake ransa ba. Dik in ta motsa a kan idanunsa ne, tin bata gane ba har ta fara ganewa, dan dik in ta ɗago sai sun haɗa ido, zata ga ita yake kallo, da farko bata ɗauki hakan a komai ba, sai daga baya da ta ga kallon ya yi yawa sai ta fara jin wani tinani a ranta. Da yake wayayyiya ce, ba kauyanci da shirme a kanta, sai ta ce. “Daddy I’m feeling sleeping”…… Daddy Noor ya amsa mata da ta je ta kwanta mana. Dan ta tabbatar da zarginta ne ta yi hakan, miƙewa ta yi tare da yi masu goodnight ta fito izuwa room da aka saukesu.Tana fitowa ta ɗan yi gaba kaɗan sai ta tsaya, shiru ta yi tana tinanin meyasa GAT yake kure mata kallo haka?. Bata dawo daga duniyar tinanin ba sai ganin mutum a gabanta ta yi yana faɗin. “Meyatsayar dake a nan pretty?”. Ɗan firgita tai kafin ta ce. “Daddy me ya fito da kai?”…….. Waskewa GAT yai da cewa. “Nothing, kawai zan je room ne”……. Ta gano saboda ita ya fito, amma ta nuna bata gane ba ita ma, ta basar tare da yi mashi goodnight zata wuce. Da sauri ya ce. “Let me escord you!”. “Thank you daddy”. Cikin ladabi ta faɗa…… “Nevermind dear”. Ya faɗa a lokacin da yake isa dab ita, da hannu ya nuna mata hanya ta wuce ya rufa mata baya, dik wani takunta a kan idanunsa har suka isa room ɗin, har ciki ya rakata, a gaban bed ta tsaya tare da cewa. “Thank you daddy”. Kai kawai ya jinjina, ya gagara yin magana kuma yana jin kamar ba zai iya juyawa ya tafi ba. Ganin haka yasa ta ce. “Daddy akwai wani abin ne?”. Kai ya girgiza mata alamar a’a babu, amma ya gagara tafiya. Da ta sake tambayarsa rasa me zai ce mata yasa ya ce. “Room ɗin ya yi maku ne ko a canza maku?”. Dik wani take-takensa ta ganosa amma ta basar tare da cewa. “Ya yi sosai daddy”…….. “Ba wata damuwa?”. Ya faɗa a ɗan dake. Kai ta gyaɗa zuciyarta cike da mamakinsa. “Goodnight”. Ya faɗa tare da juyawa, da kyar ya iya daina kallonta ya nufi waje. Dab zai fita ya jugo dan ya saci kallonta, sai suka haɗa ido, ashe shi take kallo, da alama ita ma ta folawa haɗaɗɗen GAT namu, uba ga su V ai kun san ya haɗu.Still goodnight ɗin nan dai da yaki karewa shi ya sake ce mata kafin ya juya, hannu ta sanya ta toshe baki tana murmushi, dan dik ta gama ganosa. Nauyinta da yake ji yasa bai sake juyowa ba dan kada su sake haɗa ido, sai ya yi zafin namar ficewa, yana jin nauyinta sosai, musamman yadda take ce mashi daddy, yana jin kamar ba zai iya tinkararta da kalmar so ba!. Yana ficewa ta daka tsalle tare da faɗawa saman bed ɗinta, a fili ta ce. “Ooooo, ta ko’ina ya haɗu, and ga shi so silent, saukin kai and natsuwa”……. Bata san su ya gwadawa saukin kan da natsuwar ba tin da akwai abin da yake so a wajensu, amma GAT na soja ina ya ga saukin kai, tab GAT fa? Lallai sunan kawai suke ji, mutumin da ganinsa ma kawai tashin hankali ne saboda bataliyar sojojin dake take mashi baya, amma dik ya takawa sojojin birki da umartansu su koma cikin barrack su bar kwaranni a gidan dan kada su firgita mashi abin kauna, amma ban da haka ai in yana gida zaku rantse da ALLAH dikka barrack ɗin ne a gidansa, dik ta in da ka juya kaki da bindiga zaka ga suna shawagi dan tsaronsa, sojoji sama da 30 ke gadinsa idan yana gidan, idan zai fita yana tafiya dasu ya bar basu wuci 10 ba a gida dan tsaro ga gidansa da family ɗinsa, kunga kuwa babu sauki wai ciwon arne, su dai sun ga saukin tin da ƙararrawar zuciyansa ta buga a kan Aunty Lisanmu!. Haka GAT ya kwana da tinanin Lisa a ransa, while ita ma da tinaninsa ta kwana, taki faɗawa su Luna meke going, ta bar abin a ranta, washegari da sassafe suka hau shirin tafiya US, GAT bai fita office da wuri ba, ya tsaya tabbatar da cewa bakinsa sun tafi cikin aminci.A lokacin da suka fito zasu tafi, shi ma ya fito zai masu sallama, bai bari kansa ya kulle ba, sai ya ce su Luna dik su bashi phone number ɗinsu dan su dinga gaisawa, dik basu kawo komai a ransu ba, suka bashi. Da ya zo kan Lisa sai taki badawa, can ƙasa ta ce. “Daddy I don’t have phone”. Cikin zolaya ta faɗa, amma bata bari ya gane zolayarsa take yi ba. Ɗan kamewa ya yi kafin ya ce. “Please daughter, I know you have it”. Ya faɗa yana ɗaga mata gera guda…… Satar kallon daddynta dake tsaye da su V and Angelie ta yi kafin ta ce. “Faɗa mun meyasa kake son numberta?”. Ta yi maganar ta yadda babu wanda zai iya jiyota sai shi…… Shi ma satar kallon su Arya dake can gefe da jama’a ya yi, sun keɓe kansu ita da Manassa suna tsaye, dole ce tasa suka fito, da ba zasu zo ba ma!.”Please daughter, zan faɗa maki dalili ta waya”…….. “Are you sure?”. Ta faɗa tana mai da kallonta gabaɗaya a kan kyakkyawan face ɗinsa. Uhm wai wata farar hula ce ta samu damar cewa GAT da kansa are you sure, kai ku tafawa mata, da namiji ne fa da ya ji kamshin lahira, watau mata dik mulkinsa sai ka jira!.Gyaɗa mata kai ya yi alamar he’s sure, dik a takure yake, baya son hankalin su Arya ya dawo kansu, kuma baya son daddynta ita ma ya farga, gara mashi idan suka fahimci juna sai ya yi magana da daddyn nata kai tsaye, su Arya kuwa yasan za’a kai ruwa rana, dan saboda Arya ya ki sake yin wani aure tsawon shekaru, mugun kishi gareta, kuma mom ɗinsu take tayawa kishi, dik matar da ya nema yaran nan sai sun yi ƙullah-ƙullah sun watsa maganar, tin suna ƙanana sosai basa jin magana, ga iya shirya munafurci, dalilin kenan da ya sanya ya maidasu jami’ai, dan ya gano akwaisu da kaifin ƙwaƙwalwa tin da har suke iya shirya munafurci kuma ba’a iya gane su, yaga gara ya kaisu can da ya bari kwakwalwar tasu ta tafi a banza wajen shirya makirci da munafurci, yanzu baya son su sani ne, yana son idan abin ya tabbata sai dai su ga an shigo da amarya kawai!. E KAM AKWAI DARU KUWA!.Sai da ta dinga ja mashi rai kafin ta bashi number, sanna ya wuce zuwa in da su aunty luna ke tsaye kusa da daddynsu dake bankwana da su V, V sarkin son jiki tini ta rungume daddy Noor ta ɗan kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa tana yi mashi shagwaɓa, tin da ta ji shi ne daddyn heartbeat ɗinta shikenan kuma. A daidai lokacin Noor ya shigo gidan, dan daddynsa ya kirasa kan ya zo gidan GAT ya samesu daga nan zasu wuce airport. Yana goye da jakarsu na sojoji a bayansa mai ɗauke da kayansa, hannunsa rike da wayansa da na V, da zai shigo gidan sai ya ɓoye wayan V a aljihu, ya yi sallama da su Leo, Zaysh and Vash kafin ya taho, ba dan sun so ba suka rabu. Ya sha mamakin ganin V a jikin daddynsa, ɗan zuba mata ido ta kallon ƙasan ido ya yi tare da karisowa gaban daddynta, ya ƙame tare da sara mashi cikin girmamawa, sai da GAT ya jinjina mashi kai alamar ya karɓi gaisuwar kafin nan ya wuce ya nufi wajen daddyn nasa. Sai kallonsa V take yi tamkar zata cinyesa da ido har ya kariso, ta gefen da take ya tsaya, sai faman kallonta shi ma yake yi, ga shi har lokacin sleeping dress ne a jikinta, sam bai lura da su Arya ba, ita kawai yake ta faman kallo. “Good morning daddy”. Ya faɗa yana zura hannayensa a cikin aljihu. Su Aunty Lisa zasu yu magana ya yi gaggawar yi masu alamar da su yi shiru. Basu san dalilinsa na hana su yi magana ba, dan haka sai suka yi shirun. Cikin dabara ya zaro wayarta daga aljihunsa, ya matsa tamkar zai cirewa daddynsa wani abin a fuska, cikin zafin nama ya zura mata wayar tata a aljihun gajeran wandon jikinta, sannan ya ɗan shafa fuskan daddy kamar ya share mashi wani abin.Da sauri ta ɗago ta kallesa jin waya a aljihunta, kallon gefen ido ya wurga mata kafin ya matsa daga wajen ya koma jikin motocinsu, ya jingina da jikin motar yana ta binta da kallon kasar ido har suka gama sallama kowa ya shiga cikin mota. Tana ta kallonsa ta turo ɗan bakinta gaba. Dab zai shiga cikin motar ya kashe mata ido ɗaya tare da motsa lips ɗinsa ya furta so cutie a yanayin da sam sauti bai bayyana ba bare a jisa, amma ita ta gane me ya ce daga karantar motsin lips ɗinsa da ta yi. Da sauri ta mayar mashi da martanin kashe ido ɗaya kafin ta matsa da sauri wajen motar. A kusa da shi ta tsaya tare da cewa. “Aunty baku bani phone number ɗinku ba”. Su biyu ne a gidan baya, da Lisa and Lusi, sai Noor da ya shiga yanzu, Aunty Luna na ɗayar motar da daddynsu!. Ciro wayarta da ya sanya mata a aljihu ta yi tare da miƙawa Aunty Lisa kan ta sanya mata number, sai ta ɗan jingina da jikin marfin door da Noor ya rufe tin shigarsa, ta ɗan zuro kanta ta glass ne ta miƙa masu wayar.A zaton daddynta kawai number zata karɓa sai ya ja da baya yana kara ɗagawa daddy Noor hannu. Karɓar wayar Aunty Lisa ta yi ta fara shigar mata da number. Dik da sojan da zai yi driving ɗinsu yana cikin motar hakan bai hana Noor da V kurawa juna ido ba, tana jin kamar tasa hannu ta shafi lallausan kumatunsa, amma tana shakkarsa.Har suka gama sanya mata number suka miƙo mata wayar tana duniyar kallon love ɗin nata. Sau uku suna magana bata jisu ba, sai da suka ɗan taɓa hannunta, ƴar firgita ta yi tare da sanya hannu ta karɓi wayar, tana ƙoƙarin janye jikinta ta basu hanya sai jin soft lips ɗinsa ta yi ya suman lallausan kumatunta ya bata hot sumbata, da sauri ta kallesa, ya yi ƙasa da kai tamkar bashi ya yi ba.Ganin su Aunty Lisa na kallonta suna murmushi ne yasa ta yi saurin zare kanta a wajen glass ɗin, da sauri ta nufi cikin gida, murmushi ne ya cika mata baki tab, amma ta danne kar su daddy su ganta, da gudu ta shige ciki. Tana zuwa ta faɗa saman bed tare da sa hannu ta rungume in da ya sumbaceta ɗin, wani irin ƙayataccen murmushi ta saki har sai da open teeth ɗinta ya bayyana wanda ya kara fito da kyanta. Jin tashin motocinsu Noor yasa ta diro kasa da gudu ta nufi balcony, tana zuwa daidai lokacin motocin suka fita waje, kurawa motar da Noor yake ciki ido ta yi. Kamar yasan tana kallonsa ya sauke glass ɗin motar, da yatsunsa biyu ya kyasta mata tare da yi mata alamar heart da hannu kafin ya ɗaga glass ɗin. Wani irin daɗi ne ya mamayeta, da sauri ta ɗauki numbersa a wayan Angelie, ta koma cikin ɗaki ta hau ƙoƙarin shigar da shi Whatsapp ɗinta dan ta faɗa mashi ya yi kyau sosai yau cikin shigar suit da ya yi.A can waje kuma wucewa daddy ya yi, ya fita office, su Arya suka dawo ciki saboda basu da zuwa school yanzu!. ————————–🔥Mu koma baya kaɗan. A lokacin da Zaysh ya bi Ummie suka sauƙo ƙasa waje suka fita, suna fita ya sake jawota zai rungume cike da murya. Sai yaga ta yi baya da sauri tana faɗin wash. Cike da mamaki ya kalleta kafin ya ce. “Ummie lafiya?”……. “Lafiya, cikina ne yake ciwo shiyasa, a ciki ma da na rungumeka kawai karfin halice na yi, amma ina da ciwo a ciki”. Ai wani irin zabura ya yi tamkar wanda aka kwaɗawa guduma a kai, ciwo kuma ya maimaita a gigice. Murmushi ta ɗan yi kafin ta ce. “Anmun aiki ne last week a ciki, mun je asibiti ne da yayanka aka gwadani a kan rashin haihuwar nan, a nan muka samu wani kwararren likita da aka haɗa yayanka da shi, shi ne ya ce wani kuraje ne suka fito a bakin mahaifata suka hana ciki shiga, sai ya ce sai an mun aiki an cire, shi ne aka yi aka cire mun dik wata cuta, ka tayani murna, ina sa ran In Sha ALLAH zan samu lafiya har in samu ciki”. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. “In Sha ALLAH kukanki ta zo karshe, yanzu mu je in ɗauki jakata mu wuce hotel da kika sauƙa, a can zan kwana, da sassafe gobe zamu wuce, na ƙosa mu je gida in ganki da kyau”……. Cikin zolaya ta ce. “Ka zama cikakken namiji, gwarzo kuma jajirtacce, yanzu saura aure, ya batun surukar tawa?”. Hannunta ya kama suka wuce yana faɗin. “Na bar maki zaɓi”….. Zazzaro mashi ido ta yi kafin ta ce. “Kana nufin baka yi budurwa a nan ba?”….. Shiru ya ɗan yi, can ya ce. “Na dai taɓa kallon wata, ta shiga raina, kuma har yau ban sake ganinta ba, kyakkyawa ce sosai, ban san a ina take ba, dan haka manta da ita kawai”. Kai ta girgiza tare da cewa. “Ba zan manta da ita ba, zan cigaba da addu’ar ku sake haɗuwa, ba zan so ka rasa wacce ka fara jinta a ranka ba”….. Shiru ya yi bai sake magana ba har suka shiga gidansu, ya ɗauki jakarsa, ya shiga room na su Leo ya yi masu sallama, a lokacin ya iskosu suna magana da Noor, dik da basa magana da Leo har lokacin amma ya shiga dan yi masu sallama, saboda bai san me zai faru gaba ba, kun san har yanzu zazzafar gasa ce take a tsakanin mutane ukun nan, Leo, Zaysh and Unays, baa jituwa, musamman da Leo ya zama shugaban tawagarsu a yanzu, ban san sai yaushe Unays and Zaysh zasu zubar da makaman yakinsu su rungumi dahir ba. Ganin Ummie yasa Leo ya ɗaure faska yaki amsawa Zaysh, dan a tunaninsu budurwar Zaysh ne, kun san tana da kyan jiki, ga shi yanzu ya fita tsawo, ga jikinsa a murɗe, in kuka gansu zaku zaci saurayi da budurwa ne. Shi dai Noor cike da farinciki ya tarbi Ummie hannu bibbiyu, dan in baku manta ba sun saba da ita a waya, har video call suna yi, dan haka da suka ganta a zahiri ba karamin daɗi suka ji ba. Noor ya bata kyautar 5000$, kin karɓa ta yi, sai da ya sanya mata a jaka, haka da suka yi sallama da Vash ma, 5000$ ya bata, nan ma taki karɓa, sai da ya sanyawa Zaysh a aljihun jaka kan ya bata, daga nan suka yi sallama a mutunce ya kama hannunta suka bar gidan, sai tambayarsa take yi meyasa Leo bai amsa masu ba, ya ce ta kyale wannan mahaukaci ne, ɗan zafin kai ne da shegen girman kai, haka suke fama da shi.Da yake tana da hankali sai ta ce. “Anya kuwa ba wani laifi kuka yi mashi ba? Haka kawai mutum ba zai yi gaba da ku ba! Dole kun mashi ba daidai ba, faɗa mun me kuka yi mashi?”……… Dole ya bata labarin waye Leo, tin farkon haɗuwarsu a zone one har yau, ta sha mamaki sosai, sai dai kuma bata ce komai ba face ALLAH ya shirya Leo kawai. Da amin ya amsa, daga nan suka fito suka sami abin hawa, suka hau sai hotel da ta sauƙa. A nan suka kwana washegari suka hau jirgi sai Naija.A washegari suma Leo suka wuce US da yayansa…… To dikkan mazajenmu sun tafi hotu, me kuke tinani? Kai dik fa yanzu sharan fage muke yi, yanzu muke shirin afkawa cikin labarinmu gadan-gadan, dama wuyarta su gama horo su shirya zuwa Mission ne, yanzu ainahin labarin zai fara, get ready!. ———————–🔥SERAPH. A hanyar komawarta cikin school ta haɗu da Rimsha tana zuwa in da take. Da ganinta da sauri Rimsha ta zo ta riketa tana faɗin. “Madam said it was your uncle who pick you up?”…….. Kai ta jinjina alamar haka ne, sannan ta kama hannunta suka nufi class, tana son Rimsha sosai, saboda kaunar da yarinyar take nuna mata, shiyasa ita ma ta saki jiki sosai da ita, ta ɗauketa tamkar ƴar uwa!. ———————🔥Basu suka fita daga wannan ɗakin aikin nasu ba sai da rana ta faɗi, sannan suka ɗauki wayoyinsu, yadda kuka san wasu gumaka haka suke aiki, babu uhm bare umm umm ko hira a tsakaninsu, aiki kawai babu kama hannun yaro. Da suka miƙe dikkansu Lion ya fisu tsawo da faffaɗar kirji, dik da suna sanye da jacket saboda sanyi, amma shi zaku iya ganin yanayin murɗewar jikinsa shi da Champions sun fita sosai. Waje suka yo, ɗaki ɗaya suka shiga. After 1h suka fito cikin shiga iri guda, fuskokinsu sanye da nose mask, daga ta ciki ƙasa wandon jeana ne baki, sama kuma white polo t-shirt, sai suka ɗaura winter jacket zuwa gwiwa a jikinsu, sun sanya hular kayan a kansu, kafafunsu da socks baki, while sun sanya boot mai zubin waterproof haka shi ma baki. A ido dai sun yi mugun kyau sosai, amma kada a tona zuciyansu. A tare suka sauƙo ƙasa, kowanne ya shiga motarsa daban, Champion ne ya fara yin gaba lafin guru, sannan Lion ya rufa masu baya a karshe. Kai tsaye star hotel suka nufa, a wajaje daban-daban suka paka motocinsu, da yake parking space na hotel ɗin yana mugun girma, sai suka bada rata sosai a tsakanin motocin nasu. Lion ya rigasu fita ya nufi elevator, amma kafin nan sai da ya kama ɗaki a hawa na goma sannan ya nufi elevator ɗin, yau sun sanya korean face ne, dan kana ganinsu zaka ɗauka koreans ne, saboda ɓadda kama ma Lion Chenise face ya sanya, guru and champion suka sanya korean face. Kai tsaye hawa na 10 Lion ya haura, Champion yana fita daga motarsa ya wuce izuwa bakin ruwan dake gaban hotel ɗin, cikin takun jarunta da kwazo, zallar kwarewa a iya aiki. Shi kuma guru ya wuce wajen kayan kwalama, ya sayo masu chips and drinks, ya zo ya isko Champion a bakin ruwa yana zaune saman ɗaya daga cikin chair na table da aka shirya a wajen dan kara ɗaukar hankalin jama’a su ziyarci wajen. Zama suka yi tamkar wasu bayin ALLAH, cikin natsuwa suka zame nose mask dake fuskokinsu, dan dole suka hau cin chips ɗin nan ba wai dan suna so ba. Kana ganinsu ka ga abokai ƴan korea. Lokaci guda tsaro ya kewaye wajen, wasu manya-manyan jiga-jigan sojoji ne suka kewaye bakin ruwan, wasu mada karti da su, suna wani muzurai, kai ka ce zasu iya hana mala’ikan mutuwa ratsawa ya ɗauki rai. Kallon gefe-gefen ido su Champion suka yi wa jami’an, sai kuma suka haɗa ido. A lokacin da dattijon ya sako kafafunsa bakin ruwan sai da ko’ina ya yi tsit, a natse wannan dattijo ya tako ya shigo ciki. Ɗaukar drinks a glass cup Champion ya yi tare da kashewa guru ido ɗaya, kamar zai kai drinks ɗin bakinsa sai ya kauce, ya sanya lips ɗinsa ya ɗan taɓa gefen babban yatsansa dake rike da cup ɗin, take wajen ya kawo wani haske blue sau biyu a jere sai kuma ya ɗauke. Tsabar bala’i da kwarewarsu a aiki jikinsu ma da na’urorin isar da saƙo tamkar wasu saƙaguna. Saƙo ya isarwa da Lion cewa dattijon ya iso, tsaro ya yawaita a wajen, idan suka ce zasu yi waya ko typing message in an zo binciken gawa ana iya cewa a nemo masu yin waya tin bayan shigowar ministan ko a nemo masu typing, kun ga zasu shiga alamar zargi, bugu da kari idan aka kalli irin wayoyin da suke rike da shi, da sh ma ana iya amfani wajen kamasu, dan haka ba ruwansu da waya, suna da hanyar isar da saƙo a natse ba tare da barin wata alama ba. Kai ku dama ai tin da aka ce maku duniya dikka nemansu take yi kun san haɗarinsu ya zarce yadda ake zato, fin haka ma zasu aikata.Lion dake kwance a saman bed na ɗakin da ya kama ne ya samu saƙon Champion, shi ma gefen babban yatsansa ne ta kawo blue light sau biyu. A natse ya miƙe tare da nufar restroom na ɗakin. Jim kaɗan ya wuce WC side. Wani abu kamar powder ya buɗe a leda tare da fito da handkerchief fara daga aljihunsa, sai da ya gyara nose mask ɗinsa kafin ya yaga ledar wannan powder ya zuba a saman handkerchief ɗin, ya sanya hannunsa dake ɗauke da dogayen yatsu sosai, ya jujjuya powder a saman handkerchief ɗin sosai, sannan ya zubar da powder ɗin a cikin WC, ya yi flushing da ruwa. Ya ninke hankey ɗin ya tura a aljihunsa tare da fitowa, sai ya dunkule hannunsa da ya taɓa powder.Ƙasa gabaɗaya ya sauƙo, cikin takun zallar jarumta kai tsaye ya tinkari wajen. Sai shiga side ɗin jami’an dake tsaron ministar suka dakatar da shi, ɗaya daga cikinsu ne ya ce ya nuna masu card ɗinsa dake nuna cewa ya kama ɗaki a hotel ɗin nan, idan ba haka ba ba zai shiga wannan waje ba, saboda tsaron lafiyan ministar…. KUN GA AMFANIN KAMA ƊAKIN NASU KO? Shaggun kai ne, akwai basira sosai.Card na buɗe door na room da ya kama ya fitar daga aljihunsa da ɗayan hannunsa ya miƙa masu, ɗayan hannun nasa dai har yanzu a dunkule. Tsabar yarda da kansa a kwarewar aiki har da zame nose mask ɗinsa ƙasa dan ma su ga face ɗinsa da kyau. Duba card ɗin da kyau suka yi kafin su miƙa mashi kayansa, ko sannu bai ce masu na tamkar kurma, ya karɓa ya wuce cikin wajen.Yana takowa a natse cikin jarunta ya nufi jerin securitys guda shidda take takewa mai kawo abinci a wajen baya, ya ɗauko abincin ministar ne suka take mashi baya dan tsark. Babu shakka ko tsoro Lion ya tinkaresu gadan-gadan. Sai da ya iso tsakaninsu taku biyu sannan ya ɗan kauce masu hanya, kaɗan suka ɗan bugi juna da jami’in dake gefen mai ɗauke da abincin. Sorry ya yi wa jami’in tare da ware tafin hannunsa ya ɗan yi wa jami’in alamar ban hakuri, juyawa jami’in ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya dai jinjina kai alamar to. Daga nan Lion ya wuce ya nufi in da ake oder abinci. Su kuma suka wuce suka kaiwa ministar abincinsa. Kunsan waje da ake oder abinci dole akwai fili na musamman dan wanke hannu, nan Lion ya shiga ya wanke hannunsa kafin ya fito ya saka oder abinci, sannan ya koma saman chair daban nesa da su Champion ya zauna yana jira.After 5 mins sai ga masu kawo abinci sun kawo mashi abin da ya yi oder. Kan babban yatsansa ya danna, take red light ta bayyana sau biyu a wajen, red light alama ce ta zubar jini, saƙo ya turawa su Champion a kan lokacin zubar jini ya yi, dik yatsun hannunsu cike yake da na’urorin dan balai, kuma kowanne sun san saƙon da suke aikawa da shi, kai sun zarce yadda kuke tinani. Ni kaina sun zarce yadda nike tinani, makasa ne masu bala’i basira, kun ga kuwa kama waɗan nan ba abu bane ma mai yiwuwa, amma a haka wai suna cikin list na FIVE MISSION nasu Noor namu! Kuna ganin hakan zai yiwu kuwa? Su Noor zasu iya kamasu? Tsorona ALLAH tsorona rasa ko mutum ɗaya daga team ɗin su Leo, wannan Mission ɗin babbar abu ce, kai na ce yanzu wasan zai fara.Wannan saƙo na isanwa su Guru ko second goma ba’a ƙara ba ministar ya fara tari, ai sai jini daga bakinsa. Da wani irin masifaffen gudu jami’an dake tsaronsa suka yi kansa, Lion kuwa drink na kankana da yasa a kawo masa ya ɗauka ya ɗan yi sipping ya ajiye kafin ya motsa daga in da yake.Ganin jinin dake fita ta hanci da ta bakin ministar ne yasa jami’ansa suka yi gaggawar kiran ambulance. Cikin ƙasa da minti biyar sai ga ambulance ɗin ta iso, sai dai kafin lokaci ministar ya jima a lahira, dan Lion bai taɓa haran abu kuma ta rayu ba, baya saɓa saiti, salon kisansa a second goma rai ke yin halinta.Take wajen ta rikice, nan fa aka ce lallai a rufe hotel ɗin kada kowa ya fita. Miƙewa Lion ya yi tare da nufar wajen da likitocin dake tafe da ambulance ɗin suke. Kusa da wani babban likita ya tsaya, tamkar zai faɗa mashi wani abu, cikin dabara ya cire hankey dake aljihunsa ya karkaɗe masu a wajen. Kafin a ankara dik su uku dake wajen sun fara aman jini ta baki da hanci. Wucewa ya yi tare da barin hankey ɗin a wajen, wannan hankey ɗauke take da hoton tambarin da suke bari idan sun yi kisa, watau dan ma a san sune kada a sha wahalar zargin kowa ko ɓata lokaci da kuɗaɗe wajen bincike, sun sauƙaƙawa kowa!. Gaskiya waɗan nan balai ne. Dik da rufe wajen da aka ce ayi hakan bai hana Lion wucewa ya fita daga bakin ruwan ba. Champion da guru sun ma fita daga hotel ɗin, shi kuma Lion ya koma room ɗinsa da ya kama, hankalinsa a kwance ya shiga wanka, tamkar ba rayuka har huɗu ya kashe ba, ga likitoci uku, ga ministar. Taya kuke tinanin ya kashe ministar? Kada ku manta bai taɓa abincin ministar ba, bai ma je kusa da in da yake ba! Nasan kun fahimci guba ministar ya ci, to how? Nima na ce how? STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

Back to top button