Uncategorized

Maciji Ne Page 89-90 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 89/90

_______________Waziri kuwa,daskarewa yayi agurin,tsabar shiga ruɗu da yayi,sakamakon jin abinda tareeƙ ke faɗa.

Ihu ya sanya tare da faduwa agurin yana birgima da kuka.shikenan ya rasa yarsa, Zulaihat ta tafi ta barshi,ita kadaice ƴar da ya mallaka a duniya,yanzu gashi sakamakon mugun nufinsa ya rasata.kuka yake sosai cike da tarin nadama da dana sani.

Gaba daya sun ji mutuwar Zulaihat,cike da alhini suka dunguma har waziri,saidai yana karkashin kulawar dakaru,saboda karyayi yunkurin aikata wani abu.

Haka akayiwa Zulaihat wanka,tare da sallar gawarta aka kaita gidanta na gaskiya.sai muce Allah ya yafe mata kurakuranta.

,Kai tsaye daga gurin makoki,kurkuku aka wuce da waziri.

Sukuma suka dawo falon Sultan suka zauna.anan Adeeb ke sanar dasu Queen Suhaimat cewar akwai wanda ya rike fattu,ma’ana wanda ya tsinceta tun tana karama,kuma shine ya raineta harta girma.

Sannan shine mutumin da suka taimakeshi tare da Fattun.dan haka idan ansami nutsuwa yana  son  zasu tafi da fattu domin dubo halin da yake ciki.

Sultan Habeeb ne yayi gyaran murya kafin yace “ai wannan tafiya damu ya kamata ayi ta,dolene muje musaka masa da abinda yayi mana,dan kuwa ya cancanci yabo da kyautatawa agaremu”

Sultan ya faɗa cike da jinjinawa bawan Allah daya kula masa da ɗiyarsa.

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Shiru falon yayi nadan lokaci kafin Adeeb yayi gyaran murya,yana mai kallon kowa cike jinjina maganar da yake son fadi.

Baisan ya zasu dauki maganar ba.ko zasu yarda da batun aurensa dake kan fattu?duba da yanayin shekarunta.

Dan haka cikin nutsuwa ya fara magana”Abie,uncle  da sauran mutanen dake cikin dakin nan,akwai Abinda nake son sanar daku,amma bansan ta yaya zaku fahimci maganar tawaba, saidai nayi hakan ne bada wata manufa ba,saidan kare hakkin addinina.yayi shiru yana da kallon yanayin fuskokinsu,kafin ya maida kallonsa ga fattu,wacce ke jikin mahaifiyarta,ta ɗora kanta akafadun innarta,jikinta yayi mugun sanyi,dan sosai taji mutuwar Zulaihat,dan adam ba abakin komai yake ba,yanzu duba fa dazun nan Zulaihat tana raye,amma yanzu har an kaita makwancinta.Allah kasa mudace.

Haɗa ido sukayi da Adeeb wanda yake kallonta cike da kauna,yana fatan Allah yasa iyayensu su yarda da batun auren dake tsakaninsa da fattu,dan bazai iya rayuwa ahalin yanzu batare da fattu ba.

Fattu ta zama jinin jikinsa,ta zame masa,mahadin  rayuwa,kuma farin cikinsa.

“Muna jinka dana, ka fadi abinda ke cikin ranka karka damu,zamu zama masu fahimtar ka”Sultan Habeeb ya faɗa yana mai dafa kafadun Adeeb,dan yana kusa dashi ne.

Jinjina kai Adeeb yayi kafin yaci gaba da faɗin”lokacin da zamu taho kasar nan da Fatima,nayi tunanin haramcin yin tafiya da yarinya mace,wacce ba muharramarka ba,dan haka,nayi shawara da tareeƙ akan cewar,zan auri Fatima in taho da ita amatsayin matata,kuma zata ci gaba da zama matsayin matar tawa,har zuwa lokacin da iyayen ta zasu bayyana.sai In sawwake mata ta koma garesu,lokacin da aka daura auren itama kanta bata sani ba,sannan tareeƙ shine wanda ya zama waliyyinta,shina bawa sadakinta,kafin aka daura mana aure.yayi dan shiru kansa akasa  kafin yaci gaba”awancan lokacin nayi aurenne da nufin idan iyayen Fatima suka bayyana zan sawwake mata,saidai kuma ahalin da ake ciki yanzu,bazan iya rabuwa da Fatima ba,ina rokon alfarmar ku barmu, mu rayu tare muci gaba da zama matsayin ma’aurata,domin ina sonta”Adeeb ya kai karshen zancen sa cike da faduwar gaba,yana fatan Allah yasa su amince da batunsa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukansu, hakika wannan batun yayi matuƙar daɗaɗa musu rai,domin Adeeb mutum ne wanda duk wasu iyaye zasuyi fatan ya kasance mijin ga  yarsu,dan haka ta bangaren su Queen Suhaimat kam,ba wata matsala,dan kallon juna sukayi ita da mijinta cike da jin dadi,suna murmushi.

Download>>> Kwarata Complete Document

Abie ma abun yayi masa daɗi,saidai dole abawa yarinyar da iyayenta dama,idan sun amince da batun auren shikenan,sannan itama yarinyar sai sunji ta bakinta idan ta amince shikenan.

Amma ma taji daɗin maganar Adeeb sosai,domin ta jima tana fatan ace,inama  Adeeb   zai auri fattu,dan ta yaba da hankali da kuma nutsuwar fattu,saidai awancan lokacin ba damar fadin abinda ke cikin ranta.

Abie ne yayi murmushi cike da jin daɗi,kafin ya kalli Sultan Habeeb,ya fara magana”Sultan kaji abinda ɗan nata ya faɗa ko,ina fatan dai zuciyarka tana irin tunani da fatan da nakeyi, dan haka ina jiran jin ta bakinka,kaida mai dakinka”

Murmushi uncle Habeeb yayi kafin yace “ai ranka shi dade,wannan abun yayi min daɗi fiye da yadda kake tsammani,dan haka mudai ba abinda zamuce, sai Allah ya haɗa kansu,ya basu zaman lafiya, sannan ya karesu daga dukkan sharrin abin ki”ya kai zancen sa fuskarsa ɗauke da murmushi.

Wani irin sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Adeeb, Alhamdullah shikenan iyayen fattu ma sun amince da aurensu, shikenan bashi da wata matsala.

Kallonshi ya kai ga fattu,amma bai sami damar hada ido da itaba,dan kanta na duke,murmushi yayi wato  fattu irin  matan nan ne masu,kunyar ,hmmm zama ta ware ne ,dan shikam wllh zagewa zaiyi ya koyar da ita salon soyayya kala -kala,dan shi mutum ne mai son soyayya daga matarsa.

Hamdala abie yayi kafin yace “tunda yanzu mu Dukansu mun amince da wannan auren,yana da kyau muji ta bakin yarinyar,dan kar’ashiga hakkinta,tunda bada saninta akayi auren ba.dan haka Ƴata karki cuci kanki,ki sanar dani shin kin amince da wannan auren ko kuwa?”abie ya faɗa yana mai kallon fattu,da fatan Allah yasa itama tace ta amince.

Fattu kuwa kunyar duniya ta gama cika mata ciki,ji take kamar ƙasa ta tsage  ta shige ciki,yanzu ta yaya zata amsa muce cewar tana son Hamma?tab !wllh bazata iyaba.

Gaba ɗaya dakin yayi shiru,amsar fattu kawai ake jira,saidai ba alamun fattu zatace wani abu.

Ƙuri !!Adeeb ya kure fattu da ido,karfa Hulwa ta ki amincewa da aurensa?kai baya wannan tunanin, domin yasan Hulwa na sonsa sosai bazata taba kin zama dashi ba.dan haka kallonta yake danjin mezatace.

Download>>> Ingarman Namiji Complete Document

Ganin fattu ta kasa magana sai kara sunkuyar da kanta take,yasa ammi dafa kafadunta cikin murmushi tace “karki ji tsoro yata,ba wanda zaiyi miki dole,amsarki kawai ake bukata”nan ma dai shiru fattu tayi bata ce komai ba.kunya take ji sosai.

Ajiyar zuciya abie yayi kafin yace “to alamu dai sun nuna Fatima bata amince da wannan auren ba,dan haka habeebee dole kayi hakuri ka sawwake mata”abie ya faɗa yana kallon fattu dan ganin yanayinta.

Aikuwa da sauri ta ɗago kai tana zaro ido waje,cikin muryarta mai kama da shagwaba tace “a’a Abie nifa bance bana sonshi ba,dan Allah karkasa ya sakeni,na amince Nima Ina sonshi”fattu ta faɗa cike da kuruciyarta, idonta akan Adeeb.

Gaba daya saida ta basu dariya,dan dai kawai suna cikin alhinin rashin Zulaihat ne, ya hana su darawa.amma saida suka murmusa.

Ajiyar zuciya Adeeb yayi yana mai kafeta da ido,sosai yake jin tana kara shiga cikin zuciyarsa.

Koda su Sultan zasu koma Ghana,sun bukaci tafiya da fattu, domin ta gana da yan uwanta,sannan ta dan saba dasu,amma ba jimawa zatayi ba tunda da aurenta.

Adeeb ji yayi kamar ya kwalla ihu, dan yasan zai sha wahala zama ba tare da fattu ba,amma ba yadda ya iya dole ya amince,akan idan komai yayi daidai, zaizo sai su wuce Nigeria wajen baffa.

Queen suhaimat kuwa tayi hakanne,dan tana son ta gyara yarta sosai,yadda zata kara martaba agurin Adeeb.

Cikin yanayi na gajiyar jiki da zuciya,ga tarin kewar fattu da Adeeb ya fara tun yanzu,ya mike tare da cewa”Anty bari muje dan ta shirya kayanta”ya faɗa yana kallon fattu,fuska amarairaice.

Kallonsa fattu ma keyi,cike da tausayinsa,dakuma kewarsa,amma dole tabi iyayenta,dan kuwa tana bukatar jin duminsu ajikinta,sannan tana son ta san yan uwanta.

Queen suhaimat ce ta kalli fattu tace “Zara kije ki shirya kayanki maza “ta fada tana shafa kan diyar Tata cike da so da ƙauna.

Download>>> Ana Dara Ga… Complete Document

Mikewa fattu tayi,cike da kunya,tabi bayan Adeeb dan tuni yayi gaba.

Tana fita ta ganshi ya jingina bayansa da jikin bango,idanunsa alumshe.tana zuwa ta tsaya akusa dashi,tare da sanya hannu ta rike hannunsa.ahanakli ya buɗe idonsa tare da saukewa akan kyakykyawar fuskarta.baice komai ba ya rike hannun nata suka nufi part dinsa.

Suna shiga ya janyota jikinsa ya rungume tsam.ahankali yake sauke ajiyar zuciya,idanunsa alumshe.fattu ma lumshe ido tayi cike da jin tsananin so da kaunar Adeeb cikin zuciyarta.

Ahankali ya fara magana”Hulwa komai yazo ƙarshe,Allah ya bayyana mana azzalumai,mun ganesu, yanzu lokacine da nake bukatar kulawar ki  da soyayya,saidai kuma gashi zakiyi nisa dani, alokacin da nake tsananin bukatarki kusa dani,Hulwa zanyi kewarki sosai”Adeeb ya faɗa cike da jin kewar fattu sosai yana kara kankameta ajikinsa.

Cike da tausayi fattu tace”Hamma nima fa zanyi kewarka, amma ai ba dadewa zanyi ba,ina son zama tare da iyayena,dan inji dadin da ake ji idan ana tare da su.amma Hamma zanyi kewarka sosai”itama ta faɗa ahankali tana mai ƙara kwantar da kanta cikin faffadan  kirjinsa.

Sun jima ahaka,rungume da juna,Adeeb yana ta saukewa fattuhadda, wanda har bata san lokacin da ta biye masa ba itama,duk abinda yayi mata, itama shi take masa.basu rabu da juna ba har saida Adeeb ya samu nutsuwa sosai.kafin suka daure suka rabu da jikin juna,sai lokacin fattu ta fahimci ko kaya babu ajikinsu.kunya ce ta kamata,da sauri ta janyo bargo ta rufe jikinta tare da lumshe idonta.

Download>>> Matar Hariji Complete Document

Murmushi Adeeb yayi yana mai gyara mata gashin kanta daya barbaje,kafin yace “Hulwa meye kuma na  rufe ido?nifa bana son wanna kunyar taki,Please ki buɗe ido ki kalleni,kinji?”ya faɗa yana hura mata iska akan idanunta.

Cikin wani irin salon murya mai cike da nishadin soyayya tace “Hamma Ni wllh kunya nakeji,kayi ta gane min jiki”ta faɗa ahankali tana rungumeshi.

Rungumeta shima yayi cike da soyayya kafin yace “hulwata idan ban kalli jikin ba,jikin wa zan kalla?jikinki mallakina ne,shine abinda zan kalla ya debemin kewa dan Allah karki hanani kallon abinda ke sani nutsuwa” ya faɗa cikin salon sa na shagwaba yana ɗan turo baki.

Murmushi fattu tayi tana mai kara cusa kanta akirjinsa,cike da kaunarsa.

Gaba daya sun shagala da nunawa juna soyayya,sun manta da su, Sultan Habib dake jiran fattu,saida wayar Adeeb tayi kara sannan suka farga,kiran Abie ne dan haka cike da kasala ya mika hannu ya daga wayar,

“To Abie gamunan “kawai ya faɗa tare da kallon fattu yace “Hulwa su anty na jiranmu”ya fada kamar zaiyi kuka.

Da sauri fattu ta mike tana zaro ido,wllh sam ta ma manta da batun tafiya Ghana,gaba ɗaya Hamma ya mantar da ita komai da soyayyarsa.

Shagwabe fuska tayi tana mai faɗin”Hamma kaga kasa na manta da su inna suna jirana ko?”ta fada tana nufar toilet da sauri tana tafe tana bubbuga kafa,ciki da tabara.

Lumshe ido Adeeb yayi yana mai faɗin “wayyo hulwata,zaki kasheni da salonki”kafin ya bita toilet din,wanka sukayi tare sannan suka fito,da kansa ya shirya fattu,kafin ya haɗa mata kayan da yasan zata bukata,sannan suka fito.

Haka Adeeb da Hulwa suka rabu cike da kewar juna,Adeeb ji yake kamar yayi kuka.

Tunda fattu ta tafi Ghana,kullum sai su wuni suna waya da Adeeb,sosai yake nuna mata yadda yayi kewarta,ita kuwa tausayinsa duk ya gama kamata,ba abinda yake son ji da gani sama dashi.saidai tayi tararrashinsa,tun tana kunyar fada masa kalamai harta zo ta daina,take zagewa tana nuna masa soyayya.

Ba irin gatan da fattu bata ganiba,agurin iyaye da danginta,kowa sonta yake,yana riritata,gyara kuwa tunda suka zo innarta ke fama,an tsuma fattu sosai,ta yadda da kanta wataran take jin tana bukatar Adeeb akusa da ita.

Tayi kyau jikinta ya kara gogewa,kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin jin dadi da annashuwa,komai yaji ajikinta.

Download>>> Ingarman Namiji Complete Document

Satinta biyu a ghana Adeeb ya kasa daurewa ya shirya kayansa yace ya tafi Ghana.

Amagarkama kuwa,lamarin ammi ya gwabe sosai,dan kuwa zuwa yanzu bai zama lallai ka gane ta ba,wasu abubuwa take tamkar na mahaukata,tayi ta  ihu kenan tana faɗin irin abubuwan da ta aikata,ƙafarta ɗaya ta lalace sakamakon ciwon da taji,banda wasu irin kuraje da suke fito mata masu tsananin karni da doyi.haka zatayi ta ihu tana yagunin jikinta.duk wanda yazo inda take,da gyar yake iya tserewa dan kuwa hauka take sosai,tana dukan mutane.hakan yasa aka kulle gurinta,saidai atura mata abinci ta kasan kofa.

Waziri kuwa,an yanke masa hukumcin daurin shekaru arba’in agidan yari, yayi nadama sosai kullum cikin kuka yake da neman gafara.

Rashad kuwa zuwa yanzu jiki alhamdullah,dan sosai yaji sauki walwalarsa ta dawo, Amma ma hankalinta ya kwanta sosai take kula da abie,abin sai godiyar Allah.

Ranar da Adeeb ya sanar da zuwansa Ghana,ba ƙaramin farin ciki fattu tayi ba,murna sosai takeyi har saida innarta ta fahimta,shiri akayi mata na musamman,cikin shiga irin ta ya’yan sarakuna, tayi matukar kyau kamar kasace ta ka gudu,sai ƙamshi take zubawa,gashi tadanyi kina kwanin sha’awa.

Wani kayataccen daki aka sauki Adeeb,ko ina yayi fes sai ƙamshi ke tashi,an jere masa kayan ciye- ciye,amma ko ruwa ya kasa sha,burinsa kawai yayi tozali da hulwarsa.

Wani sihirtaccen kamshine ya bugi hancinsa,wanda ya sanya shi saurin ɗago kai,cikin hanzari ya mike tsaye tare da kafe fattu da lumsassun idanunsa,wadanda ke cike da tarin gajiya da bukatar fattun tare da kewarta.

Murmushi take sakar masa cike da shaukin ganinsa.tana takawa kamar wata tarwada.

Cikin wani irin salo da zaƙuwa Adeeb ya bude mata hannayensa,alamun ta taho gareshi,da sauri ta ƙaraso tare da fadawa jikinsa,shikuma ya mayar da hannunsa ya rungumeta tsammm.

Muje zuwa masu karatu.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment

More typing.

Back to top button