Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 10 Complete Novel

Matar Damisa Book 1 Complete Document

🐅 MATAR DAMUSA*🐅

(The Wife Of Tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

The writers of…

1️⃣ Ikram ko Kausar.
2️⃣ Rayuwar Siyama.
3️⃣ Baby Ogah.
4️⃣ Yayana Zan Aura.
At now
5️⃣ *MATAR* *DAMUSA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 25 to 26.

Tsaki yaja ya nufi yanda jerin kayan baccin sa yake ko sauraronta baiyi ba, haka yake taku tsindir ba kaya a jikinsa ga towel kuma a yashe a ‘kasa, Riga da wando ya zaro marasa nauyi sleeping dress milk colour ya sanya su a jikinsa ba ‘karamin kyau kayan sukayi masa ba, sai hasken sa ya Kara bayyana!
Ya feffeshe jikinsa da turare mai sanyaya zuciya, yana kammalawa ya nufi hanyar fita zai dubo mommyn sa kamar wanda aka dakatar da shi ya tsaya cak sannan ya dubi clock dake manne a jikin bango 3:30 fasa fita yayi a bayyanai yace “nasan kinyi bacci yanzu, rest in peace my Mom” juyawa yayi ya nufi gurin bed d’insa yabi ta gefen Ayush ya kwanta, jawota yayi close him ya kashe light d’in d’akin sannan yaja musu mayafi rungumarta yayi suna fuskantar juna, da haka har bacci yayi awun gaba da shi! Itama Ayush daga suma ta wuce da yin bacci,
Asubar fari anata ‘kiraye- kirayen sallah dai dain lokacin wayar Junaid ya hau ringing
Juye-juye Ayush ta Fara yi tana mur’tsika ido tana ‘ko’karin bud’e idonta taji an ‘kan’kameta juyar da kanta tayi tana fuskantar Junaid Wanda numfashin su yake gaurayuwa, a firgice ta zaro ido waje ga tsananin tsoro da ya bayyana akan fuskar ta, a hankali take janye jikin ta daga nasa har ta samu ta zame kanta tana maida numfashi tare da dafe kan kirjinta tana kallon kyakykyawar fuskarsa shi kuwa sai sharar baccin sa yake lokaci guda tasau murmushi har saida dimple d’inta ya bayyano, haka kawai take jin nutsuwa a tattare da ita..
Wayarsa ce ta sake ringing a Karo na biyu, idonta na kan wayar batada niyar picking har sai da ya kusan katsewa sannan takai hannun ta kan wayar, Doctor Hasheem taga an rubuta picking tayi ta Kara akan kunnen ta tana sauraron Wanda ya Kira “Hello Captain Junaid, mahaifiyarka tana cikin mawuyancin hali sunanka kawai take ta ambato, please kazo yanzu har saita ganka kafin mu iya magance matsalar ta….! Shuru yaji anyi ba amsa, ya sake cewa “Hello Captain Junaid kana jina kuwa…?” Katse wayar Ayush tayi ba tare da ta amsa masa ba, wani irin kuka ne mai cin rai yazo mata, tana cikin kukan taji wani ‘kiran ya sake shugowa wayar da sauri ta katse ‘kiran tayi switch up d’in wayar gaba d’aya ba tareda tasan Ina ta danna ba domin Ayush ko keypad bata iyaba balle wannan ‘katuwar waya ‘kirar iPhone 11. Bud’e wardrobe tayi ta tusa wayar cikin kayansa ta katse wayar ne saboda kar ya Kai mata naushi kumadu, tayi waje da gudu tana toshe bakinta da hannayenta kuka ne yaso ku6uce mata….
Bedroom d’insu ta nufa tana shiga ciki ta doku a saman gado, lokaci guda ta fashe da kuka tana fad’in “innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, mahaifiyata ta tafi ta barni itama wacce take kula dani tana kwance rai a hannun Allah, Allah ka taimake ni ka bawa Auntyna lafiya, idan ta mutu bansan Ina zan sa kaina ba, wayyo niii”…
Bayan ta gama kukanta mai isanta ta tashi ta shige toilet jiki ba ‘kwari Alwala tayi sannan ta tsayar da sallah tare da lafulfuli, Addu’o’i ta shiga karantowa tayi Addu’a a mahaifiyarta tare da nema mata gafarar ubangiji sannan tayiwa momin Junaid Addu’ar nema mata lafiya…

Junaid yana kwance yanaji har an shiga sallah yanaso ya tashi yayi sallah amma dai dai lokacin aka shagaltar dashi da wani mafarki mai ban tsoro da kuma firgici….!
Gashi a cikin tsakiyar ruwan da bashi da iyaka, crocodiles ne sun kai goma suka nufo shi a cikin ruwan nan, yanata gudu a cikin ruwan ya kasa isowa karshen ruwan su kuwa sunyi daf dashi suna bud’e manya-manyan bakinan su, wani ‘karamin jirgin ruwane yazo ya tsaya ta gabanshi sai dai jirgin ya d’anyi nesa da shi wata kyakykyawar Yarinya ce mai sanye da fararen kaya dogi da suman gashin ta har gadon bayanta yarinyar farace soll ta ware hannayenta biyu tana fad’in “Junaid taho, kazo gareni don ka tsira da rayuwarka….”
Tsayawa yayi cakk a cikin ruwan yana kallon kyakykyawar yarinyar dake masa magana, zazza’kar muryarta ne ya sake dukan dodon kunnensa “JUNAIDDDDD ka kula bayanka” kafin ya ankara har sun kawo masa hari, “JUNAIIDD ga wannan, ta cillo masa wata doguwar tokobi mai she’ki irinta sarakuna.
Hannunsa yakai ya cafko wu’kar kafin yakai musu sara har sun rufa mishi ‘kasin ruwa suka lumar da shi.
“Junaaiidddd” yarinyar ce ta kwalla mishi ‘Kira sannan ta ce “karka bari suyi Nasara akan ka, ka zamo jarumi na gaske, kayi ya’ki dasu kamar yanda kake a filin dagaaa…… Bata ‘karisa maganar ba taga jini duk ya malale ruwan, fashewa tayi da kuka tana fad’in “why! Why!! Why!!! Meyasa zaka bar ma’kiya suyi Nasara akan ka Junaiid..”
Ji tayi an ri’ke jirgin da sauri ta le’ka ‘kasin ruwan
Junaid ta gani ya d’ago da kansa duk ruwa ta ko Ina a jikinsa, kallon juna suka tsayayi murmushi yasau mata itama ta mayar masa da martani
Mi’ka mata hannu yayi ta ri’ko shi d’aya hannun kuma yana ri’ke da takobin nan ya haura cikin jirgin still bai daina kallonta ba itama idonta akansa
Daga bisani ya soma motsa lips d’insa zaiyi magana tayi saurin katse shi ta d’ora yatsanta akan lips d’inta “Shhhhhhh 🤫🤫 you wanted to ask me who I’m again…?”
Abun ya d’aure mishi Kai a ransa yace “wace ce wannan” kamar tasan abunda zai tambayeta kenam!
Murmushi tayi ta kanne masa ido d’aya 6atttt ta 6ace masa, a firgice ya mi’ke tsaye yana waiwaye baiga kowa ba….
Firgitt ya tashi daga baccin da yake duk gumi ya wanke masa jiki duk da A.C dake d’akin
Yana furta “Laa’ilaha ilalla, Muhammadu rasulullah S.A.W”
Agogo ya kalla 8:30 waro ido waje yayi “A’Uzubillahi Mina shaid’anin rajin, sallar Asuba has already pass” a gaggauce ya tashi ya shige toilet yayo alwala ya tsayar da sallah………..

Mommy kuwa tana kwance a gadon asibiti tana ‘kiran sunan Junaid har numfashin ta ya d’age cak oxygen aka sanya mata domin da sauran bugun zuciyar,
Likitoci sunyi ta ‘kiran wayar Junaid switch up daga farko ya shiga amma daga karshe kuma switch, bodyguards kuwa suna kawo mommy hospital suka fece Junaid yafi karfinsu zai iya hallaka su wata Rana.
Doctor Hasheem har gidan yaje dubo Junaid saidai an’ki bud’e gate, shima mai gadi yana kwance zazza6i mai zafi ya rufeshi ko kwakkwarar motsi baya iya yi, hakan yasa Doctor Hasheem juyawa yayi tunanin babu kowa a gidan, shima kanshi ya shiga damuwa ganin Doctor Fateemah a wannan halin
Yana tu’kin motor yana nazarin “shin meya faru da Junaid? Kodai ciwon shi ne ya tashi a wani gurin! Amma Ai Doctor Fatima bata shiga irin wannan tashin hankalin akan ciwon Junaid saboda ta Saba dashi tin yana yaro…”
Haka ya ringa tunani har ya shiga cikin hospital.
Wata Nurse ce ta nufi gurin da Doctor ya parker motorsa tana fad’in “Doctor baka samu Junaid bane? Zata iya rasa rayuwar ta indai bata sa Junaid a Idonta ba, bugun zuciyarta ya Fara low! Doctor please we should help her..”

Junaid bayan ya idar da sallar baccinsa ya cigaba da yi
Allah sarki duk a tunaninsa momminsa na a cikin gidan….

Itama Ayush bacci ne yayi awun gaba da ita domin jiya bata samu isashshen bacci ba, duk ta mance da wayar da tayi da Doctor akan Ana neman Junaid, amma tasan mommi tana asibiti sai datayi mata Addu’a kafin bacci ya d’auketa………

 

Click Here To Read Matar Damisa Book 1 Chapter 11 Complete Novel

Some of related Hausa Novels

 

[ads1]

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

 

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

Back to top button