Karfe A Wuta Chapter 47 By Ayshercool
Suna tafe a hanya, Nabila na ta saƙe-saƙe daban daban a cikin ranta, har suka iso dai-dai in da ta sauka wancan zuwan, ta sallami mai napep ɗin, ya din ga kallonta yana tunanin ita kuwa me za ta yi a irin wannan wurin haka ranar tsaka.”Malam lafiya, ka tafi mana” ya ce “To, tafiyar zan yi” ya ja baburinsa ya tafi.Sannu a hankali ta bi waccan hanyar da Walid ya bi da ita wancan karon, amma ta kasa gane hanyar da suka bi, balle ta gano gidan.Ta din ga nausawa cikin wurin, tana bulayi, amma ko rabin gano hanyar ba ta yi ba, gashi ta fara gajiya ga rana tana yi.Sosai take bulayi, tana sake nausawa wani wurin, amma sai ta ga ta ɓulla wani wurin daban.”Ke baiwar Allah” ta ji muryar wani a bayanta, ta waiwayo tana kallon mutumin, sanye da uniform ka security.”Me ki ke yi a nan wurin rana tsaka haka?”Ta ce “Dan Allah malam wani gida nake nema”Ya kalleta ya ce “Gida a nan kuma?”Ta ce “Eh””Gida fa ki ka ce?””Eh wani ƙaramin gida ne, rannan na zo ma amma hanya ta ɓace mini” ya girgiza kai ya ce a’a babu wani gida a nan haka, duk kamfanunnunka ne, sai gonaki, can kuma idan ki ka bu dutse ne, daji zaki shiga dan haka babu wani gida a nan”Nabila ta ce ‘Malam akwai gida a nan haka, na je gidan fa”Cikin tsawa ya ce “Ke babu wani gida a nan, ki bar wurin nan tun ban sakar miki karnuka ba, ko na kama ki na haɗaki da jami’an tsaro”Ta ƙare masa kallo ta ce “Ni zaka saka a kama, na yi maka kama da ɓarauniya ne?”Ya ce “To wa ya sani, yanzu ai ɓarayi ne kawai ɓata gari ba, kuma ba a goshi ake ganin ɓata garin ba, ta cigaba da ƙarewa wurin kallo, ba ta ga hanyar gidan ba” ta ja guntun tsaki ta juya ta fara tafiya, sai mamaki take yi, tabbas gidan a nan haka yake, amma ya aka yi haka ta faru? Haka ta koma ba tare da ta gane wurin ba.Tun daga haraba yake murmushi, kamar bakinsa zai yage, cikin ƙarfin hali ta ƙaƙalo murmushin ita ma, ta ƙarasa ta ce “Welcome home DSP” ya miƙa mata hannu, ta miƙa masa na ta suka gaisa ya ce “I really miss you barrister””Me too, ya aiki?””Aiki Alhamdilillah, daga shekranjiya zuwa yau duk ina cikin damuwa, an ce ba ki da lafiya, ba kya ɗaga wayata”Ta ce “Ka san ni ɗin ce a lallaɓa, auren zamani, yau da lafiya gobe babu, bari na je na yi wanka na ci abinci”Ya ce “Take your time, ki huta sosai zuwa yamma, zan je office ne, zan ga mutumin da aka kama, aka ce ya san in da Viper yake, kan na dawo ki bani abun da ki ka ce” dammm! Ƙirjinta ya buga, amma ta maze ta ce “Ok bye bye, sai ka dawo” ya ɗaga mata hannu ta shiga cikin gidan.Sai yanzu ta tuna tayi alƙawarin gaya masa wani abu idan ya dawo, wanda dama wayar Viper take son ba shi, wanda a yanzu ko me za’ayi mata ba zata miƙa wayar nan ba, sai ta ji ƙarshen labarin nan.Tana wanka tana zancen zuci, idan ta ce za ta yi wa Nasir bayani, ba ta da wata cikakkiyar hujja, da za ta sanya ya fuskanci in da ta dosa, kuma sai ta tonawa kanta asiri na cewa ta haɗu da Viper.***Ɓangaren ramma kuwa, tun da ta yanki Abdul da wuƙa, ba ta sake ganinsa ba, har gari ya waye, duk abun duniya ya ishe ta, wai ita ta yi wa mutum illa da wuƙa har ya zubar da jini.’sai me, ke kin manta abubuwan da ya aikata miki?’ wata zuciyar ta tambayeta.’Duk da haka, da kuma na caka masa in da zai mutu fa?” Ta tambayi kanta.Ta buɗe falon, ta fito da rigarsa sai towel da ta ɗaura, ta rufe jikinta da ɗan kwalin kayanta, ta fito falon ba kowa.Solomon ya fito zai shirya abinci a kan dining, ta ce masa “Ina kwana?”Cikin gurɓatacciyar hausarsa ya amsa mata, ta ce “Yana ina?” Yayi mata saroro ba ya jin hausa.”Kai ba ka jin hausa ne? No hausa?” Ya jinjina mata kai tare da yin murmushi.Hausa da turanci take haɗawa, tana tambayar sa ina wannan mutumin, mai gidan nan?”Turancin nata ya bashi dariya, da turanci ya ce mata bai kwana a gida ba.”Ina ya tafi?”Ya ce “Ba a tambayarsa in da ya tafi” tayi ajiyar zuciya ta kalli, kwanukan abincin ta ce “Duk kai ka ke dafa wannan? A ina ka iya girki?”Ya ce “Catering school na yi, tun ina ƙarami kuma, ina taimakawa mamana wurin yin girki, tana sayar da abinci”Ramma ta ce “Ka san koko?”Ya yi shiru yana kallonta, kwatanta masa ta shiga yi, yayi dariya ya ce “Pap” ta ce “Eh, shi ka din ga yi mini turancin ƙanana yadda zan gane”Yayi dariya ya ce “Ai normal turanci ne, kawai dai pidging ne” a dai-dai lokacin Abdul ya shigo falon, ya tarar da ramma a tsaye, tana magana da solomon tana murmushi.Wani abu ne ya tokare masa wuya, suka ɗago suna kallonsa, tana ganinsa ta haɗa fuska, ta din ga satar kallon hannunsa, da ya naɗe da bandeji.”Solomon, yaushe na zama sa’anka da zan ajiye yarinya ka din ga hira da ita? Kai ka ajiyeta? So kuna shirya yadda za ta gudu kenan?” Da sauri solomon ya girgiza kai ya ce “Ba zan taɓa cin amanarka ba sir, abu ta tambayeni nake ba ta amsa””Babu ruwanka da ita, idan tambayar ce ta tambaye ni”Ya jinjina kai. “Bar wurin nan” da sauri ya bar wurin.Ya ƙarasa dining ɗin, zai zauna ramma ta tashi. “Zauna ina zaki je? Haɗa mini abinci in karya”Cikin tsananin takaici take bin sa da ido. “Zaki haɗa mini, ko sai na turmusheki na yi breakfast ɗin da ke, ‘yar dabar ƙauye kawai, ki na ‘ya mace kina ɗaukar wuƙa”.”Ni ba ‘yar daba ba ce ba, kare kaina nayi yinƙurin yi daga mugu irinka mara imani”Ya ɗora ƙafarsa a kan dining ya ce “Na ji, haɗa mini, ko kuma wallahi na yi abun da na ce”Tuni hawaye ya cika mata ido, ta haɗa masa tea, da doyar ta tura masa gabansa, ta tashi zata tafi ya riƙota, ya ɗaga mata hannunsa na dama, wanda a nan ta yanke shi, ya ce “Da wani hannun zan ci?” Ta tsaya tana kallonsa.”Oya feed me, tun da kin riga kin yi wa hannun illa, idan ba haka ba kin san condition ɗin” babu kalar tsinuwa da zagin da ba ta yi masa a zuciyarta ba.Cike da ƙwarewa a fannin iya rashin mutunci da bariki, haka yake haɗawa da hannun ta idan ta bashi a bakin, yana wani ƙare mata kallo. Sai ƙanƙame jikinta take yi, gaba ɗaya wani iri take jin ta.Ya cinye doyar ya ce ta ƙara masa, a ranta ta ce “Shege jaki”Lomar ƙarshe, ya riƙe hannunta, da yatsunta a bakinsa, kokowar ƙwacewa take yi, amma ya riƙe su a bakinsa yana yi mata kallon ‘yan iska a cewarta. Ba ta san lokacin da ta dunƙule ɗaya hannun nata ta ɗirka masa duka a kafaɗarsa ba, ɗan dukan da babu in da ya je, ya saki yatsun yana murmushi, da ƙoƙarin tauna sauran doyar, wani irin mugun kallo take yi masa, tare da goge yatsunta a jikin rigar jikinta, ba ta fargaba ya sake tashi, ya haɗe bakinsa da nata, yana ɗura mata ragowar abincin bakinsa, cikin tsananin jarumta, take naushinsa ta ko ina, amma ya saka hannu, ya danna maƙogwaronta, babu shiri ta haɗiye, ya cikata ya nufi 3seater ya kwanta.Iya ƙarfinta ta zage ta din ga zaginsa, har da kalar wanda ba ta taɓa tunanin ta iya ba, ya lumshe idanunsa ya yi mata banza ya ce “Na san maganinki”Nasir ya ƙarewa liti kallo, sannan ya kalli sageant ɗin da suke tare ya ce “Kana nufin bai yi magana ba gaba ɗaya?””Eh sir, ya ƙi yi”Ya mayar da idonsa kan liti ya ce “Ka sauƙaƙawa kanka, ka sauƙaƙa mana aiki, ka gaya mana abun da muke tambayarka a kai. Ina Aminu Viper?””Ban san in da yake ba””Ƙarya ka ke yi, rahoto ya zo mana a kan ba shi da wasu makusanta bayan iyayensa sai ku, babu iyayensa a lissafi tun da dama sun riga sun sallama shi, ka fi kowa sanin in da Aminu viper yake”Liti ya ce “Tun da ka samu wannan rahoton, kai ka san amanar da ke tsakaninmu ba wadda zan yadda ta rushe ba ce a kan ƙaramar bazarana ba ce. Kalleni da kyau, na yi gwagwarmaya na ga rayuwa, prison ceil, na shiga kala-kala. Kuma ban taɓa zuwa gaban ɗan sanda na yi magana biyu mabanbanta ba, idan zan yi zan yi kawai. Eh ko a’a. Ko kasheni zaku yi a yanzu, ban san in da yake ba”Nasir ya kaɗa kai ya ce “Kar ka cika baki, wataƙila wannan karon, ka zo in da zaka yi magana biyu, ina Aminu Viper yake”Liti ya ziraro harshen sa, kamar yadda Al’amin ya ke yi ya ce “Allah ya ja da ran mahadi mai dogon zamani. Ambaton sunansa kawai, girma muke bashi na musamman. Abun da ba ka gane ba shi ne, shi fa mai gida ya ci dubu sai ceto wallahi. Idan ba haka ba tayaya za a saki mutumin da yake tsare, kuma a dawo ana nemansa? Gangan ma kenan”ya yi maganar yana dariya.Nasir ya ce “Babu laifi, zaka yi magana dan dole””Magana biyu, abun da liti bai taɓa yi ba kenan, ko wace irin azaba kuwa zaka gana mini, ai ƙarshen ƙwarewar taku kenan, ku yi ta ganawa mutum azaba, ya amsa laifi nasa da ba nasa ba. Idan har manyanka ba su saka na yi magana biyu ba, ba ka da wata izaya da zaka yi mini na yi magana biyu, idan kuwa na yi magana biyu ashe ba yaron Viper bane ni”.Wata inkiya Nasir yayi, kamar yadda liti ya faɗa kuwa, aka saka wasu kurata, suka din ga jibgarsa da kulki, kamar sun samu tumu, suka yi iya yin su suka yi masa lilis, sannan suka kai shi wani ɗaki mai duhu suka kulle shu.Gaba ɗaya Nabila tana ɗakinta, tana ta lissafin yadda za ta ɓullowa al’amuran nan da suka sakota a gaba.Ta idar da sallar isha’i, ta zauna a kan daddumar, sai tufka da warwara take yi, gashi ta rasa da wa zata tattauna maganar ta ji daɗi.”Tunanin me ake yi haka ne?” Ta ji muryar Nasir.Tayi ajiyar zuciya ta ce “Yaya sannu da zuwa”Ya zauna a gefen gadonta tare da cewa “Yauwwa arfa, kin ga ban dawo da wuri ba ko? Na je na ga mutumin da ki ka yi mini bayani, na saka aka kama, ta tabbata yaron Aminu Viper ne, amma riƙaƙƙen mara mutunci ne, ya ƙi magana, duk wani nau’i na tuhuma an yi masa amma ya ƙeƙashe ƙasa yaƙi magana”.Nabila ta ce “Ikon Allah, bai faɗi in za yaken ba kenan?”Ya girgiza kai ya ce “Bai faɗa ba. Amma muna nan muna trying, alamu sun nuna ya sani, ɓoyewa yake yi. Yauwwa yanzu gaya mini me ki ke son ki gaya mini lokacin bana nan”Tayi ajiyar zuciya ta ce “Nothing much, dama dai duk a kan case ɗin nan ne, na ce me zai hana ka bibiyi case ɗin daga tushe, misali daga gidansu, iyayensa mutanen kewayen da ya zauna da su”.”Me hakan zai amfana?” Yayi maganar yana kallonta.Ta ce “Kawai ji nake kamar akwai lauje a cikin naɗi, a kan sha’anin Aminu Viper, kamar abun da aka baka a kansa is not complete, something is missing, yakamata a fara samo full details na abun da ya faru”.Ya girgiza mata kai ya ce “Duk bani da isashshen lokacin yin haka, na yi ƙoƙarin yin hakan, aka ce ba shi aka sakani ba, kuma duk maganar nan da ki ke yi is a very long way, gara shortcut, idan ya zo hannu muka gama da shi, kotu zamu tura shi, a can ne aikinki yake idan ma tssya masa zaki yi” tayi murmushi ta ce “Hakan fa zai iya sawa na yi suna ko?”Yayi dariya ya ce “Ke dai kin damu da maganar yin sunan nan, gaba ɗaya kin canza, ko dai haryanzu jikin ne? Gaba ɗaya kin rage ɗokin case ɗin Vipern ma, ko akwai wani abu ne ki gaya mini ” ta girgiza kai ta ce “Babu komai”Ya ce “Are you sure?” Ta jinjina masa kai, ya tashi tsaye ya ce “Ban yarda iya abun da ki ke son gaya mini ba kenan, akwai abun da ki ke son gaya mini ki ka fasa, amma da sannu zan gano menene da kaina” Shiru kawai ta yi tana murmushi ya fita, yana ƙoƙarin fita daga falon, ya ci karo da mama, sai da ya ɗan tsorata ya ce “Mama””Me ka ke yi a ɗakinta da daddaren nan?” Tayi maganar rai a ɓace.Ya ce “Subhanallah, dan Allah mama kar ki kawo komai a ranki, muna magana ne a kan aiki… “Rufe mini baki, aikin banza da na wofi, sai ubanka ya farga ya fara yi maka terere a cikin gidan nan ko, kana zuwa ɗakinta da daddare, ka dai san ita ba zai tagayyarata ya nuna laifinta ba sai kai. Duk lokacin da na yi ƙoƙarin fahimtar da kai, irin wannan abun ba ka gani, daga dawowar ka, zaka fara sakani magana saboda wannan sheɗaniyar yarinyar ko Nasir? Ka cigaba ban ce ka fasa ba” ta nufi ɗakinta ta bar shi a tsaye a wurin saroro yana kallonta.***Ramma tana kwance ta sha kuka har ta gaji, tunanin halin da mamanta take ciki kawai take yi, ta san tana can hankalinta a tashe, tana faɗi tashin neman in da take.Ta gaji da kwanciyar, ta ɗauki ruwan da yake ajiye, a kan side bed, ta sha fiye da rabi, saboda maƙogwaronta duk ya bushe, saboda kukan da ta sha.Ta kwanta tana jiran bacci ya kwasheta, amma bacci ya gagara, sakamakon wani irin yanayi da ya din ga bijiro mata, har wani irin gumi take yi, ta tashi cikin matsananciyar damuwa, amma ta rasa takaimaimai meyakamata ta yi. Ta nemi wuri ta kwanta, ta takure, tana ta mamakin wannan wane irin abu ne haka.Abdul ne ya shigo yana fito, tayi shiru ba ta motsa ba, ya nemi wuri ya kwanta a bayanta.Ba ta yi masa tashin hankali ba, ko ƙoƙarin yin gardama ba, babban abun da ya ɓata mata rai, ya sanya ta ji tamkar ta kashe kanta, bai wuce yadda ta iya biyewa Abdul ba, ta tabatta mazinaciya!. Kuka take yi iya ƙarfinta, har da sheshsheƙa ko a jikinsa, kaɗa ƙafa kawai yake yi, daga baya ya tashi zaune yana kallonta, yayi dariya ya ce “Ba dai ke taurin kai ba, ai na san maganinki, you are very healthy and unique, zaki yi mana baƙin ciki. Ba kya buƙatar komai kan ki yi functioning lafiyayyiya ce ke, amma tsinanane taurin kai irin na ɗan ƙauye ba zai bari ki yi abun da ya dace ba”. Ya ɗago wata ƙwaya ya ce “You force me to use it on you. Idan ki ka bari muka cigaba a haka ke zaki sha wahala, dan zata iya cutar da ke, aikin gama ya riga ya gama ba wani sauran amfani da zaki yi, ni ban ga abun ƙi ko damuwa ba. Na aika a gaya wa babarki ta daina nemanki na ajiye mata ke a in da ya dace”.Cikin kuka ramma ta ce “Ba zan taɓa yafe maka ba, Allah ya isa, mazinaci mugu”.Ya ce “Mazinata dai har ke””In sha Allah ba zaka gama da duniya lafiya ba”Ko a jikinsa ya ce “Idan Allah ya nufa na gama da ita lafiyan, sai ki hana ai” ta cigaba da kuka, shi kuma ya juya ya hau bacci.Ta bi shi da kallo, ba ta tunanin ko wankan janaba yana yi, sai da tayi mai isarta, ta tashi ta yi wanka, ta saka wata jallabiya, ta leƙa fuskarsa, ta ga bacci yake yi sosai.Ta lallaɓa ta fita daga ɗakin, ta fara laluben ƙofar fita, sai dai ta nemi hanya ta rasa.Ko ina a rufe ta girgiza manyan ƙofofin, amma ko motsi ba sa yi, ta zauna a falo, ta cigaba da kuka, ta din ga jin haushin karnuka, tsoro yakamata, ta tashi ta koma bedroom ɗin, ta tarar da shi a zaune yana danna wayarsa.Ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa.”Idan ki ka kuma yinƙurin guduwa, sai na bar garin nan da ke, ba garin nan ba kawai, zan iya barin ƙasar nan da ke, babu wanda zai sake jin ɗuriyarki, gara ki shiga hankalinki”.”Ai ba zan tabattar da kai tabattacen azzalumi bane, sai ka rabani da duniyar” ya kalleta, kamar ba daga bakinta maganar ta fito ba.Duk a yawon barikinsa, babu karuwar da ta isa ta ci masa mutunci ko ta zage shi, amma a garin kwashe-kwashensa, ya kwaso ‘yar mitsitsiyar yarinya tana cin zarafin sa, yayi mata shiru, yana jin ta tana yi masa Allah ya isa ƙasa-ƙasa har da Allah ya tsine masa, amma ya shareta, tun da yau ya samu abun da yake so.Nabila tana office ɗin ta a zaune, tana ɗan danna system, sai dai hankalinta ba a kan system ɗin yake ba.Aka danna ƙarrarawar office ɗin, ta bada umarnin a shigo, matasan matan nan ne, wani masinja ya rako, ya ce “Hajiya Nabila, ga baƙi kin yi”Ta ce “To na gode sosai. Bisimillah ku zauna” suka zauna tare da gaida Nabila.A kallo ɗaya zaka ga Nabila ta yi kalar mata masu izza da jin kai, amma kuma kana zama da ita zaka ga saɓanin hakan.Suka gaisa ta ce “Jiya ina sauri zan fita, mun fara magana bamu ƙarasa ba, duk da yau ɗin ma ina son fita ne” Ɗayar ta ce “Ai mun gode ma saurarmu da ki ka yi. Lauyan gwamantin sai yawo yake yi mana da hankali, aka ce mu ɗaukar wa baban lauya mai zaman kansa kawai, mun zata abun mai sauƙi ne, ashe yafi ƙarfinmu”.Nabila ta yi musu tambayoyi, ciki har da in da aka ajiye mahaifinsu, ta yi musu alƙawarin za ta je da kanta, ta tattauna da shi, za ta bibiyi komai, kafin a shiga zaman kotu.Suka yi ta yi mata godiya, ta ce “Kar ku damu, ku bani lamabar wayar da zan iya samunku”Suka bata, ɗayar ta ce “To ƙanwata nawa ke zamu baki?”Nabila ta ce “Karku damu, ku yi mini addu’a kawai, akwai abun da na saka a gaba, Allah ya sa na yi nasara baki ɗaya, da case ɗin ku da ɗaya abun da na saka a gaba” da suka fara yi mata addu’a, sai da ta fara jin nauyinsu, dan tamkar ta yi musu bushara da mahaifinsu ya fito, suka hau yi mata hira da labarin yadda sunan mahaifin na su ya ɓaci, a cikin unguwa. Tayi ta basu ƙwarin gwiwa, da tabbacin da yardar Allah za su yi nasara.Bayan tafiyarsu, kawai ta yi wani tunani, ta ɗauki jakarta ba ta zame ko ina ba, sai wurin aikin sumayya, ba ta tarar da ita ba sai Lawisa, sai zuba iko take tana hura hanci.Nabila ta yi murmushi ta ce “Anty lawisa, Sumy ta shigo kuwa?” Ta ɗaga kai da ƙyar ta kalli Nabila ta ce “Eh””Tana ina?””Recording take yi”.Ta ce “Ok, bari na jirata a nan” tayi maganar tana ƙoƙarin zama.”No please, ba na son takura, ko zaki jirata a reception?”Nabila ta ce “Ba zan iya zaman reception ba, kujerun ba su da daɗin zama a nan zan zauna” tayi maganar tana zama a kan kujerar office ɗin.Baki buɗe lawisa take kallon Nabila, ta maze ko a jikinta, ta na danna wayarta.Ta kalli lawisa ta ce “A kan kujera kawai na zauna, ba hira na ce mu yi ba, 10-20 minutes, ai is not that much da zaki ce ba kya son takura” ta cigaba da danna wayarta.Bayan mintuna goma sha biyar, Nabila ta ji yo muryar sumayya, ta ɗauki jakarta ta fice, ba tare da ta sake kula lawisa ba.Sumayya na ganinta ta harareta, Nabila tayi murmushi ta ce “Haba masoyiyya daina hararata mana””Matsa ko na make ki, ni ki ka yi wa wulaƙanci ki ka daina ɗaga wayata””Ba haka bane ba, ayyuka ne suka yi mini yawa, daga nan ma wani wuri zan je na ce bari na biyo mu yi magana”Suka shiga wani office da babu kowa suka zauna, Sumayya ta ce “Wai ni me zaki gaya mini last week ne? Ki ka shanya ni da yake ba mutunci ne ya ishe ki ba, wayarki ma gaba ɗaya ta daina shiga, har gida na je ina nemanki”Nabila ta kaɗa kai ta ce “Aiki ne ya zo mini unexpected, mun je court ne, ina da shari’a kuma zan ga wasu clients ɗina. Dama a tsakanin lokacin nayi tunanin zan iya squeezing time ɗina, mu haɗu, kuma bai yiwu ba”.Sumayya ta ƙare mata kallo tayi murmushi ta ce “Ko dai kin sake komawa wurin Aminu Viper ba?”Nabila ta yi murmushi ta ce “Kina zargin na koma ne?””Na san hali zaki aikata ai, ina gargaɗinki a kan kasada da rayuwarki Arfa”Tayi murmushi ta ce “Ina ma zan iya jin maganarki”Sumayya ta ce “Baki yadda ba kenan?”Nabila ta ce “Mu bar maganar nan, ni wani taimako nake son ki yi mini “Sumayya ta ce “Ina jinki””Ke ce uwar neman labari, bincike nake son yi a kan honorable ma’aruf Indabo”Sumayya ta kalleta ta ce “Kamar yaya?””Kamar yadda na gaya miki, taimaka mini nake son ki yi, ki binciko mini duk wani labari da yakamata a kansa””Me ku ke so ku mayar da ni ne daga ke har shi?”Nabila ta ce “Shi wa?”Sai kuma sumayya ta farga da katoɓarar da ta kusa tafkawa.”Indabon yayi miki wani abu ne?”Sumayya ta ce “No kar ki damu, haushi ki ka bani ne, kin ce Naja’atu Bunkure, kin ce Aminu Viper yanzu kuma kin ce Indabo, Nabila me ki ke son ki zama ne?”Nabila ta tashi tsaye ta ce “Zan je wani wuri yanzu, Ina jiranki dan Allah sumayya, da tarihinsa da tarihin siyasarsa komai da komai da yakamata ina son sani a kansa”Sumayya ta ce “Wai me zaki yi da shi to?””Amfani mai muhimmancin gaske, sai anjima, ki gaida umma zan zo har gida na gaisheta, kwana biyu ba mu gaisa ba. Ina jiranki dan Allah” ta ɗauki jakarta ta yi waje.Kamar ta tafi gida, sai ta fasa ta ɗaukar mai napep, ta tafi police station ɗin da aka ce mata dattijon nan yana tsare, da ta je ta tarar an canza masa wuri, an mayar da shi sashen kula da manyan laifuffuka.ID card ɗin ta kawai ta nuna, aka bata damar ganinsa, aka fito da shi, dattijo ne amma ba tsoho cancan ba.Suka gaisa ta ce “Baba ni ce, wadda ‘ya’yanka suka same ni, a kan maganarka, yaya meyafaru?”.Nan ya ba ta labarin duk abun da ya faru, ta ce “To baba yaya sunan shi ɗan yayar matar?”Yayi shiru ya ce “Wallahi ban sani ba, yana dai zuwa gidan da yake ban daɗe da fara aiki a wurin ba”Ta ce “Yanzu ina ne gidan da ka ke aikin, sannan ina yarinyar take, dole zan ganta “Ya share hawayensa ya ce “Wallahi ban sani ba” Nabila ta tambayi ‘yan sandan suka ce sai dai ta koma can in da aka fara binciken case ɗin”Ta ɗauki bayanan da zata ɗauka, ta yi musu sallama ta tafi.***Kasancewar Abdul da wuri ya fita, solomon ma baya nan, Ramma ta din ga yawo tana neman hanyar fita tana kuka, amma ta rasa, tayi-tayi ta samu hanya ta rasa, ƙarshe ta koma falo ta zauna tana kallon Tv.Wata magazine da tarin takardu ta gani, ta ɗauka tana kallo, signing ɗin sa mai kyau, Abdul yassar ma’aruf Indabo.Shiru ta yi tana tunanin, kamar ta san sunan nan.Ƙofar falon ya saka key ya buɗe ya shigo, yayi sallama ta amsa a hankali, sai dai yayi kissing ɗin kumatunta sannan ya zauna, ta tsuke fuska tana matsawa.Ya kuma matsawa kusa da ita ya ce “Kin ci abinci kuwa?” Ta yi masa shiru.Ya ɗago mata jakar hannunsa ya ce “Yakamata ki san menene a jakar nan” taƙi kula shi.Ya buɗe jakar, ya zazzage mata, kayanta ne a ciki, da kuma wasu sababbin kayan ya sayo mata.”Babarki tana gaishe ki”Ta kalleshi idonta fal hawaye ta ce “Me ka ke nufi?””Na ce ta sallama mini ke, ba sai ta cigaba da nemanki ba”Ta sake kallonsa ta ce “Waye indabo?”
Ayshercool 08081012143
